34

379 16 4
                                    

🏨KURMAN GIDA 🏨

        Na
Rashida Usman
     (Rashma)

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

Page 34

بسم الله الرحمن الرحيم

   Alhaji Garba kuwa duk inada hankalin sa ya ke ya yi bala'in tashi  gashi bayada wani abu da zai yi amfani da shi domin ya ankarar da mutanen su,  murmushi Hassana ta yi tana miƙewa tsaye "to tsoho sai kayi tunani da kyau yanda zaku iya kare kanku domin kuwa ƙarshen ku ya zo babu ja sai kun durƙushe."

    Daga haka ta fice sai aka bar DEEDAT kaɗai ya yi shiru yana ƙare masa kallo cike da takaicin wai akan son abin duniya ka rufe idanu kayi ta shuka tsiyar ka kallon da yaga DEEDAT na yi masa shi ya ƙara ruɗar da shi murmushi ya yi sannan shima ya miƙe a mota ya same su gida suka koma dukan su babu walwala akan fuskokin su DEEDAT kuwa sake fita ya yi yayinda Hassana da Hayat suka wuce ɗakin da aka sauke su kwana biyu da zuwan su aka saka date ɗin auren Anas da Fatima inda aka saka wata ɗaya cib  a yau suke shirin kaima Ƙungiyar su Manga hari inda duk sungama bincike akan gurin da zasuyi taron saidai haɗarin gurin ya saka duk jikin wasu yin sanyi daga ciki kuwa harda Hassana wacce ta kasance itace jagoran tafiyar ba abinda takeyi sai addu'a sai Alhaji Garba da zai nuna musu hanya domin kuwa duk binciken su sun kasa gane taƙamamen hanayar mota uku suka tafi da ita tafiya mai nisan gaske sukayi sannan suka kawo wani irin fallelen daji babu komai a cikin sai wasu dogayen bishiyoyi kallon Hassana Alhaji Garba ya yi sannan ya ce "ki ɗaura wannan sarƙar a wuyanki."

    Wani murmushi ta yi sannan ta ce "haba dai tsoho ko kamanta wacece ni da zaka jefani a ramin kura ai ina ɗaura srƙar nan nasan abinda zai faru domin kuwa zankashe duk waɗanda muke tare ne dan haka ka iya bakin ka nafa san komai dangane da wannan Ƙungiyar."

    Daga haka taci gaba da tafiya shi kuma ya sauke kai ƙasa jin idanun mutane dake yawo akan sa bayanta suka bi har suka kawo wani fili wanda babu ko tsiro ɗaya na ganye waigowa ta yi ta kalle su ta ce "to kowa ya yi shiri domin kuwa ina dannawa a tsakiyar su zamu tsinci kanmu dan haka kowa ya shirya."

    Duk ƙamewa sukayi sarƙar dake hannuta taƙarema kallo sannan ta danna wani wani jan stone take ya buɗe sai ga wasu stone guda biyu fari da ja jan ta danna take komai ya bayyana sai kawai suka gansu a cikin wani fallelen gida mai azababen kyau sauran duk suna can suna kallon gidan sai jin muryar Hassana na cewa "kowa ya shirya ya riƙe addu'a."

    Sai sannan wasu suka dawo hankalin su duk ga mutane nan tsaye tsirara kowanne da ƙoƙo a hannu sa hannu Manga ta ɗaga domin ta danna wani stone dake hannu kujerar da take zaune da sauri Hassana ta danna farin stone dake jikin sarƙar hannun ta take kujerar ta kama da wuta ba ƙaramin girgiza mutane dake gurin sukayi ba domin kuwa wata irin ƙara ce marar daɗin saurare ke fita cikin murya marar daɗin saurare ake cewa "lallai ƙarshen ku ya zo dan haka kowa ya yi takansa koda kuwa an kama ku tabbas bazaku kai ba domin kuwa  jinin ku ya fara ƙonewa tare da duk abinda kuka mallaka.........."

   Wata ƙara aka saki take gurin ya gauraye da hayaƙi baka gani koda tafin hannu ka addu'a kawai ke tashi  a hankali gurin ya fara washe wa har ya gama tafiya sai gashi gidan ya ɓace ɓat sai mutanen da suka sama gasunan a zube ƙasa a some take DEEDAT ya kira ma'aikatar su yana buƙatar jirgi mai saukar ungulu cikin ƴan mintina sai gasu haka aka kwashe su akayi cikin gari dasu kafin su sauka kuwa ƴan jarida sun cika maƙil suna ɗaukar bayanai take duk wata ƙafar sadarwa ta ɗauka sai nuno su akeyi a tv yayinda gidan su Hassana ya cika da ƴan uwa sai ƴaƴan mama dake ta kuka ana basu haƙuri manyan yaranta kuwa  duk kunya ta rufe su Baba kam faɗuwa ya yi saboda hawan jinin sa da ya tashi hakan ya saka hankali mutane ƙara tashi Hassana kam gida aka wuce da ita kasancewar ita ta buƙaci haka tana kwanciya sai ga wayar Husaina tana gaya mata abinda  ke faruwa hakan ya sakata kiran Hayat dake asibiti hankali a tashe duk da gajiyar dake cin su haka suka kama hanyar Kaduna sai kusan magariba suka sauka asibiti suka wuce basu ma tafi gida  koda sukaje yana bacci hakan ya saka ta rungumi ƙannan ta sunata kuka saida Hayat ya musu magana sannan suka sassauta da misalin goma na dare ya farka lokacin Hayat ya tafi ya bar Hassana anan da baby su Jawahir akan Hassana ya sauke idanu hawaye na sauko masa miƙewa ta yi ta ƙara sa gurin sa "sannu da ƙoƙari ƴar nan ina so nasan komai domin komai a bai_bai naji shi."

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Mar 17, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

KURMAN GIDAWhere stories live. Discover now