PART 1

28 9 0
                                    

                              
*❣ƁOYAYYEN SO  ❣*



*PAGE 1_2*



_Story & Written_
           _BY_
      *_BILLY QUEEN_*
       

'''DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINK'AI, GODIYA TA TABBATA GA ALLAH MAD'AUKAKIN''' '''SARKI, TSIRA DA AMINCI SU TABBATA GA ANNABI MUHAMMAD (S A W) CIKA MAKIN ANNABAWA''' '''SHUGABAN MANZANNI.'''
 


*Bismillahr Rahmanr Raheem*


 
Babban compound ne sosai dake ɗauke da shuke shuke, da bishiyoyi masu ɗaukar hankali da zautar da yanayin mutum.

Duplex ne babba sai kyakkyawar farar mace da take zaune cikin wani matsakaicin sashi, Doguwace siririya wacce bazata wuce kimanin shekaru goma shatakwas ba a duniya.

Tanada manyan kyau gashinta baki sudul hargadon baya, irin matan da akebmasu take da masu zubin larabawa, idan ka hangeta daga nesa babu tantama zakayi zaton jinin sarauta ce, saboda yarda taci ado da kwalliya,

Wani irin  ƙayataccen murmushi ke bayyana bisa kyakykyawar fuskarta dahar yasa dimple dinta yalotsa, dagani kasan tana cikin farin ciki da annashuwa.

Yanayin garin babu rana sosai saboda lumlumi, iska ce mai sanyi take busawa cikin sararin samaniya, tana zaune hannunta riƙe da takarda da pencil tasaki ajiyar zuciya da'karfi tace "Wow.... Na gama zanawa" Ta faɗa cike da murna da gan'doki kamar wacce aka aikowa da tikitin shiga aljannah.

Tana zaune ta'kara kallon zanen dakyau azahiri tafurta "duk wannan wahalar danasha Samir ina fatan zakasoshi, wallahi gwandama yabaka sha'awa inba hakaba bazanji daɗiba".

Tamike tare da zanen rungume akirjinta tayi ajiyar zuciya ta lumshe ido cikin yananyin shauki tace "oh My Samir" bata tsaya 'bata lokaciba tatashi daga garden d'in dasauri har tana haɗawa da gudu.

***********
A saman haɗaɗden gadonsa tasameshi yayin da alarm ɗin wayarsa ke bugawa.
Tace "Samir,  ka tashi I have a surprise for you" 
Murya bata fita cikin barci yace "please kibarni nayi bacci" yana kokarin sa hannusa ta bedside ya kashe alarm ɗin,
Bayan ya kashe ya'kara jawo blanket yarufe fuskarsa dashi.

"Katashi pls da daddare kace bakajin bacci,  amma kuma da safe kace bazaka tashiba bazaiyuhba mazza katashi, ka tashi mana lokaci na tafiya" duk wannan maganar da takeyi baisa Samir yatashi ba.

Hakan yasa taje wurin window, ta yaye labulen window, hasken rana ya haska fuskarshi ya yamutsa fuskar yace "dan Allah kibari Farha,"
"Nidai katashi"
"Toh wai maiyasa zaki tasheni a bacci?" Samir yafada yana shagwaɓe fuska, tare da ɗaukar pillow ya jefeta dashi,
Kafin pillow yakai gareta ta cafe, tana mai yi masa murmushin bai samu nasarar jifanta ba.

Yamaida kansa bisa katifar yana fadin "Nidai bacci nakeji ki barni kawai nayi abuna"
Cikin haushi tasa hannu tadau'ki wayar dake kan bedside dinsa ta maida alarm din,
Tajuya zata tafi ba tare da tayi masa magana ba, yayi sauri jawota tabaya ta faɗa kan gadon.

Yakalleta cikin ido yace "Kinyi fushine bazakimin maganaba?"
Batace 'kalaba ta zun'bura baki,
Cike da mamaki ya 'daga gira yace "Dafarko kintadani, kuma yanzun saikice bazakiyi magana ba miyasa? Okay kiyi shiru kawai karkice komai, zancema boss yaturani india, kinga idan na tafi can babu wanda zai dinga tashina daga baccina, bye-bye" Yana gama faɗa yaja blanket ya sake kwanciya.

"Okay Samir katafi duk inda kakeso kaje" Farha ta faɗa tare da tashi tayi tafiyarta.

Dasauri yamike yana kiran sunanta yace "Farha! Farha! I'm going to get ready"
Bata tankamaiba tayi tafiyarta.

************
Washe gari da sassafe

"Samir! Samir! ina kashiga? Samir toh ina yatafi?" Farha ketsaye tana nazari tana duba duk wani sa'ko da lungu nagidan tana kwala Kiran sunan "Samir"

Ta dubaba ko ina bata ganshi ba hakan ya ƙara tayar mata da hankali,
Ganin abun bana wasa bane dasauri taje ta ɗauko waya tahau kiran numbern shi bata shiga,
Nandanan tafita haiyacinta tafita ɗakin da gudu tana mai kwala kiran sunan "Haseena" d'aya daga cikin  mutanen da suke cikin quarters ɗin.

"Ina kwana Madam" Haseena tagaisheta cikin girmamawa.
"Haseena shinko kinga Samir wani gun?" Farha ta tambaya aru'de batare da ta amsa gaisuwar Haseena ba.

Dasauri Haseena ta girgiza kai tace "a'a Madam ina gyara carrot ne"

"Haseena ina neman mijinane ba carrot ba"

Ganin Kabir zaiwuce tace "Kabir please kaga sameer?"

"Yes madam naganshi jiya"

Dan guntun tsaki taja tace "Ina maganar yaune kanamun maganar jiya"

"Uncle shin ko kaga samir ?" "Eh naganshi yafita da safe yana sanye  a hoodle jacket"

Dafe kirji tayi tare da ajiyar zuciya tace "Ahh, ashe jijjiga jini yaje,"
Ta'daga kai takalle yadda sukayi cirko-cirko atsaye tace "yafita motsa jiki, kuyi hakuri na kiraku duka wallahi hankalina ya tashi sosai ne inata nemansa ban ganshiba"

"Bakomai madam" sukajuya zasu tafi.

Dasauri ta dakatar dasu tace "dan Allah ku jirani ina zuwa kad'an, zannuna muku wani abune kufaɗamun ra'ayinku akai bakiɗaya, "

Dasauri tashiga fallonta sa'annan tashige wani ɗaki, Bata jima sosaiba tafito riƙe da wannan 'yar takardar datai zane, tanuna masu dauke da fara'a afuskarta ta tambayesu;
"Ya kuna ganin yaha'du? Ku faɗa mun"
Ido Haseena tazaro tace "Wow madam wannan abune mai matuƙar kyau" Takallah su Uncle da Jamil tana yabawa tace
"Toh amma wannan menene?" kabir ya cafke maganar da faɗin; "wannan ai giwa ce ko kuma doki"

Yadda Farha taga suna sharhi ta 'daga gira  takallesu tace; "doki ko kuma giwa"
Gaba daya suka haɗa baki suka ce; "eh Madam giwace ko kuma doki"

"Duk baku fahimci menene ba"
Sukaji murya daga bayansu,
Gabaki ɗaya suka juya ",
Murmushi dauke afuskarshi yace "wannan abune na musamman.

Sameer ya faɗa yana kallo fuskar Farha maicike da tarin zunzurutun farin cikin bayyanarsa, ya'daga mata gira cikin salon so  yace; "bansan miyasaba ina matuƙar ƙaunarki Farha".

"Natabbata wannan zuciyarkice kikeso kimallakamin ko?"
Dasauri Farha ta rungumeshi tana faɗin; "absolutely right"
Shima ya rungumeta yana mai shafa lallausan sumar kanta.

https://www.facebook.com/groups/3087301804823393/
*COMMENT*
  *AND*       
   VOTE

ƁOYAYYEN SOTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang