Ashfaq ya gwalo ido Yana kallon sa da yanayin tuhuma.Dad yayi gyaran murya don Allah Kar kuyimana shirme anan,har yanzu ku baku girma ba?amman in Sha Allah na San yadda zanyi da ku,sannan ya kallo Abban su Aleena ya Kara da cewa idan Abokina ya taimaka mini ya bani hadin Kai.

Abba yace "ni kuwa  wani irin taimakon ka zanyi don ni bani da abinda zan taimaka ma da shi Alhaji".

Sai Dad ya Kara juyowa ya fuskance shi da kyau,yanayin fuskar sa ta nuna cewa maganar da zasuyi ba ta wasa ba ce." Abokina dama Ina son muyi wata magana ne muhimmiya a tsakanin mu sannan bansani ba ko zaka ce nayi maka Sauri ko abin ya yi wuri! Amman kafin nace komai me ka fahimta a maganar da yarinyar nan Afnan ta fa'da"? Abba dai yayi shuru ya kasa cewa komai saboda abubuwan suna zo masa a duhu ne. " Bari dai na fito fili na gaya maka ba wani zancen 'boye'boye tsakanin mu though dai da yau muka Fara haduwa but to me Ina jin kamar mun da'de da sanin juna,Abban su Afnan ba wata magana ba ce illa Ina nema wa 'da ne Ashfaq auren 'yar ka Aleena idan ka amince mini,sannan Ina son yardar ka ta kasance Sai da zuciyar ka ta amince ma ba Wai don ganin girma na ba ko yanayi da muke ciki ba ko Kuma ka hi kunya ta ba,zan baka cikakken lokaci da zaka je kayi bincike akan iyalina da shi kan shi Ashfaq idan ka ga halaye mu ko abinda kaji ba suyi maka ba game damu,to don Allah kar kaji kunya ko ganin mutunci ka fito ka fa'di gaskiya hakan ba zai sa mutunci da ke tsakanin mu ya ragu ba.kuma Ina dai Kara baka yadda nayi maka gaggawa cikin wannan abun,ba wani abu ne yasa haka ba sai irin yadda naga Ashfaq ya ka mu da son Aleena damu dumi,abinda muke fata ke nan muga ya fito da wacce ya ke son tuntuni amman yaki yadda Sai yanzu,to ka ga kuwa ai bama yi Wasa da damar nan ba ko..?" Dad ya Kara she maganar sa da dariya,Shima Abba ya taya shi.

Mutumin kuwa an wani sunkuyar da Kai kasa ana ta faman tantankwashe yatsun hannayen(hmm ji Ashfaq kamar gaske  An zo neman aure Sai ma nayi addua kasa Abba ya baka Aleena Sai dai ka Kira Afnan hhhhh)Yana ta addua a zuciyar sa Allah yasa dai Abba ya amince da maganar neman auren yanzu ba ma Sai anne wani dogon bincike ba,shi dai boring sa dai dai Abba ya ce ya Basu Aleena in ya so daga Baya yaje suyi ta bincike da zasuyi.ohoo ya Allah kasa ya amince hmmm da kuwa directly wajen yarinyar nan zan Nufa don na nuna mata yanzu fa ita ta wa ce shafa dariya kawai za su jira.
Don Allah Abba kace ka bani ita baka san yada nake ji a zuciya ta ba,duk Sai mutanen falon suka tsaya kallon shi,shi kuwa Bai ma San maganar da yake yi a zuciyar sa ta fito fili ba😃
**********

Aleena kam da kyar da su'din goshi ta yarda ta fito daga kitchen din Sai da Amira ta rinka yi maya rantsuwar cewa ba kowa a falon Sai mom sannan ta yadda ta biyo bayanta tana 'buya kamar wata munafuka Wai ita kunya,zasu hakura sama ke ann Mom ta dakatar da su tare da tambayar su abinda take faruwa,Amira zatayi magana Sai Aleena ta riga ta da cewa babu komai Mom abu zan karbar wajen ta,to menene na 'buya a bayan ta kuma,ta 'dan kakalo murmushi bakomai Mom tare da tura Amira gaba suka hau stairs din Amira na dariya.

Bayan ta kimtsa ne Sai Kuma suka zauna sunan cigaba da Hira Amira na tsokanar ta Wai kunyar ta tayi yawa.Aleena tace" haba sis namiji ne fa ya ga nayi staining din fa namiji ma Kuma ya Ashfaq ai wallahi da kunya Wai har da cemin na girma fa!"

Hahhh ni kam soyayyar ku da ya Ashfaq tana bani sha'awa wallahi kuna burgeni sosai dukkan ku kuna son juna amman Sai kurinka wani basarwa  kamar ba ku damu da juna ba,Wai me yasa?

.." to Wai ke cewa akayi miki soyayya muke yi da shi ne? Kin wani dameni nuna burgeki to ta Ina? Yadda yake cinzali nane take burge ki ko ko me?" No sis wallahi ke na kina yi masa fa kawai dai Yana shanyewa ne saboda son da yake miki,ni abin har mamaki yake bani ni da nasan ya Ashfaq Baya daukar nonsense Sai gaji akan k......."

Aleena ta katseta da hanzari,ba abinda ke tsakanin na dashi ni Sai nake ganin kamar ma ya tsane ni ne fa! Ta fa'da fuskar ta dauke da abin tausayi. "wallahi wallahi ya Ashfaq na mutukar son ki ki yarda ko karki yarda,ni bari ma na tambaye ki tsakanin ki da Allah kin taba yin soyayya? Kinsan yadda take da me ake ji cikin ta? "Aleena ta girgiza Kai kirjinta na bugawa tana jin wani irin fa'duwar gaba.

"Da alama ke ma kin fada' cikin soyayyar ya Ashfaq ba tare da kinsani ba ko kin shirya ba,dukkan ku taurin Kai ya hanaku ku fahimci kuna son juna,amman shi yaya ya gane har ya Fara nuna miki Yana sonki amman ke kin ki ki gane haka,da ace Zaki dan bashi dama a zuciyar ki da Kuma zahiri da kin fahimci hakan sister." Ta dago ta kalle ta,yes dagaske nake sis,ta tashi ta zo gaban Aleena ta tsugunna ta rike hannun ta yanzu ki kwanta anan zan baki one hour kiyi tunani akan maganar nan da dik wasu abubuwan da suke faruwa tsakanin ku da ya Ashfaq,kin tantance ki ray raye from there you will understand.sannanvta tashi tayi hanyar fita waje zata bar dakin "Amira yanzu da gaske ya Ashfaq Yana iya sona?zai iya soyayya dani har ya aure ni?" Yes sis duk abinda Kika tambaya amsar su shine yes,sannan ta fita ta rufe kofar.Aleena ta kwanta ajikin kujeran tare da Kuma she ido har da sakon wata naunauyar ajiyar zuciya.nace hmm su Aleena an fada kogin tunani hahhh
*********
07038185042

Comment

Comment

Share vote and follow me on my wattpad.

Nagode sosai fans sakon in ku Yana iso wa gareni Kuma Ina godiya mutukar,love you all😘


SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now