EL-BASHEER 59

546 45 0
                                    

: *EL-BASHEER*



*Zanyi amfani da wannan dama wajen sake miko SAKON TA'AZIYYA GA 'YAR UWA NANA HAFSAT(MISS XOXO) na rashin MAHAIFI da tayi, ina rokon ALLAH (s.w.a) daya jikansa da RAHMA, ya GAFARTA MASA, yakai HASKE KABARIN sa, MANZON RAHAMA ya karbi BAQUNCIN SA ya ALBARKACI ABINDA YA BARI AMEEN, Dashi da dukkan 'yan uwa MUSULMAI wanda suka rigamu gidan GASKIYA, Muma idan tamu tazo ALLAH yasa muyi kyakkyawan karshe AMEEEN*



Na
Nuceeyluv😘

59

Sosai take falfala gudu har sukayi kamar zasu bar garin kano, sunyi nisa sosai kafin haj suwaiba ta gangara wata hanya inda ta ninku cikin daji, tayi tafiya medan tsawo inda ta sadata da wani tamfatsetsen gida a dokar daji, sbd yanayin dajin bazama ka dauka akwai gida mekyau haka ba, batare da bata lkci ba gate man dinsu ya bude mata kofa direct inda suke parking tayi, wasu jibga-jibgan motoci ne reras bisa layi masu sheki dakyau wannan yana wane wannan a fagen tsada da kyau, da alama haj taso makara kenan tunda har an taru ssai haka, cikin sassarfa ta kashe motar kafin ta kashe wayarta dan babu me shiga da waya ciki dan haka ta barta a motar, zagawa tayi ta bude wajen ummi tana nan yashe kamar yadda ta ajeta tun farko, sanin daukar da sukayi mata dazu bata da nauyi yasa ta tattare hannun rigarta ta dauki ummi kamar er baby nan tayi hanyar da zata sada ta ga parlon gidan.

Tinkis...tinkis.. Ta isa tsakiyar parlon rike da ummi batare da tayi mgn ba sbd ba'a sallama a wajen, da yawan mutane an hallara dama tun ana gobe meeting ake haduwa a gidan zasu kwana washe gari a tattauna sannan a watse, dan haka duk wanda yazo wajen babu fita sai an gama,

Wani shirgegen katon mutum ne a gabansu zaune a kasa babu riga baki wuluq dashi sai kaqon tumbi ya rataya wasu layoyi a wuyansa yana tsiyayo jini a wani tulu yana sha ga 'yanmata nan reras gabansa an jere kowa na fatan ace zabinsa aka dauka, Mudu Mai kano kenan shugaban su wanda jami'an tsaro ke neman sa ruwa a jallo, a cikin enmatan wasu suma bcci suke wasu ko idon su bude aka kamo su haka haj suwaiba ta aje ummi a cikin jerin su, still ummi na bcci sbd abinda aka shaqa mata sai ta zama ita ba'a raye ba ita ba matacciya ba.

Bayan ta ajen ummin taje ta shiga wani daki ta fito sai gata ta canja zuwa wasu jajayen kaya nan kusa da sauran mutanen ta zauna itama suna jiran jin ta bakin leader nasu.

******
El-basheer ganin zaman bazai gamshe shi ba ya aje komai dan komawa parlo ya ganta da gaske, maida wayar yyi kafin ya fito dakin, cikin murmushi yake takowa kasa saidai me? Yana isowa yaga babu ummi a wajen, tunani yyi ko komawa daki tayi? Maybe wata zuciyar ta bashi amsa, zama yyi kan kujera yana me rufe idonsa ummi kawai yake kallo, ji yyi ya kasa hakuri ya mike dakinta ya nufa harya dora hannun sa kan handle din kofar ya cire yana me cusa kansa cikin gashin sa tunani yake to idan yaje mezai ce? Just pretend like always zuciyar sa ta bashi amsa, dan murmushi yyi yana cije lips dinsa kadan yace 
     "maybe ma bcci take" ya fada kasa2 yana me tura kofar, wara ido el-bash yyi sbd ganin dakin wayam ba ita ba alamar ta, a hanzar ce ya tura kofar toilet yaga bata nan, ha'a? Ya furta yana me kama habarsa to kodai garden taje? Ko kitchen? Nan ya sakko da sauri kitchen ya fara dubawa ba ummi, garden ma ba ummi abu kamar wasa yana nema ya dawo babba hankalin el-bash ya fara tashi,

duk wani lungu da sako na part din ba inda be duba ba, Something bad is happen yaji zuciyar sa lkci guda ta bashi amsa, batare da tunanin komai ba El-bash ya isa ga camera yanason ganin abinda ya faru yasan dai haka nan ummi bazata fita ba besani ba, tun daga fitowar haj suwaiba da sakina a bangaren su har kawo parlon sa camera ta nuna masa, daidai sanda suke kinkimar ummi El-bash ya saki wata irin kara jikinsa na tsuma, gashin jikinsa suka mike idanun sa suka canja kala a matukar haukace ya fito adakin sa yana haye 3step na beni sbd sauri,

direct part din su haj ya nufa yau haukan karya ya kare hakuran sa yakai makura Zuciyar sa har daci take sbd bakin ciki, baram...ya tura kofar parlon nasu da kafa daidai lkcn sakina tana zaune kan kujera tana shan fruit salad hade dayin kallo tanaji a ranta ta kusa zama matar El-basheer, a gigice ta tashi sbd yadda ta ganshi kafin tayi wani yunquri El-bash ya damki wuyanta cikin karaji yace,

EL-BASHEERDonde viven las historias. Descúbrelo ahora