EPISODE 8

5 0 0
                                    

♦️AL'AJABI♦️
(DAGANI BABU TAMBAYA)

   BY
HAJARA YUSUF
(REAL HAJARA YUSUF)

Episode 8

Fati kuwa tayini tana zuba ido dan taga zuwan zainab amma shuru ba zainab ba alamarta, ta tashi taje waje tabude kofa zata leka taji anrikota, afirgice tajuya sai taga ashe jibrin ne, da  mamaki take kallonsa sannan tace ba yanzu nabarka a daki kana bacci ba?

Jibrin yace ai zanyi baccine kawai idan kina kusa dani, inajin kintashi shine nabiyoki, fati tace to ai nakulle maka kofa to ya akayi banji karar bude kofanba? Jibrin yace to waima me yafito dake kuma me zaki nema awaje.

Fati tace wllh zee ce tace yau zata kawo mana ziyara amma shuru gashi wayarta bata shiga, jibrin yace watakila wani uzurinne ya hanata zuwa shiyasa kika jita shuru, fati tace wllh ni yanzu abun yafara damuna.

Jibrin yace kamarya abun yafara damunki, zainab din karamar yarinyace bare kice zaa saceta ko kuwa.

Fati tace ba saceta akayi ba kuma ba bata sukayi ba gidanne basu ganiba, kuma wannan bashine karon farko da ake neman gidan arasa ba. Dan haka gaskiya kasamo mafita. Kanemi wani gidan kawai Wanda yake cikin mutane Dan gaskiya Bazan iya zama a wannan gidan ba.

Jibrin yayi shuru nadan wani lokaci sannan yace mushiga ciki bai tsara jiran me zatace ba yayi gaba tabisa abaya. Bayan sun zauna jibrin yace! Kinsan ni mai karamin karfine kuma wannan gidan shi kadai na mallaka, yanzu idan kikace mubar nan gidan ya kikeso nayi.

Fati tace to kasayar da gidan mana munemi wani koda dan karamine ai zaifi mana kwanciyar hankali.

OK to ba matsala ranki shidade zanyi kokarin yin hakan.

Fati tace yauwa D wllh shiyasa kullum nake kara kaunarka duk damuwa danake ciki da zaran natuno dakai sai naji duk namanta, Allah dai yabarmu tare har karshen Rayuwa.

Ameen yar Albarka.

To amma yaushe zamuje gidane kagaida kaka, Kasan akwaita da mita, sannan nima ina son ka kaini garinku naga iyayenka da danginka da sauran yan uwanka kuma....

Kafin fati takarasa magana kawai sai tashin guguwa da sukaji iska ya banke kofar parlour guguwa ya mamaye ko ina, daga nan sai suka farajin kuwwa da gurnani na muryoyi ma bambanta.

Kan kace kwabo fati taga jibrin yawuce daki yakulle kofa daga parlourn take jiyo gurnaninsa kuma yana magana da wani kalan yarenda fati bata taba jiba a rayuwarta...

Nan take tafara Addua tana kuka jikinta na rawa ta tashi ta nufi daki inda jibrin yake danta tabbatarwa kanta abunda take jiyowa.

Tana isa takama kofar tatura kawai sai taga jibrin ya rikide yadawo wata halitta mai girman gaske wanda take yawan ganinsa a mafarki. Fati tace A'uuzubil.... Kawai sai taga yayi kuwwa yayi kururuwa yayo kanta kawai saita yanke jiki tafadi kasa sumammiya.

♦️AL'AJABI♦️ (DAGANI BABU TAMBAYA) Where stories live. Discover now