EPISODE 6

6 0 0
                                    

♦️AL'AJABI ♦️
(DAGANI BABU TAMBAYA)

            BY
   HAJARA YUSUF
(Real Hajara Yusuf)

Episode 6

Ta kurma ihu tareda juyowa tayi ido hudu da wani kalan halitta, jikinsa na mutane amma fatarsa irin ta dabbobi gashi ya mamaye ko ina acikin jikin nasa, ta rumtse ido tafara karanta Addu'a a baiyane taji shuru nadan wani lokaci sannan tabude idanunta a hankali taga mutumin ya bace, tayi sauri tabude kofa takoma parlour tana kuka, ana cikin haka kawai taga wani haske kamar wal walkiya ya wuce tagabanta tayi saurin jada baya tana addu'a, tana ganin hasken mai siffar mutum yashige jikin bango yafita waje, itadai bata bar addu'a ba tanayi tana kuka har karfe ukun dare sannan bacci ya dauketa, bayan awa daya tafarjin kiraye-kirayen Sallah da sauri ta tashi tashige toilet kanta na muguwar sarawa, ta dauro Alwala tafito tafara sallah tadade tana nafilfulu kafin tayi sallar asuba ananma tayita zuba Addu'a tana rokon Allah ya yaye mata wannan damuwar, awajen bacci yasake daukarta cikin bacci taji kamar da mutum agefenta tana bude ido taga jibrin sai kawai tafashe da kuka, jibrin yayi saurin janyota jikinsa yafara rarrashinta ahaka har tayi shuru, jibrin yace meya farune daga tashinki kawai sai kuka, fati takwashe abunda yafaru gaba daya ta fada masa, shi kuma saiya nuna mata ai hakan ba komai bane kawai tayi hakuri data nuna masa itafa bazata iyaba sai yace gaskiya wannan abun dubawane kuma zan dau mataki, cikin kankanin lokaci jibrin yasa fati tamance da dukkanin damuwarta tazauna tana shan labarai awajen jibrin, taduba agogo taga karfe 8:00 daidai sannan tace wayyo Allah nifa yunwa nakeji jatarabusna sunanda take kiranshi dashi kenan wanda shine yafada mata tarika kiranshi da hakan, yace ai bakida damuwa dana shigo naga kina bacci shine nashiga nagirka mana abinci, da mamaki tace Ashe dawuri kadawo yace ay, tace amma ahanya ka kwana ba yasake cewa ay, tayi saurin daga kai takalleshi sannan tace to ya akayi ka shigo bayan nasa sakata akofar gidan, yace mutum da gidansa zaki tambayeshi ta ina yashigo ko kinmanta irin basiratane kinsan mu maza akwai basira sosai, zata sake magana yamike tareda cewa zo muje muci abincin, fati tace to amma bari nadan watsa ruwa yanzu zan dawo, yace to kiyi sauri nima yunwan nakeji, ta tashi tashige toilet, shi kuma yamike yana jira tagama tazo suci abinci, fati tayi wanka ta mulka mai ajikinta sannan tasa wani riga da wando mai kamar kayan sanyi ta feshe jikinta da turare sannan tafita tana zuwa ta iskeshi a dining table yana zaune ya zurawa kofin ruwa ido, takaraso kusa dashi sannan tace kofinne yayi maka kyau ko ruwan cikin yadanyi murmushi sannan yace ruwan cikin dai, tazauna tabude warmer abincin taga dafaffiyar shinkafa, tabude dayan taga stew maikyau sai tashin kamshi yake, atake yawunta ya tsinke yadau plate da cokali tafara serving dinsu da tazo kan stew din tanasa cokali taga miyar rabi duk hantace aranta tace dama nasan zaa rina shi wannan mutumin bashida wani abuncine sai hanta, ta dubeshi tace gashi abincin sai tashin kamshi yake Allah yasa yayi dadi inba hakaba... Ya kamota ya rungume da karfi yace inba hakaba me? Tana dariya tafara kokarin kwace kanta amma takasa, tace kasakeni inajin yunwa yace saikin fada inba hakaba me?? Tace ina nufin inba hakaba nadafa wani, ya saketa yana dariya sannan yace matsoraciya.

♦️AL'AJABI♦️ (DAGANI BABU TAMBAYA) Where stories live. Discover now