Episode 2

48 1 0
                                    


♦️AL'AJABI♦️
(DAGANI BABU TAMBAYA)
         BY
HAJARA YUSUF
REAL HAJARA YUSUF

Episode 2

Kaka tace yimaza kishiga kizauna kada kidamu indai damuwarkice kinsan bana kasa agwiwa wajen ganin na kawar miki da ita, fati tashige daki tazauna amma hankalinta yakasa kwanciya, sai sake-sake take cikin ranta, mamace tashigo da sallamarta tasamu waje tazauna, fati tace ina kwana mama, lfy lau fati tace atakaice sannan takallin fatin kana takara dacewa meya farune fati duk kinbi kin kidime ga idanunki duk akumbure ince dai ba fada kikayi da mijin nakiba, kaka tashigo dakin tacewa toke hamsatu dawa zatayi fadan inba dashi mijin nataba, dubi yadda idanunta yakada yazama jajur tsabar kuka dama saida nace kada a aura mata wannan mai zubin murucin amma akayi banza da maganata to gashi ai har anfara korota gida da sanyin safiya, kaka dai ta inda tashiga batanan take fitaba saida tayi minti biyar tana masifa sannan tace fadamin abunda yayi miki yanzu inbawa Hashimu dubu daya yaje ya gwaramin kansa da bango. Fati tayi ajiyar zuciya sannan tace kaka ba yadda kike tunani bane, banyi fada dashiba hasalima tunda mukayi aure bamu taba koda musanyar kalamai ba, kaka tayi kwafa sannan tace sannu yar na iya, to abinci ne baya baki kome, gashi kam kowa na ganin yadda kika rame nide Allah ya isa gaskiya da barinki da yunwa dayake ai gara kuyi fadan, mama dai shuru tayi tana sauraronsu batace uffan ba, fati tace kaka inada abinci kuma bana fada da mijina, kullum cikin dare nakanji sauti ban tsoro kamar gurnanin aljanu, da farko ban damuba sabida atunanina zai daina amma abun yaci tura kullum nakan kasa bacci ina cikin tashin hankali mai tsanani sabida jiya abun ya tsananta sosai, mama tace toshi mijin naki wani mataki yadauka akan hakan, Gaskiya bai saniba sabida ban fada mishiba kuma kinsan shidin matafiyine idan yadawo baya wuce kwana biyu yake komawa, kaka tace to tsuguno bai kareba kenan wadannan alamune dake nuna akwai  aljanu a gidan naku, indai wannan ne kada kidamu bari baban naku yafito sai asan abunda zaayi akore mikisu, mama tace to gashi mallam din yana shirin fita bari nayi maza nasanar dashi kafin yafita, kaka tace saurin me kike hamsatu? Sai kace ba gidan ubanta ba, kina nufin ayi a sallameta takoma kome kike nufi, mama tace aa ba haka nake nufiba, gani nayi kwanannan idan yafita baya dawowa dawuri shiyasa, to kar yaje bai dawo da wuriba yaganta kinsan bazaiji dadiba musamman da bada izinin mijinta tafito ba tunda dai kinga baya gari, kaka tafara salati tana sallallami sannan tace yanzu hamsatu Aljanu suna bibiyar yarinya kice saida izini zata taso tazo tanewa kanta mafita, nifa nafara tantamar bakece kika haifi yarnan ba, kodan sunan kanwata aka saka mata shiyasa kike gaba da ita, mama tace haba inna mezaisa nayi gaba da yarda na haifa, kaka tace yo ba gashi ba aljanu sun biyota kuma kina maganar izinin miji, mama tace to kiyi hakuri niba haka nake nufiba, amma dukda haka dai bari nafadawa mallam din, da sauri mama tafita bata tsaya jin amsarda kaka zata bayar ba, bayan wani dan lokaci sai mama tafito tace nafada masa matsalolinki amma kamar yadda nayi zato bazai dawo dawuriba dan haka kije ku gaisa, ga wannan hayakin kije dai Ku gaisadin dan ba lallene yazo yasameki ba. Kaka tace to wallahi hakan bazai yiwuba yau dinnan kam bazata komaba sai gobe idan kinje kifada masa injini yasawa ranshi cewa zai dawo gidannan yasameki dan bazaki tafi yauba.

♦️AL'AJABI♦️ (DAGANI BABU TAMBAYA) Where stories live. Discover now