EPISODE 5

5 0 0
                                    

♦️AL'AJABI ♦️
(DAGANI BABU TAMBAYA)

           BY
Hajara Yusuf
(Real Hajara Yusuf)

Episode 5

A hanya zainab tace fati kin bani mamaki kizo unguwarnan ki kwana baki nemeni ba saida zaki koma sannan zaki shigomin, fati tace kedai bari wllh zuwar bata dadi bace, zainab tace subuhanAllah  me kuma yafaru, fati takwashi dukkanin bayanan tafada mata, zainab tayi ajiyar zuciya sannan tace badan karna fadi wani abu kimin mummunar fahimta ba dana fadamiki abunda ke raina, gaban fatine ya yanke yafadi amma bata nunaba tace to kibar abunki karki fada tunda kema kince zanmiki mummunar fahimta, zainab ta daga kafada sannan tace oho kedai kika sani nidai fatana Allah ya kubutar dake daga sharrin mai sharri mutum ko aljan, fati tace Ameen amma yaushe zaki kawomin ziyara da sauri zainab ta daga kai tace ziyara kuma fafi? Fati tace ay mana laifine dankin kawomin ziyara, zainab tace aa ba laifi bane saidai ni bazan iya wahala ba, ko kin mantane karona na farko dazanje gidanki nabar gida tunsafe har azahar tayi ban samu gidanba ahaka nahakura nadawo gida agajiye, fati tace kedai baki gane kwatancen bane, zainab ta harareta sannan tace aiba ni kadai hakan yafaru daniba, su kaka da matar ya hamisu suma ai sunyita neman gidan naki basu samuba haka suka hakura suka dawo, fati tace duk Baku gane kwatancen bane shiyasa, zainab tace to shikenan Allah ya ganar damu idan mai ganuwa ne, fati tace dama akwai gidan da baya ganuwane, zainab tace sanin gaibu sai Allah, fati tace zee dan Allah gobe kizomin mana, zainab tace nifa ba inda zani, da farko dai zainab taki amincewa amma ganin yadda fati ta matsa saita amince, suna isa bakin hanya suka samu wani mai adaidaita suka tsayar dashi fati ta fada mishi inda zai kaita sukayi ciniki sannan tacewa zainab ko zaki karbi numbernsa ne tunda gobe zaki zo kinga idan muka tafi dashi yanzu zaiga gidan gobe idan kin shirya saiki kirashi ya kawoki kinga kenan baxaki sha wahala ba, zainab tace tunani maikyau suka yiwa mai adaidaita bayani yadau number yabawa zainab sukayi sallama suka wuce, suna tafiya fati tana yiwa mai adaidaita kwatance har suka isa gidan mai adaidaita yace Hajiya kice gidan naki abayan garine fati tace ay amma zaka gane hanya kam, mai adaidaita yace tabbas zan gane hanya fati tace to ngd dan Allah gobe kadau wancan kawar tawa ka kawota yace to angama haliya yaja machine nashi yayi gaba ita kuma tashige gida, ta kama aikace-aikacen gidan tagama gaba daya, taje kitchen ta daura abinci sannan tadawo parlour tazauna, karfe 6:30 daidai tadau kasko tadebo garwashin wuta ta ajiye tashiga daki tadau Jakarta tasa hannun danta dauko hayakin amma bata ganiba tayita nema harta zazzage jakar nata tana nema amma babu, ikon Allah tafada a baiyane tana mamakin ya akayi da hannunta tasa kullin hayakinda abba yabata acikin jaka amma yanzu babu, ta dade tana jimamin abun sannan ta tashi jiki asanyaye taje kitchen tagama girka abincin, sannan taci kadan takoma daki tayi Alwala tayi sallah sannan tayi addu'a ta kwanta, taji takasa bacci gashi duk sanda zatayi kira sai service ya dauke inma akwai service to bata samun wanda zata kira saidai taji akashe ko kuma not reachable, ta tashi ta janyo wayarta taduba saidai kamar kullum yauma babu service, tashiga file manager tana neman kiraar sheikh Ahmad Suleiman amma bata samu ko dayaba, bayan Complete Quran nashi take dashi, wannan ne karo na 7 da take neman abu awayarta tarasa musamman ma kiraa dazaran ta tura zai goge kanshi, tun dare baiyi sosai ba tafara fargaban mezai faru anjima, tun karfe takwas da rabi ta kwanta tana addu'a ahaka har bacci ya dauketa, cikin bacci taji ana kiran sunanta da wata iriyar murya mai ban tsoro, firgigit tayi tafarka ta duba agogo taga sha biyun dare, aka sake kiran sunanta akaro na biyu yayinda ta buga tsalle daga saman gadon tafadi kasa, sabida muryar data jiyo kamar daga karkashin gadon yake. Fhaaateee tasakeji ankirata dagudu tayi hanyar waje, tana isa bakin kofa zata bude kofar kenan taji anrikota tabaya.

♦️AL'AJABI♦️ (DAGANI BABU TAMBAYA) Where stories live. Discover now