EPISODE 1

69 4 0
                                    

♦️AL'AJABI ♦️
(DAGANI BABU TAMBAYA)
  BY
HAJARA YUSUF
REAL HAJARA YUSUF

Cikin sauri da firgici take tafiya tana waige-waige, duk jikinta na rawa ta karanto addua ta nufi kofar parlour, tana isa wajen ta tsaya cak, numfashinta na kokarin daukewa yayinda takuma jin wannan mummunan sautin dake tada mata hankali, awajen ta durkushe tana kuka tana karanto sabbin addu'oi, bayan wasu dakikai sautin karar ta dauke sai shuru ya biyo bayan hakan, da farko taje da niyyar fita tsakar gida domin taganewa kanta sautinme takeji, sai kuma tsoro ya lullubeta tayi maza ta gyara labulayen parlourn dakyau takoma cikin dakin takwanta ta lullube duk jikinta da bargo sannan ta toshe kunnuwanta ta runtse idanunta tana addu'oi azuciyarta, ahaka har barci yayi awon gaba da ita.
Washe gari tunda ta idar da sallar asuba ta shirya tsaf ta kosa gari yayi haske taje gida domin tasanarda iyayenta meke faruwa, sabida tadade tana fama da wannan matsalar bata fadawa kowaba dan atunaninta ba komai bane, saidai tunda yanzu abun ya tsananta bazata iya jurewaba dole tafadawa iyayenta damuwarta kodan a samo mata mafita, da gari yayi haske tadau mayafi ta lullube jikinta gaba daya sannan tafita takau adaidaita sahu ta nufi hanyar gida da sake-sake cikin ranta. Taje gida ta iske mama a tsakar gida tana tana shara, tayi sallama cikin sanyin murya, sannan tasa kai zata wuce da mamaki mama take kallonta sannan ta budi baki tace lafiya kuwa fati, fadar haka yayi daidai da fitowar kaka daga zaurenta, yayinda itama ta kurawa fatin ido gana jira taji amsar da zata bayar, cikin yanayin damuwa fati ta bude baki tace lafiya lau mama saidai akwai damuwa, kaka tace lallai kam akwai damuwa dan DAGANI BABU TAMBAYA.

♦️AL'AJABI♦️ (DAGANI BABU TAMBAYA) Where stories live. Discover now