LABARINSU 12

52 0 0
                                    

*LABARINSU*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*TAURARI WRITERS*
*12*
~~~
_-*I think the most beautiful thing you could ever experienced is finding someone who wants your all, even if your all is a mess*-_
***
Follow my Wattpad account 👇
https://www.wattpad.com/user/Salma_Ahmad_Isah?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
*DSS Headquarter, Maitama Evenue, Abuja*
KULIYA POV.
“Wannan shi ne file ɗin next assignment ɗinka!...”
Cewar Chidera, a sa'ilin da yake miƙa masa file ɗin aikin da ya kamata a ce ya aiwatar a gaba.
A karo na farko tun bayan fara aikinsa, Kuliya ya ji wani abu me kama da tsoro ya kama shi a kan aikin, tun da yake bai taɓa ja da baya a kan ko wani aikin da ya sa ƙafa ba, bai san tsoro ko koma ba ya kan aikinsa ba, amma a yau sai ga shi ya na jin ɗar-ɗar na karɓarsa sabon assignment. A da shi da kansa yake neman assignment ko ba'a ba shi ba, ko ya karɓi na wani ya ƙarsa, amma a yau sai ya ke jin kamar ba zai iya ba, kuma tsoron da yake ba na komai ba ne, sai na gudun kada wani abu ya zo ya faru da makusantansa.
A da sam ba shi da kalar wannan tsoron, ko da rayuwarsa zai salwantar zai a kan aiki sai ya karɓa, bai damu da kowa ba dan ba shi da kowan da ya wuce Anna, tun da ya mallaki hankalinsa be san ya raɗaɗin zafin rasa makusanci yake ba, sai bayan da Abubakar ya mutu ta dalilinsa.
Kamar me shirin karɓar zunubansa haka ya kai hannu ya karɓi file ɗin, kafaɗarsa ta dama ya ɗaga sannan ya kalli Chideran da ya fara masa bayani a kan aikin.
“Case ne a kan kisa da kuma fyaɗen da aka ma wata yarinya a Life Camp”
_“Dama na san wata rana dole za ku so ku san waye mahaifinku... A zahirin gaskiya Aliyu da Zaid ban san mahaifinku ba. An gayyace ni zuwa wurin bikin wata ƙawarmu ne.... Kuma a wurin aka zuba min abun gusar da hayyaci a cikin abun shana. Har aka samu wani ya haike min!. Kuma a lokacin ne na samu cikinku!...”_
Kalaman mahaifiyarsu kenan garesu, a ranar da Zaid ya tambayeta labarin mahafinsu, kuma tun bayan lokacin ya tsani wannan kalmar ta fyaɗe, a duk sanda zai jita, sai ya ji kamar an watsa masa maɗaci a kan zuciyarsa, ko da wasa ba ya son sauraron kalmar.
Don shi ko aiki aka ba shi wanda ya danganci fyaɗe hukuncin da yakewa me laifin ma da ban ne. A hankali ya gyaɗa kansa ya ba buɗe file ɗin.
*
Sharon, Kamis, Sani, Mubarak da Symon su ne zaune kan kujeru, yayin da suka kasa kunne suna sauraronsa.
“...Gaba ɗaya akwai tarin bayanai game da kisan, akwai hujjojin da 'yan sanda suka samo a wurin da aka yi kisan. Na farko, wuƙar da aka yi amfani da ita wurin kisan. Wuƙar na ɗauke da jinin victim ɗin, sannan akwai shatin yatsun me lefin a jiki. Hujja ta biyu kuma ita ce; autopsy report, bayanan da likitan da ya bincika gawar ya bayar sune; farko sai da aka mata...”
Kamar kullum, yau ma sai da ya tauna maganar kafin ya faɗeta, kallonsu ya yi gaba ɗaya, amma su ba shi suke kallo ba, ko wanne a cikinsu da takardar da yake dubawa, wadda ta ƙunshi bayanan case ɗin, hakan ya ba shi damar yin gyaran murya, ya na ɗaga kafaɗarsa ta dama, sannan ya ci gaba.
“...Fyaɗe, kafin ya kasheta, kamar yanda na faɗa muku tun farko, ya yi amfani da wuƙa ne wurin yanka wuyanta, sannan kuma rahoton ya bayyana cewa makashin ba hagume ne, ma'ana yana amfani da hannun hagu!”
“Amma ni sai nake ganin... Kamar waɗanan hujjojjin ba su isa susa mu gano wanda ake zargi ba, muna buƙatar ƙarin wasu hujjojjin”
Cewar Sani, bayan da Kuliyan ya gam zayyano musu kaf bayanan cikin file ɗin. A hankali Kuliya ya gyaɗa kansa ya na kurɓar coffen dake hannunsa.
“Kai ma ka ce wani abu”
“So what are we gonna do next?”
Sharon ta tambaya.
“Zan yi magan da Ram, sannan zan yi magan da ɗansandan da ya kula da case ɗin kafin ya zo nan, na san za'a iya samun wasu bayanan”
Kuliya ya bata amsa.
“Amma ya kamata mu yi magana da iyayen yarinyar” Cewar Kamis yana aje takardar hannunsa.
“Ƙwarai wannan ma babbar makamace, wata ƙila za su iya bamu wani hint”
“But babu wani wanda zargi ya hau kansa?, i mean ko da ɗaya daga cikin mutanen gidansu ita yarinyar ne?”
Cewar Symon.
“A bayanan cikin file ɗin dai babu, amma idan muka nitsa cikin binciken ba za mu rasa ba”
Kuliya ya amsa masa yana sosa kansa.
“Gaskiya makashin nan ba shi da imani, kalli yanda aka yanka wuyan yarinyar, kuma a profile ɗin yarinyar na ga ba ta wuci 18 years ba” Cewar Mubarak, sanda yake kallon hotunan da aka wa gawar.
Sai da Kuliya ya ɗan yi jim, tunowa da ita da ya yi, ita ɗin da a yanzu zai iya kira da matarsa, ita ɗin da zai iya cewa zuciyarsa ta raurawa a kanta, ita ɗin da ta zama sanadiyyar haɗuwarsa da wata wanda yake ganin kamar ta jiɓanci rayuwarsa ta baya.
Haka dai suka yi ta tattaunawa a kan case ɗin, kafin kowa ya tashi ya fita, ya rage daga Kuliya sai Sharon, wadda suke ƙara tattaunawa kan yanda za su ɓullowa batun.
“Ya kwanan amarya?”
Sharon ɗin ta faɗi tana harhaɗa kan papers ɗin da suka barbaza, sai da Kuliya ya ɗan kalleta, sannan ya amsa mata da.
“Tana lafiya”
Sharon ta ɗan yi murmushi tana rufe file ɗin dabta gama haɗawa.
“Na san yarinyar, ba ta da wasu shekaru masu yawa, na san ba lalle ma a ce tasan menene ɗaukar nauyin miji da na gida ba... Amma idan ka daure, ka yi haƙuri komai zai zo maka da sauƙi, ka yi ta ɗorata a kan hanya, za ta dawo dai-dai. hmmm?”
Sai ya aje mug ɗin hannunsa ya na gyaɗa mata kai, kaf abokansa ita ce mutum ta biyu da yake iya sauraron maganarta.
“Thanks for the advice”
“Not at all”
Ta faɗi da wani guntun murmushi a kan fuskarta, ta haɗa abin da za ta haɗa ta fice daga office ɗin.
Kuliya ya shafo kansa yana fitar da iska daga bakisa. Da alama wannan assignment ɗin zafin kai kawai zai ƙara masa, bayan wani ɗumin da kan nasa ya ɗauka.
*Unguwar Madalla, Suleja, Niger state*
RABI'A POV.
“To yanzu Rabi gurin wa zan tura su?”
Cewar Antu Saratu, bayan da saurayinta Fu'ad ya zo zance ya shaida mata da ya kamata ta sa masa ranar da zai turo magabatansa. Yayin da suke zaune ne a ɗakinsu, kan katifar Anti Saratun.
Rabi ta ɗan yi shiru tana nazari, can kuma tace.
“To me zai hana ki turasu wurin kawu Habu, ki ga shi ne kawai wanda za'a iya nemar aurenki a wurinsa”
“Kuma fa haka ne, kai amma na ji daɗin shawarar nan taki Rabi... Sam ni tunanin hakan bai zo cikin raina ba”
Rabi ta ɗan yi murmushi. Ta na so ta ga an yi wannan auren, ko ita ba ta fita daga rayuwar ƙuncin gidansu ba, wata ƙila ita anti saratun za ta fita daga rayuwar ƙuncin gudan.
Kusan sati biyu kenan da tafiyar Mama, duk wanda ya tambayesu ina Mama sai Habiba ta yi wuff ta ce wai ta tafi ziyara.
Hira suka ɗan yi kafin Rabi'an ta fara jin bacci, hakan yasa ta yiwa Anti Saratu sallama ta koma kan tata katifar ta shimfiɗe, sai dai kafin ta gama addu'ar baccin da ta saba yi, waɗanan fuskokin guda biyu masu kama da tata da kuma ta Umma suka gifta ta cikin idonta.
Hakan yasa ta buɗe idon nata, tana shafa addu'ar da ta ida, ba ta san lokacin da wani guntun murmushi ya suɓuce mata ba, tunawa da ta yi da shi, wannan innocent voice ɗin, waɗanan drunken eyes ɗin, wannan nitsataiyar tafiyar da ma yanda yake ɗaga kafaɗarsa bayan shuɗewar duk wani ƙaramin lokaci.
Wai me kike shirin yi ne Rabi?, kar fa ki zarme da yawa, don ya na kama da ke ya sa kar ya sa ki dauka cewar shi sa'an ki ne!, Raj sam ba sa'an ki ba ne, kamar da kuke ba ita za ta sa ku dace ba, dacewa da ban kamanni ma da ban!. Yayan da kika samu shi ne dai-dai ke, kar kuma ki shiga shirin ɓallowa kanki ruwa!.
Wani yanki na zuciyarta ya ba ta wannan shawarar, kuma ta yarda da shi ɗari bisa ɗari, don da alama zuciyar tata na shirin sakata ɗaukar dala ba gammo, don kuwa sam babu haɗin zuma da maɗaci, Raja ba sa'anta ba ne ita ma ta sani. Saboda haka duk wani abu da za ta bari ya shiga tsakaninsu yaudarar kanta za ta yi.
RAJA POV.
Cike da mamaki suke kallon ire-iren muggan makaman da mutumin da Alhaji Bala ya haɗusu da shi ya turo musu wai su zaɓi wanda suke so, daga Raja har Rhoda babu wanda bai saba riƙe makami ba, amma kalar waɗanan makaman ko jami'an tsaron Nigeria ba su da irinsu.
“Zaid this thing is getting worst!”
Rhoda ta faɗi, mamaki kwance a kan fuskarta.
Raja be iya amsa mata ba, kansa kawai yake girgiza wa. Mamakin abun da yake gani ya hana shi cewa komai.
“Raja we have to do something about this”
Yanzunma kansa ya girgiza mata yana ɗaga kafaɗa, shi ji yake kamar an sakawa bak8nsa wani shirgegen kwaɗo an kulle.
Lalle Alhaji Bala ya wuce yanda suke tsammani, abun nasa ma ya wuce hankali, ko da wasa ba su taɓa tunanin cewa ya kai haka ƙarfi a harkar tasa ba.
Kallon hotunan kawai yake yana ƙarawa, ya rasa wanne daga cikin hotunan zai nazarta.
Ture ko wani tunani ya yi, dan yasan zuwa yanzu lokacin tashinsu ya kusa, hakan ta sa ya rufe laptop ɗin, dan ba ya so ko da wasa ya yi missing ganinta.
Rhoda ta bi shi da kallo a sanda ya miƙe tsaye ya nufi ƙofa.
“Wait for me Abeg”
Rhodan ta faɗi tana miƙewa, tare da bin bayansa, dan so take ta je ta yi neman tsokanar da ta saba.
*Brickhall school, Kaura District, Abuja.*
MISHAL POV.
A karo na barkatai, Rabi'a ta kuma ɗaga jerseyn da Mishal ta kawo mata, ta juya rigar a hannunta ya fi sau abun da ya fi.
Yau gaba ɗaya ba su haɗu ba sai yanzu, kasancewar yau ita Rabin har ɓangaren hostel ɗin mata ta je yin shara, kasantuwar makarantar a haɗe take da boding. Wadda ta saba yi ma 'yan hostel ɗin shara ce ba ta nan, hakan yasa aka turata ta je ta yi.
Kuma ta na gama sharar hostel ɗin ta ɗora da ta makarantar, hakan ta sa ba su haɗu ba sai yanzu da aka tashi, ba wai iyaka jerseyn ta kawo mata ba, akwai wani baƙin baby hijab, da leggins, da kuma short ɗin jersyn, sai wani farin canvas.
Mishal ɗin ta faɗawa Rabi'a cewa Akinta ne ya siya mata mata kayan saboda da farko cewa ta yi ɓangaren ball za ta zaɓa a sport, amma bayan ta ga cewa ana koyar da kungu fu a makarantar sai ta sauya ra'ayi, hakan yasa ta aje kayan, yanzu kuma da ta ji cewar yayarta na son buga ball sai ta kawo mata su.
“Ki na ji ko?, gobe ki saka su, ina san na ga irin wasan da kike”
Cewar Mishal tana zuge zip ɗin jakarta, Rabi ta kalleta da mamaki.
“Na sa kuma?, da wa zan buga ball ɗin?”
Mishal ta yi dariya tana saɓa backpack ɗinta a baya.
“Akwai matan da suke buga ball a makarantar nan... Da su nake so ku buga”
Ido waje Rabi take duban Mishal.
“Ni zan buga wasa da su?”
Ta tambaya tana hango waɗanan marasa mutuncin 'yan matan dake yawan buga ball a filin.
“Seesee kin iya ball ko ba ki iya ba?”
Mishal ta tambaya. Rabi'a ta sunkuyar da kanta tana faɗin.
“Na faɗa miki cewar I can't recall when last na buga ball, amma na san na iya, kuma a yanzu ma zan iya buga ball”
“To me yasa kike jin tsoro?, na san tsoron su Precious kike, kisa a ranki cewar su ba su isa komai ba, kuna na san cewa kina ganin saboda ke ba 'yar makaranta ba ce shi ya sa ba za ki iya bugawa da su ba, ki barni da wannan, nasan yanda zan yi da su”
Rabi'a ta ci gaba da kallonta, kafin ta rungume ƙanwar tata da take jinta kamar ƙanwarta ta jini.
“Na gode sosai ƙanwata”
“Don't mention it Seesee”
Daga haka suka yi sallama, Rabi'a ta fita daga makarantar, kasancewar har zuwa lokacin Kuliya be zo ɗaukan Mishal ba, ya sa ta samu bencin me gadin makarnatar taeu ta zauna kusa da shi, za ta iya cewa for the very first ita ce yau ke jiran a zo a ɗauketa, kullum kafin ta fito Malam Ali ya riga ya zo, shi ma Kuliyan ya mata hakan na kwana ukun da suka wuce, amma yau sai ga shi ya makara.
Kamar yanda aka saba Rabi'a na fita ta haɗu da shi, to yau ba ma shi kaɗai ba ne, ya na tare da Rhoda, wadda zuwa yanzu suka ɗinke ita da Rabi'a, don sosai suke hira idan sun haɗu.
“Menene wannan Ammata?”
Raja ya tambaya a sanda suka jera su ukun suna tafiya, Rabi ta kalli ledar hannunta da yake magana a kai.
“Jersyna ce a ciki”
“Kin iya ball ne?”
Rhoda ta tambaya ido waje, Rabi ta gyaɗa mata kai.
“Wow?, da ma a arewa akwai matan da suka iya ball?”
Raja ya ranƙwashi kanta, ta yi sauri ta dafe tana sosa wurin.
“Me kika mayar da matan arewan ne?, ko da yake ai ke ma a arewan aka haifeki, don haka ba ki isa kin ce wani abu a kansu ba”
“To ai ban ce komai ba... Kawai dai ina mamakin abun ne”
“Wannan kuma ke kika jiyo”
Rabi ta yi dariya kamar yanda ta saba musu idan suna faɗa irin haka.
“Wani club kike?”
Raja ya tambaya.
“Bacerlona”
“Aaa!, ki ce ke tamu ce, mu 'yan PSG ne (Paris Saint Germain)” Cewar Rhoda.
Daga haka kuma sai hirar tasu ta koma ta ball, har suka iso bakin titi hirar ba ta ƙare ba, sosai Raja ya yi mamaki jin yanda Rabi'an tasan abubuwa da dama game da ball, kuma ya yi mamakin jin yanda tace musu ta na son buga ball, dama ce kawai ba ta samu ba. Su suka tsaida mata mota ta shiga, sannan suka juyo,suna tafe suna 'yar hira.
Kamar daga sama suka ji wata murya na faɗin.
“Hello!”
Hakan yasa suka kalli inda sautin muryar ya fito. Wata yarinya ce tsaye a gabansu, sanye cikin uniform ɗin makarantar Brickhall, a ƙiyasin shekaru ba za ta wuce 17 ba.
“Hy”
Rhoda ta amsa mata, yayin da idanuwan Raja ke kallonta ƙasa-ƙasa.
“Ko zan iya sanin sunanka Bro?”
Mamaki ya kama Raja, to me za ta yi da sunansa?, tukunna ma waye ce ita?.
“No, kada ka damu fa, ni ba 'yar yankan kai ba ce...”
Maganar tata ta bawa Raja dariya, hakan yasa suka murmusa a tareshi da Rhoda, ya na ɗaga ƙafaɗarsa ta dama.
“Sunana Raja, ke kuma fa?”
“I'm Mishal”
Mishal ta faɗi tana gyara zaman jakarta dake goye a bayanta.
“Me yasa kike son sanin sunana?”
Sai kuma ta yi shiru, da ma gajiya ta yi da jiran zuwan Kuliya, hakan yasa kawai ta fito ta fara tafiya da ƙafarta, kuma a kan hanyar ta ci karo da wannan me kama da Kuliyan, shi ne ta tsaya don ta samu ta masa magana, wata ƙila za ta tabbatarwa da kanta abun da take san sani.
“Akwai wani yaya na da yake min kama da kai that's all”
Ta zaɓi da ta masa wannan ƙaryar, don a ganinta wata ƙila ita za ta fi bada ma'ana, saboda babu yanda za'a yi ta faɗa musu cewar da mijinta yake kama, don ba ma lalle su yardar da cewar ita ɗin matar aure ba ce, to taya ma za'ayi su yarda?.
Ba ƙaramin duka maganarta ta yi wa Raja ba, wai meke shirin faruwa da shi ne?, farko Rabi'a, yanzu kuma wannan yarinyar na faɗa masa cewar akwai wani ɗan uwanta me kama da shi, sai dai kuma shi yasan basu da wasu 'yan uwa na kusa. Da ace ma Rabi'a ce za ta faɗi hakan sai ya yarda, amma shi yasan cewa su ba su haɗa jini da shuwa arab ba, saboda daga gani wannan yarinyar jinin shuwa arab ce, haka zalika kuma yasan cewa duk wanda ya mutu babya dawowa, Allah ya riga ya amshi rayuwar Aliyunsa, hakan tasa ya dangana, ita ma Rabi'an abun da ya sa yake bibiyarta ba komai ha ne face son sanin wani abu game da danginsa.
“Ya alaƙarku take da yayan naki ?”
Rhoda ta tambayi Mishal, dan babu labarin Raja da ba ta sani ba.
“Uwa ɗaya uba ɗaya”
Ta amsa tana kallon fuskar Raja, yanda ya yi da fuskar tasa kaɗai yasa ta tabbatar da abin da take zargi, tabbas babu makawa, duk yanda aka yi wannan ɗan uwan Kuliya ne, amma me ya shiga tsakinsu har suka rabu haka?, tana buƙatar sani.
“Ni zan wuce, Bro and Sis sai an jima”
Da kallo suka bi bayanta har ta fara tafiya.
“Yarinyar nan akwai shirirta”
Rhoda ta faɗi tana 'yar dariya.
Raja da ya gama tabbatarwa da wannan yarinyar ba a kan Aliyunsa take magan ba ya mata murmushi kawai, yana ɗaga kafaɗarsa ta dama, kafin ya ci gaba da tafiya, hakan yasa ita ma bin bayansa.
Mishal na tafe tana saƙe-saƙe a ranta, tana son sanin abin da ke tsakanin waɗanan mutanen biyu masu kama ɗaya, sai de kuma suna da mabanbantan halaye, tsayuwar da ta yi da wannan Rajan ba ta fi ta minti biyar ba, amma ta gane banbancinsa da Kuliya, wannan yana da fara'a, yayin da Kuliya ba shi da ita, wannan yana da sakin fuska, fuskar Kuliya kam kullum a ɗaure take, sannan muryar wannan akwai sanyi da taushi, yayin da ta Kuliya ke cike da hargagi da faɗa, ko maganar arziƙi yake da mutum sai ya maka tsawa, bare kuma a ce ransa ya ɓaci.
Sai kawai ta yi murmushi tana jinjinawa kanta, na sanin halayen Kuliyan a kwana huɗu kawai da suka yi tare, duk da ba wani zama suke sosai ba, haɗuwarsu ba ta wuce uku a rana, da safe kafin ta tafi makaranta, sai kuma idan ya zo ɗaukanta, sai da daddare idan ya dawo. Kuma kwana biyu ma ba sa haɗuwa da daddarren dan sai ta yi bacci yake dawowa.
KULIYA POV.
Cikin matsanancin gudu yake tuƙa motarsa, tunawa da ya yi ya bar 'yar mutane ta na jiransa, aikin da yake ne ya sha masa kai, har ya sa ya manta da lokacin tashinta daga makaranta, kuma tun a sanda ya fito daga headquarter ya riga ya yanke hukuncin cewa dole sai dai ya nema mata driver, don ayyukan dake gabansa sun fi ƙarfinsa, idan yau ya tuna a kan kari, gobe ba llalle ya sake tunawa ba.
Amma idan ya sama mata drivern, aikin zai masa sauƙi, kuma ko ba komai shi ma zai huta, saboda a kullum sai ya dakatar da aikinsa yake iya samun zarafin zuwa ɗaukanta.
Wata yarinya ya hanga a gefen titi, kamar ita kamar ba ita ba, gashin kanta da kuma farar fatarta da ya gani ne  ya tabbatar da cewar ita ce, ya kamata ace ya mata magana kan fita babu ɗankwalin nan ma, don a matsayinta na matar aure hakan be dace da ita ba.
Parking ya yi a kusa da ita, yanda ta tsaya tana kallon motar tasa ya sa ya gane cewa ita ma ta san cewar shi ne a cikin motar, to amma me take jira da taƙi zagayowa ta shigo?, ko jira take sai ya mata magana?.
Kusan shuɗewar muntina goma suna a haka, ita tana tsaye, ta kafe motar da ido, shi kuma ya kasa mata magana ta shigo, ganin kamar tana shirin ɓata masa lokaci ne yasa ya zuge glass ɗin setinta ƙasa. Sannan ya kalleta. Sai da ya ɗaga ƙafaɗarsa kafin yace.
“Za ki iya shigowa idan kin gama tsayuwar!”
Mishal ta yi murmushi tana zagayowa, aka ce da ba ya ji, sarai ta gane shi, amma jira take ta ƙure masa miskilancin da yake ji da shi, duk da Anti Adawiyyanta ta ce kada ta na masa irin haka, amma ta lura da idan ba haka ta masa ba, ba zai dena mata wannan abun ba.
*No.181, Guzape, Abuja....*
*08:30pm*
MISHAL POV.
Zaune take a ɗakinta, assignment ɗin da aka basu take ta ƙoƙarin yi.
Ƙofar ɗakin da aka turo yasa ta ɗa ga kanta ta kalleshi, don tasan daga ita sai shi ne kawai a gidan, kuma ta yi mamakin dawowarsa da wuri. Kamar yanda ta saba ganinsa, sanye yake cikin baƙaƙen kaya. Wai shi ba shi da wasu kaya sai baƙaƙe ne?, kullum sai ya yi ta saka baƙin kaya kamar me shirin zuwa jana'iza #AbuAswad Sai kawai ta yi dariya a sanda zuciyarta ta raya mata sunan, ABU ASWAD! sunan ya karɓe shi kuwa.
A hankali Kuliya ya saki hannun ƙofar yana kallonta, sanye take cikin wata blue and white boxed tie crop top da farar three layers ruffle skir. Duk da a zaune take, yana iya ganin alamar skirt ɗin ba ta sauƙa har kan idon sawunta ba, kamar dai sauran kayan da ta saba sakawa, don duk kayan da yake ganinta da su ba sa kaiwa ƙasa. Gashin kanta naɗe cikin french twist, daga saman gashin ta saƙala farin hair band. Kai kace wata Disney princess ce, kallonsa take kamar yanda shi ma yake kallonta, daurewa ya yi yace.
“Ki shirya ki fito za mu je wani wuri”
Zai iya cewa ya ga wacewar wani abu me kama da farin ciki a cikin idanunta, kafin ta miƙe da sauri, ƙafarta da bakinta har rawa suke wurin faɗin.
“Fita zamu yi?”
Ya kalleta na wasu 'yan sakkani. Jin ya mata shiru yasa ta kuma faɗin.
“Ai a shirye nake, mu je kawai”
Ta faɗi tana ƙoƙarin raɓa shi ta wuce, a karo na farko ya riƙo tsintiyar hannunta, ya na dawowa da ita baya, ba shi kaɗai ba, hatta da ita sai da ta ji kamar hysterianta na neman ta shi, sai kuma ya saki hannun nata da sauri yana kawar da kansa.
Ita kuma sai ta kalli hannunta, yati6n da take kokawa da numfashinta da ya ƙi dai-daituwa, da ƙyar ta iya ɗagowa da kansa ya na ɗaga kafaɗarsa.
“Be kamata ki fita a haka ba, saboda yanzu ke matar aure ce!” Ya faɗi ba tare da ya kalli fuskarta ba.
Mishal ta sunkuyar da kanta ƙasa, yayin da abun da ya faru da ita waccan ranar ya shiga yawo a kanta, ba ta son tuna me ya furu a waccan ranar, amma daga zarar wani abu makamancin wanda ya faru a waccan ranar ya sake faruwa da ita sai ta tuna, yanda Yazid ya finciki hannunta da ƙarfi a waccan ranar haka shi ma ya yi a yanzu, tuna sunansa kaɗai yasa numfashinta fara ciccikowa.
Da sauri ta kai hannunta kan wuyanta tana riƙewa, yayin da iskar ɗakin ta mata kaɗan wurin shaƙa, babu shiri ta shiga jan numfashi da sauri, hakan ya ankarar da Kuliya halin da take ciki. Kallonta ya yi da sauri, a lokacin da ta kai ƙasa, tana kokawa da numfashin nata, idanuwanta sun kaɗa sun yi ja, yayin da hawaye ya shiga fita ta gefen idonta.Ji take kamar za'a zare mata numfashinta gaba ɗaya.
A ruɗe Kuliya ya zube a gabanta yana kiran sunanta.
“Hafsat!, Ke Hafsat!, Hafsat!”
Inaa, ko ganinsa ma ba ta iya yi, bare har ta saurari abun da yake faɗi, ba shiri ya kai hannun ya riƙe fuskarta, yana goge mata gumin da ya shiga tsatsafo mata, har zuwa lokacin ba ta iya numfashi, can kuma sai komai ya tsaya cak, shure-shuren da take, da kokawar da take da numfashinta, da ma hawayen da take duka suka ɗauke, jikinta ya saki, kamar wadda ta mutu.
Ba shiri Kuliya ya miƙe daga kanta, hankalinsa a mugun tashe, shi tun da yake be taɓa ganin abu makamancin haka ba, bai ma san me yasa meta ba, to ko aljanu gareta?...
Tunaninsa ya katse a sanda idonsa ya sauƙa kan wata robar ruwa dake ɗakin, ba shiri ya miƙe da sauri ya nufi robar, ya ɗako ya dawo kanta ya na buɗe robar, tuninsa ne ya bashi cewar wata ƙila suma ta yi. Don haka ya shiga yayyafa mata ruwan a kan fuskarta da ta yi jajir, amma shiru, haka ya miƙe ya nufi work table ɗin da ɗazu ta taso daga kansa, ya ɗauko littafi ɗaya sannan ya dawo kusa da ita, fiffita ya shiga mata yana kiran sunanta.
Kamar wadda aka tsikara da allura, lokaci guda numfashinta ya dawo, ba shiri ta miƙe zaune tana wani irin tari, har lokacin Kuliya be fasa mata firfita yana jero mata sannu ba.
Sai da ya ga ta dawo hayyacinta ne ya dubeta da kyau, ya ga yanda take ta sauƙe ajiyar zuciya, be san lokacin da ya ja ta jikinsa ya rungumeta daga zaune da suke ba.
Idanuwan Mishal ne suka ƙara girma, a lokacin da ta fuskanci cewar ita ce a tsakiyar hannayen Kuliya, ita ce a kusa da shi, kusan da har suna iya jiyo bugun zuciyar juna, babu abun da ya ba ta mamaki sai yanda ta ji zuciyarsa na aiki da sauri, mamaki ne ya kamata na me ya tsorata shi har haka.
Yanda ya ƙara matseta a cikin jikinsa ne ya sa ba shiri jikinta ya shiga kyarma, tun da ta zo duniya ba za ta iya tuna lokaci guda da ta shiga yanayi irin wannan ba, tabbas tana rungumar 'yan uwanta, amma wannan rungumar ba irin waccan ba ce, wannan ta sa ban ce, kamar akwai wani abu na musamman tattare da kusancin nasu, sai ta ji ba ta son ya saketa, kamar su ci gaba da tsayawa a hakan, saboda ta ji rungumetan da ya yi kamar ya na son kangeta daga wani abu mara kyau dake shririn faruwa da ita ne.
“Daga magana sai ki suma?!, me ya yi zafi haka Hafsat?!”
Muryarsa ta faɗi bayan wani lokaci, kuma amon muryar tasa ne yasa Mishal ta ƙara matse jikinta cikin nasa, muryar kamar ba tasa ba, kamar ba Kuliya ne ya yi maganar ba, da ma ya iya magana a tausashe kamar haka?, To ai gwara da ba ya yin magana a tausashen, don wata ƙila da ace yana yi, da duniyar ce gaba ɗayanta za ta yi haske cikin duhun daren.
A hankali ya saketa yana kallon fuskarta, a karo na farko Mishal ta ji ba ta san haɗa ido da shi, hakan ya sa ta sunkuyar da kanta ƙasa.
Kamar wanda aka jefowa tunaninsa daga sama haka Kuliya ya dawo hayyacinsa, sai yanzu ya gano abun da ya yi, ba shiri ya miƙe tsaye yana ɗaga kafaɗarsa ta dama, kansa ya kawar gefe, zuciyarsa na ƙara saurin gudun da take a ƙirjinsa, don sai yanzu ma ya ji wani irin shock a jikinsa na riƙetan da ya yi. Da ƙyar ya lalubo muryarsa cikin faɗin.
“Ki... Ki kwanta ki yi bacci kawai, sai da safe!...”
Ya faɗi ya na shirin juyawa, amma sai muryar Mishal dake ƙoƙarin miƙewa ta dakatar da shi.
“No... na ji sauƙi za mu iya tafiya”
Juyowa ya yi ya na kallonta, amma ita kuma ta ƙi yarda su haɗa ido. Shi ya masa gane mata, yanzu fa ta suma?, kuma sai ta ce su fita?.
“No, kina buƙatar hutu, don haka ki kwanta kawai...”
Cewar Kiliyan yana ƙoƙarin juyawa a karo na biyu, amma sai muryar Mishal ɗin ta ƙara katse shi.
“Da gaske nake na ji sauƙi, babu wani babbar matsala, na riga da na saba da wannan ciwon, so it's common”
Juyowa ya kuma yi ya na kallon fuskarta dake kallon ƙasa, kamar me shirin san tantance gaskiyar abun da ta faɗi.
*
Da gudu motar Kuliya ke tafiya  a kan titi, yayin da Mishal ke zaune a gefensa, kayan da suke jikinta ɗazu su ne a yanzu ma, sai dai wani baƙin gyale da ta ɗora a kanta, hanya kawai take kallo tana tuna abun da ya faru ɗazu, yanda Kuliya ya matseta a cikin jikinsa, da yanda damuwa a kulawa suka bayyana ƙarara a cikin muryarsa, abun ya burgeta ya kuma bata mamaki, ba ta taɓa ɗaukan cewa Kuliya na ɗaya daga cikin irin waɗanan mutanen ba.
Kuliya ya juyo ya kalli side ɗinta a hankali, akwai wani abu da yake buƙata a tare da ita, ba komai ba ne face son sanin alaƙarta da wannan me kama da shi ɗin, ya na son ya san inda ta san yarinyar, amma idan ya tambayeta kai tsaye ba lalle ta ba shi amasa ba, ya zama dole ya yi taka tsan-tsan wurin samun bayanen da yake buƙata a wurinta.
“Wani irin ciwo ne ke damunki?”
Tambayar ta fito daga bakinsa, bayan ta ratsa ta tsakanin mayaƙan dake san hanata fita daga bakin nasa.
A hankali Mishal ta juyo da dubanta gare shi, kafin ta juya ta ci gaba da kallon windown, sannan muryarta ta fito a hankali cikin shirun motar.
“Hysteria!... na gamu da ita ne sakamako wani bad memory da na taɓa samu”
Sai ya yi shiru ya na san ganr inda kalaman nata suka dosa, a hankali ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, yayin da yake juya kan motar zuwa wata kwana.
“Wani bad memory kika samu haka?”
A wannan karon shi kansa sai da ya jinjinawa kansa na iya jefo mata tambayar, don shi ba ya surutai barkatai irin haka, idan ka ga hirsara da mutum na tsayi to a kan aikinsa ne, bayan nan kuma ba ya wata doguwar hira da kowa sai da Anna, ita ma sai su shafe tsawon wattani ba'a samu hakan ba.
“Wani cousin brotherna ne, ya... Yi attempting min... Fyaɗe!...”
Duk da ita yarinya ce ta san cewa sam kalmar 'Fyaɗen' ba ta da daɗin saurare, musamman ma ace miji za'a faɗawa faruwarsa a kan matarsa, abun akwai ƙona rai.
Kuma sai da ta lura kamar kan motar na shirin ƙwacewa daga haannunsa, kafin ya seta kan motar da ƙyar, ya juyo ya kalleta na wasu 'yan sakkani, amma kuma ya kasa cewa komai.
“A lokacin mun je hutu Maiduguri hutun Sallah... Sai ɗaya daga cikin cousins ɗina ya aike ni ɗakinsa, kasancewar tare suke kwana da shi Yazid ɗin ya sa a sanda na shiga ɗakin na gashin kwance a kan gado... Ban masa magana ba, dan da ma can Allah bai haɗa jinina da nasa ba, na nufi lokar Mu'ammar, wato shi wanda ya aikeni ɗin... Ban za ta ba na ji ya tura ƙofar ɗakin... Na tsorata amma ban nuna masa tsoron ba, na dake har na ɗauki abun da na zo dominsa, a sanda na juya sai na iske shi tsaye a jikin ƙofar... Ban ƙara masa kalo na biyu ba na nufi ƙofar dan na fita, ina zuwa kusa da shi ya kamo tsintsiyar hannun, ya finciko ni da ƙarfi zuwa baya... Ba shiri na faɗa kan gadonsa, ni kuma sai na shiga ƙoƙarin tashi, a lokacin ne ya daka min wata tsawa da har na koma ga Ubangijina ba zan manta da ita ba. A kan idona ya shiga cire kayan jikinsa. Ba ni da tsoro amma na tsorata a lokacin, ban ankara ba har ya iyo kaina ya danne ni, kuma cikin ikon Allah sai aka bankaɗo ƙofar daga waje. Aki Abubakar da Aki Arman suka shigo ɗakin, ganin na jima ban dawo ba ya sa suka biyo baya na. Ko a sanda aka fita da ni daga ɗakin ba na hayyacina. Tun daga lokacin na gamu da Hysterianan!”
A lokacin da ta kai ƙarshen maganar hawaye har ya wanke mata fuska,duk da ita ba ta gama mallakar hankalin ba, amma tasan ciwon kanta, mace ta zauna ta na baka labarin yanda aka haike mata ba ƙaramin abun baƙinciki ba ne. Kuma ita kanta ba ta ce ga dalilin da yasa take ba shi labarin ba, wata ƙila don zuciyarta na faɗa mata cewar a yanzu shi ne gatanta, ba ta da wani gata nan duniya bayan shi, tun da ba ta da uwa, ba uba, ba ɗan uwa.
Tun da ta fara bawa Kuliya labarin wani abu me kama da mashin ɗin yankan katako yake dagargaza zuciyarsa, ji yake ina ma ya na da damar da zai iya ganin bayan wannan mutumin, ko a baki ya tsani kalmar, bare kuma a ce matarsa aka yi kokarin aikatawa hakan.
“Wani hukunci aka ɗauka a kansa?”
Ya zaɓi da ya tambayeta ko zai ji salama game da yanda zuciyarsa ke masa zugi, ji yake kamar ya kurma ihu, ko raɗaɗin tsagewar zuciyar tasa zai ragu. Mishal ta share hawayenta da gefen gyalenta.
“Cewa suka yi ai abun na gida ne, dan haka sai dai ayi haƙuri. Wani abun takaicin ma shi ne; kakarmu Jadda ita ce tace babu wani wanda ya isa ya taɓa mata jika, kamar ni ɗin ba 'ya ba ce, ko wata ƙila dan ba ni da iyaye a raye ne, kullum ba ta da abun faɗi da ya wuce tana sanmu, amma ni sam ba na ganin son!...”
Ta ƙarshe tana sakin kuka me sauti a hankali. Ashe kallon kitse Kuliya yakewa rogo, wasu abubuwan idan ta yi sai ka ce 'yar shekara 10 ce, amma idan ta yi wani abun kuma sai ka zaci ta kai 20, wani lokacin yarinta ce fal a zancenta, wani lokacin kuma sai ta yi maganar hankali, kamar ba daga bakinta take fita ba, hannunsa yasa a cikin aljihunsa, ya zaro mata hanki, sannan ya miƙa mata.
Mishal ta karɓa tana share hawayenta.
“Wannan na ɗaya daga cikin matsalolin societynmu. Sai ki ga mutum ya aikata laifi, amma a ƙi ɗaukar mataki a kai, saboda ana ganin me laifin na gida ne, idan aka ɗaga maganar zumunci zai iya rabuwa. Wannan zai bawa me laifin damar ci gaba da aikata laifukansa yana fakewa da kasancewarsa na gida. Haka abun zai ci gaba da ƙaruwa kamar wutar daji” Cewar Kuliya.
Mishal ta juyo ta kalleshi, ita kam yau ya na bata mamaki, bata taɓa ɗaukar cewar yana magana cikin sanyi irin haka ba, kuma ta ɗauka cewar maganganunsa basu da tsayi kamar yanda ta saba jinsu daga bakinsa, amma yau da banbanci.
*
“Maraba Lale!”
Cewar Anna a sanda suka iso gidanta, tsaye take daga cikin falonta tana ta zabga murmushi, ta kasa gaskata abun da idonta ke gane mata, wai yau ita ce take ganin matar Aliyunta?.
Suna ƙarasa shigowa cikin falon ta kama haannun Mishal ta zaunar da ita a kam kujera, sannan suka gaisa, fara'ar matar ya sa Mishal sakewa da ita.
“Ni ce surukar ki 'yata, fatan ba za ki riƙa min ɗanyen tuwo ba”
Anna ta faɗi tana dariya, hakan ya sa Mishal ma yin dariya, banda Kuliya da ya haɗa girar sama da ta ƙasa, kamar baƙin hadarin dake shirin zubar da ruwa, don shi bai ga wani abun dariya a maganar ba.
“Kenan ke ce mamarsa?”
Ta tamabaya tana kallon Kuliya. Anna ta gyaɗa mata kai.
“Ni ce nan mamarsa”
Mishal na murmushi ta ci gaba da ƙarewa fuskar Anna kallo, wai ko za ta tsinto wani abu guda da ya haɗa kamarta da ta Kuliyan. amma har ta gama yawo da idonta a kan fuskar Annan ba ta gani ba.
“Sunana Anna. Ke kuma ya faɗa min suna ki Hafsatu ko?”
Mishal na murmushi tace.
“Hafsat dai, amma Mishal ake cemin”
Anna ta yi dariya tana kallon Kuliya da ya maze yana kallon tv, kamar ma be san abun da suke ba. Anna ta ƙwalawa Siyama kira.
Ba tare da wani ɓata  lokaci ba, sai ga Siyama ta bayyana a falon. Kamar yanda dalar ƙanƙara ke zaftarewa ta faɗi a yayin da zafin rana ya bugeta, haka zuciyarta ta zaftare ta faɗi lokaci guda, sakamakon idonta da ta ɗora a kan wata kyakkyawar yarinya me kama da 'yartsana, zaune a gefen Anna.
Ganin Kuliya da ta yi a gefe guda ya sa ta ji ƙarar faɗowar wani abu a ƙirjinta, kenan wannan ita ce matar Kuliya?, in dai kuwa wannan ita ce matar da ake ce ya aura, to babu ta yadda za ayi Kuliya ya kalli inuwarta bare ita kanta.
Duk da ta san cewa ita ma tana da kyau dai-dai gwargwadon, kuma a shekaru ba za ta wuce 23 ba, amma tun da Kuliya ya riga ya samu wannan kyakkyawa kuma sabon jini irin wannan yarinyar babu abun da zai yi da ita.
Yanzu ita shi kenan ta rasa Kuliya?, to yanzu ina za ta sa kanta?, ba ta jin za ta iya rayuwa me kyau tare da wani namijin da ba shi ba, ko da da take faɗin ta haƙura da shi faɗa kawai take, don ba ta hangowa kanta rayuwar da babu Kuliya a cikinta.
“Ba ki ga matar yayanki ba ne? Ki gaisheta mana”
Muryar Annan ta dawo da ita zahiri, hakan yasa ta ɗauke idonta daga kan Kuliya da ta kafe da kallo, ta dawo da su kan 'yar ficilar yarinyar dake gefen Anna, duk da ba za ta kirata da yarinya can ba, don jikinta a murje yake, ta na da duk wata cikar sura irin ta 'ya mace, babu abun da Siyama za ta faɗa mata da ya wuce yawan shekaru.
“I'm the one that supposed to greet her... Tun da ita ce babba”
Sassanyar Muryar yarinyar ta kuma katse mata tunani.
“A'a ita ya kamata a ce ta gaida ki”
Siyama ta haɗiye wani ƙullutun baƙin ciki a sanda take gaida yarinyar, cikin mutuntawa Mishal ta amsa ta, cikin san gano wani abu tsakaninta da Kuliya, don da ace ƙanwarsa ce kamar yanda Anna ta faɗa, ko kallonta ya yi, amma ji yanda ya hakimce ya na kallon tv abunsa kamar bai san akwai wasu hallitu a falon ba, kuma duk ta lura da irin kallon da Siyaman ke binsa da shi tun sanda ta shigo falon.
“Anna! Na roƙi wani abu a wurinki?”
Mishal ta tambaya, bayan da Annan ta sa aka kawo mata abinci, zuwa lokacin Kuliya ba ya falon, don waya ce ta sameshi daga wani wai shi Symon, kuma bisa ga dukkan alamu maganar aiki ce, hakan yasa ya fice daga falon baki ɗaya, wannan Siyamar ma ba ta falon, saboda ba ta jima da shigewa ɗaya daga cikin ƙofofin dake falon ba.
“Ina jin ki 'yata, faɗi ko me kuke so, in dai bai gagara ba zan miki shi da yardar Allah!”
Mishal ta aje spoon ɗin hannunta tana sosa kai.
“Da ma so nake ki masa magana kan ya siyo min kaya girki, ina so na riƙa yin girki da kaina. Abincin wajen nan ba ya min daɗi”
Anna ta yi 'yar dariya.
“'Yata kin iya girki ne?”
Da sauri ta gyaɗa kanta tana faɗin.
“Sosai ma kuwa, tun ina da shekara goma sha ɗaya na fara girki fa”
”Aaaa, ahse 'yar tawa babbar cooker ce”
Mishal har da dariya, irin an yabeta ɗin nan.
“To kada ki damu. Da yardar Allah zan sa ya sai miki kayan girki, ta yadda za ki riƙa yin girkinki da kanki”
“Kai amma fa da na ji daɗi Sweet Anna”
Anna ta kwashe da dariya, da ma Rahila na ba ta bayanin yarintar Mishal ɗin, ba ta taɓa ɗaukar cewa haka take ba sai yau, amma ita yatinyar tata ta birgeta, don akwai nustuwa a ciki.
Siyama dake cikin ɗaki ta silale a kan gado tana danne bakinta da hannunta, gudun kada kukan da take riƙewa ya suɓuce mata, da ace ta na da ikon cire son Kuliya a ranta da ta yi ta huta da wannan azabar da take sha, ta gaji, Wallahi ta gaji har ranta, amma soyyayarsa ta hanata gannin gazawarta.
Ta riga ta yankewa kanta hukuncin gobe da sassafe za ta haɗa kayanta ta koma gidan Anti Karima, don su sake sabon lale.
___________________
_Salmanians, shin ba mu jawa Siyama kunne kan kada ta fara ba?_
_Godiya ta musamman zuwa ga dukan Salmanians na fili da na ɓoye, haƙiƙa kune ƙwarin gwiwata a ko da yaushe_
#Labarinsu
#SalmaAhmadIsah
#TaurariWriters

LABARINSUWhere stories live. Discover now