LABARINSU 10

40 0 1
                                    
*LABARINSU*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*TAURARI WRITERS*
*10*
~~~
*Do something for her that no one has ever done, love her for who she is.*
***
*Shekara ta 2000.*
“Malam Ila ina kwana”
Cewar Zaid yana tsugunnawa har ƙasa, a sanda ya shigo shagon Malam Ila, wanda ke saida kayan provision a 'yar ƙaramar containerrsa.
Baki washe Malam Ila ya amsa masa, kafin Zaid ya miƙe ya zauna a kan bencin da Malam Ilan ke kai, suka kuma gaisawa, kafin Malam Ilan ya ba shi abincin da ya siya ya aje masa, kamar yanda suka saba kullum.
Don a kwanakin kullum idan ya zo sai ya ba shi abinci, karɓa ya yi sannan ya ci, suna 'yar hira jifa-jifa. Kuma a cikin hirar ne Malam Ilan ya sosawa Zaid inda ke masa ƙai-ƙayi.
“Ya kamata ka je ka dubo ƙanin naka, ka ga fa yau kusan satinsa ɗaya a can!”
Aliyu ya aje kwanon hannunsa sannan yace.
“Ai wai kar su ga gaggawata ne shi yasa, amma ina kewarsa, don ba mu taɓa nisa da juna irin haka ba... Tazarar awa ɗaya ne tsakanina da shi a haihuwa, kuma bayan wannan tazarar ba mu sake samun wata tazara ba... A ko da yaushe muna tare”
Cike da tausayawa Malam Ila ya girgiza kansa.
“Ka ga abun da za ayi shi ne; zuwa gobe sai muje mu duba shi ko?”
Cike da zumuɗu Zaid ya ɗagaa  kafaɗarsa.
“Allah ya kaimu goben, na gode Malam Ila, Allah ya saka maka da alkairi...”
Washegari da sassafe Zaid ya dira a ƙofar shagon Malam Ila, ko fitowa ma bai yi ba, haka ya zauna ya na jiran fitowar Malam ilan.
Sanye yake da wani farin yadi, wanda Malam Ila da kansa ya bashi, don yace ba ya san ganinsa da wannan uniform ɗin. Kana ganin kayan za ka san cewa ba nasa ba ne, saboda yanda kayan ya masa yawa.
Ya na zaune a wurin har Malam Ila ya fito, babu yanda be yi da Malam Ila kan su wuce gidan marayun katsaye ba. Amma Malam Ilan ya dage kan sai ya sai masa abinci ya ci tukunna. Hakan kuwa aka yi, sai da ya sai masa abincin ya ci ya yi taf, sannan suka kama hanyar gidan marayun.
“Bawan Allah, Lafiya kuwa na ga kamar gidan marayun nan a kulle, kuma na... Na ga kamar ma gobara aka yi!”
Cewar Malam Ila a kiɗime, hankalinsa ya yi wata mummunar tashi, bayan da suka iso gidan marayun, suka ga gate ɗinsa a kulle, kuma ko daga bakin gate din za ka gane cewa an yi gobara a wurin.
Mutumin da Malam Ila ya tambaya ya kalle su.
“Kwana huɗu kenan da wuta ta kama a gidan, kuma babu wanda ya fita da ransa daga gidan!...”
Iyaka abinda Zaid ya iya fahimta kenan a zancen nasa, bai san sanda ya yanke jiki ya faɗi ba.
Kwanansa uku a asibiti kafin ya farfaɗo, kuma da ya tashi farfaɗowar ma ba a hayyacinsa ya farka ba. Abubuwa ya riƙa yi kamar wanda ya samu taɓun ƙwaƙwalwa, sai zantuka yake barkatai, an kasa gane kansa.
Ganin abun ba na ƙare ba ne ya sa Malam Ila ɗauke shi daga asibitin, don ya ga abun ba na asibiti ba ne. Tashin farko gidansa ya kai shi, amma matarsa tace fafur ba za ta karɓi tsinttaciyar mage ba.
“Wa to kai ga ka juju ko?, Ub*n yaye-yaye, to Wallahi ba za ta saɓu ba!, a ina zan saka wannan gardin ƙaton?, A gida ɗaki ɗayan?, Ga ka, ga ni, ga 'ya'yana, to Wallahi Malam da sake!”
“Haba Gambo, be kamata kike faɗin haka ba, yaron nan na faɗa miki cewar maraya ne, idan ba ki manta ba; babarsa ce ta ba ni kuɗin da na miki yankan sunan Audu...”
“Wallahi ba ka isa ba, wato dan kawai uwarsa ta ba ka kuɗi ka sai mana ragon suna, sai na karɓi ɗanta ko ?, na rantse maka da Allah wannan yaron ba zai zauna min a gida ba!”
Duk da Zaid ba ya hayyacinsa sosai, amma yana iya tuna yanda matar kewa mijinta masifa da bala'i, ya na iya tuna yanda ta haƙiƙance kan ba zai zauna da ita ba.
Tun bayan da ya fuskanci cewa Aliyun da ya rage masa ya bar duniya, rayuwarsa ta shiga halin ƙaƙa na ka yi. Ya ji gaba ɗaya ya gaji da duniyar, babu abun da ya fi buƙata sama da mutuwar shi ma, ya ji cewar yana son ya mutu kamar Momma da Aliyu, tun da da ma su ne kaɗai gareshi, to ga shi ya rabu da su, to ina zai sa kansa?.
Ba dan Malam Ila ya so ba, sai dan babu yanda zai iya, ya ɗauki Zaid ya mayar da shi gidansu na da, amma kullum sai ya kawo masa abinci da ruwan rubutun da yake karɓo masa a gun wani malami mai almajirai da yasa a yi masa, don ya temaka masa wurin dangana da halin da ya shiga ciki.
Safe, rana, dare, ba ya taɓa tsallakewa, har takai ga Zaid ɗin ya dawo hayyacinsa gaba ɗaya, amma yanayinsa da ɗabi'unsa duka sun sauya, ba ya son yawan magana, ba ya son fita, ba ya son shiga jama'a. Ya koma rayuwar ƙunci. Ƙarshe ma ya yanke shawarar barin gidan.
Rana tsaka Malam Ila ya shigo gidan kawo masa abinci amma ya nemeshi sama ko ƙasa babu alamarsa. Ya ɓata ɓat! Kamar almara.
Ranar da ya gudu cikin garin kano kawai ya bazama, ya kwana a titi, kafin da safe ya ci gaba da yawatawa. Har Allah ya kawo shi rumfar wata inyamura me ƙosai, sunanta Ebere, tana da marainiyar yarinyarta Rhoda, da mijinta ya mutu ya bar mata.
Ganinta da Zaid na farko Allah ya saka mata tausayinsa, hakan yasa ta kira shi.
“Menene sunan ka ?”
Ta tambaya cikin gurɓattaciyar hausarta.
“Zaid”
Zaid ya amsa mata kansa a ƙasa.
“Kai maraya ne ?”
Sai ya girgiza kansa yana ɗaga kafaɗarsa ta dama.
“Ni maraya ne, ba ni da kowa”
Maman Rhoda ta waiga ta kalli 'yarta Rhoda dake zaune a raufar ta na wasa.
“Za ka zauna da mu?”
Zaid ya ɗago da kansa ya kalli matar, sannan ya kalli 'yarta, a take ya ga sun rikiɗa a idonsa sun koma masa Momma da Aliyu.
Ba jayyaya ta amince mata, a ranar tare suka wuni a rumfar saida ƙosan nata, bayan dare ya yi ta ɗauke shi da Rhoda 'yarta suka tafi gidanta.
Gidan ba wani babba ba ne, amma nata ne, kuma mallakinta, ɗaki ɗaya ta bashi tace masa ya yi zamansa, daga yau shi ma ɗanta ne, kuma ba ta hana shi yin addininsa ba, zai iya ci gaba.
Tun daga wannan ranar Zaid ya yi sabin ahali, ga su dai ba musulmai ba, amma sun nuna masa karamci da hallacin da ya kamata a ce 'yan uwansa musulmai ne suka nuna masa.
Maman Rhoda ta mayar da shi kamar babban ɗanta, Rhoda kuma ta ɗauke shi a matsayin wa, sai suka koma kamar 'yan biyu, duk da shi Zaid ɗin ya fita shekaru, amma hatta da kaya iri ɗaya suke.
Maman Rhoda ta saka Zaid a makaranatar su Rhoda, sannan ta biya masa kuɗin shekarun da zai yi har ya gama makaranatar kamar yadda ta yi wa Rhodan ita ma, don tace akwai mutuwa, ba ta son ta mutu ta barsu cikin wani hali.
Kullum da safe Maman Rhoda za ta haɗa kayan ƙosanta. Kuma tare da su Zaid ɗin take tafiya, idan suka je suka aje mata kayanta a rumfar da ta saba yi, sai su wuce makaranta idan a cikin sati ne. Bayan sun taso kuma kai tsaye can rumfar tata za su wuce, ba su suke dawowa ba sai rana, idan sun dawo da rana za su zauna su huta, idan suna da wani aikin yi su yi, idan kuma ba su da shi sai su hau aikin haɗa ƙosan yamma.
Yamma na yi za su ƙara komawa, ba sa dawowa sai wajajen sha ɗaya, wani lokacin ma Rhoda tun a can take fara bacci, sai dai Zaid ya goyota su dawo gida.
Zaid ya sake da su sosai, ya na rayuwa cikin farin ciki, dan Maman Rhoda ba ta rage shi da komai ba, ko azumi ne zai zo tana ta ya shi yin hidindumun azimin, kuma duk sallah sai ta masa sabon ɗinki.
Kamar yanda take tafiya da shi can Enugu garinsu idan Christmas ta zo, kuma hatta da 'yan uwanta na can ba sa nuna masa ƙyama, sannan ko da sau ɗaya ba ta taɓa masa tayin shiga addininsu ba, shi ma kuma bai taɓa musu ba, dan ya ga kamar idan ya musu ma bazasu karɓa ba.
Rayuwarsa ta ci gaba da wanzuwa a haka, cikin farin ciki da samun nasarori, kafin giftawar wata ƙaddara, wadda ta tarwatsa komai na rayuwarsu shi da Rhoda, ta yi fata-fata da jin daɗinsu!, Ƙaddarar ta hargitsa komai!.
*Present day...*
RABI'A POV.
Da sassafe ta farka kamar kullum, sai da ta yi sallah, sannan ta gyara alkama, ta kai niƙa, ta ɗauko niƙan, sannan ta haɗawa Habiba kayan suyar funkasonta kamar yanda ta saba.
Kana ta share gidan tas, sannan ta shiga wanka, a lokacin da ta fito har masu siyan funkaso sun fara taruwa a gidan, don Habiban da kanta take soyawa, tun da yau akwai makaranta.
Ɗakinsu ta shiga, ta saka kayanta, ta ɗan shafa mai, sannan ta yi wa Anti Saratu sallama, ta fita.
Yau ta yi mamaki sosai ganin har kusan kwana uku kenan ba ta ganin Mishal a makarantar, ita kuma ba ta santa da wata ƙawa ba bare ta tambayeta, wannan baturiyar ma da ta saba ganinsu tare ba ta san inda za ta sameta ba.
Hakan yasa tunanika sukai mata yawa, ta shiga saƙe-saƙe kala-kala, har zuwa lokacin da aka tashi. Kuma kamar yanda zuciyarta ta raya mata, kamar yanda ta saba ganinsa.
Tana fita idanuwanta suka sauƙa a kansa, jingine jikin gate ɗin estate ɗinsu, sanye cikin wasu ash jogger set. Hannayensa sanye cikin aljihun hoodie ɗin kayan, sai dai saɓanin kullum, yau ba shi kaɗai ba ne, shi da wannan budurwar ne, wadda ya kira da ƙanwarsa, sanye take ita ma cikin irin kayan jikinsa, hatta da takalmansu iri ɗaya ne.
Kamar yanda suka saba a kwannakin hannu ta ɗaga masa, hakan yasa Rhoda ta juya ta kalleshi, sannan ta kalli Rabi'an.
Bisa ga mamakinta sai ta ga Rajan ya sha mur, ya na bin bayan Rabi'a wadda ta fara tafiya, sai kawai ta yi murmushi ita ma ta bi bayansu.
“Me ya same ki yau ?”
Raja ya tambaya, ganin yanayinta ba kamar yanda ya saba ganin ba, Rabi'a ta ɗago ta kalleshi, sannan ta kalli Rhoda dake biye da su, ganin hakan yasa Rhodan ta ɗauke kanta sama tana fito, sannan ta ƙara da.
“Ni fa ba na jin komai...”
Raja ya tsaya, sannan ya waiga ya kalleta.
“Da ma biyoni kika yi ?”
Ta girgiza kanta.
“A'a fa, ni saƙo zan je na karɓo a nan bakin titi”
Raja ya finciko hannunta yana kama kanta ya matse, hakan yasa ta saki ƙara. Duk abun da suke Rabi tsaye a gefe tana kallonsu.
Sai kuma ya dafa Rhodan, sannan ya yi wa Rabi alama da su ci gaba da tafiya. Tafiyar suka ci gaba da yi, Raja na dafe da kafaɗar Rhoda. Ya ɗaga kafaɗarsa sannan yace.
“Baki amsa ni ba Ammata”
Ko kafin ta ba shi amsar Rhoda ta yi wuf tace.
“Ammata?, What a wonderful name!”
Raja ya kama kunnenta ya murɗe, hakan yasa ta saka ƙarar azaba.
“Raja mana!”
Ta faɗi a shagwaɓe.
“Ammata manta da wannan yarinyar, neman magana take”
Sai faɗan nasu ya bawa Rabi dariya.
“Kwana biyu kenan wata ƙanwata ba ta zo ba shi yasani a damuwa!”
“Gidan ku ɗaya ?”
Rhoda ta tamabaya daga ɗayan ɓarin, Raja ya ranƙwashi kanta daga sama, kasancewar ya fita tsayi. Ta dafe wurin tana turo baki. Rabi'a kuwa sai murmushi take.
“Ki kwantar da hankalinki Ammata, lafiya ita ce ke ɓuya, da yardar Allah tana cikin ƙoshin lafiya”
“Kawai ki manta”
“Rhoda hoo!”
Raja ya faɗi yana ƙara dukan kanta, ta ƙwace kanta, sannan ta koma layin da gudu, tana faɗin:
“Kada ki dumu Ammata! She dey fine oo!”
Daga Rajan har Rabi'a sai da suka yi dariya. Tafiya sukaci gaba da yi suna 'yar hira, har suka iso bakin titi, kamar kullum haka y tsaidamata ta hau, har suka ƙulewa ganinsa ya na ɗaga mata hannu. Kamar daga sama ya ji muryar Rhoda daga bayansa.
“Hooo!, Raja ya kwarewa soyyayar me kama da shi...”
Juyawa ya yi ya kalleta, tsaye take a bayansa, kenan dawowa ta yi?.
“Ki bari na zo na sameki a nan”
Ya yi maganar yana nufar inda take. Rhoda ta fita da gudu tana dariya, shi ma ya bi bayanta yana dariyar, har ya cimmata, kafin ya riƙe kumatunta yana ja.
“Ke ba kya jin magana ko?”
Rhoda ta dafe wurin da ya ja mata tana kumburo baki.
“Ayya mana Zaid, wannan ai mugunta ce ”
“Ni ne mugun?”
Ya faɗi yana ƙoƙarin ƙara kamata. Ta kuma saka gudu tana dariya.
“I'm sorryyyyy!”
Ta faɗi tana kama kunnuwanta, a sanda ya kuma cimmata, sai ya dafata kamar ƙawarsa, suka jera suna tafiya. Har suka koma gidansu.
*No. 213, Naf belly Estate, Asokoro, Abuja.*
“Assalamu Alaikum... Karima!”
Muryar Anna ta faɗi, yayin da wayarta ke kare a kunneta, bayan da ta aikawa Karima yayar Siyama kira. Daga cikin wayar muryar Karima ta amsa da.
“Wa Alaikumu Salamu, Na'am Anna, ya kike, ya gidan ?”
“Lafiya ƙalau Karima, ya Siyama da yaran, da kuma me gidanki ?”
“Suna lafiya”
“To da ma so nake dan Allah ki kira mijin naki ki sanar masa da cewar ina son ganinki, idan xai iya miki lamuni”
Karima ta ɗan yi jim, kafin ta amsa da:
“Ba damuwa, Insha-Allah zai bari, amma Lafiya kike nemana Anna ?”
Anna ta ɗan shafo gefen fuskarta, sannan tace.
“Lafiya... Ban faɗa muku ba ne,  An ɗaurawa Kuliya aure, kuma yau za mu je mu ɗauko amaryar, su Laraba ma duk na kirasu, dan haka kema sai ko taho...”
Tsabar razanar da Karima ta yi sai da ta miƙe tsaye, hannunta kan ƙirjinta wanda ya shiga bugu da sauri.
“Aure kuma Anna!, Kuliyan ?!, Shi da wa ?!”
Sai da Anna ta ɗan yi shiru, kafin ta amsa mata da.
“Wannan ba huruminki ba ne, matar Aliyu kuma idan kin zo za ki ga ko wacece!...”
Daga haka ta sauƙe wayar. Ɗazu da safe Kuliya ya zo yace mata kawun su Abubakar yace tun da jiya aka yi bakwai ya zo ya ɗauki matarsa yau. Kuma su yake so su je su ɗaukota. Shi yasa ya zo ya sanar da ita.
A lokacin kallonsa kawai ta ci gaba da yi, ganin yanda ya rame, ya yi wani irin baƙi, kamar wanda ya tashi daga jinya. Kafin ta daure ta tambayeshi shirin da ya yi domin bikin.
Ya shaida mata da; babu wani abun da ya tanada, kawai a je a ɗauko amaryar, koma miye daga baya sai a yi, ba ta ƙara cewa komai ba, dan wata ƙila a ganinsa hakan ya masa, a irin halin da yake ciki ba ta jin za ta iya tirsasashi kan wani abu da baya so ba.
Daga can gidan Anti Karima, Siyama dake kan danning ta nufota a razane, jin ta ambaci aure da kuma suna Kuliyanta.
“Anti Karima wai menene?”
Cike da baƙin ciki da ƙunar zuci Anti Karima ta kalleta tace.
“Wai Kuliya aka ɗaurawa aure!”
Wani irin duka gaban Siyama ya yi, har ta ji kamar an daki zuciyarta da ƙarfin da aka saka a wuta, kamar da Anti Karuma ta watsa mata barkwano, zuciyarta ta shiga mata ɗaci, wanda ya zagayo har zuwa bakinta.
Kuliyanta ?, Kuliya ya yi aure?, wai me Anti Karima ke faɗi ne?, anya ma kuwa tana cikin hayyacinta? Inna! Ba za ta saɓu ba, wannan zancen ƙarya ne, Kuliya na ta ne ita kaɗai, wata mace ba ta isa ta rabata da shi ba, babu wanda ya isa ya shiga tsakaminta da shi.
Ba ta san ta fara hawaye ba, sai da Anti Karima ta dafata.
“Kada ki damu Siyama, ko wace sh*giya ya aura za mu raba shi da ita, Kuliya naki ne ke kaɗai, dan haka ke kaɗai za ki same shi”
Kamar wadda ta bada ajiyar hankalinta haka ta kalli Anti Karima, hawaye na mata zuba.
“Anti Karima Wallahi ina sansa... Na rantse miki da Allah ina san Kuliya, na shiga uku ni Siyama! Yanzu wai Aliyuna ne ya yi aure?, Wayyo Allahna, Anti Karima... Anti Karima Ina sansa, I love him Anti Karima... I can't live without him, I can't, i can't...”
Gaba ɗaya ta fita hayyacinta, sambatu kawai take tana ƙarawa. Anti Karima ta rungumeta tana bubbuga bayanta.
“Ba za mu rabu a su ba, dole sai mun rabasu!...”.
Haka Siyama ta ƙarar da yinin ranar kamar mara lafiya, kuka kam ta yi har ta gode Allah.
Sai da yamma Anti Karima ta shirya dan zuwa gidan Anna, amma sai wayar Annan ta risketa kan ta yi zamanta ba sai ta zo ba, Kuliya yace zai je ya ɗauko matarsa da kansa.
Tun daga lokacin ta riga ta tabbatarwa da kanta ba zata bar wannan auren ya ɗaure ba, sai ta ga bayan wannan auren, ta ko ta halin ƙa-ƙa.
*No.234, Efab Estate, Gwarinfa, Abuja.*
MISHAL POV.
“A gidan Ub*n wa aka ɗaurawa jikar tawa aure?... Tukunna ma ub*n waye ya aurar da ita?!”
Jadda kakarsu ce ke magana cike da masifa, a sa'ilin da Ammu Musa ke sannar musu da batun ɗaurin auren Mishal da aka yi, tare da faɗin wai ga mijinta nan ya zo ɗaukanta su tafi.
Yau kwana takwas kenan da rasuwa Abubakar, gaba ɗaya ahalinsu na Maiduguri babu wanda bai zo gidan ba, haka aka yi zaman makoki aka share a jiya, sannan kowa ya koma Maidugurin, ban da Jaddan da ta ce ba za ta koma yanzu ba, sai Nimra wadda gidanta ke cikin garin Abuja.  To yau ma ita da yaranta gaba ɗaya suna gidan.
Mishal dake kwance a kan doguwar kujera ta miƙe zaune, ta na jin wani zance da ba shi da ƙafa bare kai, aure ?, wa aka yi wa auren wai ?,  wai ita?, ita akawa aure?, ta na cikin sallalamin rasuwar ɗan uwanta za'a wani zo mata da batun aure?. Duk da ba wani sosai take shiri da yayan nata ba, amma tasan da cewa ya na santa, kuma yana yin duk wata hidima da za ta faranta mata, ba ta yi kuka ba a rasuwar tasa, amma ta shiga cikin ƙinci mara misaltuwa, don ko makaranta ba ta zuwa.
Ammu Musa ya sunkuyar fa kansa a gaban matar kawunsu, sannan yace.
“Aure Jadda, Abubakar da kansa ya bayar da auren Hafsat ga abokinsa Aliyu! Kuma wannan ɗaurin auren shi ne abu na ƙarshe da Abubakar ɗin ya nema kafin Allah ya amshi ransa!”
Ba Jadda kawai ba, hatta da Nimra da kuma Hajjara sai da suka yi mamaki, amma me yasa babu wanda suka faɗawa batun auren har tsawon kwana takwas?.
Tun da bakin Ammu Musa ya ambaci sunan Aliyu, zuciyar Mishal ta hasko mata fuskarsa, wannan fuskar me kama da ta Adawiyya, kazalika irin wannan fuskar da take ganin mamallakinta na yawan tsayawa a tsallaken makarantarsu, kenan shi aka aura mata ?, wai tsaya ma, ita Mishal akai wa aure ?, wai har nawa ma take ?, da za'a mata aure, aure fa?.
“To Wallahi ba Abubakar ba, ko Muhammad ub*n Abubakar ne zai dawo duniya yau ba ku isa ba, nawa ma yarinyar take ?, duka-duka fa bata fi shekaru 16 ba, shi ne za ku cuci rayuwarta ku mata aure?”
Anna ta faɗi tana miƙewa, kamar ta kaiwa Ammu musa bugu haka take ji.
“A'a Anna, kin san dai Ammu ba zai miki ƙarya ba, dan haka batun auren nan an riga an ɗaura, kawai dai mu yi wa Mushal fatan alkari, tare da danƙata a hamnun mijinta, kinsan dai Abubakar ba zai taɓa aurawa Mishal mijin da bai dace ba”
Cewar Nimar ta na miƙewa tsaye, Jadda ta juyo ta kalleta tare da wurga mata harara.
“Ba ke ba, ko Fatima kakarki ba ta isa ta faɗa min haka ba! Kar ki ga ina sakar miki fuska, ki ɗuka cewar za ki iya kawo min raini Falmata, Wallahi ina iya ɓatawa da ub*n kowa a kan jikokina!...”
Daga nan Jadda ta shiga buɗe musu wutar bala'i, ta inda take shiga ba tanan take fita ba, masifa kwando-kwando haka ta riƙa sauƙewa.
Sai da Nimra ta kira escort ɗinta, waɗanda gomnati ta bata dan kariya, a matsayinta na general, kasancewar a waje suke suna jiranta ba ɓata lokaci suka shigo, cikin su har da yaranta biyu, Ijaz da Arman.
Su suka saka bakin Jaddan yin shiru, ba dan ta na so ba a gaban idonta Nimra da 'yarta Iqra suka shiga ɗakin Mishal suka haɗo mata kayanta kaf. Sai da suka so shiryata ma, amma da suka duba kayan nata suka ga babu na arziƙi sai suka barta haka, dan Mishal ba atamfa ko leshi take sawa ba, ita dai barta da ƙanun kaya.
Ita kuwa Mishal tun da aka fara wannan dambaruwa ta rasa gane kanta, ba ta ma fahimtar zancen da ake, dan zantukan nasu sun wa ƙwaƙwalwarta girma, wai yau ita aka yiwa aure, ita ɗin da take cewa ko da candy ta yi, ba za ta yi aure ba sai ta fara aiki, ga shi tun ba'a je ko ina ba har zancen ya warware.
KULIYA POV.
Tsaye yake a harabar gidan Abubakar, ya jingina da jikin motarsa, tunanika iri-iri na kai kawo a cikin kwanyarsa, shi kansa ba zai ce lafiyarsa ƙalau ba, dan yasan ba shi da lafiyar a irin halin da yake ciki. Kuma ba ya jin akwai maganin damuwarsa, komai ya masa duhu, ya kasa gane ainahin kan lamarinsa, shin farin ciki yake don ya samu wadda zuciyarsa ta gama tabbatar masa da sonta yake ?, ko kuma yana alhinin mutuwar amininsa, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wurin ceton tasa rayuwar?.
Ya kasa ganewa, ya kasa gane dai-dai da akasinta, ya kasa gane duhu da haske, ya kasa gane sarƙaƙiya da warwara. Ba ya fahimtar komai, ya na jin kamar rayuwarsa ce ke tangal-tangal a cikin kwale-kwalen katako, wanda ke tsakiyar tekun dake ambaliya...
Tunaninsa ya katse, a sanda ya hangi mutane na fitowa daga cikin gidan, sojoji ne guda huɗu a kan gaba, kowannensu riƙe da akwati, sai mata uku daga baya, sun saka ɗaya tsakiyarsa, wadda yake da tabbacin ita ce Mushal ɗin, duk da fuskarta a rufe take da gyale.
Har suka ƙaraso inda yake ya na kallonsu, ɗaya daga cikin sojojin ne yace ya buɗe musu booth, bai musa ba ya buɗe, suka saka akwatunan a ciki. Dai-dai da lokacin da mata nan biyu suka saka Mushal a cikin motar tasa a seat ɗin gaba.
Ɗaya daga cikin matan ce ya fusaknci cewa babbace, don ga shekarunta nan sun bayyana hakan, kuma sai yake ga kamar ma yasan fuskarta. Gaishe da ita ya yi cike da girmamawa.
“Kai ne Aliyu right? ”
Sai ya gyaɗa mata kai idonsa a ƙasa.
“Ba ka gane ni ba ko?”
Sai ya gyaɗa kansa yana ɗaga kafaɗa, don ya kasa ganotan.
“Mun taɓa haɗuwa sau ɗaya, General Adamu Nimra Arab”
Take fuskarta a ranar da suka fara haɗuwa ta dawo masa, tabbas ita ce, ita ce matar da ta babshi award a wani taron karramawa da ya taɓa zuwa.
“Ni uwa ce, kuma yaya a wurin Mishal, ba sai na zauna na maka dogon bayani ba, nasan ka mallaki hankalin kanka, ka kuma san hakkin mata a kan mijinta, na kuma san da ka san hakkin Maraya, don haka sai ka kiyaye!”
Maganganun nata ba su da yawa, amma baƙaramin taɓa shi suka yi ba, shi kuwa ya san maraici, ai yana jin babu wanda zai bada labarin maraici sama da shi...
RAJA POV.
Zane yake a kan kujerar dake facing Alhaji Bala, wanda ya buɗe akwatin dake cike da hodar ibilis, wadda su Rajan suka ƙwato masa a hannun waɗanda sukai haɗa kasuwanci da su. da ma haka Alhaji Bala ya saba saka su aiwatarwa tun suna garin kano.
Sai ya yi yarjejeniya da dilolin cocaine, kan yana so a kawo masa zai biya kuɗin, sai kuma ya tura 'yan daba karɓar kayan, idan waɗanda aka aiko da kayan ba su yi gardamar hana kayan ba, 'yan dabar Alhaji Bala za su karɓi kayan salin alin, idan kuma waɗanda aka aiko da kayan sun yi gardama, 'yan dabar Alhaji Bala za su kashesu su ƙwaci kayan.
Fuskar Alhaji Balan, ɗauke take da wani irin yanayi, wanda yake cakuɗee da farin ciki da kuma mamaki, tun da ya fara safarar hodar ibilis, bai taɓa yin wadda ta kai wannan yawa ba.
Kuma masu kayan suna da matuƙar haɗari, bai ɗauka cewar su Rajan za su iya ƙwato kayan cikin sauƙi kamar haka ba, wannan aikin da suka masa yasa ya ƙara basu matsayi me girma a cikin zuciyarsa, tare da ɗaura niyyar ɗorasu a kan sauran harkokinsa, zai buɗe musu cikinsa, ya faɗa musu sauran ayyukansa da ya saba yi, don su taya shi ya tara kuɗin da yake buƙata, wajen yin campaign ɗin takararsa.
“Da kyau Zaki, aikinki na kyau! Na ji daɗin wannan aikin, Dan haka zan ƙara baku wani aikin!”
Kusan a tare Raja da Rhoda suka kalli juna, a cikin idon Raja roda ta hango 'Ba na faɗa miki ba?', ita ma ta idon nata ta mayar masa da 'Na gani'. Sai kuma suka juya dubansu kan Alhaji Bala dake ta washe baki.
“Wani aiki ne wannan ?”
“Safarar makamai!”
RABI'A POV.
Zaune suke ita da Zara a tsakar gida, yayin da Habiba da Mama ke ɗaki suna ƙus-ƙus ɗin da suka san na miye, wai yau suke faɗin Maman za ta yi tafiyar, kuma tun safe suke ta shirye-shirye. Anti Saratu kuma na banɗaki tana wanka, Fatima da Mahmud kuma basa ma gidan.
Fitowar Mama da Habiban ce tasa su dakatawa da hirar da suke, a tare suka kallesu.
“Allah ya tsare Mamana, Allah kare min ke gabanki da bayanki, Allah ya kauda idon maƙiya a kanki!...”
Haka Habiba ke ta faɗi har Maman ta sa kai za ta fita. A lokacin Saratu ta fito daga banɗaki, kallonsa kawai ta yi, ta kama hanyar ɗaki cike da takaici. Daga Mama har Habiba bin bayanta suka yi da harara. Har waje Habiba ta bi Mama tana ta mata addu'a. Kuma kafin ta dawo ne Anti Saratu dake ɗaki ta ƙwallawa Rabi kira.
“Gani Anti Saratu!...”
Rabin ta faɗi a sanda ta shiga ɗakin , ta iske Anti Saratu zaune a bakin gado tana shafa mai.
“Awara za ki siyomin”
“To kawo... Ki ban ɗari biyar a cikin kuɗina sai na ƙaro mana da kifi”
“To”
Anti Saratu ta amsa tana miƙewa, tare da nufar jakarta inda take aje kuɗi, kuɗin ta shiga lalubowa, kuma kafin ta gama lalubo kuɗin, wani yaro ya rangaɗa sallama daga bakin ƙofa, Zara dake tsakar gida ce ta amsa masa, abinda ya fito daga bakin yaron ne ya sanya duniyar Anti Saratu da ta Rabi girgiza, don abu ne da ba su taɓa zato na, wani abu da kaf tsawon zaman Rabi a gidan ba ta taɓa gani ko jinsa ba.
“Wai saratu ta zo in ji Fu'ad!”
Abun kamar mafarki, abun kamar wasa, wai yau wani ne ke sallama da Anti Saratu, wani abu sabo, wani abu da bai taɓa faruwa a tarihinta ba, ko da wasa ba ta taɓa yin saurayi ba, tun tasowarta babu wanda ya taɓa cewa yana sonta da soyyaya. Ko dan Allah maji roƙon bayinsa ne, kuma ma an ce wai haƙuri me tadda rabo.
*No.181, Guzape, Abuja...*
MISHAL POV.
Zaune take a bakin gadon da a yanzu yake amsa sunan nata. Ita fa har yanzu ba ta ganewa komai, ta kasa ganewa halin da take ciki, gani take kamar mafarki ne, kamar ba gaskiya ba ne, babu abun da ta yi kewa a gidansu sai Daala da kuma su Mama Ladi.
A karo na barkatai ta ƙara kallon ɗakin, sannan ta ja guntun tsaki a ƙasan numfashinta, miƙewa tsaye ta yi a hankali, ita ba ta saba zaman ɗaki ba, dan haka ba za ta iya zama gu ɗaya ba.
Shi ma wanda ke amsa suna mijin nata bayan ya kawota gidan ya ajiye , ba ta ƙara ganinsa ba, ga shi har kusan ƙarfe tara na dare. A ƙofar ɗakin nata ta tsaya, tana kallon corridorn dake ɗauke da ƙofofo uku, wanda take da tabbacin ɗakuna ne.
Ba ta damu da buɗe ko da ƙofa ɗaya ba, ta ci gaba da takawa zuwa cikin falon, kasancewar gidan bungalow ne. A falo ta ci birki, ta shiga kalle-kalle, har idonta ya sauƙa a kan wata farar kyakkyawar mage, kwance a kan sofa. Ba ta san sanda murmushi ya suɓuce mata.
Da sauri ta yi wurin magen ta na ɗaukarta, hakan ya sa magen ta farka, sosa jikin magen ta shiga yi ta na mata wasa kamar wadda ta samu ƙarimin yaro.
Jin ana buɗe ƙofar shigowa falon ya sa ta ɗora magen a kanta ta kalli ƙofar, dai-dai da shigowar Kuliya, sanye cikin baƙaƙen ƙananun kaya. Kamar yanda take kallonsa haka shi ma yake kallonta.
Sanye take cikin wani short trouser, wanda bai rufe gwiwarta ba, sai wata half vase da bata rufe duka cikinta ba, ta ɗora falmaran ɗin wandon a saman half vase ɗin, wadda take da ɗan tsa yi, ƙafafunta sanye cikin wasu pink fluffy sliders, gashin kanta fake cikin ponytail.
Zuciyar Kuliya ta yi tsalle daga ma'ajiyarta, wani abu me kama da garwashi ya shiga bi ta kan  zuciyarsa, yanda ta kafe shi da olive green eyes ɗinta kaɗai ya isa ya sa shi a uku.
Da ƙyar ya haɗiye wata iska, sannan ya fara takowa zuwa cikin falon. Mishal ba ta san wa ta kunya ba, hakan ya sa ba ta ji komai ba dan ya ganta a cikin irin wannan shigar.
“Wannan kuliyar, take ce?”
Muryarta ta fito a sake, kamar ta san shi, kamar ta saba da shi, haka ta masa maganar tana shafa bayan kuliyar. Ba tare da ya kalleta ba, ya aje ledar hannunsa a kan coffe table, ya ɗaga kafaɗarsa sannan ya ce.
“Ayra”
Mishal ta ƙyal-ƙyale da dariya, dan ta fahimci cewa sunan Kuliyar ne Ayran. Ɗagowa ya yi ya kalleta, wai ita ba ta san rashin sabo ba ne?, ji yanda ta ke, kamar wanda suka saba tsawon shekaru.
“Wato saboda kada a kirata da irin suna ka, shi ne ka yiwa Ayra star takwara, tab ɗi jam, Ayra star go sue you oo!”
Kallonta ya ci gaba da yi, yanda take maganar a sake, da yanda take shafa jikin kuliyar, da kuma yanda take abu cike da yarinta ne ke nuna masa ƙarancin shekarunta. Leda ɗaya ya miƙo mata, cikin ledojin da ya shigo da su.
“Ki ci!”
Mishal ta ɗan kalli ledar, wai shi ba ya doguwar magana ne ?. Ba tare da tace masa komai ba, ta karɓi ledar, sannan ta ɗora Ayran a kanta, tana zama a kan sofa, tare da yunƙurin buɗe ledar.
Gadan-gadan Kuliya ya ga tana shirin fara cin abicin da hannunta ba tare da ta wanke hannun nata ba. Da sauri ya dakatar da ita ta hanyar faɗin.
“You have to wash your hands first”
Sai ta dakata da shirin kai lomar da take, ta ɗago ta kalleshi, ya na tsaye a yanda yake, sai kuma ta aje take away ɗin, sannan ta sauƙe Ayran dake kanta.
Ta nufi ɗakinta dan ta wanke hannun nata. Kuliya ya bi bayanta da kallo yana mamakin irin halin da yarinyar ke ciki, Abubakar ya sha ba shi labarin irin halayenta, bai taɓa yarda ba sai yau.
Lalle akwai aiki ja a gabansa, dole ne yasan yanda zai seta yarinyar nan, saboda sam ba ta san ma mecece rayuwa ba, rayuwarta take kanta tsaye.
*Washe gari...*
*07:30 AM.*
Kuliya na tsaye a falo yana fitar da abincin da ya siyo daga leda, wanda ya siyo a restaurant ɗin da ya saba siyan abinci.
Jin motsin buɗe ƙofa a corridor ne ya sa ya juya ya kalli ƙofar, kamar yanda ya sa ni, ita ɗin ce ta fito, sanye cikin kayan da ya fara ganinta da su, wato uniform.
Backpack ɗinta riƙe a hannunsa na dama, yayinda suit ɗin uniform ɗin ke riƙe a hannunta na hagu.
Ba tare da ta tambayashi ba har ta riga da ta yankewa kanta hukuncin cewa za ta je makaranta. Da alama ma dai ita ba ta san hakkin aure ba, ba zai yi wa kansa ƙarya ba idan yace ba ta ma san miye auren ba, ba ta san cewa yanzu tana ƙarƙashin wani ba ne. Sai ya ɗaga kafaɗarsa ta dama a hankali, kana ya Juya, ya ci gaba da fitar da abincin.
Mishal ta aje backpack ɗinta a kan sofa, sannan ta ɗora suit ɗin nata a kan jakar. Ta ɗan kalli inda yake, wai shi ba shi da aiki sai saka baƙaƙen kaya, ta faɗi a ranta tana kallon baƙar suit ɗin dake jikinsa, amma kuma ai kwana kin da take ganinsa a tsallaken makarantarsu ba baƙaƙen kaya ba ne. Sai kuma ta taɓe bakinta kaɗan tana ƙarasawa kusa da shi.
“Ina kwana”
Ta gaida shi tana kallonsa, ba tare da ya kalleta ba ya amsa mata da:
“Ummm”
Wai shi ba ya magana ne?, sai kuma ta kawat da komai, ta yi masa tambayar dake ranta tun jiya da ta gama cin abincin da ya kawo mata.
“Babu kayan girki a gidan nan ne ?”
A hankali Kuliya ya juyo ya kalleta, kayan girki?, to me za ta yi da su?, ita nan ɗin wai har wani girki ta iya?, inaaa, shiriritar ta ce kawai, dan a haka idan ka kalleta kai ka ce babbace wadda take da tunani, sai ka yi magana da ita za ka ga tsantsar yarinta. Ba tare da ya amsata ba ya ci gaba da abinda yake.
“Magana fa nake...”
Ya ƙi ko kallonta.
“To ni dai ba na iya cin abincin waje, ina san na yi girki da kaina!”
Still be kalleta ba har ya gama fitar da kayan, ya ware mata wasu robobi biyu, sannan ya tura mata.
“Ki ci ɗaya yanzu, and you can take the other one to school”
“Yanzu fa na ce maka ba na iya jurewa cin abincin waje...”
Ba tare da ya ko kulata ba ya ɗauki nasa, sannan ya yi corridor.
*
Tafe suke a motarsa, yayin da Kuliya ke tuƙa motar Sharon da ta ba ahi aro a kwanakin, dan har yanzu bai samu damar siyan wata motar ba, tasa kuwa da ma bai ƙara bi ta kanta ba.
Da yake yasan makarantar tasu, kansa tsaye can ya dosa, har cikin makatarantar ya shiga, sannan ya yi parking a harabar makarantar.
Ba tare da ta kalleshi ba dan fushi take da shi , Mishal ta buɗe motar za ta fita.
“Da ƙarfe nawa kuke tashi?”
Ta juyo ta kalleshi tana turo baki gaba, ciki-ciki ta amsa masa da:
“Ƙarfe biyu, idan kuma ina da class ɗin kungu fu sai ƙarfe uku muke tashi...”
So yake ya tambayeta a wasu ranaku take da ajin kungu fu ɗin, amma sai miskilancin dake cikinsa ya hana, ba tare da ya sake cewa komai ba, ta ja jakarta ta fita.
Ya bi bayanta da kallo har ta shige can cikin makarantar. Ya ɗaga kafaɗarsa sama yana furzar da iska, Allah ya haɗashi da mata. Amma ba komai, zai yi ƙoƙarin daure duk wata shirirtarta, zai san yanda ya yi ya ɗorata a hanya, don zai iya yin komai saboda Abubakar.
_____________________
_Jama'a, kun ji fa dramar dake faruwa a cikin wanga tahiya_
_To... Ga Kuliya ango, ga kuma Mishal amarya😂😂. Dan Allah ya kuka ga yanayin zaman nasu?_
_To Mama ta shilla zuwa Ingila, sai ki taya ta da addu'a_
_Ga kuma oga Raja ma anasa ɓangaren, yana nan yana gina mana soyyayar Rabi a zuciyarsa_
_Wani ya faɗa min ina labarin nan ya dosa?_
#Labarinsu
#SalmaAhmadIsah
#TaurariWriters*LABARINSU*

LABARINSUWhere stories live. Discover now