LABARINSU 11

39 1 0
                                    

*LABARINSU*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*TAURARI WRITERS*
*11*
~~~
*Let's never forget, it's you and me vs problem, not me vs you...*
***
Follow my Wattpad account 👇
https://www.wattpad.com/user/Salma_Ahmad_Isah?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
*Brickhall school, Kaura District, Abuja*
RABI'A POV.
Tsaye take a kusa da filin buga ball na makarantar, daga nesa take leƙen yaran da suke buga ball a cikin filin, ji take kamar ita ma ta shiga cikinsu don a buga wasan tare da ita, amma ba hali, tun da ko kusa da su ma ba ta isa ta je ba.
“Ke 'yar aiki!, Me kike a nan?!”
Ta juyo da sauri tana kallon mammallakin muryar, wasu yara ne maza su uku, sanye cikin kayan sport na ball, kuma ta san 'yan wani aji ne, 'yan ss2 ne, ta na zuwa shara ajinsu, kuma a duk sanda za ta shiga ajinsu sai sun ci zarafinta. Da ƙyar ta haɗiyewa wani abu, sannan ta ce.
“Ba... Ba komai”
“Ƙazama kawai! Bar nan!”
Ɗaya daga cikin yaran ya faɗi.
“Dan Allah dubeta, kamar wata jaka, wai ƙwallo take san bugawa, in banda daƙiƙiya wa ya faɗa miki cewar matan arewa sun iya ball?!”
Suka kwashe da dariya suna tafawa, Rabi ta juya za ta bar wurin jiki a sanyaye, sai ta ci karo da Mishal, wadda ke tsaye a bayansu ta na jin duk cin mutuncin da sukewa yayarta. Farin cikin ganin Mishal ɗin ya mantar da Rabi cin zarafin da aka mata yanzu, dan ta haura sati rabonta da ita.
Sai dai yanayin fushin dake kwance a kan fuskar Mishal ɗin ya hanata yin komai, Misal ta ci gaba da kallon Rabi'a, hannyenta harɗe a ƙirji, kafi ciki ɗacin murya tace.
“Seesee!”
Rabi'a ta kasa amsawa. Mishal ta sa hannunta ta janyo Rabi'a zuwa bayata, sannan ta taka har gaban yaran ta fuskance su.
Yaran da suka tsorata dan ganin Mishal suka fara ja da baya. Amma sai ta kamo kwalar ɗayansu, sannan ta kai masa mari, ta mangareshi harda haɗa masa da naushi a ciki, ta durƙusar da shi a kan gwiwoyinsa, sannan ta kamo ɗayan ma, shi ma marinsa ta yi, kafin ta durƙusar a shi, haka ta yi wa na ukun ma. Ta ja da baya tana tattare hannun suit ɗin jikinta.
“Oya! Ku bata haƙuri!”
Tsaresu da ta yi da idanu yasa jiki na rawa suka kalli Rabi'a, a tare suka bata haƙurin.
Rabi da ta gama tsinkewa da lamarin Mishal ta kasa ko motsi, wai ahse da ma haka Mishal take?.
“Seesee! Did you accept their apologies?”
Rabi'a ta yi saurin gyaɗa mata kai tana dubanta.
“Ku tashi ku ɓace min da gani”
Jiki na ɓari suka miƙe, har da gudunsu wurin barin wajen.
“Seesee kina san ball?”
Mishal ta tambaya tana kallon Rabi'a, a sanda suka zauna kan ɗaya daga cikin kujerun 'yan kallo dake wurin wasan. Rabi ta kalli filin ball ɗin, sannan ta sauƙe dubanta kan Mishal.
“Ina san na buga... ball wani sashe ce na mafarki na... Amma yanzu wannan mafarkin ya mutu, kusan shekaru biyar kenan rabona da bugata, amma har yanzu ina san buga ball”
Mishal ta gyaɗa kanta cike da gamsuwa, ita ma kanta ta iya ball, amma ba ta da wani ra'ayi a kan buga ball ɗin, koyon kungu fu ya fiye mata amfani, tun da tana ga idan ta gama makaranata za ta shiga aikin soja ko na DSS.
“Abu ne me kyau Seesee, kuma ina san na ga mutum ya tsaya a kan ra'ayinsa, musamman ma mu da muka kasance 'yan arewa, wani yanki da ba'a cika bawa mata hakkin kansu ba, a mafiya yawancin lokuta a arewa ana dannewa mata hakkinsu. A wasu lokutan ma za ki ga iyaye ne ke hana yarinya abun da take san yi, wata ƙila dan maganar mutane, ko dan suna so su aurar da ita, ko kuma dan suna ganin hakan ya saɓawa al'adarsu... Kuma hakan na ɗaya daga cikin abubuwan dake kawo mana koma baya a Nigeria, shi ya sa kudu suka fi mu ta ko wani fanni... Mu da muke da yawan addinin musulunci, addinin da bai tauyewa 'ya mace hakkinta ba, amma kuma al'adu sun danne hakan... Kin ga yanzu kamar wannan ball ɗin da kike san yi, a gaba ɗaya tarihin ƙungiyar ball ta mata a nigeria, 'yar arewa bata taɓa buga ball ba, ban ce babu masu so ba, akwai waɗanda suna san wasan, amma kuma an hana su, ana ganin kamar ball wasan maza ne, yanzu idan kika duba 'yan wasan super falcons, duka 'yan kudu ne, daga yarbawa sai iqbo, musulman cikinsu ma yan kudun ne, babu 'yar arewa ba haushiya ko ƙwara ɗaya... Insha-Allah Seesee zan baki goyon baya, idan har kin tabbatarwa da kanki cewar za ki iya, i will support you”
Rabi'a ta yi shiru, ta tsirawa 'yar ƙaramar Mishal ɗin dake gabanta ido, ta yi tunanin sam Mishal ba ta da wayon da za ta iya yin magana kamar haka, duk zantukanta shiririta take ɗaukarsu. Bisa ga mamakinta sai ta ga Mishal ɗin ta na dariya.
“Kin ji ni ina ta zuba ko?... Ni ma ban san daga ina zancen yake ta zuwa ba... Kwai ina jinsa ne a baki ne”
Suka kuma yin dariya a tare.
“Me yasa ba ki zo school ba wancan satin?”
“Yayana ne ya rasu, sai kuma auren da aka min!”
Rabi ta kasa ganewa abun da take ji, yayanta da ta tace shi kaɗai ne ya rage mata ta ke faɗin ya mutu, kuma ba ma haka ba, wai an mata aure?, Aure?, Kuma wai duk hakan ma ya faru ne cikin sati ɗaya da wasu 'yan kwanaki.
“Kin ji abun wani banbarakwai ko?, Yayana ma'aikacin DSS ne, sun fita wani aiki, sai aka harbeshi, abokan aikinsa suka kaishi asibiti, kuma kafin ya rasu sai da ya bayar da aure ne ga wani abokinsa... Ni ma ban san da zancen ba, sai jiya da wani kawunmu ya zo yace wai mijina ya zo ɗaukata, yanzu haka ma shi mijin nawa ne ya kawo ni makaranta”
Iko sai Allah, da ma irin haka na faruwa?, Rabi ta tambayi kanta. Ta ɗora hannunta a kan kafaɗar Mishal.
“Ki yi haƙuri kin ji ƙanwata, ki ɗauki abun da ya faru da ke a matsayin ƙaddara, kowa yana da tasa kalar ƙaddarar, Allah ya ba ki ikon ɗaukan ƙaddararki, mijinki kuma ki masa biyyaya, ki bishi sau da ƙafa”
Mishal ta yi murmushi tana sosa kanta.
”Aure?, Seesee abun mamaki yake ba ni, wai ni ce da aure?”
Rabi'a ta yi murmushi. Saboda tuna irin farin cikin da suke kwana su tashi da shi ita da Anti Saratu a kwanakin nan, ba fon komai ba, sai don sabon saurayin da ta yi.
_“Na kasa yarda Rabi, wai ni... Ni ce zan yi aure?, Aurena fa yace zai yi Rabi, aure?!”_
Abun da Anti saratun ta faɗa mata ke nan jiya, bayan da Fu'ad ɗin ya zo ya sanar mata da cewar shi aurenta yake san yi, kuma a shirye yake. Babban abun farin cikin ma shi ne, Kawu Habu yayan Abbansu ya yi bincike a kan Fu'ad ɗin, kuma an tabbatar masa da kawawan halaye da ɗabi'unsa.
“Da ma haka abun yake ƙanwata, kana naka Allah ma ya na nasa, amma idan aka yi haƙuri aka jure, komai zai dawo dai-dai, ke dai ki yi haƙuri da abin da za ki gani a gidan auren ki, ki ji, ki ƙi ji, ki gani, ki ƙi gani, ki yi haƙuri, sannan ki riƙe addu'a...”
Mishal ta shafi gefen fuskarta.
“Seesee shi fa mijin da aka aura min ɗin, ba ya yawan magana, sai ya yi ta cin kunu, ni ba na gane kansa”
“Haƙuri dai ake ƙanwata, wannan shi ne auren, idan ki ka daure zai dena fushin, har ya riƙa zama yana miki hira”
“Wai da gaske ?”
Cike da tabbatarwa Rabi ta gyaɗa mata kai. Kuma daga haka ta shiga mata nasihu kala-kala, irin waɗanda Anti Saratu kan mata a lokuta da dama.
KULIYA POV.
Tsaye yake a harabar wani wurin saida motoci, yayin da ɗaya daga cikin ma'aikatan wurin ke ta nuna masa kalar motocin da suke da su a wurin.
“Wannan fa?”
Ya faɗi a yayin da ya nuna wata Audi RSQ. Ma'aikacin ya kalleshi.
“Ranka ya daɗe wannan fa tana da tsada sosai”
Nan take Kuliya ya hango kansa a cikin zuciyarsa yana kashe sauraye a fuskar mutumin. Kuma ba tare da wani tunani ba yace.
“Ka ga na maka kama da wanda ba zai iya siyan motar ba ne ko me ?”
“Haƙuri ranka ya daɗe, ba haka nake nufi ba...”
Kuliya ya masa baza ya juya ya nufi hanyar fita, da gudu mutumin ya bi bayansa yana bashi haƙuri, amma haka ya ƙi ko kallonsa bare ya amsa, ya riga ya yi zuciya, ba zai siyi mota a wurinsu ba.
Haka ya fita daga wurin, ya nufi wani wurin da ban, a inda ya je ɗin ne ya siyi wata baƙar Honda Breeze. Sannan kai tsaye ya wuce wurin aiki. Ƙarfe biyu dot, ya tashi don ya je ya ɗauko Mishal, ba wai don lokacin tashin aikinsa ya yi ba, sai don yasan babu wanda zai ɗauko ta idan ba shi ba, shi ɗin da a yanzu yake amsa sunan mijinta!.
A harabar makarantar ya yi parking, ya na raba idonsa a kan ɗaliban dake ta tunkuɗowa daga cikin makarantar. Ya kwashe kusan minti goma zaune cikin motar, kafin ya hangota tana tafiya ita da wasu mutum biyu, be damu da kallon waɗanda take tare da su ba, tun da Allah ya sa ya ganta ai shikenan.
Ya san ba gane shi za ta yi ba, tun da ba waccan motar da ya kawota ba ce, shi yasa ya fito daga cikin motar, ya fara takawa zuwa wurin da suke. Zuwa lokacin ɗayar ta tafi, saura su biyu.
A tare Rabi da Mishal dabkuma Angelica suka fito daga cikin makatarantar, kafin Angelica ta musu sallama ta tafi, suna tafiyar ne kuma suka ga mutum tsaye a gabansu.
Kusan a lokaci guda suka kalleshi, gaban Rabi ne ya yi wata mummunar bugawa, ganin wani mutum, wani sak... sak Raja, nan take ƙwaƙwalwarta ta wasto mata hoton ranar da ta tsinci wallet ɗinsa, har ta buɗe taga hotonsu su biyu, tabbas wannan ɗan uwansa ne, ɗan uwansa dake matuƙar kama da ita da kuma shi Rajan kansa.
Mishal kuwa kallonsa ta shiga yi, daga ta kalli Rabi, sai shi ma ta kalleshi, sai a lokacin ya kalli wadda suke tare. Allah ne kaɗai yasan cikin wani irin shock ya shiga, wata fuska yake gani, wadda zai iya cewa ta Mommansa ce, fuskar sak ta Zaid ɗinsa, Zaid ɗin da ya rabu da shi na tsayon shekaru masu tarin yawa, wannan fuskar da kammaninta ke kwance a kan tasa fuskar. Ƙwaƙwalwarsa ce ta hautsina, sannan ta kuma hautsunawa, tunaninsa ya birkice, ya kasa gane shin mafarki yake, ko kuma zahiri ne?. Bakinsa yana rawa ya kalleta tun daga sama har ƙasa. Zuciyarsa na bugawa da sauri.
“Ka santa ne?”
Mishal ta faɗi tana dubansa, me makon ya bata amsa, sai ya kalleta kawai, sannan ya haɗiye duk wani mamakin da yake ciki, ya ɗaga kafaɗarasa ta dama.
“Zo mu tafi!”
Allahu ƙadirun ala man ya sha'u, hatta da muryarsa sak irin ta Raja ce, sai dai akwai wani abu ɗaya da ya banbanta muryoyin nasu; muryar Raja na fita cikin sanyi da taushi ne, ta wannan kuwa ba ta da wannan sanyin, sanna babu innocent a cikin muryarsa.
Da sauri ya juya ya nufi motarsa, ba tare da ya jira Mishal ɗin ba.
“Seesee kin san shi ne?”
Mishal ta tambaya tana kallon Rabi'a, wadda ta bi bayan Kuliya da kallo.
“Ba shi na sani ba, wani ne da ban!... Ki je ya na jiranki”
Cewar Rabi'a, bayan da ta gama tabbatar da cewa duk yanda aka yi wannan me kama da Rajan shi ne mijin Mishal ɗin. Ba tare da Mishal ta ce komai a kan maganar Rabi ta farko ba, ta gyaɗa mata kai, tare da mata sallama ta nufi motar ta shiga, kuma ba jira Kuliya ya figi motar a guje kamar yanda ya saba, suka bar cikin makarantar.
Kamar yanda Mishal ta saba ganinsa haka yau ma ta ganshi, jingine jikin gate ɗin wannan estate ɗin dake tsalleken makarnatarsu, ba shiri ta juyo ta kalli wanda ke zaune a gefenta, sannan ta juya ta kalli na jikin gate ɗin a lokacin da suka wuce layin.
Kanta ya kulle, saboda sau a yau ta gano banbancin da suke da shi, wancan na jikin gate ɗin yana da zaje da kuma ɗan gemu kaɗan, wannan na zaune a gefen nata kuma, ba shi da gemu ko kaɗan, sannan ƙwayar idon wancan gray ce, yayin da wannan tasa take baƙa.
To me yake faruwa?, shin su 'yan biyi ne ko me ?, sun san da zaman junansu ?, ta ina suka haɗa alaƙa da Seeseenta?. Gaba ɗaya tambayoyin su ne suka cika kanta fal!, ta kasa banbance fari da baƙi, har hakan ya sa ba ta lura da irin gudun da Kuliya ke shararawa da su ba.
Ba ita kaɗai ba ce kanta yake a kulle, hatta da Kuliyan shi ma kansa a kulle yake, ya kasa ganewa abun da yake shirin faruwa, rayuwarsa ta baya da yake ta kokawar mantawa da ita, ita ce ke dawo masa bayan ganin wannan fusakar, wacece ita?, me yasa take kama da su?, a ina Mishal ta santa?, don kayan jikinta ba kalar na 'yan makarantar ba ne, bare yace makarantarsu ce ɗaya. Ya rasa takamemen tunanin da zai kama. Tunaninsa da nutsuwarsa suka sake dugunzuma fiye da da.
Ruɗani da cukurkuɗaɗɗun zantunka da tunanika suka yi wa ƙwaƙwalwarsa tsinkaye, ya kasa tantance meke shirin faru, wata ƙaddara ce za ta haɗa shi da wannan yarinyar?, wadda ke ɗauke da kammanin fuskarsa da ta Momma da kuma Zaid.
Har suka kai gidan babu wannda ya samu amsa ɗaya daga cikin tarin tambayoyin dake kawunansu, parking ya yi a harabar gidan, kuma kusan a tare suka fito,amma shi ya rigata shiga cikin gidan.
Me aikin da ke masa aikin shara da goge-goge ce kawai a gidan, da can ba wai shi takewa aikin ba, 'yar aikin gidan Anna ce, kuma Annan ce ta sakata ta riƙa zuwa gidan nasa duk sati tana masa shara. Kuma shi kullum ba ya dawowa gidan sai bayan sallahr isha'i, ha kan ya da ko kalarta bai sani ba sai yau.
Ita ma a ruɗe ta shiga dubansu su duka, don ba ta taɓa ganinsa ba sai yau, kullum haka za ta zo ta yi aikinta ta fi, ko a gidan Amman ba haɗuwa suke ba, yau kuma sai ga shi ya dawo gidan a lokacin da ba ta taɓa zata ba, kuma ba shi kaɗai ya dawo ba, harda wata yarinya tare da shi.
Mishal ta kalli matar a sanda take gaisheta, amsawa ta yi tana maida mata martanin gaisuwar, hanyar corridor ta kama, amma sai muryarsa ta dakatar da ita.
“Zan koma wajen aiki, anjima kaɗan za'a kawo miki abinci...”
Daga haka ya juya ya fice, Mishal ta bi bayansa da kallo.
Ba tare da tace komai ba, ta nufi ɗakinta, tunani da yawa birgit a ranta, wanka ta yi, ta sauya kaya zuwa wani distressed jeans, da wata peach long sleeves tees, ta saka sliders ɗinta ta fito, kanta ko ɗankwali babu, sai band ɗin da ta saka a tsakiyarsa. A parlo ta zauna tana kallo, har zuwa lokacin da me aikin ta gama aikinta.
“Ranki ya daɗe ni zan wuce”.
Mishal ta janyo idonta daga kan Tv ta kalleta.
“Ina za ki je?”
Matar ta ɗan sosa ƙeya tana faɗin.
“Gidan Anna zan koma, ai da ma nan ɗin shara kawai nake zuwa na yi”
Mishal ta gyara zamanta.
“Wacece Anna kuma?”
Mamaki ya kama matar me suna Rahila, ta ya za ta auri ɗan mata, kuma tace ba ta santa ba.
“Ita ce babar me gidan naki”
Babarsa?, kenan ya na da 'yan uwa, to duk yanda aka yi ya san da zaman wannan ɗan uwan nasa. Kuma kafin ta ƙara cewa komai, aka ƙwanƙwasa ƙofar falo, ita ce ta bada izini, me gadin gidan Ilu ya shigo, hannunsa riƙe da ledojin abincin da aka kawo daga restaurant ɗin da suka saba kawowa Kuliya abinci. Har cikin falon ya shigo, ya aje mata abincin a gabanta, sannan ta sallame shi.
“Ki zauna mu ci abinci, sai ki wuce”
Ba musu Rahila ta amince, ta zauna har Mishal ta miƙo mata abincin, ita kuma Mishal ɗin ta miƙe, ta shiga neman Ayra, har ta samota a kitchen, ba ta fita ba sai da ta bi kitchen ɗin da kallo, babu komai a ciki sai coffee maker da kuma stove, sai kayan shayi. Ko da ta buɗe firdge ma duka kayan gwangwami ne a ciki.
Ba tare da ta taɓa komai ba, ta fito ta dawo falo ta shiga cin abincinta tana bawa Ayra.
Rahila sai satar kallonta take, wato kowa da kalar yarintarsa, ita kuma wannan kalar tata kenan.
Sai ƙarfe 09:00 dai-dai Kuliya ya kamo hanyar barin headquarter, kuma kai tsaye gidan Anna ya nufa.
“Ɗazu Rahila take faɗa min cewar yarinyar tana da kirki, dan bata barta ta dawo ba ma sai da suka ci abinci”
Cewar Annan, bayan ya isa gidan. Girar Kuliya ta haɗe guri guda, alamun kokwanto.
“Wacece Rahila?”
Anna ta yi 'yar dariya.
“Me aikina”
“Oh na gane”
Kafin kuma ya sake cewa komai, Siyama wadda ta dawo gidan Anna a yau da safe ta bayyana a falon, kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kai, dan sai a yanzu ma maganar da ya saurara tsakaninta da yayarta ta faɗo masa a rai.
Anna ma binta da kallo ta yi, tana mamakin irin halin Siyaman, zuwa yanzu ya kamata a ce ta cire Kuliyan a ranta, tun da ta riga da ta ji cewar ya yi aure, amma duk da haka ba ta haƙura ba, neman wata hanyar da za ta cusa kanta gareshi ma take.
Cike da so da ƙauna Siyama ke kallon Kuliya, don ba za ta iya kwatanta yanda zuciyarta ke fama da ciwon sansa ba, a koda yaushe cikin raunata zuciyarta yake, amma hakan ba ya hana sansa ƙara ninkuwa a zuciyar tata, a duk sanda zai yi wani abu don ya bata haushi, to a lokacin yake ƙara burgeta.
Kanta a ƙasa ta kama hanyar shiga kitchen, ba wai dan akwai abun da za ta yi a can ɗin ba, sai dan kawai ta shiga kitchen ɗin ta laɓe, ko za ta samu damar sauraron muryar sahibin ranta.
Kuliya ya kamo hannun Anna ya matse, a sanda ya tabbatar da Siyama ta bar falon, jin hakan yasa Anna ta tattara gaba ɗaya hankalinta kansa. Ya ɗaga kafaɗarsa, sannan yace.
“Anna... Yau na ga wata me kama da Mommana, me kama da Zaid ɗina, kuma me kama da ni!”
Wani irin shiru ne ya ratsa falon, yayin da babu ƙarar abun da ke tashi sai na tv dake a kunne, sai kuma ƙarar acn dake fita a hankali, kuma da a ce Kuliya ya kasa kunne sosai, da ya ji sautin bugun zuciyar Anna, yanda take kallonsa kawai shi ne zai shaida masa kalar tashin hankali da mamakin da take ciki.
Siyama dake kitchen ta ɗora hannunta a kan bakinta, yayin da zuciyarta ke tambayarta; shin da ma Kuliya na da wasu 'yan uwan bayan Anna?, ita dai haka ta taso ta ganshi a gidan Anna, kuma ce mata aka yi maraya ne da Annan ta samoshi a tsohon gidan marayun da ta taɓa aiki.
*Shekarata 2000*
Aliyu ne zaune kan wani benci da ke Garden ɗin gidan marayun da aka kaishi, matar da ya saba da ita cikin kwana uku kacal me suna Rahama na aikin share garden ɗin, jifa-jifa Rahaman da tace ya riƙa kiranta da Annan ke masa hira.
Sai dai shi kuma gaba ɗaya hankalinsa ba ya kanta, hankalinsa ya karkarta kan ɗan uwansa da ya shafe kwana uku ba tare da shi ba.
Babu kowa a garden ɗin, daga Annan sai shi, saboda gaba ɗaya yaran gidan na ajin ɗaukar karatun Alkur'ani.
Wata iriyar ƙara da ta cika wurin ce ta sa Anna da Aliyu firgita, a kiɗime suka dubi ginin wurin. Wanda ke taci da wuta.
Wata kalar ƙara haɗe da salati Anna ta saki, tunawar da ta yi kowa na gidan na cikin ginin, babu kowa a waje sai ita da. Wannan ɗan marayan Allahn.
A dugunzume ta ja hannun yaron suka yi waje, sannan ta shiga neman ɗauke, har aka samu wanda ya kira 'yan kwana-kwana, aka zo aka kashe wutar, amma babu wanda ya tsira a cikin gidan, tun daga kan yaran gidan har ma'aikatan.
Ba Anna kaɗai ba, hatta da Aliyu da bai jima da zuwa gidan ba sai da abun ya taɓashi, haka gwamnati da sauran masu faɗa a ji suka riƙa sintiri a gidan marayun, kafin daga bisani aka rufe shi.
Tun bayan faruwar lamarin Anna ta ɗauki Aliyu suka koma gidan wata ƙawarta a nan garin  Kano, kasancewar da ma da ta zo garin a nan ta sauƙa.
Bayan da ta gama haɗa kuɗaɗenta na mota ta ɗauki Aliyu suka koma mahaifarta Abuja, inda mijinta da 'yan uwanta suke.
Da ma can nemawa mijinta kuɗin da za'a masa tiyata ne ya sa ta zo garin kano neman aiki, har Allah yasa ta samu a wannan gidan marayun.
Kai tsaye gidan mijinta ta wuce da Aliyu, kuma da isarsu ta zauna ta masa bayanin inda ta samu Aliyu, be musa mata ba, haka ya amince da zaman Aliyun tare da su, ya tiƙe Aliyu kamar ɗan da ya haifa, kasancewar Allah bai taɓa basu haihuwa ba. Haka Aliyu ya ci gaba da zama a gidan Anna. Wadda ita ce ke kula da kaf nauyin gidan nata, kasantuwar shi mijin nata ba shi da lafiya, har makaranta ta saka shi, bayan da ta samu aikin dafa abinci a wani restaurant, da albashin da suke bata take kula da kaf matsalosalun gidanta.
Anna ita ce wadda ta ƙarawa Aliyu sunan Bhici a gaban sunansa na makaranta, kasacewar mijinta hifaffen garin Bhicin jahar Kano ne. Shi kuma mijin nata shi ne yake kiran sa Kuliya, saboda yace halayensa kaf irin na wani ƙaninsa ne da ya rasu, kuma sunan kanin nasa Kuliya!.
Har zuwa lokacin Zaid na maƙale a ran Aliyu, sau tari yakan keɓe kansa ya sha ƙuncin kewar yayan nasa. Da haka har ya kwashe shekaru biyar tare da su Anna, a cikin wannan shekaru biyar da suka shuɗe, Allah ya yi wa mijin Anna rasuwa, sakamakon jinyarsa ta ciwon ƙoda da ya kasa sakun sauƙinta.
Haka Anna ta ƙara rungumar Aliyu a matsayin wanda ya rage mata, ta manta da cewar shi ba ɗanta ba ne, ta manta da cewar ba ita ta haifeshi ba, ganin bayan mijinta da 'yar uwarta ba ta da kowa, kuma ga shi mijinta ya rasu, sai ƙanwar tata da kuma shi Aliyun.
Lura da Anna ta fara yi da yanayin damuwar da Kuliya ke ciki ne ya sa ta ritsa shi da tambayoyi, har ta samu nasara a kansa, ya bayyana mata abun da ke cin ransa.
Da haka ta masa alƙawarin za ta je har Kano tare da shi don su duba ɗan uwansa. Sai de me?!. A sanda suka isa Kano suka je gidansu Aliyu na da, basu iske kowa a cikin gidan ba, hakan ya sa Aliyu da kansa ya shiga gidansu Naufal ya tambayi Maman Naufal ɗin, shin ta san inda ɗan uwansa yake?, kuma Maman Naufal ɗin ce ta sanar masa da cewar ai rana ɗaya suka tashi suka ga babu Zaid ya gudu.
Jiki a saɓule cikin tashin hankali da sallalami Anna ta dawo Abuja da Aliyu, kuma tun daga lokacin yanayinsa na shiga ƙunci ya ƙaru fiye da da. Babu yanda Annan ba ta yi da shi ba, kan ya dawo yanda yake amma ya ƙi. Har ta haƙura ta zubawa sarataura Allah ido.
Bayan da Kuliya ya kammala secondary, Anna ta ƙuƙuta ta sa ma masa gurbin karatun diploma a wata makaranta dake cikin garin Abuja. Bayan ya kammala diplomar ne ya shiga fafutukar neman aikin da suka taso cikin burin yinsa shi da ɗan uwasan, aikin da Momma ta ƙarfafa musu gwiwa a kai, tun suna ƙananu suka yi wa kansu alƙawarin yin aikin DSS!.
Sai da ya gama shan wahalar neman aikin, kafin Allah ya sa wani ɗan uwan mijin Anna ya kawo masa offern aikin DSS ɗin. Da an ce mutum na da hannaye shida, da Kuliya ba zai yarda ba, amma a sanda aka ba shi offern zai iya cewa ya ga hannayensa sun nunku daga biyu zuwa shida wajen karɓar takardun, ya yi matuƙar farin ciki da samun aikin.
Kuma ba tare da ɓata lokaci ba ya shiga aiki gadan-gadan, bayan da aka musu training, ƙwarewarsa kan aikin da kuma gaskiya da maida hankali ne yasa shi samun nasarori da dama, tare da samun ƙarin girma cikin ɗan ƙanƙanin lokaci.
*Present day...*
RAJA POV.
_🎶...We're not in love..._
_We share on stories_
_Just something in your eyes..._
_Dont be afraid..._
_The shadows know me_
_Let's leave the world behind...🎶_
Waƙar da yake saurare kenan, ta cikin headphones ɗin dake saƙale a kunnensa. Jingine yake jikin gate, idonsa a kan ƙofar gate ɗin makarantar tasu.
Ya na kallon sanda ƙafafunta suka fito daga cikin gate ɗin, kuma zai iya rantsewa kan abu na farko da ta fara kalla daga fitowar tata shi ne.
Ya ga sanda ta yi wani siririn murmushi, shi ma kuma martanin murmushin ya mata, sannan ya miƙe a kan ƙafafunsa, ya fara takowa zuwa inda take tsaye, wato ƙofar makarantar. Hannunsa ya kai ya tura headphones ɗin ƙeyarsa. Tare da ɗan ɗaga kafaɗarsa ta dama.
“Mu je ba?”
Tana wannan sirirn murmushin ta fara tafiya, yayin da shi ma ya jera tare da ita, be san me ya sa ba, amma bayan son sanin asalinsa ta dalilinta, yana san samun kusanci da ita, sai dai ba ya jin abun kamar yanda Rhoda ke faɗi ne, da ta ce wai ya na santa ne, shi sam bai ga hakan ba, kawai dai ya na jin son wannan haɗuwar da suke, don idan weekend ya zo ba ya jin daɗi, shi da za'a bi ta tasa ma da an dena yin weekend ɗin. Sai kuma ya yi wa kansa da kansa murmushi.
Da ya hango tarin ɗaliban da ba sa son zuwa makaranta, wasu ma ba su da lokacin hutu sai wannan weekend ɗin, wata ƙila idan suka ji wannan batun nasa sai  sun naɗa masa na jaki.
“Yau ina Rhoda?”
Muryar Rabi'a ta faɗi bayan wani lokaci. Kamar me neman Rhodan, sai da ya waiga bayansa ya kalli ƙofar Estate ɗinsu, sannan ya juyo da kansa yana kallon hanya.
“Yau ba ta zo tsurkun ba”
“Ku kaɗai kuke rayuwa a gidan naku ne?”
Sai da ya ɗan kalleta, sannan ya amsa mata da.
“Eh, amma akwai wasu abokai na guda uku, mu 'yan Kano ne, aiki ne ya kawo mu Abuja, kuma da zarar mun gama za mu koma”
Sai ta gyaɗa kanta. A sanda take ƙara tabbatarwa da kanta duk yanda aka yi bai san da zaman mijin Mishal ba, amma sai dai idan matsala suka samu, har ta kaisu ga rabuwa, ko kuma dai sun rabu ne ba tare da sani ba, ma'ana ko ɗaya ne ya ɓacewa ɗaya. To ita yanzu mamaki da ruɗanin sai suka zame mata biyu, tana san sanin wace alaƙace tsakaninta da su, tana kuma son sanin abinda ya raba waɗanan 'yan uwan biyu, amma ba ta san ta inda za ta fara ba.
Kawai sai ta tare shi tace masa ta ga ɗan uwansa?, to idan kuma da ma ya san da zaman ɗan uwan nasa fa?,ya kammata ta fara sanin abun da ke tsakaninsu tukkuna, ta na buƙatar sanin farkon LABARINSU, kafin ta san wani mataki ya kamata ta ɗauka a kan lamarin.
“Ke fa?, tare da wa kike rayuwa?”
Wannan innocent muryar tasa ta faɗa, a sanda suka tsaya a bakin titi, ta kalli hanya sannan tace.
“Ni da yayata da kuma Ummanmu, kafin Allah ya yi wa yayartawa rasuwa, daga bisani kuma Mamata ma ta rasu, sai kuma na dawo da zama a gidan babana, akwai matar babana da yaranta huɗu, Anti Saratu, Mama, Fatima da Mahmud... Sai kuma shi baban nawa”
“Shi ne yasa kike aikatau a nan?”
Ya tambaya kansa tsaye, kuma ya lura da ta haɗiyewa wani abu, kafin wannan siriryar muryar tata tace.
“A'a, ba babana ba ne, matar babana ce”
Raja ya gyaɗa kansa ya na ƙara tabbatarwa kansa da abun da zuciyarsa ke zargi a kan yarinyar.
Ba tare da ya sake ce mata komai ba, ya tsayar mata mota kamar kullum, ta shiga sannan suka yi sallama. Sai da suka yi nisa, sannan ya juya ya koma layinsu.
Da Rhoda ya fara haɗuwa a bakin ƙofa, ta jingina da jikin ƙofar part ɗinsu tana kallonsa, fuskarta ɗauke da murmushi. Ransa ya haɗe ya na ɗauke kai, ya yi kamar be ganta ba.
Sai da ya zo wucewa ta gefenta, sannan ta ɗaga hannunta tare da saka masa wani fito me ƙarfi, har da wani tafa hannu, hakan yasa ya tsaya yana kallonta.
“Idan na ce you fall in love, sai ka ce ba haka ba, amma ga shi nan kullum sai ka karakata har bakin titi, idan ana cikin weekend sai ka riƙa ɓata rai, dude ko ka yarda... Ko kar ka yarda, ka... Faɗa.. can cikin kogin soyyaya! ”
Raja ya kai hannunsa ya dunguri kanta yana kamo wuyanta. Ya ɗaga kafaɗarsa yana faɗin.
“Cuzzie yaushe kika fara sa ido?”
“Sanda ka faɗa soyyayar gaskiya... Ba irin wadda kake a da ba”
Maganarta ta tuno masa da ita, Uchechi!, Wani sashi na kansa ya ambato masa sunanta, a hankali ya saki wuyan Rhoda, yana tuno alaƙar dake tsakaninsa da ita, kenan da shi ba son Uchechi yake ba?, to kenan da me yake ji a kanta?, kuma me yake ji a kan Ammantasa?. Tukkuna ma wani hali Uchechi ke ciki, tun bayan zuwansa Abuja ba su yi waya da ita ba.
Naushin da Rhoda ta sakar masa a ƙirji ne yasa shi dawowa cikin hayyacinsa, a hankali ya ɗaga kafaɗarsa yana kallonta.
“Tunani ba? Ai da ma sai da na faɗa maka cewar ba son Uchechi kake ba,  kuma ita ma ba sanka take ba, kuɗinka take so, kai ne ka kasa banbancewa tsakanin son gaskiya da na yaudara!...”
Kallon ta ya yi na wasu 'yan sakkani, kafin ya kamo kunnenta.
“Thunder go fire your head Rhoda! Ki ce har zarar zance kika koya?”
“Zaid...”
“Shiru! Ba na san wata magana!”
Sai ta yi shiru tana sosa kunnenta da ya saki, tare da turo masa baki gaba.
“Sorry”
Ta faɗi tana sinne kai ƙasa, janyota ya yi ya mata side hug, kafin ya ɗaga ƙafaɗarsa ta dama yace.
“Ke ɗin ce bakya jin magan Cuzzie... Maza mu je akwai aiki a gaban mu”
Nan da nan Rhoda ta dawo serious, tunawa da ta yi da aikin dake jiransu a gaba, aikin shigo da makaman da Alhaji Bala ya ɗorasu a kai.
*Hotoro, Ring Road, Kano...*
Uchechi ce zaune a ɗakinta, ta sa gabanta yamma tana kallon mirror, yayin da take zaune a kan stool, kallon fuskarta take a mirrorn, yayinda take neman wani abu a fuskarta da wata ƙila shi ya sa Raja yake mata abun da ya so, wata ƙila ba ta da kyau yanda ya kamata, ko kuma akwai wani tabo a fuskarta da ya sa Rajan ba ya san kusantarta.
Ƙofar ɗakin aka turo, kuma ba tare da ta juya ta kalli ƙofar ba, ta hango wanda ta shigo ɗikin, Mesoma ce, yayarta wadda take riƙe da ita. Ba ta juya ba har Mesoman ta zauna a bakin gadon dake bayanta, ta na ci gaba da kallonta.
“Wai Uchechi ba za ki manta da wannan Rajan ba?... Tun da har ba za ki iya sato zuciyarsa ba, kuma ba za ki iya samawa kan ki ruwan da zai kashe miki ƙishin ruwar ki a kansa ba, zai fi kyau ki manta da shi”
Juyowa ta yi ta kalleta.
“Mesoma ina san Raja... Ba na jin zan iya rabuwa da shi, duk munin abun da zai min kuwa, batun samun Raja kuwa zan daure na yi haƙuri har zuwa lokacin da ya tsara mana dan mu yi aure, tun da yace ba zan taɓa samunsa ba idan har ba aure muka yi ba”
Mesoma ta rage girman idonta tana kallon ƙanwarta.
“Hanyoyi nawa na tsara miki na yanda za ki samu kuɗi a hannunsa ?, Da na tsara mikin ba ki samu ba ?”
Uchechi ta girgiza kanta.
“Na samu, na samu abun da ban yi zanton samu ba”
“To me yasa da na tsara miki hanyar da za ki samu kansa ba ki bi ba?”
“Mesoma ba zan iya bin hanyar da kika tsara min ba, waɗannan hanyoyin naki sun yi tsauri da yawa”
Mesoma ta miƙe tsaye.
“So... That was the only way that i have, tun da kin ga ba za ki iya bi ba, sai ki yi ta zama cikin ƙunci”
Da sauri Uchechi ta miƙe tana kamo hannunta.
“Ki temaka ki nemo min wata hanyar”
“Ba ni da wata hanya bayan wadda na riga ma baki, idan kin ga za ki iya binta, fine, if not sai ki sa haƙuri a zuciyarki”
Mesoma ta kama hanya ta fice daga ɗakin, cike da neman mafita Uchechi ta koma ta zauna a kan stool, ta furzar da iska daga bakinta. Cike da takaici ta yi fatali da kayan dake kan mirrorn.
To wai ita ya za ta yi ne?, me ya kamata ta yi dan samun kan Raja?, wata hanya ya kamata ta bi don ta mallakeshi?!.
*No.234, Efab Estate, Gwarinfa, Abuja.*
“Wallahi Musa tun muna shaida juna ka kira wannan yaron da kuka aurawa jikata, ya faɗa  mana ina ya kaita! In ba haka ba Wallahi sai nai maka abun da kowa zai zo yana nadamarsa!”
Muryar Jadda ke faɗin hakan cike da masifa, yayin da wayarta ke kare a kunneta, daga gefenta kuma Hajjara ce zaune tana ƙunshe dariyar muguntar dake cinta, dan ita ta kunno wutar.
Suna zaune ne a falon gidan, yayin da Jaddan ke ta sirfawa Ammu Musa buhun bala'i.
“Wai dan Allah Jadda haka ake rayuwa?, Ta ya za ki ce na kira mutum na tambayeshi inda ya kai matarsa?”
Muryar Ammu Musa ta faɗi cike da gajiyawa da halin Jadda.
“Au haka ma ka ce? To ka kyauta, Wallahi za ka ga abin da zan maka, shashasha, wanda bai san inda ke masa ciwo ba!”
Daga haka ta latse wayar ta cillar da ita gefe tana hucin bala'i.
“Gaskiya Jadda Ammu Musa bai kyauta ba, ta ya zai ɗauki 'yarmu ya bawa wani wanda ba musan shi ba? Ba mu sani ba ma wata ƙila ɗan ya kan kai ne?”
Cike da san tittilawa wutar fetir Hajjara ke bayanin, dan har yau ba ta manta da abun da Mishal ɗin ta yi mata ba, gashi dai takaba take, amma baƙin cikin Mishal ɗin bai bar ruhinta ba.
Aiko fiterin da ta bilbila ɗin ya sauƙa a tsakiyar zuciyar wutar, don ta tashi sama ta ƙara ruruwa fiye da yanda take ci a da.
“Aiko ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa, ko ni ko Musa, dan Wallahi ba zan zauna ina gani ya sabautar min da jika ba, duk in da zai je dole ya dawo ya sameni, dan Wallahi ba zan bar garin Abuja ba sai na san gidan da ya kai min jika”
Nan take murnar da Hajjara ke ti ta koma ciki, don kuwa ita ba haka ta so ba, ta so a ce da zarar Jaddan ta gama abun da za ta yi ta kama hanya ta koma Maiduguri, ita kuma a bar mata gidanta ita ɗaya, tun da yanzu ɗayar abokiyar gabar tata ba ta nan, sai ta mulka gidan san ranta, duk da Ammu Musa ya ce idan an yi arba'in za'a raba gado, don akwai dukiyar Mishal da Abubakar ɗin ya ba shi riƙo.
Wutar da take ganin ta hura sai ta dawo kanta,sakamakon mantawa da ta yi ba ta janye hannunta daga saman wutar a sanda ta tittila fetirin ba, Zama da Jadda?, tashin hankali kenan.
_____________________
_Wayyo Allah cikina!🤣🤣_
_Kai jama'a, wai aka ce idan za ka haƙa ramin mugunta, ka gina shi gajere, kuma an ce mugunta sayin faƙo, idan baka iya ba ka ɓata jikinka_
_Ga Uchechi a kan layi..._
_Wani ya faɗamin abun da zai faru a aanda Uchechi ta san cewa Raja ya faɗa soyyaya da wata_
_Sannan ga kuma Jadda a nata ɓangaren, da alama ita ma za'a fafata da ita_
_Ga kuma Uncle Kuliya a gefe, kada fa kumanta da ya ga Rabi'a, wani ya faɗa min meke shirin faruwa..._
#Labarinsu
#SalmaAhmadIsah
#TaurariWriters

LABARINSUWhere stories live. Discover now