LABARINSU 2

32 0 0
                                    
*LABARINSU*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*TAURARI WRITERS*
*02*
~~~
*No.234, Efab Estate, Gwarinfa, Abuja*
*06:00pm*
Me gidan Abubakar Muhammad Auwal, tare da matarsa Hajjara, sai yaransu guda biyu, Hammad wanda ya ci sunan kakansa da kuma fahima, 'yar jaririyar da bata wuce wata biyar ba. Su ne zaune a kan danning table. Wanda ke shaƙe da kayan buɗe baki kala-kala.Da alama jiran kiran sallah suke, dan ƙiris ya rage a kira sallahr.
Ƙofar ɗaya daga cikin ɗakunan falon ce ta buɗe, farko keken guragu ne ya fara bayyana, zaune a kan keken kuma, wata matashiyar yarinya ce, wadda ba za ta wuce 9yrs ba. Kallo ɗaya zaka mata ka ga nakasarta, dan bata da hannaye gaba ɗaya, sannan kanta a langwaɓe gefe guda, bakinta nazubar da yawu.
Mishal ce ta biyo baya,wadda ita ce ke turo keken, sanye take da wata farar linen tunic dress, da kaɗan rigar ta sauƙo gwiwarta, ga kuma rigar ko hannu bata da shi, kanta babu ɗankwali kamar yanda ta saba zama, gashin kanta tifke cikin braid(kalaba) guda ɗaya, ta saka hair band daga sama.
Gaba ɗayansu suka kalli wurin, kuma daga Hajjara har mijin nata basu ɗauke idonsu a kansu ba har suka ƙaraso danning area ɗin.
Kujera ɗaya Mishal ta kawar ta mayeta da keken Firdaus, wadda take kira da Daala.
Sannan ita ma ta samu kejera kusa da ita ta zauna, sai da ta ɗauki tissue ta gogewa Daalan yawun da ya zubo mata sannan ta juyo tana kallon mutanen dake kan danning ɗin.
Hajjara ta kawar da kanta tana taɓe baki, Allah ya sani, har cikin zuciyarta bata san Mishal, wata ƙila dan igiyar aurenta da ta taɓa zama sanadiyyar tsinkewa ne, ko kuma dan rashin kunyar da take mata.
Mishal ta kalli yayanta,wanda shi ma ita yake kallo, hannunta na dama ta ɗago, wanda ke riƙe da envelop, ta miƙa masa.
Abubakar ya girgiza kansa, ya san duk yanda aka yi wani laifin ta aikata, ba yau ta saba kawo takardu irin wannan ɗin ba, hasalima suna nan tili guda yana ajewa, dan sun ma fi yawan report ɗin ta na makaranta da take kawowa. Abu ɗaya ne yasa ba zai cireta daga makaranta ba kwata-kwata, hazaƙarta ce tasa hakan, dan ba ma shi ba, hatta da makarantar suna tinƙaho da ita, gashi de ba wasu shekaru ne da ita ba, amma girman jikinta ne zaisa ka zaci wata babbace.
“Me kuma kika yi ?”
Ya tambaya yana karɓar envelope ɗin, kanta ta sunkuyar, tana wasa da yatsunta.
Murmushi kawai ya yi a sanda ya buɗe ya karanta, dan bi da bi ya gama haddace kalaman da ke ciki, saboda a kullum abu iri ɗaya suke turo masa tun tana junior. Ya rasa irin abunda ke damun ta.
“Hammad yace min yau baki yi azumi ba, bayan shi ma yau yana yi”
Ta ɗago da kanta ta kalli Hammad ɗin dake gefen uw*rsa, kamar yanda bata san uwa*r yaron shi ma haka ta tsaneshi, dan kaf halayen uw*rsa babu wanda bai ɗauko ba.
“Saboda makarantar da nake zuwa ne...”
“Makaranta sai ta hanaki azumi?”
Sai kawai ta miƙe tsaye tana faɗin.
“Bari na je waje.....”
Bayanta ya bi da kallo yana mamakin halin yarinyar, du-du-du ba za ta wuce 17-16 ba, har yau yana tuna yanda ya ɗauketa da hannayensa ranar da aka haifeta, da kuma irin maganar da mahaifiyarsu ta masa a wancan lokacin.
_“Sadiq, ka kula da ita, nasan za ta tashi cikin maraici, bata da kowa sai kai, kada ka danƙa renonta a hannun kowa, ciki kuwa harda Amma (tana nufin mahaifiyarta), ka kula da ita, ka kula da ita......”_
Kuma kalamanta na ƙarshe kenan, a kan idonsa a ka shiga da ita ɗakin tiyata. sai kawai fito masa aka yi da jairiya, aka ce ta haihu, amma ta rasu sai dai babyn da ta haifa.
“Wai haka za'a zuba ido ana kallon yarinyar nan tana abinda take so?.....”
Hajjara ta faɗi a ƙufule, dan Allah ya sani ta gaji da halin yainyar, kuma da ma tun sanda ta ɗora idonta a kan yariyar ta washeta.
“Me ta yi ?”
Ya furta hakan cikin halin ko in kula, yana ninke takardar da Mishal ɗin ta bashi.
“Jiya fa na yi baƙi, baka ga rashin kunyar da ta min a gabansu ba”
“Yarinta ce take damunta, idan ta girma za ta dena”
Haushi kamar ya kashe Hajjara, dan dama abin da ya saba faɗa mata kenan, a duk sanda ta kawo masa ƙarar Mishal ɗin, yau ɗin ma tsautsayi ne yasa ta kawo ƙararta, a ranta ta yi ƙwafa, Allah ya kawo ranar da za ta ga bayan yarinyar nan.
Idonta ya sauƙa a kan Daala dake ta zubar yawu, ita ma yarinyar Hajjaran take kallo. Tawarta ɗaya kenan a duniya, wannan yariyar da Allah yasa ta haifota a nakashe, kuma nakasar yariyar yasa ta gujeta, babu wani abu dake shiga tsakaninta da yariyar irin na uwa da 'yarta, Mishal da Naani ɗin da Abubakar ya ɗauko su ne ke kula da yarinyar har wa yau.
Mishal na fita daga falon gidan BQ ta wuce, dan bata da wurin zama a gidan da ya wuce BQ ɗin, in baka sameta a BQ ba zaka sameta tare da Daala suna wasa, dan Allah ya ɗora mata ƙauna da tausayin yarinyar.
Ganin yanda Hajjara ke bagarar da lamarin yarinyar saboda nakasar dake tare da ita, ita kuma Allah ya hallici zuciyarta da wani irin tausayi, kuma tausayin ne ke sakawa bata da aminan hira a gidan sai masu aikin gidan.
A bakin ƙofar BQ ɗin ta tsaya, tana ƙare musu kallo. Mutum biyar ne zaune a kan bujukura. Ladi, wadda ita ce ke kula da Daala sai mijinta Malam Audu, wanda ke musu gadi, sannan Khalifa, ɗan Mama Ladin na farko, wanda shi ne yake musu sharar garden da ta compound da ma aike idan ya taso, sai Shatu 'yar Mama Ladin ta biyu, sai autar Mama Ladin wato Ummul.
A taƙaice de duka ahalin Mama Ladin ne, waɗan da suka kasance ahalinta ita ma, dan bata da wurin zuwa da ya wucenasu, Shatu kuma ita ce wadda zata iya kira da ƙawarta, Mama Ladi ta zame mata uwa.
“Ah-ah, Hafsatu, ƙaraso mana”
Sai ta yi murmushi har ƙarafunan braces dake saman haƙwaranta na bayyana, tana ci gaba da kallonsu, su ma sai hadaniyar haɗa kayan shan ruwansu suke, a hankali ƙafafunta da babu takalmi suka ci gaba da takawa har zuwa kan bujukurar. Guri ta samu kusa da Shatu ta zauna.
“Yau kin yi azumi ?”
Mama Ladi ta tambaya, yayin da take juye tiyara a cikin wata doguwar roba, Mishal ta girgiza kanta.
“Ban yi ba”
“Haba uwata, sau nawa zan faɗa miki cewar kin isa azumi ?, bai kamata ace ki na shan azumu ba gaira ba dalili ba”
Cewar Malam Audu yana aje radion hannunsa.
“Rabu da ita Baba, ai kullum gaya muku nake cewar yarinyar nan raguwace, amma bakwa yarda” Cewar Khalifa.
Mishal ta turo baki gaba tana sosa kanta.
“Allah ni ba raguwa ba ce, a class ɗin Kungu fu ɗinmu fa kullum ni nake zuwa a farko, kuma watan da ya auce ma saida na karya wani malamin mu....”
Hannunta ta kai ta rufe bakinta, sakamakon suɓul da bakan da ta tuna cewar ta yi, dan tasan yanzu Mama Ladi za ta shiga mata faɗa.
“Kema kin san cewa ba dai-dai kika yi ba kenan, shi yasa kika rufe baki” Cewar Mama Ladin tana miƙawa Baba pure water.
Sai kuma ta sauƙe hannun nata.
“To ai shi ne ya min tsawa, kuma ya dake ni....”
“Ai haƙuri ake uwata, idan kika yi haƙuri sai labari, dan wata ƙila ma kina gama makarantar auren ki za ki yi”
Ido waje take duban Baba.
“Aure fa Baba ?, a'a ni ba wani aure da zan yi yanzu, nawa ma nake da har zan wani yi aure?”
Abinda bata sani ba shi ne, waɗanan kalaman nata zasu mai-maita kansa a cikin kanta kwanaki kaɗan masu zuwa, dan bata da masaniyar ƙaddarar da Allah ya hukunta za ta faru a 'yan kwanaki masu zuwan. Wata iriyar ƙaddara da zata tarwatsa komai, sannan ta zama silar shiryiwar wasu lamura, ta kuma zama silar ɓacin wasu.
A wurinsu ta zauna ta sha ruwa, har sanda su Baba suka fita Sallah, Sai da Mama Ladi ta mata jan ido a kan ta tashi ta je ta yi sallah, dan Allah ya sani, zuciya ɗaya take zaune da yarinyar, ganin ta ɗauketa kamar uwa, shi yasa ita ma ta ɗauketa kamar 'ya.
Saboda rayuwar yarinyar tana buƙatar kulawar uwa, gashi ita kuma bata taso ta samu hakan ba.
Ko da ta koma cikin gidan ɗakinta ta wuce. Wani haɗɗaɗe kuma ƙawattacen ɗaki wanda aka cika shi da kayan buƙata irin na matasa dai-dai shekarunta. Komai na cikin ɗakin peach color ne, sannan ga tarin teddies a ko wata kusurwa ta ɗakin.
Lokarta ta buɗe, da ƙyar ta samu hijabin da ta saka, dan ba saka hijabai take ba, hatta da kayanta yawancinsu ƙananu ne, bata sakka kayan hausawa sam, a cewarta takura mata suke.
Bayan ta yi sallar ta fita falo, a lokacin Daala ce kaɗai, zaune kan kujrarta tana ta gwalantunta, bakinta sai zubar da yawu yake.
Zama ta yi kusa da ita, ta kunna musu tashar mbc 3, sannan ta shiga bata labarin da ita kanta tasan cewa Daalan ba fahimta take ba.
Hammad ne ya shigo falon ta ƙofar ɗakinsa,byana shigowa ya ɗauki remote control ya sauya tasha. A fusace Mishal ta yi kansa.
“Sh*ge ub*n baƙin hali, dan me zaka sauya mana tasha?, dan ka ga ban maka magana a kan munafurcin da ka min ɗazu ba ko?”
Ta ƙarashe tana ƙwace remote control ɗin tare da maida mbc 3n da suke kalla.
“Bar falon nan kafin na karya maka wuya”
Da gudu ya yi sama. Kuma bai tsaya ko ina ba sai a ɗakin Hajjara, wadda ke kwantar da Fahima a kan gado, sakamakon baccin da ta yi. Ƙarya da ƙarerayi ya sameta ya zayyana mata.
Kafin ita kuma ta bazamo ta sauƙo ƙasan ta samu Mishal ɗin tare da balbaleta da masifa, cikin ƙaraji da ɗaga murya take faɗan.
“Wai ke yarinyar nan me kike nufi ?, so kike mu fice mu bar miki gidan ko me ?, to wallahi baki isa ba, shi har gwara shi, tun da nan gidan ub*nsa ne, ke kuma fa ?, sakabu fa kike, to wallahi ki fita idon yarana!......”
Ba komai Mishal ke fahimta cikin kalaman nata ba, sakamakon ciwonta da ya shiga ƙoƙarin tashi, dishi-dishi take ganin komai, numfashinta ya shiga ƙoƙarin ɗaukewa daga ƙirjinta, waccan ranar ta soma dawowa cikin kanfa.
_“Yau daga ni sai ke, kuma babu me ƙwatarki a hannu na!....”_
Abinda ya biyo bayan kalaman nasa sune ya zama silar shigarta cikin halin da take a yau.
Numfashinta ya ci gaba da yin sama, da ƙyar take iya janyo shi. Zuwa lokacin Hajjara ta tuna da ciwon nata, sai ta tsaya a gefe tana kallonta kawai, a ranta addu'a take, kan Allah yasa idan nunfashin nata ya yi sama kada ya dawo.
Mishal ta kai ƙasa tana dafe da wuyanta, sai neman iskar da za ta shaƙa ta ke, duk da sanyin acn dake falon sai gumi take, tuni idanuwanta sun kaɗa sun yi ja, har hawaye ya fara sulalowa ta gefnsu, sai jan nunfashi take kamar me asthma.
Fatan Hajjara bai karɓu ba, dan a dai-dai lokacin da ta faɗi ƙasa gaba ɗaya, a lokacin ne ƙofar falon ta iyo ciki, alamun wani ne zai shigo, kuma bai fi tazarar sakan ɗaya ba, siffar Abubakar ta bayyana a cikin falon.
RABI POV.
Zaune take daga gefe a kan dakalin ƙofar ɗakinsu, yayin da Habiba da sauran yaranta ke zaune a kan tabarma suna kiciniyar shan ruwa.
Ba yau aka saba haka ba, kusan kullum hakan ake, a duk sanda za su taru irin haka, to ita za ka ganta daga can gefe tana kallonsu.
Amma yau ɗin ba kallonsu take ba, tunanine fal kanta, tunani take kan abinda ya faru ɗazu a makarantar da take aiki, abinda ya faru ɗazu tsakanin Malamar nan da yarinyar da ta kira kanta da Mishal.
Yanda yarinyar ta haƙiƙance kan ba za ta kwashe sharar ba, ita da ta mata magana, sai ta ganta a matsayin me sauƙin kai, ashe ba haka ba ne.
Dan da ƙyar ta samu ta tausheta, sannan ta haƙura ta tafi, kafin ita Rabin ta dawo kan malamar ta bata haƙuri, kana ta ci gaba da sharar da ta fara.
“Ni ban ga Abba ba”
Cewar Saratu, kuma maganar tata ce ta dawo da Rabi zahiri.
Habiba ta yi tsaki tana taɓe baki.
“Yana can yawon gantalinsa mana”
“Gaskiya Umma bakya kyautawa Wallahi, kullum ina faɗa miki cewar abinda kike bai dace ba....”
Cewar Saratu, kuma tun kafin ta ƙarashe Mama ta tari numfashinta.
“Eh, me u*a, an taɓo mata ƙahon zuciyarta, yau ni Allah na tuba har na kalli wannan abun na ce shine ub*na?!....”
“Mama ya isheki haka.... Da kike rena shi a yanda yake, gwara shi sau dubu da iyayen wasu, kuma ub*n mutun ko a bola yake kwana indai har shi ne ya haifi mutum ro ub*nsa ne, ko miji bai isa ya amsa sunan uba ba.... Kuma ki sani cewar; da ub*a ake ado.....”
Kuma Saratun na kaiwa nan ta miƙe daga kan tabarmar ta faɗa ɗakinsu har tana ƙoƙadin bangaje Rabi.
“Aikin banza.... Umma mi ye na faɗa ba dai-dai ba ?”
Mama ta tambaya tana tauna doyar bakinta, dan bisa ga dukkan alamu ma ba ta yi azumin ba yau”
“Wallahi baki da laifi, me ake da Ɗan Lami a rayuwa?!, ita ma in ta gaji da abinda ake masa ne a gidan nan,ta yi zuciya ta nemi mijin aure....”
Ita dai Rabi sai ido, dan bata isa ko tari ta yi ba, bata da wani kataɓus a gidan, yau wanda ya kawota ya aje ma bashi da iko da gidan bare ita karan kaɗa miya.
“Umma babu ruwan sanyi fa...”
Habiba ta kalli Fatima, sannan ta kalli ruwan dake aje a can baranda.
“Yanzu ke dan baƙin hali kinsan babu ruwan sanyi a gidan shi ne kika yi shiru, yanzu da an kira sallah fa?”
Ta kawar da kanta.
Habiba ta yi ƙwafa tana cince ƙullin dake gefen zaninta, ta fito da nera ɗari biyu, sannan ta cillawa Rabi.
“Karfa, uw*r 'yan baƙin hali, tashi ki je ki siyo mana ruwan sanyi leda ɗaya, kuma idan kin so ki zauna a can kin ji ?”
Rabi ba tace komai ba, ta miƙe tsaye, sannan ta shiga ɗakinsu ta ɗauki hijabinta, ta fita.
Mama ta bi bayanta da harara.
“Wallahi na tsani yarinyar nan, dan Allah Umma ki koreta ta koma inda ta fito”
Habiba ta yi dariya.
“Baki da hankali Mama, ai idan na barta haka ban amsa sunan Habiba ba, so nake sai ta tagayyara tukunna, ba na  so ta koma wurin dangin uwarta ta ji daɗi, dan kinsan ai 'yan uwan uwar tata suna da kuɗi, so nake sai ta gama lalacewa, so samu ma ta haɗa da cikin she*e, sannan zan sa Ɗan Lami ya koreta daga gidanan, tunda dama ni ce na saka shi ya kawota!”
Mama ta tintsire da dariya, Fatima na na tayata.
Rabi na fita kai tsaye bakin titi ta nufa, a hanya ta tsaya tana kallon wasu yara dake buga wasan ƙwallo.
Ba yau ta saba ganinsu suna ƙwallon ba, kusan kullum a lokaci irin wannan suna buga ƙwallo, a wasu lokutan ma ba su ne suke yi ba, manya ne ke yi a filin, kasancewar ana azumi shi yasa manyan basa bugawa.
Tsaiwarta ta gyara tana ci gaba da kallonsu, ƙwallo na ɗaya daga cikin burukanta na duniya, ƙwallo mafarkin rayuwarta ce, a da bata da wani fata sai na ta zama shahararriyar 'yar ƙwallo.
Sanda Ummanta na raye burin nata ya ɗauko hanyar cika, dan akwai wata football academy da Umman nata ta sakata, kuma kullum tana zuwa yin training, sai dai bayan rasuwar Umman tata komai ya sauya.
Komai ya ruguje, ciki kuwa harda burinta na zama 'yar wasan ball, dan a nan gidan makaranta ma ba'a barta ta je ba, ta ina za'a barta ta wani samu damar tarining.
A gidan kakaninta kuwa cewa suke ai ƙwallo ba wasan mata ba ce, dan haka ita ƙwallo ba ta dace da ita ba, ko a sanda Umman na raye babu yanda ba'a kai ruwa rana ba a kan wannan ball ɗin.
Ganin tsaiwar ba zata kaita ba hasa ta kwashi ƙafafunta ta yi gaba.
*FHA 2 lugbe, abuja*
*11:00am*
Wasu baƙaƙen motoci ne har guda biyu suka yi parking a gaban wani gida cikin layin. Yanayin gudun motocin ne kaɗai zai tabbatar maka da ba lafiya ba.
Ƙofar gaba ta ɗaya daga cikin motocin ta buɗe, wani matashi ya fito a fusace, yanayin yanda yake fitar da iska daga hancinsa ne kaɗai zai tabbatar maka da cewar a fusace yake.
Sauran ƙofofin suka buɗe, sannan ɗaya bayan ɗaya mutanen ciki suka firfito, yanayin shigarsu ne kaɗai zai shaida maka matsayinsu.
Duka sanye suke da baƙaƙen kaya, sannan a jikin kowannensu akwai bullet proof jacket, wadda a jikinta aka rubuta DSS. Na farkon da ya fito ne kaɗai babu bullet proof jacket ɗin a jikinsa.
Kuma shi ne a kan gaba wajen shiga cikin gidan, a harabar gidan suka tsaya. Matashin sai safa a marwa yake, kamar wanda aka ɗorawa maganar duniya. Ɗaya daga cikin ma'aikatan ne ya taho kusa da shi, hannunsa riƙe da bullet proof jacket, a tsorace yace.
“Sir baka saka wannan ba...”
Wani irin kallo da ya masa ne yasa bai ƙarasa faɗin abinda ke bakinsa ba.
Hakan yasa jami'in ja da baya, ya matsa kusa da mace ɗayan dake cikinsu, dan kaf wurin maza ne, ita kaɗai ce mace.
“Ki masa magana”
Kanta ta gyaɗa, sannan ta sofare bingarta ƙirar pistol a aljihun wandonta na baya. Ta sa hannu ta karɓi rigar, ta matsa kusa da shi.
“KULIYA kana buƙatar wannan......”
Sai da ya fitar da wani huci na takaici, sannan ya miƙo hannunsa ya fisgi rigar ba tare da ya kalleta ba, rigar ya saka yana ta hura hanci. Sannan ya yi alama da kawo masa abun magana.
“Ta ko ina gidanan a kewaye yake da jami'an tsaro, zai fi muku da ku miƙa wuyan ku cikin ruwan sanyi, idan kuma ba haka ba!.......”
Ya kai ƙarshen maganar yana haɗe haƙwaran sama da na ƙasa cikin fusata, sai da ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, sannan ya ci gaba.
“Idan ba ku miƙa kanku ba, sai na binne kowannenku da ransa, idan kuma kun musa, kada wanda ya fito a cikinku!....”
Wani irin shiru ya ratsa wurin tsawon muntuna biyar, cikin gidan babu wani motsi kamar babu kowa, alhalin akwai mutum har biyar a cikin gidan.
“Wallahi wannan mara mutuncin ne!....”
Wani matashi ya faɗi daga cikin gidan, bayan ya sauƙe labulen ɗakin da suke ciki. A tsorace ya yi maganar, kuma daga yanda jikinsa ke rawa zaka fahimci hakan kalar tsoron da yake ji.
Cikin halin ko in kula wani cikin mazan dake ɗakin yace.
“Wai wa kake nufi?”
“KULIYA!”
Kusan a tare gabansu su duka ya buga, ciki kuwa harda wanda ya furta sunan, KULIYA!, wani suna ɗaya da yake firgita duk wani me laifi a garin abuja da kewatenta.
Sunansa kawai kan sa cikin mai laifi ya ɗuri ruwa, KULIYA wani irin bahagwan mutum ne, wanda ba'a gane gabansa bare bayansa, ga saurin fushi da fusata, bashi da imani ko kaɗan.
A razane suka miƙe tsaye gaba ɗaya, kuma ɗaya bayan ɗaya suka shiga leƙa windown dan tabbatar da abinda ɗayan nasu ya faɗa.
“Yanzu miye abun yi ?”
Ɗaya daga ciki ya tambaya, fuskarsa na nuna tsantsar tashin hankali.
“Kawai mu miƙa wuya”
“Kai baka da hankali, mu miƙa wuya fa?”
“To mu ci gaba da zama har ya shigo ya harbe mu”
Daga harabar gidan, Kuliya ya fiddo da bindigarsa wadda ke saƙale a bayansa, sannan ya nufi hanyar shiga cikin gidan gadan-gadan.
“Kuliya!, what are you trying to do ?”
Wannan macen cikin nasu ta faɗi tana bin baya sa.
“Sharon, kar ki takuramin!”
“Ba'a bamu umarni ba, dole sai mun jira umarni.....”
Sharon bata rufe bakinta ba, Kuliya ya raɓata ya wuce cikin gidan. Cike da takaicinsa ta ɗaga kanta sama tana girgiza shi, har abada Aliyu ba zai taɓa sauyawa ba.
Matasan nan na tsaye a cikin ɗakin, suna ta nemawa kansu mafita. Basu ankara ba suka ji an banko ƙofar ɗakin, kuma a cikin ƙasa da sakan sittin.
Ƙarar harbin bindigar Kuliya ya cika gidan. Kafin aka samu wani harbin da ya fito ba daga bindigar tasa ba!.
*Kano....*
*11:30pm*
Motoci biyu ne parker a wani filin Allah, wurin ba gida gaba da baya.
Duka fitilun motocin a kunne suke, kasancewar babu wani haske a wurin bayan na motocin. Motocin na kallon juna ne, yayin da wasu mutane shida ke tsaye a tsakiyarsu.
“Ku bamu saƙon”
Muryar macen cikinsu ta faɗa, wasu gardayen maza ne guda uku a bayanta, alamun dai tare suke. Yayin da take fuskantar wani matashi, wanda shi kuma mutum ɗaya ne tsaye a bayansa.
Matashin ya yi murmushi.
“Ku bamu kuɗi tukunna....”
Ya faɗi cikin rainin wayo. Sai macen ta yi murmushi, tana kawar da kitson kalabar attachment ɗin da ya sauƙo mata kan fuska.
“Ka...bamu saƙon!”
Ta maimaita masa abinda ta faɗi tun farko, sai ya kuma yin murmushi.
“Ku kira ogan naku ya zo ya karɓa muku....”
Daga cikin motar dake bayan su macen, mutum ɗaya ne zaune a gidan gaba, kansa a sama, yayin da bayansa ke jingine da jikin kujera. Waƙar lonely at the top dake tashi a cikin motar yake biyawa, yayin da idanuwansa ke a lumshe.
“Zuwan RAJA nan ba zai mana daɗi ba, dan haka ka bamu saƙon, mu juya....”
A wannan karon fushi ne kwance a fuskar matashin.
“Waye shi ?, kira mana shi ya zo ya ƙwata da ƙarfinsa”
Bisa ga mamakinsa sai ya ga budurwar tana murmushi. Sannan ta juya kanta kaɗan, ba tare da ta kalli bayanta ba, idonta a kan matashin ta kira sunan na cikin motar.
“RAJA!”
A hankali mutumin cikin motar ya buɗe idonsa dake rufe, kafin ya sauƙe kansa, idonsa ya sauƙa a kan mutanen dake gaban motar tasu, ɗan guntun tsaki ya ja. Sannan ya buɗe ƙofar motar ya fito.
Hannunsa kan ƙofar motar ya ci gaba da kallonsu. Kafaɗarsa ta dama ya ɗaga, sannan ya kai hannu ya sodai tattoo ɗin kan zakin dake bayan wuyansa, ya fara takawa zuwa wajen da suke tsaye.A gaban matashin ya ja ya tsaya.
“Ka bamu kayan za mu juya”
Muryarsa me cike da kamala da kuma nutsuwa ta furta, idan ka ji muryarsa ba tare da ka ganshi ba sai ka rantse da Allah ba daga bakinsa ta futo ba, dan sam yanayinsa baya kama da yanayin muryar tasa.
“Sai kun bamu kuɗi tukkuna“
Raja ya kuma yin guntun tsaki, ya ɗaga kafaɗarsa ta dama.
“Kana ji ko bana san jayyaya, sannan nakan jima banyi fushi ba, ka bamu kawai mu juya”
Wannan karon muryar tasa cikin wani irin taushi ta fito.
“Ni ma bana san jayyaya.....”
Bai ko gama rufe bakinsa ba, Raja ya ɗauke shi da mari, sannan ya ci kwalarsa da hannunsa na dama, tare da zaro bindigarsa da hannunsa na hagu, ya ɗorata a kan matashin.
Yaron dake tsaye a bayan matashin ya fiddo da tasa bindigar ya nuna Raja da ita, yayin da mutanen Rajan ma suka fiddo da tasu bingidar. Matashin ya shiga ƙoƙarin motsa bakinsa cike da tsoro.
“Shhhhh!”
Rajan ya faɗi yana ɗauke bindigar daga kan matashin, tare da ɗora bindigar a bakinsa, alamun ya masa shiru.
“Bana san jayyayya!......”
Ya ƙarshe yana maido da bindigar kan matashin, cike da tsoro matashin ya gyaɗa  kansa, sannan ya yi wa mutuminsa alama da ya basu kayan.
Da sauri mutumin ya juya cikin motarsu ya buɗeta, sannan ya ɗuko wani brief case, ya danƙa a hannun macan nan, ita kuma macen ta miƙawa ɗaya daga cikun mazan dake tsaye a bayata.
Kuma har zuwa lokacin Raja na riƙe da kwalar matshin nan, sannan bindigar Rajan sete a gosbinsa.
Sai da mutumin su Rajan ya buɗe brief case ɗin, ya tabbatar musu da sahihancin abin da ke cikin brief case ɗin, sannan Raja ya saki matashin.
Kafaɗarsa ta dama ya ɗaga, sannan ya maida bindigar bayansa, yana kallon matashin da shanyyayun idanuwansa, hannunsa ya kai yana gyarawa matshin kwalar rigar jikinsa. Da farko saida matshin ya razana, ya ɗauka cewar wuya zai shaƙe masa. Kuma har lokacin cike da tsoro yake kallonsa.
“You are such a good boy, ka kyauta, da ka yi abinda na ce”
Kuma daga haka ya juya. Da hannu ya yi wa yaransa alama da su shiga mota.
Har motar tasu ta bar wurin matashin na tsaye a wurin yana kallonsu, a ransa yake hasaso irin masifar da ogansa zai masa idan har yasan cewa ya basu kayan ba tare da sun bashi kuɗi ba.
*Unguwar Karkasara....*
*12:30am*
“Da kyau Raja!”
Cewar Garuje, wanda yake shugaba a wurin Rajan, yana faɗin hakan tare da bubbuga kafaɗar Rajan. Bayan da ya duba kayan da ya aikasu su karɓo masa.
Raja ya yi murmushi yana ɗaga kafaɗarsa ta dama.
“Ka ga yanzu nan muka gama waya da me gida, yana ta tambayata akan kayan....”
Garujen ya kuma faɗa. Kuma yanzun ma Rajan bai ce masa komai ba, sai juyawa da ya yi ya kalli yaransa huɗu dake tsaye a bayansa,Rhoda, ta hannun damansa kenan, sai Zuzu, Alandi da kuma Jagwado. Sannan ya juyo ya kalli Garuje, a hankali cikin nutsuwarsa wannan kamillaliyar muryar tasa tace.
“Kai ma ka sanni ai”
“Ai dole ne ma na sa me gida ya maka kyauta, sbd wannan ƙwazon da ka nuna”
Lumsassun idanuwansa na ci gaba da kallon Garuje, yayinda ya ɗaga kafaɗarsa ta dama.
*No. 213, Naf Belly Estate, Asokoro, Abuja*
KULIYA POV.
Har zuwa yanzu a idonsa yana ganin abinda ya faru a ɗazu, ɗazun da ya buɗe ƙofar kai tsaye wuta ya buɗe musu. Bai ankara ba ashe wani daga cikinsu yana riƙe da bindiga, kuma shi ne ya yi yunƙurin harbinsa. Sai de cikin ikon Allah sai ya bashi damar kaucewa, bullet ɗin ya samu bango.
Kuma bayan ya juya ta kalli bangon da bullet ɗi ya fasa, juyowa ya yi ya kalli yaron da hannunsa ke karkarwa, kuma bai jira komai ba, ya riƙe gaban rigar yaron, ya shiga dukansa da hannunsa, har saida yaransa suka shigo sannan suka raba shi da shi......
“Yau ma halin aka sake?....”
Muryar Wata dattijuwar mata ta dawo da shi zahiri. Hannunsa na dama ya sauƙe daga kan bakinsa, kafin ya ɗaga kafaɗarsa ta dama.
Bai cewa matar komai ba, har ta samu wuri ta zauna kusa da shi, matar ta ci gaba da kallonsa tana nazarinsa.
Kamar kullum, kamar yanda ya taso a wurinta, kamar yadda ta rene shi, sanye yake cikin baƙaƙen kaya, wasu jogger set ne sanye a jikin nasa, ya rufe kansa da hular hoodie ɗin rigar.
Idonta ya sauƙa a kan hannunsa na dama, rauni ta gani, kuma da ma ɗazu tun da taga labarai, ta ji an sanar da cewa hukumar DSS sun yi kame a wani gida, har sun kashe mutum ɗaya, ta tabbatar da shi a cikin aikin.
Dan yanda tasan Kuliya, haka ta san yunwar cikinta, bata jin akwai wani da zai faɗa mafa halayensa. Hannun nasa ya farfashe daga kan yatsunsa, alamun dai ya daki wani abun da shi.
Kanta ta girgiza sannan ta miƙe ta bar falon. Jim kaɗan sai gata ta dawo, hannunta riƙe da plate ɗin abinci, sanna firstaid box. A kan coffe table ta aje masa abincin, sannan ta ɗauki firstaid box ɗin ta ɗora akan cinyarta kafin ta buɗe.
Hannun nasa na dama ta kama sannan ta shiga shafa masa maganin zafi a wurin. Kafaɗarsa ta dama ya ɗaga yana kallonta. A duk sanda Anna zata nuna masa kulawa, idan ya kalleta sai ya ga fuskarta na rikiɗewa tana koma irin tata.
Mahaifiyarsa, mahaifiyarsa da a duk sanda zai tuna da ita sai ya tuna da mahaɗinsa, ɗan uwansa, abokin tagwaitakarsa, Zaid ɗinsa, Zaid ɗin da ya ƙara sunansa a gaban nasa sunan, sai dai kuma idan ya ci gaba da san zurfafa a cikin tunanin LABARINSU na baya zuciyarsa ƙuna take, wani abu ne ke maƙale masa a wuya, shi bai faɗa cikinsa ba shi bai fito daga bakinsa ba.
“Ga abinci ka ci”
Anna ta faɗi a sanda ta gama shafa masa maganin,tana miƙa masa plate ɗin. Yanda yake kaiwa lomar abincin ne kawai ya shaida mata da kalar yunwar da yake ji, bisa ga dukkan alamu ko da aka yi buɗa baki bai ci abinci bw.
Masifar zurfin cikinsa da miskilancinsa da kuma taurin kansa shi ne ke haɗata faɗa da shi, dan da ace bata kawo masa abincin ba, haka zai ƙaraci zamansa a gidan, har ya tashi ya tafi ba tare da ya ce ta bashi abincin ba, alhalin shi ne wanda ya siyo kayan abincin. Kuma bama iyaka kayan abinci ba, komai ma na gidan shi ne ya siya.
“Aliyu!”
Ta kira sunansa a hankali, shi ma kuma sai ya saki spoon ɗin hannunsa ya juyo ya kalleta.
“Dan Allah ka rage yawan fushin nan, ka rage wannan zafin zuciyar taka”
“Anna ba na iya controlling kai na, as far as zan ga ana aikata laifi bana iya hana kaina ɗaukar mataki!......”
A karo na biyu ya yi magana tun bayan zuwasan gidan, tun da ya gaisheta cikin jimla ɗaya bai sake cewa komai ba sai yanzu.
“Haka ne, amma ya kamata a ce kana ragewa, ka riƙa sanyaya zuciyarka, Aliyu babu macen da zata aureka da wannan halin naka”
Ransa ya soma ɓaci, ita Anna ana gabar tana yamma, shi ya faɗa mata cewa zai yi aure ?, shi fa sam babu aure a lissafinsa, bai shirya masa ba, kuma baya jin zai shirya masa ko a nan gaba.
Sai dai ban san abinda Allah ya ƙaddaro ba, bai san ƙaddara da zata kasance ƴan kwanaki ƙalilan ba, ƙaddarar da Allah ya hukunta zata faru a 'yan kwanaki masu zuwan. Wata iriyar ƙaddara ce da zata tarwatsa komai, sannan ta zama silar shiryiwar wasu lamura.
“Ni na faɗa miki cewar aure nake san yi ?!”
Annan ta yi murmushi, jin muryar tasa na fita a zafafe, ko bai buɗe baki ya faɗa mata ba tasan cewa ransa ne ya ɓaci. Kuma shi da ma haka yake, abu ɗan ƙalilan ne ke ɓata masa rai.
Kuliya ya ɗaga kafaɗarsa ta dama yana ƙoƙarin saita kansa, dan sai bayan muryar tasa ta fito ne ya fuskanci abinda ya yi.
“Sorry Anna, zancen auren ne bana so”
Har a lokacin Anna na iya tsintar sauran fishin da bai gama sauƙe shi ba, kuma da ma shi haka muryar tasa take, kullum cikin darari, ba'a iya maganar arziƙi da shi ta minti goma, kullum idanuwansa a waje kamar me zarewa mutane su.
“Aure shi ne cikar kamala Aliyu, duk wannan muƙamin naka, da dukiyar da ka tara, da wannan shekarun naka, ba zasu baka kimar da aure zai baka ba!....”
Bai ƙara kallonta ba, bare ya amsata, dan ya lura da yau so take suyi faɗa.
TALLAH!
Salma's Graphics:
•Muna haɗa book cover.
•Banner
•poster
Kuma duka a kan ₦ 300 kacal.
Domin neman ƙarin bayani: 08130172702.
#Labarinsu
#SalmaAhmadIsah
#TaurariWriters*LABARINSU*

#TaurariWriters

LABARINSUजहाँ कहानियाँ रहती हैं। अभी खोजें