LABARINSU

111 1 0
                                    

*LABARINSU*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*TAURARI WRITERS*
بسم الله الرحمن الرحيم
*01*
~~~
*Unguwar Madalla, Suleja, Niger state*
*06:00am*
“RABI'A!, nasan cewa bayan na mutu za ki koma gidan mahaifinki ne.... ADAWIYYA  ina da tabbacin bayan kin koma cikin 'yan uwanki da zama za ki sha wahala, na san cewa za ki shiga taskun rayuwa kala-kala, na san cewa Habiba ba ta sona, bare kuma 'ya'yana, na san cewa ba za ta taɓa barinki ki huta ba..... Amma ki riƙe addu'a, ki riƙe addu'a a ko wani irin yanayi kika tsinci kanki. Ki yi haƙuri, domin na san cewa ƙaddarorinki yanzu suka fara. Yanzu LABARINKI zai soma.........”
Zubar ruwan da ya cika bokitin da ta saka a famfo ne ya jawo hankalinta daga duniyar tunanin da ta faɗa.
Kanta ta ɗan ɗaga sama ta kalli sararin samaniya, har yanzu garin akwai sauran duhun asuba, yanayin gashi kuma yanayin garin akwai zafi, kasancewar ana tsakiyar kwanki goma na ƙarshen watan azumi ne, dan bai fi saura kwana huɗu sallah ba.
Kanta ta sauƙe ƙasa ta kalli bokitin da ya cika har ruwan ciki na zuba, ta tsugunna zata janye bokitin, wata murya ta daka mata tsawa cikin faɗin.
“Ub*n me kike ne wai Rabi?!, Tun ɗazu bokitin ya cika har yana zuba amma ba za ki ɗauke ba?,Saboda baƙin halli da kika gada a wurin uw*r ki ko?, to ki ci gaba da tsayuwa a wurin, idan ƙarar ruwan nan ya tada min yara sai na ci uw*r ki Wallahi!....”.
Rabi ta ɗago da kanta ta kalli inda matar ke tsaye, hasken wutar nepar dake haske tsakar gidan ya haska mata fuskar matar tar, matar babanta ce, Habiba, matar da akodayaushe burinta ta ga ta lalata mata rayuwa.
Kuma bata tsaya iyaka nan ba, har cikin garin Abuja take turata aikatau, yau shekarunta biyar a gidan, tun bayan rasuwar mahaifiyarta, mahaifinta ya je har garinsu mahaifiyarta ya ɗaukota, ya dawo da ita cikin gidansa, gidan da ita zata iya kiransa da kurkuku. Domin ko da da sakan ɗaya bata taɓa jin daɗin zaman gidan ba.
Babu wanda take jin daɗin zama da shi a gidan sai Saratu, 'yar Habiban ta biyu, a wasu lokutan ma idan Habiban na mata faɗa har baki take sakawa.
Tun a shekararta ta farko a gidan ta fara ganin uƙuba irin ta matar uba, da ta saba jin hakan a labarai, labarin yanda matan uba kan ƙuntatawa 'ya'yan mazanjensu, ko da wasa bata taɓa hasaso cewa rayuwarta zata fuskanci abu makamancin wannan ba. Sai gata tsundum cikin wannan hali.
Kuma ƙalubalen nata ya fara ne tun daga sanda ta nemi da Babanta ya maida ta makaranta, yace ai ta gama karatu, shi bq zai iya wahalar da kansa wurin sakata a makaranta ba. Ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba a lokacin, dan Allah ya sani tana san karatu, kuma burin mahaifiyarta ne ta yi karatu.
Bayan wannan sai ta koma baiwa kuma jakar aikin gidan, 'ya'yan Habiba ko tsinke basa ɗaukewa a gidan sai de ita ta yi. Duka wannan bai ishi Habiba ta gama da rayuwarta ba sai da ta fara turata aikatau.
Kullum iƙirari take kan cewar ba zata ciyar da ita a banza ba, tun da ub*nta bashi da aikin yi, ita take riƙe da gidan, kuma kusan hakan ne, dan Mahaifin nasu ba shi da wani aikin yi, kasancewar an koreshi a wurin aikinsa.
Babu abinda yake sai zaman baza, zuciyarsa ta riga ta gama mutuwa, babu abinda yake sai caca da bin matan banza. Haka Habiban za ta saka shi a gaba tana tsigeshi, kamar wani ɗan da ta haifa, amma ko tari ba ya iya mata, saboda yasan ba shi da gaskiya.
Babu yanda Rabin za ta iya, haka ta yarda ta fara zuwa aikatau ɗin, da ko wani ƙalubale dake fuskantar rayuwarta, Kalaman mahaifiyarta na ƙarashe su ne ke yawo a kanta.
A sanda take mata maganganun, gani take kamar zafin ciwo ne ke nuƙurƙusarta, gani take kamar kawai sambatun ciwo mahaifiyar tata take, dan waɗanan kalaman nata sune maganarta da ta ƙarshe, bata sake magana ba har ta koma ga ubangijinta.
Sai a yanzun take ganin duk abunda take faɗa mata, duk abinda ta ce mata zasu faru gareta su take gani. Dan yanzu haka a wata makaranta dake cikin garin abuja take aikin goge-goge da share-share.
Bata da wani buri a yanzu, bata da wani fata, bata da wani abin da take san cimmawa, dan a ganinta kamar rayuwartace ta zo ƙarahe, kamar LABARINTA ne ya ƙare, babu wani abu da ya yi saura.
Ƙwara ma kawai ta zauna ta rungumi ƙaddararta da ta zo mata a haka, tun da Allah yasa a bautawa wasu rayuwarta za ta ƙare to ta amshi hakan......
Ƙarar turowa ƙofar gidan nasu ce tasa ta juyawa takalli ƙofar. Mama ce ta shigo, 'yar Habiban ta uku. Amma kuma ba wai hakan ne yasa Rabi mamaki ba, mamaki take na san sanin sanda Maman ta fita ta daga gidan.
Ta san cewa jiya daddare tare suka kwanta, tun da ɗakinsu ɗaya, amma ko da asuba bata ganta ba, fitar tata a daren ba wani abun mamaki ba ne, dan ta saba kwana a waje ma, ta saba bin samarinta su tafi yawon banza.
Sunan 'karuwa' da Habiba ta saba kiranta da shi ne ya dawo cikin kanta. Sai kawai ta juya ta ɗauki bokitin da ta juye ruwan cikinsa a randa, ta koma bakin famfo ta kunna famfon ta ci gaba da tsaiwa a wurin tana jiran ya cika. Dan Habiba na gama masifar tata ta koma ɗakinta.
A rayuwar gidansu ta tabbatar da karin maganar nan da hausawa ke faɗin 'Laifi tudu ne, ka take naka ka hangi na wani', ita zata bada shaidar wannan, domin duk abinda Maman ke yi da sanin Habiba, dan idan ta samo kuɗi ko kayan kwaɗayin da samarinta kan bata Habiban take kawowa. Ita abun haushinta a nan shi ne; ganin cikin watan azumin Allah ta ala ma bata bar abinda ta saba ba. Sai ta girgiza kanta a fili tana kashe famfon da ruwansa ya cika bokitin gabanta.
“Ub*an miye kike wani girgiza kai ?!”
Maman ta tambaya cike da masifa, dan in dai ruwan bala'i ne, to kaf cikin yaran Habiba babu wanda ya gado shi kamar Maman, dan bata da mutunci, Rabi ta kalleta,  sannan ta girgiza kanta.
“Babu komai”
Sai da ta ɗan tsaya na wasu sakanni tana aikawa Rabin harara, sannan ta juya kanta ta shige ɗakinsu.
Rabi ta kuma jijjiga kanta a sanda ta juye bokiti na ƙarshe a cikin randar. Share gidan ta shiga, ta share tsakar gidan tas, kana ta shiga ɗakinsu, dan ɗaukan kayan da za ta sa, saboda wankan da za ta yi.
Tana ɗage labulen da harar Mama ta fara cin karo, sannan ta bi ɗakin duka da kallo, Saratu ce zaune tana guga, sai Fatima ƙaramar ƙanwarsu tana kwance a kan katifarta, sai sharar bacci take.
Bata cewa kowa komai ba, ta ƙarasa shiga cikin ɗakin tana nufar inda take aje jakarta ta Ghana must go.
Zip ɗin jakar ta buɗe, idonta ya sauƙa a kan kayan da suke a saman jakar, kayanta ne, kayan da ta zo gidan da su tun shekaru biyar da suka wuce, dan tun bayan zuwanta gidan ba'a ƙara mata sabon ɗinki ba. Kuma a halin yanzu kayan sun mata kaɗan, ba wai dan ta ƙara ƙiba ba, sai dan girma da shekaru suka ƙara mata.
A yanzu ba ma ta saka kayan, kayan yayarta Baby da ta rasu su takesakawa, dan a sanda Babyn ta rasu ba zata wuce shekarunta ba, duk da Babyn na fama da cutar sickler.
Baby?!, sunan ya maimaita kansa a cikin ranta, a sanda ta ɗago wata doguwar riga sama, rigar ta Babyn ce, kuma ba wannan ne yasa ta tsaya ta ci gaba da kallon rigar ba, sai dan tunawa da ta yi da yanda Babyn ke matuƙar san rigar.
_“Umma ki ce ta bani....” _
Muryar Rabi'an ta faɗi a wancan lokacin, mahaifiyarsu dake zaune a kan sofa tana duba wasu takardu ta juyo ta kallesu, sannan ta kalli rigar da suke kokawa a kanta.
_“To wai ke Adawiyya me za ki yi da wannan rigar ?, in ce de ta miki yawa” _
Rab'ia ta turo baki gaba tana wata shagwaɓa irin tata ta autanci.
_“Wallahi Umma ina san rigar” _
Baby ta fisge rigar daga hannun Rab'ia tana hararta.
_“Ai ko ba zan baki ba....” _
“Yayar ummanta Adawiyyan Umma, rabu da ita, zan sai miki sabuwa, wadda ta ma fi tata kyau.....”
Sai kawai ta ninke rigar ta maida ta cikin jakar, Allah ya sani sam bata san tuno LABARINTA na baya, dan hakan sam bai da amfani a ganinta, saboda wannan wata rayuwace da ta shuɗe a baya, sannan rayuwace wadda ta tafi da abubuwa da dama.
Ciki kuwa harda ita kanta, saboda gani take kamar wannan ba waccan Rabi'ar data sani ba ce, wannan wata baiwa ce dake aikatau a gidan mahaifinta, ba kamar waccan Rabi'ar ba, me rayuwa cikin gata da kulawa, autar ummanta, ƙanwar yayarta, jika mafi soyuwa a wurin kakkaninta.
Wata doguwar riga wadda Saratu ta bata kunce ta ɗauko, ta haɗa da hijabin Baby, sannan ta zuge jakar tana miƙewa. Bayan da ta aje hijabin a kan jakar, hannunta kuma tiƙe da rigar da ta ɗauko ɗin.
“Rabi dan Allah yaushe za ki min ƙunshin ?”
Saratu ta tambaya tana aje rigar da ta gama gogewa. Rabi ta ɗan dakata da tafiyar da take, sannan ta juyo ta kalli Saratun dake kallonta ita ma.
“Saura kwana nawa ne sallar ?”
Saratu ta amsa mata da “Ehhh to!, gaskiya ba na ce ba, amma jiya na ji Umma (wato Habiba, dan haka suke kiranta) na faɗin saura kwana huɗu ne ko uku?...”
“Gobe za ayi hutu a makarantar yarana nan, sai na miki goben, nima ina so ki min kalaba”
Ta ƙarashe tana ɗan dukan kanta da ke ɗauke da manyan kalaba guda huɗu, dan bata kitso, kuma ba komai ya ja hakan ba sai santsi da tsayin da gashin nata ke da shi. tun mahaifiyarta na da rai bata kitso,  sai dai Ummar tasu ta kaisu wurin gyaran kai.
Amma yanzu fa ?, gashin nata ma ya fara raguwa saboda rashin gyara, kalabar da Saratun ke mata ita kaɗai kan nata ke samu.
Saratu ta gyaɗa kanta sannan ta ce.
“Allah kai mu goben”
Har Rabi zata fita da ga ɗakin sai ta juyo.
“Wani kala zan miki ?”
“Ɗan gama nake so”
Da ga haka bata ƙara cewa komai ba ta gyaɗa kanta, sannan ta fita da ga ɗakin, wanka ta je ta yi, ta fito bayan da ta gama wankan, saboda yanzu ana cikin azumi shi yasa ayyukanta suka ragu a gidan.
Dan idan baki buɗe ne, sai ta kai niƙan alkamar da Habiba ke yin finkason safe, idan kuwa a week end ne ita ce ma da kanta take suyar finkason. Kuma ta hanyar kuɗin da take samu a finkason, da albashi da ake bawa Rabin a wurin aikinta, Habiban ke iya kula da gidan, dan komai na gidan ita ce ke yi.
Bayan ta shiga ɗakin, mai kawai ta shafa, sannan ta ɗauki hijabin da ta fitar ta saka, ta yiwa Saratu sallama, ta fita.
“.....Kin ji matsalata da ke, dan Allah Habiba yanzu idan baki rufa min asiri ba waye zai rufa min?....”
Rabi ta ja ta tsaya a sanda ta ɗora idonta a kan mahaifinsu tsaye yana ƙanƙan da kansa a gaban Habiba,wadda ta wani ɗaga kai sama tana shirin zazzago buhun masifa.
“Wallahi Ɗan Lami baka isa ba, a kan me zan ɗauki kuɗi na baka?, bacin na san caca za ka je ka yi da su......”
Rabi bata tsaya ta gama jin abinda take faɗi ba ta sa kai ta fita. Kuma abinda Habiban ta faɗi gaskiya ne, dan baban nasu babu wani aiki da yake face cacar, duk kuɗin da zai samu a caca suke ƙarewa.
Sai da ta ɗan tsaya a ƙofar gidansu, ta ɗan ɗaga kai saka,  da ga nan inda take tana iya hango dutsen zuma rock, dubanta ya kai kan tarin bolar dake tsallaken ƙofar gidansu.
Bolar har tsiri take dan tsabar yawanta, da sauri ta ɗauke kanta da ga barin duban bolar, dan Allah ya sani idan ma takalleta zuciyarta har wani tashi take, dan ta tsani ƙazanta a rayuwarta.
Haka ta ci gaba da tafiya a cikin ƙazamin layin nasu, wanda kwatanni da datti suka masa ƙawa.
Akasarin mazauna unguwar ta Madalla masu magana da harshen gwari da baagi ne, sannan akwai hausawa sai nufawa, da wasu sauran yarukan, sannan a cikinsu akwai musulmai da cristian.
“.....Rabi!”
Ta juyo saboda jin an kiran sunanta, gamin wanda ke kiran nata yasa ta yi murmushi tana juyowa gaba ɗaya, Zara ce, mutum ɗaya da za ta iya ɗagawa ta kira da ƙawarta.
“Aikin za'a je?”
“Eh mana, keda kika sani”
Suka ɗan yi dariya.
“Kunu kika siyo ?”
Rabi ta tambaya yayin da idonta ya sauƙa  kan jug ɗin dake hannun Zaran.
“Eh wallahi, bari na wuce, kafin Umma ta soma faɗan na daɗe....”
Kuma daga haka suka yi sallama, bakin titi ta fita, a titin ma sai da ta yi wata doguwar tafiya a ƙafa, kafin ta iso Ɗan kogi motor park.
Inda ta saba hawa mota, ta biya kuɗin da ta saba biya a kullum, wanda Habiba ke bata dan yin kuɗin motar, saboda da ga gidan nasu zuwa makarantar da take aikin akwai nisa. Tafiyar kusan minti 40 ce.
Sun yi doguwar tafiya a motar, kafin suka isa Joy Emodi CI inda za'a sauƙeta, daga nan ta soma tafiya a ƙafa, wadda ta ɗauketa tsawon lokaci, kafin ta iso makarantar da take zuwa aikin shara.
*Brickhall School, Kaura district, Abuja*
A hankali wata farar mota ƙirar Corolla hybrid ta yi parking a harabar makarantar.  ko minti ɗaya ba ta yi da parking ba, ƙofar gidan baya na motar ta buɗe.
Wata matashiya ta fito,sanye cikin wata baƙar pleate skirt, da kaɗan skirt ɗin ta sauƙo gwiwarta, sai farar oxford shirt, wadda ta ɗora maroon suit a kai, daga gefenta suit ɗin na dama an manna symbol ɗin makarantar, wuyanta saƙale da tie, kanta babu ko ɗankwali, sai gashin kanta wanda ya ji gyara, an ɗaureshi cikin pony rail, jelar sai reto take a bayanta. Bayanta goye da backpack ɗinta me kyau, ƙafafunta sanye cikin baƙaƙen sneakers.
Kuma ba ita kaɗai ce ke sanye da irin kayan ba, dan gaba ɗaya ɗaliban dake kai kawo a harabar makarantar sanye suke da irin kayan jikin nata, maza ne kaɗai ke saka wando, kuma shi ne abinda ya banbantasu, hakan ke nuna cewa kayan shi ne uniform ɗin makarantar.
Tafiya ta fara cikin takunta na wanda ƙuriciya bata gama saki ba.
“MISHAL!, kin manta abincin ki....”
Muryar drivernta malam Ali ta faɗi da ga cikin motar.Tsayawa ta yi da tafiyar, sannan ta juyo ta kalli motar, kafin ta fara takowa zuwa wurin motar.
Ba tare da ta ce masa komai ba, ta buɗe gidan baya ta ɗauki lunchbox ɗin nata, ta rufe ƙofar motar, kana ta ɗaga masa hannu alamun bye, sannan ta yi gaba.
Malam Ali ya girgiza kai yana murmushi, a cikin ransa ya na wa Mishal ɗin fatan shiryuwa, ita duk gari ana azumi amma banda ita, zai iya cewa tun da aka fara azumin ma bai fi guda goma ta yi ba, da ya mata magana ma sai tace masa wai akwai wahala haɗa azumi da zuwa makaranta.
Duk inda ta wuce sai an bita da kallo, amma ita ko a jikinta, dan bata damu ba, saboda wannan ba shi ne karo na farko da aka saba bintada kallon ba, wasu kallonta suke cikin tsoro saboda sanin halinta, wasu kuma cike da burgewa saboda sanin jarumtarta, wasu kuma suna kallonta ne cikin jin haushi, wata ƙila saboda faɗa ya taɓaa haɗasu.
Bata ko kalli kowa ba, duk da tasan cewa kowa kallonta yake. Har ta kai ƙofar class ɗinsu, ta saka ƙafarta a cikin ajin, sai kuma ta dawo da baya, ta gyara tsaiwarta tana kallon wannan yarinyar.
Yarinyar da ke aikin shara a makarantar tasu, ba yau ne karo na farko da ta fara ganin yarinyar ba, hasalima tafi wata shida tana ganin gilmawarta a makaranta.
Ba wannan ne yasa take kallonta ba, kawai rayuwar yarinyar ce ke bata tausayi, dan da alama yarinyar na cikin halin ƙuncin rayuwa, ita kuma haka Allah ya yi ta, duk da baƙin halinta da rashin jin maganarta da wasu ke gani, Allah ya hallici zuciyarta da tausayin wanda bashi da shi, haka Allah ya saka mata tausayin yarinyar.
Duk da ba za ta iya kiranta da yarinya ba, saboda da alama ta girmeta, saide bata kai sa'ar Akinta(Yayanta) ba.
Da alama ma ita yarinyar bata lura da ita ba, dan moping ɗin floor take bil haƙƙi da gaskiya. Ba tare da ta yi komai ba, ta juya ta shiga ajin nasu.
Malamin geography ne a ciki, kuma tana shiga ajin ya yi tsit!, kallo ya dawo kanta kamar kullum. Ba tare da ta damu ba ta nufi seat ɗinta.
“Ke Hafsat Muhammad Auwal!”
Uncle ɗin geographyn ya daka mata tsawa, ta juyo ta kalle shi da sauri, idonta babu ko da ƙwayar tsoro a ciki, dan bata saba jin tsoron kowa ba, kowa gani take kai kai ɗaya yake da ita.
A hasalle Uncle ɗin ya cillar da littafin da ke hannunsa, ya ɗauki wata cane ya yi kanta, yana ƙarasawa kusa da ita ya ɗaga bulalar sama zai zabga mata ta kai hannunta ta riƙe bulallar.
“Babban kuskuren da za ka yi shi ne duka na da wannan bulalar, dan Wallahil Azim ka kuskura ka dakeni sai na rama”
Ta ƙarashe tana wancakalar da bulalar, Uncle ya haɗiye wani abu a maƙoshinsa, yana ci gaba da kallon yarinyar, Ba ƙaramin jajircewa ya yi ba da har ya iya yunƙurin dukan yarinyar, dan malamai da dama na yawan bada labarin yarinyar a staffroom, wasu da ga cikinsu ma kan ce wata ƙila aljana ce, dan normal ɗan adam ba zai iya abin da yarinyar nan ke yi ba.
Ta addabi kowa a makarantar, watan da ya wuce har wani malami ta mara, ɗalibai kuwa kullum sai an samu wanda zai kawo ƙararta.
Sai da ta aika masa harara, sannan ta aje jakaarta a kan desk, ta zauna tana baza ƙwayoyin idonta a cikin ajin, hakan yasa kowa ya shiga taitayinsa.
Sai da ta yi ƙwafa sannan ta buɗe jakarta ta ɗauko littafi ta gyara zamata ta shiga kwafar note ɗin da uncle ɗi  ya ci gaba da yi.
MISHAL POV.
“Wai me yasa ke bakya azumi kamar 'yan uwanki musulmai”
Muryar Angelica yarinyar Mishal ta faɗi a sanda aka fito break, dan sai dai a kirata da yarinyarta, saboda duk wani aike ko bautar Mishal ɗin ita Angelican ce ke yi. Kuma kaf makarantar Mishal bata da ƙawa ko ɗaya, ita ma Angelican ita ta cuso kanta gareta. Mishal ta ture flask ɗin gabanta tana miƙe ƙafa.
“Saboda bana san wahala, bazan iya haɗa azumi da zuwa makaranta ba”
Ta bata amsa cikin harshen turanci, kamar yanda itama Angelican ta mata maganar cikin harshen turancin, kasancewarta baturiyar Engiland. Aiki ne ya kawo mahaifinta zama a nigeria.
“Amma su Rashida su na yi”
“Baki ji me nace ba ?”
Sai Angelica ta girgiza kai, tana kai loma bakinta.
“Kai ka ga wata balarabiya”
Wani sabon ɗalibi da ya fara zuwa makarantar ya faɗi yana kallon Mishal da ga nesa, abokin nasa da ake nunawa Mishal ɗin ya juyo ya kalli wurin, kuma a lokaci guda idonsa ya zare cike da tsoro da kuma mamaki.
“Kai!!, karfa kace min santa kake!”
Sabon ɗalibin me suna Abdul ya yi murmushi.
“Ka jika da wani zance, waye zai ga wannan kyakyawar ya ce ba ya so, Allah da da na ganta na ɗauka balarabiyace”
Abokin ya haɗiye wani abu.
“Abdul da ka je ka ce kana san wannan, gwara ka samu Madam Joke (Malamarsu ta Math) ka ce kana santa”
Abdul ya ƙyaƙyale da dariya.
“Kai ana gabar kana yamma, me zan yi da wata Joke arniya kuma tsohuwa, ga kyakkyawar baby a nan”
“Idan za ka ka bar jirana, tun da na haneka baka ji ba, idan ka je ita zata maka bayani....”
Kuma yana kaiwa nan ya fita da gudu ya bar wurin zaman cin abincin nasu. Abdul ya bi bayansa da kallo yana dariya, ya gyara tie ɗin wuyansa, sannan ya gyara stocking ɗin wandonsa, ya nufi wurin da kyakkyawarsa take.
“Ke rabu da assignment ɗin nan, wallahi bazan yi ba, in yaso idan mun haɗu da python ya kasheni” Cewar Mishal
Pytho shi ne sunan da suke kiran malamin math ɗinsu da shi, kuma sunan ya samo asaline tun sanda suna jss3, lokacin da ya koyar da su Pythagoras rule.
“Ke idan ki ka ƙi yi ba damuwa, ni fa ?, wata ƙila ya karyani, gwara na je na yi”
Angelica ta ƙarashe tana miƙewa tare da barin wurin.
Mishal ta gyara zamanta tana aika lomar abincinta baki, kafin wata murya ta daki dodon kunnuwansa.
“Salam!”
Kuma kafin ta ɗago da kanta ta amsa sallamar, har wanda ya yi sallamar ya ja kujerar da Angelica ta tashi ya zauna. Mishal ta ɗan kalleshi na wasu sakkani. Bata taɓa ganinsa a makarantar ba, hakan kenuna mata cewar sabon zuwa ne, dan in ba baka ba,babu yaron da ya isa ya yi gigin mata magana kaf brickhall.
“Ba kya azumi ne na ga kina cin abinci?...”
Bata amsa shi ba, sai kallonsa da ta ci gaba da yi da olive green color eyes ɗinta.
“A wani class kike ?”
Yanzu ma bata amsa shi ba, hakan yasa Abdul tunanin ko de bata jin hausa,sai de kuma farin fatarta baya kama da na larabawa, farace, fara kuma sosai, sai dai ba irin farin fatar larabawa da turawa ba.
Kyan fuskarta, idanuwanta da kuma gashin kanta sune suke kama da na larabawan, idan zai iya sakata a jerin mutanen nigeria, sai dai a danganta ta da jinin shuwa arab.
Mishal ta zuƙi taliyar indomien da ke bakinta,sannan ta ci gaba da kallonsa.
“Can't you speak hausa ?”
“Me kake buƙata ?”
Ta tambaya da hausa tana kallonsa.
“Ashe dai kina ji....”
“Na ce me kake buƙata ?”
Abdul ya ɗan shafa kansa sannan ya ce.
“Idan ba zaki damu ba, shin zamu iya yin soyyaya”
Sai ta yi murmushi, wanda ya bayyana ƙarafunan braces ɗin dake saman haƙwaranta, wanda Abdul ya ɗauke shi a matsayin amasar tambayarsa, sai shi ma ya yi murmushin.
Mishal ta rufe flask ɗinta a karo na biyu, sannan ta miƙe ta zagayo ta ɓarin da Abdul yake.
“Miƙe pls”
Yana murmushi ya miƙe tsaye. Tashi ɗaya Abdul ya ga yanayin fuskarta ya sauya zuwa fushi mabayyani.
Sannan ba ta yi wata-wata ba, ta ɗaga hannunta na dama ta ɗauke shi da maruka uku kyawawa.
*
Tsaye suke a office ɗin principal ita da Abdul ɗin da ta fasawa baki da marin da ta masa, bayan shi Abdul ɗin ya kawo ƙararta office ɗin principal ɗin.
Principal ɗin nasu ya kalleta da kyau, bayan da Abdul ya gana tsara masa aabin da ya faru, kuma ko musu ba ta yi ba, ta amsa lefinta, shi a rayuwarsa bai taɓa ganin yarinya irin wannan Hafsat ɗin ba. Kullum cikin kawo ƙararta ake, ba ga malamai ba, ba ga ɗalibai ba, kuma shi yarasa yanda zai yi da yarinyar. Shi dai ba zai iya korarta daga makarantar ba, saboda tana da ƙoƙari, tana ɗaya daga cikin ɗaliban da suke alfahari da su a makarantar.
“Hafsat, me yasa kika mare shi?”
Mishal ta wani juya idonta a cikin office ɗin, sannan ta ɗan sosa hannunta.
“Zuwa ya yi yace wai yana so na...”
“Kuma da ga cewa yana sanki sai ki mareshi ?”
“Ai dokar makaranta ya karya, shi yasa na mareshi, ya godewa Allah ma da ban karya masa hannu ba”
Principal ya ci gaba da kallon yarinyar, ba wai da wasa take faɗar hakan ba, a bakin gaskiyarta take faɗin zata karya shin, dan ta karya ɗalibai biyu a makarantar, kuma tun daga junior ta fara makarantar, sannan tun da ga lokacin kullum sai an kawo ƙararta.
Wani lokacin ma a ajinsu na koyon kung fu take dukan 'ya'yan mutane, hakan yasa shi da kansa yace ta fita da ga anjin koyon kung fu ɗin, amma yarinyar fir taƙi, kuma taƙi ɗaukar ko wani sport sai kung fu ɗin.
“Ga wannan takardar, ki kaiwa yayanki”
Hannu ta kai ta karɓi takardar, sannan ta sa kai ta fice, ba wannan ne karo na farko da suka taɓa bata takardar suka ce ta kai masa ba, dan idan da sabo ma yayan nata ya saba zuwa makarantar a kan matsalarta.
A kusa da staffroom ɗin malamai mata ta ga wannan yarinyar....wannan yarinyar da ke tsananin bata tausayi. Sai kawai ta tsaya da tafiyar da take, ta nufi wurin yarinyar, dan tana so tai mata magana.
“Sanu da aiki!”
Yarinyar da ke sharar ta yi saurin ɗagowa ta kalleta, ita ma yarinyar ta gane Mishal ɗin, tana yawan ganinta a makarantar.
“Menene sunan ki”
Mishal ta tambaya fuskarta ɗauke da murmushi. Sai da yarinyar ta haɗiye wani abu, sannan ta amsa mata da.
“Rabi'a”
Mishal ta gyaɗa kanta.
“Me yasa kike aikin shara a nan?...”
Rabi ta gyara ruƙon tsintsiyar dake hannunta, to me yasa take mata waɗanan tambayoyin ?, amma kuma abun yaso ya bata mamaki, dan gaba ɗaya ɗaliban makarantar babu wanda ma yake kallonta da kima ko mutunci, kallon banza suke mata, ga wahalar da suke bata, wasu ma har tsokanarta suke.
“Am....Imm...ummm”
Ta kafa inda-inda, dan bata santa ba, batama san me za ta ce mata ba.
“Is it personal issue?”
Kuma tun kafin Mishal ɗin ta yi tunanin cewa ba lalle ace tana jin turanci ba Rabi ta amsa mata da sauri.
“Yeah, it's personal”
Mamaki ya kama Mishal, duk da dama yarinyar bata mata kama da irin villegers ɗin nan ba, ta fi kama da waɗanda ke cikin ƙuncin rayuwa, duk da ba a walaƙance take ba, amma kana ganinta zaka ga hakan, sai dai kuma yanayinta na wayyayun 'yan mata ne.
Sai kawai ta gyaɗa kanta.
“Gobe za ayi hutu, inaso ki min siffa, kin iya ?”
Girar Rabi ta haɗe wuri guda alamun kokwanto.
“Menene siffa ?”
Mishal ta ɗan daki gaban goshinta.
“Lalle nake nufi, kin iya?”
Sai Rabi ta yi murmushi, a shekaru zata iya girmewa yarinyar, amma da alama yarinyar tana da kirki.
“Na iya, kina so na miki ne?”
Da sauri Mishal ta gyaɗa mata kai, kuma da gaske tana buƙatar amata siffar, dan sallar azumin ba a Abuja zasu yi ba, a mahaifarsu zasu yi, wato Maiduguri.
“Wanne kike so, ɗan gam ko ɗan zane ?”
“Ni dai baƙa nake so, kuma a hannu za ki min”
Sai Rabi ta gyaɗa kanta.
“A ina zan miki ?”
Mishal ta juya tana kallon inda suke, to a ina da suka haɗu ?, a makaranta suka haɗu, to a ina zata mata da ya wuce makarantar ?.
“A nan mana”
Rabi ta zaro ido tana jinjina yarintar yarinyar.
“Makaranta ce fa”
“To sai me?, kin ga kawai zan sa a siyo min lallen, gobe zaki min, sunana Mishal”
Rabi ta kuma gyaɗa kanta....kafin wata murya ta yi magan da ga ƙofar staffroom ɗin malamai mata.
“Ke!, da kika tara wannan sharar a nan ub*nki ne zai kwashe!”
Rabi ta zabura za ta koma ta ci gaba da sharar da take.
“Kawai sai ki zagi ub*nta, me ta miki ?”
Muryar Mishal ta katse mata hanzari, da sauri Rabi ta juyo ta kalli Mishal ɗin, wadda ta wani haɗe rai, tana kallon malamar.
“Ke ba na ciki da rashin kunya, ki bar ganin sauran malamai su na ƙyaleki, wallahi ni ub*nki zan ci....”
“Ahir ɗinki Abu, ub*ana ya fi ƙarfinki, wallahi ki fita sabgata, in ba haka ba yanzu zan nuna miki kalar nawa rashin hankalin, kuma ki musa ki gani”
Mishal ta katseta tun kafin ta rufe bakinta, kuma cike da rashin kunya take maganar, tana yi tana nuna malamar da ɗan yatsa.
“Bamu taɓa haɗuwa da ke ba ne, dan kina malamar art ba shi zai hana na bi ta kan mutuncinki da kika zubar na wuce ba, dan haka ki kula, kuma sharar ba zata kwashe ba, ki yi abinda kike ganin zaki iya....”
TALLAH!
Salma's Graphics:
•Muna haɗa book cover.
•Banner
•poster
•Certificate
Kuma duka a kan ₦ 300 kacal.
Domin neman ƙarin bayani: 08130172702.
#Labarinsu
#SalmaAhmadIsah
#Taurariwriters

LABARINSUWhere stories live. Discover now