A duniyar Faisal bai taɓa kallon wata mace da sunan SO ba face Fatima, ita ce kaɗai yake ji a ranshi, ta kasance mahaɗin rayuwarshi, muradin ranshi, wacce yake yi wa so guda ɗaya tak maras algus. Burinshi a rayuwa ya mallake ta, ta zama uwar 'ya'yanshi, ta zama ita ce birni da kauyen zuciyarshi. Duk da waɗanan burikan da suke kwance a ma'adanar sirrinshi, ranar da mahaifin Fatima ya umarce shi ya turo magabatanshi, fargaba ta lullube shi har ya kasa gane farinciki yake ji ko akasin haka.
7 parts