DIYAR DR ABDALLAH

By Aynarh_dimples

44.4K 6.3K 1.1K

Zuciyar sa yana mashi wasiwasi, abinda yake gudu shi ke shirin faruwa dashi. Bai taɓa samun kansa cikin wanna... More

One - Kankana
Two- Ruwan Sama
Three - Ummata
Four - IPhone
Five - Annoba
Six - Wanene Mahfooz I
Seven - Mahfooz II
Eight - Mahfooz III
Nine - Mabuɗin Zuciya
Ten - Kallon Kallo
Eleven - Farin Wasa
Twelve - Mugun Mafarki
Thirteen- Permanent Stalker
Fourteen - Rarrafen Carpet
Fifteen - Ƙarfi Yaci
Sixteen - Bazan Barki Ba
Seventeen
Eighteen - Ni Ce Asalin Diyar Dr Abdallah
Nineteen - Naga Wajen zama
Twenty - Mijin Tauraruwa
Twenty-one - Annihilation
Twenty-two - Pound Of Flesh
Twenty-three - Ribar Haƙuri
Twenty-four Bazan Barka Ba
Twenty-five - Love That Hurts
Twenty-six -Rendezvous
Twenty Seven- Idan Tayi Ruwa Rijiya
Twenty-eight - To Be Tainted
Twenty-nine - By Whatever Means Necessary
Thirty - Sun Shuka Sun Girbe
Thirty-one- Miscreant

Thirty-Two - Déjà-vu

2K 234 90
By Aynarh_dimples

Mahfooz zama yayi yana tagumi, tuna abubuwan daya faru dashi yake tun sanda iyayen sa suka rasu. Da kuma zaman dayayi a gidan Fauziyya har kuma barinsa. Sannan kuma da yanda yayita zaman kansa kafin su Faisal suka dauke shi. Tabbas yaga rayuwa kala kala kuma kullum fatan ƙarewan wahalar sa yakeyi. Haƙiƙa mutanen da bai masu komai ba sunci zarafin sa. Sai kuma wata zuciya ta raya masa, 'kaima kayi ma Naseera'

Sam ya daina tunata, komai nata ya riga ya ɓoye a chan ƙasan zuciyar sa. Shifa har yanzu baiga abinda yayi mata ba. Na farko bashi bane yace tayi kama da Fauziyya, sannan bashi bane yace ta fita har mutane suka yi mata fyade. Ai kowa zai iya bin wannan hanya a lokacin, yasa yasan ba laifin sa bane. Amma duk da haka ya cire girman kai ya bata haƙuri. Maimakon ta haƙura ta barsa shine ta nema illanta shi. Cikin ransa shi yana ganin wautanta saboda meye zata ki faɗa masa cewa tanada kanjamau dan cin zali. Haka yayita tunane tunane akanta tareda kwashe mata albarka sabida ya tsallake rijiya da ƙafar baya. Yana cikin haka sai wani notification daga email ɗinsa yazo masa.

Kungiyar kwallon ƙafa ne a chan Ontario dake ƙasar Canada suke buƙatar sa akan yazo da gaggawa domin ya buga masu. Shi a duniya yana bala'in san Arsenal, amma ko wannan ɗin babu laifi. Tunani ya soma akan ya zaiyi da auren Rumasa'u dake kansa, sannan ga Zubaida da zai aura nanda sati biyu. Yasan tabbas idan yagaya ma Daddy cewa ga abinda ya faru za'a ƙarya ta shi ace saboda baya san auren ne yana neman guduwa. Abubuwa dayawa yayi tunani akansu daga karshen saiya yanke shawara ya naɗe kayansa ya gudu.

Balle gudu ba yau ya saba ba, ya gudu daga gidan Alhaji Sani ya dawo Kaduna. Yanzu kuma zai gudu daga Kaduna ya koma Canada. Saidai yanzu ba kamar da bane. Abu kaɗan za'a iya tracking ɗin mutum. Yafi so yaje chan ayi training da sauran abubuwan fitness kafin season ɗin kwallo ya gabato gadan gadan. A lokacin sai ya dawo hutun sati ɗaya yayi masu bayanin, kuma ma yayi signing contract ɗinsa ba damar breaking promises, suba ƴan Nigeria bane masu saɓa alkawari. Yanzu sai a ƙulle mutum. Idan kace zakayi abu dole kayi.

Haka yayi replying email ɗin yace ya yarda, coach ɗin wanda yana tareda wayansa a lokacin yayi mugun jin daɗi. Dama tuntuni yake kwakwan Mahfooz bayan ya buga ma Naija a Fifa. Nan ya sake amsa Mahfooz yace ya shirya kayansa, visa ɗinsa zai zama ready nan da kwana biyu. Murna mara mitsaltuwa ya mamaye Mahfooz. Anan yayi maza yayi uninstalling su whatsapp, twitter, Instagram da Crowwe ɗinsa. Yasa baisan abinda Kankana tayi ba a Instagram. Koda ya isa gida bai ganta a falo ba. Ya dai ji motsin ta cikin ɗakin ta. Baibi ta kanta ba yanata haɗa travelling bag ɗinsa. Komai nasa ya tattara. Sauran kuma ya ninke ya saka cikin akwatuna.

Da asuba wanda yasan dama Kankana tana barci kuma ba jinsa zatayi ba, ya fito da jakarsa ya ajiye a corridor. A Masjid ya haɗu da Baban Anees makwabcinsa ne, nan ya bashi mukullin motansa akan ya tayashi ajiyewa gidansu idan gari ya waye. Baban Anees bai kawo komai cikin ransa ba ya karɓa, sai kuma Mahfooz ya ajiye ma Rumasa'u takarda.

'Na tafi' ya rubuta kacal sai kuma chèque ɗin dubu ɗari. Abuja ya wuce ta jirgin ƙasa zuciyar sa yana cikin zulumi akan sabon rayuwar da zai ɗaura. Ita Rumasa'u koda da tashi wajen goma sha ɗaya. Batayi asuba ba kuma batada alamar yi. Instagram ta buɗe inda taga tanata trending. Abin ya ɗan taɓata, bata ji daɗi ba yanda ake tsine mata anata kiranta matsiyaciya. Saidai kuma data tuna cewa kuɗi zata samu sai zuciyar ta yayi sanyi. Wajen sha biyu ta fito falo, taga takarda akan tebur amma batabi takai ba. Kitchen ta shiga ta soya kwai da dankalin hausa. A falo ta dawo tana ci tanata fito ta ɗaura ƙafa ɗaya akan ɗaya. Tik tok ta shiga tanata kallace kallace. Sai kawai idanta yakai kan tebur, nan ta jawo saita karanta. Taɓe bakinta.

"Kafi ruwa gudu," ta faɗa a fili sai kuma taga chèque. Nan ta soma washe baki sosai. Abaya ta saka nan take ta wuce first bank dake kawo inda yake amfani dashi. Anan aka bata kuɗin. Ta fito sai taga mutane masu surkule. Sai yasa allura a hanci sai ya fito ta baki. Anan kowa ya washe baki yana kallo. Itama ta tsaya wajen. Ta shafe wajen minti talatin sai kallo takeyi tana babbaka dariya. Abubuwa kala kala sukeyi harda yanka harshen su, laso wuta. Bayan ƙafarta yayi soma zafi. Juyawa zatayi ta tafi sai taga abinda ke hannunta. Ashe ba handbag ɗinta bane kamar yadda take tunani.

Buhu ne aka mayar mata dashi a matsayin jaka. Nata jakar garin kallo an tafi dashi.

"Innalillahi na shiga uku na lalace," ta faɗa da karfin gaske.

"Menene ?" Wani mai saida albasa ya tambaye ta.

"Wallahi anyi min sata ne, an ɗauke min jaka sai aka saka min buhu ban lura ba,"
"Ke dama banda abin ki kinzo nan kinata kallo me kike tunanin zai faru dake?"

Idan ranta yayi dubu yayi mugun ɓaci, gashi bata san wa zata kama ba. Haka tayita sababi ta wuce gida. Shikam Qwaro Ibro Grande Hotel yayi lodging, hankalin sa kwance yanata duba Riyadhul salihin abinsa. Dayake akwai Masjid a hotel ɗin, lokacin sallah yanayi yake fitowa yayi saiya siya abinci ya koma ciki. Haka ya gama kwanakin sa a Nigeria har ya shiga jirgi ya tafi Canada.

Ontario, Canada.

An sallame Naseera daga asibiti, surgery ɗinta yayi kyau sosai ta samu lafiya. Labib har yanzu yana tareda ita bai bar ɗawainiya da ita ba. Ganinta tareda kanjamau, ciki sannan an saketa abin yana mugun bashi takaici. Baya kwana biyu baije gidansu ba, kullum yana cikin lura da ita. Harya samo mata aiki a wani wajen haka, Doctor on call ɗinsu nada family emergency zaiyi wata shida baya nan, shine aka nema replacement. Daɗin abin Labib yasan wajen, ba wani aiki mai wahala zatayi ba. Kawaici check up ne da petty abubuwan. Ko surgery ba zatayi ba, zatayi referring ɗinsu asibitin su Labib tunda shine babban.

Yaune ranar farko da Naseera zata je aikin, Labib da kansa yace zai kaita. Amma sai ta raka shi yayi round a wards tukun. Batayi musu ba ta bishi, dama ita bamai magana bace. Shine yayita jifar ta da hira kala kala. Ita kam daga 'uhm' sai 'uhm uhm' take cewa. Sanye take da riga fara mai chiffon, sai palazzo crape wando kalar ruwan toka. Jacket ɗinta kalar ruwan bula dogo har gwiwarta tasa, sai kuma ta yana kai da ash Gyale. Tunda yaune ranar farko da zata, sai ta fesa kwalliya sosai, koda yake light make-up ne. Idan baka san kwalliya ba bazaka gane tayi wani abu ba.

"Muje muci Crossaint tunda akwai time," yace yana kallon ta.
"Banjin yunwa, muje kaci dai." ta faɗa ba tareda ta kalle shiba.
Ya soma motsa baki zai yi magana saiya fasa, hanyar bukkan da ake siyarwa suka nufa. Shi kuma Mahfooz ya isa garin Ontario murna fal ransa. Ya bar Nigeria tareda wahalar dake cikinta. Wani team member ɗinsa Wanda suka tafi tare Dave yace ya raka shi, ya yanke hannun sa da kwalbar giya yanaso a dinke mashi a asibiti.

Babu musu Mahfooz ya raka Dave suka wuce, sun gama suna kokarin fitowa sai Mahfooz yaga wata mai kamada kalar Naseera a wajen. Mitsike idanu yayi yana kokarin kara ganin lallai itace. Tayi kiba sosai kuma kana ganinta kasan tana tareda ƙoshin lafiya. Da sauri ya ƙarasa wajen cikin rudewa yana so yasan me takeyi a wajen.

"Dan Allah Naseera, idan kinji abu ko yayane ki kirani. Ga beeper ɗin na..."

"Karka damu, I'll be fine." ta katse shi tana murmushi. Girgiza kansa yayi cikin rashin gamsuwa.

Labib ne ya takura ma Baba Abu akan ya bari Naseera tayi aiki, zaman kadaici tana tunani zai mata illa. Gwara tayi aikin datake so tayi koba komai bazata zauna tana tunanin rayuwar data shiga ba.

Matsowa dab da ita yayi, yana kallonta. Ta kumbura tayi fam cikinta yana shiga wata biyar. Idan baka santa ba bazaka taɓa tunanin cewa ciki gareta ba saboda tanada tsawo sai yabi jikinta.

"Ki zauna waje daya kiyi consulting ɗinsu, you know you're pregnant. I don't want to regret this decision..."

Daidai lokacin ne Mahfooz ya ƙarasa wajen, zancen ciki ya saukar masa a dodon kunne. Tauraruwan sa ce tayi aure harda ciki?

"ciki!!!" abinda yayita nanatawa kenan cikin ransa. Da kyar ya saisaita kansa daga cikin shock ɗinda yan shiga. Kwata kwata baisan ya yake ji akan wannan abin ba. Shifa ba santa yake ba amma mamaki yakeyi harta iya cigaba da rayuwar ta tayi aure tanada ciki. Watau harta iya kasancewa tareda wani namiji bayan shi? Duk maganar soyayyar data ke fadi bazata iya rayuwa ba babu shi karya ne. Tabbas mata butulci suka fi iyawa.

Kallon sa tayi saita harɗe girar sama dana ƙasa tamau. Batace mashi komai ba banda kokarin shiga motar Labib watau Aston Martin ɗinsa da takeyi.

"Taura...." ya fara faɗi, saiya buga goshin sa ya gyara, "Naseera... Dama zan sake ganin ki."

Dakata wa tayi ta soma mashi kallon sama da kasa. Shima Labib ya kalle shi, tabbas tunda bamai fita bace yasan wannan a Nigeria ya santa. Cikin mutunci Labib ya miƙa mashi hannu domin suyi musabaha amma Mahfooz yaki. Banda watsa mashi harara kishi tsantsan yana ɗawainiya dashi. Da Labib yaga haka saiya zagaya ta wajen driver ya shiga ya barshi.

Ita kuma kallonsa tayi har lokacin batace mashi komai ba, shine ya sake ƙaƙalo murmushin takaici. Ya soma mata ƙarya.

"Ai kwanaki na haɗu da Doctor a masallacin juma'a, mun gaisa sosai kuwa," ya faɗa yana dariya. Kai kace yayi abin kirki ne, tunda dai DNA ya nuna cewa Rumasa'u ne yarinyar Dr Abdallah, ai dole ya gaida shi tunda surikin sa ne.

"Shine nace masa zani na gaida Umma amma kuma sai tafiyar nan ya kamani banje ba..." ya cigaba da mata bayani kamar ta aike shi.

"Uhm hmm," tace tana mashi kallo cikin idanu. Duk ya tsargu, mamaki yakeyi wai har Tauraruwa ta daina sansa ne? Jikinsa ya hau rawa sosai. Sai kuma ya tuna akan me zata soshi bayan shiya koreta kuma yanzu ta samu wanda yake santa gashi tanada ciki. Sake kakalo murmushi yayi saiya nuna gefen Labib.

"Husband ?" ya nuna shi. Itama kallon Labib tayi amma batace komai ba. Sai ya sake nuna jikinta, "Congratulations ! Allah ya sauke ki lafiya."

Mamaki take sosai yanda yake magana akan cikin kamar ba nasa ba. Tabbas soyayyar Rumasa'u tayi tasiri wajensa harya mance komai. Amma tunda baya so kamar tun farko itama bazata sake matsa mashi ba. Zata raina kuma ta haifa abinta.

" Bye," tace saita shiga.

Haka ya tsaya sororo kamar wanda ruwa yaci. Dave yayi kiran duniya amma baiji ba. Takaici yayi mugun rufe shi. Mamaki yakeyi yanda ganinta farad ɗaya ya zama wawa. Naseera tanada wannan illa a rayuwarsa. Mutsu mutsu kaɗan yanzu zata birki ta mashi lissafi.

Ita kuma hawaye ne ya soma gangaro mata, har suka isa wajen bata lura ba. Labib ne yayi magana cikin babban murya kafin ta karkato ta kalle shi. Cikin kallon tausayi yayi mata magana.

"Lafiya dai ?"

Jan majina tayi tareda share hawayen ta da tissue ɗin motarsa, saita kakalo murmushi ta kalle shi.

"tears of joy, I'm nervous ne." saita bude ƙofa ta fita daga motar. Bai yarda ba amma kuma baiso ya takura mata.

Labib kaita yayi wajen receptionist, anan akayi introducing ɗinta suka bata badge da komai. Saida ya tabbatar ta zauna cikin office ɗinta tareda ganin cewa fridge ɗinta ya cika da diet coke. Tun cikin nan bata marmarin wani abu sai shi musamman idan yayi kankara.

Su Mahfooz da Dave sunje academy inda za'a fara training. Basu kaɗai aka dauka ba, harda wasu daga Asia, Europe da sauran wurare. Su talatin da bakwai ne aka kwaso hazuƙai. Daga nan wanda suka yi training da kyau zasu zama official athletes ɗin Canada.

Suna zaune Coach yayi briefing ɗinsu akan abinda ya dace suyi da wanda basuyi ba. Duk bayanin dayake yi hankalin Mahfooz baya jikinsa. Ya dulmiya chan kogin tunanin Naseera. Ta ƙara kyau, da kwarjini da wani manyanta. Gashi murmushin dayaga tanayi ya kashe mashi jiki. Cikin ya bala'in amsarta. Tuna sanda sukayi alkawarin samun yara tare yayi. Runtse ido yayi zuciyar sa yana mashi nauyi. Farad ɗaya ya susuce. Yama za ayi haka?

"Matar wani ce fah" zuciyar sa yana raya masa. Kokarin kauda tunanin yayi amma ya kasa. Komai yakeyi ranar idansa ita yake gani. Takaici sosai yaji, me akayi da Naseera da zata hanashi sakat? Tanada kanjamau fah? Jin kansa yayi yanaso yayi bincike akan ciwon. Yaga da gaske bazai kamaba. Yanaso yaga kota yaudare shi kamar yadda yake tsammani.

"Idan ka gani me zakayi?" wani zuciyar ta sake faɗin masa. Runtse ido ya sake. Sai kuma ya soma jin haushin kansa. Suna cin lunch sai aka ce suzo za'a yi masu medical check up. Ga doctor ɗin tazo.

Gwiwa a sanyaye ya miƙe, yaje wajen ya zauna. Yayi tagumi yana dana sanin gudu wa, saboda da bai gudu ba bazai ganta ba balle ya shiga yanayin nan. Layi ya matso an kai kansa. Cikin sanyin jiki ya tashi, anan ya ganta. Cak ya tsaya. Sai gabansa ya soma faɗi zuciyar sa yanata gudu. Itama ta kalle shi. Duka nata yakeyi itama kamar gudun jirgin. Coach ne yayi magana.

"Mahfooz, go on she's waiting."

Da kyar ya murza ƙafar sa ya ƙarasa, yanda yake tafiya kai zaka rantse gurgu ne. Cin tuntube yayita yi.

Shi kuma Labib tun jiya yake kokarin ya gayama Naseera abinda ke ransa. Bai damu da cewa bazawara bace, bai damu da Kanjamau ɗinta ba, bai damu da cewa zai raina yaron wani. Ya yarda da kaddarar ta kuma ya aminta da halinta. Yanaso tana haihuwa a daura masu aure. Saidai baisan yadda zata ɗauki abin ba. Ya lura tsohon aurenta yayi mata giɓi mai wuyan cikewa. Amma abinda ya sani shine martaban mace shine cikin ɗakin mijinta. Yanke shawara yayi gwara yabi ta hanyar mahaifanta Baba Abu, shine zai gaya mashi matakin da zai bi.

Sanda Mahfooz ya ƙarasa wajen ta ya matsar da kujera ya zauna. Yanda ta haɗe rai kamar bata taɓa ganin sa ba shi yafi mashi takaici. A kalla ai murmushi sunna ne kuma shi dan uwanta musulmi ne. Sai kuma ya tuna ganin karshe dayayi mata, yanda ta mirgino daga bene damun sa. Yanda ya guje ta a bainar jama'a. Inda ta nema alfarman sa amma yaki aminta da ita. Cikin rawar murya ya motsa bakin sa kaɗan tareda magana.

"Tauraruwa," yace chan ƙasan maƙoshinsa yana kallonta cikin idanu.


Wannan kenan!

#Naseera
#Rumasau
#Mahfooz
#Tauraruwa
#MijinTauraruwa
#DiyarDrAbdallah
#Dimpilicious
#FullyDimplated


Ainakatiti ⚡

Continue Reading

You'll Also Like

62.1K 1.6K 10
مافيا - حب - قسوه - غيره renad231_5 مرت سنه والقلب ذابحهه الهجر ومرت سنه والهجر عيا يستحي الروايه موجوده في انستا : renad2315
525K 21.1K 89
Join the ride full of possessiveness, love,hate,pain,happiness,joy,rudeness.
50.8K 6.5K 72
"Se refiere a la belleza de corta duración de la flor de cerezo" ╰──➢ Advertencias ✧ ⁞ ❏. Omegaverse < SLOW BURN ⁞ ❏. Todoroki Bottom! ⁞ ❏. Smu...
563K 6.7K 26
Lost, Lose (Loose Trilogy #1) She's a girl of hope, Lisianthus Yvonne Vezina. A teen-year-old girl who focused on her goal... to strive. But everyth...