SOYAYYA KO SHA'AWA

Da jami1020

81.8K 4.4K 610

labarine da ya kunshi rikitacciyar soyayya da ramuwa,Wanda masoyan suna son juna Amman sun kasa gasganta haka... Altro

page 1
page 2
page 3
page 4
page 5
page 6
page 7
page 8
Page 9
page 10
page 11
page 12
page 13
page 14
page 15
page 16
Page 17
page 18
page 19
page 20
page 21
page 22
page 23
page 24
page 26
page 27
page 28
page 29
page 30
page 31
page 32
page 33
page 34
page 35
page 36
page 37
page 38
page 39
page 40
ONE YEAR ANNIVERSARY 🎂🎂🎂
page41
page42
page 43
RAMADAN KAREEM
page 44
page 45
page 46
page 47
page 48
page 49
page 50
group din maza
page 51
p52
p53
p54
p55
Announcement

page 25

1.3K 81 3
Da jami1020

SOYAYYA KO SHA'AWA

BISMILLAHI RAHMANUR RAHIM

Zauren jarumai writers association

Allah ka bawa mahaifina lafiya ka jikan mahaifiya ta kasa aljanna makomar ta ka haskaka kabarinta amin.

Mallakar jamila(maman amir)

Wattpad jami1020
***********************

Page 25

Not edited

Ina jiran amsar ki fa ta kara yin shuru , sai ji tayi ya wani kyal kyale da dariya, ke kar fa ki dauki magana ta serious da wasa nake yi miki fa, ina so kawai naga yadda zaki yi ne, hmmm kawai ta iya cewa amman jikin ta yayi sanyi don wani iri kawai take ji a jikin ta.

To ga lemon naka nan ni zan tafi kasa, no ki dan dakata don Allah akwai abinda nake so na tambaye ki in ba damuwa, kallon da tayi masa shi ya nuna masa cewa zata saurare shi don Allah wacce makarantar kike zuwa kuma ajin ki nawa yanzu?

"Ai ina ganin wannan bai shafe ka ba akan abinda ya shafe ni" to ai abinda ya shafe ki ni ma ya shafe ni madam, to ta ina ya shafe ka? Yayi shuru (yarinyar nan ta na da wayo ya fada a ransa) saboda ke sister din kawata ce kuma kanwata afnan kin ga kuwa abinda ya shafi afnan ai ya shafe ni, to ni bansani ba! Sai kaje ka bincika ai ta harare shi, to kika sani ko na bincika din amman bakomai zanje na kara bincikawa din madam.

To ka ban hanya zan wuce ko "ga abinda kace a kawo maka zaka sha baka sha ba ka tsaya kana ta surutu" eh ai ke kika koya min surutun don ni ba ma'abocin magana ba sai a kanki, wai yau me yake damun ka ne? "Ni ma bansani ba fa don Allah ki taya ni binciken abinda ke damuna pls! Ki hakuri kuma da abinda amatullah tayi miki, ta kara hararar sa yace eh bakomai tun da ni na janyo miki ko? To nan gaba ya za a yi ke nan, kamar ya nan gaba ta tambaye shi, no bakomai kawai ina fatan dai kawai komai ya zo mana cikin sauki.

Salamu alaikum amira ta bude kofar tare da yin sallamar ni fa ya ashfaq ban.... Bata kara sa ba maganar ta makale mata ganin yadda suke, ita kuwa aleena wata irin kunya ce ta kama ta ta yadda amira ta riske su, amira ta kalli
A

shfaq tace " ya ashfaq ya dai" nothing ya mayar ma ta don shi ko a jikin sa, tasa dariya kawai tana hasko wani abu a zuciyar ta.

Ni fa na duba na duba ko ina axikin motar banga takardun da ka ce ba, is ok ma lil sis kije kawai na duba anjima yanzu ina son nayi wanka ne, ok ta juya zata fita aleena tai saurin ce ma ta ki tsayani ma na mu ta fi tare, dama tare kuka zo ne da ita da zaki ce ta tsaya? Amira ko na jin haka tai sauri tayi gaba tana murmushi.

Wai don Allah meye haka ne meke damunka? Ka kyale ni na wuce mana ni ban ma ji dadin yadda amira ta zo ta same mu ba saboda bana son zargi a rayuwa ta kar ta dauke ni mai wani hali daban! Ko? Yace mata, wallahi zan ture ka na wuce idan ka fadi kaji ciwo ba ruwa na," you are welcom dear "ya ce mata har da wani bude hannu, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, to ko dai dama dan iska ne iskanci yake son yayi da ni, eh fa haka ne gaskiya in ba haka ba meye na wani tattareni haka tana ta tunani, nan zuciyar ta ta kara amince mata ai ga abinda ya ke son yayi da ita.

Sai kawai ta fashe da kuka " don Allah ya ashfaq kar ka aikatamin haka karka raba ni da kima ta wallahi in ma don ina yi ma rashin kunya ne na dai na ba zan sake ba don Allah" me ashfaq zai yi in ba dariya ba sosai ya rinka kyal kyalewa da dariya har da rike ciki lallai yarinyar nan yarinya ce ga kuma tsoro she is innocent, i like her.da ya gai ta cigaba da kukan ne yace ke tsaya me kike tunanin zan yi miki ne?ni dai na roke ka da Allah ka bar ni naje gidan miji na lafiya, hahhhh to waye mijin na ki?

Ta rasa wa za ta ce sai cewa tayi Aliyu sunan sa, nan da nan dariyar ta makale masa ya wani hade rai da gaske kike kina da wanda zaki aura? Ganin ta samu chance tai sauri ta daga kai, magana zaki yi mini ba daga kai ba ya fada cikin tsawa ran shi ya kara baci, eh da gaske nake amman me kika gama cemin dazu ?cewa kika yimin ba kya kula kowa ko ko dama karya kikeyi? Eh ta fada muryarta na rawa don bakaramin tsorata tayi ba da shi.

What!!! Just get out from here i said get out from here! ya kara fada cikin karaji to ta dan raba ta kusa da shi don yaki bata hanya ta wuce sai huce yake yi, tana gani ta sami hanya sai ta jiyo ta kalle ahi still bai juyo ba yana yadda yake sai huci yakeyi, hmmm yqnzu in na kyale shi ya sani kuka a banza ke nan tab tayi kwafa tare da tunanin me zatayi masa kuwa sai kawai ta dauki warin takalmin sa daya da ya dawo da su daga office, ta kira sunan sa ya ashfaq yaki juyowa ta kara maimaitawa sannan ya juyo idanun sa sunyi ja, tace ga ladan sani kukan da kayi ta jefe sa da takalmin sai a kirjin sa gafff, ya yar kara kadan tare da rike kirjin nasa ni kika je fa saboda kin raina ni?eh di wa yace ka sani kuka ta murguda masa baki, kawai sai ya biyo ta a guje, ita ma ta kwasa a guje tayi hanyar sakko wa daga kan bene.

Ta sa karfa daya ke nan a kan step din zata sauka daidai lokacin ya kawo hannu zai rike ta, ya janyo hijab din ta to bai rike da kyau ba hijabin ya kubce ita kuma kafar ta ta zame sai ta fara gangarowa daga step din jikin ta yana rolling, shima kuma hijabin da ya kuf ce masa kuma ya riga ya bada karfin sa a gaba sai shima ya fara gangarowa, aleena tana gaba shi kuma yana ba yanta suna gangarowa a tare.

Su mom da amir suna zaune falo suna hira suka ji karar kamar ana fadowa daga step ba suyi aune ba sai ga aleena a kasa wanwar, kafin suyi magana suka ga shima ashfaq a kasa kusa da aleena, a tare suka sa ki salati gaba daya suka yi kan su, mom ta dagaaleena tana cewa subhanalillahi, shima amir ya daga ashfaq din yana cewa garin yaya haka kuka fado daga kan bene daga kai har aleena?

Wayyo Allah mom bayana ciwo kai na tna rike kan tana kara shigewa jikin mom.ashfaq ko duk da ya dan ji zafi sai bai nuna ba kawai ya hau kan kujera ya zauna, mom tayi masa sannu sannan ta kwalawa amira kira ta zo ta dauko mata ruwan sanyi don dama tana kitchen din tana kara sa aikin da aleena takeyi kafin ahsfaq ya sa su aiki, "to mom ga ni nan zuwa" ta fito da ruwa ganin aleena kwance jikin mom sai ta karasa da sauri tana tambayar me ya faru,

Wallahi gangarowa su kayi daga kan bene, suwa kuma mom ta tambaya da mamaki a fuskarta, ga su nan mana aleena da ashafaq, gangarowa mom kuma duk su biyun a tare? Eh mana ko zan miki karya ne, sai kawai ta kama dariya sosai har da rike ciki, la'ilaha illallahu amira meye na dariya me makon ki tausaya musu sai ki kama yi musu dariya? To ai mom abin ne abin mamaki ta ya akayi suka fado? To amir ka taya ni jin wannan batu, ko kai zaka gaya mata tafi yarda ne.

Sai a sannan amira ta ankara cewa ya amir fa na cikkn falon, lil sis baki yarda ba ne?a'a na yarda mana ta fada tana kimtsa nutsuwar ta , taje wajen aleena da take ta rakin bayan ta da kan ta na ciwo tace sannu sis Allah ya sauwake ya kiyaye gaba sannu, aleena dai bata ce komai ba yan shagwaban sun tashi, to karbi ki sha ruwan kin ji 'diyata mom bazan iya ba ta kwabe fuska to bari na baki, mom wacce irin shagwaba ce wannan da kawai ta fado daga kan bene tace ruwa ma ba zata iya sha da kanta ba ni ya akayi banji ciwo ba sai ita!

To in ban da abinka ka hada kanka da ota ne kai da kake namiji kato ota kuwa fa mace ce fa ku jimin ikon Allah ya ma kamata ka zo kayi mata sannu ai ba katsaya kana ta faman magana ba, ita ko amira ta shiga tunanin to ya akayi har suka fado daga bene kuma duk su biyun kuma a tare, kai duk yadda akwayi akwai wani abun wallahi a tsakanin su to ko dai ya ashfaq san aleena ya keyi ne ba ya so a sani yanzu sai nan gaba, hmmm bari dai sai na bincike su dukkan su naji ta bakin kowa har da ya ashfaq din sai na tambaya duk wani hade ran sa da zaiyi kuwa.

Mom ta saki salati kun ji yadda jikin ta yayi zafi kuwa kai ka zo ka duba min yarinyar nan fa kada wani abu ya same ta fa, bari na cire miki hijabin ki ko aleena sannu ita kuwa da gaske zazzabin ne ya zo mata don dama ba wahala jikin ta ya fara zafi idan taji wahala.haba mom meye abin dubawa a nan kawai dai lalaci ne in ji ashfaq, kai idan ba zaka zo ka duba min ita ba sai na kira amir ya zo ya dubata da dinta dai ba kai ka dai ne likita ba a dan harar shi, kai amir zo ka duba min ita.

Ashfaq na jin haka sai kawai yayi sauri ya mike yace sorry mom ai abin bai kai haka ba, amir yasa dariya kawai don yasan dalilin da yasa yayi sauri ya ce zai duba ta din wato don kar na taba ta hahhhh.yana kara sawa wajen ta ya dan rankwafo kanta yace to mom ki cire mata hijab din mana ta ya zanyi na duba ta a haka, sai mom ta cire mata hijabin duk da aleena tana ta dan rike hijab fin don ba ta so a ganta babu hijab, da dai ta ga ba sarki sai Allah dole ta sako hijab din amman sai ta sa hannuwan ta ta dan kare kirjin ta a wayance, duk yana lura da ita, gaban sa ya shiga faduwa ganin surar ta a bayya ne, ya kalli kirjin ta da mamaki ganin baiwa da Allah yayi mata a wajen shi duk tunanin sa bai ta ba kawo cewa tayi cika haka ba, ga farar fatar ta ta bayyana jikin nan fari tas da wani irin sheki da fatar ta takeyi.duk wannan gane gane da yayi cikin 'yan secon ni yayi su nan ya gofe Allah da ba amir din ne zai duba ta ba da tuni duk shi zai ga wadannan abubuwan na sa(kai kuji ashfaq dama har ta zama mallakin na sa ne bamu sani ba to ko son ta ya keyi ne hmmm)

Ya tsugunna a gabanta tana jikin mom ya kai hannu zai taba kan ta ta dan ture hannun sa ba tare da kowa ya lura ba ta banka masa harara duk da ransa a bace yake sai da yayi murmushi ba wanda ya lura da su sai amira ashe shi ma amir idansa na kan su ya gani, ita kuwa mom baiwar Allah ta dauka ko duk cikin zazzabin ne yasa ta ture masa hannu ya hakuri aleena ya duba min ke cinji, ta amsa da ka sai kawai ta rufe idon ta.

Ya kurawa fuskar ta ido na wasu dakiku shi ya ma man ta da cewa akwai mutane a wajen sai da mom tace son ka duba ta mana ka tsaya kana kallon ta sai kunya ta kama shi, ya kai hannu ya taba goshin ta sanna ya taba wuyan ta, duk wanna abin da ya keyi karfin hali kawai yake yi duk yakai hannu jikin ta sai ya ji shock a jikin sa, ita ma kuma takan ji wani irin bakon yanayi a jikin ta.

Ya ga dai ba zai iya cigaba ba, ya tashi tsaye mom na komai bane ba fa fever ne kawai ya kamata saboda fadowar da tayi bari na kawo mata pain relief da paracetamol in tayi barci ta tashi zata warke yayi sauri yahau sama amir ya bishi da kallo yana dariyar mugunta saboda ya gano irin yanayin da abokin sa ya fada.

Yana shiga dakin sa kan gadon sa ya fada yayi rub da ciki ya shiga tunanin abinda da ke faruwa da shi, wannan yana yin da yake shiga wani irin abu ne haka me hkan ke nufi sai akan aleena kawai ya ke jin haka.
******

07038185042

Comment

Comment

Pls share, vote and follow me on my wattpad.

Love you all fans

Continua a leggere

Ti piacerà anche

Alina Da ihidethisapp

Narrativa generale

1.4M 36.7K 75
The Lombardi family is the most notorious group in the crime world. They rule both the American and Italian mafias and have many others bowing at the...
275K 7.9K 77
(Fixed/Fan-TL) Top idol group Stardust, whose members disappear like dust. The group that used to have seven members ends with four members... "Is...
934 24 8
ADAM da BIE mata da miji ne da suka yi auren soyayya, kamar kowanni aure TOGETHER FOREVER suka yiwa junansu alƙawari, sai dai bayan shekara goma Bie...
11.1K 1K 56
Shin abinda nayi zan samu sassaucin allah kuwa bare na iyayena,wanda sun yi alkwarin duk wanda yayi mua'amala dani bashi basu. Taya zan tunkaresu bar...