DIYAR DR ABDALLAH

By Aynarh_dimples

44.4K 6.3K 1.1K

Zuciyar sa yana mashi wasiwasi, abinda yake gudu shi ke shirin faruwa dashi. Bai taɓa samun kansa cikin wanna... More

One - Kankana
Two- Ruwan Sama
Three - Ummata
Four - IPhone
Five - Annoba
Six - Wanene Mahfooz I
Seven - Mahfooz II
Eight - Mahfooz III
Nine - Mabuɗin Zuciya
Ten - Kallon Kallo
Eleven - Farin Wasa
Twelve - Mugun Mafarki
Thirteen- Permanent Stalker
Fourteen - Rarrafen Carpet
Fifteen - Ƙarfi Yaci
Sixteen - Bazan Barki Ba
Seventeen
Eighteen - Ni Ce Asalin Diyar Dr Abdallah
Nineteen - Naga Wajen zama
Twenty - Mijin Tauraruwa
Twenty-one - Annihilation
Twenty-two - Pound Of Flesh
Twenty-three - Ribar Haƙuri
Twenty-four Bazan Barka Ba
Twenty-five - Love That Hurts
Twenty-six -Rendezvous
Twenty Seven- Idan Tayi Ruwa Rijiya
Twenty-eight - To Be Tainted
Twenty-nine - By Whatever Means Necessary
Thirty - Sun Shuka Sun Girbe
Thirty-Two - Déjà-vu

Thirty-one- Miscreant

1.1K 196 42
By Aynarh_dimples


Hello Dimplicious Empire, sorry for my abrupt silence. Abubuwan ne sai a slow, anyway in sha Allah I am back for good. Thanks for all the calls and messages. Godiya to Hajia Baby Nice for keeping me on my toes, Maman Eemad for dragging me back. Ƴan TASKAR AINAU DIMPLES ance kunyi quiet saboda bana nan sorry for that. Anyway y'all should remain fully dimplated. Don't forget to like, comment and share with your friends.

Jama'a nayi wata uku banci abinci ba, dan Allah a siya littafina Hasken Lantarki ta manhajan Okada ko na samu na kai wani abu bakin salati na. Link yana bio ɗina.

***

Yan biyu babu abinda ya samesu cikin ikon Allah. Sadiya ce ta buge a gwiwa inda jini ya taru saboda farin fata. Sannan tana dingishi kaɗan kaɗan amma bayan nan ita ƙalau take. Haɓon datayi a hanci shima ya tsaya.

Salima kuwa ƙafarta ne ya tsage, sai aka wuce da ita tiyata domin a dinka wajen. Kowa yana cikin jimamin mutuwar Jamila har lokacin. Suna mamakin yanda ta mutu da Darbuzu a bakinta. Al'ajabi suke suna tunanin irin saɓon da takeyi da bata samu damar mutuwa da sunan Allah ba. Aisha ce ta kira Anty Amina domin ta sanar da ita abinda ya faru. Tayi kiran duniya na mamanta amma bata ɗauka ba. Lokacin taje bayi tanata kukan kila Sadiya da yaranta sun mutu. Dana sanin abinda tayi sosai takeyi sannan tana kaico da Mahfooz. Duk wani masifa da bala'in duniya daya auku mata dashi take kuka. Harta idan taci tuntube Mahfooz take tsinemawa.

Cewa takeyi ta tabbata yana daga gefe ya laɓe yana kallonta yasa ta kusan faɗi. Anty Amina babu arziki ta faɗa ɗakin Fauziyya, bata ganta ba cikin falo saita wuce uwar daka. Yau yana cikin rana kwarara data taɓa shiga bedroom ɗin Fauziyya. Sam bata yarda kishiya ta shigan mata ɗaki ba, ko ƙawayenta bata yarda su shiga. Iyakacin su corridor da parlor.

“Me kike min cikin ɗaki?” ta tambayi Amina, a lokacin itama ta fito daga kewaye kenan. Cikin rawar baki da tashin hankali Amina ta soma magana.

“Kiyi haƙuri Anty, dama Aisha ce tace bakya ɗaukar wayan ki wai su Sadiya sunyi hatsari,”

Dayake Fauziyya tasan dawar garin bata kulata ba, dama jiran da takeyi kenan kafin ta faɗa asibiti ace ya akayi ta sani. Mayafi ta ɗauka tayi hanyar falo inda Amina tana bin mata baya, fafur Fauziyya ta hana Amina shiga motar saidai taje ta hau napep tunda bata iya tuƙi ba. Haka ta figa mota ta wuce, a hanya ne ta kalle wayarta inda Aisha tace ga inda suke ta saƙo.

Cikin ikon Allah Amina tana fita ta samu adaidaita sahu, sai tayi chata suka tafi. Idan ranta yayi dubu yayi mugun ɓaci amma babu yanda Amina zatayi da Fauziyya. Idan da sabo yaci ace ta saba da halin Fauziyya.

Lokacin Salima tana emergency ana dubata, hatsarin yayi mugun illanta ta. Gabaki ɗaya ta fita hayacinta.

Halimomo yar kungiyar su na One Love Kankana take so ta nuna ma bariki. A da chan da kyar aka sakata a kungiyar saboda kwata kwata bata iya wanka ba. Sannan batada kyau. Fatar jikinta tayi bleaching ɗinsa kamar mai shafa kumfar lux. Tayi kwana biyu bata social media kamar anyi ruwa an ɗauke, sai yanzu ne ta dawo da zafin ta.

Kamar Kankana itama Halimomo yar talaka ce, gwara Mallam Salisu yana koyarwa. Babanta kam yankan farce yakeyi a bakin tasha. Hotunan data soma bazawa ya firgita Kankana. Sannan gata koda yaushe gefen mota. Kirar Honda ce Camry 2016 model. Ga hannunta sun sha zobben zinare kuma ga hakorin Makka. Cewa tayi zatayi aure ta samu wani mai hannu da shuni.

Kankana ta tsani Halimomo, ko magana bata mata. Cewa takeyi kamar ƙanzo take duk abin kyama. Amma yanda Halimomo ta goge yanzu kamar ba ita ba. Tayi allurai da ake ƙara haske ba wancan wawan bleaching ɗin ba. Jikinta yayi luhu luhu sannan duk baƙin yatsunta babu shi.

Cewa tayi ya kamata yan One Love a haɗu a shaƙata, duk wanda ya samu lokacin ranar Asabar azo aje Crystal dinar, wani sabon wajen cin abinci na ƴan ƙarya. Roban Coca-Cola a wajen dubu ɗaya da ɗari biyar. Sannan roban ruwa kuma dubu ɗaya. Anyi haka ne saboda kada talaka ya samu ya shiga.

Kuɗin dake wajen Kankana dubu biyar ne, tasan bazai isheta ba amma haka ta haƙura tace saita je domin kada a raina ta. Duk kayan data saka sai taga baiyi mata ba, haka tayita canza kaya saida ta saka wani Off shoulder riga da skirt. Abin ya zauna ɗas a jikinta. Haka ta sheƙa kwalliya a fuska tareda shaka eyelashes. Saita ɗauko wani siririn mayafi ta haɗa dashi. Atamphan mai kala da yawa ne, saita ɗauki yellow jaka da kuma jan takalmi duka zai shiga dashi.

Mahfooz yana daga bakin varanda abin duniya ya ishe shi, neman hanyar da zaiyi ya bar Kankana yakeyi. Baya ƙaunar auren kuma ya dauki alwashin saiya rabu da ita. Duk runtsi saiya nemo yanda iyayen sa zasu aminta su yarda ya saketa. Kamshin turaren ta ya dawo dashi daga kogin tunani wanda ya shiga. Tayi kyau ainun amma wannan ba kalar kwalliyar data dace yar musulmi tayi idan zata fita bane. Uwa uba matar aure. Tabbas Rumasa'u ta maida shi baho sai yanda tayi dashi.

“Ina zaki?" yace mata fuskansa babu alamar wasa a cikinta.
Harara ta watsa mashi tana tura hanci saita ce, “Baba inda ka aike ni," saita soma tafiya.
“Dan rashin mutunci abinda zaki ce min kenan a matsayin mijinki.”
Cak ta tsaya ta fara dariya. Hannunta ta soma tafawa saita ce," miji? Wannan ne miji? Idan maza sun tsaya ka isa ka fito? Ka ajiye wuya tsololo kamar mariƙin lema,"
Shiru yayi jikinsa yayi mugun sanyi, wai Rumasa'u wanda tayi komai domin ta aure shi shine take zagin sa kamar sa'anta. Ita kam wucewa tayi ta tare napep ta nufa inda zata.

Duka ƙawaye dake wajen sai kallonta akeyi, ta rasa meyasa suke ta mata kallo. Sai tace "Wai lafiya kunata bina da kallo haka?"

Miemie ce tace, "Naga kamar a napep kika zo, ke kam ba kiji kunya ba. Kina auren Qwaro babban dan kwallo amma bakida mota.”

“Yana wajen gyara ne,”

Tayi masu ƙarya, saita soma tunani. Tabbas ta bada mata kuma ta bada bariki. Meye amfanin kana bariki bakada motar kanka. Dabara ya faɗo mata akan ta tilasta Salima ta siyan mata koda 206 ne kokuma taje gidan radio tayi shela tace ita yar madigo ce wanda ke bin yara ƙanana.

Anata ci anata sha kowa sai gatsa yakeyi saboda ƙoshi, bayan nan suka kunna shisha sunata busa wa. Mazan su da matansu anata hutawa ana chilling hankali kwance anyi hotuna sosai kowa yanata roƙon Kankana tayi tagging ɗinsa idan ta watsa. Tunda tafi kowa yawan followers.

Kafin su tafi Halimomo ta ce an fito da ankon ta dubu saba'in ne. Anan kowa ya soma zare ido suna cewa gaskiya yayi tsada. Ita kuma tace bazata rage ba. Wanda zata aura yana aiki a oil and gas ne kuma bata san ƙaranci. Yin anko shine katin gayyatar ka. Ko maza su siyan ma yan matan su ko kanne.

Gaban Kankana ya soma duka uku uku, abin duniya ya soma yin mata yawa. Ga zance mota data ke so, sannan kuma gana anko. A wajen Miemie ta tura ma Halimomo dubu hamsin. Tayi sabon saurayi dake ji da ita. Kowa daga bada 20k sai 30k. Kankana ne kawai bata bada ko sisi ba. Duk taji babu daɗi. A hankali sunata gaya mata magana wai tayi baƙi ta soma lalacewa. Anan tace tayi barin ciki ne yasa haka. Jaje akayi mata ana mata addu'a.

Halimomo ta rage ma Kankana hanya, tunda ita a NDC take zaune, ita kuma ta dawo gida zuciyar ta duk ya jagule. Bataga Mahfooz ba. Taɓe baki tayi sai ta wuce kitchen domin tasha ruwa.

Shi kuma wajen la'asar Daddyn Faash ya kirasa domin yana san ganinsa, anan ya samo dabara akan cewa zaiyi karyan zai bar gari zashi Arsenal kwallo. Yasa gwara ya sake Rumasa'u kafin ya tauye mata hakkin ta. Tun daya shiga falon yaga fuskan Mommy akwai damuwa. Hajia Fati tana bala'in tausayin Mahfooz, amma zaman aure takeyi kuma bazata iya yin ma mijinta musu ba. Saidai tabbas bata goyon bayan abinda Daddy yake so yayi.

Mahfooz yana zaune saiga Faash ya shiga, dukansu sun zauna sunyi shiru. Shi karin kansa Daddy yana jin nauyin abinda zai faɗa masu. Jiya wani tsohon amininsa ya nema alfarma wajensa. Kuma da farko yace zaiyi tunani akan zancen. Amma yau ya kira sa akan cewa matarsa ta rasu. Abin ya razanar dashi, idan ya kasa biyan masa bukata zai zama kamar yayi masa butulci ne.

Gyaran murya Daddy yayi, ɗakin baka jin komai sai TV dake aiki ƙasa ƙasa. Tashar BBC Lifestyle ne ana nuna interior decoration.

"Faisal!” Daddy ya kira sunan sa.

“Na'am Daddy,” ya amsa mashi.

“Mahfooz !” ya kira sa shima.

“Na'am” ya amsa gabansa yana duka uku uku.

“Kunsan cewa duk wani halarci da uba yakema yaronsa nayi maku, ban rageku da komai ba na jin daɗin rayuwa. Yasa nakeso kuyi min wannan alfarman.”

Shiru yayi yana tunanin yadda zai gayama Mahfooz yana so ya aure yar abokinsa Zubaida, koda yake ance yarinyar babu laifi tanada kyau kuma yaran zamani sunada neme neme. Koba komai ai ba'a gudun mace kuma Mahfooz ya huta. Shi kuma Faash zai aura yar ƙanwar sa Maimunatu.

“Kai Mahfooz tunda kanada aure da kai zan fara, jiya muna majalisa sai wani aminina ya neman alfarma wajena. Yanada yarinya wai ta ganka kuma kai takeso a matsayin miji. Babu abinda zamu kai na kayan aure, kawai shafa Fatiha za'a yi. A farko nace ban yarda ba, amma ganin mahaifiyarta ta rasu jiya yasa nace gwara na taimaka masu. Kuma ina fatan zan iya cin alfarman ka....” daga wajen inda zaiyi aure ya daina saurara. Gaba daya jikinsa sai rawa ya keyi. Gumi ya soma keto mashi ta ko'ina. Sai kansa ya hau sara kamar ana yi da guduma. Daddy ya kalle Faash saiya soma magana.

“Kai kuma Faisal inaso ka aure yar uwanka Maimunatu, yar wajen Aisha....” murna wajen Faash saboda tabbas yana kallon yarinyar daga nesa. Saidai bai taɓa mata magana ba. Ya daɗe bai samu labari mai daɗi kamar wannan ba. Haka yayita washe haƙora kamar gonar auduga.

Sautin kukan Mahfooz sukaji yana tashi, anan kowa ya maida hankalin sa wajen shi. Mamaki Daddy yakeyi akan yadda yake kuka saboda an bashi mata. Wasu da kuɗin su sunje an hanasu shi kuma ya samu a sama yana kuka. Magana Mahfooz yayi ƙasa Ƙasa wanda saida ya sake maimaitawa kafin aka fahimce abinda yace.

"Dan Allah ku rabani da Rumasa'u, Daddy ka taimaka min ka rabani da ita.”

Shiru Daddy yayi, sai ya soma nazari. Yasan aure saida haƙuri. Ba abun wasa bane kuma. Baiga dalilin da anyi faɗa ba sai saki. Ko harshe da haƙori ana samun matsala balle mutane biyu.

“Kayi hakuri Mahfooz, amma nace maka babu zancen saki tsakanin ka da Ita. Kaje ka fahimci matarka ku daidaita. Mata nada rauni ka rinka haƙuri da ita ba komai bane zatayi ka biye mata. Dan Allah Mahfooz karka bani kunya. Balle ma faɗuwa tazo daidai da zama. Yanzu za ayi mata kishiya, wannan abin alheri ne a wajenka. Tabbas zata shiga hankalinta idan taga kishiya zata kwace mata miji. Allah ya yi maka albarka.

Sallah aka kira wanda Daddy ya miƙe ya fita, shima Faash harya kai ƙofa saiya lura Mahfooz bai taso ba. Da da ne da bai damu ba, amma yanzu ya soma sauka daga dokin ƙarfen daya hau. Dawowa yayi ya dafa kafadan Mahfooz, "Man tashi muje muyi sallah,"

Idansa ya ɗaga wanda yayi jazur kamar garwashi, kana ganinsa kasan yana tafasa ne kawai. Leɓansa yana rawa kamar zaiyi magana amma kuma sai baice komai. A haka ya tashi yabi bayan Faash suka wuce Masjid.

Ita Kankana tana zaune akan gado tana kokarin kiran Salima. Tun jiya data tura mata hotuna bata sake nemanta ba. Haushi taji sosai kada ace Salima zata gudu ta barta ne.

Miemie ne ta kirata tace ta tura mata hotunan da sukayi ta wayan ta. Sai a lokacin ta tuna da cewa ashe bata watsa kafafen sada zumunta ba. Nan ta lanƙwasa kafa ta soma editing tanata saka wa. Kamar yadda tayi alkawari haka tayi tagging ɗinsu duk kuma sunyi comment suna gode mata. Sai da ta gama tas sai taga wani wanda tayi ita kaɗai. Hoton yayi mata mugun kyau, ga rana yana haska ta. Ga kuma yanda tasa multi colours da kalan rainbows. Aikam nan tasa caption, tana cewa. "Prouldy a rainbow" saita saka emoji ɗin rainbow a gefe.

Duk abin nan bata san meta ke ciki ba, kungiyar turawa masu kare hakkin yan daudu da madigo da luwadi suke amfani da tambarin nan. Ganin tasa shine sukayi mata magana ta private. Ita kuwa Kankana tana ganin turawa sunyi mata magana sai ta gyara kwanciyar ta soma fara'a. Bayan sun gaisa da ita Lilian, tace itace take kula da hakkin yan kungiyar a kafafen sada zumunta.

Sai take tambayar Kankana ko tana cikin kowane kungiya, dayake Rumasa'u ba kan gado gareta ba bata gane abinda take faɗi ba. Sai tace mata tana kungiyar One Love. Sai Lilian tayi mata bayani akan kungiyar da kyau. Kuma tace taga tasa logo ɗinsu yasa ta biyota domin suyi magana.

Lilian tace mata suna so su shigo Nigeria to make gay tolerance cool. Kuma tunda sunga tanada followers sosai gashi ita musulma ce, idan tana masu campaign mutane zasu aminta da harkan. Gaskiya cikin ranta bataso tayi, saboda tasan illan abinda ake neman ta datayi. Haramun ne kuma tasan cewa a kundin dokokin Nigeria an hana. Idan aka kama mutum yana madigo, luwadi ko daudanci zai zauna a gidan yari na shekaru goma sha haɗu.

Lilian tace mata akwai office ɗinsu a Abuja, sunada da hadaka da united nations wanda suke mara masu baya. Sunce idan taje Abuja tayi signing contract ɗin zata zama official ambassador, ba wani abu mai yawa zatayi ba. Kawai ta rinƙa saka rainbow ne idan tana posting abubuwa. Daga nan kuma sai tayi posting tuta mai yanayin rainbow. Idan mutane suka ga wannan zasu gane tana goyan bayansu ne. Lilian ta lura Kankana batada wani ilimi yadda take magana. Sai tace ma Rumasa'u zata bata dala dubu biyu. Daɗi ne ya kashe Rumasa'u sosai. Tana sha wani mugun kuɗi ne. Ita a tunanin ta zai kai wajen miliyan goma a Naira.

Wani link Lilian ta tura mata tace ta cika. A ciki akwai komai na personal details ɗin mutum dasu BVN da account number. Bayan ta gama cikawa ta tura. Baiyi minti biyar ba sai taga alert ɗin dala dari biyar. Dama wani lokaci datake tareda Lala ta buɗe domiciliary account. Nan ta miƙe da sauri tayita daka tsalle. Sai gashi Lilian ta kirata tunda ta rubuta lambar ta a form ɗin.

Nan suka sake magana sosai inda suka ce a gaskiya suna so suyi aiki da ita, ba ƙaramin jin dadi zasuyi ba idan ta zama jakadiya a kungiyar su. Sun ƙare wayar a cewa gobe Kankana zata Abuja domin tayi signing form da kyau. Murna fal ran Kankana, saita fito falo zata kitchen domin ta dafa indomie. Mahfooz ya shiga yana tafiya da kyar. Duk ya galabaita ga azabtacciyar yunwa yana damunsa. Nan suka haɗa ido, saiya soma magana.

“Rumasa'u dan Allah yunwa nake ji, ki ɗan...” bai ƙarasa ba ta dakatar dashi.

"Zoka gwaguye ni!" saita wuce ta barshi. Haka ta dafa yana jin kamshi ta hana shi. Saida ta gama da kyar ya tashi ya tafasa ruwan zafi ya haɗa ma kansa shayi. Akwai raguwur biredi saiya haɗa shi ya samu ya kwanta. Ranar yadda yaga dare haka yaga rana. Bai iya runtsawa ba. Wai ace auren mata uku cikin shekara ɗaya. Laifin me yayi da nasa jarabawan ya zama haka. Wani fannin yana jin daɗin auren, kila matar tafi bambanta da Rumasa'u. Sai kuma ya tuna Rumasa'u tace tana sanshi kuma bayan aure tana gasa mashi aya a hannu.

Kashegari...

Rumasa'u da asuba ta tashi tayi wanka domin taje ta shiga jirgin ƙasa, daɗin abin Halimomo ita ta biya ma kowa kuɗin abinci yasa Kankana bata kashe kudinta ba. A Maitama Office ɗin yake, bataga Lilian ba tana Peru, amma taga wasu turawa biyu sai kuma wasu yan Nigeria. Gaba daya babu yan arewa a cikin wajen sai ita kaɗai. Nan sukayi ta gode mata suna cewa she's cool. Sunyi sunyi su ɗauki musulmai amma sunki sunce ya saɓa ma addinin su.

Ita kuma kallonsu batace komai ba, Saboda tanayi saboda kuɗin da zata samu. Tasan idan ta kwantar da kai zata samu duniya sosai. Anan sukayi mata bayani ya kamata yan arewa su fahimci kowane mutum yanada yancin zaɓan wanda zai so. Suka ce mata soyayya ai ba haramun bane, yafi kisa. Idan mutum yace jinsin sa zai so bai kamata a hanasa ba. Anyi mata ƙaramin training kamar workshop na awa huɗu. Wajen biyar a Highlander aka kaita Kubwa Train station domin ta tafi gida.

Rumasa'u koda ta koma gida tunani ta somayi, gashi an bata 20k na mota kuma anyi mata siyayya a Jabi lake mall. Haka ta zauna akan gado da kaya niki niki. Tunanin abinda zatayi takeyi. Ance mata kawai tambarin rainbow zata rinƙa amfani dashi, musamman idan zata saka hotuna. Sannan kuma ta haɗashi da love emoji.

A karo na farko tayi tunanin maganan da zata jawo ma yan uwanta idan aka gane ta zama yar misho masu baɗda musulmi. Sai kuma ta tuna dalan da zata samu ta wannan harkan. Wannan ne final dama da zata zama wani abu a duniya. Zata shahara kamar yadda ta daɗe tana bege. Zata fito cikin manyan mata, zata yaƙe yan group ɗin One love. Duniya zasu santa. Lilian sunce idan suka ji daɗin aikinta zasu bata tikiti domin taje headquarters ɗinsu a England.

Wani hoto ta ɗauko nata tayi posting, "it doesn't matter who you love, everyone deserves to love. Nothing should ever stop you, not even gender or religion," saita poster shi da kuma rainbow gefe. Sune suka aiko mata abinda zata rubuta kuma tayi tagging ɗinsu.

Anan ta kashe wayanta tasa charging saita kwanta, har rana wayar Salima baya shiga. Kowa a social media suka bi kasan comment ɗinta sunata tambaya cewa ko ita yar gay ce. Ta samu comment dubu biyu daga taran dare suna takwas din safe sanda ta tashi. Wasu Arnan da Yahudawa suna ce mata congratulations, musulmai kuma suna laanta ta. Cikin haka ne sai Fa'iza tagani itama. Hankalin ta yayi mugun tashi ta rasa yadda zata gayama Inna.

Ranar za'a kai sadakin Fa'iza, tun safe Inna take shara gidan tana goge ko'ina. Tayima Kankana saƙo akan tazo amma bata kulata ba. Fa'iza sai kallon Inna takeyi ta rasa bakin da zatayi mata bayani. Masu meatpie da Samosa wanda aka bada kwangila sun kawo. Ga katan ɗin maltina da Fanta duk an ajiye.

Wajen azahar ya kamata suzo, amma har la'asar babu su babu alamar su. Hankalin Fa'iza ne yayi mugun tashi ta rasa yadda zatayi. Mallam ne ya kira wanda zai zama waliyin Alhaji Sulaiman yace mashi lafiya, saida yayi shiru kamar bazai ce komai ba sai kuma yace gashi nan zuwa. Haka ya tuƙa motarsa yaje dab da magrib. Mallam duk jikinsa yayi sanyi, shima wanda Fa'iza zata aura yaƙi ɗaukar wayanta. Banda kuka babu abinda takeyi. Tsoron ta kada silar Kankana ta rasa miji.

Yana shigowa babu wutan lantarki, candle aka kunna masu suka zauna. Saida yayi ajiyar zuciya kafina ya soma magana.

“Dan Allah kuyi haƙuri, wallahi yaron nan ne ya tsayar damu. Babu yanda bamuyi ba a gyara zance amma yace ya fasa auren.”

Hankalin Mallam ne yayi mugun tashi, amma ya dake yana so ya kai bakin zaren.

“Lafiya dai koh?"

“Eh toh ni bansan yadda zan faɗa ba, amma kayi hakuri kada maganan ya ɓata maka rai."

"Ba damuwa, faɗa kawai ina jinka,"

“Yace bazai iya haɗa zuri'a daku ba, wai ku ɓatattu ne bakuda Allah. Dayayi min jawabi kuma na gamsu.”

Mallam bai gane ba, amma yasan aikin maƙiya ne.

“Kai kam yanzu akan jita jita sai ku fasa babu bincike.”

“Ba jita jita bane Mallam Salisu, na gani da idona. Yarka ce Rumasa'u tayi fito na fito da addinin islama. Kowa yasan yanda mutanen annabi ludu suka ƙare, amma shine ta haɗa hannu dasu ɓaro ɓaro tana tallata munufar su.” saiya nuna masa hoton.

Nan take Mallam ya cire hularsa ya soma fifita, ji yayi kamar za'a cire mashi rai domin zafi. Sai Alhaji Sulaiman ya cigaba da magana.

“Haba Mallam kowa yana maka kallon mutum mai dattako amma sai ka biye ma Yahudawa. Abin duniya ai zai ƙare, ko nawa zasu baku ku tuna lahira yana jiran kowa....”

Nan yayi magana sai yace sun bar kaya da kuɗin na gani ina so da suka kawo. Allah ya haɗa kowa da rabon su. Tafiya yayi ya barsu cikin takaici, sai Fa'iza ta fito domin taji meya faru. Anan aka gaya masu abinda yasa aka fasa auren. Daga ita har Inna suka suka soma. Rumasa'u bata gidan amma annoban ta yaƙi barin su. Idan ka kalle su saika tausaya masu. Suna wahalar akan wacce bata damu dasu ba.

Ita ranar Rumasa'u tsoro ya kamata yanda ake ta zagin ta a comment, saida ta kira Lilian tace gaskiya bazata iya ba. Lilian tace mata baƙin ciki ake mata akan zata samu kuɗi, kuma ta jaddada mata cewa rashin ilimi ke damun yan Nigeria. Ana kokarin UN ta saka hannu domin ayi legalizing same sex marriage, idan lokacin yayi ita ai ta daɗe a kungiya kuma sune zasu jagoranci Najeriya.

Su Inna suna zaune suna kuka sai suka ji an buga masu ƙofa da karfi, kafin kace kwabo yan anguwan su ne na da chan inda suka baro wanda suke Instagram suka gane Rumasa'u. Nan suka biyo su nan domin suci masu mutunci. Duk wanda ya gansu hanya idan aka tambaye su ina zusu sai suce zasu wajen wasu azzalumai ne wanda zasu kawo masu annoba cikin gida. Kafin a kifar da duniya kamar na annabi ludu.

Haka akayi gangami sai ƙofar gidan Mallam. Nan akayi ta dukan kofan har saida ya ɓalle. Gashi anata harbin roof kamar zai faɗo masu. Da sauri suka zura hijab sai Mallam ya fita.

"Rumasa'u muke so
Rumasa'u muke so
Rumasa'u muke so"

Suke ta faɗi suna bubbuga ƙarafai, Anan Mallam yace ba'anan take zaune ba amma basu yarda ba. Sun faɗa gidan sunata fasa masu kaya suna dubawa. Masu sata na yin abinda suka kware. Wani yana zuwa ya wawuso Fa'iza ya soma ja, saida aka ce mashi ba ita bace. Sun ɗauki alwashin daidai da ita zasu.

Da kyar makotan su suka samu suka cecesu. Mallam an zabga mashi gora a bayan sa da kyar yake tafiya. Itama Inna tasha mari anata kiranta uwar tsinanna. Kaca kaca akayi da gidan bazai shiga ba. Harta roof an saka sanduna anata tokarewa

Sai suka shiga maƙota suna hutawa, bayan mutanen sun tafi wajen Isha sai su Inna suka ce gwara suje gidan Rumasa'u su kwana yafi masu arziki. Makotan suka ce su bari da safe amma Inna tace gwara taje chan.

Shi Aliyu yana Zaria inda yake aiki a NBIAS. Haka suka wuce gidanta dake kawo. Mahfooz yaje wajen wani abokinsa da sukayi Kad poly, mota ya kaɗe shi ya karye yaje mashi jaje. Rumasa'u taji ana kwankwasa ƙofa. Tana zuwa taga su Inna da Mallam anyi charko charko. Haɗe rai tayi kamar an aiko mata da saƙon mutuwa.

“Wai menene ?" ta faɗa cikin tsawa.

Takaici ya kama Mallam, bai iya magana ba. Fa'iza cikin kuka tayi magana.

“Dan Allah ki taimaka mana mu samu mu huta anan, samarin unguwa sunyi mana kaca kaca akan...”

Hannu ta daga domin tayi mata shiru, bata bari ta ƙarasa taji cewa itace dalilin dayasa aka cin masu fuska ba.

“Dalla ni ina ruwana, idan kunje an cin maku zarafi meya dameni. Nina ce karku biya kuɗin haya? Nifa banida alaƙa daku. Ni yarinyar Dr Abdallah ce. Wai sau nawa zan faɗa maku. Kuje wajen Kanjamau ta taimaka maku. Dan Allah karku sake dawo min gida. Musamman ke Fa'iza, nasan ke kika kawo su, idan kika ƙara kotu zata raba mu, "

Saita rufe ƙofa da karfin gaske ta wuce, sunfi minti biyu tsaye a wajen babu wanda yace komai. Tasan sarai sunga yanzu zata samu daloli shine suka zo mata maula cikin dare. Matsalanta da talaka kenan, kwadayi da hassada. Sunzo suna so su wawushe ta da labarin su na ƙarya. Sam batayi dana sanin abinda tayi ba, abinda ta sani duk girman laifinta idan ta roƙe gafara kafin ta mutu Allah zai yafe mata. Yasa take kokarin yanzu ta samu wannan contract ɗin yayi kyau, ko bayan shekara biyar ne saita barsu tareda neman yafiya. Lokacin tabbas tasan ta tara dukiya mai bala'in yawa. Sai taje ummara ta shafa kaaba ta nema yafiya. Kenan ta dake tsuntsaye biyu da dutse ɗaya. Murmushi tayi saboda dabarar ta yayi mata mugun kyau.
Mallam ne yayi na maza yace su tafi. Sun fita daga farfajiyar gidan sun somawa tafiya, sai Inna ta soma tari. Zuciyar ta sai zugi yake mata. Tun tanayi a hankali har ta somayi da karfi.

" Innalillahi, Inna jini ne,” Fa'iza tace dataga bakin Inna wanda yayi kaca kaca da jini. Anan numfashinta ya soma daukewa. Kan kace kwabo ta soma lumshe idanta.

Wannan kenan !

#Naseera
#Rumasau
#Mahfooz
#DiyarDrAbdallah
#Dimpilicious
#FullyDimplated

Ainakatiti 🌠

Continue Reading

You'll Also Like

10.9K 508 26
MAFIA STEP - SISTER OF BANGPINK
54.1K 1.4K 21
You, an infamous serial killer in New Orleans, feed on the young. Your days are numbered, but soon you meet a charming man named Alastor. He fills th...
12.5K 1.9K 22
جۆنگ کوک:بە نەفرەت بیت وازم لێ بێنە چیت لە من دەوێت تایهیۆنگ:ششـ ئازیزم بۆچی هاوار دەکەی ئارام بە بۆ باروودۆخت خراپە ༄༄༄༄༄༄༄ جۆنگ کوک:تـ تۆ چیت کرد ت...
Doffy By Loki Pepper

Mystery / Thriller

9.1K 98 3
Have a good vibe