JINAH (Matar Aljani)

By Al_Ashtar

29K 2.1K 242

Soyayya da aure tsakanin jinsi biyu, jinsin aljanu da jinsin mutane More

Prologue
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapitre 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
End

Chapter 24

686 67 9
By Al_Ashtar

💞 JINAH (Matar Aljani)💞
by Malik al-Ashtar ✒️

On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5

You'd like this New ❤️ Story

CHAPTER 24

~*Wilaya Writers association of Nigeria*~
(Home of peace & hospitality).💦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest💦

Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp

Ana yawan fadar cewa duk ana haihuwar mu ne a matsayin mutanen kirki, idan kuma daga baya muka zama miyagu, dalilin irin tarbiyar da muka samu ne, da irin jarabawowin da muka gani da kuma dalilin mutanen da ke kewaye damu... Wata kila haka ne, domin muna zuwa duniyar nan ne bamu san komai ba, bamu iya komai ba, komai muna koyonshi ne anan. Ta dalilin wasu da muke ganin suna aikata abun.

Nasan kun taba ganin yaro na kwarai da zuciya mai kyau amma kuma gidan da ya fito, tasu zuciyar ba mai kyau ba ce? Akwai kuma wani yaron wanda bakar zuciya gareshi, amma gidan su mutanen kirki ne.

Haka akwai wani wanda cikin rayuwarshi, ya taso a na kwarai, rana daya zai juye zuwa mugu dalilin wani abu da aka yi masa, ko kuma wata rayuwa da yake fuskanta...

Toh Fally yana cikin irin wannan rukunin na masu sauya halinsu, kamar an tsoma zuciyarshi cikin ruwan kwalta ta tashi daga launin ja zuwa bakakirin har taso tafi kwaltar baki. Kiyayya ta rufe masa ido, shi da ba zai iya cutar da wani ba ma, amma yau gashi yana cutar da abar kaunarshi wadda a shirye yake ya sadaukar da rayuwarsa saboda ita. Kamar yanda yake yi a halin yanzu. Tana son ta bude ido, amma ya sanyata cikin doguwar suma.

-Baba, me yasa mama taki tashi?
Ayu ya tambayi baban nashi.

-Saboda tayi sadaukarwa saboda ku, saboda ita ne muke har yanzu a raye.

-Kamar yaya, me ta aikata?
Aya ta tambaya.

-Toh zata farka?
Shima Ayu ya kara jefo wata tambayar.

-Eh, amma kuma dole sai na kaita wani guri mai nisa, nesa da nan.

-Toh me muke jira, mu tafi mana!

-Hakan ba sauki gareshi ba, ku ba zaku bimu ba.

-Toh me yasa haka?

-Inda zamu je, basu son da akwai ku ba, kuma idan kuka bimu, zasu ce ku zaku zama fansar ceto mahaifiyar ku. Kuma kunsan mamarku ba zata taba yarda da hakan ba, nima kuma haka. Nasan Sarah zata kula da ku har lokacin da zamu dawo.

Karyar da Fally ya shiryawa yan biyu kenan ba tare da sun harbo jirginshi ba. Yasan idan yace masu zai dauki Jinah ya tafi da ita, ba zasu yarda ba har sai ya fada masu dalili. Yanzu kuwa ya riga da ya karance su, idan zai fada masu wani abu, kuma yasan karya ne, to sai ya fara fadar wani abun da yake gaskiya. Gashi kuma ya hanasu binciken tunanin mutane.

-Ya kamata naje yanzu, domin duk wata dakika barazana ce ga rayuwar ta, zan shiga jikinta domin fadawa yan gidan zata je wani guri.

-Baba kana da tabbacin wannan ita ce mafita?
Ayu ya tambayeshi cikin rashin yarda.

-Domin mahaifiyarku zan yi wannan, domin na ceto ta.
Ya bashi amsa.

Shiga jikin Jinah yayi tare da fitowa daga cikin dakin. Tarar da Sarah da su Nafi tayi waje sannan tace masu :

-Zan fita, yanzu na dawo.

-Ina zaki je ne Jinah?

-Ba dadewa ba zanyi.

-Bari na rakaki.
Cewar Abdul.

-A'a!
Ta fada da karaji.

-Lafiyarki kuwa Jinah?
Cewar Sarah cike da kulawa.

-Eh lafiya nake, kar ku damu, ina son na dan fita ne na sha iska kuma ni kadai nake son tafiya. Dan Allah Sarah ki kular min da yarana.

Kalamanta na karshe sun sanyaya jikin kowa, amma ganin dai tace ba dadewa zata yi ba suka barta ta tafi ita kadai. Tana fita daga gidan, Fally ya bace da ita. Zuwa cen sai gasu sun bayyana a cikin wani surkukin dajin da babu kowa sai kukan namun dawa. Fita yayi daga jikin Jinah, wani daki ne ya bayyana a gabansu, ya dauketa ya kwantar da ita a ciki, har yanzu ba'a hayyacinta take ba. Shima zaunawa yayi dirshen a kasa yana kallonta. Yanayin dakin ne, ya tuna mashi da ranar aurenshi da Jinah, ranar da suka yi alkawarin zama na har abada, alkawarin soyayya har abada, ranar da suka yi alkawarin har abada dayansu ba zai ci amanar daya ba.

-Amma kuma ita taci amanata!
Ya fada da kakkausar murya kamar yana magana da wani.

-Ta yaudare ni! Ya sake fada. Me nayi da na cancanci haka, shin ban sota ba fiye da yadda kalmar so take ba, ban kasance mai kulawa da ita tun daga yarintar ta ba, ban sadaukar da abubuwa da dama saboda ita ba, wace irin wahala bace ban sha ba saboda ita, meye ban rasa ba saboda ita? Me yasa ba zata iya sadaukarwa daya ba saboda ni, sadaukarwa daya... Ta cancanci ta wahala kamar yanda na wahala, ta cancanta, ta cancanta...

Kalamar karshe yayi ta maimaitawa domin tabbatarwa zuciyarshi.

Zafin ma abun gareshi, yanzu babu wata alaka dake tsakaninsa da ita face yan biyu. Alakar auren dake tsakaninsu ta tarwatse, eh sosai ma, domin wanann shine a matsayin fansar kasancewarsu duka hudun a raye. Wannan yake kara sa wutar dake ci cikin zuciyarshi tana kara azalzala. Cewa yake, yanzu shikenan Jinah zata iya tarayya da kowanne irin namiji da take so, ba tare da wani abu ya samesu ba kamar a baya. A takaice dai bai san me zai yi ba, amma a halin yanzu zai nisantata da kowanne namiji, sannan zata biya bisa cin amanar da tayi.

(.....)

Har karfe tara na dare yayi, babu labarin Jinah, hankalin Sarah duk ya tashi, tana tsaye bakin kofar gida, tana kai kawo.

-Har yanzu bata dawo ba?
Cewar nafisa da suka nufo inda Sarah take, ita da dan uwan ta.

-A'a.
Sarah ta bata amsa a takaice.

-Mama ba zata dawo ba yau.
Suka ji muryar Aya a bayansu. Juyawa suka yi suna binta da kallo.

Ayu ne ya kara da cewa :
-Mama ta tafi neman magani, ba da dadewa ba zata dawo.

-Aya, fada mana ina mama?
Abdul ya dan durkusa yana tamabayar Aya.

-Ban sani ba, amma lafiya take.

Dan uwanta ya kara da cewa :
-Eh ku kwantar da hankalinku.

Shuru kowannen su yayi, kowa da tunanin da yake kafin Sarah ta katse shurun ta hanyar cewa :

-Toh ku tashi ku ci abinci kar yayi sanyi.

Washe gari ma, shuru babu labarin Jinah. Sarah bata samun damar runtsawa ba tsawon duka daren. Rana na fitowa, bayan sun gama karin kumallo, ta fita ita kadai neman Jinah, tana tambayar makota da masu wucewa amma shuru ba labari. Haka ke ta faruwa har tsawon kwana biyu. Sarah tabi duk ta rame, bata iya cin abinci, bata samun wani cikakken bacci. Su kuwa yan biyu basu gushe ba suna fada mata, mamarsu tana nan lafiya.

-Kar fa yaran nan da gaske suke?
Cewar Abdul.

-Jinah bata san kowa ba sai mu, bata tuna komai na rayuwarta ta baya, ta yaya zata iya irin wannan tafiyar?
Sarah ta fada tana goge kwalla.

Kafin wani ya kara cewa wani abu, suka ji ana kwada sallama.

-Assalamu Alaikum!

-Wa alaika salam!
Suka amsa amsa sallamar a tare.

Sarah ce ta kara da fadin :
-Bismillah!

Wani mutum ne ya shigo da yar karamar jaka a hannunshi. Mutumin nan ba kowa bane face INFA, wannan wanda ya kusan kashe Hindu, wannan wanda ya dawo ya dau fansar iyayenshi da ta kashe, wanda a hanya ya gamu da tsofin abokanan shi Fally da Jinah...

Bayan sun gama gaisawa, nan yake fada masu shi matafiyi ne, yana bukatar wurin zama ne na kwana biyu kafin ya wuce kauyen Bayana. Yayi tafiya mai nisa ne yana son ya huta.

Ba tare da wani dogon tunani ba, Sarah ta amince. Hakan yanada alaka da ala'adarsu ko kuma nace wasu kauyukan dake iya sauke bako gidansu ba tare da sun sanshi ba, har su bashi duk wata kulawa. Kuma ma da yake Sarah tanada babbar zuciya.

Nafisa da Abdul kuwa mamaki ne yake neman kashe su, ganin yanda Sarah ta karbi bakon da bata sani ba, har suna ganin ma kamar tayi wauta. Koda yake su sun zo ne daga wata kasar kuma a birni suke, basu saba ganin irin haka ba.

Dayan dakin da ba kowa Sarah ta gyara masa, sannan ta kai masa ruwan wanka a bayi. Bayan ya gama ta kai mashi abinci.

-Ina mai gidan ko yayi tafiya ne?
Infa ke tambayar Sarah yayin da takai masa abinci.

-Ya koma ga wanda ya fimu bukatarshi...

-Ayya, Allah ya jikanshi, yasa ya huta.

-Ameen.

Bayan Sarah ta fito daga dakin ta bar Infa shi kadai, ba'a jima ba, sai ga yan biyu sun bayyana a gabanshi, da ganinsu murmushi ya bayyana a fuskarshi kafin yace :

-Yan biyu kuma ruwa biyu! Na dade ina son haduwa daku. Lallai Jinah da Fally sunyi sa'ar samunku.

-Waye kai? Kuma me kake nema?

-Ni abokin babanku ne, mun san juna tun muna yara, amma mun jima bamu ga juna ba har zuwa ranar da kuke tsakanin rayuwa da mutuwa.

-Ta yaya kasan wannan?
Aya ta tambayeshi babu alamar wasa.

-Ina tare da su a ranar da suke kokarin cetonku.

-Abinda kake yi yanzu anan muke son sani.
Cewar Ayu.

-Domin hana baban ku tabka wani kuskure.

-Baban mu? Toh ai ya tafi da mamar mu!

-Kash! Na makaro.

-Me? Meke faruwa ne wai?

-A wancen lokacin da muka hadu, mahaifin ku yayi fushi sosai da mahaifiyar ku, saboda ta zabi ta sadaukar dashi domin ceton ku.

-Amma ai bai mutu ba!

-Eh na sani, sai dai Jinah ta manta dashi da kuma labarin su, kuma yanzu babu wannan alakar dake tsakanin su. Yana tunanin taci amanar shi. Kuma idan aljani yasan anci amanar shi, dawowa yake mahaukaci.

A take, Ayu ya rikida zuwa wani garsakeken mutum, maji karfi sannan yace :

-Bayada hujjar taba koda gashin mahaifiyar mu. Idan kuwa ya cutar da ita, zan manta da cewa mahaifina ne.

-Ka kwantar da hankalin ka. Cewar yar uwar shi, zamu nemo mama.

A hankali ya fara dawowa mutum dai dai, amma bai sake hannun da ya dunkule ba.

-Zamu nemo inda suke!
Cewar Infa.

-Zai yi wuya mu gansu. Cewar Aya da ta rufe ido da alamun tana neman wani abu. Shi ma haka dan uwan nata yayi.

-Yasan zamu san gaskiya, shi yasa ya goge duk wata alama da zamu gane inda suke.

-Kada mu bata lokaci, zamu iya anfani da tsohuwar dabarar mu; mu dinga bi muna tambayar duk wani aljani da muka gani.

-Idan kuma yayi mata wani abun kafin mu gansu?
Cewar Aya.

Girgiza kai Infa yayi kafin yace :
-Baban ku, yana cikin fushi, amma ina tunanin ba zai iya cutar da maman ku ba. Nayi mamakin yanda kuka yi saurin yarda da ni...

-Idan da kanada wani kudirin, da tuni mun sani, babu abinda yake guje mana.
Cewar Ayu.

-Banda plan din baba.
Aya ta gyara maganar dan uwan nata.

-Dan mun yi masa alkawarin ba zamu taba karanta tunanin sa ba, shi yasa yayi mana haka.

Sai da suka bari dare yayi, suka tafi neman Jinah. Sai dai babu alamar Fally bare kuma na Jinah.

(.......)

Har yanzu idanun ta a rufe suke, kokarin motsawa ta fara yi, ji tayi gurin da take kwance bai yi kama da gadon ta ba. Da sauri ta bude idanu, wani irin bugawa zuciyar ta tayi ganin a inda take. Ba'a gidan su ba, bare a dakin ta kuma wannan gurin ba dai ban tsoro ba. A tsorace ta tashi tsaye da niyyar guduwa amma taji kamar an rike mata kafafuwa. Ihun neman taimako ta shiga yi amma babu alamar za'a taimaka mata. Bata jin motsin kowa face kukan dabbobi da iska dake kadawa. Kokarin kwace kafafuwan ta ta fara yi, amma ta kasa.

A wannan lokacin, a maimakon tayi tunanin kanta, tunanin 'ya'yan ta take. Kuka ta fara tana tunanin a yanzu duk inda suke suna cikin matsala. Tambayar kanta take : A ina yaranta suke? A wanne hali suke a yanzu?

Ta kasa gane ya aka yi tazo wannan gurin da babu kowa sai kukan namun daji, kuma ya aka yi ta kasa motsa kafafuwan ta. Kara fasa wani ihun tayi tana fadin :

-A taimake ni! Ku taimaka mini dan Allah!

Fally kallonta yake ba tare da yace da ita kala ba, ita ma kuma ba ganinshi take ba domin ya bacewa ganinta. Yana kallon yanda duk ta tsorata, hankalin ta ya tashi, amma bai da alamar yin wani abu.

Kiyayyar da ke cikin zuciyar shi babba ce, kamar ma jin dadin ganinta yake a wannan halin. Wani bangaren kuwa na zuciyar sa yana gargadin shi akan kada ya aikatawa Jinah haka.

A wannan lokacin ne, soyayyar da yake mata tayi nasara akan kiyayyar. Jinah ji tayi kafafuwan ta sun dawo daidai, da ganin haka kawai sai tayi kokarin guduwa, shi kuwa kiyayyar ta sake maye gurbin ta. Jinah taji kafafuwan nata sun sake komawa gidan jiya.

-Jinah!!!

Zuciyarta ce taji tayi wani mugun bugawa da taji an kwalo mata kira.

-Waye nan? Ku taimake ni dan Allah!

Shuru Fally yayi.

Sautin kukan ta gaba daya ta bude, shi kuwa abinda ya tsana kenan. Baya son jin kukan ta kuma baya son ya sake ta.

Daga karshe, shiga yayi jikin ta sannan ya fito da ita daga dakin.

Tafiya yayi ta yi har ya kai cikin wani kauye. Mutane suna ta kallonshi, amma fa bashi din suke gani ba a zahiri face Jinah da ya shiga jikinta. Wasu har tsayawa suke suna yaba kyawunta, wasu kuwa cewa suke suna sonta, ta nuna masu gidan su, domin su ga iyayen ta. Wannan abun shi ya kara harzuka Fally. Wani makirin murmushi yayi, lokacin da wata shu'umar dubara tazo masa. Ya raya a ransa : yau zan dandana irin shedancin Hindu.

Zuwa yayi bakin wata rijiya yayi zaune. Cen sai ga wani mutum yazo wucewa, ganin Jinah bakin rijiya ya tsaya tare da matsawa kusa da ita.

-Masha Allah! Baiwar Allah daga ina kike haka? Tun da aka haifeni ban taba ganin irin wannan kyan ba. A wannan lokacin, kunnuwa, zuciya, hanci da kuma bakina sun shiga hassadar idanuna sakamakon su kadai suke iya ganin wannan kyakyawar halitta taki. Kalamai sun min karanci. A kanki a shirye nake na rasa duk wata dukiyata domin ki zamo matata.

Mutumin matsowa yayi dab da Jinah, shafa gashinta yayi sannan yakai hannunsa kan kuncin ta.

Kalmar "fusata" ba zata iya kwatanta fusatar da Fally yayi ba. Ji yayi kamar ya shako wuyan mutumin nan ya jefashi cikin rijiya. Amma kuma da ya tuna da shirinsa sai ya kyaleshi kan a fara ta kanshi, ba zai kara yarda wani katon banza ya sake fadawa Jinah irin kalaman da wannan mutumin ya fada.

-Zan so na kashe qishi na a tare da ke.
Mutumin ya fada da wani shu'umin mumurshi.

-Kana nufin kana bukata ta?
Cewar Jinah ko kuma nace Fally.

-Abinda nake bukata kenan, kuma zan mayar dake matata.

-Toh ba damuwa, amma mu fara zuwa kaga iyaye na domin su sanka.

-Yanzu kuwa, babu bata lokaci sarauniya ta.

-Aha biyo ni.

-Dakata, bari na je na debo wani abu daga cikin dukiyata domin so nake nayi saurin shiga zuciyar iyayen ki.

-Toh, ina jiran ka.

Bayan wasu yan mintuna sai ga mutumin ya dawo da wata 'yar jaka a hannun sa. Suka dauki hanyar zuwa gidan su Jinah, yana ta zumudin zai auri wadda zata kece masa raini a wajen mutanen kauyen su. Sun yi tafiyar da ta kai mintuna talatin, mutumin ya fara gajiya.

-Bamu kai bane? Ya tambaya.

-A'a, mun dai kusa.

Sun taka yar tafiya kenan, sai gasu a daidai dakin da Jinah take kwance dazu.

-Anan kuke? Toh ina iyayen naki? Mutumin ya jerowa Jinah tambayoyi cike da mamaki.

-Sun tafi gona, amma ka zauna, yanzu sun dawo.

-Zan iya zaman jira har illa masha Allahu, idan har zaki zamo matata.

Ya tsorata sosai lokacin da suka shiga dakin, ganin yanayin dakin da kuma duhun dake gareshi. Juyowa yayi da niyyar yiwa Jinah magana, amma babu alamarta sai fuskar Fally da yayi tozali da ita. Kokarin guduwa yayi, amma yaji kamar an sakawa kafafuwansa siminti. Bayan kuma dan lokaci, yaga fuskar Jinah ta dawo daidai. Murza idanunshi yayi domin ya tabbatar ko sune ke zagin shi.

-Zamu iya yin wani abun kafin iyayena su dawo.
Cewar Jinah. Shuru yayi yana tunani, kafin ya yankewa kansa cewa wata kila gizo ne kawai ya gani dazu. Jinah ta kara da cewa :

-Kana son ganin abubuwan dake boye a cikin kayan nan?
Ta fada tana nuni da kayan dake jikinta.

Shi kuwa wani bude idanu ya shiga yi kamar tsohon maye, cike da sha'awa.

-Na fara ganin wannan lafiyayyan jikin naka tukun.
Cewar Jinah.

Cikin kyaftawar ido, sai ga wannan mutumin ya kwabe kayan jikinsa baki daya. Idanun Jinah suka fara zubar da hawaye, da alama yanzu tana cikin hayyacinta amma ba duka ba, hakan na nufin kwalwarta na aiki amma jikin ba ita ke controlling dinshi ba, ta zama tamkar yaron da ake koyawa tata..tata. Duk wani motsin ta wani ke yi mata shi ba ita ba. Wuka ta dauka, ta rike hannu, ta dumfaro wannan mutumin.

-Me..me kike yi haka?
Mutumin ya fada cike da tsoro, kokarin ja da baya yake. Kuka Jinah take cigaba da yi, bata son aikata abinda take kokarin yi, shi kuwa Fally abinda yake so kenan. Ta sha wahala, yana son ganin ta wahala kuma yayi nasarar hakan. Jinah tana kuka, tana girgiza kai, ta kama mazantakar wannan mutumin tasa wuka ta yanke gaba daya.

Wata razananniyar kara ta saki, ta cutu iya cutawa, ta yanda take jin kamar zuciyarta zata fasa kirjinta ta fito. Ita da ko kaza bata taba yankawa ba, yau gashi tana aikata wannan danyen aikin.

Fita Fally yayi daga jikinta gaba daya. Sakin wukar tayi da sauri, ta dora hannu a ka, jikinta ko ina rawar tsoro yake.

-Me na aikata haka? Meke faruwa da ni? Wayyo Allah na!
Ba tare da taji an rike mata kafafuwa ba, ta ari na kare ta fito daga dakin da gudu. Tayi ta gudu, sai da tayi nisa, sai gata kuma ta dawo gaban kofar dakin. Haka tayi ta yi, idan tayi tafiya mai nisa sai ta sake tsintar kanta a daidai dakin. Ta gaji sosai, kwantawa tayi a kasa, tare da rufe idanu da tunanin ko zata farka ta ganta gida tare da yaranta da su Sarah. Domin wannan abun ya wuce hankalin ta, sai dai ko mummunan mafarki!

-Mafarki ne nake! Mafarki ne nake!...
Ta shiga maimaitawa ba kakkautawa har sai da taji wata murya tace mata :

-Wannan gaskiya ne ba mafarki ba, kuma yanzu kika fara gani...!

------------------------------------------------------------

Idan naga comments mai yawa zan yi saurin update 😡 domin naga da alama babu readers a yanzu.

©Al_Ashtar

Continue Reading

You'll Also Like

2.4M 153K 97
လူတိုင်းပါးစပ်ဖျားမှ ဇမ်းဆိုတဲ့ကောင်က အပေအတေကောင်လို့သမုတ်လဲ သူတို့သတ်မှတ်ချက်အတိုင်းသွားပါစေ.....ကိုယ့်ထမင်းကိုယ်စားပြီး သူများစကားတွေကိုထိုင်ခံစားန...
383K 9.4K 83
"ပူတင်းလေးကဘာလဲ" "ကိုကို့အပိုင်" "ကိုကိုတို့ကရောဘာလဲ " "မောင်နှမ" "ဟာ..."
148K 7.6K 56
TSANTSAR HALACCI labarin khausar da Aman. TSANTSAR HALACCI labari ne dake qunshe da abubuwan mamaki..yaudara..cin amana. ..uwa uba kuma TSANTSAR HAL...
4.7M 526K 58
{Both Zg&Uni} အသေမခွီးရတောင် တစ်ချက်တော့ပြုံးမိဖို့ အာမခံပါတယ် ..💚 Start - { 11,8,2020 } End - { 25,11,2020 } အေသမခြီးရေတာင္ တစ္ခ်က္ေတာ့ျပဳံးမိဖို႔...