MATSALAR RAYUWA(COMPLETED✅)

By missxoxo00

3.9K 187 5

Labarin wata ba fulatanar budurwa mai suna FANTA! Da matashin saurayin ta MAHBUB dan birni😉 Written by MI... More

1
2
3
4
6
7
8
9
10
11

5

244 17 0
By missxoxo00


jirginsu mahbub yasauka a safiyar ranar asabar bejira kiran driver ba yaxo yadaukeshi danyasan koyakira baxai samu ba.hanxari yai yatsaida taxi yakaishi har gida.begakowa a parlor ba sede masu aiki daketa Kai kawo wajen ganin sun gyara ko ina agidan.

Dakinsa yawuce kai tsaye Dan agajiye yake ,wanka yai yabi lapiar gado yakwanta danso yake da sassafe yaje hayin ruga yasanarwa baffanin Fanta abinda ke xuciarsa nagaba da fanta.

Safiyar wayewar garin ranar lahadi,mahbub yai wanka yai shirinsa shigar Shadda yaina light golden sannan yasaka hula da takalmi dark golden.

Indomie yadafa yaci da kwai sannan yadau mukullin mota yafita.hayin ruga yanufa amma kafin yakarasa seda ya tsaya awani store yasai cartons na taliya da lemon roba se lemu da ayaba Dan yasan cimar fulani bata wucce haka.

Minti arba'in yai sannan ya Isa kauyen na hayin ruga,ya faka motarsa a'inda yasaba parking.sannan ya'isa kofar gdansu Fanta Wanda yasa almajirai suka tayashi da Kayan,yana xuwa kafin yakarasa gidan wasu yara dake wasa a dakalin kofar gdan suke fadamasa cikin hausarsu wadda bata fita sosai cewar Fanta bata gdan takoma gdan Baffa lado can hayin shanu.nemayai dasu rakashi gidan,nande cikin tafiyar sassarfa suka rakashi rugar ta Baffa lado.

Godia yaiwa yaran tare da zaro kudi yamika masu,girgiza Kai sukai tareda doriyar anhanasu karbar abu agida gun wanda basu saniba,yabawa yai kwarai da hankalinsu.sallama yai asauren gidan wata yarinya taleko taga waye ?kice mahbub ne sanin cewar su baffan sunsanshi.komawatai cikin gidah tareda fadawa baffan shikuma yafito hade da bada umarnin shinfida masu tabarma asauran.

Bayan sungaysa ne mahbub yasa almajiran suka shigo da kayan suka Saka asauro ,Baffa lado yayi godia sosai haryakewa mahbub wasan ya akai yasan cimarsu ta fulani.mahbub yai dangyaran murya kafin yace Wlhy nima baffa tafiya naine shiyasa banxoba naje Lagos nadubo kanwata datai rashin lapia.

Baffa lado yadangutsiri goro aibana kam ana ciwo canjin rani ne,babu komai mahbub Allah deyasaka maka da alkhairi abubuwan dakakeyi.mahbub yace amin baffa,nima de akwai maganar da nakeso miyi dakai idan Kanada lokaci baffa .baffa yawashe baki har inada wani lokaci dayafi yanxu?karkaji komai mahbub fadi komenene karkaji dar dar!yanxu de bari akawomana fura da abinci muci tukun.

Fura aka kawo masu damammiya da tuwon dawa miyar kuka dayaji nama ga manshanu ci sukai suka koshi har lokacin sallah yai sukai sannan suka koma suka zaune,Baffa lado yai murmushi to yanxu tunda ciki se ai magana sosai.mahbub yace Baffa kana Hausa kamar bahaushe hakama innah wuro kun iya hausa sosai akan su Baffa Sheri.ehh kam munfisu iyawa dayake ni nafi shekara sama da goma Ina aikin gadi awani gida a habuja(Abuja).itakuma wuro itama ai itada ardo megidanta sunyi zaman bunni,to kaji yadda akai.ohh okay hakane.

To dama maganar daxan fadama kashine ehm....Baffa tunsanda nafara ganin Fanta nake Santa,to amma kuma banfadamataba saboda naga da alamin yarinta atattare da ita ,toh sena gayawa innah wuro ko anmata miji?setace Dani a'a ba'ai mata miji ba.amma sede neman auren Fanta ba'a wajenta yakeba yana wajen baffaninta.haka mukai da ita.

Baffa lado ya fadada murmushin dayake miji kam ba aima Fanta shiba hasalima yarinyar ita bakula maxan takeba,kuma koda anyi auren da daya daga cikin maxan garinnan batare da anba dangin mijin al'adar da aka Saba yiba to tabbas amaryar xata xama abun nuni kuma gori xeshiga tsakaninta da mijinta.tabbas mahbub naji dadin wannan maganar taka kuma na yaba da hankalinka kwarai dagaske saboda kai Dan mutuncine tunda Kasan mutunci kuma Kanada mutunci .sede inaso Kasan yarinyar nan marainiyace banaso tashiga MATSALAR RAYUWA ,wallahy yadda nakejin Fanta ajinina kamar diyar dana haifa take.sobada haka nabaka auren Fanta katuro magabatanka muyi magana Nima xankira kannena da baffaninta na Uwa.

Mahbub dadi yacikashi kamar Wanda akama bushara.gwiwoyi akasa yai godia sannan yamike xe tafi?haryasa Kai xefuta.baffa lado yatsayardashi bari nakira fantan taimaka rakiya ko.nixankarasa can hayi,nagode agaida mutan gidan.sa yaro yai akakira fanta.wadda tafuto sanye cikin hijabi ja.atare suka jera Suna tafiya bayan tatsugunna harkasa tagaisheshi.

Mahbub ne yakalleta Fanta jia nadawo daga Lagos nawwara Ma tace tana miki gaisuwa kafin taxo.Allah sarki nagode.

Munga Kaya ankai shikin gida angode Allah yasaka da alkhairi.

Mahbub yakalleta muryarsa Na rawa Dan besan tayaya xefadawa Fanta abinda ke cikin xuciarsa ba nagame da ita.ai munyi magana sosai da Baffa.wato Fanta abunda xanfada maki babu wasa cikinsa ko rainin hankali,nande mahbub yakwashe tunfarkon haduwarsu da ita yadda yaji Santa aransa da yadda sukai magana da innartata dakuma baffa lado.

Hawaye Fanta tasoma yi,yanxu xaka iya auren yar kauye dasuke rayuwa cikin bukka?shin xaka iya auren Marar ilimin boko?kaga munashikin MATSALAR RAYUWA!

Mahbub yakalleta Wanda idanunsa sunyi ja saboda tsabar bacin ran maganar datai masa..sssh kakki sake yimin irin wannan maganar,yan kauyen ba Allah ne ya hallucesuba ko ko mutan kauyenma basufi na birni cikin kwanciyar hankali ba,ko ko ahadisi akarubuta baxa'a auri mace ba setana ilimin boko?koko kudaine masu MATSALAR RAYUWA???ance maki mu damuke bunnin bamida matsala?

Sekuma yasassauta murya cikin sanyi wadda xata dadada mata rai,ke nakeso Fanta ba wai a inda kike RAYUWA ba wannan ba MATSALA tabace,kinada ilimin boko ko baki dashi bashi a lissafina,kuma MATSALAR RAYUWA kowa yanada ita bawanda xece maki RAYUWARSA tana daidai ba MATSALA .so please ke nakeso Fanta dake kadai nakeso inyi RAYUWA har karshen xamana adunia.kitsaida hawayen nan naki Dan Allah inba sokike Nima nafara ba ,inkwa harkinaci gaba da kuka to wallahy Nima kukan xanyi!

Da wannan yasamu ya lallasheta tareda fada mata da dadan kalamai masu sanyaya zucia.ahaka sukai sallama haryake cemata acikin satinnan xeturo iyayensa suyi maganar aurensu da baffaninta.yana murmushi yana tuki harya Isa gida dadi yakeji na shima yakuma futa daga bachelor xe more Rayuwarsa in har ya'auri fanta!!!!!







To ko gwaggo xata yadda da wannan sabon al'amari????


Bayan mahbub ya Isa gidah dr haydar yakira yake fadamasa baffan fanta yabashi damar neman auren Fanta kan yaturo magabatansa asa ranar aure,dr haydar yatayashi murna kuma yananan tafe shima dashi za'ai komai.

Bayan mahbub yagama waya da dr haydar watsa ruwa yayi yadauro alwala yai sallah,tare da addu'ar Allah yabashi nasara akan abinda xefadawa babansa yanxu.shafawa yai sannan yamike yanufi parlor din babannasu dake sama tare yake da yar anacinsa gwaggo agefe ,shiga yai da sallama yaiwa baban barkada yammaci shida gwaggo sannan yanemi guri yaxauna akasa kusa da babannasa.

Mahbub yasaukar da kansa kasa baba magana dama xangaya maka.kafin alh sulayman ya amsa gwaggo harta warce to waye bare anan gurin?da har inxaka fadi magana sekanayi kana wani sunkuyar dakai kamar munafiki wani feleke wai baba xanmaka magana.shide mahbub kawai kallon ta yai yakalli baban Wanda dakyar ya iyacewa inajinka mahbub ya akai?

Baba dama Kasan tunsadda Mami tarasu kace na nemo matar aure nace maka bansamu ba tukun.to Allah cikin ikonsa de yanxu naga wadda nakeso kuma marainiyace de amma kafin mahaifiyarta tarasu ta amince ta yadda dani dayake fulanine to Neman aurenta yakoma wajen baffanninta kuma dayake sunsanni saboda munsaba dasu sanadiyar zaman makokin mahaifiyarta.to jiya naje canwurin baffan ta kanin babanta ne toshine yabani damar inturo magabatana ayi maganar aure.

Dafe kirji gwaggo tai,aure???au Neman aure kajeyi batare da saninmuba?to wallahy Baka isa ba,naga namaka maganar izzatu shine hadda wanicemin Kai aure baya schedule dnka,to wallahy Baka Isa ba lalle kanunamin niban isa dakai ba kenan bani nahaifekaba *seta fashe dakukan munafunci*nande alh sulayman yarude yataso yana bata hakuri,Kai mahbub tashi kaje kasa naji abinda kace xanyi tunani akai.dakyar mahbub yatashi da sanyayyar tafiyarsa dawani abudaya tsaya masa awuya amma lalle gwaggo tacika makira bakomi Allah shine shahidi...,

*******

Kwana daya,biyu,uku,suka wuce alh sulayman benemi mahbub ba,gashi harwani Rama yake saboda rashin sanin inda xancen yakwana,nande yayanke shawarar samin wan babansa Wanda suke cema uncle rufa'i shima awata unguwa yake can kasansu da akecema ambassadors street.

Wanka yai yafito sukai kicibis da gwaggo yatsugunna harkasa yagaisheta tadauke kanta kamar bango tagani.bedamuba rakabawa yai tagefanta yawuce bedamu da tambayarta mukullin mota ba danbaxata bayarba,keke napep yatarar yace ambassadors street aka kaishi yasauka yashiga gidan ,gidane flat (bungalow) mekyau dashi.

Ya shiga da sallamarsa parlor ne Wanda xesadaka da kofa amsawa akai sannan yashiga xaune suke uncle rufa'i da matarsa da akecema Ammi laila.gayshesu yai sannan yaxauna.sekwa Ammi Laila tafara Mai wasa lalle farin Wata sha kallo ,yau mahbub ne agidan maraba da mutan cyprus ,captain dakansa,shide mahbub murmushi yai ,uncle rufa'i yace a'a aikwa mahbub yanada xumunci dade dayar ja'irar ce data gudu Lagos sede waya kullum.nande Ammi Laila tatashi takawo masa snacks da milkshake na vanilla sannan tanufi Bari inje in wanka .

Mahbub yadan gyara xama uncle wajenka naxo,uncle rufa'i yadan gyara Karin hularsa to to inajinka...wato uncle dama baba yadade yanacemin innemo aure tun Mami naraye to Bayan rasuwarta Ma yakumamin xancen to alokacinde gaskia bansamu wacce nakesoba.to Allah da ikonsa Mina xuwa kauyen hayin rugar fulani saro nono na barnyardfresh factory to anande nahadu da Wata yarinya bafulatana hakade mukasaba muna sarar nono .marainiyace saboda senasami baffan ta kan maganar Seya amincemin Dana turo magabatana.

To sena sami baba inaso mi maganar to tare suke da gwaggo.nadanyi jinkiri kan nasanar masa amma gwaggwo tatakura kanse nafada ba bare agurin.nande nafadi komai,wallahy uncle kafin baba yabani amsa gwaggo takarbe wai wallahy ban isaba baxanyi aurenba tunda naki auren kanwarta izzatu kuma wai bandauketa uwaba nande tasa kuka ,hartasa baba kamar yai fushi Dani yakecemin wai naje xe nemeni to wallahy uncle xancen da nake fadamaka yau kwana 3 kenan kuma bansake sa baba a'idonaba.kuma ita izzatun datakeso sena aura wallahy uncle yarinyar batada hali duk wani joint se ance yana gurin hakama night parties .

Uncle rufa'i yajinjina Kai xancen banxa kenan wallahy sulaiman yabani mamaki wannan banzar matar tashanyeshi tamaidashi kamar wani waina,wacece kuma izzatu data like seka aureta?wallahy tayi Kadan tatsoma baki amaganar aurenka tunda itan batajan girmanta .kayi hakuri mahbub insha Allah nixanshige maka Bari xankira uncles Dinka anjima su tajuddeen duk xamuje can hayin rugar mune mamaka auren katabbar de kintsattsiyace ko?

Mahbub yace eh uncle yarinyacema 14 nakega xatayi,uncle rufa'i yawashe baki oh ashema yarinyace to Allah yaxabi abinda yafi alkairi yasanya albarka aciki kakka damu .yanxude bari nakira Ammi Lailan taimana serving abinci muci xuwa anjima inka huta seka tafi.kuma muxamu nema maka auren batare da sanin daya dagacikinsu ba shi sulaiman da gwaggon.

Mahbub yai godia sannan yakoma kan sofa yakwanta tare da daukar milkshake yana sha....


Zungureriyar mota kirar siena ce uncle rufa'i ,uncle tajudden da uncle sameer Wanda akecemasa uncle sam,se dr haydar da mahbub Wanda ke agaba titin kauyen hayin ruga suka nufa bisa jagorancin mahbub tundashi yasan gidan ,a gefen rugar sukai parking sannan sukatafi gidan akasa saboda mota bata shiga ciki.

Hayin shanu gidan na Baffa lado suka tsaya inda mahbub yatura yaro akira baffan dukda cewar yasanar masa daxuwan nasu .ba ajima ba baffan yafito daga cikin gidan tareda sauran baffanin nafanta su uku,bayan sunyi musu jabbama jabbama,atare suka jera suka nufi Wata bukka da akatanade danyin taro kowani meeting .

Xama sukai gaba dayansu su bakwai Banda mahbub dayakoma mota bisa umarnin uncle sam,gaggaysawa sukai sannan Baffa lado yasa aka kawo masu abin motsa baki kamarde cikin birni lafiyayyar fura da nono aka kawo da soyayyun kaji se abinci damiyar zabi ga lemo da ruwan roba seda sukaci sukai nak dasu sannan uncle rufa'i yafara magana.

Mungode kwarai da wannan hidima da aka nuna mana,Allah yasaka maku da mafificin alkhairi amin.to abunda yakawomu wannan ruga taku me albarka munxone nemawa mahbub auren diyarku fatma bintu.muna neman yardarku bisa hakan.

Baffa lado yace to Masha Allahu naji dadi kwarai kuma ubangiji Allah yamasu albarka dukkansu,aure kam baxancen hanaku tunda wa'innan yara sundedeta kansu,kuma koda yarinyarnan batasansa tabbas xanbaiwa mahbub ita saboda nayaba da hankalinsa gashi kuma yafito daga xuri'ar gdan mutunci.wallahy nabaku auren fanta babu matsala wallahy,fatanade ubangiji Allah yasanya alkhairi kuma Allah yakaresu daga dukkanin sharrin MATSALAR RAYUWA.yajuya yakalli baffa jaure ko xaka kara wani abin akai?baffa jaure yace a'a duk abunda xanfada kariga kafada dabo (yaya)Allah yasa alkhairi.

Uncle rufa'i yace Masha Allahu mungode kwarai dagaske yanxu xamu bada kudin nagani inaso ne koyaxa'ai?baffa jaure yace ehh tohm mude al'adar rugarnan damuka tashi mukaga anayi tun kaka da kakanni shine maimakon kudin dakuke bayarwa munan anabawa diyar da akeso sa da saniya guda biyu kawai sannan ba a baiwa iyayenta sede baffanta shine xekula dasu yana basu abinci ,abincin dayake basu shine gudunmawar baffan,shixeta kiwonsu harse saniyar tahaifi yaya 10 sannan xemaidawa yarinyar wannan dukiya tata.

Uncle tajuddeen yace toh yanxu shanun xamu siyo mukawo ko kwa kudi xamu bayar se asiya?baffa lawunde yace eh to duk Wanda kuka bayar yayi.nande akai kudin shanun biyu aka dankawa Baffa jaure saboda yanasaida shanu kuma yana kiwonsu.

Uncle rufa'i yace toh yanxu munasan mutsaida ranar daurin aure dan mude kam wajenmu ba matsala ashirye muke yanada gida kuma yanada aikinyi.baffa lado yace eh muma ashiryen muke amma kuma akwai biki da ake na kwana 7 na al'adah xakuganshi bannarakwai bakamar wanda ake abirni ba:1-anayin ranar ice wadda amarya da babbar kawai da kawaye xasu shiga jeji suyo icen daxa'ai amfani dashi har agama biki,

2-akwai ranar rawar shadi Wanda abokan ango xasuyi shadi ammafa nawasa.uncle rufa'i yaidaria yakalli dr haydar tokai seka shirya kaga kuma akwai ranarku,Baffa lado yace kwarai kuwa sannan akwai

3-gasar tatsar itama anayi arana ta uku inda kawayen amarya xasuyi gasar tatso nono wadda taruga cika bokitinta to xa'a bata bijimin sa kyauta.sannan akwai

4-ranar bakin rafi inda xa'akira makida na fulani nan Samari da yammata xasi fati (party).

5-sannan akwai gada daxa'ai akofar gidan megari da yamma.

6-itace ranar daxa'ai walima xa'akira malamai suyi wa'azi.

7-Rana ta akwai itace ranar daxa'a daura aure.to kunji yadda abun yake.

Uncle rufa'i ya washe baki kace xamu sha biki ubangiji Allah yakaymu.yanxu sati biyu yayi?baffa lado yace yayi Allah yakaymu lokacin,nande sukacigaba da hira yadda kasan sunyi shekaru da sanin junansu.uncle tajudden yace haydar kira mahbub kace mungama yaxo su gaysa muxamu wuce tohm uncle.

Dr haydar yafita yana hangowa koxe ga mahbub,canyahango su shida Fanta akasa karkashin wata bishiyar dogon yaro,mahbub yanaganin dr haydar yamike tsaye ya aboki antsayar?haydar yakyalkyale da daria calm down aboki sekace kaixaka daurawa kanka auren ..yakalli Fanta amaryarmu yakike?kunsan fulani dakunya tasa hannunta dayasha lalle tarufe fuskarta inayini dakta anxo lapia?lapia qalau amaryarmu dan nanda sati biyu kinxama amaryar wannan senior bachelor din yakalli mahbub.

Itade murmushi tai,shikwa mahbub dadi kasheshi,Alhamdulillah ya Allah at long last.dr haydar yai Daria to inkagama addu'ar da godiar kaje kagaidasu baffan danxamu wuce yanxu nina koma ciki,mahbub yakalli Fanta .fatma na kinji aurenmu nanda sati biyu ne,xakixama matata Allah nagode maka yakalli Fanta kebaxaki addu'a ba itade murmushi tai yakalleta xaki daina wannan kunyarne very soon.sallama yamata sannan yawuce bukkar dasu baffan suke.

Yana xuwa yatsugunna harkasa yagayshesu ,wasa da raha sukai dasu baffan sannan suka tashi tafiya ,akakira Fanta tagayshesu ita axuciarta take fadin lalle so shu'umine jibi iyayen mahbub gakyau gakudi ga asali itade kam tagodewa Allah bisa wannan babbar kyauta dayayi mata sannan tanufi gida.

Har sunshiga mota aka biyosu da irin katin katin karkaji cike da nono jarka bakwai hade da fura kulli dayawa acikin irin ledojinnan masu baki da yalo (black and yellow)da zabi da kaji dayawa,godia suka masu na wannan kabakin kyauta dasuka basu.sannan suka ja mota suka tafi!

Har suka Isa gidah suna maganar karbar arzikin dasuka masu tabbas Fanta tatafito daga cikin gidan dattako .mahbub yamusu godia shida dr haydar sannan suka tafi.har gidah mahbub yaraka dr haydar tareda Kara masa godia,shikwa dr haydar cayai shine da godia wannan kabakin arxikin dasuka kwaso na Nono da kaji da zabi .


Ana saura sati daya biki,Ammi laila da nawwara da sauran auntys din mahbub matansu tajudden aunty nafeesa da aunty halima da abokan arxiki sukaje hayin ruga Kai lefe akwati saiti biyu Shake da kaya yan gaske tabbas sunsamu tarba suma saboda ammusu cima Iri iri ankuma basu sa da saniya manyan gaske da kudi dubu dari amatsayin tukwici tabbas sunyaba kuma sun Amina da Fanta amatsayin yar Uwa.

Akwana atashi bawuya tsantsar soyaiya mahbub yakewa fanta to ita dinma hakane a wajenta dakyar suke rabuwa kamar wasu Romeo nd Juliet tabbas Suna Bawa soyaiya hakkinta kamar wasu larabawa abinde gwanin sha'awa biki yana dada matsowa dakansa yadauki fanta yakaita spa aka gyara mata jiki sannan akaimata steaming hade da strethening gashin,biki yarage saura kwana biyu yakaita gun lalle akaimata shi both ja da baki,Fanta de tafuto kamar Wata yar Ethiopia abinse yaxama tubarkAllah masha Allah.

Ana I jibi daurin auren uncle rufa'i dakansa shida mahbub sukaje wajen alh sulaiman yana parlor dnsa nasama shida manne masa gwaggo,uncle rufa'i yaxauna bayan sungaysa da alh sulaiman da gwaggo wadda ke aikamasa da sakon harara,shiko mahbub tsakarewa yai waje daya kamar wani bako.Uncle rufa'i yace sulaiman tunda kaga naxo dakaina amatsayina na wanka magana naxo muyi kuma gaskia matarka seta Bamu wuri saboda maganace wadda tashafi xumunci idan kuma baxata tashiba to ni xantashi natafi kuma duk abunda yabiyo baya kada kaxargi kowa se kanka.

Alh sulaiman yakalli gwaggo wadda tabudi baki xata mayarmasa yagirgixa mata kai,tashi kije.tashi tai tsaye kerere naji xanfita amma kasani duk abunda xaka fadamai kmar naji ne ,kuma nagane Kunamin hakane saboda bana haihuwa ai Allah be mebayarwa.Uncle rufa'i yakalleta ya girgixa kai yafada miki mana babu abinda de xaki iya akai tunda bakya wurin aka fada sannan inke jahilace niba jahili bane haihuwa ai awurin Allah take shike bayarwa kuma shike hanawa,dauke kanta tai tafice fuuu kamar iska jan kofa tai amma talabe tana sauraron mexasuce!

Tana futa Alh sulaiman ya dawo kasa yatsugunna yaya Dan Allah kayi hakuri.uncle rufa'i yagirgixa Kai bakomai ai kawaide bakai sa'ar mata bane.abunda yakawoni shine kwanakin baya mahbub yaxo nan yana maka magana kan Neman auren yarinya dayakeso,matarka tayi kane kane tahana kace masa xaka nemeshi amma bakanemeshi ba ,saboda yasan na Isa shiyasa yaje yasameni nakuma share masa kukansa mukaje muka nemamasa auren nida sameer da tajuddeen muka samesu gidan mutunci da karamci sunkarbemu hannu biyu yadda Kasan munyi shekara da sanin juna!

Yanxu de intakaice maka xance muka xaune muka sa ranar aure sati biyu a wannan lokaci kenan sannan sati daya za'ai Ana bikin dayake fulanine acan kauyen hayin ruga nan karamar hukamar Anka to yanxu de jibi ne daurin aure abinda yasa kuma banyi saurin fadamakaba saboda nasan na isane nine nabada kudin nagani inaso dukda sa da saniya suka bukata amatsayin yadda al'adar su take.kuma munhada kudi nidasu tajudden munhada lefe ankai kuma dr haydar abokin mahbub gashinan shine yabuga katin daurin aure dama sauran events din daxa'ai dukda bayan ankawo amarya abokan ango sunhada masu dinner.yanxu gashinan katittinan munrabawa yan'uwa yanxu abokanka xaka rabawa.kokanada abun cewa?

Alh sulaiman ya girgixa Kai Banda abinda xance Yaya se Allah yasanya alkairi kwarai ai mahbub dankane kanada damar kasashi abunda kaga dama ,shiyasa nawwara tacemin taxo amma tana kaduna duba kanin mijinta amma xata iso yau.yanxu jibi asabar daurin auren kenan?Uncle rufa'i yace kwarai kuwa .

Nande suka shiga hirarsu ta xumunci su ukun harda mahbub.....,gwaggo tana labe tagamajin duk abunda suke cewa wani gumi ne yaketo mata yanxu jibi ne daurin auren mahbub?to wallahy basu Isa inko hakan tafaru to wallahy matar seta gwammace bata aureshi ba dansetasan yadda tai tasata a MATSALAR RAYUWA!amma Bari taji mexeje yadawo agurin bokanta bokan Wanda akema lakabi da xokaji aiki.mota tadauka tafice izuwa wani kungurmin daji tashiga ciki tafi minti 30 sannan yamata ixini tashiga xaune yake duk jikinsa wani dige digen ja .shiga tai da sallamarta,tsawa yamata ke mantawa kikai ba a mana sallama anan?ke kanki kinsan sabon Allah muke anan yaxa'ai kimana sallama.jiki narawa tabashi hakuri meyakawoki???

Dama xuwanai gurinka kan wannan yaran danwajen mijina mahbub,Ashe wai yau daurin aurensa saura kwana biyu kenan .wan mijina rufa'i shine yakarfafawa yaran gwiwa yasai kudin auren akai komai na shirye shirye yanxu de kawai so nake ahana auren .bokan yasa hannunsa awani kofi ya ajiye yagirgixa kansa baxan iya Hana auren ba saboda yarinyar da yaron sunada karfin addu'a,gwaggo ta narke fuska yanxu baxaka iya komai akaiba?bokan yasake xubarda ruwan kofin yaxuba wani gaskia baniba bawani bokan daya Isa yaraba wannan auren.to yanxu yaxa'ai kenan?abinda za'ai shine kakki bari su tare awani gidan face Wanda kike acikinsa,sannan kakki Bari Wata auratayyar tashiga tsakaninsu,tahaka xansan yadda xanyi daga karshe naraba auren...toh boka mexan bayar na aiki???yai Wata bazawar Daria ladan aikin aikema kinsani !

Gwaggo ta gwalalo ido boka da aurena da yanxu,yakalleta yawurga mata harara keyanzu harkiran kanki kike da matar aure ?to inde baki bani hadin kaiba togaskia babu abunda xan iyayi maki.daga kaitai sama alamar toh sannan suka nufi wani daki se bayan awa daya darabi tafito da alama taci wahala dakyar ta iya buda Motar taja tatafi!!!!!

Continue Reading

You'll Also Like

12.4K 606 53
MAKAUNIYAR RAYUWA- KASHI NA UKU- BABI ASHIRIN### Fatan alkhairi gareku masoyana a duk inda kuke,alherin Allah ya kai gareku, ubangijin Allah ya biyaw...
13.2K 387 7
Y/n L/n is a Saiyan born of a noble family loyal to the royal family of Vegeta, and the young Saiyan is charged with the role of being Princess Vegee...
12.2K 1K 56
Shin abinda nayi zan samu sassaucin allah kuwa bare na iyayena,wanda sun yi alkwarin duk wanda yayi mua'amala dani bashi basu. Taya zan tunkaresu bar...
185K 369 19
Just a horny girl