UMMI_A'ISHA (THE MAGNIFICENT)...

By missxoxo00

10.6K 549 9

Labari ne dake dauke da darussa kala kala na rayuwa, Mai dauke da tausayi, Al'ajabi ga kuma kauna agefe d'aya... More

1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
18
17
19
END

16

348 28 0
By missxoxo00

Ashraf nagama parking d'in motarsa yashiga cikin gidan hannunsa d'auke da ledojin dayasiyo Kayan k'walam da mak'ulashe,shiga d'akunan yai yana duba Ina Ummi Aisha take d'akin karshe na cikin corridor yaganta k'udundune cikin bargo tana munshari,daria abin yaso yabashi yasan sarai ba bacci take ba yaga side lamps d'in gadon a kunne kaf futulin d'akin ma a kunne suke,k'arasawa yai cikin d'akin yana bin d'akin da kallo sosai yamasa Kyau komai na d'akin k'irar royal ne gawani k'amshi dake tashi na khumra da turaren wuta,yajima yana kallon santala santalan cinyoyinta da suka fito waje kad'an gashi ne ajiki a kanannad'e ga wani sihirtaccen k'amshi dake tashe daga jikin nata,dak'yar ya iya seseta Kansa yasa hannu yana d'an dukan k'afarta ahankali,yitayi kamar baxata farka ba tacigaba da munsharin k'aryarta,

"Ke!"ashraf yace da Ita yana cigaba da tashinta,

"Uhm uhm"tace hakan tana ture hannunsa,

"Wake up abeg ko kuma na hau gadon natasheki"

Ummi Aisha najin haka ta mik'e tana murza idanuwa kamar gaske,

"Ga abinci nan kitashi kici"yace hakan yana mata nuni da ledar

"Na k'oshi nagode"

Murmushi ashraf yai da ke k'ara masa kyawunsa yajima yana kallonta kafin yasa hannu a aljihu ya ciro wayarsa yafara danna nambobi da alama kira xeyi,Ummi Aisha naganin haka ta ware ido tana binsa da kallo murya narawa take fad'in

"Mekake shirinyi hakan?!"takarashe maganar kamar xatai kuka,

"Baffa xankira nagaya masa tunyanzu munfara gardama dake kafin akai ko'ina nasihar daya mana bata shiga kankiba"

"To to naji zanci,naga ba yunwa nakejiba shysa"

"Haba wa y'ammta seda ruwan ciki akejan na rijiya ai"yafadi hakan fuskarsa ba yabo ba fallasa,

Itade shiru tai tana tunanin maganar dayai yanxu take jikinta yafara rawa,ahankali tasakko daga kan gadon tasa hannu a ledar daddad'an kamshin aroma na kajin ya bugi hancinta,hannu tasa taciro cinya k'wara d'aya tafara ci ahankali dakyar tacinye tasa hannu tafara rufe ledar alamar ta k'oshi,

"what the fu.."ashraf yace hakn yana kallonta Sannan yak'arasa kusada ita yasa hannu a ledan yabud'e ta duka yasake tura mata gabanta,

"Nak'oshi wallahi"tace dashi a shagwabance harda langwab'ar dakai wai dukdan yaji tausayinta ,

"Wallahi kinsan Allah sekinci dayawa waxakiwa yanga?!sannan ki bud'e yoghurt d'innan kishanyenshi tatass ba wasa nake dake ba inkuma baxakici ba sena fad'awa baffa"

Bayadda Ummi Aisha ta iya haka tadinga d'urawa cikinta kajin tana korawa da yoghurt,ashraf dake gefe se dariar mugunta yake mata ahankali gashi ko d'an tausaya mata yak'i yayi,seda yaga taci sosai Sannan yace tabarshi haka,dakansa yad'au wanda tarage yasa acikin mini freedge d'in dake gefen gadon,sannan yashiga band'aki gaban Ummi Aisha se dukan uku uku yake,bejimaba yafuto yacanxa kayansa xuwa pajamas(Kayan bacci)kashe fitilun d'akin yai yabar side lamps 'din kawai dasuka bada dimlight,ahankali yakashe d'ayar saura ta b'angaren Ummi Aisha jikinta se kyarma yake,ya lura da hakan yana sane yahau kan gadon ganin haka yasanyata ja baya yasake matsawa takoma c'an k'uryar gado yasake binta,har jikin bango suka Kai ahaka numfashinsu yana dukan na juna,dede kunnenta yai kamar Wanda xe bata side kiss sekuma yafara mata magana a kunnenta cikin wata irin murya me dad'in sauraro ga k'amshin mint da bakinsa yake ,ahankali yafara fad'in;

"Stop thinking negative 'yammata,keda kika tab'a yi menene na tsoro ?!after all ni ba abinda xanyi maki"yakarashe maganar yana taune pink lips d'insa had'e da girgixa mata kai Sannan yasa hannu yakashe fitilar data rage ya mik'e tsaye yafita,

Nannauyar ajiyar zuciya Ummi Aisha tasaki ganin ba abinda ya mata wani b'angaren na zuciyarta kuma haushin kalaman da ashraf yafad'a taji,ahankali ta mik'e daga kan gadon tashiga band'aki tajima tana kallon band'akin don tsaruwarsa komi pink ne harda jacuzzi d'in gashi ansa komai na Kayan wanka ciki,wanka tai,tayi brush ta kuskure bakinta da mouthwash na strawberry tayo alwala tafito,da sauri tasaka Kayan baccinta ta murxa mukulli a d'akin tahau sallar nafulfulinta tajima tana sallah sannan tad'an tab'a karatun alqur'ani tarufe tahau kan gado,bacci yak'i xuwa whatsapp tashiga sosai ta tarar da conversations kala kala Kuma duka messages ne na tayata murnar auren datai haka ma grps d'in ciki ,tabawa kowanne amsa sannan takashe wayar ta ajiye agefe,addu'oi tai tashafa ba ajima ba daddad'an bacci yai awun gaba da Ita,

     Ashraf daya koma d'akinsa ba abinda yake se tunanin Ummi Aisha,daya rufe idonsa donyai bacci ba abinda yake gani se Ita da kyakkyawar surarta,wayarsa yad'akko yashiga kallon selfie d'in daya masu tare zooming fuskarta yai yana kallonta,yasa hannu yana shafa fuskarta,se juyi yake yakasa bacci dayaga abin bana k'are bane adole ya mik'e yashiga band'akinsa yayo alwala shima yatada sallah bashi yai bacci ba se bayan asubah bashi yatashi ba se wajen 12 shima wayarsa ce tafara ringing da sauri ya d'auka don ganin wake kiran?jay shine sunan dayake rubuce ajikin screen d'in,d'auka yayi yasa a handsfree don bacci ne sosai a idonsa,

"Yo dude"jay daya kira yake fa'din hakan dayake a speaker ashraf yasa,

"Yass jay"

" kan balai baku tashi daga bacci ba har shabiyu?!temaka kutashi mutumin banxa sekaje ka sukurkurta masu d'iya kafin wata shekarar kayo wata sabuwa tunda ita kamayar da Ita second hand"

Tsaki ashraf yayi kamar yasa hannu tawayar ya janyo jay don haushi,

"Kai wannan ya dama shine agabanka,ya akai yanxu??"

"Dama batun wannan construction 'dinne tetfund sun amince so xamuje around 12;30"

"Oh bouy"ashraf yace hakan yana dafe kansa,

" kaga babu takurawa anan idan you can't make it babu matsala ciki semuyi replacing da wani yanxu de are you in or out?!kalma d'aya pls saboda bansan abinda xasuxo sunajin haushi"

"I'm in"ashraf yace hakan atakaice sannan yakatse wayan batare dayaji abinda jay xece ba,

yafad'a band'aki yayo wanka within 15 mins harya gama shiryawa,sanye yake cikin yard ash and black yasaka komi black se k'amshi yake,futowa yai daga cikin d'akin yana d'aure agogon hannunsa,dadda'dan k'amshin turaren khumra ne yadaki hancinsa,atake ya lumshe idonsa yana shak'ar k'amshin ko'ina tatass dashi yajima yana kallon babban parlorn saman dayake tashin k'amshi kafin yasauka k'asan nanma k'amshin ne ke tashi daga k'wanyar Kansa ya tsinkayo sanyayyar muryar Ummi Aisha,

"Ina kwana?!"tace dashi tana k'arasa sakkowa daga saman sanye cikin doguwar riga k'irar a shape purple and black tayi ture kaga tsiya da d'ankwalin sosai tayi Kyau tulin gashinta yafito ta gefe kamar kasaceta ka gudu don kyau

"Lapia"yace a takaice amma yakasa d'auke idonsa akanta wani Kyau tayi masa ga lips d'innan sunsha purple jambaki yaso yad'auke kansa  amma gangar jikinsa tak'i

" mama ta aiko ayush da abinci takawo tun da sassafe,

"I'm okay"yace da Ita yana cigaba da tafiya,har yaje bakin k'ofa yajiyo,yaceda ita

"Nafita"

"Allah yadawo dakai lapia"tace dashi tana langab'ar dakai

Ko kallonta beyi ba yasakai yafita amma har cikin zuciyarsa yaji dad'in adduar datai masa,sannan yace amiin cikin zuciyar tasa,fita yai yatafi gidansu jay daketa tsokanrsa sannan suka tafi branch na tetfund dake kano,se wajen to 5 suka gama abubuwan daxasuyi successfully anbasu aikin,wanda kwangila aka basu nasaka pipes a cikin k'asa ta federal university dake dutse saboda banbancewa tsakanin magudanar ruwa data kwata dake k'asan.A wahale yadawo gidah saboda sun cike documents yafi a k'irga dakyar yake driving d'in yai parking motar cikin compound ko takan megadin sa dake doka masa sannu da xuwa bebiba,yashiga cikin gidan dede lokacin da Ummi Aisha da Waliyya ke futowa da alama waliyyan ce taxo wajen aminiyarta ta jayai yatsaya donsu gaysa da waliyyan,gaysawa sukai inda waliyyan ke fad'in;

"Tunda nazo nake tambayanka tace kafita aiki tun safe"

"Ehh wallahi bade harzaki tafi ba?"yace da waliyyan hakan yana kallon Ummi Aisha da ita d'inma shi take kallo,bashigar safe ce ajikin taba wannan karon riga da skirt ne na atamfa ja tayi Kyau sosai,

"Tafiya xanyi aunty ce ke jirana xan rakata unguwa kuma ma na jima tun kafin d'aya nake gidannan"

"ai kamatayai Ki wunar mana har dare ko ba haka ba??"

"Hakane na amsa kuskurena sexuwa nagaba Kuma nagode"

"To bari musau keki"ashraf yafadi hakan dukkoda ba har cikin zuciyarsa yafad'i hakan ba don yagaji lik'is,

"Nagode sosai ango,amma antaromin d'an adaidaita yanxu xekaini gidah Insha Allah"

"To Shikenan kigaida aunty mungode "yace hakan,sannan yaciro kud'i yasakawa Ummi Aisha a hannu alamar tabiyawa waliyyan kud'in mota sobada bayasan waliyyan tagani,sallama sukai sannan yashiga cikin gidah sukuma suka fita wajen gate d'in taya d'an sahun daxekai waliyyan gidah,



"Ummah lapia kuwa meyasa kike acting very strangely?!"cewar baby Kay dake bin magajiya da kallo wadda tasa hannu biyu tana girgixa kanta kamar mahaukaciya,

"La..l..f,lafiya ta lau"magajiyan tafadi haka dakyar se rawa jikinta yake,

"To bakici abinci bafa nakawo maki tea?!"

Kad'a Kai kawai magajiyan tai,da sauri baby Kay tashiga kitchen tahad'owa magajiyan kakkauran shayi cikin kofi yellow tataho dashi takaiwa magajiyan dakanta asunkuye yake tasa hannu biyu tana girgixa shi,tana d'ago kanta tasa hannu tai fatali da kofin yatararratse a k'asa,

"Ummah are you okay?!"baby Kay tace haka damuwa k'arara ta bayyana a fuskarta,

"E"kawai magajiyan tace atakaice,

"No you are not kitashi muje asibiti ummah pls I beg of you"

"Lapiata lou"

"Kode kitashi ko kuma nafad'awa baffa kinada brain cancer/tumor"

Bayadda magajiya ta iya adole ta mik'e suka tafi asibiti gwajin farko likitan Wanda shine de yace tanada cancer yad'ago Kansa yana bin magajiyan da kallo sekuma yamaida dubansa ga baby kay yafara fad'in;

"Tun yaushe takeda Aspergers syndrome?!"

"Asper what?!"baby Kay tace hakan tana ware ido tana kallon magajiyan,

"Aspergers syndrome nace"

"I don't know dr abinda nasani kawai cikin week d'innan tafara acting so strangely tana magana ita kad'ai,jikinta was always shaking ga yawan nightmares datakeyi,kuma at times seta dinga maimaita magana ko abu nace to setaita repeating abun over and over again"

"Shikenan kawai abinda take?!"

"Yh shikenan yawwa sekuma throughout yau bataci abinci ba se nace barin had'a mata tea nahad'o mata tea d'in sekuma tasa hannu ta ture cup d'in yafashe"

"Meye color d'in cup d'in?!"

"Yellow ne"

Girgixa kansa yai yana rubutu a paper dake gabansa,

"Well abinda ke damunta de aspergers syndrome ne duk abinda kikace yanxu symptoms 'dinsane Allah ya kyauta kawai amma sekin d'an dinga binta a hankali saboda yanxu kwa'kwalwarta xata fara aiki da tunani kamar ta yara"

"Toh"kawai baby Kay tace a takaice,

"Yawwa sannan kidinga mata sadaqa abubuwan yanxu seda haka barin ita dakeda cuta kala kala akanta ga brain tumor ga cire mahaifa da akai ga aspergers syndrome kuma"yakarashe maganar yana girgixa kansa,

"Cire mahaifa kuma?!"baby Kay tace hakan tana kallon magajiya da kanta ke asunkuye tana girgixa shi batada maraba da tab'abb'iya

"Of course nan sukaxo suke fad'a itada wata lokacin da ake bata chemotherapy na cancer kidinga mata addua kawai"

Shiru baby Kay tayi tana tunani canta nisa tai ajiyar xuciya godia taiwa likitan daya basu takardar magungunan daxasu siya  dakuma shara'do'din duk bayan sati d'aya suzo,sannan tatemakawa magajiyan suka tafi gidah,suna zuwa gidah bobo yafara kiranta awaya batad'au wani lokaci ba taci kwaliiya ta fita yana waje cikin mota daga bayan layinsu yana danna wayarsa;

"Honey boo"tace dashi tana kallonsa

"Better half"yafadi hakan yana kallonta sannan yasa hannu yana murxa hannunta,

"Wai haryanxu su baban basu dawo ba?!"

"Ohh damn it,better half nikam meyasa baki trusting d'ina ba nace maki suna qatar wani aiki baba yake acan"

"Shikenan"tace dashi a takaice,

"How about a frozen yoghurt?!"

"I'm already drooling sweethrt"

"That's my gurl"

Juya kan mota yai yatasheta suka bar wajen,

    ___Akwana atashi kwanan su Ummi Aisha biyar da aure kullum jiya I yau,ba abinda yatab'a shiga tsakaninsu na auratayya,kullum de xataci kwaliyarta tagyara gidan tsaf,abinci kuwa kala kala mama ce keyi take aiko masu dashi,kodah Ummi Aisha tayi masu wani abin marmarin itadashi bayaci kullum cikin fad'in ya k'oshi yake,bawani hira dake shiga tsakaninsu,takanyi kuka tagayawa Allah buk'atunta kodah sunyi waya da amminta bata tab'a fad'a mata halin datake ciki ba,tun safe yake fita aiki dagacan yawuce school baxe dawo ba se gaf da magrib insabone harta saba,takuma tsaida k'arshen satin aranar daxata fad'a masa itama tanaso tai resuming school tunda ankusa fara exams,ranar lahadi da yamma tana xaune taji tana sha'awar tuwo don rabonta da tuwo tun kafin afara bikinta gashi tunda mama ke aiko da abinci bata tab'a aikowa da tuwo ba,da sauri ummi Aisha tashiga kitchen tad'ora ruwan shinkafar tuwonta,zafi taji garin dukkoda sanyin na'urar ac n dakeyi hakan be hanata jin zafi ba,da sauri tahau sama tashiga d'aki ta canxa Kaya cikin jeggings wando iya gwiwa tasaka vest kad'ai,sannan tad'akko hijabi tasakko dashi kodah taji muryar ashraf tai sauri tasaka,cikin awanni k'alilan tagama tuwon shinkafarta miyar kuka da manshanu dayake duksu Kuka da sauran kayan kad'in miya amminta tayo matasu,sedataci tai nak sannan tahau sama tayo brush tai sallah,xama tai a parlorn saman ta kunna channel na foreign policy tana kalla dayake suna saka updates na diplomatic issue/affairs Kuma field d'intane tunda international relations take,se bayan magrib da dad'ewa ashraf yadawo yai parking motarsa yashigo cikin gidan da sauri yaxaro handkerchief yatoshe hancinsa dashi yanabin parlorn dakallo dake cike da k'amshin kuka da manshanu,gashi babu warin abunda yatsana a duniya irin warin miyar kukan datasha daddawa gashi warin ya baibaye  ko'ina na parlorn,

"Ummi Aisha"ashraf ya k'walla mata kira da k'arfi yanasake toshe hancinsa da handkerchief,

Ummi Aisha dake sama tana kallo tajiyo muryarsa ba kanta kenan tafadi hakan azuciyarta dayake ashraf d'in bame hayaniya bane,maganarsa bata futa sosai shiysa tayi mamaki k'warai dataji sunanta da k'arfi dayakira kamar a loudspeaker,da sauri ta rarumo hijabinta ta d'ora akan vest d'in jikinta gashi hijabin roba ne yana nanewa ajiki se asannan ta tuno vest ce kawai jikinta da sauri tai hanyar d'aki don saka abaya akai muryarsa ce ta tsaida ita daga shiga cikin d'akin,

"Ummi Aisha"yasake kiranta a karo na biyu,

"Na'am just a minute"tace hakan sannan tasaka hannunta cikin hijabin tad'agoshi tayadda baxe kwantar mata ajiki ba,tasauka k'asan da sauri........

                    •✨•

•✨•✨•✨•✨•✨•

K'arasawa tai cikin parlorn  tana sanye da hannunta tacikin hijab,ashraf yadubeta daga sama har k'asa sekuma yad'auke Kansa haryanxu hannunsa rik'e da handkerchief yana toshe da hancinsa..

"Warin me wannan?!"yace da Ita yana binta da kallo

"Wari Kuma?!"ta bashi amsa tana d'an bud'e hancinta don ita kam banda k'amshin kukar datasha daddawa da manshanu ba abinda takeji ,

"Tambayarki fa nake"

"Nide gaskia banajin warin komai"

"K'arya namaki kenan??" hakan yana watsa mata wani sihirtaccen kallo da manyan idanuwansa,

"Bance ba"tadauke kanta don baxata iya jure salon kallonsa ba

"To bani amsa na" yafadi hakan yana sake kafe ta da ido,

Tagane kallonta yake dukkoda kanta a k'asa yake  a hankali tace

"Tuwo nayi shi nake marmari tunba yau ba"

"Amma ki rasa mexaki se

miyarnan me wari"

"Miyar kuka ce fa"

"To nikamde duk abinda natsana a duniya yabi bayan miyar kuka saboda haka kisan yadda xaki wannan warin yafita"yakarashe maganar yanabin Kayan jikinta da kallo wanda tafito d'as kamar barbie doll,

"To"kawai tace atakaice sannan tanufi kitchen d'in

Cikin k'ank'anin Lokaci ta d'ora gawayinta irin na sachet d'innan akan gas minti d'aya ya huru,cikin sauri ta janyo kwalbar turaren wuta dayake ta ajiyeta musanman saboda k'aurin abinci,bulala turaren wutar tai nandanan kitchen d'in ya fara tashin k'amshin turaren Wutar har cikin parlorn, ashraf dake cikin parlorn se asannan yacire handkerchief d'in hancinsa  yana shak'ar k'amshin turaren Wutar dayake tashi,futowa Ummi Aisha tai daga cikin kitchen d'in d'auke da kaskon Wutar tana turare lungu da sak'o na parlorn haryanxu taki cire hannunta tacikin hijab d'in,kasan hijabin tasa tana kame da kaskon wutar,bayan tagama ta ajiye kaskon agefe k'amshin yacigaba da tashi,sannan tai hanyar bene xata koma sama,muryar ashraf ce ta tsaida ita.

"Ke" yace da Ita yana kauda Kansa gefe bayasan ta lura da kallon dayake mata,

Don sosai a idon ashraf xaka gane yana matuk'ar buk'atar matarsa,

Jiki sanyaye tadawo harga Allah ta tsani ke d'in dayake ce mata kamar wata y'ar aikinsa,

"Gani" tace dashi tana isa Inda yake,dagacan baya ta tsaya tana sauke da kanta k'asa tana wasa da faratanta da suka sha maroon nalle/lalle.

"Me zaki a saman da kike sauri haka??"

"Kal..kallon news nake na foreign affairs" tabashi amsa a d'an tsorace muryarta na rawa,

"To bansallameki ba,Kuma inasan kicire hijabin jikinki waye xe kalli wannan jikin naki ?!" Yakarashe maganar yana tab'e bakinsa had'e da d'auke kansa amma axahirin gaskia so yake yaganta ba hijabin don da hijabin ma tayi Kyau ballantana ta cire,

"Sanyi nakeji fa" tafadi hakan tana komawa bayan k'arfen benen,

"Kinsan Allah sekin cire awannan xafin xakice sanyi kikeji??"

K'in cirewa Ummi Aisha tai tana rik'e da hijabin nata kamar wanda xa'a k'wace,ganin baxata cire ba yasanya ashraf mik'ewa daga inda yake yana nufar wajenta,tana ja da baya yana binta har bango suka kai sannan yasa hannu d'aya yatokare ta ajikin bangon tareda sa d'ayan hannun ya xare jan hijabin nata,kasa aikata komai yai ganin abinda ke jikinta Lokaci k'alilan k'wak'walwarsa tafara ayyana masa abubuwa,tunda ga k'afarta yake kallonta har xuwa kanta da yadda tai parking shukunta na baya ga jelar gaban yala yala ta zubo a fuskarta,samin kansa yai dabin rigar jikinta da kallo yadda ta kamata ga rigar transparent ce sleeveless ana ganin komai na ciki don batada maraba da net na sauro gashi Ita kad'ai tasaka,ya jima yana bin jikinta da kallo itako idonta a rufe yake ta takure atsorace gani take duka xekai mata,da sauri yacire hannunsa daga jikin bangon yakoma kan kujerar dake facing inda take a tsaye yaxauna yana kallonta wadda da alama batasan yabar wajen ba sosai ta runtse idanuwanta tana tsakure,zuciyarsa ce tafara kawo masa abinda yaci alwashin baxe aikata ba ahankali yadafe kansa yana girgixa shi,yana taune da lips d'insa yana fezar da zazzafar iska daga bakinsa,seda Ummi Aisha taji alamar yabar wajen sannan ta bud'e idanuwanta a hankali taga baya wajen yana xaune kan kujera ya tsurawa tv ido kamar me kallo amma ba kallon yake ba yanayin da yasameta cikine yasashi wani tunanin na daban daya dad'e beyinba,ahankali taja sayyadar k'afafuwanta ta tsakure a kujera tanayi tana kallonsa gaba d'aya ta tsorata da shi,sallar isha'i ce ta ceci Ummi Aisha daga tsakuren datake ahankali ta mik'e tahau saman ko takanta bebiba,tana shiga d'akinta tai saurin fad'awa band'aki tayo wankanta had'e da d'auro alwala,kakkaurar atamfar daviva tasaka me style bubu sannan ta yane kanta da mayafin abaya bak'i dake akwai ratsin bak'i ajiki,sallah tayi had'e da tab'a karatun alqur'ani sannan ta xauna tana naxarin yadda xata b'ullowa ashraf yabarta takoma makaranta,





"Kasani zikiri ga Allah ta'ala ba k'aramin babbar kariya bace izuwa ga bil adama,ace de mutum kullum besan ya kamataba Ina karatun arabin ka yake?!bokon nan da kukafi bawa mahimmanci babu inda xata kaiku"Mahaifin muhannad ne keta wannan banbamin masifar yanayi yana kallon muhannad d'in da suka fito daga masallacin dake cikin gidan nasu,

"Baba nayi fa"

"K'arya namaka kenan ko angaya maka ba na lura dakai kullum haka kake"

Har cikin gidan suka shiga magana d'aya ce de suketa maimaita ta,ta inda uban yake shiga  ba tanan yake fitaba,se haurawa yake yana saukewa muhannad d'in kwandon masifa da alama ransa yakai matuk'a a b'aci,

"Haba alhaji hayaniyar me kukeyine haka?!tundaga gate akejiyo muryoyinku lapia kuwa??"

Hajia sakeena mahaifiyar muhannad Ita ke fad'in hakan lokacin da ta amsa sallamarsu da suka shigo cikin parlorn xama mahaifin muhannad d'in yai akan doguwar kujerar dake parlorn yaxare hular kansa ya ajiye agefe,se huci yake shi kad'ai,seda ya nutsu sannan yakalli muhannad daya rakub'e agefen kujera daga k'asa yana sunkuyar da Kai kamar munafuki,siririn tsaki yasaki yamaida dubansa ga Hajia sakeena dake jiran yalabarta mata abinda yafaru,

"Wannan yaron da kike gani nibansan wane iri bane shi,acede kullum mutum kamar me k'wak'walwar kifi aita masa magana amma da ike yanuna shid'in d'an yaune seyasa k'afa yai shuri da abinda akace masa?!"

"Alhaji ni kasani cikin duhu Wai meyayine? "

"Wallahi inde mutum yace shi se boko kawai to Wlhy rayuwarsa baxata tab'a tafiya daidaiba,kwita ganin abubuwanku basa tafiya daidai duk wata sabuwar cuta tafito se mutum yayita saboda baya karatun alqur'ani baya lazumi baya azkhar naneman kariya daga ubangijinsa shiyasa ko sihiri akaima mutum ko kanbun baka da na ido ke saurin kama irinku,kullum ga k'anwarka nan cikin karatun qur'ani take da lazumi kala kala babu dare babu rana amma Kai kaine kullum cikin bawa aikin yahudu muhimmanci,gobe kaine kallon wasan barcelona jibi kaine wani had'add'en joint to kasani duk wasu moves d'inka ana kawominsu,Kuma shi karatun islama ba'a girma dashi komai girmanka ance kafita ka nemo ilimi,gashinan samarin unguwarnan harda Wanda suka fika suna had'uwa suna karatun qur'ani da littattafai da daddare,kaikuwa ina kai ai gani kake ka wuce ajinnan kana can kana xargawa karenka igiya se inda k'arfinka yak'are" yak'arashe maganar yanajan dogon tsaki

"Nima ina masa maganr hakan alhaji"

"Babban abin takaici liman na sallamewa xakiga ja'irin yaron nan ya mik'e yafita ko zikirin bayan an idar da sallah ne bayayi,ko addua yayi yashafa bayayi seda yai hanxarin dawowa gidah kulllum 24/7 rik'e da wayar hannunsa yana chatting yana murmushi sekace tab'abb'e bakiji kunyar danakeji ba inyai hakan.Don haka xakiga mutanen cikin masallacin sunbishi da kallo ,kowa yana jiran liman yashafa addua amma shi sauri yake yafuto yadawo gidah,Allah ya kyauta"

"Gaskia kam baya kyautawa tanan b'angaren,Wlhy alhaji namasa,namasa bayajine kawai"

"Ai kunnen k'ashi ne dashi,yadda kikasan shiya haifi kansa haka yake Kuma shi kad'ai ne halinsa yafita daban"

"Ayi hak'uri de alhaji,Kai muhannad kabawa mahaifanka hak'uri ka kuma yiwa kanka fad'a"

"Hak'urin me xebani?! aini beyi mun komai ba yasamu de yayiwa rayuwarsa karatun ta nutsu"

"Baba dan Allah kayi hak'uri kayafemin kuma Insha Allahu xan dingayi" muhannad yafad'i hakan muryarsa da alamar nadama donshi Kansa rabonda yad'auki qur'ani yakaranta ko yai adduar kariya baxe iya tuna yaushe bane,

"Niba kamin komai ba Allah ya yafemu gaba d'aya amiin"

Seda muhannad yatabbatar hankalin iyayen nasa ya kwanta sannan ya mik'e yashiga d'akinsa,

      _____Ranar lahadi ranar  Ummi Aisha tacika sati d'aya agidan mijinta ashraf,xaune take akan gado tagama waya kenan da amminta,tashi tai tana zagaye d'akin da alama naxarin wani abin take,da sauri ta d'auki mayafinta akan stool na mudubi kalar kayanta ta yafashi akanta tulin gashinta yafuto ta baya,sauka k'asan tai da sauri ganin ashraf yasanyata tafiya ahankali,tundaga saman datake sakkowa yake binta da ido sosai tamasa Kyau cikin shigar filtex blue and yellow datai Kayan ya amshi jikinta dukkoda ba kwalliya tai ba amma fuskarta tayi Kyau sosai,ganin tana kallonsa yasashi had'e rai yana cigaba da kallon jaridar weekly trust dake hannunsa yayi hakanne  don karta gano kallonta yake,k'arasawa kujerar dake nesa dashi tai taxauna,ahankli tafara fad'in;

"Dan Allah inaso nai resuming school"tafad'i hakan cikin muryarta me dad'in sauraro,

Shiru ashraf yai bebi takanta ba sema sake bud'e wani shafin yai na jaridar yana cigaba da karantawa amma axahirin gaskia ba karantawar yake ba kallon k'asa yake mata yajima yana bin y'an yatsun k'afarta da kallo dake d'auke da nalle sosai sun burgeshi matuk'a yashagala da kallonsu muryar Ummi Aisha tasake masa reto a kunnensa,

"Kaji"tace dashi kamar xatai Kuka....

"Wai kaji?! ni d'ankine?! Nifa ba d'anki bane kullum maganar ki kenan ko kanajina?ko kaga...haba wannan wacce irin rayuwace? ko ni Idan xankiraki kinji nake ce maki?!sekace wani d'anki na fari" yakarashe maganar fuskarsa cike da takaici,

"Kayi hak'uri toh,inaso nai resuming school ne xa'afara exams pls ashraffff.....!"Yadda taja raffffff d'in har cikin k'wak'walwarsa,

Samin Kansa yai cikeda jin dad'in yadda takira sunansa duk duniya seyaji babu Wanda ya iya kiran sunan nasa kamar Ita,barin yadda tajashi takuma fitar da haruffan yadda suke har magudanar jininsa yaji dad'in hakan, da saurinsa kamar xa'arugashi yace;

"Shikenan ki shrya gobe Idan Allah yakymu xaki fara xuwa"yafad'i hakan yana binta da kallo

"Yeyh thank you so very much Allah yasaka da alkhairi amiin"tace hakan cikeda jin dad'i don bata xaci amsar daxe bataba kenan

"Ameen" yace atakaice har cikin zuciyarsa yaji dad'in abinda tace,shyasa take sake shiga ransa saboda akwaita da addua da Kuma yaba kyauta komai k'ank'antarta,

Haka suka xauna xaman kurame suka tsurawa tv ido suna kallon Indian film d'in 'prem rotan don payo' amma kowannensu da abinda yake sak'awa cikin zuciyarsa.Har shabiyu ta gota itade Ummi Aisha b'ingirewa tai tana bacci se ashraf ne yatasheta yace taje ta kwanta,

Washegari;da sassafe da yake lectures d'in 10 ne dasu da wuri Ummi Aisha tatashi tun asuba datai sallah take shirin sch don d'oki take tayi,tashiga kitchen ta soya chips and egg da ruwan tea,sannan takoma saman tai wanka kafin 8 harta gama kintsa ko'ina nagidan  takuma shirya cikin abayar Lebanon ja ta yane kanta da mayafin abayar light makeup tai had'e da saka jambakinta na kiley 24hrs red se k'amshin strawberry yake ,mild turaruka tasaka,handbag d'inta ta rataya bak'a da covered show d'inta shima b'aki tasauka k'asan parlorn cikin hanxari taxuba chips and egg d'inta taci takora da ruwan tea tasake kuskure bakinta da mouth fresh,se gurin k'arfe tara saura ashraf yasakko sanye cikin manyan kaya riga da wando blue da hularsa xanna bukar light kalar xanen dake gaban rigar se k'amshi yake yayi Kyau abinsa,ya jima yana kallon Ummi Aisha sosai tamashi Kyau musanman dayake red abu yana fito da mace yana Kuma yiwa Ummi Aishan Kyau ga jambakin datasa yasake fito da d'an k'aramin bakinta yayi Kyau dashi,

"Ina kwana?!" Tace dashi tana kallonsa don shid'inma yamata Kyau ba kad'an ba,

"Yana kwano" yace da Ita yana shiga kitchen,

Ko kad'an bata damuba don inde arrogant halinsane tuni ta saba dashi , tun abin yana damunta harya dena,cikin mintina kad'an yafito da cup ahannunsa da alama coffee ne ciki don k'a idane kullum dashi yake karyawa Kuma shi yake had'a abinsa don bayacin abincin datai shiyasa koxatayi cikinta kad'ai take girkawa se megadi datake xubawa,seda yashanye tass sannan yaxuba mata idanuwa yana kallonta,murmushi yai dake k'ara masa kyau yana taune pink lips d'insa,itakwa banda kallon agogo ba abinda take Allah Allah take karsu makara don bataso malami yafara lectures bata class gashi mentor d'intane xe masu lectures d'in wato professor tajuddeen...

"Ina zaki jene?!" Yace da Ita yana murmushi,

Ware Ido tai tana kallonsa cikeda mamaki,ahankali tace

"Makaranta mana jia fa kace yau xanje"

" a hakan xakije?!"yace hakan yana nuna shigarta

Bin doguwar rigar abayar dake jikinta tai da kallo ko kad'an bataga makusaba,sosai abayar take a baje ko kamata batai ba ga mayafinta wadatacce,

"Ai rigan be kama ba"

"Ance maki matan aure na xuwa da kwalliya makarntane?!"

"Ba kwalliya nai ba fa, abaya ne fa"

"Ba dressing d'inki nake magana ba"yafad'i hakan tareda mik'ewa yanufi inda take,

Hannunsa yasa akan lips d'inta masu laushi,

"Is either ki goge wannan jambakin da kikasa koki xauna agidah abinki"

Tissue taxaro da sauri cikin jakarta tashiga goge jambakin,shaf ta manta 24 hrs ne baya goguwa Lokaci d'aya,

"Na goge" tace dashi ,

"I'm not kidding,kode ki goge shi konai tafiyata nabarki kidena b'atamin Lokaci"

Mudubin console d'in dake jikin bango ta duba fuskarta se asannan ta tuno 24hrs kiley jambaki tasa,

"24hrs ne baya fita yanxu kaji?!"tafadi hakan ahankali cikin shagwab'a

Siririn tsaki yasaki had'e da k'arasawa kusa da Ita yasa hannunsa ya jinginata ajikin bango ahankali  yasaka bakinsa kan leb'anta seda ya lashe jambakin tatas gawani kamshin strawberry dasukeyi,sannan yafara kissing nata passionately harda sa hannu yatallab'o k'ugunta,sosai yake kissing d'inta romantically seda Ummi Aisha taji yana k'ok'arin sa hannunsa cikin  rigarta tai saurin k'watar kanta takoma baya,se maida numfashi take har ashraf d'in dake gefenta maida numfashin yake Lokaci d'aya idonsa ya kad'a yai ja,da sauri yadedeta Kansa yafita waje binsa tai abaya tashiga motar,banda murmushin mugunta ba abinda ashraf yake itako Ummi Aisha se sunkuyar dakai take cike take da kunyarsa gefe  d'aya Kuma tsoransa takeji,ganin yadda lips d'inta har d'an kumbura sukai,har suka isa makaranta babu Wanda yakewa wani magana cikinsu....!

Continue Reading

You'll Also Like

23.7K 1.5K 75
Emotional and love story
98.5K 1.4K 49
𝐈𝐭𝐬 𝐭𝐑𝐞 𝐟𝐒𝐫𝐬𝐭 𝐝𝐚𝐲 π›πšπœπ€ 𝐭𝐨 𝐬𝐜𝐑𝐨𝐨π₯ , π€πšπ₯𝐒𝐲𝐚𝐑 𝐒𝐬 𝐧𝐨𝐰 𝐒𝐧 𝟏𝟎𝐭𝐑 𝐠𝐫𝐚𝐝𝐞, 𝐰𝐑𝐒π₯𝐞 𝐬𝐑𝐞𝐬 𝐭𝐑𝐞𝐫𝐞 𝐬𝐑...
126K 7.2K 45
Complicated🀐🀐🀐 Find outπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡
12.3K 606 53
MAKAUNIYAR RAYUWA- KASHI NA UKU- BABI ASHIRIN### Fatan alkhairi gareku masoyana a duk inda kuke,alherin Allah ya kai gareku, ubangijin Allah ya biyaw...