UMMI_A'ISHA (THE MAGNIFICENT)...

By missxoxo00

12K 564 9

Labari ne dake dauke da darussa kala kala na rayuwa, Mai dauke da tausayi, Al'ajabi ga kuma kauna agefe d'aya... More

1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
16
18
17
19
END

15

392 19 0
By missxoxo00



     •✨•✨•✨•✨•✨•

Shirin biki ake ranga ranga from both site na couples 'din bikine Wanda kowa yake lale marhabun dashi,kasancewar ashraf shine namiji babba agidansu Kuma shine auren farko daxa'ayi na babban 'da namiji agidan,to ta 'bangaren amarya Ummi Aisha ma hakan take shiri ne aketata yinsa bikin fari Kuma bikin babbar 'diya agidan....Ankon dasu Waliyya suka fitar yayi Kyau ba 'karya kafin kace me ya 'kare ansake ordering wasu,kowanne event da ankonsa sede ba a tsawwala ba iya nagida-nagidah ne kawai xasuyi amma saboda halin karamci da dattako irin na hafst shiyasa har ma'kota wasu sukai dashin xubin 'daukar farko dukde akan suma su samu suyi ankon Ummi Aishan.

Sosai hafsat da 'yan uwanta suka shiga gyaran Ummi Aisha,gyara ne akeyi matashi wanda yakama daga gyaran jiki ciki da wajensa,harwani 'kamshi ne yake tashi na musanman inde taje waje koda kuwa giftawa tai,yakaka kala itace wadda ke mata gyaran jikin,yanxu kam babu laifi Ummi Aisha tafara maida jikinta duk 'kasusuwan wuyanta dasuka futo kamar sar'ka sunkoma ciki ta'kara fari hasken fatarta ta bayyana sosai,jikinta kuwa harwani luwai luwai fatarta tayi kamar na jarirai,sosai akayo iv cards kala kala na events 'din Wanda 'kwara uku daga ciki na gidansu ashraf ne xasuyi;bu'dan kai,barbecue day da kuma dinner se katin 'daurin aure na musamman da aka bugoshi,sosai akabi dangi da abokanan arziki aka raba masu katinan gayyatar,tun biki na rage sati 'daya gidan ya cika taf da yan uwa na maiduguri,jimetan yola,hadejia da Kuma 'yan kaduna angyare gidan tsaf har fenti aka sakeyi,sosai captain adam yabada ishashshen ku'di aiwa Ummi Aisha komai dakansa kuma tun sanda aka kawo lefe yatafi dubai yai mata siyayyar kayan gadaje da kujeru da komai ma daxa'a sanya agidan na kitchen ne kawai yabada ku'din asiya mata anan,ranaku suxo su wuce harde bikin Ummi Aisha ya rage saura kwana uku Kuma haryanxu ashraf baya kiranta awaya ba Kuma yaxuwa gidan koda ta kirashi baya 'dauka,

Washegari;

Xaune Ummi Aisha take ta kifa kanta tana rera kuka ahankali acikin 'dakinta,knocking 'kofar 'dakin akai da sauri ta mi'ke tana goge hawayen nata gudun kar agano kuka take kuma bataso ta tada hankalin ammin nata,itakam batasan me ashraf yake nufi da hakan ba,bu'de kofar tayi Waliyya ce tashigo janye da akwatinta da alama taxo kenan har agama biki,rungume juna sukai kowanne da murmushi a fuskarsa sun 'danyi hira kafin waliyya tace;

"Tawan meyafaru?!"

"Me kika gani bestie?!"Ummi Aisha tace hakan tana 'ko'karin 'ka'kalo murmushi,

"Haba tawan,ai baxaki 'boyemin damuwar kiba shekarar mu nawa tare?!kinsan halina nasan halinki wallahi kuka kikai Kuma akwai abinda ke damunki dan Allah menene?!"

"Bakomi bestie"

"Allah fa nace"

Hawayen datake 'boyewane ya xubo,tai saurin sa hannunta tana gogewa,

"Bestie bansan me ashraf yake nufi ba bansan meya 'boye cikin zuciyarsa ba,bakya ganin wannan auren da mukai akwai wani wani 'boyayyen lamari cikinsa?!nifa inaganin yasa ankawo lefen nanne kawai saboda wani abu daya 'kudurta azuciyarsa banso ingayawa ammi ne kada tasa damuwa aranta"

"To ke ki kirashi mana tawan"

Ummi Aisha tasa hannu ta'dakko wayarta agefen kujera ta mi'kawa waliyya,

"Duba kigani"

Kar'bar wayar Waliyya tai tagani sau 22 Ummi Aisha tana kiran ashraf be 'daukaba ga texts 'din datai masa nan ba'adadi,Ita kanta bataji da'diba bakuma taso ta nuna mata kada ta'kara tayar matada hankali,

"Babu komai tawan kicigaba da addua kawai kinsan dama dole ya'danyi fushi na wani 'dan lokaci  amma I assure u komai xedawo yadda yake da yardar Allah,aida bedamu dake ba kotakaina baxe biba amma muna waya dashi muna shirya duk yarda xa'ai komai yacemin ma xasuje bridal tea party 'din shida abokanansa amma baxasu da'deba"

"Allah ya kaymu"tace ata'kaice,

"Yaya batin rigunan da xa'asa ranar bridal tea party 'din"

"Aikinsan yau mukace xamu kar'bo,jia ma hudayya fadoul ta aiko da kayana duka suna gurin aunt Mjay ta ajiye"

"To makeup artist 'dinfa wacece xatai meenah 'dince?!"

"A'a beejay ce xatamin sannan mekyaj fandy ma xatamin ,na ranar bridal tea party kuma monavee ce xatamin kinsan 'kawar aunty mjay ce tace xatamin kyauta"

"Allah yakymu tawan aizamu matso kyau"

Daria kawai Ummi Aisha tai,sannan suka cigaba da hirarsu ta yadda bikin xe kasance,

Rana bata 'karya sede uwar 'diya taji kunya yau take 23 ga watan January 2017 ranar farko da xa'afara hidimar bikin Ummi Aisha,bridal tea party shine event 'din xa'a fara dashi Wanda iya couples 'dinne kawai xasuje da Kuma frnds dinsu wanda xa'a yishi a royal tropicana,'karfe 7;30 shine lokacin daxa'a fara event 'din tun safe su waliyya ke shirin event 'din 'kawayen Ummi Aisha kaf sunxo dayake hardasu xa'aje wajen make up din kowacce tace xa'a mata casual makeup ko Allah xesa suma su samu nasu mijin acan, rigunan su suketa gwadawa wanda bayan rigan ke arubuce boldly daga sama da btp (bridal tea party) se tsakiyan of se 'kasan Kuma ansa#UMASH017(bridal tea party of Ummi Aisha and ashraf 2017)tun magrib su ummi Aisha suka tafi wajen kwalliya bayan sunyi sallah,suna xuwa can tasa rigarta aka fara mata kwalliyan,sanye take cikin doguwar rigan 'floral cape dress'amma iya gwiwa ce rigan se wando irin me ha'de da 'kafarnan,rigar blue ce wandon kuma yellow ne,ammata curly gyaran gashi ya kananna'de wuri 'daya harda crown tasa,takalminta da accessories 'dinta duk blue ne,tayi Kyau beyond beautiful she looked super adorable,kamar ba Ita ba,'kawayen nata ma sunyi kyau kamar ba gobe,sanye  suke da rigar shirt ce dama se wasunsu sukasa leggings wasu Kuma jeggings sukasa wasu ma skirt sukasa but they looked beautiful dayake shirt 'din yellow ne da rubutun blue ajiki,duka monavee tai blending masu kyansu sosai suka futo cass dasu,su waliyya kyau kamar ba gobe,baby kay ma tayi kyau dukkoda ba'kin ciki ne fal ranta musanman dayake saura wata 'daya da kwana goma magajiyan iddarta ta 'kare sunrasa madafa kullum cikin sabon ciwo take gashi sun kasa dena nuna hassada akan auren,'kawayen amarya tundaga kaduna wasu sukaxo sauran Kuma yawanci duk course mates 'dintane yan buk,7;40 dot suka fara tafiya royal tropicana donyin event 'din,hall 'din cike yake da springy flowers yasha decorations blue and yellow,ga abinci kala kala na buffet dogon dinning table akai me cin mutane 50cike yake da Kayan da'di dasu desserts harda su ice creams different  flavours ga cups na tea tunda bridal tea party ne kowanne cup 'dauke yake da #umash017 ajiki,'kawayen amarya su suka fara gaba yarage daga waliyya sai Ummi Aisha dake jiran jay yaxo 'daukarsu suna jiransa wurin kwalliyan dake titin lamido cresent,se gurin 7;50 dede jay yakira waliyya kansu fito yaxo,

"Kinyi Kyau tawan"Waliyya tace da Ita lokacin da suke sakkowa daga stairs na makeup studio 'din da aka masu kwaliiya

"Allah bestie?!nikam bakiji yadda nakejiba kamr na fasa xuwa gabana fa'duwa yake"

"kinsan farko dama haka akeji sekisaki jikinki tunda yaune farko akwai many more events agaba wanda mostly da rana ne ma"

Daria suka kyal'kyale atare sannan suka 'karasa sauka daga kan stairs 'din hango jay sukai tsaye ajikin motarsa 'kirar benz sanye cikin suit shima amma light blue yasa hannunsa daya cikin aljihu 'dayan Kuma yana danna waya,yana hangosu yafara murmushi,

"Su jay anmatso kyau"cewar Ummi Aisha tafadi hakan tana kallon Waliyya,

"My man ba yayi Kyau kam babu laifi"

Daria Ummi Aisha tayi,

"Lalle shi yace maki my woman ke kice mashi my man"

Daria kawai Waliyya tai sannan suka 'karasa wajen jay gaysawa sukai sannan yasa hannu da sauri yabu'de gaban motar inda Waliyya xata shiga sedata shiga suka 'danyi ra'darsu sannan yaxagaya ta 'bangaren Ummi Aisha xebude mata saboda yace karta bu'de tatsaya shixe bu'de mata itama,Ummi Aisha dake gefe daria 'kasa 'kasa tai ,sosai kuma burgeta suke don agaban kowa yin soyayyarsu suke,murmushi jay yayi cike da kunya yake kallon Ummi Aisha,

"Mrs ashraf"yace da Ita yana bu'de mata murfin 'kofar

"Aiban xama ba tukun"tabashi amsa tana daria tashiga cikin motar







                   

                     •✨•

                      82









Manyan idanuwanta ne suka firfito waje ganin ashraf datai dake gefen owners corner yana danna waya,sanye cikin blue blazer yake,wow yayi Kyau ba karya ,hasken wayarsa ya haske masa fuska,gashin kansa yasha gyara shigen irin nata don shima curly din aka masa,pink lips 'dinnan sunsha chapette hankali kwance yake danna wayarsa yana murmushi ko kallon gefenta baiyiba,shagala tai tana kallonsa yanayin yadda yake murmushi seya 'Kara masa Kyau,juyowar da Waliyya xatai xataiwa bestienta magana suka ha'da ido da ashraf daya dago Kansa alokacin,

"Ango dama dakai akaxo?!"cewar waliyyan,

"Dani akazo sister ya kike??"

"Lapia qalau,Ina sauran groom's men (abokansa)din kuma?!"

"Sunyi gaba tuni"

"Ohh okay"waliyyan tace sannan ta juya kanta suka cigaba da hira da jay 'dinta

Ahankali Ummi Aisha ta juyar da kanta ganin Kota masa magana ba lalle ya amsa ba,juyawar datai yabawa ashraf 'kare mata kallo,sosai tamasa kyau hartafi koyaushe kyau,kallonta yake sosai ba ko 'kyaftawa,sexy heterochromia iridum (two different eyes color)'dinsa yaxuba mata yana kallonta,dede street light suka tsaya dayake traffic instructor yatsaida su,hakan yabashi damar kashe flash 'din camera dinsa yasetata kamar wani abin yake yashiga 'daukar hotanta ahankali wanda baxaka ta'ba kawo abinda yake ba,suna isa jay yai parking motar a parking space sannan yakashe motar suka fita shida Waliyya,Ummi Aisha tasa hannu xata bude murfin mota tafita ashraf yai saurin ri'ko hannunta,da sauri yacire don wani sparkling shock ne yabi hannayensu,ahankali tasauke kyawawan fararen idonta akansa,kasa jure salon kallonta yai,yai 'kasa da Kansa kamar mace,yana taune pink lips 'dinsa as usual,

Missing 'dinta kawai yake,sosai fuskarsa tanuna hakan to ita 'dinma hakan take awurinta,dataji shirun yayi yawane muryarta harwani rawa take tace ;

"Xantafi bestie najirana and it's getting late,ammi tace kar ai dare"tafadi hakan tana wasa da yatsun hannunta,

"Just pretend like nothing's wrong okay"yace hakan yana kallon waje don bayason yahada ido da Ita,

"Banganeba"tace dashi tana kallonsa,

"Just do as I said karki bari mutane sugane akwai abu atskaninmu"yafadi hakan yana bude murfin motar,

Ta'be baki tai sannan itama ta bu'de kofar tafita ahankali suka jera suka shiga cikin hall din Wanda mc dama yayi announcing shigowarsu wa'kar mad over you ce take tashi take hall din  ya'dau tafi raf raf,kowa sebinsu yake da kallo don harwani kama sukeyi da junansu gaskia sun dace kowa se fa'din hakan yake,addua kawai akai akafara cin abinci,duk motsin da Ummi Aisha tai idon ashraf na binta da kallo gashi ya'ki sakin hannunta tun shigowarsu ko anzo 'daukar pic da Ita se de ahada ai dashi ya'ki barinta taje ko'ina Kai kace ba abinda yake tsakaninsu,harwani kallon soyayya yake mata,ga wani magana dayake mata ahankali Kai kace kalaman soyayya ne sam ba hakan bane keep pretending kawai yake cemata,ansha selfies,light music ne ke tashi,anci abinci da snacks da desserts ga ice cream da pop corns su lasagne duk wani Kayan da'di su pizza duk akwai,sosai akaci akasha akai abin daria,'kawayen amarya sunyi samari abokan ashraf,bridal tea party yayi da'di ba karya to 10 akatashi kowa fuskarsa 'dauke da murmushi sannan aka fara haramar tafiya kowanne 'dauke hannunsa yake  da jaka rubuce ajiki thanks for coming to the btp of #umash017,abokanan ango su suke takai bridal train gidah,guri yarage saura Ummi Aisha,Waliyya,jay,ashraf..

Jay ya bu'de motar da sauri Ummi Aisha tashiga ciki don tagaji,ashraf de yana gefe yana danna wayarsa da alama waya yake 'ko'karin kira

"Dude shiga mutafi "jay yace da ashrf haka ganin bashida niyyar tafiya,

"Jay kuje kawai Ina jiran mansoor ne xamu le'ka nan la sultana kasan yau madrid suke wasa"

"Bari mu wuce to"

"Okay amma barinyi sallama da Ita ko"yafadi hakan yana nuna motar,ahankali ya karasa yabude motar yaxauna,itade kallon waje take abinta

"Thanks for pretending,and you looked super amazing tonight" ya bu'de kofar ya futa bejira cewarta ba,murmushi kawai Ummi Aisha tai najin  abinda yafa'da wato pretending xasu dingayi kenan kamar suna shiri?ganin yafuto yasanya Waliyya tashiga ciki suka cigaba da hira suna jiran jay,yana futa sukai sallama da jay yaja mota shikuma yatsaya jiran abokin nasa,

Washegari da sassafe me lallen dataxo tundaga Sudan itace tai wa amarya da 'kawayen amarya lalle,tun safe ake shirye shryen kamun daxa'ayi 'karfe 4,'karfe 4 nayi aka fara haramar tafiya wurin event 'din the afficent,amarya da 'kawayenta wajen makeup by beejay sukaje inda tatsantsarawa amarya kwalliya itada frnds 'dinta sanye take cikin wani tsadadden french royal lace multi color tasa komi purple,tayi Kyau ba karya rigar buba ce tadora zanin akai kamar yadda de akeyi yanxu sar'kanta na beads ne daya xaxxago asoeke 'dinta duk purple ne ha'de da hill takalminta da clutch bag,suma frnds dinta asoebi dinsu na atamfa ne irin yoruba style 'dinnan ash da kwalliyan purple suma buban ne sukai sunyi kyau suka nufi wajen kamun,bayan anyi addua an 'danyi refreshments ne aka fara kamu,kuka ne kawai Ummi Aisha batai ba amma tajigata ba 'karya kamu akai har kala uku,dafarkode aka fara mata normal kamu na turare se akai Kuma na fullanci tasha ruwan nono akanta,bayan angama akazo akaimata na kanurin yerwa tasha wankin Kai har lallenta seda suka sake wankewa,agaban kowa,se abin ya birge kowa 'kwarai matu'ka tunda basaba yin hakan akai ba,ansha li'ki,tabbas yan uwan mijinta nasonta kamar su cinyeta danso mintina ka'dan saje su'dauketa a hoto,sake shigar wani Kayan tayi gaf da xuwan angwaye tasaka wani flamboyant doguwar riga red and black yanajan kasa anmata 'daurin turban knot,tasha li'ki awajen angwaye da abokansa,ashraf kamar yamaidata ciki dukkoda cikin pretending ne. Anci ansha anyi hani'an anraba savouniers kala kala,da daren ranar ne bayan isha'i aka tafi dinner 'din gidan maxa wacce akai a hall 'din tahir guest palace Kano dinner tayi Kyau couples sunsha Kyau babu 'karya,washegari akai Elegants evening wannan karon shigar Fulani Ummi Aisha tayi,'kawayenta ma haka sukai abin gwanin ban sha'awa yayi kyau event 'din abinci gashinan birjik harda masu take away,uwar amarya taci Kyau taci ado itada tawagarta su mjay,

To cut it short haka aka dinga shagalin bikin Ummi Aisha,washegarin elegants evening ko ince custome day akayi yini a farfajiyar gidan captain adam,dandatsetsiyar atamfa Ummi Aisha tasa datasha 'dinkin Senegalese tasha 'daurin indimi style,su muna_b kuwa sakin le'be da sale'ba sukai kawai suna kallo,duk yarda sukaso su 'bata bikin hakan beyiwuba,kowa yasharesu akacigabada shagali,washegari akai barbecue day tabbas yaci sunan barbecue gasasshen sa aka yanka da raguna akai gashinsu da kaji aka sakale su wajen event din sede kasa wuka ka yanka kaci ga plates nan atanade anci da'di ranar event 'din (tatass na lashe hannuna na kumayi takeaway da abuna no shame!)shigar polo ango da amaryan sukai suda bridal train 'din  harda boots sukasaka,da daddare Kuma akai royal/dinner/ball a harabar meena event center,tabbas fa'dan kyan dasukayi baxe misaltuba sanye couples din suke cikin english wears farar doguwar riga tana flowing Ita Ummi Aisha tasaka komi fari tasa shima ashraf din suit yasa fara kal da ita,bridal train Kuma suka sa black akai decorating gurin da black and white cake ma 30layers ne dauke da hoton amarya da angon,washegari akai english dinner ko li'ki ba aiba saboda english dinner ne sede kasaka ku'din likin cikin wani 'dan box se dance competition kawai da aka dingayi dinner yayi Kyau saboda mutane basu saba ganin irin taba aunty mjay ko xama bata yi se rabon savouniers take kala kala,on friday akai cocktail party it was beyond amazing baby kay bataje da wuri ba se to 5 tanata sauri tashiga gate 'din meena event center tana danna waya batako kallon gabanta gbam taci karo da mutum da niyar rashin mutunci ta'dago kanta tana ayyana rm 'din daxataiwa koma waye,shikansa Wanda sukai karon jira yake tadago fuskarta yaga wacce ballagazar ce haka,'dago idon daxatai idanuwanta sukai toxali da kyakkywan matashin dayatafi da xuciyarta Lokaci daya meyakwan tai abinda ta ayyana a xuciyarta batai hakan ba sema sa'kon kyakkyawan murmushi data aikamai,shikansa seya samu Kansa da mayar mata murmushin musanman daya lura dayanayin shigarta irin tasuce wannan,

"Hello beautiful!"yace da Ita yanabinta da kallo,

"Hi gorgeous"

"Kinxo bikine?!"

"Yeah ana bikin sister na ne nayi latti ma"

"Ayyah,I'm kamal yaxeed ana kirana da bobo"

Meyakwan tabashi amsa tsayawatai tanabin Kayan jikinsa da kallo jin yace bobo tasan sunan masu farcen susane(masu ku'di)hannunsa tabi da kallo mu'kullin motar hannunsa daya nuna tambarin mercedez benz shiyabata damar yin murmushi,

"I'm khadija adam popularly called baby kay"

"Wow,that's nice,so what's popping up??"

"Nothing much I was kinda late xanshiga ciki"tace dashi tana nuna tent din dake cikin meena event center inda ki'dan wakar tekno 'panaa'ke tashi,

"Ohh gosh,nikuma xankoma gidane yanxu muka gama namu bday celebrating akai na abokina gashi inason number ki Kuma yaxa'ai?!"

"To a'ina xan rubuta"tayi hakanne saboda tanasan taga irin wayar hannunsa,ciro wayarsa yai 'kirar iPhone 7 yami'ka mata,number tasa ta mi'ka masa sannan sukai sallama yatafi itakuma tashiga ciki xuciyarta cikeda farin ciki,

Da dare Kuma akai shirin tafiya gala night Wanda bakowane xashi ba saboda washegari akwai bu'dar Kai dakuma wushe wushe night,gala night 'din kanurin dangin hafsat sune suka ha'da shi Wanda xa'ayishi ne a harabar fabs event center 'karfe 8 nadare aka fara ba'a tashi ba se gaf da asubahi saboda haka al'adar take Kuma duk sanda xa'ai gala night 'din akan wuce hakan ma wasu har safiya sukan Kai suna shagalin bikin al'adar tasu,komi irin na al'adar barebarin/kanurin yerwa akai,kama daga kan abincinsu har yanayin rawar da akai acan 'din har savouniers duk irin na yarensune su humra da sauransu,

baby Kay nakomawa gidah bayan antashi daga gala night tafara fa'dawa su magajiyan abinda yafaru sabon saurayin datayi Bobo kyakkyawa mai ku'di shine abinda taketa fa'da Kuma shegiyar ce dashi wato(benz)....

    ____sosai Ummi Aisha ke mamakin irin pretending din ashraf dankoda xata dafa qur'ani ta shekara tana rantsuwa babu Wanda xe yarda baya mata magana ganin irin son da yake nuna mata cikin mutane,li'ki Idan yafara mata se mc yace ya'isa haka,ranar royal ball din da akai harda tsugunnawa a'kasa agaban mutane akan stage na rawa ya karbi mike yana magana yakuma dur'kusa I love you,you are the best woman on earth hardasu fa'din i will worship you,duk sanda tatuno kalmomin dayai pretending dasu kuka takeci sosai saboda batasan meya 'boye cikin xuciyarsa ba,gashi in su biyu ne ko kallonta baxeyiba Kota masa magana baya bata amsa,amma cikin mutane kuwa ruwan romantic words harse tagaji dasu,babban abinda take tsoro shine daga gobe bikin ya 'kare idan aka kaita gidansa tashiga dubu bama biyu ba,

Da misalin 'karfe goma sha 'daya na safe dubban mutanene suka shaida knuptial knot (daurin auren)'din Ummi Aisha adam abdulrasheed da angonta ashraf Kabeer kamilu akan sadaki naira dubu talatin kamar yadda limamin yafa'da saboda albarkar auren akeso ba yawan ku'din ba,every who is who in nigeria attends the knuptial knot a masallacin Umar bn khattab dake kan roundabout 'din gya'di gya'di kano state,ango ashraf yay Kyau kamar babu gobe cikin getzner shadda coffee tasha aiki brown yayi Kyau babu 'karya duk inda yai camera na binsa yanashan 'dauka a hoto,bayan anyi 'daurin aurene akai reception a event center na darul tawhid anci kayan 'kwalam da ma'kulashe gefe 'daya Kuma cikin masallacin sauka ce ta qur'ani akai wa ango da amaryan na Allah yabasu xaman lapia yakuma kawo ya'ya nagari masu yawan albarka...

   Daga gurin 'daurin aurenne angwaye(ango da abokansa)suka wuce gidansu amarya Ummi Aisha,can gidan su amaryar ma shagali ake kowa fuskarsa 'dauke da farin ciki da Kuma annushuwa bakin hafsat ya'ki rufewa saboda farin ciki se hamdala take tana Kuma taya tilon 'diyar tata adduar Allah yasa tayi kenan yakuma inganta rayuwar auren,kaf kowa murna yake fyace su muna_b da Ummi Aisha wadda tata rashin jin da'din bewuce na tashin hankalin da xata fuskanta wajen ashraf ba,ga 'kawayenta sunsata agaba suna ta mata wa'ka taxama taxama taxama,taxama 'dakko riga taxama dakko wando taxama,taxama 'dakko hula,takaici ne yakaita ma'kura adole ta tashi tashiga cikin 'daki tabarsu sunata mata sha'kiyanci irin nasu na 'kawayen amarya,sanye take cikin wani tsadadden lace peach and purple tasha kwalliya tasaka accessories 'dinta na gold da baffa yasiya mata a dubai,kakkauran mayafi tasa da takalmi duk purple tayi kyau babu 'karya,kusan shine shigarta na biyar kenan tasa ta cire tasa tacire wannan na musanman ne tasa saboda xuwan angwayen miri mirin kitson alluran 'yan maiduguri shi aka yarfa mata a yala yalan gashinta 'kirar shuku da Kuma na gaba har 'bangare biyu dama da hagu se ya 'Kara mata Kyau abinde se Wanda yagani kawai,

Ba'ajimaba tawagar angwaye suka iso se bulbala 'kamshi suke gasu 'yan gayu zokuga 'kawayen amarya yadda suke gyare gyaren mayafai,masha Allahu ansha hotuna ango da amarya sunyi kyau kamar gaske ashraf se wa'ke ha'koransa yake kamar gonar auduga dakansa ya seta wayarsa yamasu selfie shida Ummi Aisha wadda agarin kallonsa ne tadago Kai tana mamaki shikuma ya 'dauka sesuka bada wani ha'dad'den style,angwaye sunci sunsha sannan suka fara rage tagwagar mutanen xuwa gidansu ashraf dayake 'karfe 1;30 xa'afara bu'dar kan wanda xa'ai a farfajiyar gidansu ashraf,dandatsetsan material tasa ash and peach,sosai mekyaj fandy ta zizara mata kwalliya,alkyabba peach color Ita ta'dora akan kayan tayi kyau babu 'karya,nan aka tattara aka tafi gidansu ashraf,yasha decorations multi colors ga wani special guri na serve ur self cike da abinci kala kala(oh bouy harda jollof rice *lol*)guri na musamman akaiwa ummi aishan taje taxauna tareda 'kawayenta,nande aka fara addua,Sannan aka 'dan taba jokes se bu'dar Kai yabiyo baya,ga wani 'katon basket cikeda Kaya da alama na amaryar ne da dangin ashraf din ke tara mata alokacin 'yan uwan ashraf se xuwa suke suna saka kaya cikin basket 'din,kafin a bu'de kan amarya seda aka tsadance da 'kawayen amarya Wanda suka yanko ku'di dangin ango sukace sunji sunyadda suka bayar,sannan akaci akasha an'dan ta'ba kida ba laifi,idon ashraf nakan Ummi Aisha ko 'kwak'kwaran motsi bata iyayi wannan takura har ina?!an warwasa sosai a bu'dar kai Kuma yayi da'di fiye da yadda mutum ze kwatanta,se gaf da magrib aka fara watsewa saboda akwai wushe wushe nan gaba Wanda kowa yake son yaje yakashe tsutsar idonsa......

   Su Ummi Aisha nakomawa gidah aka fara shrye shryen wushe wushe,baffa yanadawowa daga majlisi kenan yake tambayan amarya xa'akai?!akace a'a wushe wushe xa'aje tukun banbamin fada yafarayi kan lalle adole tinda aka daura aure se ankai yarinya gidan mijinta dakyar gwaggo tashiga xancen captain adam yashafawa Kansa lapia ya janye maganar Kai amaryar xuwa da safe,shigar Ummi Aisha ta wushe wushe taxarce tunanin duk wanda yaganta shigace irinta alfarma wani had'add'en voil lace tasa white da torches red,se aka nad'amata laffaya red sosai beejay ta tsantsara mata kwaliiya abinda se Wanda yagani,'kawayen amarya sunyi Kyau suma cikin shigar su ta dogwayen riguna farare na material style 'din cape dress se sukai moppling da mayafi kalan kayan wasun su Kuma sukai turban dashi suka fito sak kanurin yerwa/manga,sosai yan 'Uwa da abokan arziki suka ci kwalliya,'yammata sosai sukai shigar abaya wasunsu Kuma laffaya suka na'da suma,kowa bakinnan yasha b'akin jambaki,kusan kowa shigar kanurin yai tsirarinne sukai shigar lace yawanci kuma yan 'bangaren captain adam ne sesuka sake bada wani style..,,

  Wushe Wushe Night;(which literary means welcome to everyone)cike marhaba event center yake da taron yan uwa da abokanan arziki decoration din was beyond my expectations komai red and white da black,shrye gurin ango da amarya yake ak'awace,yan uwa kowa ya hallara ana jiran shigowar ango da amarya da bridal train,kowanne zaune yake a'inda number card dinsa ta nuna,anci kwalliya babu laifi wani table cike yake da 'yan xoxo's palace kowa ya hallara su ayush duk suna table 'din,gefe 'daya Kuma 'yan home of novels ne duk 'yammatan nan ha'daddu sunje,su khadija candy,miss hafsy,dr sumayya,kameela da dai sauransu harda aunty amarya da jameesh duk suma nagansu bakin nan yasha painted black jambaki,suma 'yan grp 'din mjay ba'abarsu abaya ba dayake mrs mu'ayyad ta mutane ce,xahra novels,novellas lodge harda 'yan grp din duniya makaranta da musha karatu suma sun hallara,waiga kaina nai can nahango su nafee anka mrs imran tasha kwalliya cikin abaya ga nusnim agefanta gefe 'daya kuma aunty ummah ce tareda ayusha axaune,mom heenah,da Kuma 'kawata billyn abdul tare suke da mrs naseer (rano theorist)datasha turban knot itada 'kawata miemee bee,da duk ma sauran wanda na gayyata duk nagansu awajen ina mi'ko godiata ta musanman...

Motoci da suka amsa sunan motoci ne suke shiga titin marhaba event center 'din da alama amarya da ango sun danno,cikin tent 'din tuni mc ya shedawa mutane cewar amarya da ango sun iso,Kuma amarya xata fara shigowa da tawagarta kamar yadda al'adar wushe wushen take,



"Bestie boo kwallina ya xaxxago kalla idona kiga"cewar Ummi Aisha dakewa Waliyya magana suna xaune cikin mota su ka'dai abaya da alama ango ashraf yana wata motar,

"Muga ba sosai ba"Waliyya tace hakan tana gogemata kwallin daya kwaranyo,

Mjay ce ta lek'o da kanta ta window 'din motar sanye cikin laffaya sak kanurin yerwa se kamshi take,

"Baxaku fito ba ga baffankican yace shi tafiya xeyi nibansan zaman me kukeba jan ran ya isa haka"

"Aunty kwalline ya xaxxago shine bestie take gogemin"

"Yayi Kyau to kufito"

Tsakiya aka saka ummi Aisha,gabanta Kuma bridal train 'dintane gefe  da gefenta Kuma Waliyya ce da kausar 'kawarta,ciki hardasu batul mamman da khadija sidi,bayanta kuma dandaxon dangintane na kanuri da suka sha laffaya suma se bulbula kamshin khumra suke kanajiyo kamshin hakan xe tabbatar maka da cewa amarya ta iso,wani abin daxesa ke burge duk Wanda yagansu shine harda ammi da baffa da sauran luwali's d'inta aka shigo da ummi Aisha kamr yadda al'adar take hakan sukai,'yan uwan ammi maxan shigar kulwu sukai dasu gemage harda Wanda sukai dankiki da yange ciki hardasu arfaan da mus'ab...

Bayan amarya taxauna da yan uwanta tawagar ango yabiyo baya shigar ba'ki yai da fari 'kirar bauchi style seyasake fitowa sak ashraf 'dinsa su jay ansha fararen shaddodi shida sauran abokai se suka sake bada very colorful and exciting event,addua aka farayi,light music na wagge shiyake tashi abin gwanin sha'awa,jokes of the night ya biyo baya ciki harda na yaren kanurin anayi ana fassarawa Wanda basaji,Waliyya Ita tafito tabada tarihin amarya cikin harshen turanci,se babban abokin ango jay shima yafito yabada na ashraf,abinci kala kala na kanuri da normal shi aka dinga kawowa mutane,Kayan da'di abin ba'a magana,bayan anci abinci aka fara rawa inda aka kira couple da yan uwa da abokan arziki kan sufito ayi rawar 'ganga kuraa' kowa seda yayi rawar kamar yadda al'adar takanyi babba da yaro kowa sedaya taka harta dattijan yerwa dake wajen seda suka taka bayan an gama rawa ashraf yabawa amarya kyautar sulallen gold (gold coins)har 'kwara goma sha biyu kai guri seya sake kicemewa da murnar ashraf yayi kamar yadda al'adar ta tanadar,,yanayi yanasa babbar rigarsa yana goge wa Ummi Aisha gumin fuskarta duk cikin iya shegen ashraf ne,gashi yaki sakin hannunta duk inda xasu xaga awajen da shi ake xuwa har traditional abubuwa na wushe wushe su tulur da ta ru'da duk dashi akai yana wajen,

Conclusively haka aka dinga hidimar wushe wushen abin gwanin sha'awa,anci ansha an watsa naira antaka naira  an raba naira,muna_b da magajiya dake gefe tagumi suka xabga ko 'dan hotan da ake xuwa aida amaryar basujeba kowa yagane ba'kin ciki suke shysa aka tattara lamarinsu aka watsar,savouniers kala kala haka aka dinga rabawa awajen,sama ko 'kasa tunda baby Kay tashigo da tawagar amarya ta ware waje wajen bobonta,zaune suke Ita dashi cikin motar sa bayan baffansu yahana xancen mota 'kirmishishi ta toshe kunnenta tabad'awa idonsa kasa don taga ba idon mutane awajen,

"Sweetest love yaushe xaka aiko?!"baby Kay tace da bobon hakan tana kallonsa

"Sugar pie nace maki su daddy sunje Qatar se sundawo tukun,Meyasa kike yawon kawo xancen nanne nace maki ke kadaice a xuciana trust me"

"Shikenan sweetest love Allah yadawo dasu lapia"

"Amiin"yace a takaice yasa hannunsa kan nata yana murxawa passionately

Da sauri tacire hannunta tana kallonsa,

"Why?!"yace da Ita yana dubanta

"Kabari idan munyi aure mayi hakan ko?!"

"Just a romance nothing beside the romance kinji sugar pie trust me kobaki yadda dani bane?!"

"Nayadda mana"tafadi hakan tana rufe fuskarta

Tashin motar yai suka bar wajen suka koma cikin dimlight dake gefen tent din suna shek'a alfasharsu(Allah ka karemu da kariyarka ameen),haka aka dinga event dinnan har wajen 12 na dare Sannan aka tashi fuskar kowa 'kal da Ita yana jin dadi gakuma tulin Kayan rabo fal a hannun jama'a,seda baby Kay taga amarya tashiga mota xasu tafi sannan tacewa bobo yakaita gidah kar anemeta,

Washegari;

Tun da safe ake shrye shryen tafiya bud'ar kai saboda xa'afara kaita gidan sirikanta kafin akaita gidan mijinta,ummi Aisha tasha kuka sosai da iyayenta sukai mata fa'da da Kuma jan kunne,sosai fadan I nayi  bari nabari yashigeta ba ka'dan ba musanman inda baffanta ke cewa tabi mijinta Kuma karta kuskura ta tauye masa hakki saboda mala'ikun rahma xasuyi ta tsine mata wata ruwayar aka ce xasuyi fushi da Ita,shigar atamfa tai kalar blue and orange babban mayafi orange ta lullub'a light makeup aka mata,gidan su ashraf aka fara kaita nanma iyayen mijinta(Hajia sakeena da Hajia barira)sukai mata fa'da sosai tareda doriyar kome ashraf 'din yayi mata taxo ta fada tadaukesu iyaye ba surikaiba....daganan Kuma aka sake dawowa da Ita da Kansa captain adam yakaita har gidan mijinta dake unguwar sultan road inda alhaji kabeerun yabawa ashraf dank'areren gidan kyauta lakadan kyauta opposite the afficent duplex gidah sama da kasa komi yaji,yasha Kayan alatu irin na xamanin yanxu iyayenta  sunyi mata fiye da tunaninta sunyi mata Kaya nagani na fad'a babu raini,captain adam ya dank'awa ashraf amanar Ummi Aisha  sannan yasake masu fada me shiga kunne yai masu sallama yatafi,

   A lokacin ne kuma kafin yan uwan amarya su fara watsewa abokan ango suka shigo da akwatuna guda 6,kyauta daga ango xuwaga amaryarsa sak irin yadda al'adar kanurin take haka ashraf yaiwa Ummi Aisha komai to wannan karenma akwatunan kwara 6 cike suke da Kaya,hudu dagaciki kususuram ne sekuma biyu daga ciki wato ra'aki shikuma rabin kususuram ne shikuma akwati biyu ne making it 6 duka,shewa da gu'da haka kanuri's dinnan suka dingayi,bayan manya suntafi se yammata kawayen amarya akai siyen baki sukai ciniki suda abokan ango Sannan aka watse aka bar amarya Ummi Aisha Ita kadai sunkife cikin wadataccen mayafinta...



"Dude nace maka anwatse fa anbar yarinyar nan Ita kadai da Allah katashi katafi kaxauna kana shegen murmushi kana taune wannan banxan pink lips din naka kamar na mace"jay yace da ashrf hakan

"Kana ba'kin ciki kenan?!beside niban huta ba kabarni na sake hutawa naga bawani nisa"ashrf yafadi hakan yana sake gyara kwanciyarsa,

Dundu jay ya d'umawa ashraf abaya,ashraf yamike yana sosa bayansa,

"Haba jay wannan childish stuff ne ba girman ka bane"

"Dole kafadi hakan mana tunda yanxu kanada iyali wai kaima kanada mata yanzu,kade siyi wani abin karkabar 'yar mutane da yunwa"

Tsaki ashraf yai Sannan ya xuri carkey dinsa akan stool yana cillawa jay harara wanda shikuma gwalo yake masa,ahnkali ashraf yake driving dede madallah suya yatsya yasai dakwalen kaji kwara biyar da drinks kala kala ya saka agaban mota yai hanyar gidansa 'kira'ar manshawi ce ke tashi ahankali cikin motar ha'de da turaren bahreinul oud da suka ha'du suka bada daddad'an kamshi,yana xuwa ya danna horn da sauri megadi yabu'de masa yashiga da motar,Ummi Aisha najin 'karar motar tai saurin lullube kanta cikin bargo tana munsharin  'karya kamar tayi nisa a baccinta........

Continue Reading

You'll Also Like

386K 29.4K 58
Anwar Bankudi, the Handsome Young Millionaire ke zagaye da matan Aure uku, kowacce da salon halinta da matakin matsayinta a zuciyarsa. Shin wacece Ta...
12.6K 314 17
True life story. labarin zanan ƙaddara wanda babu wanda ya isa ya hana shi faruwa sai Ubangiji al'arshi. soyayya mai cike da tausayawa wacce ƙaddara...
58.8K 1.7K 80
Nice and amazing dishes. follow me and have an idea on many recipes
3.9K 303 18
AMJAD-Aikin da aka aiko ni zan iya yinshi kuwa? Tuntuɓen da nayi a hanya bazai kawo min matsala cikin aikina ba? Zan iya ceto rayuwan dubbanin mutane...