UMMI_A'ISHA (THE MAGNIFICENT)...

By missxoxo00

10.6K 549 9

Labari ne dake dauke da darussa kala kala na rayuwa, Mai dauke da tausayi, Al'ajabi ga kuma kauna agefe d'aya... More

1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
15
16
18
17
19
END

14

324 17 2
By missxoxo00

•✨•✨•✨•✨•✨•

Tunda captain adam yafice Ummi Aisha da Hafsat suka bude sabon shafin kuka,Ita Ummi Aisha kukan ta akan meyasa muhannad xe mata haka duk yardar da ke tsakaninsu amma yaci amanarta haka?!ita kuwa hafsat nata kukan tanayinsa ne kan abinda muhannad yaiwa tilon 'diyar tata da Kuma yadda rayuwarsu ke shiga halin tsaka me wuya,har lokacin bacci basu dena kukan ba sede suyi su tsagaita su cigaba babu me tausar wani dakyar Hafsat tadanne zuciyarta taiwa Ummi aisha nasiha me shiga jiki tareda bata wasu addu'oi daxata dingayi saboda kariya daga shaidan dakuma sharrin masu sharri..,

Bayan kwana biyu da abinda yafaru kafin kace me Ummi aisha ta rame tashiga damuwa tunma baga hafsat dinba itama tata ramar ta bayyana sosai sefa mama da mjay ne ke tausar su,Ummi Aisha ko abinci bataci kullum se amminta tamata dagaske sannan take iya tsakula taci yawanci tafishan oats shima dan bayadda xata yine,ko makaranta ta'ki zuwa aganinta kowa yanxu yasan xancen 'kawayenta sunxo sunyi kiran amma fafur ta'ki komawa, ashraf ma yakira ya kira taki 'dauka daga karshe ma kashe wayar tata tayi tun Hafsat na matsa mata kanta shrya taje makaranta Kar awuceta a abubuwa har ta kyaleta domin intace tajema kukan takeci gaba dashi ba ''kak'kautawa shiysa kawai ta kyaleta tasaka mata ido tana Kuma mata adduar Allah yakawo 'karshen wannan abu da yafaru,gaba 'daya tacanxa kamar ba Ummi aishan ta ta da ba ta rame taxama kmar wacce aka canxawa kamanni ,dama haka magajiya keso Itako zaman iddar dake kanta badamunta yaiba dukkoda saura wata biyu da 'yan kwanaki ta tattara tabar gidan,Ita kawai rayuwarta tafuso ta bu'de ido taga rayuwar Ummi Aisha da hafsat acikin ba'kin ciki(Allah ya karemu daga sharrin masu sharri)

A ranar muna_b taxo da safe lokacin baby kay nashiri xata makaranta bayan sun gaysa muna_b ke tambayar baby kay;

"Tana xuwa makarantar kuwa?!"

"Bata xuwa ko'ina ai ko 'kofar gidah"

"Ah'to dama ina xata da wannan abin kunya dole se xaman gidah ai,Yaya asharf din kuna magana kuwa?!"

"Ba lefi muna magana a matsayina na 'kanwar budurwarsa ba,sister in law yakecemin"

"Se ahankali xata fita ransa"

"Allah aunty kullum seya tambayeta fa wai yana kiranta bata 'dauka wai tama kashe wayan nata gaba daya lapia kuwa?!nace ai sunyi tafiya daxan gaya mashi abinda yafaru sena fasa saboda karma yace xezo gidah ya ganta yaji tausayinta"

"Gwara da kika fasa tunda anga yayar kice xa'ace da'di kikeji har sugano wani abin kibari ahankali xamu fitar da komi kowa yagani Kinga shima daga lokacin xata fita ransa"

"Sosai kuwa,barin tafi sch aunty"

Takarashe maganar tana gyara mayafin jikinta

"To Shikenan sekin dawo"

Baby Kay nafuta muna_b tadawo kusada magajiya,

"Yaya 'kawata lapia kika kirani bade jikinneba?!"

"Ai asibiti xaki rakani dubi gashina gaba daya ya xaixaye babu komi akaina"

Tafadi hakan tana bu'de 'kwanyar kan nata da babu ko silin gashi kamar kan namiji dayasha 'kwal'kwal,jimami muna_b ta mata na ganin yadda kan nata yaxama sannan suka fita xuwa asibitin standard dake kan titin tarauni,bayan likita yagama gwaje gwajensa kenan ya dago ya kalli magajiyan datai zuru da idanuwa 'can tace;

"Likita me result 'din yabayar?!"

"Dafarkode xan lissafo signs na ciwon ki duk Wanda kike irinsa seki gayamin ko?!"

"To dr"

"Ko kinajin new onset or change akan yanayin ciwon kan Ki?!"

"Sosai dr kusan kullum seya canxa"

"To,ciwon kan naki gradually yake becoming more frequent and more severe?,sannan kawai kina samin kanki cikin nausea ko vomiting?!"

"Wallahy duk abinda ka lissafo inayi 'daxun nanma  nagama amai"

"Allah ya kyauta to yanayin ganinki fa shin kina ganin abu blurred ko double vision?!sometimes harda pheripheral vision?!"

"Wallahy Ina gani da naxata ma yanayin ganinane ya 'Karu harxan koma wajen optometrist 'dina"

Shiru yai yana rubuce rubucensa 'can ya 'dago yana kallonta;

"Shekara nawa kikai kina cancer?!"

Baki,hanci,Ido haka magajiya da muna_b suka saki suna kallon likitan kafin muna_b tai karfin halin magana;

"Likita kaf gidansu ba mai cancer fa"

Likitan yai murmushi kafin ya ajiye biro din dayake rubutu

"Karki sako jahilci mana aciki,karki manta ko yatsu da Allah ya tashi yinsu seya yisu wasu sunfi wasu,sannan komai ki kaga yafaru da bawa mu'qaddarine daga Allah,ze kuma yiwu genetically tasamu gashinande Allah ya kadai yabarwa Kansa sani"

Itade magajiya shiru tai tana kallonsa takasa kodah motsi,dan ko amafarki bata ta'ba kawo wa kanta cutar cancer ba,sannan likitan yacigaba da magana;

"Ki godewa Allah ma dayasa brain cancer/tumor ce,sede taci 'karfin ki sosai"

"Yanzu dr surgery xa'a mata ko me?!"

Muna_b ke tambayar hakan,

"Treatment de na irin cancer 'dinsu should be individualized for each patient,sannan shekararta nawa?!"

"49"

Muna_b tabashi amsa

"Toh kuma bayan cancer batada wani ciwon?!"

"Banajin akwai se mahaifa da aka cire mata"

"To fa,to yanzude gashi ga size din tumor din da inda yake a kan nata dakuma grade na yadda tumor 'din yaci,gaskia tayi sakaci da bataxo da wuri anyiwa gurin riga kafi ba yanxu gashinan tumor din yacinye gashin kanta tas,yanxu xamu fara bata chemotherapy treatment tunda abin yayi worst daga baya Kuma xamu yi mata surgery radiation"

"Toh dr"

Magajiya in Banda kuka ba abinda takeyi najin abinda likitan yace Wai cancer,har sukabaro asibitin bata dena kuka ba da wanne xataji da cire mahaifartata da akayi koda sabon tashin hankalin da taji yanzu Wai brain cancer'?!har suka koma gidah bata dena kuka ba yanxu me xatagayawa Yaya adam?!dakyar muna_b tamata sallama tatafi,wunin ranar haka magajiya tadinga kuka kamar wacce akaiwa mutuwa,(ka'dan ma kika gani da yardar Allah,duk 'karshen me sharri da yardar Allah baxeyi kyauba)

Da yamma lis Waliyya tai sallama part 'dinsu Ummi Aisha,bayn sungaysa da Hafsat tatashi tabasu waje,Waliyya tajima tana kallon Ummi Aisha ganin yadda ta rame ta jeme kamar ba 'Ita ba,

"Tawan dan Allah banasan kukan nan dakike,jiya muna waya da jamil ashraf dinki ya karba Wai ance kinyi tafiya?!nace wacce irin tafiya kuma amma xanduboki nagani"

"Shi yasani"

"To shikuma meya miki bawan Allah dashi?!"

"Ke 'kyaleni da xancen maxa pls nacire su kaf a  policy 'dina"

"Wai kina nufin dagaske muhannad....ya"

Bata 'karasaba Ummi Aisha ta katseta

"Na miki 'karyar dana saba"

"Meyai zafi tawan nayi shiru amma dama tunfarko ni muhannad 'din nan kam se a slow kuma kinyi shirme da kika bishi ke ka'dai"

"Hakama baffa yace,to saboda Allah aibansan gaibu ba kuma Allah zemana hisabi ranar gobe 'kiyama"

"Nace kode yanada ta'bin hankaline??"

For the first time tunda akai wannan abin se yanxu Ummi Aisha tai daria,sosai taci daria harda siraren hawaye,kafin tabawa Waliyya amsa;

"Xe iya yiwuwa,tunda nanfa yaxo ya 'karyatani gurin baffa,naji mamaki 'kwarai matu'ka kuma koyanxu nai sallah nasa goshina a 'kasa senace Allah yabimin ha'k'kina"

"To yanxu mu sako maganar ashraf 'dinki Wallahy guy 'dinnan yadamu yana sonki soyayyar da ko a littafi Wallahy da wuya a samu irinta"

"Kai,innalillahi wa'inna ilaihirrajiun,bestie kina shiga min rayuwa dayawa nace maki nacire maxa kaf a zuciyata gaba 'daya banasan zancensu"

"To kince baffa yace maki lalle kifito da mijin aure aganinki waxa kice??"

"Addu'ata kullum itace Allah ya za'bamin abinda yafi alkhairi kawai,nikam nagama tsorata da maxa xaki trusting namiji kibashi zuciyarki daga karshe yasa kafa yai fatali da Ita kuma babu yadda kika iya fyace rungumar 'kaddara"

Hakade sukaita hirarsu itada Waliyya suna bawa junansu shawarwari kan yadda xasu 'bullowa al'amarin...dakyar da da'kyar'kyarewa Ummi Aisha ta yadda ashraf yaxo,

     ___Washegari da rana ashraf yaxo bayan sungaysa da ammi tatashi tabasu waje setabar 'yar 'kanin babanta kawai wata 'Yar karamar yarinya da taxo hutu jiya anakiranta da sajeedah,Ummi Aisha bayan gaisuwa bata karawa ashraf magana ba se shine yaketa faman yiwa sajeedah wasa dayagade abin bana 'kare bane yace;

"Life partner kinyi shiru wannan ba halinki bane,Wai meke faruwa dake kwana biyu?!ko makaranta bakya zuwa why?don Allah nikam kinsani cikin wani Hali Dan Allah Kiyi magana karki azabtar da xuciata pls"

Ummi aisha looked up quickly batace dashi komai ba dama kanta a 'kasa yake,ahankali take kallon kyakkyawar fuskar ashrf dake kallon gefen tv he was sad and in pain gaba 'daya shikansa ya rame kamar ba shi ba,a hankali murya narawa take masa magana;

"I'm sorry ashraf niyanxu bandace da kaiba"

Ashraf ya ware ido yana kallonta lokaci 'daya yanayinsa ya canxa,

"WTF,Life partner you belong to no one but me forget your beloved muhannar yake kowa?!nasan akanshi kikace haka"

Sekuma yasakko daga kan kujera yasa gwiwoyinsa a 'kasa idonsa yaciko taf da hawaye muryarsa na rawa yake mata magana wanda ba Ita ba har 'karamar yarinyar dake gurin sedata tsaya tana kallonsu;

"You don't have to say anymore you are different from the others,life partner you r MAGNIFICENT...dan Allah kitausayamin Wallahy baxan iya rayuwa bakeba,

Sirririn tsaki Ummi Aisha taja ahankali tana takaicin kalmomin maxa da irin salon yaudararsu akan mata,a hankali take 'ko'karin furta masa magana wadda baxata tadar masa da hankali ba;

"I belong to no one but my self, ashrf kayi ha'kuri pls mu rabu da juna bawai bana....ba wai..,"

Sekuma tasa kuka,ashrraf ya mi'ke daga dur'kushen dayake,

"Noo don't cry pls,pls Kiyi shiru idan wani laifi nayi dan Allah Kiyi hakuri idan wani halina nane beyi makiba nayi al'kawarin xan canxa,dan Allah kibar kukannan pls kinji dan Allah idan kuma nine bakyason gani xantafi sena dawo daga baya i can't take it anymore yanda kike xubar da hawayen nan pls"

" ashraf!muhannad ya...muhannad ya"

"Me muhannad 'din yamaki?!"

"ashraf,muhannad yayi raping 'dina"

Shiru tai tana jiran kalmomin ha'kuri da tausasa zuciya daga bakin ashraf,shirun dataji yayi yawa yasa ta'dago kanta ganin ashraf tai yana girgixa kansa alamar taci amanarsa 'dinnan bece Mata komai ba illah girgixa kan takaici dayai sannan yasa takalmansa yafice ko takan yiwa hafsat sallama bebiba...takaici goma da ashirin ya tsayawa Ummi Aisha ha'de da wani makokon bakin ciki suka dunkule waje 'daya suka tsyar mata da abu a ma'kogaronta harwani jiri takeji Lokaci 'daya kanta yafara ciwo,sabon kuka tafarayi ahankali me tsuma zuciya kukan da bashida sauti sede xubar hawaye..

"Innalillahi wa'inna ilaihirrajiun allahumma ajirni fi musibati wa'aklifli khairn minha"

Shine abinda Ummi Aisha taketa maimaitawa dama ashraf basonta yakeba kenan,tana cikin kukanne hafsat tafuto daga kitchen duk taji abinda sukai ahankali tasa hannu tarungumo tilon yar tata,itama hawayen take,

"Kiyi hakuri ummi Aisha Allah ka'dai yasan abinda ya 'boye duk naji komai kibar kuka Allah ya kawo maki Wanda yafi alkhairi amiin......!"

Kwana 6 kenan da fya'den ummi ,gaba 'daya Ummi Aisha ta shiga tsananin damuwa ta rame manyan idanuwanta sun shige ciki kamar ba itaba,yan makarntar su sun zazzo dan ganin ko lapia?!har professor tajuddeen shima yaxo danjin anya lapia kuwa UMMI AISHA(THE MAGNIFICENT)bata xuwa school,ganin ramewar datayi hakan yabasu tabbacin batada lapia ne,ma'kasudin ramewar tata kuwa yawanci kan tafiyar da ashraf yai jiya bebata amsa bane ta'dau hakan ta ajiye amatsayin 'kaddara da kuma yaudara  na halin mazan yau'

         •LAMIDO CRESCENT;

Kwance ashraf yake a kan gadonsa yana kallon saman p.o.p 'din 'dakinsa shikansa ya rame kamar bashi 'dinba,wayarsa ce take ringing kamar baxe dauka ba sekuma ya 'dauka dan ganin jay ne ke kiransa,

"Yo man,yh ina gidah ina ciki mana"Sannan ya katse kiran ya ajiye wayan agefe,

Jay ne yashigo cikin 'dakin da sallamarsa,

"Dude thought yau akwai school bakajeba kenan"

"Uhm" ashraf yace hakan yana gyara kwanciyarsa yakalli damansa,

"Wai meke faruwa ne dude?!nifa banganeba,bansan menayiba ko ince bansan meka janyo minba my woman(waliyya)tadena 'daukar wayana tamin text wai kayi deceiving best frnd heart 'dinta Wai itama tarabu dani shiyasa kaganni da safe haka dude ko ishashshen bacci banyiba jiya dan Allah menene?!"

"Play boy Allah yakama ka kenan kaine me playing da zuciyar 'ya'yan mutane thank goodness daka kasa baccin"

"Dude ba wasa nakeba,dan Allah me ya'daku da Ummi Aisha?!"

Ashraf yai shiru yana tunanin shin yafa'da abinda muhannad yaiwa Ummi Aisha ko ya ya?!girgixa Kansa yai alamar hakan be kamata ba,to Kuma ai yana bu'katar shawara nanmade sake girgixa kansa yai yana fezar da iskar bakinsa ha'de da sa hannu yana shafa kansa,

"Ba abinda ya'hadamu" yafa'di hakan with full confidence,

" 'karya ne wallahi akwai abinda ya ha'daku my woman baxata maku 'karya ba ai"

Ashraf yai murmushin da kyakkyawan dimples 'dinsa suka lotsa ya da'de yana kallon jay ganin yadda jay 'din yashiga damuwa sosai after all play boy ne na 'karshe inde yaudarace jay yayi degree akanta segashi yasamu wadda take tamaule da tasa zuciyar,

"My lips lie not jay,I'm damn serious ba abinda yaha'damu da ita kawaide kasan halina sometimes bansan hayaniya shysa ko school bana zuwa"

"To nide pls Kasan yadda xakai my woman ta'dau wayata ko muryarta ne naji"jay yafadi hakan yana marairaicewa sekace Wanda xeyi kuka

"Seka bari inkaje wajenta seka marairaice mata murya ba feminine gender bane abeg bu'de muryanka"

"Pls"

"Naji nace"

"Thanks dude"yakarashe maganar yana mi'kewa tsaye sannan yaiwa ashraf sallama yatafi wajen aiki dayake yariga ashraf din gama degree tun a umyuk yanzu haka aiki yake a ministry of education...

Ashraf ya jima yana sa'ke sa'ke azuciarsa sannan yatashi yashiga ban'daki ya 'dauro alwala yafuto yai sallah raka'a biyu ta nafila da niyyar Allah yasa abinda yasa agaba alkhairine idan ba alkhairi bane Allah yasa abin baxeyiwuba dama kullum yana sallolin darensa yana ro'kon Allah mabuwayi gagara misali kan yaxa'ba masa mafificin alkhairi cikin halin dayake ciki,Kuma dama yakira mahaifiyarsa awaya yaso yaje yasameta ma besamu Lokaci ba seya kirata awaya yashedamata abinda akeciki takumayi na'am tareda sanya albarka yakuma gayawa Hajia aisha(abokiyar xaman mahaifiyarsu wadda suke xaune a wajenta)itama tasaka albarka 'kwarai tayi murna Kuma ta amince kan xata shige gaba tayiwa abban nasu magana..... Ayush 'kanwarsa Ita tashigo cikin 'dakin nasa bakinta 'dauke da sallama ganin addua yake yasanyata jiransa sedata bari ya 'daga hannu xeshafa itama tadaga suka Shafa atare sannan tace,

"Yaya ashraf kazo injisu abba suna parlor"

"Toh kice ganinan"

Seda ya ninke sallayar tsaf  ya ajiyeta akan stool Sannan yafice yanufi parlor 'din,gaisheda iyayen nasa yai yasamu gefe daga 'kasa ya xauna,

"Babana yau babu makarantar ne?!"cewar mahaifin nasa

"Akwai abba banajin da'dine shyasa banjeba kuma ma munyi covering revision akeyi"

"Allah yatemaka"

"Amiin abba"

"Duk karame ashraf nace muje asibiti ka'ki,Allah de yabaka lapia" maman tafadi hakan tana jinjina kanta,

"Ba komai mama kawaide major stress ne na makarnta inyai yawa dama haka yake seyasa mutum kullum cikin rashin 'karfin jiki"

"To Allah yatemaka"

"Amiin"

Alhaji kabeer mahaifin ashraf yai gyaran murya yana gyara xamansa,sannan yafara magana;

"Babana munyi magana da iyayen naka(hajia barira da Hajia aisha)kuma na amince 'dari bisa 'dari na abinda sukace,kuma Ina adduar Allah yasanya albarka aciki,kun fahimci junanku da itane Kuma shin mahaifin nata yasan kana Neman 'yar tasa?!dukko dade babu matsala amma Kasan Neman aure acikin wani aure babu kyau a musulunci karmuje da magana muji yarinya anbada Ita ko ko??"yakarashe maganar yana kallon hajia aisha,

"Wannan haka yake alhaji,Kuma nima natambayeshi hakan yace babu matsala yarinya batada wani bayanshi Kuma sun fuskanci kansu gashide hakan yace" Hajia aisha ke fa'din hakan,

"To Masha Allahu,babu de wata matsala ko babana kun dedeta da yarinya??"

"Babu abba" ashraf yafadi hakan Kansa a 'kasa jiyake kamar yafuto yafadi abinda muhannad yamata sede bayasan tona mata asiri,

"To shikenan abu yaxo adede kenan dama kaga gobe asabar semuje in Allah yakymu yanxu xankira su kawu sale nafa'da masu yadda akeciki jibi kuma Insha Allahu xanje katsina can sena gayawa mahaifiyar taka da kuma su baffa na lagos,seka maida hankali kan karatunka ka kuma fara xuwa company 'din kafin ka 'karasa makarantar asan gurbin daxa'a maidakai Allah yasanya alkhairi"

"Amin abba nagode"

"Yawwa babana xaka iya tafiya"

Ashraf ya du'ka yasake godia sannan yatashi yatafi,bayan yatashi yatafi ne alhaji kabeer yake cewa;

"Lalle neman aure me canxa mutane yasunan yarinyar ma?!gashi tacanxa halayyar babana tsaf"

"Ummi Aisha sunanta akwai halin kirki da tarbiyya ai,duk arrogants 'din ashraf gashi yanxu babu dama niya birgeni sosai tunda dama Idan yaro yanuna yanason aure gwara ai masa sekaga idan ba'ayi dinba irin shine yara ke jefa kansu cikin wani hali,ga 'ko'kari Kuma itace kwanaki aka bata award 'din danace maka xamuje aka bata babban title ma 'THE MAGNIFICENT'"

"Hakane sosai nima nayaba da hankalinsa anan 'din,to Allah ya basu xaman lapia Allah yasa matar sace .Ai komai yaxo da sau'ki naji da'di ba ka'dan ba tunda mahafinta amininane sosai Kuma mahaifiyarta munyi xaman mutunci da Ita lokacin da taxauna a katsina"

"Allah sarki hafsatu ba"

Hakade alhaji kabeer suka xauna sunata maganar da Hajia Aisha,sun sanya albarka yafi a 'kirga Kuma sun amince sunyi na'am da abin atake a alokacin yakira yan uwa yafa'da masu dakuma aminansa da xasuje goben suyi tambayar...











                    •✨•

                      78









WASHEGARI;

      ___da safe da misalin 'karfe 10 aminan alhaji kabeer 'kwara biyu sun hallara alhaji ateeku da alhaji barau se 'kanin alhaji kabeerun da ake cewa saje su kenan dayake yayyun alhaji kabeer a katsina suke da xama wasun su Kuma suna yola shiyasa ya hutashshesu yace su zauna tunda sun manyanta.Bayan sun gaggaysa ne alhaji ateeku abokin alhaji kabeeru ke cewar;

"Amma de harda ku'din nagani inaso xa'akaiko base anje Kuma asake komawa akai ba"

"Eh to gaskia da kawai tambayar xamuje kudin kuma sedaga baya xa'a Kai"

Alhaji barau dake gefe yana shan kakkauran shayi yai saurin girgixa Kansa tareda fa'din;

"Yadda ateeku yace shine wannan duk wahalane Ai tambaya Kuma akoma daga baya akai kudi amma yanxu atafi da ku'din kaga anjefi tsuntsu biyu da dutse 'daya kenan ko ya kagani??"

"Hakane kuma hakan yayi,yamafi sau'ki to kamar nawa xa'a Kai kenan??"

"Dubu 'dari yayi alhaji barau??"alhaji ateeku ke fa'din hakan yana kallon alhaji barau

"Eh to ammade da 'dari biyu aka kai kudin zance dubu 'dari ku'din nagani inaso dubu 'dari yafi a mutince"

"Ehh yayi sosai to Allah yashige mana gaba ameen"

Atake alokacin alhaji kabeer yaciro wrapper 1k notes kwara biyu,nande alhaji atiku da barau sukace yabada dubu 'dari inda suka cika hamsin hamsin kowannensu kan cewar sunyi hakanne a ka'dan daga cikin gudunmawarsu,bayan sun gama tattaunawa ne Sannan suka tashi suka shiga mota suka nufi gidansu Ummi Aisha,ashraf dake le'kensu ta window se asannan yasaki labulen yakoma yakwanta akan gadon wani 'bangare na zuciyarsa cike da farin ciki da Kuma hagunta'

       •SARDAUNA CRESCENT;

Captain adam ne zaune akan kujerar parlor 'dinsa dayake asabar ce babu aiki kansa asama da alama tunani yake dama duk kwanakin nan haka yake tunane tunane sunmai yawa shiyasa dayaje asibiti tashin farko akace bp dinsa yayi high yarage damuwa,damuwar kuwa aksari akan Ummi Aisha yake yinta,kusan kullum shi kadai haka yake yiwa kansa magana yanzu yarinyar nan shikenan yaron nan yacuceta ya latata mata rayuwa kenan?yanxu waye xe'aureta,addua kuwa kullum seya yiwa iyalinsa kan Allah yatsaresu yakuma karesu daga sharrin masharranta amiin,yana cikin tunaninsa yaji ana knocking 'kofar,

"Waye?!"yafadi hakan yana xaune saboda bayasan tashi shiko parking 'din motar da akai bejiba saboda tsabar tashin hankalin dayake ciki,

"Damuna....."

Da sauri captain adam ya mi'ke yana murmushi sanin waye,sannan yasa hannu yabude kofar,

" 'dan kabiruwa"sekuma yasa hannu yarufe bakinsa

ganin yan ajinsu da shekaru kenan basu ha'duba

"Su ateeku nake gani ko ido nane?!"

Daria aka hau yi sannan suka shiga cikin parlor 'din gaggaysawa sukai tayaushe gamo?suka hau tsokanar junansu kowa ana fadar yarintarsa lokacin suna barewa college,captain adam yakira hafsat awaya kan tasa akawo drinks da snacks takuma 'dora abinci yayi ba'ki na musanman,da axama hafsat ta mi'ke tashiga cikin 'dakin Ummi Aisha don takirata tatayata da wani aikin,lokacin xaune Ummi Aisha take akan gadonta tana karanta littafin 'Americanah na chimamanda ngozi adichie'

"Ummi Aisha" amminta ta kirata bayan tashigo cikin 'dakin

"Na'am ammi"tafadi hakann tana ajiye littafin hannunta,

"Ya kan naki yayi sau'ki?!"

"Yayi sau'ki ammi gashi harna 'dakko littafi ina karantawa"

"Allah ya 'kara sauki dama wani abin xaki kamamin a kitchen baffankine yai ba'ki yace adafa masu abinci"

"Toh ammi"

"Yawwa yanxu kiramin habule(me wankinsu)yaxo yakai masu drinks 'din"

Mi'kewa Ummi Aisha tai tafita kiran habule tare suka shigo dashi ya'dauki drinks yakai ya sake dawowa ya'dau snacks yakai dayake weekly hafsatun keyin snacks ta ajiye saboda irin haka shi yasa captain adam din baya shiga fargaba saboda yasan tana fitar dashi kunya barin girki da sauri xata gama Kuma tayishi me 'dan'dano atsaftace cikin foodflasks 'cikin awanni 'kalilan hafsat da Ummi Aisha suka gama ha'daddiyar jollof rice 'dinsu datasha duk wani ingredients daya kamata sannan sukai sauce na kayan ciki da vegetables,gefe 'daya Kuma soup sukai na kaji dayasha tafarnuwa da kuma gashashshen kifi dayasha dankali da 'yar sauce harwani lemon 'bawo akai slicing agefe,lemon gargajiya sukai na zo'bo mesanyi da 'kan'kara se ha'din salad dayasha 'kwai da sauran Kayan ha'di gefe 'daya Kuma egg into egg sukai da kuma lemonade na ayaba(don't mind me I'm hungry*lol*)suka 'debi na ba'kin abokan captain aka zuba a tsaftatattun warmers sannan suka 'debi nasu inda akajera akan food holder akakai part 'din captain adam se hira suke sha bayan habule ya jere musu abincinne suka hau kan dinning sunaci se asannan sukai tsit da alama dadda'dan abincin hafsat yafara aiki a ma'kogaro,bayn sungama cin abincinne sunyi godia alhaji ateeku ke fadin;

"Mufa neman aure muka zo,munxo neman auren 'yarmu awajenka"

Captain adam yai murmushi,

"To awajena kuma?!wacce daga ciki kasan yaran biyune"yakarasa fadin hakan yana dubansu amma azuciarsa babu wadda yakawo se baby kay'

Alhaji barau yakalli alhaji kabeeru,nan alhaji kabeer yace,

"Ummi Aisha de ta farin itace mukaxo nemawa ashraf aurenta"

Murmushin dole captain adam yai yana kallon alhaji kabeer,sekuma yai shiru yarasa abinda xe ce,

"Tanada wani ne a 'kasa?!"alhaji barau yafadi hakan ganin shirunda captain adam yayi

"Babu kowa kawai de..."bekarasaba alhaji kabeer yai saurin katseshi

"Base kace komai ba damuna,yarinyar nan koni inada ikon aurarda ita ko bandashi?!"

"Kanadashi mana 'dan kabiruwa"

"To saboda haka,duk wani abu ashraf komai yafadi Kuma babu matsala Allah yasanya albarka munji mun amince nasan Idan ana neman aure ba'asan a'boye komai Kuma duk munsan yarinyar nan munsan halinta saboda haka mun amince" alhaji kabeer yai saurin fa'din hakan axatonsa ji yake captain Adam xece basu shrya bane ko makamancin hakan,

Jin hakan captain adam yai xaton ashraf yafada masu halin da Ummi Aisha ke ciki,sosai yaji da'din wannan abu yakuma 'Kara godewa Allah azuciarsa,

"To shikenan Allah yasanya albarka aciki banida bakin godia sede nace Allah yasanya alkhairi Amiin"

"Mune da godia damuna Allah ya albarkacesu amin yasanya albarka acikin auren"

"Amiin"

"Sannan da ku'din xance mukaxo fa dan mu ashrye muke"

"To to Shikenan sede nika'dai xankarbi kudin kenan?!"hannu yasa a aljihu yaciro wayarsa yakira yaya sameer 'din hamdalah yayan yayi najin wannan abu don yaji xancen Ummi Aishan Kuma shi dama 'daukar hakan yai ya ajiye a matsayin kaddara,yakuma ce yakarbi kudin babu komai Allah yasanya albarka,

Atake awurin akai komai suka ciro kudi suka bayar captain adam yace yayi yawa dakyar ya yarda ya karba don sunce Wallahi baxasu koma dasu gidah ba,sannan akatsaida biki kafin axumi Idan ankawo lefe se a tsaida ranar 'daurin aure da saurin shagalin biki,shima yabada tukwici da kuma sauran abun motsa baki sannan suka mai sallama suka tafi cikeda jin da'din anbasu aurenta shima yakoma part 'din su Ummi Aisha zuciyarsa fes nadaga abinda yafaru yanxu yakuma ajiye hakan amatsayin wata baiwace daga rabbus samawati,









                    •✨•

                      79







Yana shiga da sallamarsa yasamesu a parlor suna kallon sunnah tv,amsa sallamar sukai inda Ummi Aisha ta mi'ke xata bar wajen captain adam yai saurin dakatar da ita,

"Tsaya akanki zanyi magana"

"Toh Baffa"Sannan ta nemi waje a 'kasan carpet ta xauna gaba daya gabanta faduwa yake don batasan wacce maganar bace,

"Nace menene tsakaninku da ashraf 'dan wajen alhaji kabeeru?!"dukkoda yasani so yake ya tabbatar da hakan daga bakinta

"Baffa...."sekuma tai shiru,

"Saurayin tane hayatee"Hafsat tafadi hakan don tasan Ummi Aisha baxata iya bawa uban amsa ba tanajin kunya,

"Kunyi magana dashi ne kan ya turo iyayensa?!"

"Baffa bamuyi ba,yazo de nan shekaran jiya saboda yaga bana zuwa makarnta Kuma bana picking calls,shine yaxo yaji ko lapia?!nace masa lapia qalau shine nafa'da masa abinda yafaru to kumade ko magana beyiba yatashi yafita"

"Wani abunne yafaru Hayatee??"

"Dana kiraki nace ki 'dora abinci nayi ba'ki ai alhaji kabeerun ne yaxo da 'kaninsa da abokananmu 'kwara biyu inda sukaxo nemawa shi ashraf 'din auren ita Ummi Aishan maganar da nake miki ma ga ku'din aure sunkawo dubu 'dari biyu kudin nagani inaso da ku'din xance muntsaida biki ma kafin axumi Insha Allahu tunda ba wani bincike xa'ai ba nasan mahaifinsa shima yasanni yaro yanada abinyi danma yayiwa Kansa shirme datuni ya hada degree dinsa"yakarashe maganr yana ciro ku'din a 'aljihunsa ya ajiye akan center table din dake tsakiyar parlorn..

"Alhmdulillah ya rabbi for the unlimited blessings lalle"take awajen Hafsat tai sujjada tana hawaye,

Ita kanta Ummi Aisha dake gefe wani nauyayyan abune yatafi mata daga ma'kogaro xuwa ciki ta tsaida hakan a amtsayin damuwarta ce ta fa'da,ita  kanta tarasa mema xatai  don da'di kamar taje ta rungume iyayen nata haka takeji,take wata zuciyar tafara raya mata to kuma  ai ashraf 'din bece mata xa'axo tambaya ba hasali ma tunda yatafi basuyi waya ba ko 'dan text 'din daya sabar mata da,to me hakan ke nufi?!Allah ka'dai yabarwa Kansa sani,captain adam ya jima yanawa Ummi Aisha nasiha sannan yatashi yafice xuwa masallaci,nanne hafsat ta 'dora da tata nasihar daga inda captain 'din yatsaya,hawaye sha'be sha'be kwance a fuskokinsu na farin ciki,bayan hafsat tagamaiwa Ummi Aisha nasiha tajanyo waya tafara kiran yan 'uwa da abokanan arziki kan kawo ku'din tilon 'diyar tata da akayi ana gama gayawa Mjay tace gatanan xuwa ba a waya xaai xancen ba,ba'afi mintina ka'dan ba ta 'karaso dayake se bayan sallah xata koma can capetown 'din bayan sungaysa ne Mjay tabi Ummi Aisha da kallo Ita Kuma tasaukar da kanta 'kasa irin kunyar nan,

"Ja'ira harkin fara kunyar amarcin?!"

Itade Ummi Aisha shiru tai tana daria 'Kasa 'kasa,

"Kingani ba ko ya hafsa dama nace maki Allah yana tare da me gaskiya gashi adduar da muke Allah ya 'karbi kukamu"

"Hakane kuma to Allah ya 'Kara karemu da kariyarsa ameen"

"Ameen ya rabbi"

"kince kafin azumi ko?!"

"Eh haka baffansu yace to Kinga kuwa ba doguwar rana xa'asakaba kenan"

"Ai nima na'ki jinin saka doguwar rana jide bikina sati biyu akasa kintuno?!"

"Natuno lokacin da cikin Ummi Aisha ne"

"Tabbas hakane ashe fa ba'a haifeta ba"

"Ba'a haifeta ba mana lokacin de da cikin yatsufa a lokacin ni inaga bayan bikin da sati biyu ne nahaihu"

"Tabbas natuno lokacin Ina can banxoba seta skype naga baby"

"Ehh"

"Bari tun wuri mu fara dashi dan anko semunyishi kala kala senayi 'kara'i xan ajiye nana inkwaso shoki"

Hafsat da Ummi Aisha suka dinga daria ganin yadda Mjay tai da hannu xata kwaso shokin,

"Ai banajin xa'ai wani bidi'a daga 'daurin aure se wuni"

Mjay ta ware ido,

"Haba Yaya hafsat,sekace bikin baxawara yo ko bikin baxawara aiba'ayi haka ba ballantana,yaxa'ai bikin fari kuma babbar 'ya acikin gidan kice baxa'ai wani shagalin biki ba to kwa inde lami xakuyi baxanxo ba count me out"takarashe maganar tana girgixa kanta

"Bikin 'yar kune Kuyi abinda kukaga dama mjay nina isa nahana?!"tafa'di hakan tana daria,

"Yawwa yanxu naji xance ai duk wani ha'dad'dan event da akeyi abikin 'yangayu muma semunyi bikin first niece 'din nawa,tundaga kan bridal tea party har cocktail dinner semunyi da izinin Allah"

"To Allah yakaymu darai da lapia"

"Ameen"

"Kuma su magajiya sun sani?!"

"Ai ba sarasa ji ba ko?!"

"To Allah yashiga tsakanin nagari da mugu"

"Amiin de"

Hira suka shiga yi ta yan uwa suna Kuma bawa Ummi Aisha motherly advice tana 'dauka,



"Ummah wai magungunan me kike tashane?!"cewar baby kay

"Nace maki banajin da'dine"magajiya tafadi hakan tana share gumin  dayake tsattsagowa daga kanta,

"Gumi fa kike ummah ga Kuma ac tanayi"

"Dan Allah khadija ki kyaleni kaina ciwo yake"

Hannu baby Kay tasa tadauki ledar maganin me tambarin well care pharmacy,ware Ido baby Kay tayi ganin magungunan dakuma abinda suka 'kunsa da sauri magajiya ta wafce ledar amma ina baby Kay tagama gani,

"Brain cancer ummah"baby Kay tafadi hakan tana rufe baki,

"Eh itace dani khadija nima se shekaran jiya nakeji awajen likita amma dan Allah karki fadawa baffanku"takarashe maganar tana rufe san'kwan kanta da dankwalinta,

"Dole naje asibiti ayimin checkup nasani ko nima nayi inheriting daga gurinki"

"Guduna kike khadija?!"tafadi hakan tana ware Ido

"Ba wani gudunki ai gaskiyace ummah dole naje nai confirming"tana rufe baki kenan  captain adam yai sallama yashigo ciki dayake kullum yana shiga daman yabasu ku'din cefane kamar yadda aka fada cewar inde mace xatai iddah gidan mijinta to cinta,shanta yarataya awuyan mijin har iddarta ta 'kare,bayan sungaysa ne captain adam ke kallon khadija yana tambayarta;

"Akwai abinda kuke bu'kata ne?!"

"Akwai abinci baffa sede  handouts ce tafito na wannan week 'din shine nakeson insiya"takarashe maganar kamar gaske bayan babu wani handouts ku'di de kawai takeso,

"Nawane??"

"Sunada yawa Kuma kowannesu daga 500 yake kamawa sauran manyan kwara uku Kuma dubu 'dai  'dai ne"

Ciro ku'di yai da yawa xasi dubu goma ya mi'ka mata,godia tai sannan yai hanyar 'kofa xefuta sekuma yadawo yana kallon gefen da magajiya take,

"Ankawo ku'din Ummi Aisha 'daxu seku sanyata cikin addua"Sannan yasakai yafice

"To"kawai magajiya tace atakaice,

"Ummah kinji meyace?!"

"Naji kila wani 'dan abokin nasa ne kowani a hadejia suka hadashi da Ita"takarashe maganar irin ko ajikin nan nata

"May be"baby Kay tace hakan sannan ta mi'ke tashiga cikin 'daki..dan duk axatonsu wani ne davan basu ta'ba kawowa ashraf bane,

Ta 'bangaren ashraf kuwa Mama ce tasashi agaba kanlalle yakira Ummi Aisha yatambayi size 'dinta na Kaya da takalmi da inner wears tunda lokaci akure yake gwara aikomai agama,gashi ba waya suke ba rasa yadda xeyi yayi adole yashiga 'daki maman sunata tsokanrsa shikwa shiga 'dakin dayai akan danbada Ita xeyi wayar bane shiysa,ringing biyu waliya ta'dauka dayake Ummi Aisha Tafada mata komai,nan yatambayeta komai tace xata mashi text suna gama wayar kuwa ba'ajimaba text dinta yashigo harma da abinda yamanta dukta rubuto harda favourite colors 'din Ummi Aisha da irin kayan datakeso kaf waliyya sedatamai text 'dinsu,















                     •✨•

                       80











Kafin sati biyu tacika gidansu ashraf sun ha'da lefe yan gaske babbar yayarsu ashraf 'din itada hajia aysha su suka tafi dubai suka ha'do Kayan lefen babu ce kawai babu aciki akwatuna guda talatin da takwas(38) yan gaske customized akayosu daga designer company 'din dkny(donna Karan new york)mama takira Hafsat tace mata xasu kawo lefe ranar asabar nanda kwana uku kenan,atake a gurin Hafsat takira yan uwa da abokanan arziki harda ma'kota tashisshiga Tafada masu da kanta,rankataf 'yan uwansu na uwa da na uba sedata fadawa both site,har yan borno sedata fadawa dayake asalin mahaifiyarta kanurin yerwa ne,yan uwan mahaifinta kuma asalinsu 'yan yola ne fulanin yola shysa hafsatun take Kama da jinsin larabawa saboda ruwa biyu ta ha'da,kaf yan hadejia duksunji su sadeeya da safeeya duk xasuxo har gwaggo data tsufa tukuf itama tace da'ita xa'ayi,

Ranar asabar 'karfe 3;30 shine lokacin da aka saka xa'a karbi lefin gidan yacika ma'kil babu masaka tsinke,kowa yanaso yakashe tsutsar idonsa yakuma sanya albarka ga tilon 'diyar hafsatun,muna_b ma taxo amma su 'yan ganin 'kwa'kwaf ne se tuntsururun dariya suke aganinsu lefan jigari jigari xa'ayo mata irin ha'din 'dambatta suke fatan gani,sosai akai ordering abinci da snacks agurin meena,da leda da akayota musanman idan mutane xasu tafi se'abasu cike take da Kayan 'kwalam da ma'kulashe,,Ummi Aisha da sauran 'kawayenta na part 'din baffansu itakam gatanan gatananne don haryanxu ashraf be kirataba tayi mamaki kwarai dataji bestienta tace Ita yanakiranta,bu'dewar gate 'din gidanne yatabbatarwa  Ummi Aisha da 'kawayenta 'yan kawo lefi sunxo,aguje suka fice suka barta ganin haka yasa tatashi tashiga ban'daki tadauro alwala tafara sallar godia ga ubangiji da ya azurtata da wannan babbar baiwa yakumasa takeda rabon aure a doron duniya....

     _____Motoci ne da suka amsa sunan motoci sukai ta shigowa kala kala wasuma basu samu wajen parking ba dukkoda katon parking space din dake gidan wasu motocin awaje aka barsu,kayan su shinkafa da su masara buhu buhu akaita shigowa dasu harda Kayan tea cartons cartons da carpets kwara uku manya sekuma akwatuna suka biyo baya haka aka dinga shigowa dasu kala kala pink,amber orange dakuma purple,red sauran ba'ka'kene har guda talatin da takwas,kallo seya koma kan akwatunan da mutanen dake shigo dasu,gasu 'yan gayu,magajiya da muna_b da baby Kay xuba na mujiya sukai suna kallo baki bu'de hassada ta nuna 'karara a fuskarsu kowa yagane ba'kin ciki suke,bayan anyi addua aka fara bu'de akawatuna kamar yadda al'ada ta tanadar,aunty fareelah auntyn ashraf itace takalli akwatunan kamar an manto wani abu waigawa tai tana kallon ayush 'kanwar ashraf,

"Ina basket 'din yake?!"

"Laa yana motar jay bari na 'dakko"tafadi hakan tana mikewa,suka fita itada wata kansu 'daya

Ba'ajimaba suka shigo da katon basket 'katoton gaske dakyar suka ajiye suna maida numfashi cike yake da sacks kanana na henna/lalle/nalle da goro da alawoyi da chewing gums kwali kwali harda sabulai kala kala da slippers dayawa dakuma perfumes da incense(turaren wuta)da humra fal cikin basket 'din se 'kamshi ke tashi,se kallo Kuma yakoma kan basket din da aka ajiye agefe,sosai aka shiga ciro  Kayan akwatin 'daya bayan 'daya kamar yadda 'yan sa'ido suke,kowa idonsa yayo waje don basu ta'ba tsammanin hakan ba,sosai baby Kay dasu magajiya sunyi mamakin ganin lefen wani babban tashin hankalin Kuma ashraf ne mijin ashe abinda sukai yatashi abanxa kenan?! akwatin gold ma daban yake 'dan babban kit dashi design har uku da dubai,Saudi dakuma english gold harda awawwaraye daban suma dakuma zobuna,banda fashions kala kala 'yan gaske kowa na gurin was deeply suprised ganin kayan, komi naciki sabon fitowa ne na watan Kuma yawanci ma customized ne.

Laces ma abin kallo ne Kaya de kam baxasu 'kirguba,takalma da jakankuna kaf designers ne daga su dkny,yvsl,giogio armani harda designer dinsu kardashians wanda bakasafai ake sakosuba sefa ya'yan who is who.Da mayafai kala kala harda design 'din basma k,turarukama ba'a magana,na 'karkare maku xance de lefen Ummi Aisha was beyond your expectations duk wani yadda xaka kawo lefen azuciyarka to yawuce haka,ku'din 'dinki ma abin kallo ne to cut it shot lefen THE MAGNIFICENT yayi babu 'karya ko hasidin iza hasada baxe kusheba babu itace kawai babu aciki,bayan angama kalla tsaf aunty fareelah tajanyo babban basket 'din dakyar ta ajiye atsakiyar parlorn,

"munji ance rabin amaryarmu kanurin borno ce kanurin ma Kuma yerwa ko?!"

Nanfa kanuri's dangin hafsat na uwa suka fara gu'da suna yarawa suna maganar wannan haka yake,

"To wannan Kayan amaryar mune don munsanta tanasan 'kamshi itada aunties 'dinta na uwa, humran ciki Kuma abawa aunties 'dinta na uba(bawaa)"

Sosai sukaji da'di both dangin Ummi Aishan kanurin 'bangaren hafsat dasu sadeeya aunties 'dinta na uba da irin wannan karramawa da aka masu,kanurin 'bangaren hafsat sune suka fa'di yadda al'adar take Kayan basket 'din da aka kawo suka suka rarraba tsakaninsu sannan suma suka basu nasu tukwicin kamar yadda akeyi,wasa suka dingayi tsakanin Fulani da kanuri kamar yadda akeyi ada suna tsokanar junansu kowanne yana kare yarensa,sannan aka kai dangin ashraf babban parlor din gidan da abinci da aka jere musu na buffets/serve ur self,,,Se 'karar cokula kakaje(nima miss xoxo special kujera naja naxauna naci nai nak tattass na lashe kwano na!No shame!)bayan dangin ashraf sunci sunsha suka Fara haramar tafiya nansuma gidan su Ummi Aisha sukai tasu bajintar ku'din tukwici sosai suka bayar me tsoka da lots and lots and lots of cartons na drinks,huge coolers na abinci shi akasaka kaji se manyan trays aka saka snacks harda gasassun kifi,mjay Kuma tata tarbar gashashshen rago taiwa dangin ashraf suka tafi dashi,godia both dangin couples din sukai wa junansu anyi raha kamar sundau shekaru da sanin juna,Hafsat dake 'daki Banda sallolin nafila babu abinda takeyi na Allah yasa yadda aka kawo lefen nan a sa'a yasa agama komi a sa'a yamaida kowa gidansa lapia yakuma ka'de fitina amiin,

  

Kafin kace me magajiya,muna_b da baby Kay sunbar wurin suntafi bangarensu ba'kin ciki karara a fuskarsu sede Allah ya kyauta kawai,kowa yayi murna ciki harda su sadeeya kannen captain adam,lefe yasha 'dauka a hoto yakuma sha posting a social media,,mutane sunyi addua Kuma sun kashe tsutsar idonsu,duk maitar mutum sede ya hakura base yaga 'karshen Kayan lefen nanba don yawon Kayan maidasuma aikine,sede muce Allah yasanya alkhairinsa ciki amiin,an tsaida date 'din biki wata 'daya cif on 28 of janaury shine ranar da aka tsayar na 'daurin aure,

  

Da dare captain adam yaga lefen yakuma sanya albarka,Hafsat ma haka dayake atare suka gani,Ummi Aisha kuwa se washegari da safe suka sake gani itada Waliyya,sosai tayi mamakin wannan Kayan haka kamar wani mini mall ace duk natane??lalle Allah shine abin godia me azurta wanda yaso aduk lokacin dayaga dama,a washegarin Mjay tafara bawa hudayya order na Kayan events din Ummi Aisha Wanda amaryar xatasa,akuma ranar suka shiga kasuwa fitar da anko na events kamar yadda Mjay da Waliyya suka tsara,xa'ai bridal tea party,kamu,elegants eve,yini,royal ball,dinner da kuma wushe wushe night ,gala night, duk haka suka tsara danda captain adam beyardaba Mjay ta nace da magiya da komi sedaya shafawa kansa lapia ya yarda,amma duk wannan abin da ake ko sau 'daya ashraf tun rabuwarshi da Ummi Aisha besake kiranta ba,har aka kawo lefen ake Kuma shirye shryen biki tun tana damuwa harta ha'kura se addua datasa agaba kawai...

        •

Continue Reading

You'll Also Like

308K 18.4K 40
You live in a different time zone Think I know what this is It's just the time's wrong
24.8K 129 2
kallo yake Mata cikin ido kallo Mai cike da tsantsar so da kauna Wanda harya Sanya jikinta yay sanyi........ #1 in katsina stories 🥳 June 15, 2022 #...
298K 20.8K 156
Tác phẩm: Toàn thế giới đều đang đợi người động tâm. Tác giả: Tố Tây Người gõ: Mia của bạn nè Beta: Hoa Hoa của bạn đây Ý là truyện này gõ nhanh quá...
806K 69.4K 59
Zanen ƙaddaransa yana cikin zuciyarta, kamar yanda zanen nata ƙaddan ke cikin tasa zuciyar. Idan zuciyoyi suka haɗe waje guda akan samu wata irin zaz...