DIYAR DR ABDALLAH

By Aynarh_dimples

44.4K 6.3K 1.1K

Zuciyar sa yana mashi wasiwasi, abinda yake gudu shi ke shirin faruwa dashi. Bai taɓa samun kansa cikin wanna... More

One - Kankana
Two- Ruwan Sama
Three - Ummata
Four - IPhone
Five - Annoba
Six - Wanene Mahfooz I
Seven - Mahfooz II
Eight - Mahfooz III
Nine - Mabuɗin Zuciya
Ten - Kallon Kallo
Eleven - Farin Wasa
Twelve - Mugun Mafarki
Thirteen- Permanent Stalker
Fourteen - Rarrafen Carpet
Fifteen - Ƙarfi Yaci
Sixteen - Bazan Barki Ba
Seventeen
Eighteen - Ni Ce Asalin Diyar Dr Abdallah
Nineteen - Naga Wajen zama
Twenty - Mijin Tauraruwa
Twenty-one - Annihilation
Twenty-two - Pound Of Flesh
Twenty-three - Ribar Haƙuri
Twenty-four Bazan Barka Ba
Twenty-five - Love That Hurts
Twenty-six -Rendezvous
Twenty Seven- Idan Tayi Ruwa Rijiya
Twenty-eight - To Be Tainted
Twenty-nine - By Whatever Means Necessary
Thirty-one- Miscreant
Thirty-Two - Déjà-vu

Thirty - Sun Shuka Sun Girbe

1.4K 247 47
By Aynarh_dimples

Zabura da ihu Fauziyya tayita yi kamar wanda ta haukace, amma lafiyar ta lau. Jifa ta samo yi da duk abinda ta gani. Haka taje wajen hular Alhaji Sani tayi fatali dashi. Sosai suka firgita suna zare ido cikin ɗakin kafin ta illanta su. Wanda tafi tsorata itace Jamila, haka tayita baya baya kada Fauziyya ta damƙeta. Ana cikin haka ne sai akayi sallama. Muryan da kowanne daga cikin su ne ya sani sarai cikin dodon kunnen sa.

Hannunsa riƙe yake da travelling bag ɗin Fendi, sai tabarau siriri baƙi a saman idansa. Rigar mai layi layi blue ne ya saka, sai kuma wando baƙi. Kafansa sanye yake da takalmin Michael Jordan fari tas babu kala ko datti.

“Lafiya na ganku charko charko haka?” yace masu.

Da sauri ta ƙarasa wajen dayake ta soma mashi magana tana kuka, “Wallahi Al-amin karka yarda da abinda suke cewa, zasu raba mu ne, na rantse maka da Allah ni ce asalin mahaifiyar ka”

Ajiye jakarsa yayi a ƙasa yana kokarin fahimtar abinda Fauziyya take faɗi, kwata kwata batayi ma'ana ba a batun ta. Anan ya soma bin yan ɗakin da kallo wanda sukayi charko charko cikin tsoro.

“Wai lafiya?” ya sake faɗi.

“Lafiya lau Al-amin, shigo ciki.” Alhaji Sani ya ce. Saiya kalle Fauziyya wanda take haki tana zare idanu.

“Wallahi koki natsu koki sha mamaki, kin mance na sanki sarai ne halan. Kuma nasan abinda zaki iya aikatawa da wanda bazaki aikata ba.”

Share hawayen ta takeyi da hannu ɗaya, saita riƙe ma Al-amin hannu da ɗayan hannun. Tare suka ƙarasa falon suka zauna. Mai aikin Fauziyya lokacin tazo tana share inda aka fasa table ɗin. Har lokacin Jamila bata bar fargaba ba, ta bala'in tsorata da Fauziyya. Al-amin ne yayi dogon ajiyar zuciya, sannan ya kalle baban shi.

“Abba, wai me yake faruwa ne?”

“Ina so ka natsu ka saurare ni Al-amin, nasan kai yaro ne mai hankali da kaifin basira. Toh inaso kayi amfani da wannan hankalin akan abinda zan gaya maka a gaba. Kalle Mahaifiyarka,” saiya nuna mashi Hajia Fauziyya. Anan Al-amin ya kalleta saiya sake kallon Alhaji Sani.

“Kaga wannan matar dake zaune kana kallo a matsayin mahaifiyarka, yanzu labari yazo mana wai ba ita bace ta haife ka...”

“Wallahi ƙarya ne... Na rantse da gemun mahaifina.” tace tana kuka.

Gaba ɗaya ɗakin mamakin ta sukeyi, basu taɓa jin cewa ana rantsuwa da gemu ba sai ranar, tana abu kamar yar tasha ko yar bori.

"Zo ki fita,” Alhaji Sani yace mata yana zare idanu.

Ita kuma saita ruga bayan Aisha ta ɓoye tana kuka, bataso ta fita kuma bata so ta tsaya ta bari su gama maganar su. Jamila ne ta sake magana wanda ya gigita Fauziyya.

“Ai nasan inda Rumasa'u take aure, idan kunaso sai na kaiku, abu kuma na zamani ga DNA. Zai nuna idan ƙarya nakeyi,” Jamila ta sake maimaitawa.

Fauziyya ne ta kasa haƙuri da abinda Jamila tayi, mamaki takeyi yadda ta ɗauki alwashin saita tarwatsa mata rayuwar aurenta. Rayuwar data daɗe tana ginawa. Gashi cikin mintuna kaɗan ta tarwatsa komai. Nufanta tayi tareda damƙar mata kwalar riganta. Saita soma kilarta tako ina.

“Saina halaka ki! Kafin ki kashe min aure saina kashe ki, ” tayita nanatawa tana kuka.

Da kyar aka kwace Jamila, Aisha ne ta wuce da ita ɗakin masu aiki ta rufe. Saboda muddin sukayi arba da Fauziyya na lahira saiya fita jin daɗi.

Alhaji Sani ya yanke shawara zaije Kaduna da kansa ranar domin yaga Rumasa'u tareda iyayenta. Shima Al-amin yace zashi domin a yi komai a gaban sa. Sau da dama ya saba samun shakku akan inda ya fito. Musamman yadda kamannin sa ya fita daban dana sauran yaran, gashi kuma genotype ɗinsa AA ne na sauran gidan AS. Wannan abubuwan sun daɗe suna cinmasa tuwo a ƙwarya amma babu wanda ya bashi amsar tambayar sa sai yau.

A yau komai yayi mashi ma'ana, a yau komai ya fito mashi dalla dalla. Tunani kala kala suka rinƙa faɗo mashi, wasu masu hankali wasu na rashin dalili. Wanda yafi tasiri shine yanzu menene matsayin sa a wajen Alhaji Sani. Su waye iyayen sa? Wani rayuwa zai kuma fuskanta idan yaje wajensu?

An riga an tsaida tafiya wajen su Dr Abdallah a Kaduna, mota daya ya jiɓanci Hajia Salima da Nurse Jamila, watau motan su da suka zo dashi. Sai Sadiya ta roƙe alfarma maimakon mijinta dazai zo daukar ta gobe idan babu damuwa zata shiga motan su domin ta koma gida. Salima bata damu ba ko kaɗan, dama kujerar gaba babu kowa tunda ita da Jamila suna baya ne abin su.

Ɗayan motan Al-amin ne zai tuƙa Alhaji Sani, da Aisha da kuma mijinta. Kwata kwata babu zancen Fauziyya a tafiyar. Alhaji Sani ya gargaɗeta akan idan ta kuskura ta bisu a bakin aurenta. Amina ce kishiyarta tafito domin tayi ma Alhaji Sani magana akan Zainab yarta, yarinyar tana fama da ɗan kankare wanda ke mata bala'in zugi. Ganin mutane datayi charko charko a farfajiyar gidan yayi mugun bata mamaki. Cikin natsuwa da nuna kula saita ta tambaya ko mutuwa akayi. Yanayin fuskan su yayi kamada da wanda aka aika masu saƙon mutuwa. Fauziyya ce tayi karap ta soma masifa.

“Munafuka, idan ba'a kasa dake ba kada ki ɗauka. Ina ruwan ki da al-amuran gidana? Matsayiciya kawai”

Cikin mamaki ta zare ido tareda dafe kirjinta, koba komai ta cancanci ace akwai girma da mutunta juna tsakanin ta da Fauziyya. Tunda a ƙalla tafi shekara ashirin tana aure a gidan. Amma kullum banda mugayen kalamai babu abinda Fauziyya ke binta dashi. Ita kuma ta ɗauki alwashin bazata taɓa tanka ta suyi hayagaga ba. Bazata taɓa bari yaranta suga tana sa'in sa da kishiya ba. Saidai Fauziyya tayi ita kaɗai. Kuma wannan shirun yana bala'in ƙona ma Fauziyya rai. Ita batada wani buri daya wuce suyi kaca kaca harya kai ga dambe su yaga ma juna kaya.

“Haba Yaya ! Me yayi zafi daga tambaya. Allah ya baki haƙuri,” saita juya ta fuskanci inda Alhaji Sani yake zaune a 'owner's corner' na mota.

Bata ankara ba saiga Fauziyya ta nufeta da sauri, da badin Al-amin daya soma gani ba, kuma yayi maza ya sha gaban Fauziyya, da ranar Amina sai an gotan mata da ƙashi. Numfashi Fauziyya takeyi tana kokarin fizge kanta daga riƙon dayayi mata. Shima da kyar yake iyawa tunda Fauziyya tanada jiki sosai. Daɗin abin yana zuwa gymnasium yana motsa jiki.

“Dan ubanki nasan da saka hannun ki, kinga bakya haihuwar ƴaƴa maza shine kika haɗa baki da maƙiya na domin azo a tafi da Al-amin. Amma wallahi saina ci kutumar ubanku ku duka. Saina koya maku darasi. Gasarshen nama baiga wuta ba, balangu baiga wuta ba, soyayye baiga wuta ba, tsire shine yaga wuta tunda ido huɗu sukayi dashi harya nuna,”

Saita sake zabura domin taje tayi ma Amina laga laga, ita fa duk tunanin ta Amina ce umul aba'isin shigan ta wannan tashin hankali. Tana ganin Amina ce ta haɗa baki dasu Nurse Jamila domin a yaga mata rigar mutunci, amma abinda bata sani ba shine ta ina suka haɗu ma tukun.

Alhaji Sani ya fito daga mota, yayi mugun gajiya da takaicin Fauziyya. Ta manyanta amma tanada bala'in yarinta. Banda abu ina ita ina dambe a wannan marra. Gyara zaman babban rigar sa yayi saiya kafa mata ido. Itama dole ta natsu tunda shiba sa'an yinta bane.

“Wai ke meyasa kike yi kamar mai kwakwalwar kifi ne? Nace meyasa bakya abu da dattako ko hankali? A gaban yara da jikoki kike zubar ma kanki mutunci. Haba Fauziyya ! Idan baki girma yanzu ba sai yaushe? Sanda na mutu? ”

Ajiyar zuciya yayi cikin takaici, saiya soma nuna ma Fauziyya hannu.

“Watau ke baza'a maki magana kiji ba koh? Kuma bazaki yi hankali ba ko tuba ga Allah? Allah ya baki sa'an dukanta,"

Kallon Al-amin yayi saiya soma magana, “ka saketa,” saiya sake kallon Fauziyya.

“Kada ki fasa bugun Amina. Kinji koh ? Nace idan ke yar halas ce ki kasheta ki aika ma iyayenta gawan ta,”

Saiya shiga mota, “tuƙa mu Al-amin muje,”

“Wayyo Allah na shiga uku, yanzu Alhaji har zaka tazorta ni a gaban kishiya ta. Wayyo na shiga uku boka yana aiki sosai. Ni ce fah mukayi auren saurayi da budurwa, bafa saura bace kamar Amina amma kake gayamin magana dominta,” ta ɗuka tana shela amma babu wanda ya tanka ta.

Amina ta koma sasanta, suma mai gadi ya buɗe masu mota suka nufa hanyar Kaduna. Zuciyar Alhaji Sani idan yayi dubu to ya ɓaci. Allah ne ya haɗa jininsa dana Fauziyya. Shi tausayi take bashi, saboda bazai iya nuna wani halin kirki datake dashi ba a shekara arba'in da biyu na auren su. Tabbas da wani ne ko wata ɗaya bazata haura gidan sa ba.

Tun sanda take amarya da sati ɗaya tayi ma ƙanwar mamansa watau Innan sa rashin kunya, da ba'a shiga tsakanin suba kila da Fauziyya ta kara dambe da ita. Abin dambe baya mata wuya, yanzu zata ɓalle kallabi taci ɗammara su fafata.

“Al-amin rage gudun nan,” Alhaji Sani yace mashi. Yaga yanata zura gudu kamar zasu tashi sama. Koda yake yasan bada gangan yakeyi ba. Ya dulmiya cikin tunani ne saiya ke zura gudu.

Fauziyya ita kaɗai a farfajiyar tana watsa ashar, duk wanda ya ganta a wannan yanayin dole yace tanada ƙaramin hauka. Sam mai hankali bazai taɓa yin kwatankwacin abinda takeyi ba. Dabara ne ya faɗo mata nan take, aikam ta zabura tareda miƙewa tsaye. Ɗaki ta koma domin ta ɗauko jakarta. Saita wuce ɗakin Alhaji Sani tareda buɗe bedside drawer ɗinsa. Kuɗi ne ya ɗebo daga kasuwa wani yana son rance, haka ta kwasa wrap ɗin yan dubu gudu uku, dana ɗari biyu guda biyu.

Mayafi ta ɗauko tareda makullin mota, bawai ta wani iya mota bane. Tana zuwa cikin anguwa da inda bashida nisa, a cewarta honk ɗin mota yana bala'in firgita ta, saita tsure tareda hargitsa lissafi. Amma yau tanada abinda yafi honk ɗin mota firgitarwa, dole ta dake zuciyarta ta hau titi.

Itama Kaduna ta nufa, dole saita tarwatsa al'amuran Jamila, idan kuɗi ne yake damunta zata bata kowa ya zauna lafiya. Ita kuma Jamila tana mota tana murmushi, zobunan Fauziyya wanda ta watsa mata take kallo. Ashe ta faki idon mutane ta kwashe tas. Haka ta jera su a yatsunta. Sai wal wal yatsunta suka rinƙa yi. Tunda take bata taɓa saka zoben gwal ba. Saidai ta gani a wajen mutane. Koda ta sace yaro, kokuma tayi musanya idan an biya ta bata wani abin kirki da kuɗin. Balle kuɗin haram.

Koda yake sau ɗaya ta taɓa samun abin arziki. Wata Hajia takeso akai ɗan kishiyar ta gidan marayu, shine tace ma Jamila idan ta sace yaron zata bata 100k. Duk sauran idan tayi wuta dubu hamsin, harna 20k tana yi. Ita Jamila ta kasance mace mai masifan san kuɗi. Ita marainiya ce sanda take tasowa, babu abinda bazata iya yi ba domin ta samu kuɗi. Idan da ace iyayenta na raye zata iya musanya dasu domin a bata sisi da kwabo. Tunda take a rayuwarta wannan ne karo na farko data fara hangen nesa wajen neman Naira. Wannan karan ne ta kalle abinda zata samu a gaba idan Zubaida ta auri Mahfooz.

Tasan idan maganar kuɗi ne Fauziyya zata bata fiye da abinda zasu samu wajen Mahfooz. Saidai abinda ta sani shine Mahfooz matashi ne kuma ɗan kwallo mai tasowa. Idan ya taki sa'a zai shiga babban kamfani a Turai wanda zasu koma baki ɗaya.

Gagarumin hadari ya haɗu a sararin samaniya, daga nan ruwa marka marka aka rinƙa yi. Hankalin Alhaji Sani yayi mugun tashi harya so ma tunanin su koma Kano tunda basuyi wani nisa da barin garin. Ko Tashan Yari basu kai ba.

Gabansa yanata duka uku uku, saiya rinka lazimi yanata salatin annabi domin samun natsuwa. Ita kuwa Fauziyya kamar ƙara ingiza ta akeyi. Danna accelerator ɗin mota tayi takai ƙarshe tana figan mota. Bata ji bata gani. Maganar nan da bahaushe yace da mai rai akeyi, sam bata damu dashi ba.

Dayake motan Alhaji Sani wanda Al-amin ke tuƙawa shi ke gaba, suma su Jamila sun rage nasu gudun ana tafiya a hankali. Salima tana daga gefe tana chatting da Kankana. Sosai Kankana ke zuba mata shagwaba wai tana kewar ta tareda mata maular dubu goma.

Dariyar mugunta Salima takeyi, sai tace mata kada ta damu tayi tafiya amma tana hanyar dawowa gida. Kuma tazo mata da babban tsaraba. Kankana bata kawo komai cikin ranta ba. Ita duk tsammanin ta za'a kawo mata kimono ko Jakar Aldo ne. Dama ta tura mata wasu jakunkuna data gani a Instagram wai irinsa takeso. Bata taɓa tsammanin za'a kai mata asalin mahaifinta bane a matsayin tsaraba.

Anan ta bukaci Rumasa'u akan ta tura mata hotunan da zasu kwantar mata da hankali. Aikam nan ta cire rigar datake sanye dashi watau T-shirt, saita ta kuma ɓalle rigar mamanta ta lanƙwasa jiki tana zaro harshe tayi hoto tareda tura ma Salima.

Mai ya kai idon Jamila sai taga Salima tana kallon Kankana tumbur tana murmushi.

“Anji kunya,” tace tareda kauda fuska tana tsaki.

“Bansan iskanci, jibe yanda kikayi kamar kinga mugun abu.”

“Mugun abu ne mana. Da tsufan ki kina ajiye farka, haba Salima ki tuba mana.”

“Ah Lallai! Ba laifin ki bane. Ni ce danazo taimaka maki akan ki cinma burin ki. Shine kike ganin nawa burin kamar abin banza. Amma banida wani buri yanzu kamar na mallake Rumasa'u.”

Kallon ikon Allah Jamila tayi, mamaki kalar nisan datayi takeyi. Wai fah mace ke kaunar mace yar uwanta koko dai idanta ke mata ciwo. Saida ta buɗe taga ta tsidda yawu saboda kazantan abin cikin ranta. A garin haka ne sai Fauziyya ta hangesu data zo wucewa.

Batayi wata wata ba sai ta bangaje su da motarta. Nan sunata tangal tangal gashi titi yayi santsi sai suka antaya daji. Haka sukayi ta shiga ciki suna rapka ihu kala kala. Banda direba da Sadiya babu wanda yake yin salati.

Ita kuma Fauziyya tana ganin haka saita tsaya tana taren numfashi, akwai ɓarawon hanya ta wajen inda mutun zai bi ba sai yaje U-turn ba, nan tabi ta koma gida kafin wani daga gidan ya ankara da ita.

su Alhaji Sani wanda suna kallon su Salima ta rear mirror suma suka tsaya. Haka cikin tashin hankali suka koma baya. Wannan abu ba ƙaramin tashin hankali ya jawo mashi ba. Cikin ruwan duka suka fito. Al-amin shima yayi bala'in rudewa, sun saba da Sadiya sosai duk da ba kansu ɗaya ba. Yana yawan zuwa Kaduna wajenta harya kwana wata sa'in.

Haka ya fantsama dokan daji yana salati, da ruwan dayake dukansa amma baya ko damuwa. Kuka kawai yakeyi yana rokan Allah ya raya mashi yar uwan sa. A idansa yaga motan ta soma ƙundunbala har sau biyu. Sai yaga abu ya fita daga tagar gaba. Jaririya Hassana ce ta fita tayi daji. Nan take ya kara tsandara ihu ya ƙarasa inda ta faɗi. Cikin ikon Allah batayi babban rauni ba, saiya ƙarasa inda motan take domin ya agaza masu. Ga ruwa, ga jaririya hannunsa, ga kuma ƙofa yanaso ya buɗe domin su samu su fito. Tunda motar ta kife. Haka yake kallon jini yana malala ma Sadiya ta hanci duk ta fita hayacinta.

Da kyar ya samu ya balla kofan saiya fito da ita, lokacin ruwan ya tsagaita saiya ajiye Hassana a gefe. Sannan ya zaro Sadiya ya kwantar da ita gefe. Ita kam Hussaina babu abinda ya sameta.

A lokacin su Alhaji Sani da Mijin Aisha tareda ita sun isa wajen. Haka suka taimaka aka fito dasu Salima, Jamila da direba wanda duk sun galabaita. Salima ne take numfashi kaɗan kaɗan kuma idanta a buɗe. Ita kam Jamila tayi dogon suma rai yana hannun Allah. Wayan Salima yana hannunta wanda take kallon tsiraicin Kankana dashi. Aisha ce take kokarin cire wa daga hannunta inda taga hoton ƙanwarta amma wanda bata sani ba. Da sauri ta ajiye shi gefe.

An kwashe su an mayar dasu garin kano a jeep ɗin Alhaji Sani. Sai sauran suka bi sahun su a motan tumatir wanda zashi garin Kano daga kauyen dake gefe.

Jamila wanda tafi samun rauni itace ta soma motsi, idanta yana buɗewa kaɗan sannan ya rufe. Ta karya bayanta tareda kanta sosai. Alhaji Sani yana kallonta yasan cewa mutuwa ce take bakunta ta. Saboda yana kusa da mahaifin sa sanda ya rasu. Anan yayi ta kokarin yayi mata kalimatus shahada amma bata amsawa.

“Darbuzu! Darbuzu!! Darbuzu!!!” tayita nanatawa saboda shine bokan data aminta dashi. Shine wanda bata iya saɓa abinda yace. Boka Darbuzu yafi shekara ashirin yana buga ma Jamila ƙarya. Ya kasance har mutane tana kwasa daga Kaduna zuwa Lokoja domin su amfana daga ƙaryan dayake rero masu. A yau kuma tana neman ceto daga Allah amma bata samu daman halin nan ba.

Jamila ta kasance cikin dana sanin daga abubuwan datayi a duniya. A yanzu ta sauko daga dokin ƙarfen data hau. Saidai lokaci ya ƙure mata. Sunan Allah wanda take bukata yanzu ta faɗi a bakinta saita nema kanta da kasa furta sunan. Darbuzu wanda ta mayar uwa da uwa tareda shirka dominsa ta iya ambato a bakin ta.

A hanyar zuwa asibiti ana kokarin ko zata kama kalma daya wuce Darbuzu, amma shi take nanatawa. Har Alif, ba'un Al-amin dake tuƙi ya faɗi amma bata samu hasken iya furtawa ba. Ga wani raɗaɗi dayake bin duk ilahirin jikinta. Wannan kawai yasa hawaye yana sharara daga ƙwayar idanta. Ana cikin haka ne har Allah ya amsa abinsa tareda boka Darbuzu a bakinta.

Motan da Fauziyya ta fita dashi cikin ikon Allah bai wani bugu ba. Tunda dama itace ta buge su, kawai lanƙwasa kaɗan ne wanda ba abin tashin hankali bane. Babu wanda zai lura da cewa dashi ta fita.

Tana ban ɗaki tana kwara ma kanta ruwan dumi tareda tunanin abinda ya wakana ranar, komai yazo mata duka a hargitse. Na farko zancen da Sadiya tace akan ganin Mahfooz a raye, gashi kuma wai su Salima da Jamila sunzo da nasu zancen.

Tana cikin tunani saita tuna cewa Sadiya tace zata shiga motan su Salima domin ta hutar da mijinta. Haka ta ɗaura towel ta fito da sauri ta fara daukar waya. Cikin rudewa tayi abu gashi kila zai dawo mata. Tsoro ta soma ji kada ya kasance cewa Sadiya tana cikin motan sanda abin ya faru. Balle ramin mugunta ance gina shi gajere.

Halima Sadiya ta kasance sunan mahaifiyar Fauziyya. Kuma ko Fauziyya bata faɗi a fili ba tasan gangancin ta yaja mutuwar Zanira. Gashi kuma yanzu cikin wani gangancin zata sake rasa Sadiya. Abin dayafi mata takaici shine yan biyu wanda Sadiya ta haifa, sun shigan mata rai fiye da sauran jikokin ta. Sannan duk a zancen Mahfooz ne haka yake faruwa, da Sadiya bata zo faɗin ta gansa ba, ai bazata kasance cikin motan sanda Fauziyya zatayi maganin su Jamila.

Haka tayita kiran wayar su Al-amin dana Alhaji Sani duka baya shiga. Anan hankalinta yayita mugun tashi, tabbas duk Mahfooz ne sila. Da bai shigo rayuwar ta ba da duk wannan abin bai faru ba. Da bata sanshi ba da bazata fara tunanin neman yaro namiji ba, da Zanira bazata mutu ba. Yanzu kuma Sadiya da yaranta bata san wani hali suke ciki ba. Farko da karshe duka silar Mahfooz ne. Wani baƙin ciki taji sosai har saida jiri ya soma ɗibanta.

“Wannan karan dole saina tabbatar da zaman ka a cikin kabari Mahfooz dan wajen Abubakar.” ta furta a fili.

Wannan kenan!


#Naseera
#Rumasau
#Mahfooz
#Tauraruwa
#MijinTauraruwa
#DiyarDrAbdallah
#Dimpilicious
#FullyDimplated


Ainakatiti 💫

Continue Reading

You'll Also Like

7K 465 25
Yoongi is a ruthless Mafia who disguise himself as a college student in his college (his college means he's the fucking owner of the college) for an...
OBSESSED By thisbejaja

Mystery / Thriller

96K 4.1K 26
obsessed
525K 21.1K 89
Join the ride full of possessiveness, love,hate,pain,happiness,joy,rudeness.
Peer E Kamil By storybyaina

Mystery / Thriller

30.5K 382 22
salar sikandar & imama he waits 9 years for her bad boy become religious for a girl by = umera ahmed