DIYAR DR ABDALLAH

By Aynarh_dimples

44.4K 6.3K 1.1K

Zuciyar sa yana mashi wasiwasi, abinda yake gudu shi ke shirin faruwa dashi. Bai taɓa samun kansa cikin wanna... More

One - Kankana
Two- Ruwan Sama
Three - Ummata
Four - IPhone
Five - Annoba
Six - Wanene Mahfooz I
Seven - Mahfooz II
Eight - Mahfooz III
Nine - Mabuɗin Zuciya
Ten - Kallon Kallo
Eleven - Farin Wasa
Twelve - Mugun Mafarki
Thirteen- Permanent Stalker
Fourteen - Rarrafen Carpet
Fifteen - Ƙarfi Yaci
Sixteen - Bazan Barki Ba
Seventeen
Eighteen - Ni Ce Asalin Diyar Dr Abdallah
Nineteen - Naga Wajen zama
Twenty - Mijin Tauraruwa
Twenty-one - Annihilation
Twenty-two - Pound Of Flesh
Twenty-three - Ribar Haƙuri
Twenty-four Bazan Barka Ba
Twenty-five - Love That Hurts
Twenty-six -Rendezvous
Twenty Seven- Idan Tayi Ruwa Rijiya
Twenty-eight - To Be Tainted
Thirty - Sun Shuka Sun Girbe
Thirty-one- Miscreant
Thirty-Two - Déjà-vu

Twenty-nine - By Whatever Means Necessary

1.4K 227 47
By Aynarh_dimples

Mayar da hankalinta tayi akan laptop ɗin ba tareda ta ƙarasa maganar da zatayi ba. Shima ya lura da rashin dacewar maganar. Daga nan bai sake cewa komai ba. Suna cikin kallo basu wuce mintuna goma sha biyar ba sai aka tura ƙofa. A tare suka ɗaga idansu suka kalle ƙofa, lokacin Baba Abu ne ya shigo da basket wanda ke ɗauke da abinci.

Da sauri Labib ya miƙe yaje domin ya taimaka masa, shi kuma magana ya somayi, “Ah ah Doctor ! Kaine tafe? Ai bamu san zaka shigo dubamu ba.”

“Dama ina kusa da wajen ne, nace bari nazo na duba lafiyar mai jiki.” Yayi mashi ƙarya.
“Allah sarki mun gode, nima tun safe ban shigo ba sai yanzu.”
“Sannu da zuwa,” Naseera tace cikin ladabi.

Kallonta Baba Abu yayi yana murmushi, “Yauwa ya jikin ki?”
“Alhamdulillahi, dan Allah yaushe zan tafi?” tace cikin shagwaba tana sosa kanta.

Kallon Labib sukayi su biyu da Baba Abu, shi kuma sai ya soma tunani. Daga bisani kuma yayi ajiyar zuciya, “Bari muga zuwa juma'a mai zuwa idan komai ya tafi daidai sai a sallame ku in sha Allah,”

Ƙarara Naseera ta nuna farin cikin ta, saboda ta fara takura da Labib. Kawai haka kurum tafi ganin dacewar barinta asibitin. Gwara ta koma gida tayi rainon cikin ta, itama likita ce kuma idan taga akwai wani matsala da kanta zata koma.

Likitan dake duty ya shigo dubata, anan sukayi musabaha da Labib suka sake tattauna ciwon Naseera. Shi a nashi tunanin ko ranar zata iya tafiya domin komai yana tafiya daidai. Labib ne ya nace yace case ɗinta daban ne saboda HIV ɗin.

Tare suka fita da Dr ɗin inda Labib yayi masu sallama ya tafi. Shi Baba Abu bai kawo komai cikin ransa ba, yana alaƙanta kirkin Labib akan ƙabila da suke ɗaya watau na Hausa.

Ranar an kai gaisuwan Fa'iza, inda aka saka bikinta nanda wata uku. Inna taso ace Rumasa'u tana wajen amma ko ranar da safe bata ɗauki wayar ba. Ita kwata kwata ta riga ta yanke wani alaƙa dasu. Ranar Salima ta ziyarci Rumasa'u, a ranar Rumasa'u kwata kwata bata sakan mata fuska ba.

Ita a lokacin abin ya fita kanta, ta lura Salima mugun yar rainin wayo ne yanzu. Banda 5k ko abinci daga bakery babu abinda yake haɗasu. Ko makon daya wuce tace mata ta bata dubu hamsin tanaso tayi photoshot na nishaɗi.

Bata so mutane suce tunda tayi aure ba'a ga haskenta a social media ba, ita kuma Salima ta hanata. Shine itama Rumasa'u ta hanata kanta. Da Salima ta riƙo hannunta saita fizge a wayance. Abin yayi mugun bama Salima takaici. Babu arziki ta ɗauki jakarta ta tafi. Gashi yanzu duka yan matan ta bata fiye kulasu ba tafi san Kankana.

Abin yayi mugun ma Kankana daɗi, idan zasu rinka haka tana ganin zata gwada zuwa wajen Mahfooz taga ko zata haukace, ta soma lura cewa kamar Salima karya takeyi. Saidai bataso ta gwada kuma ace abin da gaske ne tabi duniya. Amma ta soma ma kanta faɗa kaɗan, tana auren namiji da matan duniya zasu je wajen boka ko malam domin su mallake shi, ita kuma ta same shi cikin ruwan sanyi.

Ranar da yamma tayi wanke wanke, saita tafasa macaroni zasu ci da miya, saida ta gama ta lura babu kayan miya tun sanda Mahfooz ya wanke fridge bai sake siya ba. Dabara ya faɗo mata, anan ta soya manja sai suci macaroni garau garau da manja. Haka ta saka a cooler, sai manjan cikin ƙaramin cooler. Sai ta kai dinning ta ajiye, daga nan taje tayi wanka. Dama tun ranar batayi wanka ba, sai ta saka riga da skirt na material.

Torquoise blue ne da lilac, ɗinkin akwai peplum sannan da beads a design ɗin. Ɗaurin turban tayi tareda fese jikinta da turaruka. Ranar tana neman sulhu da Mahfooz. Haka tayi ta zama tana jiran sa ya dawo amma bai dawo ba. Ganin gidan yakeyi kamar kurkuku, yasa baya san zama ciki.

Haka Kankana tayita zaman jiran sa tun mangariba har Isha, dama bawai sallah ya dameta bane balle taje tayi. Shikam gogan bai koma ba sai wajen goma da rabi. Tayi gyangyaɗi harta soma barci kaɗan kaɗan sai taji shigan sa cikin gidan.

Yana shiga cikin falon sallama yayi kamar kowane musulmi na kwarai sai ya nufa hanyar ɗakinsa. Tun randa tace mashi ɗan wahala ya dawo daga rakiyar ta. Yana mugun jin haushinta, duk wani bege ko ɓurɓushin soyayya dayake tunanin da yana mata yanzu babu shi cikin jikinsa. Salap yaji yake ci kamar ruwan rijiya.

“My husband ka dawo?” tace tareda tashi tsaye.

Yi yayi kamar baiji ba saboda duk me take neman sa dashi yau bazata samu ba. Shi ya riga ya ɗauki kaddarar sa. Da sauri ta karasa inda yake tana magana, “My Husband tun ɗazu nake jiranka, har girki nayi maka,”

Cak ya tsaya yana mamakin abinda yaji. Saiya kalleta yana ta tunani, daga nan ya kalle gefen wajen dinning area. Kuloli ya gani jere wanda ya gasgata mashi abinda yaji.

"Da gaske nayi maka abinci my husband, zo muje.” saita janye mashi hannu suka nufa wajen. Bai hanata ba ya bita domin ya gani. Haka ta matsar masa da kujera domin ya zauna. Duk abinda takeyi mamaki yakeyi saboda bai taɓa samun wannan daga gareta ba.

Macaroni ta soma zuba mashi cikin plate, fari ne ba'a yi mashi wani kauɗi ba. Ba abin azo a gani bane amma wanda zai hau sama ya hau leda ai yayi kokari. Data ɗauko kwanon miyan mamaki yayi yanda bai soma jin kamshi ba, saidai yayi hak'uri yaga kila sai an zuba zai ji. Anan yaga ikon Allah, manja yaga yana saka mashi akan macaroni.

"Keh meye haka?” yace cikin takaici.

“My husband wallahi ina cikin aikin ne na lura babu kayan miya, shine nace bari nayi mana garau garau,” tace tana washe mashi haƙora.

Tsaki yaja saiya miƙe tsaye, saiya tafi ɗakinsa. Binsa tayi amma ya rufe a fuskanta. Anan ta tsaya sororo tana mamakin zafin daya keyi akan abinda bai taka kara ya karya ba. Yasa kwata kwata bata san mashi abin arziki, namiji ba ɗan goyo bane kuma ta ɗauki alwashin bazata taɓa mashi girki ba.

Haka ya rufe ƙofar ɗakinsa saiya zaune a bakin wajen. Ɗakin akwai duhu wanda ya kashe fitilar kafin ya fita kuma bai kunna yanzu ba. Nan ya rakuɓe yanata tunani, sai wayansa ya soma ruri. Daga aljihun rigar sa ya fito dashi, anan yaga wannan number dinne. Tsaki yayi saiya ajiye gefe yana ajiyar zuciya. Zuciyar sa yayi mashi baƙi kamar ɗakin dayake ciki.

Anan yana cikin tunani saiya mirgina ya soma barci, wajen ɗayan dare saiya soma mafarki. Wannan mugun mafarkin nasa ya somayi wanda yake ganin kamar ana shaƙe mashi numfashi. Da sauri ya farka yana salati ga zufa yana ƙaryo mashi. Rabon dayayi wannan mafarki tun ranar da ya kusan kashe Naseera a rugar su Musa.

Kankana idanta biyu lokacin tana chatting da yan One Love amma tayi burus dashi. Yana jin tana burutun ta fito shan ruwa. Abin yayi mashi mugun ciwo, amma ba wannan bane damuwar sa. Yanzu dawowar wanna bakar ciwon yake cin masa tuwo a ƙwarya. Haka ya kunna wutan ɗakin guda biyu na duka bangon. Sannan ya kunna recharageble lantern domin yaga haske. Amma yana rufe ido saiya buɗe, wani firgici da ruɗani yake mamaye shi.

Haka yayita rawar ɗari yana kwance akan sallaya, duk wanda yaga Mahfooz a wannan lokacin dole ya tausaya mashi. Baiyi barci ranar ba kuma bai bar firgita ba har asuba. Da kyar ya tashi ya iya zuwa bayi domin yayi alwala. Da kyar yake tafiya wanda ya hanashi zuwa Masjid. Ranar a ɗaki yayi sallah abinda bai saba ba. Duk runtsi duk ruwa yana kokarin yaje masallaci.

Salima da Nurse Jamila ranar bayan Asuba suka tasa driver ya tuƙa su suka nufa hanyar Kano. Ranar komai zai fito, ita Jamila batasan cewa akwai tsohuwar kiyayya da Fauziyya da Mahfooz ba, kawai zata je ne domin ta tada hankalin Rumasa'u tareda iyalan Dr Abdallah. Duk wani halarci da sukayi mata ta watsar a kwandan shara. Ta riga ta ɗauki alwashin sai Zubaida ta shiga gidan Mahfooz.

Koda isan su Kano kai tsaye gidan Alhaji Sani suka wuce dake Rijiyar zaki. Gidan ya canza masu saboda anyi sabon fenti tas, yanzu ruwan ganye ne da kuma ruwan hoda. Gashi ya watsa interlocking concrete tiles a ƙasan tsakar gidan. Sannan ya canza gate daga mai turawa manually zuwa electric. A bakin ƙofa sukayi ma Fauziyya waya domin tayi masu iso.

Bata kawo komai ranta ba dama Salima ce tayi kiran, da ace tasan da Jamila bazata yarda su shigan mata gida ba. Haka mai gadi ya buɗe masu ƙofa, Mallam Musa ɗan garin Maraɗi ne yake masu gadi.

Jamila tayi mamakin irin dalan da Fauziyya ke ciki, shine dan raini take aika mata dubu biyar. Manyan Italian furnitures farare tas sukayi maraba dashi a falon. Saiga Fauziyya sanye da Swiss lace kalar toka wanda akayi doguwan riga dashi. Kamar yadda ta saba zobunan gwal ne hannayenta, guda shida uku uku na hugu da dama.

Alhaji Sani wanda ya sake manyanta, yanada yanzu jikoki goma sha biyar yake zaune akan 3 seater. Sadiya ƴarsa wanda take aure a Kaduna itama tana falon tana zaune, a hannunta yarta ne hussaina yar kwana arba'in da biyu. Hassana kuma tana hannun Alhaji. Sadiya itace yaya ga Zanira wanda ta rasu. Ta girma Mahfooz da Shekara uku, mijinta shine APC chairman na Kaduna North Yanzu. Shekarar ta biyar da aure kuma tanada yara uku, kafin yan biyu ta haifa Aslam.

“Wallahi nace maku naga Mahfooz a Kaduna, ta wajen NNDC mall, zai shiga motarsa ni kuma ina daga ciki,” Sadiya tace cikin damuwa.

“Ke bamu san shiririta, Mahfooz daya daɗe da mutuwa shine zaki kawo mana zancen shi,” Fauziyya tace a hasalce.

“Wallahi Mommy na ganshi, Haba sai kace jahila. Ina ss3 ya ɓace fah...”

“Dalla rufe mana baki, wai muna zaman zaman mu zaki kawo mana zancen matsiyaci. Wato abinda ya kawo ki kenan? Kizo ki hargitsa min gidana?”

“Haba Mommy, kanina ne fah... Kuma kina tunanin da Zanira tanada rai zata ji daɗin yadda muka watsar dashi....”

“Wai bazaki min shiru ba ne bakar munafuka... Haba jimin yar tselan uwa. Kin wani nace kinga Mahfooz. Toh qaqa ?”

“Mommy naga dai ba wani abu zai tare maki ba, kawai dai zumun...”

“Wallahi zan fasa maki baki Sadiya,” Fauziyya ta dakatar da ita tana hayagaga. “Abinda ya baro dake kenan daga Kaduna dan gulma, yasa kona je Kaduna bana zuwa wajen ki. Mugun halin ki takaici yake bani. Ko kiyi min shiru ko yanzu na fige ki har titi na nakaɗa maki duka, shegiya kawai annamimiya,” tace tana nuna ma Sadiya yatsa.

Shi kuma Alhaji Sani yana zaune baice komai ba yana jin su, abinda ya sani shine anjima zai samu Sadiya tayi mashi bayanin sosai gameda Mahfooz. Tabbas yaci amanar yan uwantaka. Kuma sau da dama idan yaje Zaria ana wadai dashi akan abinda sukayi ma Mahfooz. A daidai lokacin Salima da Jamila sukayi sallama, nan take fuskan Fauziyya ya canza. Bata amsa sallamar ba ta soma masifa.

“Yaya ne! Me ya kawo ki gidana?” Fauziyya tace tana kallon Jamila. Anan take tasha jinin jikinta gameda Jamila. Ita kuma dayake yar bariki ce saita watsa mata murmushi mai laushi. Samun kujera tayi kafin ta soma magana.

“Karki damu Fauziyya, zakiji meya kawo ni.” Saita Kalle Alhaji Sani, “Ina wuni Alhaji?”

Cikin Fara'a ya amsa, “Lafiya lau, Sannun ku da zuwa,”

Sai Salima ta gaida shi shima, sannan Sadiya ta gaida su. Dayake Jamila tana zaune gefen Sadiya saita miƙa hannu domin a bata Hussaina, “Jibe yanda ta girma," tace tana murmushi. Saita soma dube dube.

“Ina Al-amin?”

“Wai menene Jamila kika zo min gidana, banfa da kyau. Wallahi babu riba faɗa da aljani,” tace tareda miƙewa tsaye.

“Meye haka ?” Alhaji Sani yace tareda kafa mata ido. Haka ta zauna tana huci.

“Jamila duk me kike so zanyi, na rantse zan rinka ɗaukar wayanki.”

“Anty Jamila wai Lafiya tun shigowar ki Mommy ta susuce?” Sadiya tayi tambaya cikin mamaki.

“Ina ruwan ki munafuka, kuɗi take bina,”

“Anya Mommy akwai wanda yakai kici bashin sa kuwa?”

“Karki damu Sadiya, ni Al-amin nake so yazo akwai wani magana da zamuyi dashi da Alhaji.”

“Al-amin yana China, yaje duba kayan Daddy.”

“Lafiya dai koh?” Alhaji Sani ya tambayeta.

Duk abinda akeyi Salima batace komai ba, tana zaune tana kallon drama. Banda harara babu abinda Fauziyya ke watsa mata saboda itace ta kawo mata Jamila cikin gidanta. Gashi yanzu ance anga Mahfooz, ga Jamila kuma da nata. Gaba rafi baya maciji. Gyara zama Jamila tayi zata soma magana.

“Nace maki kiyi haƙuri Jamila.” Fauziyya ta sake maimaitawa.

“Kiyi mana shiru nace,” Alhaji Sani yace da babban murya.

Daidai lokacin Aisha babban yarinyar Fauziyya ta shigo tareda mijinta. Aisha tana aure a nan Kano a Sharaɗa Phase 2. Mijinta regional manager ne a banki, tanada yara huɗu dashi. Aliyu, Ahmad, Anisa da Ajwad. Autan shekarar sa biyar. Lahadi ne yasa mijin baije aiki ba, shine zasuyi ziyara gidajen yan uwa wanda suke kusa.

“Salamu alaikum,” suka ce, “Lah su Anty Salima ne a gari,” Aisha tace cikin fara'a.

Zufa ya sake ƙaryo ma Fauziyya, ga mutane kuma za'a yi mata tonan silili. Abin yayi mugun bama Jamila farin ciki. Saita soma magana.

“Alhaji Sani dama ina so ka gafarce ni, na kasance mai laifi babba wajenka...”

Gwalagwalan wuyan Fauziyya dana hannunta ta ciro da sauri ta watsa jikin Jamila, tana haki cikin tashin hankali ta duƙa gabanta tana roƙon ta, “Kiyiwa Allah zan baki abinda yafi wannan.”

Tsaye Alhaji Sani ya miƙe yana zare ido, saiya soma nuna ma Fauziyya hannu, "Koma me kikayi yau sai gaskiya ya fito, idan bazaki iya yin mana shiru ba gwara ki fita.”

Haka tayi zugum zaune a ƙasa duk ta ruɗe. Tasan yau zata bala'in ɗanɗana koɗanta. Jamila ta sake watsa mata lallausar murmushi saita kalle Alhaji Sani wanda yana kokarin zama.

“Dama shekaru ashirin da hudu daya wuce, lokacin Fauziyya tace min duk yanda zanyi nasan yadda zan samo mata yaro namiji. Saboda tana ɗauke da juna biyu, idan ta haifa ɗa namiji shikenan. Idan kuma bata haifa ba saina bata yaron dana sato. Na kasance ina aiki a asibiti yasa abin zai min sauki.”

Ajiyar zuciya tayi ta kalle duka yan ɗakin, kowa yayi shiru yana mamakin abinda ke wakana. Ita kuma Fauziyya hawaye ta soma yi. Tashin hankali ta shiga sosai. Rayuwar data gina zai rushe.

“Tunda aka ɗauko Mahfooz yaron Abubakar kaninka Alhaji, wallahi tana mugun kishi da Mahfooz. Gani takeyi batada yaro namiji kuma idan ya girma zai gaje ka a kasuwa. Shine ta ɗauki alwashin saita haifa nata yaron kota halin qaqa.”

“Ikon Allah....” Aisha tace cikin mamaki.

“Shine lokacin haihuwar ta tace zata Abuja biki amma Kaduna tazo wajena. Bayan ta haifa yarinyarta mace sai tace na samo mata yaro namiji wanda zamuyi musanya dashi.”

“Ina yarinyar yanzu?” Alhaji Sani ya faɗa ransa a ɓaci.

“Tana Kaduna har tayi aure, itace asalin yarinyar Fauziyya. Al-amin da yake zaune anan shi ne yaron Dr Abdallah Kwarbai.”

“Wallahi ƙarya ne! Wallahi ƙarya ne!! Wallahi Ƙarya ne!!!” ta rinƙa nanatawa. A hankali har ta soma ihu, side table dake gefe ta ɗauka ta rotsa tsakiyar falo. Nan hankalin kowa ya tashi, duk suka tsorata suna ja da baya.



Wannan kenan!


#Naseera
#Rumasau
#Mahfooz
#Tauraruwa
#MijinTauraruwa
#DiyarDrAbdallah
#Dimpilicious
#FullyDimplated





Ainakatiti 💫



Continue Reading

You'll Also Like

46.6K 1.4K 80
"𝐻𝑎𝑛𝑠𝑒𝑜𝑘𝑎𝑎,𝑎 ℎ𝑒𝑎𝑟𝑡𝑙𝑒𝑠𝑠 𝑝𝑠𝑦𝑐ℎ𝑜𝑝𝑎𝑡ℎ 𝑙𝑖𝑘𝑒 𝑦𝑜𝑢 𝑑𝑜𝑒𝑠𝑛'𝑡 𝑑𝑒𝑠𝑒𝑟𝑣𝑒 𝑡𝑜 𝑓𝑒𝑒𝑙 𝑙𝑜𝑣𝑒 𝑤𝑖𝑡ℎ 𝑠𝑜𝑚𝑒𝑜𝑛�...
11K 514 26
MAFIA STEP - SISTER OF BANGPINK
62.5K 1.6K 10
مافيا - حب - قسوه - غيره renad231_5 مرت سنه والقلب ذابحهه الهجر ومرت سنه والهجر عيا يستحي الروايه موجوده في انستا : renad2315
103K 3.5K 40
Y/N was a teenage introvert who enjoyed having her own space and being alone. She loved listening to music in her room, which was a great escape for...