DIYAR DR ABDALLAH

Aynarh_dimples által

44.4K 6.3K 1.1K

Zuciyar sa yana mashi wasiwasi, abinda yake gudu shi ke shirin faruwa dashi. Bai taɓa samun kansa cikin wanna... Több

One - Kankana
Two- Ruwan Sama
Three - Ummata
Four - IPhone
Five - Annoba
Six - Wanene Mahfooz I
Seven - Mahfooz II
Eight - Mahfooz III
Nine - Mabuɗin Zuciya
Ten - Kallon Kallo
Eleven - Farin Wasa
Twelve - Mugun Mafarki
Thirteen- Permanent Stalker
Fourteen - Rarrafen Carpet
Fifteen - Ƙarfi Yaci
Sixteen - Bazan Barki Ba
Seventeen
Eighteen - Ni Ce Asalin Diyar Dr Abdallah
Nineteen - Naga Wajen zama
Twenty - Mijin Tauraruwa
Twenty-one - Annihilation
Twenty-two - Pound Of Flesh
Twenty-three - Ribar Haƙuri
Twenty-four Bazan Barka Ba
Twenty-five - Love That Hurts
Twenty-six -Rendezvous
Twenty-eight - To Be Tainted
Twenty-nine - By Whatever Means Necessary
Thirty - Sun Shuka Sun Girbe
Thirty-one- Miscreant
Thirty-Two - Déjà-vu

Twenty Seven- Idan Tayi Ruwa Rijiya

1.1K 171 39
Aynarh_dimples által


Ontario, Canada

“Dr, the patient is breathing,” head nurse na cikin surgery ɗin ta faɗa da harshen turanci. A lokacin Labib ya dawo hayacinsa ya ƙarasa wajen da sauri. Jini ya daina fitowa saiya goge wanda yake wajen. Daga nan kuma komai yayi mashi sauƙi ya rufe mata kai tareda ɗinkewa.

Labib Mohammad Kakaki yanada dakarkiyan zuciya, ba kasafai abu yake razanar dashi ba cikin tiyata. Amma a karo na farko ɗaukewan numfashin Naseera ya girgiza shi. Idan yasan baza'a ci nasara a tiyata ba kokuma mutum yanada 30% chance of success, yana sanar da yan uwansa domin kada a tuhume shi. Wasu dayawa suna cewa ayi ɗin a gani rahamar Allah dayawa yake, kuma cikin ikon Allah Labib yana samun nasara kaɗan ne ba'a yi.

Surgery ɗin Naseera yayi kusan awa biyar anayi, Hajia Binti batada aiki sai kiran Baba Abu da Anty Jawahir domin taji yadda ake ciki. Tsoro takeyi sosai kada ta rasa Naseera. Gashi abu na karshe daya faru shine sanda ta wanka ma Naseera mari. Sanda ta kira na karshe lokacin ana fito da Naseera daga tiyata. Anan Anty Jawahir ta kunna bidiyo domin Umma taga Naseera. Taji daɗi sosai tagan ta kwance tana barci abinta babu firgici. Bayan Hajia Binti ta yanke wayan saida tayi raka'a biyu domin ta gode ma Allah. Tabbas shine abin godiya.

Ranar Mahfooz ya biya kasuwa ya siyo ma kanshi kayan cefane, yana jin cin sakwara da miyan agushi. Bai iyaba, kuma yasan Rumasa'u bazata dafa mashi ba. Sannan kuma ya gaji da zuwa gidan abinci, poundo flour ya siya wanda zai kwaɓa da ruwan zafi kamar teba, sai ya shiga YouTube domin yaga yadda ake girka agushi.

Tiryan tiryan abinsa yayita bin abinda ake cewa harya gama, bai wani daɗi sosai ba saboda ya cika Maggi da kuma manja. Bayan nan saiya wanke kwanonin dayayi amfani dashi tas kamar ba'a shiga ba saiya saka a cooler ya kai dinning. Ita kuma Ruma tana kwance ɗaki kamshi zai kasheta. Musamman yadda Mahfooz yayi amfani da kayan haɗi sosai. Daga kifi busarshiya da ɗanye, sai kuma kayan ciki da ganda. Harta periwinkles duka ya watsa.

Ya tafi bayi domin yayi wanka sai yayi sallah azahar saita fito falon, kamar yadda ta saba fuskanta shaƙe yake da make-up kamar zata biki. Jikinta kuma Atampha ne pink wanda aka watsa duwatsu a wajen wuya da kuma cikinta. Sai tayi ɗaurin turban tana wani fari da ido. Ita a dole yar hutu kuma yar gayu. Tanada kyan da zata janyo hankalin mai kallon ta.

Zama tayi akan dinning tareda ɗaukar kwano ta zuba ma kanta hankali kwance, yadda kasan mai aikinta yayi mata abinci. Shima yayi mugun shan mamaki yadda ya ganta. Anan ya tamke fuska tamau ya soma magana, “Watau dan kin maida ni baho shine ni zan rinka maki abinci koh? Wai Rumasa'u me kika maida nine dan Allah?”

Marairaicewa tayi tareda kane kane da fuska, “Wallahi dama zan shiga kitchen ɗin shine naga ka rigani,”

Tsaki yaja mai uban ƙara saiya janyo kujera shima ya zauna, sannan ya fizge cokalin saka abinci daga hannunta. Haka ya loda ma kansa kifi, kayan ciki, ganda da periwinkle, yanda kasan ya shekara da yunwa jikinsa. Tana kallo sai haɗiye miyau takeyi ta kasa cewa komai. Sannan ya ɗauki sakwara malmala biyu ya ajiye gefensa. Daga nan ya fara ci ko magana da ita baiyi ba. Haushinta yakeyi sosai amma babu abinda zai iya yi akai. Fata kawai yakeyi Allah ya kai masa sanadin rabuwa. Domin kuwa an daɗe ba'a laƙa mashi auri saki ba cikin anguwa.

Salima ta saba zuwa wajen azahar tunda Mahfooz zaman gidansa ya ishe shi, sai tazo su ha'ince shi kafin ya dawo. Yauma haka tazo da box of cupcakes wanda yasha decoration da waffles da oreo a sama. A waje ta ajiye motarta tunda ba dadewa zatayi ba.

Kai tsaye ta shiga cikin falon kamar nata, “Hello darling!” ta faɗa cikin raha. Duk tsammanin ta su kaɗai ne cikin gidan. Anan gaban Rumasa'u yayi mugun faɗi ta zaro ido tareda saka hannu a baki cikin tsoro. Sai kuma cikin tsoro ta soma magana.

“Gwaggo sannu da zuwa,”

A lokacin Salima ta gansa yana kwasan girki akan dinning. Abin yayi mugun bata haushi, sau da dama tana cema Kankana tayi mata girki, saidai ta ɓararraka mata wani kilafitaciyar indomie, wanda ɗanɗanon sa kamar an wanke kan tsohuwa. Ganin yawan naman dake kwanan Mahfooz gashi ma sakwara yake girba yayi mugun bata takaici. Shi kuma cikin ladabi ya rinsina ya gaida ta.

“Ina wuni Gwaggo,”

“Aha..”tace kawai saita soma bin Rumasa'u da mugun kallo.

“Gwaggo muje ɗaki na baki saƙon,”

Haka suka wuce har ɗaki zuciyar ta yana mugun tafasa dan takaici, tunanin yadda zata magance Rumasa'u takeyi domin taji sanyi cikin ranta. Suna shiga Salima ta haska mata mari kyawawa guda biyu. Haka Rumasa'u tana dafe kumatu domin zafi kuma hawaye suka taru cikin idanta

“Munafukan banza! Inace na rabaki dashi? Shine zaki ha'ince ni kina wani kulashi.” saita janyota tareda shaƙeta, “Yar banza harda masa kwalliya koh? Kin mance mena ce maki ne halan?”

Hawaye ne suka ciko idanun Kankana saboda wuya, numfashi ma da kyar takeyi saboda Salima ba ƙaramin chapka takai mata ba. Girgiza kai takeyi alamar a'a tareda nuna mata nadama ƙarara. Sai Salima ta ingiza ta saida ta bige a bango.

“Zamu haɗu,” tace tareda fita. Cupcakes ɗin yana hannunta bata ajiye ba. Duk daukarta Kankana tayi mashi liyafa, balle ta ganta fes fes cikin atampha.

“Sai anjima Gwaggo” Mahfooz yace sanda zata tafi. Bata amsa shiba saboda takaici. Fansa takeso ta ɗauka akan Rumasa'u.

Bayan awa uku da surgery ɗin Naseera, lokacin Labib ya tafi gida domin ya huta. Itama Anty Jawahir taje gida wajen yaranta sai aka bar wajen daga nurses sai Baba Abu. Yana zaune yana karanta magazine ɗin Forbes Naseera ta farka. Batace komai ba ta fara bin ɗakin da kallo tanaso ta gane meke faruwa. Har wajen mintuna goma sha biyar batayi magana ba kuma bata nuna alamar ta tashi ba. Baba Abu ne ya gaji da mujallar saiya kalle gefe wajen tabur ya ajiye, anan yaga hannunta yana motsi. Da azama ya miƙe yaje wajenta.

“Naseera Alhamdulillahi da kika tashi,” yace cikin farin ciki. Anan ta buɗe baki da kyar tayi magana.

“Ruwa.....”
“Me kika ce?” yace tareda riƙe mata hannu a hankali.
“Ruwa... Water,” ta sake faɗi.

Dispenser dake ɗakin yaje ya ɗebo mata ruwa daga ciki, baisan ko yaci ace ta fara ci ko shan wani abu ba. Abinda kawai ya sani shine ruwa rahama ne, kuma ya bata. Kurɓa uku tayi saita cire bakinta domin ta huta. Sai bayan ta huta ta sake kai bakinta domin ta sha. Daidai lokacin Nurse ta shigo cikin ɗakin, anan tace ma Baba Abu ya matsa domin ta duba ta. Tambaya tayi mata na sunanta da inda aka haifeta. Anan ta faɗa amma abinda zata iya tunawa kenan.

“Karka damu, zuwa gobe zata fara tuna sauran abubuwa. Kada a takura mata.” Nurse ɗin ta faɗa da harshen turanci.
“Nagode sosai,” ya amsa.

Daga nan Nurse ta canza mata ledan ruwa tareda kallon kanta da kyau taga ko yana jini, amma bata gani ba. Fita tayi tareda janyo mashi ƙofa ta rufe. Kirar Hajia Binti ne ya shiga tablet ɗin Baba Abu, ita dama duk ta ƙagara tayi magana da Naseera. Da azama ya ɗauka.

“Alhamdulillahi Anty, yanzu ƴata ta farka,” ya faɗa bakinsa har kunne.
“Toh Ma sha Allah masu ƴa, Allah ya ƙara mata lafiya.”
“Amin,” saiya ƙarasa inda gadon Naseera yake ya haska mata wayan a fuskan ta.
Naseera tana ganin Hajia Binti saita ganeta, “Ummaaa,” tace a hankali saita soma hawaye. “Me nakeyi a asibiti? Hope my baby is fine?” Tace tana hawaye. Umma taji daɗi sosai koba komai ciwon mantuwa bai kama Naseera ba kuma sauki ya soma zuwa in sha Allah.

“Dalla wawiya, kukan me kike yi? Shagwaba zaki min Baban ki yana kallon ki duk ki hanashi sukuni balle yaje aiki,” tace cikin barkwanci.

Shima Baba Abu ya ɗan dara, Naseera dai sake taɓe fuska tayi sosai bata ce masu komai ba. Tanaso tasan ko murna zatayi kokuma zata shiga kogin baƙin ciki.

“Umma....”

“Rufe min baki,” Hajia Binti ta dakatar da ita. “Ban san shiririta dan Allah. Bakisan wahalar da mukayi ba domin muga kin farfado, kada kizo kuma ki fara damuwa yanzu mu koma gidan jiya.”

Haɗiye maganar Naseera tayi ranta baiso ba. Tanaso a gaya mata yadda ake ciki amma babu hali. Barira ne ta leƙa cikin camera ɗin tana dariya.

“Babban Hajia bakisan me nayi ba, ai wancan ƙaramar mara kunya tasha mamaki wajena,” tace tana dariya. Naseera bata gane dawa akeyi ba, kawai dai murmushi tayi mata. Haka dai suka cigaba da mata hira kala kala domin su ɗebe mata kewa.

Kashe gari...

Dr Labib baiyi wani barcin kirki ba, abinda ya faru a tiyata da Naseera ya bala'in bashi tsoro. Yaga gangancin sa dayayi aiki cikin azama, shi a nashi tunanin idan yayi da sauri zasu ceto ta. Amma kuma sauri ya haifi nawa. Dole ya rage yin abu cikin sauri, dole kuma ya rage ego ɗinsa.

Cikin taƙama sosai wanda halinsa kenan ya fito daga bayi, sai ya wuce closet ɗinsa ya ɗauki grey suit da riga kalar burberry. Haka ya tsaya gaban madubi wanda aka kafa daga saman ceiling suna ƙasa. Anan ya fesa body spray a hammatan sa da sauran jikinsa, flavour ɗin Lavender Wanda yake amfani dashi a kusan komai. Harta kayansa idan yakai scolar ana saka mashi lavender flavour.

Sai ya naɗa tie a wuyan sa cikin kwarewa, turaren sa na Creed–Green Irish Tweed yasa. Wannan ne tambarin sa duk inda ya shiga, da sanyin turaren mutane ke maraba da zuwan sa cikin hancin su. Bayan ya gama saiya tsafe gemun sa da kuma gashin saman kansa.

Gidan penthouse ne mai ɗakuna biyu, sai wakeken falo mai haɗe da dinning area da kitchen. Haka ya fito daga bedroom ɗinsa wanda yafi girma a cikin ɗakunan ya wuce wajen kitchen, nespresso machine yaje ya kunna tareda saka coffee beans, arabian ne wanda yake siya online daga Beirut.

“Coffee is the most important part of the day,” yake yawan faɗi. Kuma ko bayan ya fito daga surgery saiya sha mai zafi tareda madarar sosai. Shi baya san black coffee kwata kwata. Sannan koda yaushe yana cikin ci crossaint da wiped cream ko syrup. Haka ya gama shan coffee ɗinsa a tsaye a wajen yana kallon weather forecast na ranar. Ance za'a snow sosai, suit jacket ɗinsa baki wanda ya ajiye tareda briefcase ɗinsa ya ɗauko. Sai yaji ana ƙokarin buɗe ƙofar gidan za'a shiga. A miskilce ya kalle ƙofa, dukda yasan wanda zai shiga.

“Morning Labib !”
“Morning Mrs Parker!” ya amsa mata. Mai zuwa gidan ne kwana uku a sati domin ta gyara mashi tsab tareda kai mashi wanki da guga.

“You're late today, what happen?” Tace mashi cikin kulawa, zata iya ɗirga sau nawa take zuwa aiki da safe ta riske shi. Kwata kwata baya latti saidai idan ba asibiti zaije kai tsaye ba. Kallonta yayi tareda murmushi wanda baya nuna haƙora.

“I didn't sleep well,” Yace tareda ajiye kofin a wajen wanke wanke saiya ɗauke jakarsa da jacket.

“I'm off,” ya sake faɗi.

Ita dai Mrs Parker batace komai ba. Kallo ɗaya tayi masa ta gane yana cikin matsanancin damuwa. Saidai bata so ta matsa mashi. Duk faɗin Ontario babu wanda ya sanshi kamarta, shekarar su goma tare. Kuma sun haɗu ne a asibiti sanda zata haifa yaronta Edward, lokacin batada Insurance policy na haihuwa gashi mijinta Mr Parker ya gudu. Labib da kansa ya biya mata kudin gado daga aljihun sa, a lokacin ya koma garin kenan da zama. Tun daga nan suka ƙulla mutunci, kuma ta fara goge mashi gida duk sati. Da farko bata karɓan kuɗin sa amma yace mata idan bazata ɗauka matsayin sana'a ba toh shi baya so. Bayan nan kuma Labib da kansa ya samo mata gida je na maƙotan sa da kuma abokan aikinsa. Daga wannan kuɗin ne take rufawa kanta asiri da yaranta biyu.

A bakin asibiti ya tsaya a wani ƙaramin shago da ake siyarda Coffee. Nan ya siya kofi huɗu. Saiya shiga ciki. Ɗakin farko na wani yaro ne dake da ciwon dariya na rashin dalili, da farko iyayen sa sunyi tunanin halitta ne, sai da yaci karo da wata likita inda tayi masu bayanin cewa akwai abinda ke motsawa a kwakwalwar sa wanda ke taɓa fannin dariya akai kai. Yanzu Labib yayi ma yaron surgery kuma anci sa'a ya soma samun sauki.

“Good Morning Mr Jones!” Labib yace yayinda ya shiga cikin ɗakin, saiya miƙa mashi kofunan shayi biyu. Anan ya ajiye sauran biyun a gefe ya soma duba Eric.

Bayan ɗakin su Eric kai tsaye ya wuce ɗakin da su Naseera yaje. Lokacin Baba Abu baya nan, ya tafi gida domin yayi wanka kuma ya canza kaya. Anty Jawahir take zaune gefen Naseera, bata komai sai dannan wayanta. Yarta Zubaida yar wata hutu tana hannun nanny ɗinta dake gefe.

Dayake Labib yasan ɗakin na musulmai ne, sallama yayi daya tura kofan. Anty Jawahir ne ta ɗago kai ta kalle shi tareda amsawa. Murmushi ƙarara bayyane a fuskan ta tareda mamaki. Batayi tsammanin akwai musulmai kuma Hausawa ba a garin Canada.

“Ina kwana?” Anty Jawahir tace mashi.
“An tashi lafiya? Ya kwanan mai jiki?”
“Lafiya lau,”

Ido yayi ma Nurse ɗinda ke mara mashi baya akan taba ma Anty Jawahir shayin na cikin kofin roba.

“Ga wannan babu yawa,” yace. Saiya miƙa hannunsa domin nurse ta bashi file ɗin Naseera. Anan yayita karanta abinda ke ciki. Daya kai shafin da HIV ɗin yake nan ya tsaya yanata nazari. Mamakin yadda ta kwasa yakeyi. Ita kuma ta farka kenan daga gajeran barcin data keyi.

“Tun yaushe ne ta zama positive?” ya tambaye Anty Jawahir.
Gyada kai tayi ta soma nazari, sai kuma tayi ajiyar zuciya, “Inaga bazai fi wata uku zuwa huɗu ba,”

Naseera buɗe idanu ta somayi a hankali taga wanene yake wannan tambayoyi, ganinsa datayi da labcoat ya tabbatar mata da cewa shine likitan da Baba Abu yayita mata labari akai. Da sauri ta rufe idanta dataga ya kusan waigawa inda take kwance.

“Kamar ta tashi,” yace tareda ƙarasa wajen.

Ita kuma ƙanƙanme idanta tayi gam, zakaga alamar girar ta yana girgiɗi wanda ya tabbatar mashi da cewa da gangan ta rufe. A file ɗinta wajen marital status yaga an saka single. Anan yayi guntun murmushi mai bayyana haƙora.

Kujera ya janyo ya kai wajen fuskanta ya ajiye, saiya zauna tareda harɗe hannun sa akan ƙirjinsa. Bai ce komai ba har kusan sakon talatin kafin ya fara magana.

“Ni sunana Labib Mohammad Kakaki, nine neurosurgeon ɗinda nayi maki aiki akai jiya. Zaki iya tunawa da sunan ki?”

A hankali ta soma buɗe idanta, sai kuma ta rufe da wuri saboda yadda ya kafa mata ido.

“Ina jin ki...”

Ido a rufe ta amsa mashi, “Naseera Abdallah Kwarbai...”
“Kina da aure?”
“Eh......” sai kuma tayi tunani, "A'a banida,”
“Kina karatu ne ko kin gama?”
“Nayi karatu tareda Residency ɗina a Oxford University,” Tace mashi a hankali.
“Wow, ashe kema likita ce...”
“Zaki iya tuna abinda ya faru dake kafin kuka zo?
“Eh”
“Zaki gaya min?”
“No,” saita juyar da fuskanta domin ta kalle gefe.
Murmushi yayi saiya soma magana, “Karki ga inata maki tambaya ne, kema Dr ce kuma kinsan yadda tsarin yake. Inaso na ga ko brain ɗinki yana aiki ta kowane fanni,”

Bata Amsa ba, shine ya gaji da zama saiya miƙe tsaye. Anan yayi ma Anty Jawahir sallama tareda ficewa.

“Banfa san taurin kai,” ya faɗa cikin ransa.

***
Kaduna, Nigeria...

Abin duniya yayi ma Zubaida cinkoso, a gaskiya tanayin ma Mahfooz sona haƙiƙa. Gashi bai san da zamanta ba. Sabon layi ta siya domin ta rinka aika mashi da saƙon barka da safiya. Ita kuma Nurse Jamila ta dawo daga wajen ɗan tsubbun ta kuma yayi mata alkawarin cewa Zubaida zata samu mashinshi ni. Koda Zubaida take gaya mata akan abinda ke damunta cikin zuciyar ta, da farko taji mugun haushi saboda mai mata ne. Amma saita tuna Rumasa'u ba asalin yar Dr Abdallah bace. Dama tana tunanin Naseera ce, amma tunda Rumasa'u ta fito yanzu sai abin ya soma dawo mata sabo fil.

Shekara kusan ashirin da biyar daya wuce, bayan tayi musanya yaron Dr Abdallah zata fita daga Nursery ɗin asibitin. Sai wata baby ta soma kuka kamar ta shaƙe, garin ajiye na hannunta ta gyara babyn, sai kuma ta mance wanda ya kamata ta ɗauka tun asali. Kuma ita tana tunanin tanada yarinyar asali a hannunta, amma tun zuwan Rumasa'u gidan taga tafi yanayi da Fauziyya. Kuma da ace Zanira ta girma kafin ta rasu irin fasalin da zatayi kenan. Saidai wannan Rumasa'u kaɗan ne babu data zama zabiya domin haske. Tar tar take jazur kamar tumatir.

Nurse Jamila taje wajen aminiyarta Hajia Salima neman shawara, saboda dama duk tare suke a Kano suna aminta. Yanzu duk sun dawo Kaduna saura Fauziyya kawai a chan.

Da farko Salima bata wani sauraron labarin saboda tana chatting da sauran yan matan ta. Sai da taji zancen DNA sai ta gane cewa da Rumasa'u akeyi. Anan ta bada duk hankalin ta tanata ji. Tabbas tana tausayin Mahfooz, kuma tana tausaya Zubaida. Cikin ranta ta ayyana cewa idan ta haɗasu aure da Rumasa'u ba ƙaramin daɗi zataji ba. Na farko zata rama abinda Rumasa'u take kokarin mata sai kuma na biyu idan sukayi aure zata fi samun lokaci tareda kulawar Kankana. Watau idan tayi ruwa rijiya, idan batayi ba masai. Domin ita bata damu ba koda ɗaukar nauyin bikin zata iya.

Wannan kenan !

#Naseera
#Rumasau
#Mahfooz
#Tauraruwa
#MijinTauraruwa
#DiyarDrAbdallah
#Dimpilicious
#FullyDimplated


Ainakatiti 💫

Olvasás folytatása

You'll Also Like

12.9K 2K 22
جۆنگ کوک:بە نەفرەت بیت وازم لێ بێنە چیت لە من دەوێت تایهیۆنگ:ششـ ئازیزم بۆچی هاوار دەکەی ئارام بە بۆ باروودۆخت خراپە ༄༄༄༄༄༄༄ جۆنگ کوک:تـ تۆ چیت کرد ت...
90.2K 3.3K 55
After his first year at the Advanced Nurturing High School, Fukazawa Yato is about to start his second year as a student. With a better understanding...
11K 731 37
Jeon Jungkook, he completed his graduation in business. he is sweet but for only his family and cold for other's. he doing internship in his father'...
62.5K 1.6K 10
مافيا - حب - قسوه - غيره renad231_5 مرت سنه والقلب ذابحهه الهجر ومرت سنه والهجر عيا يستحي الروايه موجوده في انستا : renad2315