DIYAR DR ABDALLAH

By Aynarh_dimples

44.3K 6.3K 1.1K

Zuciyar sa yana mashi wasiwasi, abinda yake gudu shi ke shirin faruwa dashi. Bai taɓa samun kansa cikin wanna... More

One - Kankana
Two- Ruwan Sama
Three - Ummata
Four - IPhone
Five - Annoba
Six - Wanene Mahfooz I
Seven - Mahfooz II
Eight - Mahfooz III
Nine - Mabuɗin Zuciya
Ten - Kallon Kallo
Eleven - Farin Wasa
Twelve - Mugun Mafarki
Thirteen- Permanent Stalker
Fourteen - Rarrafen Carpet
Fifteen - Ƙarfi Yaci
Sixteen - Bazan Barki Ba
Seventeen
Eighteen - Ni Ce Asalin Diyar Dr Abdallah
Nineteen - Naga Wajen zama
Twenty - Mijin Tauraruwa
Twenty-one - Annihilation
Twenty-two - Pound Of Flesh
Twenty-four Bazan Barka Ba
Twenty-five - Love That Hurts
Twenty-six -Rendezvous
Twenty Seven- Idan Tayi Ruwa Rijiya
Twenty-eight - To Be Tainted
Twenty-nine - By Whatever Means Necessary
Thirty - Sun Shuka Sun Girbe
Thirty-one- Miscreant
Thirty-Two - Déjà-vu

Twenty-three - Ribar Haƙuri

1.1K 183 29
By Aynarh_dimples

Da sauri Naseera tabar falon, kwata kwata bazata iya jure cin fuskan da Mahfooz yake yi ba. Farad ɗaya ya canza kamar maƙiyarsa ya maida ta. A chan ƙuryan ɗakin ta zauna a ƙasa, irin zaman dirshan kamar zatayi bori. Mamaki takeyi yadda komai ya juye farad ɗaya, masoyinta ya zama maƙiyin ta cikin ƙanƙanin lokaci. Sallar la'asar taji ana kira. Jiki babu ƙwari ta miƙe ta wuce bayi domin tayi alwala. Allah ne gatan ta, kuma bata cire ran zai fitar da ita daga cikin wannan uƙuba ba. Duk runtsi tana nan zata cigaba da addu'a, wata rana kuma zai zama labari. Tasan cewa Allah baya ɗaura ma bawa abinda bazai iya ɗauka ba. Hakan ya nuna tanada ƙarfin daukar wannan kaddaran ne. Balle ma a Q94 vs 05 Allah yace Fa'inna ma'al usri yusra. Wannan kawai yana saka zuciyarta yayi mata wani irin sanyi mai daɗi. Dole akwai ribar haƙuri, koda kuma ba yanzu bane.

An tsaida bikin Rumasa'u da Mahfooz nanda kwana huɗu, daga Amarya har ango fuskansu ƙarara da murmushi. Hajia Fatu taso tayi mashi magana akan ya daina rawar kai haka. Abin da kunya yace baya san yarinya ɗaya sannan ya nuna yana san ɗayan, abin kamar dama tuntuni haka yaso yayi. Faisal shikuma yana mota yana jiran Hajia Fatu ta fito domin su tafi, dama su uku suka je a motan. Anan Faash ya tafi yabar Mahfooz wanda yana tareda Rumasa'u tana mashi rawar kai.

Shi kuma Mahfooz yana ƙoƙarin ya saisaita zuciyar sa domin yaso Rumasa'u. Yarinyar tanada kyau, yar gayu ce amma kuma tanada bala'in rawar kai. Saidai kuma rawar kai ba abu bane dazai saka aƙi auren mace. Idan tana sanshi wanda yanada tabbacin haka, yasan zata yarda ya koya mata yadda yakeso so su tafiyar da rayuwar su. Zata kuma maye mashi duk wani ɓurɓushin soyayya dake tsakanin shi da Naseera. Murna sosai yakeyi ya tsallake rijiya da ƙafar baya.

Ita kuma Rumasa'u sarai tasan Mahfooz baya santa, tasan cewa Naseera ta fita komai. Bawai tana nufin ta kyan fuska da kyan jiki ba, idan wannan ne Naseera bata kai rabin ta ba. Tana nufin kyan zuciya, natsuwa da sanin ya kamata. Tana kishi da Naseera sosai akan wannan abubuwa, ita koda ta tursasa zuciyar ta domin tayi bazata iya ba. Duk abinda bai jiɓanci samun kuɗi ba batada juriyar yinsa.

Mahfooz ya kashe kuɗi sosai saboda bikin nan, yanaso yaga duk me Tauraruwa takeso ta samu babu ƙaranci. Amma yanzu komai ya koma kan Rumasa'u wanda tafi da cewa dashi. Shi yasan tabbas zaiji daɗin auren nan, koba komai Rumasa'u tafi sanshi kuma zatayi mashi biyayya ainun.

“My love zaka bani kuɗin lalle, sai kuma na saloon za'a min full spa. Zanyi maka list anjima na bridal shower...” ta soma gaya mashi. Wannan kawai ya bambanta ta da Naseera, da itace idan bai kawo shawara ba bazata taɓa tambaya ba. Sai kuma wani zuciyar ta raya mashi dama duk salon yaudara ce. A duniyar nan ina zakaga mace mai kunya da rashin san kuɗi? Duk tanayi ne domin ta yaudare shi harya aminta da ita.

“Muje Havilla musha ice cream My love,” ta sake faɗi. Kallonta yayi yana nazarin irin zaman da zasuyi. Tanada bala'in surutu kamar ta haɗiye radio. Amma kuma saiya tuna cewa shedan ke mashi wasiwasi akan yaga aibunta. Duk makircin Naseera ne. Wanda kuma ba'a ko'ina ta gada ba illa wajen mahaifiyarta Fauziyya. Allah wadai yayi da su biyun cikin zuciyar sa, tabbas sunada shika shikan rashin imani. Jin daɗin sa ya ƙubuta yanzu, zai aure yarinya mai usuli asalin yar Dr Abdallah.

“Babu mota a hannuna, ki bari zan maki aike anjima.” Yace tareda miƙewa tsaye. Har gate ta raka shi tana rangaji kamar reshen bishiya. Mahfooz Qwaro zai zama angon ta, gashi itace yar Dr Abdallah, what more could she ask for?

Napep ya hau ya wuce gida, koda ya isa Daddyn Faash ya sake kiransa ɗaki domin su zanta. Yace masa kada yayi saurin yanke hukunce cikin fushi. Ya kamata ya duba lamarin nan sosai. Aure ba abin wasa bane, kuma bai kamata ana saki kara zube ba. Ba tursasa masa yakeyi ba, duk abinda yake so shi za'a yi masa, kawai yanaso yayi amfani da hankali ne wajen komai. Ƙeƙeshe idanu yayi yace yaji ya gani. Tunda sukeda Mahfooz basu taɓa ganin yayi kafiya kamar wannan ba, bai taɓa yin abu wanda yasan zai kawo masu tozarci ba. Komai nashi yana ƙokarin ya faranta masu ne. Sai Mahaifin Faash yayi mashi uzuri. Ya lura Naseera ta ɓata mashi rai sosai, anan yayi mashi fatan alheri tareda addu'a akan aurensa.

Antiretroviral treatment watau ARV ɗinta ke hannunta tana kallo, tunda gari ya waye take fama da matsanancin ciwon kai. Dayake HIV yana saka fever Idan baka shan magani akai akai yasa bata taɓa wasa dashi ba. Amma ciwon sai gaba yakeyi. Barira ta shigo tareda faranti, faten Acha ne wanda yasha yakuwa, zogale, da gyada. Abin cin da Naseera tafi so kenan, kuma duk ɓacin ranta idan tagani tana ci. Tun kafin akai kusa da ita ta soma jin zuciyar ta yana tashi, amma bata kawo komai ranta ba. Murmushi sukayi ma juna, tana san Barira sona haƙiƙa. Kamar babban yaya ta ɗauketa, idan kaga yadda Barira ke saka kayan alfarma kamar ba ita bace mai aiki.

“Gashi nayi maki aminiyar ki ci.... Bana so ki cigaba da takura kanki. Komai mai wucewa ne.”

“Uhmm,” ta amsa dashi saita karɓa. Loman farko takai bakinta amma ta kasa haɗiye wa. Da sauri ta miƙa ma Barira kwanan saita wuce bayi. Kakarin amai tayi tareda zubar dana bakinta. Duk zuciyar ta ya tashi. Tunda take bata taɓa shiga wannan yanayi ba saboda fate.

Bayan ta gama saita ɗauraye fuskanta ta fito, kallonta Barira tayi tana nazari. Taso tayi wani magana sai ta fasa. Naseera ce tayi magana, “Menene?"

Sai da Barira tayi dogon ajiyar zuciya, “Dama wani mugun tunani ne ya faɗo min,”

“Name kenan?”

“Wai koh... Koh kinada shigar ciki ne... Kwana biyu na lura kin soma cika, sannan kuma ga wannan.” Saita ƙura ma Naseera ido. Itama kallonta tayi sai kuma ta bushe da dariya.

“Wai ciki!!!” sai ta wuce wajen mirror ta zauna. Kallon kanta itama tayi tana tunanin, tabbas taga kirjinta ya soma cika. Amma tana tunanin dan tana cikin kwanciyar hankali da walwala ne. Wayanta dake gefe yana chargi ta ɗauko. Sai ta shiga manhajan mai taya mutum ɗirgen kwanakin al'ada. Anan taga tayi latti kwana biyar ga danja yana nuna mata. Da lokacin datake tareda Mahfooz ne taji wannan labarin, murna zatayi. Amma yanzu kuma kamar an aiko mata da saƙon mutuwa. Da wanne zata ji, da HIV, ko Zawarci kokuma rainon yaro? Barira tagama zamanta shiru cikin ɗakin basu sake magana ba, saita tashi ta fita.

Ranar gaba ɗaya Naseera ta wuni cikin ɗaki tana fargaba, batasan yadda zatayi da wannan sabon yanayi data tsinta kanta ba. Wajen daren sanda ta tabbata Mahfooz yana gida sai tayi mashi text message akan ya kirata tanaso suyi magana. Wannan karan ne abin farko daya taɓa buɗewa. Anan yayi tsaki saiya kashe wayansa tareda kwantawa abinsa.

Batayi wani barcin kirki ba, ga zazzabi datake fama dashi wanda da chan tanata dannewa saboda tasha HIV dinne. Bayan asuba taje ɗakin Barira, bayan sun gaisa saita gargaɗeta akan kada ta gayama kowa abinda take tunani. Idan Mahfooz zai dawo mata tanaso ya dawo domin kansa ne ba tareda an tilasta mashi ba. Yasa takeso ta gaya mashi shi kaɗai ga abinda ake ciki, idan Dr Abdallah ko wani yasan tanada shigar ciki za'a fasa auren da Rumasa'u ace dole su zauna su biyu kuma bata san haka. Tanaso duk me zaiyi ya zamanto abinda yake so. Bazata taɓa daina kare shi ba. Saboda haka so ya jibanta.

Ranar ta wuni tana mashi text amma yayi banza da ita. Yan lefe sun kawo kuma an tarbe su cikin mutunci. Rumasa'u ta gayyace wasu gogaggun ƙawayenta suka zo anata suwa ana iya shege. Kwata kwata basuda kintsi sai shewa suke yi. Hajia Binti tace ma Rumasa'u dole ta gayyace su Inna tarban lefen. Tayi mata ƙarya wai Inna bata garin, duk saboda bataso dangin Mahfooz suga wanda suka raine ta su raina ta.

Har ranar ya ƙare Naseera bata samu damar ta gayama kowa abinda yake faruwa ba, bataso taga laifin Mahfooz. Kuma tasan yana cikin fushi ne, idan auren Rumasa'u zai kawo mashi sauƙi akan abinda yake cikin ransa ita bata damu ba. Shi takeso cikin kowane hali, shi takeso ya zama uban yaranta. Shi takeso ya zama garkuwa gareta. Kuma tanaso ya zo su raina babyn su tare.

Ana gobe ɗaurin auren, Rumasa'u tasha kunshi da gyaran gashi. Da gangan Mahfooz yaje gidan domin ya bama Naseera haushi. A falo aka sauke shi sai iya yi Rumasa'u takeyi. Anan Naseera ta yanke shawara tanaso tayi mashi magana. Hijab kalar zuma ta saka saita sauka ƙasa. Ganinsa datayi saida zuciyar ta ya harba. Haƙiƙa idan tace zata haƙura dashi ba ƙaramin tashin hankali zata shiga ba. Siririn hawaye ya soma malalo mata, sai tayi amfani da haɓan hijab ɗin domin ta goge. Sallama tayi mashi amma yayi ƙememe. Saima ya riƙo hannun Rumasa'u yana matsawa.

“We need to talk,” tace a sanyaye.

Kallon Rumasa'u yayi wanda ranta yayi mugun ɓaci ganin Naseera kusa da shi. Saiya soma magana cikin shagwaba.

“Baby kice mata bana san nayi mata magana har muddin rayuwa na,”

“Dan Allah, it's important.” ta sake cewa. Sai a lokacin ya ɗago ya kalle ta. Kallon raini kuma yabita dashi.

“Banida alaƙa dake, kuma banga dalilin dayasa zan saurare ki ba.”

“Dalla malama ki tafi ki bamu waje, ana dole ne?” Kankana tace a hasalce.

“Mahfooz ina....” Bata ƙarasa zancen ba saiga Hajia Binti taje wajen ta finciko ta.

“Ke mara hankalin ina ne? Koko shi kaɗai ne Autan maza? Idan baya sanki sai mène? Ai mu muna sanki kuma Allah yana sanki. Wallahi kika sake zuwa wajensa saina saɓa maki.” Saita janyeta domin su wuce. Ashe duk abinda akeyi tana daga dinning area tana gani kuma kamar ta nakaɗa ma Naseera duka.

Duk da haka Naseera bata haƙura ba, data koma ɗaki saita tura mashi saƙo kuma.
“Mahfooz inada shigan ciki. Call me”

Lokacin wayan yana hannun Rumasa'u suna selfie, saita karanta. Nan take tayi deleting kafin ya gani. Tasan kuma muddin Naseera tanada number ɗin Mahfooz dole suyi magana. Anan dabara ya faɗo mata, kukan karya ta soma rusawa.

“Wallahi bazan aure ka ba, bari Dr ya dawo nace na fasa,” tace tana kuka.

“Me akayi maki kuma, bansan shiririta.” Yace cikin takaici. Baiso ita kuma ta soma haɗa ma kanshi zafi. Yanada abubuwa dake damunsa cikin ransa.

“Ya za'a yi tsohuwar matar ka tayi tunanin cewa zata rinka maka magana koda yaushe. Me kuka maida ni? Wallahi na fasa.”

Tunani ya somayi, haƙiƙanin gaskiya yana buƙatar Rumasa'u domin aurenta kawai zai musguna ma Naseera. Dole yayi duk abinda takeso kafin ta guje shi.

“Indai kana so na yarda dole ka canza sim card dinka, duk wani hanyar sadarwa kuma ka yanke da ita. Nasan ta da bala'in karya zata iya yaudarar ka,"

Nan take ya fito da sim card ɗinsa ya ɓalla.

“Happy?” yace mata. Amma ranshi bai soba. Rumasa'u is demanding, kuma baya tsammanin zai iya jure abubuwan da zata rinƙa yi. Itama ta lura yana buƙatar ta, yasa zataci karenta babu babbaka. Shi kam yasan zai wahala a aurenta. But it's a sacrifice he's willing to make.

Wannan kenan!

#Naseera
#Rumasau
#Mahfooz
#DiyarDrAbdallah
#Dimpilicious
#FullyDimplated

Ainakatiti 💫

Continue Reading

You'll Also Like

177K 2.8K 9
❝ fate. a word meaning destiny. fate. a word meaning doom. ❞ [ a f4 thailand fanfic ] [ thyme paramaa x fem!oc ] [ currently being rewritten ] © 𝐬𝐭...
10.3K 241 21
"yeah, everything we broke and all the trouble that we made, but i say i hate you with a smile on my face" ...
2.1M 87.9K 93
•UNDER EDITING• Abhimanyu Chowdhary-A mysterious 28 years old man. CEO of Chowdary group of companies. He has looks that every girl craves and go cra...
50.5K 6.5K 71
"Se refiere a la belleza de corta duración de la flor de cerezo" ╰──➢ Advertencias ✧ ⁞ ❏. Omegaverse < SLOW BURN ⁞ ❏. Todoroki Bottom! ⁞ ❏. Smu...