DIYAR DR ABDALLAH

By Aynarh_dimples

44.3K 6.3K 1.1K

Zuciyar sa yana mashi wasiwasi, abinda yake gudu shi ke shirin faruwa dashi. Bai taɓa samun kansa cikin wanna... More

One - Kankana
Two- Ruwan Sama
Three - Ummata
Four - IPhone
Five - Annoba
Six - Wanene Mahfooz I
Seven - Mahfooz II
Eight - Mahfooz III
Nine - Mabuɗin Zuciya
Ten - Kallon Kallo
Eleven - Farin Wasa
Twelve - Mugun Mafarki
Thirteen- Permanent Stalker
Fourteen - Rarrafen Carpet
Fifteen - Ƙarfi Yaci
Sixteen - Bazan Barki Ba
Seventeen
Eighteen - Ni Ce Asalin Diyar Dr Abdallah
Nineteen - Naga Wajen zama
Twenty-one - Annihilation
Twenty-two - Pound Of Flesh
Twenty-three - Ribar Haƙuri
Twenty-four Bazan Barka Ba
Twenty-five - Love That Hurts
Twenty-six -Rendezvous
Twenty Seven- Idan Tayi Ruwa Rijiya
Twenty-eight - To Be Tainted
Twenty-nine - By Whatever Means Necessary
Thirty - Sun Shuka Sun Girbe
Thirty-one- Miscreant
Thirty-Two - Déjà-vu

Twenty - Mijin Tauraruwa

1.2K 183 23
By Aynarh_dimples

Alhamdulillahi, yar uwa kuma ƙanwata FA'IZA ADAM BARWA ta samu ƙaruwa yau. Allah ya albarkace ta da samun yarinya kyakkyawa irin ta. Allah ya raya mata ita cikin addinin musulunci. Also, my other Musketeer LUBNA SUFYAN ta gama littafin ta Abdulqadir yau. Allah ya sanya alheri, ya bamu ikon amfani da darusan da ke ciki. You know I love you.... Blah blah blah abeg don't stress me.

A hargitse ta shiga gidan Hajia Salima. Ko sallama batayi ba ta faɗa, ba ita kaɗai ta gani cikin falon ba. Su biyu ne da wata aminiyarta zaune suna shan kayan marmari. Zuwa tayi ta riƙo ma Hajia Salima hannu tana haki, “Hajia dan Allah ki taimaka min, rayuwa na zai salwanta...”

"Ki bari zamuyi magana anjima, yanzu inada baƙuwa.” Hajia Salima tace fuska a tamke. Ita bata so yadda Rumasa'u ta shigo ba babu sallama. Saboda yanzu a ɓoye take harkan ta, gashi yadda Rumasa'u tayi dole a gane akwai wani alaƙa tsakanin su.

“Hajia na rantse duk me kika ce nayi zanyi maki, ki taimaka min naci wanna yaƙin.” tace tana kuka.

“Nace ki tafi zamuyi magana anjima," ta daka ma Rumasa'u tsawa.

“Amma kin yi asara Salima, har yau baki bar wannan mugun ɗabi'an ba. Haba kinada yara da jikoki ace kina wannan shiririta.” ƙawar Hajia Salima tace tareda zabga tsaki. Kallon gefen Kankana tayi inda ta kalle matar. Tafi Hajia Salima kyau da gogewa nesa ba kusa ba. Asalin yar gayu ce, wani daham ta maƙala a wuya na gwal ga kuma zabbai a yatsun ta. Sannan ga danƙareren Leshi a jikinta wanda yasha stones. Ɗinkin bou bou ke jikinta kuma ya amshe ta. Suna haɗa ido ta zabga ma Rumasa'u harara. Da sauri Rumasa'u ta sunkuyar da kanta ƙasa.

“Fauziyya kenan! Babu ruwan ki da harka ta. Kinzo gidana kar kiyi min girman kanki da kika saba.... Ehe!” saita yarfa hannunta a iska. Kana ta juya ta kalle Rumasa'u, “Ehen my dear, me kike cewa ne?"

Anan Rumasa'u ta zayyana mata abinda takeso ayi, a canza DNA ace da nata yayi matching. Tasani har cikin ranta Dr Abdallah shine mahaifinta amma gwara ta shirya koda maƙiya zasu ce ba daidai bane. Shafa mata fuska Hajia Salima tayi tana dariya, anan ta bata haƙurin tafiyan su. Tace abubuwa ne suka bullo amma nanda mako mai zuwa zasu dubai.

“Har yanzu Latisha bata dawo daga baby shower ɗin bane daga Maldives?" Rumasa'u ta tambaye ta. Dariya Hajia Salima ta ƙyalƙyale dashi har tana sarƙewa.

“Wai ce maku tayi Maldives ta tafi?” saita cigaba da dariya tana tafa hannayenta, “Latisha yar ruɗu. Karya takeyi babu inda taje. Uban wa zai kaita Turai? Shegiya mai warin ƙashi. Yar banza kwanaki taci ma wasu hajiyoyi kuɗi sai da tayi kwanan cell...”sai ta sake bushewa da dariya.

“Wai dama yar talaka ce? Ni fah ce min tayi Mike Adenuga abokin Babanta ne, kuma rabin kamfanin Glo nata ne,” Rumasa'u tace cikin mamaki. Harɗe fuska Hajia Salima tayi tana hararar Rumasa'u. Banda jahilci a ina zakaga yaran Mike Adenuga, ita haushi ma taji kwanaki Latisha ta ara motan ta duk ta bar mata wari cikin sa.

Wayan Hajia Fauziyya ya soma ruri, cikin taƙama da ƙasaita ta ɗauka. Kana ganin yadda ta harɗe gira kasan ita ba abokiyar yinka bane. Samsun S10 ne ta fito dashi, “Son, ina jinka!” tace tanayi tana ƙarƙaɗa ƙafa. Anan Rumasa'u ta sake baki tayita kallonta. Matar ta burgeta, chas chas abinta. Sai Fauziyya ta tsaida wayan da takeyi ta kalle Rumasa'u.

“Ke juyar da fuskan ki, kuma kike sake kallo na saina ci bura ubanki. Ni ba yar harkan ku bane. Da aure na kuma har jikoki gareni. Na rantse na sake kama ki kina kallona, koni ko ke saboda sai an zubda jini...”

“Haba Fauziyya! Me tayi maki kike cin mata fuska?”

“Yo banda iskanci shegiya kamar ƙanzo, ta wani kafa min ido. Ubanki zan maki... Nace ubanki zan maki???”

“Wallahi Hajia irin ɗinkin ki nakeso nayi,” Rumasa'u tace bakinta yana rawa. Tunda take bata taɓa haɗuwa da wanda ya fita bala'i ba. Gashi kuma ta kasa rama wa. Koda yake wannan ba irin wanda za'a yi hayaniya dasu bane a kwana lafiya.

“Fauziyya sarkin bala'i, kinji irin ɗinkin zatayi.” Salima tace tana dariya, “Karki damu zan ɗinka maki irin shi,” ta kalle Rumasa'u ta fada mata. Ita kam Fauziyya harara ta watsa masu, saita ɗauki grapes ta soma ci, kana ta cigaba da wayanta.

“Son, kace har yanzu jikin baban naku babu sauƙi.....” Fauziyya wayanta tayi na kusan rabin awa, idan sun haɗa ido da Rumasa'u ta zabga mata harara. Tsanar yarinyar ya dirar mata kamar an soka mata kibiya a kirji. Ita kuma Salima tace kada Rumasa'u ta damu. Duk me takeso za'a yi mata. Ƙara gargaɗinta tayi akan samari barkatai. Saita bata dubu biyar ta hau mashin. Ta gode mata sosai saita tashi ta tafi, taso tayi ma Fauziyya sallama amma ta watsa mata harara. Da sauri tayi hanyar ƙofa ta fita.

“Yar banza kawai! Ko uban me ta rasa da take biye maki oho!” Fauziyya tace. Dariya Salima tayi sosai bata ce komai ba, wannan ba matsalar ta bane. Anan suka canza maganar suka cigaba da hirarrakin su na aminai. Hajia Salima tayi zaman Kano kafin ta dawo Kaduna kuma makwabta ne.

Rumasa'u kai tsaya Abdallah Specialist ta wuce, anan tayi masu bayani akan abinda Dr Abdallah yace. Dama tun kafin ta isa yayi masu waya yace wata zata je ga abinda yakeso ayi mata. Bata isa gida ba sai wajen ƙarfe biyu na rana. Koda takai wajen wayam babu kowa. Mota yazo ya kwashe kayan su Inna sun tashi. Makwabta Rumasa'u ta shiga tana tambaya inda suka je.

mamaki ya kamasu, kawai dai suka amsa da sun koma gidansu mana. Koko ta mance ne. Ita harga Allah bata san da maganar tashi ba, saita tambaya gidansu a wani gari. Duk tsammanin ta tana ganin kamar haya suka kasa biya an koresu kauye yanzu zasu chan Zaria gidan gado.

Fauziyya dama biki ya kawo ta Kaduna, tana zaune saita tuna da yar uwanta Auta. Anan ta tuna abinda tayi mata lokacin haihuwan Al-amin. Koda yake ta saba shiga Kaduna, amma tanada hidima. Wannan karan ne dinner sai wajen bakwai na yamma. Sai tace ma Salima tana zuwa, direba tasa ya kaita chan gidan datake tsammani Auta take zama. Koda ta shiga bata ga kowa ba.

Haka ta tambaye wani yaro dayake wasa bakin gidan, nan aka ce ai an siyar da gidan kuma Mallam Salisu sun tashi. Tambayar sa tayi ko gidan kansu suka koma. Tana so taji ko Auta ta goge ko tana nan a matsiyaciyar data sani. Yaron yace bai sani ba, Saboda shi dai yasan Malam yana koyarwa a firamari.

Daga wannan kawai Fauziyya ta tabbatar da cewa Auta tana cikin talauci, abin kuma yayi mata daɗi sosai. Nan tayi mata fatan ta dulmiya cikinsa tunda ta sanya mata leshi da Atampha, balle akan zancen har mijinta Alhaji Sani yayi hushi da ita lokacin, kiris da aurenta ya mutu. Zata shiga motar ta kenan saiga Kankana ta fito daga makota jikinta a sanyaye. Kwata kwata batada tudun dafawa. Ga ƙawar Hajia Salima wanda bata ƙaunar ta balle tace zata gidan ta kwana, gasu Inna sun tashi sun barta. Bawai ma taso ta bisu bane. Sannan Dr Abdallah baya so ya karɓe ta.

Gaban Kankana ne yayi mugun faɗi, da sauri ta juya zata koma inda ta fito. Daka mata tsawa Fauziyya tayi yasa ta tsaya, “Dan ubanki ina zaki? Yar banza kawai ! Zo nan? Shegiya jibeta kamar ƙanzo sai warin talauci.”

Gwiwa babu ƙarfi Rumasa'u taje, harara Fauziyya tayita binta dashi kafin tayi tsaki, “Dan ubanki maimakon ki kama talaucin ki, ki rufawa iyayen ki asiri a'a kina chan kina bin Hajiyoyi saboda badala. Chan ne gidan ku?” ta kalle inda Rumasa'u tafito. Ita ta ɗauki alwashin saita kai ƙarar ta wajen iyayenta. Yarinyar ƙarama ce har tasan daɗin kuɗi tana bin Hajiyoyi.

“A'a wallahi,” Rumasa'u tace bakinta yana rawa. Duk ta muzanta.

Tsaki Fauziyya tayi sai ta kalle gidan su Auta, “Kinsan wanda ta tashi a gidan nan? Yar uwata ce nazo kuma ban gansu ba,” tace tana yatsina fuska kamar tanajin warin kashi.

Mamaki Rumasa'u tayi, indai wannan sun haɗa jini toh asirinta ya tonu dan bazata rufa mata ba. Sai kuma tayi tunanin cewa yanzu ita yar Dr Abdallah ce. Anan hankalinta yayi bala'in kwanciya. Da kai ta amsata alamar a'a. Harara Fauziyya ta sake watsa mata saita shiga mota inda direba ya tuƙa suka tafi.

Ranar Mahfooz yace ma Naseera su fita domin ya siyan mata waya, taji abin babu daɗi. Bata saba karɓan kuɗin samari ba, sai kuma ta tuna mijinta ne. Fesa wanka tayi tareda kwalliya, ta mance yaushe rabon data saka wani abu a fuskanta. Amma yau eyelashes ne kawai bata saka ba. Smoky eyes tayi Wanda ya fito da dara daran idanta, sai kuma bakinta nude ne wanda yasha contour. Ita ma tasan tayi kyau. Lifaya yellow tasa da baƙin riga. Sai ta saka baƙin kallabi tareda ɗaukar clutch ɗin Micheal Kors.

Koda ta fito, haka ya sake baki yana kallonta. Faran mace hasken lantarki. Yanda yakeyi har tsarguwa ta soma yi, shima ɗin yayi kyau. Baƙin kaya ya saka da baƙin hula.

“Tauraruwa.” yace mata ta ƙasan leɓansa.

“Mijin Tauraruwa.” itama ta amsa mashi suna murmushi. Sunan yayi mashi daɗi sosai. Haka yayita nanatawa cikin ranshi. Mangal Plaza suka je, anan suka dauke waya. IPhone 11 ya ɗauko masu tace bataso, kashe kuɗin yayi yawa. Dama ita wayanta bamai tsada bace. IPhone 7 ne, bata tsufa fah bataga dalilin canza waya duk shekara ba. Haka suka ɗauka Huawei kala ɗaya, bambamci shine ta bayan waya. Duk ta muzanta, taso ta miƙa atm ɗinta domin a cire a nata. Amma ya hanata. Yace shine mijinta kuma duk wani nauyi nata ya dawo kansa. Godiya sosai tayi mashi tana shi mashi da albarka tareda mashi fatan kariya daga maƙiya.

Abin yayi masa daɗi, bai taɓa tunanin yan mata suna ma samari irin addu'an ba. Shi banda "Thanks" ana yauƙi kamar ba'a so a faɗa baya jin komai daga bakin yan mata. Sai kuma ya tuna wannan matarsa ce, gashi ta fita daban daga cikin sauran mata. Santa ya sake bin duk ilahirin jikinsa, har wani shan kamshi yakeyi. Balle da suka fita mota kowa yana kallon su yana murmushi.

Sunyi welcome back sai suka karɓa Number ɗin juna, yana kallonta ta gefen ido yaga me zata saka mashi, anan yaji daɗi sosai data saka mijin Tauraruwa. Girgiza kai yayi harda naushi iska yana dariya, wai shi Mahfooz wanda ba ɗan kowa ba ake so haka. Da sauri ya sanya Tauraruwa a nashi wayan. Yaso tazo suje gidansu Faash amma tace babu girma a ciki. Ya bari idan an kaita, duk da akwai aure tsakanin su muddin ba'a kaita gidanta ba, bazata iya binsa ko'ina ba yanzu. Mutuncin ta zai zube. Shi baiga laifin abin ba amma ya kyaleta. Dama da safe Mommyn Faash take tambayar sa labarin Naseera kuma ya take.

Sundai sha selfie kala kala a snapchat da camera, sannan sunyi video a tiktok. Kamar yan shekara sha bakwai suke jin kansu. Ba ɗan shekara talatin da ɗaya ba da yar shekara ashirin da huɗu. Basu dai wallafa hotunan ba, Saboda Mahfooz yanada bala'in kishi. Ko lifayan data saka yanaso ya gargaɗeta karta sake sawa idan zasu fita. Saidai idan su biyu ne.

Babu arziki Rumasa'u ta kira Inna domin taji inda suke, duk ta gaji da gantali tana so ta samu inuwa ta huta. Wayan yana gefen Aliyu, aikam ya saka a silent. Haka wayan yayi bugun duniya Inna bata ɗauka ba. Anan Rumasa'u ta soma kuka, wai har su Inna da basuda ko sisi sun soma juya mata baya. Ita kuma Inna tana zuba ido ko zataga wayan Rumasa'u domin tayi mata kwatance. Dama bata so su tafi ba sai Rumasa'u ta dawo, Mallam yace ya riga yayi ma direba magana. Dole su tafi, sai Inna tace to ko Fa'iza zata zauna ta jira Rumasa'u. Mallam ya sake faɗin ai Rumasa'u tanada waya idan tana bukatar su zata neme su.

Haka ta hau mashin taje gidan Dr Abdallah kai tsaye, ko zasu kasheta ne sai dai suyi. Amma ita batada wajen zuwa sai gidan. Hajia Binti ta soma arba da Rumasa'u tana tafiya kamar mahaukaciya, saiga barewa yazo gefenta. Anan zata hamɓerashi da ƙafar ta tana mashi masifa.

Falo ta riske Dr Abdallah yana zaune, saita fashe da kuka. Anan tayi mashi bayanin su Inna sun gudu sun barta. Bai yarda da zancen ba tace wallahi yaje layinsu domin a tambaya. Direba aka tura yaje layin, kuma yayi tambayoyi, an san Rumasa'u kuma ansan Malam. Sannan kuma aka ce yau suka tashi. Taji daɗin yanda abin ya faru haka. Dr Abdallah mutum ne mai tausayi sosai. Bai tashi a arziki ba. Yasan wahalar daya sha kafin Allah ya ɗaga shi.

Tausayin Rumasa'u yayi, shi haka Allah ya saka mashi tausayin talaka da mutunta su. Sabida ba ikon sa bane yasa yakeda arziki. Idan Allah yaso yau zai juya masa lamarin sa ya koma akan abinda yake kyama. Ikon Allah kala kala ne, yasa duk inda yaga zai iya sai ya bama wanda basu dashi. Dama ɗaki huɗu ne a sama ɗaki biyu a ƙasa. Sai yace ma Barira takai Rumasa'u ɗakin ƙasa inda zata zauna kafin aga iyayenta. Saboda harga Allah yasan babu yadda za ayi ta zama ƴarsa.

Ƙiƙam ta tsaya kamar an dasa ta, ita gaskiya bazata iya zaman ɗaki a ƙasa ba. Ta riga ta soma tunanin yadda rayuwar ta zai kasance. Da safe zata fito balcony sanye da nightgown tabi fuskan ta da mask ɗin Spa, tana shan iska rana yana haska jikinta. Sak yadda tagani a film sai kuma ace ta zauna a ƙasa. Watau tayi makwabtaka da Barira mai aiki kenan? Sam bazai yiwu a ba mai kaza kai ba.

“Kizo muje mana!” Barira ta daka mata tsawa. “Malama ni aiki nakeyi!”

Haka Rumasa'u tayita kallon bene batace komai ba, kana gani kasan nan takeso ta hau. Barira ta sake daka mata tsawa, “Meye kike kallon sama? Nan kike tsammanin za'a kaiki? Dalla zo mu wuce!” sai tayi tsaki. Shikam Dr Abdallah barin wajen yayi ya wuce sama, yasan Hajia Binti tace bazata zauna gida ɗaya da ita ba. Ta roƙe shi alfarma dan Allah koda yarsu ce ita ta yafe, tana so a murɗe results ɗin ace basu santa ba. Har kuka tayi tana roƙon sa bata so ta zauna da Rumasa'u.

Sanda ya shiga cikin turakar Hajia Binti tana hawaye, da sauri tayi maza ta goge sai ta miƙe zata shiga bayi. Anan ya dakatar da ita. Yanaso ya bata haƙuri, yasan tayi bala'in shaƙuwa da Naseera. Kuma yasan da wuya wata ta maye mata gurbi.

“Ko tausayin abinda Naseera zata ji bakayi! Kawai wata tazo ka amshe ta.” Tace tana kuka. Bayani yayi mata akan abinda yasa Rumasa'u ta zauna, kafin aga iyayenta. Hajia Binti tace mashi ya gargaɗeta akan ta fita harkan ta, sannan ta fita harkan Naseera. Idan ba haka ba ranta zai ɓaci sosai.

Saiya roƙe Hajia Binti ta bata abaya ɗaya da Atampha ɗaya tunda kayan Naseera bazasu shige taba. Ranta baiso ba amma tunda Dr Abdallah ya tambaye ta yasa ta kasa mashi musu. Haka tasa Barira takai mata. Lokacin Rumasa'u tana ɗakin da aka kaita, kallonsa tayi tana kwatantawa dana Naseera data shiga ɗazu. Koba a faɗa mata ba tasan wancan yafi girma, bata damu ba. Tunda dai yanzu ta shiga gidan, a hankali zata fidda Naseera. Ko tana so ko bata so. Koda boka koda Mallam.

Bayi ɗaya zasuyi amfani da Barira, kuma ta gargaɗeta akan kazanta. Tace mata wallahi zasu kwashi yan kallo idan aka bata mata bayi. Saboda tafi so taga waje kyal kyal kamar zata ci abinci a ciki. Ran Kankana yayi mugun ɓaci, kuma ta ɗauki alwashin napep ɗaya Barira zata hau da Naseera idan DNA test ya fito. Su biyun zasu bar mata gidan.

Sanda Mahfooz ya ajiye Naseera kofar gidan kamar karsu rabu, shaƙuwa mara mitsaltuwa ke ƙulluwa tsakanin su. Shi ma babu haufi yasan an halicce ta domin sa. Baice komai ba yayi shiru cikin motar, itace ta soma magana.

“Mijin Tauraruwa me zakayi anjima?”

“Nothing!” ya amsa a diƙilce. Zuciyar shi yana mashi ƙuna. Yana ganin nisan sati uku wai lokacin ne za'a kai mashi tauraruwan shi. Haɗiye miyau yayi mai bala'in zafi, tareda saka hannu akan steering mota. Duk takaici ke ɗawainiya dashi. Ji yake kamar yace ma Dr gaskiya ya bashi matarsa ya yafe wani biki ko liyafa da ake so a haɗa masu. Balle ma duka bidi'a ne.

“Mijin Tauraruwa, dama nace kazo anjima kayi dinner tareda mu,”

Kallonta yayi saiya sakar mata murmushi, ya bala'in jin daɗin tayin data masa. Dama yana neman uzurin dazai saka shi dawowa wajenta anjima. Anan ya soma jin sanyi cikin ransa. Sai sukayi gajeren bankwana tunda zasu haɗu anjima. Ta fita takai wajen gate sai wayanta yayi ruri alamar saƙo ya shiga cikinta. Anan ta buɗe sai taga saƙo daga wajen Mahfooz.

'Thank you for loving me and making my heart to smile. I love you Tauraruwa, always and forever'

Murmushi tayi sosai mai bayyana haƙora saita waiga ta kalle Mahfooz dake kallonta itama. Kashe mata ido yayi yana murmushi, hankalin sa ya kwanta yaganta tana murmushi. Anan ta jira shi harya soma tafiya yabar layin. Saita shiga ciki. Bata ga Kankana ba sanda ta shiga falo, ita lokacin tana ɗaki tana barci. Rabonta da Sallah tun jiya, wai duk jikinta ciwo yake mata.

Wanka Naseera tayi saita wuce ɗakin Umma, sai take sheda mata Rumasa'u tana gidan amma karta damu. Zata saka ido sosai akan ta, idan ta shiga harkan su zata sha madaran mamaki. Naseera bata wani damu ba, bashi bane ke gabanta. Koma waye iyayenta ta kusan komawa gidan mijin tauraruwa da zama.

Kitchen ta wuce domin tayi ma Mijin Tauraruwa girki da kanta. Multi colored fried rice tayi mashi wanda yasha su karas, peas dasu hanta. Sai tayi grilling kaza wanda yasha kayan kamshi sosai. Sannan tayi Samosa sai kuma kunun aya wanda aka zuba madaran gwangwani. Yadda taketa rawar jiki bataso komai ya ƙone ya bama Barira dariya. Aikam tayita zolayar ta.

Barira zata girme Naseera da kusan shekara goma. Ta taɓa aure kuma yaranta uku. Mijinta ya rasu shine ta soma aikatau. Tayi sakandire kuma yanzu haka ta sake zana waec. Idan taci zata je poly tana weekend classes da kuma aikinta. Yaranta suna wajen mamanta wanda duk a Kaduna suke. Tana yawan zuwa suma suna zuwa wajen ta.

A cooler masu alfarma Naseera ta zuba abincin, lokacin Kankana ta fara jin kamshi ya baɗe gidan. Balle Naseera ma'abociyar amfani da albasa ne sosai da garlic. Haka gidan yayita kamshi, miyan Rumasa'u ne yayita tsinkewa. Naseera ta ajiye komai a food tray, saboda ɗayan ƙaramin falon zata kai abincin inda zasu ci tareda Mijin Tauraruwa.

Saita wuce ɗaki domin tayi sallah tareda wanka, lokacin har magrib ya gota. Itama Barira tana ɗaki tana sallah. Aikam Rumasa'u ta fito taje kitchen ta ɗauko kwano, anan ta zuba san ranta. Babu abinda bata ɗiba ba ta wuce ɗaki abinta. Sanda Mahfooz yazo bayan Isha, ya canza zuwa farin kaya. Sai taga fari yafi mashi kyau akan komai. Murmushi ke bayyana a fuskan shi, sannan kuma kamshi ke tashi a jikinsa. Bai saka hula ba saidai ya tsafe gashin kansa.

Saida ya biya shagon Kanti Plus yayi siyayya kala kala, dama ɗazu yaso siya ta hanashi. Yanzu kuwa babu mai mashi shamaki. Haka ya siya tarkace kala kala su chocolates kayan zaƙi da biscuits na kamfani daban daban. Sai kuma su lemu. Dafa kai tayi data ganshi da kayan kamar zaiyi tafiya. Shi kuma gira ya ɗaga mata tareda kafaɗa. Barira ce ta amshe shi ta shiga cikin gidan dasu.

Ita kuma Naseera Atampha ta saka bou bou sai tayi ɗaurin ture kaga tsiya. Fuskanta babu komai, sai ƙananan baƙin shedan quraje wanda suka mutu. A haka kuma ya bala'in ƙawata mata fuska. Iso tayi mashi zuwa falon. Saita kai mashi ruwa a jug. Wani lallausar rug ta shimfiɗa mashi anan zasu ce. Saita koma domin ta kai mashi abincin.

Dr Abdallah baya gida lokacin, ita kuma Umma tace bazata fito ba. Hankali kwance bata kawo komai ranta ba takai mashi abincin. Ta durkusa tana murmushi zata saka mashi.

“Tauraruwa.... Avoɗi,” yace mata da harshen fillanci. Murmushi tayi mashi, bata san meya ce ba amma tana kyautata zaton ya yabe tane. Shima yasan bata san meya faɗa ba, duk da ba wani abu mai wahala bane, cewa yayi tayi mashi kyau.

“Kinyi kyau...”yace yana murmushi. Dariya mai sauti tayi. Saita saka hannu zata buɗe cooler, hannunsa yasa akan nata, saita kalle shi.

"Thank you.” Yace mata ƙasa ƙasa. Saiya cire nashi hannun. Tana buɗewa taga anyi mashi diɓan wulakanci. Da sauri ta rufe duk ta muzanta. Saita sake buɗewa a hankali ta leƙa. Lokacin wayan Mahfooz yana ruri ya maida hankalin sa wajen. Daddyn Faash ne ya dawo bai gansa ba yace masa karya daɗe, saboda ya soke fitan dare a gidan kafin a sake jawo masa salalan tsiya.

Fuskan Naseera nan take ya canza kala, daga nan hawaye ya ciko mata a idanu.

“Ina zuwa,” tace saita fita da sauri. Kafin ta ƙarasa har hawaye ya soma gangaro mata. Ɗakin Barira taje amma bataga kowa ba, sai taje Kitchen inda taga tana wanke wanke.

“Ke kika taɓa abincin dana dafa?" tace tareda hawaye sirara. Barira tayi nazarin yanayin ta, bata ce komai ba saita fita taje falon da Mahfooz yake. Anan ta buɗe sai ta gani. Kwasa tayi ta tafi dashi. A kan deep freezer ta dire tana mamaki. Kwata kwata sun mance da zaman Rumasa'u cikin gidan tunda basu saba zama da ita ba.

“Haba ƙaramar Hajia, kinsan bazan maki wulakancin nanba, ko sanda na fito yazo kenan. Kuma dai a gabanki akayi komai,” tace tana jimami.

Ita Naseera banda ɗaci ba abinda zuciyar ta yakeyi, yau datayi planning perfect date da Mijin Tauraruwa shine wannan abu ya wakana. Rumasa'u ce ta shigo cikin taƙama tana girgiza. Ga kwanan abinci hannun ta tana siɗe ƙashin kaza wanda ta ɓalla. Rabi ta ɗiba duka wajen kirjin da fuka fukai. Sai kuma cinya ɗaya, duwawun ta bari da abinda baza'a rasa ba. Ai gidan masu kuɗi ne, idan bai isa ba su girka wani tunda akwai masu aiki.

“Ke kika ci abinci daga wannan cooler ɗin?" Barira tace cikin zafin nama. Harara Rumasa'u ta bita dashi, batayi niyyar amsata ba. Saboda tana ganin meye abin hayaniya dan taci abinci a gidan masu kuɗi.

“Sai me ?” Rumasa'u tace tana yatsine fuska. Kwafa Naseera tayi, bata san me zata ce ko tayi ba domin ta fanshe wannan takaicin. Sai ta bar kitchen ɗin ta koma falo wajen Mahfooz. A kofa ta tsaya tana kallo shi, saita buga da hannunta domin ya kalleta.

“Yunwa,” yace a shagwabance. Murmushi tayi saita tayi magana, “Kana san Indomie?”

Ya lura akasi aka samu da abincin, gashi kuma kamshi ya cika ko'ina sanda ta kawo. Amma sai yayi fuska, ita kuma bazata bari yaci sauran Rumasa'u ba kafin ta cutar dashi.

“Uhm... Koma menene. Kawai ya zamanto kin dafa da kanki.”

Da sauri ta koma kitchen, a lokacin Barira tana fere doya. Tace Indomie babu girma. Gwara suyi golden yam. Aikam haka akayi, sai suka soya kwai da sausage suka kai mashi. Yaci sosai yanayi yana mata santi. Ranta har lokacin bai bar ɓaci ba, Saboda taso yayi duka santin a abinda ta soma girkawa.

Bayan ya gama ci lokacin an kira waya shi wajen sau uku. Faash ne yace ance ya koma. Babu damar zama suyi hira. Da chan suna kaiwa har biyun dare a waje amma yanzu babu hali. Haka rai baiso ya tashi ya tafi. A farfajiyar gidan suka ga Rumasa'u tana selfie abinta.

Da gangan Barira taje domin tayi mashi sallama, “Kayi hakuri Oga, wallahi sahibar ka tayi maka abinci gangariya. Ashe wancan ta buɗe ta cinye ba'a sani ba. Yasa kaga anyi wani,” tana magana tana nuna Rumasa'u da baki. Nan take cikin Rumasa'u ya kaɗa, bata san abincin Mahfooz taci ba.

“Abin cin nawa taci?” ya faɗa cikin fushi tareda kallon inda take. Ita kuma saita soma ja da baya tana tura baki, “Kece kika ɓata ma Tauraruwa rai kenan? Muna tare hankalinta baya wajena...”

Riƙo masa hannu Naseera tayi, sai tayi puppy face tana kallonsa, “Mijin Tauraruwa kayi hakuri, she's not worth your anger.”

Idan Rumasa'u ranta yayi dubu toh ya ɓaci. Watau Mijin Tauraruwa!!! sai ta ɗauki alwashin saita watsar da duk wani ɓurɓushin soyayya dake tsakanin su.

Haka suka wuce ta raka shi, inda sukayi bankwana ya tafi. Koda Naseera ta koma ɗakinta sai taga Rumasa'u tayi babakere akan gadonta.

“Wanda kike taƙama dashi dayake tare maki faɗa baya nan balle ya fitar dani.... Shekaru fiye da ashirin kina cikin daula. Dan baki kwana a ɗakin nan ba yau bazaki mutu ba. Dan haka fita ki kashe min wuta barci zanyi.” saita janyo bargo ta rufe jikinta tana ajiyar zuciya. Ta ɗauki alwashin zatayi mata kora da hali. Da kanta zata ji gidan Dr Abdallah ya isheta. Saboda kullum saita ƙunsa mata baƙin ciki lodi lodi.







Wannan kenan!



#Naseera
#Rumasau
#Mahfooz
#Tauraruwa
#MijinTauraruwa
#DiyarDrAbdallah
#Dimpilicious
#FullyDimplated



Ainakatiti 💫

Continue Reading

You'll Also Like

2.1M 87.9K 93
•UNDER EDITING• Abhimanyu Chowdhary-A mysterious 28 years old man. CEO of Chowdary group of companies. He has looks that every girl craves and go cra...
54K 1.4K 21
You, an infamous serial killer in New Orleans, feed on the young. Your days are numbered, but soon you meet a charming man named Alastor. He fills th...
89.9K 3.3K 55
After his first year at the Advanced Nurturing High School, Fukazawa Yato is about to start his second year as a student. With a better understanding...
Peer E Kamil By storybyaina

Mystery / Thriller

30K 379 22
salar sikandar & imama he waits 9 years for her bad boy become religious for a girl by = umera ahmed