DIYAR DR ABDALLAH

By Aynarh_dimples

44.4K 6.3K 1.1K

Zuciyar sa yana mashi wasiwasi, abinda yake gudu shi ke shirin faruwa dashi. Bai taɓa samun kansa cikin wanna... More

One - Kankana
Two- Ruwan Sama
Three - Ummata
Four - IPhone
Five - Annoba
Six - Wanene Mahfooz I
Seven - Mahfooz II
Eight - Mahfooz III
Nine - Mabuɗin Zuciya
Ten - Kallon Kallo
Eleven - Farin Wasa
Twelve - Mugun Mafarki
Thirteen- Permanent Stalker
Fourteen - Rarrafen Carpet
Fifteen - Ƙarfi Yaci
Sixteen - Bazan Barki Ba
Seventeen
Nineteen - Naga Wajen zama
Twenty - Mijin Tauraruwa
Twenty-one - Annihilation
Twenty-two - Pound Of Flesh
Twenty-three - Ribar Haƙuri
Twenty-four Bazan Barka Ba
Twenty-five - Love That Hurts
Twenty-six -Rendezvous
Twenty Seven- Idan Tayi Ruwa Rijiya
Twenty-eight - To Be Tainted
Twenty-nine - By Whatever Means Necessary
Thirty - Sun Shuka Sun Girbe
Thirty-one- Miscreant
Thirty-Two - Déjà-vu

Eighteen - Ni Ce Asalin Diyar Dr Abdallah

1.1K 181 37
By Aynarh_dimples


Tunda Naseera ta fahimci cewa Mahfooz ba canzawa zaiyi ba, saita saurara masa. Shima zaman a haka yafi mashi daɗi sosai. Ya riga ya birne rayuwarsa na baya kuma baya so ya ɗauko wannan babin. Zaune suke cikin jindadi da walwala, idan suna tare cikin ɗaki banda hira kala kala basa komai. Musamman ko a aikin Naseera kokuma akan nasa. Yana bala'in alfahari da ita yadda take malaman asibiti. Hirar asibiti sosai suke yi tareda yanda take ceto rayuwar mutane. Har yake ce mata da tana nan sanda umman sa keda rai, da ita zatayi mata operation sanda aka haife shi. Kuma bazata mutu ba, duk wannan abu bazai faru ba. Daga nan kuma sai ransa ya ɓaci ya kanne fuska.
Ita kuma mamakin yanda yana kwallo kuma yana aikin Engeering ɗinsa takeyi, nan ya gaya mata yanzu manya manyan hanyar da gwamnati sukayi shiya zana da kuma wasu gadoji.
A kwana a tashi babu wuya wajen Allah, har rana ya zagayo za'a ci kasuwa. Kuma yaune ranar da akayi sunar yaron Charo. Koda mutane suka shiga cikin gida tareda ganin su Mahfooz, basu kawo komai cikin ransu ba. Saboda dama Charo tanada wasu yan uwa a brini, kuma ansha sune suka zo sunar yaronta. A iyaka cin kwanakin nan Mahfooz ya nuna mata soyayya fiye da yadda take tsammani. Ya mutunta fiye da yadda take gani ana ma wasu. Idan suna tare zata gaya masa gameda ciwon ta, taran numfashinta yakeyi da sauri. Ya kalle ta cikin idanu babu wasa kuma a nasa. Ya sake jaddada mata cewa koma menene bazai rabu da ita ba, gwara tabar sirrinta cikin ranta. Idan tana ganin zai rabu da ita akan shi ne toh zai bata mamaki. Muddin bazai cutar dashi ba, toh bayaso yaji. Yaji kuma ya gani zai zauna da ita. Dogon nazari tayi, kuma kamar yadda yace ne idan bazai cutar dashi ba, baida amfanin ya san koma menene. Haka suka soma gina rayuwa mai tsabta irin na ma'aurata. Kallon Mahfooz takeyi a kaikace ko zai nuna alama na cuta amma bata gani ba. Koda yake ba'a ganewa a fuska, ta ɗauki alwashin idan sun koma zatayi mashi gwaji domin ta tabbatar da abinda likitoci sukayi bayani.
Shikam gode ma ranar da su Sada suka ɗauketa yakeyi, saboda da basu zo wannan kauye ba bazasu taɓa kasancewa tare ba. Sannan yayita gode ma Ardo daya nace mashi akan ya aure muradin zuciyar sa. Dama ance every disappointment is a blessing, duk ya mugun abun daya faru dakai idan aka duba ta wani fannin akwai alheri cikinsa.
Tabbas Naseera itace tauraruwan zuciyar sa, yana samun natsuwa sosai idan yana tareda ita. Yanzu ya daina firgici idan yana barci, sau daya yayi tun jituwar su sai ta riƙe shi tana kwantar mashi da hankali, tareda jaddada masa tsoro ba komai bane face abinda mutum ya ƙera cikin ransa.
Bayan asuba ranar da zasu tafi, da safe tana kwance tana ƙara barci. Saiga Mahfooz yaje wajen jakarta domin ya tayata haɗa komai. Dan shi baya so su kai azahar a garin. Zumbur ta miƙe da sauri ta fizge jakan kamar an tsikareta da mashi. Idanuwanta sunyi dara dara kamar sabbin tocila. Anan ta soma ajiyar zuciya tareda ajiye jakar gefenta. Kallonta yakeyi yana mamakin yadda ta canza farad ɗaya, kuma menene ke cikin jakar data ke masa mugun ɓuya? Ita kuma tana tsoron kada yaga AVR ɗinta, yayi mata alkawarin bazai rabu da ita ba duk runtsi amma bata so ya sani ta haka. Ta fiso itace ta fito ɓaro ɓaro ta gaya mashi.
Barin ɗakin yayi yaje wajen su Ardo, anan yake sanar dashi cewa zasu raka su gida dashi da Bamanga. Musa yaso zuwa amma aka ce ya tsaya ya taimaka ma matarsa. Anan akayi ta hada hada ana haɗa masu kayan da zasu tafi dashi. Naseera sunsha kuka da Charo kamar idansu zai fita, kuma taje wajen Fesindo tayi mata bankwana tareda neman yafiya wajen ta. Mahfooz bai mata maganar tsarguwan datayi ba. Shi ke ta sakar mata murmushi, ya lura hankalin ta baya jikinta. A cikin motar hannun sa yana maƙale da nata gam. Kamar wani zai zo ya kwace mashi ita.

“I will never leave you,”

yake furtawa idan idansu ya haɗu. Babu karya Mahfooz yana ƙara mata kwarin gwiwa. Hankalinta yaƙi kwanciya gabanta sai faɗuwa yakeyi. Ta rasa dalilin dayasa ta shiga cikin yanayin. Banda azkar cikin ranta batayin komai. Ji takeyi kamar wani mugun abu zai faru da ita.
Bayan azahar suka isa Kaduna daga garin Niger, kai tsaye gidansu Naseera aka wuce. Sai da aka nufa hanyar layin Mahfooz ya fara tsorata. Bai taɓa tunanin zaiyi mashi wahalar gayama iyayenta ya aure ta kai tsaye, ba tareda sanin su ba. Gashi ko sau ɗaya baiyi practicing irin jawabin da zai yi ba, kokuma yadda zai tsaya, zama ko gaida su. Sai a lokacin ya tuna cewa bai taɓa zuwa bikin kirki ba balle yasan yanda ake yi gaban surukai. Tsakanin shi da taro sai wajen ɗaurin aure a masallaci.
Ranar Nurse Jamila tazo duba Hajia Binta, jinin ta ya hau sosai wanda yasa saida aka kwantar da ita ana ƙara mata ruwa. Duk ta rame bata iya cin abincin kirki. Hankalin Dr Abdallah yayi mugun tashi, ya rasa Naseera gashi yanzu kuma Hajia rai yana hannun Allah. Dambun shinkafa wanda yasha zogale da nama Nurse Jamila ta kawo. Sai tayi kunun zaƙi da kuma ginger drink. Sannan ga ferfesun kayan ciki tareda yanka su kankana da abarba. Liyafa sosai tayi cikin cooler ta kai masu. Ita da yarinyar ta Zubaida suka je. A turakar Hajia Binti suka ganta kwance tana numfashi sama sama, duk ta galabaita ta zama abin tausayi. Babu haufi Anty Jamila ta tausaya mata,
Jibe yanda take wahala akan yarinyar da bana nata ba. Da kanta ta canza ma Hajia Binti ledar ruwa. Sai Zubaida ta zuba masu abinci, tareda tayasu gyaran ɗaki.
Taxi Ardo yayi masu chata su huɗu, sun isa layinsu Naseera suna kofar gidansu. Koda suka fito daga motar, wasu samari su uku suke tafiya a layin. Da sauri ɗayan ya nufesu yana murmushi.

“Makara,”

“Makara, dama kana nan ?” ya ƙarasa inda Mahfooz yake tareda miƙa mashi hannu. Shima murmushi yayi sai suka gaisa. Ajinsu ɗaya a kano kuma yazo ta'aziyyar mutuwarsa, wanda ya koma na Zanira. Mamaki Naseera takeyi da wannan mugun suna, amma dai ba tace komai ba. Buga gate tayi inda mai gadi ya buɗe ƙofa. Shine ya tsandara ihu mai firgitarwa. Dr Abdallah ne ya fito da sauri domin yaga meya faru, anan ya riske Naseera tana shiga cikin farfajiyar tareda murmushi akan fuskanta ta.

“Baba....”tace da karfin gaske saita ruga wajensa kamar ƙaramar yarinya ta rungume shi. Anan ta barke da kuka, shikam hamdala yakeyi yanayi bubuga mata baya domin ta daina. Haka Mahfooz yaketa kallon su cikin ban sha'awa. Shima irin wannan shaƙuwa yakeso ya ƙulla da yaransa, idan sun haifa da Naseera. Saboda burin sa bai wuce ya tara nashi zuriar ba.
Hannu Ardo Bello ya miƙa ma Dr, anan sukayi musabaha harda Bamanga da Mahfooz. Sai suka wuce cikin gidan. Hankalin Dr yaɗan kwanta ganinta tareda mutane wanda yana kyautata zaton bazasu cuce ta ba. A falo suka zauna su duka, lokacin Hajia Binti tana barci, Anty Jamila tayi mamakin ganin Naseera. Nan take ta tura saƙo zuwa mamanta na asali. Koda yake jiya suka gama uwaka ubanka da ita, danta sake ce mata har yanzu yarta shiru. Anan ta zage Nurse Jamila tas tace karta kuskura ta sake kiranta. Batada alaƙa da ita harkokin gabanta sun isheta.
Anty Jamila bata ji kashe din ba saboda gashi ta gaya mata anga yarinyar. Bawai dan Allah takeyi ba. Saboda tanada buƙatar kuɗi shine takeso ta samu wajen asalin maman Naseera. Zatayi mata magana akan kota bata kuɗin datake so kokuma ta fasa kwai duniya tasani.
Tanaso tayi amfani da kuɗin domin taje lokoja gurin wani hatsabibin boka. Yarinyar ta Zubaida wanda ita kaɗai ce yarta ankai sadaki da kayan aure sau biyar sai ana fasawa. Shine aka sheda mata wai ta aure aljani. Zubaida yarinyar tanada hankali da sanin ya kamata, tace masu babu abinda ke damunta, komai lokaci ne kuma lokacin nata bai kai ba. Anty Jamila ta ce mata dama mahaukaci baya taɓa yarda yanada cuta.
Naseera taje ɗaki domin taga Ummanta, anan ta riske ta tana barci. Riƙo mata hannu tayi tana murzawa a hankali, sai hawaye yana kwararo mata a fuska. Taso ta tasheta domin taga surikin ta amma babu dama. Zubaida ce ta kai masu Mahfooz dambun da suka kai tareda Lemu, tun sanda ta ganshi sai taji wani sanyi cikin ranta. Bai lura da ita ba yana chan kogin tunani, ya dafa kansa da hannu ɗaya kuma idansa a rufe yake. Kamar kowa dake amfani da shafukan yaɗa zumunta, itama ta sanshi a Instagram. Bata taɓa dogon nazari akansa ba saboda bata taɓa tsammanin zasu haɗu ba. Amma ganinsa kusa da ita ya tafi da imanin ta. Balle kuma daga dukkan alamu yana cikin wanda suka taimaka ma Naseera, wannan kaɗai ya nuna yanada zuciya mai kyau.
Bayan sunci sunyi nat, sai Ardo Bello yayi gyaran Murya, yayi bayani mai gamsar wa. Da farko hankalin Dr yayi mugun tashi, amma kuma da Ardo yayi masa jawabi sai ya fahimta, tiryen tiryen ya zayyana masu duk abinda ya wakana. Ajiyar zuciya Dr yayi saiya kalle Mahfooz wanda ya kasa haɗa ido dashi. Yanzu yadda yake jin Naseera cikin ransa, bazai so nan gaba idan ta haifan mashi yarinya ba wani chan daban ya aureta bada izinin sa ba.

“Toh yanzu shikenan zaka sauwake mata kenan?” Dr Abdallah ya tambaye Mahfooz.

Da sauri Mahfooz ya ɗago ya kalle shi, saiya kalle Ardo da Bamanga kafin ya sauke idansa akan Naseera. Rawa bakinsa yake masa, anan gabansa ya cigaba da faɗi wanda yakeyi tun asali. Ita kuma hawaye takeyi, tsoranta kada ya canza ra'ayi a kanta. Kokuma kada Dr yace sai sun rabu. Tana ganin zata fito ɓaro ɓaro tace a barta ta zauna da mijinta. Miyan bakin Mahfooz ya bushe, amma duk da haka bai karaya ba.

“Dan Allah Dr ina neman alfarma wajen ka. Nasan ba haka kaso ka aurar da ƴarka ba. Amma zamana tareda da ita duk da kwanakin babu yawa nazo na fahimci wace irin mace ce, kuma macen da kowane namiji zaiyi alfahari da ita....”
Ɗukawa yayi tareda harɗe hannunsa biyu alamar roko, Naseera tayi mamaki sosai. “Karka takura min akan na saketa, ka tambaye ta. Mun riga mun sasanta. Dan Allah banso a rabani da mata na, Dr kayi min rai ita kaɗai ce abinda nakeda shi yanzu,”

“Ai tunda yana santa ba maganar rabuwa,” Ardo yace.

Dafa kai Dr yayi yana nazari, “A cikin sasantawan ku injin dai ta gaya maka komai a kanta koh?”
Shi Mahfooz yana tunanin Dr yana magana ne akan sanda yan daba suka ɗauketa, tunda baya tsammanin sun sa yana wajen amma bai hana suba. Da sauri ya amsa mashi.

“Eh nasan komai, kuma haka nake santa babu abinda zai sa na rabu da ita,”
Jin wannan ya bala'in kwantar ma Dr Abdallah da hankali, ba kasafai bane yarinya tanada kanjamau zata samu mijin aure kamar haka. Gwara ya barsu tunda sun riga sun sasanta. Ajiyar zuciya yayi saiya ce toh babu damuwa, saidai dole suje asibiti ayi masu gwaje gwaje kuma a duba lafiyar Naseera saboda ciwanta. Bai fito ɓaro ɓaro yace kanjamau ba kafin su Ardo su kwashe takalaman su a hannu su ruga. Mahfooz saiya fara tunanin kila ko tanada cuta kamar ulcer ko makamacin haka, kuma maganin daya gani ɗazo shine. Murna yayi sosai, Dr yace bazata tare ba sai bayan sati uku. Saboda ayi shirye shirye.
Inna Nafisa taje kasuwan central na Abubakar gumi, labule taje siyowa domin gobe zasu soma tafiya. Ta fito daga mota kenan sai achaba ya bugeta, irin yaran nanne masu gyaran mashin suyita gudu titi. Da azama aka kaita Abdallah Specialist, bata karye ba kawai ta buge kanta ne, masoya annabin dake wajen suka taimaka mata. Koda ta aka kaita su Naseera suna chan suma ana masu gwaje gwaje.
Sanda Inna ta farka tayi ma Rumasa'u kiran duniya bata ɗauka ba. A lokacin ta amsa passport ɗinta kenan, ta samu wasu shaggun ƙawayenta, tana nuna masu ita yanzu babban yarinya ce Turai zata fara zuwa shaƙatawa. Saboda gobe tafiyan su tareda Hajia Salima. Har lokacin bata gane irin amintan da zasuyi da Hajia ba. Kawai tasha yadda tayi ma Latisha ƙarya shine ta tausaya mata, ta haɗata da wanda zasu rinƙa taimaka mata.
Takaicin duniya yake ɗawainiya da Inna, saboda tasan cewa Rumasa'u tana gani. Wayan kuma sauran yaƙi shiga sai nata kawai. Data sake kira na ƙarshe wanda tace daga nan bazata sake kira ba sai gashi ta ɗauka.
Koda taji an hankaɗe Inna bata wani damu ba, matsalar ta shine ta ina zasu samu kuɗi su biya na asibiti domin ita gaskiya bazata ranta masu ba. Har yanzu bata san zasu tashi ba, tunda bawai shiga sabgar su takeyi ba. Tun randa aka jata domin taje ta bama Rahina haƙuri, tayi kukan duniya. Kuma Latisha tayi mata alkawarin zasuyi ma Rahina babu daɗi idan ta dawo. Sai sun nuna mata ƙaramar qwaro ce.
Tunda gwaji akayi masu Naseera ba dadewa zasuyi ba. Sun fito farfajiyar asibitin suna wajen parking lot. Masu aiki sunzo sunata mata barka da zuwa Dr, ashe Inna tana ji. Anan ne gabanta yayi mugun faɗi. Ta rasa gane meyasa take jin Naseera cikin ranta kamar sunada wata alaƙa.
Inna dake ta wajen tana jiran Rumasa'u tazo su wuce, saita gyara mayafinta tareda rufe fuskanta dashi. Ƙarasawa tayi dab da ita domin ta kalle ta, anan taga hannun Naseera. Gabanta ne ya faɗi sosai. Kawai saita soma samun flash backs. Akwai wani tabon haihuwa akan yatsan ta na uku. Inna ta rasa dalilin amma tana ganin tasan abu makamacin haka.

“Qwaro,” Kankana ta ƙarasa wajensa tareda riƙe mashi hannu. Ko kallon Inna dake wajen batayi ba. Da sauri ya fizge saiya watsa mata harara.
"Meye haka?" yace a wulakance.
“Haba My Love me nayi maka kake guduna?"
Kallon Naseera yayi yana murmushi saiya janyota dab dashi, “Ga matana, karki jawo min matsala dan Allah," ya gargaɗeta. Itama kallon Naseera tayi saita sake kallon sa, “Ina ce wancan da muka gani kwanaki mai....”zata ce mai tallan taba saida mayar da maganar.
“Qwaro karka min haka, nasan bakada aure. Saboda ko sati uku ba'a yi ba da kazo gidan mu. Balle ma da kayi aure da naji a Instagram.”
“Koki zo mu wuce ko nazo na janyo ki,” Inna ta gargaɗe ta. Anan hankalin kowa ya koma kanta. Dayake an saka mata bandeji an naɗe mata kai, Naseera bata ganeta ba a matsayin wanda suka haɗu a police station. A tare itada Mahfooz suka gaida ta, tareda mata ya jiki. Sai a lokacin Rumasa'u ta lura bata mata magana ba. Haka tayi gaba tana tafiya haushi kamar zai kasheta. Sai Inna tabi sahunta tareda sake kallon Naseera. Mamaki ke ɗawainiya da Naseera, sunaye kala kala taji yau anbi Mahfooz dashi, itama saida ta bari suna ƙofar gida inda zata sauka sai direba ya maida shi gidansu. Bayan Isha Dr dasu Ardo za su gidansu Mahfooz domin ayi ma nasa iyayen jawabi. Kallonsa tayi tana murmushi, “Toh Makara ko Qwaro ne. Sai anjima,”
Dafa kansa yayi yana dariya, “I can explain, Wallahi ni ba ɗan tauri bane,” yace. Ita kuma saita bushe da dariya. “Toh Makara,”
“Tauraruwa, ni zan tafi” yace mata a hankali. Yana ganin nan zuwa wajen Isha idan ya dawo da bala'in nisa. Itama bataso ya tafi amma tasan dole ne.
“Toh,” ta iya amsa mashi dashi. Duk wani kalma data dace ta nema bata samu ba. Sunkuyar da kai tayi, yanzu nata tsoron ya fara. Idan yaje iyayen sa basu yarda ba. Me zai faru da ita kenan? Shikenan za'a rabata da wanda ta aminta dashi. Daga ruhinta har gangar jikinta. Hawaye ne ya soma gangaro mata, sai tayi sauri ta soma sharewa, shine ya riƙe mata hannu ya hanata tare su, daga bisani sai yayi amfani da nashi hannun yana sharewa. Baice mata komai ba, amma kuma yafi ɓakanta mashi rai. Baisan kalamai wanda zai faɗi da zai kwantar mata da hankali. Yana son ta yarda dashi. Bazai taɓa rabuwa da ita ba. Data tsagaita sai sukayi ma juna murmushi wanda ita ta fita. Dama daga ita har shi ba masu magana bane, amma a cikin shirun da sukayi sun aika ma juna saƙonni wanda su kaɗai suka fahimta.
Sanda ta isa cikin gidan Ummanta ta tashi, anan suka rungume juna sunata kuka. Abinda ya ƙara ma Hajia Binti ciwo bai wuce sanin cewa Naseera ta kwashi kanjamau ba. Anan tayita mata faɗa akan rashin gaya mata bayan duk duniya batada wata uwa data wuce ta. Haka dai sukayi take zantawa tareda bata labarin abinda ya faru a kauyen su Arɗo. Suma su Arɗo an basu ɗaki ɗaya suna hutawa.
Wajen Isha Mahfooz yazo da kanshi domin ya jagoranci su Dr gidansu Faash. An masu tarba mai kyau kuma an karrama su. Kamar yadda Arɗo yayi masu Dr Abdallah bayani haka yayi ma Daddyn Faash shima. Anan zumunci ya ƙullu sosai saboda sukayi ta fillanci. Sai Arɗo yace,“Yanzu Mahfooz da muna maganar ku da fillanci haka zakayi ta kallon mu kamar ƙananan mutane, tunda baka nuna mana kana jiba,”
Suma iyayen Faash sun yarda da bikin nanda sati uku, anan aka ce duk abinda ake yi ma amarya zasuyi. Yanzu zasu soma haɗa kayan lefe, kuma inda Mahfooz ke zaune a kawo zasu zauna. Dama duka yayyen Faash sunyi aure. Daga Mahfooz sai shi suka rage. 4 bedroom ne sai bayi uku da kitchen da falo. Za'a gyara masu tas su dasa rayuwar su anan.
Agogo Mahfooz keta dubawa saboda kada Naseera tayi barci, gashi bayada number ɗinta balle ya kirata. Basu suka gama taron ba sai goman dare. Daddyn Faash yace babu inda Mahfooz zaije cikin daren. Daga yanzu an soke fitar dare kafin a sake kama shi. Ranshi yana mashi ƙuna haka yayi masu biyayya.
Naseera tanata raba idanu ko zata ga Mahfooz tareda su Dr amma babu shi. Haka ta wayance ta koma ɗakin ta cikin takaici. Gashi batada waya balle suyi magana. Daga ita har shi ranar basuyi barcin kirki ba, kowa yanata kewan ɗan uwan sa. Zubaida kuwa itama tanata kallon hotunan Mahfooz a shafin yaɗa zumunta, a hankali sanshi yake shigan mata rai. Sosai tana kishi da Naseera akan samun sa. Taso kuma ace itace take zaune a matsayin matarsa. Tabbas zata lura dashi kuma zatayi mashi biyayya sosai. Idan ya aureta zansa yayi dace da mata nagari wanda zata ji tausayin sa. Bata damu da abinda yakeda shi ko rashin sa ba. Ita dai shi takeso ya zamto miji tareda garkuwa a gareta.
Inna tana cikin barci saita farka da sauri, yanzu ta gane a inda tasan tabon dake hannunta. Ba ko'ina bane illa hannun yarinyar data haifa shekaru ashirin da hudu a asibiti. Yanzu ta tuna da duk wani fasalin ta, kuma tabbas taga tabon haihuwa a yatsar ta na uku. Balle kuma yadda take jinta cikin ranta. Kasa haƙuri tayi saida ta tashe Mallam dake barci.
“Wallahi Mallam ina ganin anyi min musayar yarinya, saida nace maku meyasa kuka kaini asibiti. Daga na suma shine kuka kaini gidan bokan Bature gashi yanzu sunyi mani aika aika....”sai kuka ya kubce mata.
“Haba Nafisa, daga ganin sarkin pawa sai miya tayi zaƙi? Kawai dan kinga tabo jikinta sai kice yarki. Dan Allah karki jawo min magana na shiga kotu da mutane.”
“Wallahi yarinya tace,” saita cigaba da kuka, sannan ta rage murya sosai, “Kaima yanda Rumasa'u take gallaza mana bata tausayin mu baka tunanin cewa da walakin goro cikin miya?"
“Idan Rumasa'u ba yarki bace Nidai yata ce, kuma shiriya na Allah ne. Hannun ka baya ruɓewa ka yanke ka zubar,"
“Ba abinda nake nufi ba kenan, ina san Rumasa'u kuma babu mai maye mata gurbi. Ita na sani ita na saba da. Wancan Likitan danaji ana ce mata har aure tayi. Kaga babu wani sauran danganta da zamuyi da ita yanzu ai, kawai dai naso nina raina abina,”
Ashe duk abinda suke yi a kunnen Rumasa'u tana jinsu. Tana ta Chatting da Hajia Salima inda take ce mata tanada bala'in kishi, tareda gargaɗinta zatayi komai a kanta. Bataso taga ta ƙulla abota da kowa, walau mace ko namiji. Zata iya kashe su idan ta sani.
Tunani kala kala Rumasa'u ta samo yi, kamar yadda Inna bata jinta cikin rai toh itama haka. Ta daɗe da sanin cewa ita ba haihuwar talauci bane. Ita asalin ajebo ce rarrafen kapet. Anan ta ɗauki alwashin saita ƙwato ma kanta yanci. Ta lura su Inna zasuyi rufa rufa domin su barta cikin talauci kuma bazai yiwu ba.
Da safe wajen bakwai ta saka abaya ta fita, ko wani gaida su Inna batayi ba tunda batada gami dasu. Haka taje Abdallah Specialist tana tambaya ina ne gidan su Naseera. Mai gadi yasha masu zuwa mata jaje ne tunda tayi karyan ita ƙawarta ce. Anan aka gaya mata ta wuce. Koda ta isa layin tasha mamaki. Gidan yafi kowane girma da kyau. Wani danƙareren gate baƙi tayi maraba dashi, mai gadi ya buɗe mata inda tace tazo wajen aminiyarta.
Babban gida ne mai ɗakuna shida, falo uku da bayi biyar. Gidan sama ne sannan ga ɗakuna uku na masu aiki gefe. Wajen parking motoci zai ɗauki a ƙalla mota goma sha biyar. Sannan ga furanni tako ina, sai swimming pool ta chan kurya. Ɗawisu da barewa tagani sunata yawo cikin gidan gwanin ban sha'awa. Motan Dr Abdallah Maybach Mesarati tagani yana ƙyal ƙyalli a wajen parking. Ajiyar zuciya tayi tace dama nanne asalin gidansu shine dan zalunci aka yi musanya aka mayar da ita gidan talauci. Saidai babu komai yanzu, komai ya ƙare. Asalin Diyar Dr Abdallah ta dawo dole yar matsiyata ta fice mata.
Mai aiki tagani inda ta gaida Rumasa'u a ladabce, taso tace mata itace asalin yarinyar amma tayi shiru. Tambaya tayi ina ne ɗakin Dr saboda abinda Inna take kiranta dashi kenan, ita tayi mamakin wai ka tashi cikin daular nan kayi aikin likita. Da ita ce YouTube zata buɗe tana reality TV.
Kai tsaye Inda aka nuna mata nan ta wuce, Naseera tana zaune a ƙasa ta kifa kanta. Duk ta ƙosa safe yayi ko zataga waiwayan Tauraron ta. Kawai sai taji an banko ƙofa tareda shiga ciki. Ita Rumasa'u sai lokacin ta lura Naseera data gani da Mahfooz ne akayi musaya da ita. Anan ta zuciya ta ƙarasa wajen ta. Fincikar ta tayi saita sharara mata mari tana magana.
“Uban me nayi maki wai da komai nawa kika ɗauka, shegiya yar matsiyata yar malamin primary kin rabani da iyayena yanzu kuma kin rabani da masoyi na,”
Tureta Naseera tayi tana haki, “Meye haka ?Daga ina?”
“Zaki sani. Zo ki fita kibar min ɗaki, asalin Diyar Dr Abdallah ta dawo. Kuma wallahi yanda kika shayar dani baƙin ciki, na tashi ina wahala, wallahi saina rama. Zaki gwammace kiɗa da karatu. Kuma yanzu na fara, yadda na kwace nan gidan. Haka zan kwace Qwaro kamar Alewa a hannun yaro, saina rabaki da duk abinda kike taƙama dashi. Saina shayar dake baƙin ciki mara mitsaltuwa.”
Saita wuce durowa ta fara fitar da kayan Naseera, tanata fatali dasu tareda watsarwa ta balcony daga sama zuwa ƙasa.




Wannan kenan!


#Naseera
#Rumasau
#Mahfooz
#DiyarDrAbdallah
#Dimpilicious
#FullyDimplated


Ainakatiti 💫

Continue Reading

You'll Also Like

63.4K 1.6K 10
مافيا - حب - قسوه - غيره renad231_5 مرت سنه والقلب ذابحهه الهجر ومرت سنه والهجر عيا يستحي الروايه موجوده في انستا : renad2315
11.1K 515 26
MAFIA STEP - SISTER OF BANGPINK
86.2K 7.4K 171
"ငါ့ရဲ့နောက်ဖေးခြံဝန်းက ထန်မင်းဆက်ဖြစ်နေတယ်(လီယင်)" Author: Snail Carrying Home Genre: Historical, Military, Urban life Status: Completed Translator:...
11.2K 731 37
Jeon Jungkook, he completed his graduation in business. he is sweet but for only his family and cold for other's. he doing internship in his father'...