DIYAR DR ABDALLAH

By Aynarh_dimples

44.4K 6.3K 1.1K

Zuciyar sa yana mashi wasiwasi, abinda yake gudu shi ke shirin faruwa dashi. Bai taɓa samun kansa cikin wanna... More

One - Kankana
Two- Ruwan Sama
Three - Ummata
Four - IPhone
Five - Annoba
Six - Wanene Mahfooz I
Seven - Mahfooz II
Eight - Mahfooz III
Nine - Mabuɗin Zuciya
Ten - Kallon Kallo
Eleven - Farin Wasa
Twelve - Mugun Mafarki
Thirteen- Permanent Stalker
Fourteen - Rarrafen Carpet
Fifteen - Ƙarfi Yaci
Seventeen
Eighteen - Ni Ce Asalin Diyar Dr Abdallah
Nineteen - Naga Wajen zama
Twenty - Mijin Tauraruwa
Twenty-one - Annihilation
Twenty-two - Pound Of Flesh
Twenty-three - Ribar Haƙuri
Twenty-four Bazan Barka Ba
Twenty-five - Love That Hurts
Twenty-six -Rendezvous
Twenty Seven- Idan Tayi Ruwa Rijiya
Twenty-eight - To Be Tainted
Twenty-nine - By Whatever Means Necessary
Thirty - Sun Shuka Sun Girbe
Thirty-one- Miscreant
Thirty-Two - Déjà-vu

Sixteen - Bazan Barki Ba

1.1K 170 22
By Aynarh_dimples


Mahfooz ya samu sabon sana'a, kamar yadda ake kiwan dabbobi haka yake kiwan Naseera. Duk wani motsi wanda zatayi yana kan idansa. Tana sanya shi nishaɗi fiye da komai cikin faɗin duniyar. Musamman idan tana dariya, dariyar ta yafi so a komai nata. Akwai yanda sautin sa ke ratsa cikin zuciyar sa, sannan fuskanta yana ƙawatuwa kamar fure mai bala'in kyau, gashi yana sheƙi kamar lu'u lu'u.

Ita dai Naseera doguwa ce amma ba sosai ba, da wuyan ta da kanta yayi kashi uku ana kofa. Fara ce tar mai dara daran idanu. Idanta irin kalar madara ne sannan ƙwayar idanta kuma ruwan zuma ne kamar na wasu maguna. Batada hanci mai tsine, nata yaje daidai da fuskanta. Bakinta yaɗan ciko yana yanayi da Jaruman bollywood priyanka chopra.

Tanada zara zara yatsu sirara wanda ya ƙawata ta sosai tareda yin daidai da siririn jikinta. Saidai a haka duk da sirantakar tanada diri mai kyau. Wuyanta sambal ne kamar na barewa. Sai da batada tsawon gashi a kanta, amma kuma duk gajartan sa yanada laushi kuma ya nannade kamar yadda matan africa sukeda shi. Tafiyarta abin kallo ne saboda tana yinsa cikin ado da taƙama kamar ɗawisu balle kafafuwanta a miƙe yake abin kallo. Tanada cikar ido da kwarjini, uwa uba idan tayi magana, muryanta zaƙinsa kamar an busa sarewa, kokuma zakayi tunanin susa ake mata a kunne yana ratsaka.

Ta ɗuka tana juye ruwa daga tulu, sai taji duk ta tsargu kamar ana kallonta. Wayancewa tayi saita waiga domin ta tabbatar da abinda take tsammani. Tsaye ta gansa a bakin ɗakin Ardo yana kallonta, babu abinda ya dame shi da cewa nan kauye ne ba'a nuna soyayya a fili.

Matarsa ce kuma babu wanda zai hanashi kallonta, yana tsaye ya saka hannu ɗaya cikin aljihun wandonsa, sai ƙafa ɗaya ya lanƙwasa ya jingina a jikin bangon. Ɗayan hannunsa yana wajen ƙeyarsa ne yana sosawa. Da suka haɗa ido saiya sakar mata wani lallausar murmushi sannan haƙorar sa farare tas ya bayyana. Gabanta ya soma duka uku uku. Ta lura yayi nisa kuma baya jin kira. Amma ko da yanka naman jikinta za'a rinka yi bazata taɓa amsa batun sa ba.

Ta ina ma zata amsa? Tanada mugun ciwo fah? Shima yanada nashi matsalar bataso ta saka shi wani. Balle kuma bayan duk abinda Fauziyya tayi bazata taɓa yarda wani cutarwa ya je mashi ba ta sanadin dangin su. Wahalar daya sha ya isa haka. Tana cikin tunani sai taga mutum dab da ita. A firgice ta matsa baya tana kallon sa. Saita soma girgiza masa kai alamar ya bari, baiko kula ta ba. Hannusa yasa ya matsar da nata daga tulun.

"Meye amfanin zan iya taimaka maki banyi ba?" yace chan ƙasa. Banda ita, sauran mutane gidan da suke kallon su basu ji ba. Duk saita tsargu, anan ta bar mashi komai ta wuce nasu ɗakin da sauri. Tana isa saita kama gwiwar ta kamar zatayi ruku'u tana haki, yanda takeyi kamar tayi gudun famfalaƙi amma tsabaragen tashin hankali ke dawainiya da ita.

Da gaske yanada niyyar sauya mata rayuwarta, da gaske abinda daya faɗa mata zai aiwatar. Amma meyasa yakeda kafiya da naci ne? Ai ba ita bane kaɗai mace kuma rannan ta ganshi tare da wata, meye dalilin sa na zuwa wajenta yanzu. Saura kwana kaɗan su tafi menene amfanin takura mata?

Bayan ya gama juye ruwan saiya bi sahunta, ganin yadda ta birkice yake mamaki. Baiyi tsammanin tsanar datayi masa yakai haka ba. Zuwa wajenta ya soma ita kuma saita soma tafiya baya baya tana girgiza masa ido. Miyan bakinta ya bushe rau kamar ƙashi. Saida ta kai bango babu inda zata, waige waige tayi domin ta samu wajen gudu. Anan ya tsaida tafiyar sa, saiya ajiye idansa a cikin nata. Itace ta soma magana cikin takaici.

"Dan Allah ka rabu dani, bakasan me kake faɗi ba. Na tabbata trauma ke damunka, saboda mun shigo garin nan kana ganin abinda baya nan..."

"Kina nufin banda hankali ne?" ya katse ta. Sai ya soma dariyar takaici yana safa da marwa. Ita dai bata bar inda take tsaye ba. Yatsa ya nuna mata saiya soma magana, "Watau bazan iya cewa ina sanki ba sai ina hauka? Meke damun ki ne wai? Meyasa kike guduna haka? Menene aibu na ? Ban cika namiji bane koko ni ɗin ne kika mugun tsana?" kwafa yayi saiya daura hannunsa a saman ƙirjinsa.

"Naseera da kinji abinda ke faruwa anan da kinji tausayina kin kwantar da hankalin ki..."

"Nima daka san abinda ke faruwa a nawa kirjin daka kyale ni," itama ta gaya mashi. Runtse ido tayi cikin takaici. Mahfooz bazai taɓa ganewa ba, ta lura bayaso ya gane. Amma ai so ba hauka bane, dole ya duba lafiyar sa. A ina aka ce ayi makahon soyayya. Kamar yadda bayaso ya gaya mata labarin Fauziyya haka itama bataso ta gaya mashi komai game da ciwon ta. Ko miji da mata akwai sirri koda kaɗan ne, kuma wannan auren cetan rayuwa sukayi. Bayan sun bar nan bazasu sake ganin juna ba.

Magana ya soma yi a natse, kana ganin kalar idansa kasan ya canza. Bai ciko da hawaye ba amma yana hanya, "Tunda nake ban taɓa samun soyayya mai ɗaurewa ba, iyayena sun tafi sun barni ina ƙarami. Yar uwata mai sona... Mai k-kaunata ta ta-fi," in'ina ya soma saboda zafin bacin ran daya shiga. "Naseera ina sanki, kada kema ki gujeni,"

Bazata ce bata karaya ba, haƙiƙanin gaskiya ta tausaya masa matuƙa. Hawaye siriri ya soma sauko mata a idanu, koda munafinci ne Mahfooz ya nuna kaunarta a fili, yadda bayan iyayenta bata taɓa samun wannan ba.

"Mahfooz ni annoba ce!"ta furta saita fashe da kuka. Durkusawa tayi ƙasa tana sheƙawa."Idan kasan asalin waye Naseera na tabbata zaka guje ni da gudu, yasa tun wuri nace maka ka rabu dani...."

"Hey shhhh!" saiya tsaida ta tareda duƙawa shima. Tallabo mata kumatu yayi yana share mata hawaye. Bata hanashi ba, itama tana so a rarrashe ta. Tanaso a jaddada mata cewa ita ba annoba bace, kuma babu wani abu dake tareda ita. Tanaso a ƙara mata ƙwarin gwiwa. Yanda komai ya cunkushe mata tasan tana dab da kamuwa da ciwon zuciya inda kirjinta zai buga ta mutu.

"Ki sani Naseera nayi maki alkawari, ko menene ke damun ki bazan taɓa rabuwa dake ba. Basai kin faɗa min sirrin kiba, nima nasan sirri abu ne mai wuyan faɗi. Yana ɗaukar lokaci kafin ka faɗa. Amma ki sani koma menene, duk duhun dake rayuwar ki nayi maki alƙawari zan zamo maki haske a cikinta. Kamar yadda kika zamo tauraruwa cikin ɓakin rayuwa na, haka zan zame maki. Bai dameni ba koda aljana ce ke, eh zan cigaba da kasancewa dake. Lone wolf dies but not the pack. Inaso ki zaman min bindiga, ni kuma zan zame maki harsashe Naseera, domin mu taru mu harɓe maƙiyan mu, da duk wani wanda zai cutar damu cikin rayuwar mu."

Nisa yayi yana ajiyar zuciya, soyayyar Naseera sake tasiri takeyi cikin zuciyar. Ita kuma shiru tayi tana sauraron sa. Ta wani fanni ta samu natsuwa cikin kalaman sa. Taga gaskiya cikin idansa. Riƙo hannunta yayi yana murzawa a hankali yana murmushi, sunkuyar da kanta tayi ƙasa. Mahfooz yanada bala'in kwarjini, an sha gaya mata tanada kwarjini amma tana ganin nashi zai ninka nata.

"Naseera Abdallah Kwarbai, ki sani ni Mahfooz Abubakar Gwaiba bazan taɓa barinki ba. Duk runtsi duk wuya, ina tareda dake. We're a team. Inaga tun bayan dana buga ma Nigeria kwallo, ban taɓa shiga nishaɗi ba sai ranar da aka aura min ke. Kuma nayi alwashin I'll forever protect you,"

Murmushi tayi kaɗan, hawayen har yanzu suna fita amma ba da gudu ba. Zatayi magana kenan sai Nenne ta kirata dole ta fita ta barshi mashi ɗakin.

Ɗakin Charo taje domin ta riƙe babyn, ita kuma Charo zata zagaya kewaye. Anan Naseera ta sake kallon yaron soyayyar sa yana shiga birnin ranta. Itama babu haufi tanaso ta mallake nata yaran na kanta. Sai maganar Mahfooz ya rinka mata ruri cikin kunnen, kawar da tunanin take kokarin yi amma yayi kanekane cikin zuciyar ta.

Idan Mahfooz yace yaji ya gani meyasa take gudun sa? Balle idan tana shan ARV ɗinta bazai taɓa kamawa ba, itama zatayi rayuwa mai kyau kuma zata haihu. Tabbas Ummanta zataji daɗi idan ta ɗauki kaddaran ta tareda mancewa da komai.

Ta ƙofa ta kalle inda take kyautata zaton zata ga Mahfooz, anan ta gansa zaune akan tabarma suna hira da Bamanga. Murmushi ta tsinta kanta tanayi, da sauri tasa hannu ta rufe bakinta tsoron kada wani ya ganta. Bata ji daɗin data lura da cewa kallon Mahfooz ne ya sakata nishaɗi.

Koda Charo ta dawo batama sani ba, ta dulmiya cikin tunanin Mahfooz da kuma rayuwar datake tunanin zasu gina. Mahfooz baida aibu da za'a ce su Ummanta zasu kyamace shi.

"Dariyar me kike yi?" Charo tace mata tareda dafata. Da sauri ta soma saisaita kanta, amma har lokacin bata ce komai ba. Wasa takeyi da hannun Bello Adama.

Mahfooz a wajen Ardo yaci abincin dare, saboda tun haihuwar nan Naseera tareda Charo take ci. Karin kumallo ne suke yi cikin nasu ɗakin. Shine ya fara zuwa ɗaki domin ya kwanta. Ita tana chan tareda Charo sunata hira, har Charo take cewa idan tayi arba'in zata je wajen Naseera domin ayi zumunci. Da gangan Naseera taƙi tafiya, Mahfooz ya saka mata kunyar sa. Yasa bata so ta dawo balle suyi wani magana, shi kam yana kwance yasan gudun sa takeyi, yadda take haɗa ido dashi tana balla mashi harara ta daina tun sanda ya faɗa mata sirrin zuciyar sa. Yanzu suna haɗa ido sunkuyar da kai ƙasa takeyi.

Saidai abinda bata sani ba shine idan jira takeyi yayi barci kafin ta shigo zai bata mamaki, saboda yanada alamar neuroanatomic lesion. Inda ba kasafai yake runtsawa yayi barci ba.

Koda ta dawo ɗaki ko'ina yayi shiru, itama karin kanta ta soma gyangyaɗi har Charo tayi mata tayin kwana a wajen amma tace ta barshi. Duk da dai Musa baya nan yana wajen gadi.

Da sanɗa ta shiga cikin ɗakin kamar zatayi sata, yana ankare da ita jira yakeyi ta gama natsuwa ya soma mata magana. Ita kuma harta zauna akan katifar sai tayi wani tunani, miƙewa tayi tsam taje wajen aci bal bal ta hure shi.

Mamaki Mahfooz yayi na abinda tayi, saboda ya tuna sanda ya roketa akan baisan zama cikin duhu. Magana ya soma yi, "Kiyi haƙuri ki kunna wutan dan Allah, bana kaunar duhu,"

"Meyasa ?" tace. Tanaso tasan wani abu game dashi kafin ta faɗa sanshi. Saboda bayan sunan sa batada wani abin data sani.

Ajiyar zuciya yayi, baisan ta inda zai fara cewa saboda yayi zaman kabari bane yake tsoron duhu. Kuma baiso ya firgita ta da wannan zancen.

"Bani san duhu Naseera, ina tsoron sa,"

"Fear is not real Mahfooz, abinda muke ƙerawa ne cikin ranmu. Idan ka fuskance shi zakaga ba komai bane dazai dame ka."

"Bazan iya ba, karki tursasa min dan Allah."

"I want to help you, amma bazan iya ba saika taimaka ma kanka. Meyasa ka saka katanga ne a rayuwar ka? Kawai sona kake yi amma daga bakin kofar zuciyar ka zaka ajiye ne. Waya ce maka haka ake soyayya? Idan na amince maka ni ce zan wahala tunda baka yarda dani ba balle ka sakani cikin rayuwarka." tace cikin takaici.

Soyayya baƙon abu ne wajen Mahfooz, baisan duk da haka ba. Baisan haka Naseera ta fahimci komai ba. Idan kuma tana ganin zata wahala akan soyayyar sa dole ya canza, amma kuma abu ne mai wuyan faruwa.

"Abinda yasa ban san kwana cikin duhu saboda yana tuna min da...."kasa ƙarasawa yayi saboda hawayen daya soma. Daɗin abin cikin duhu ne dataga raunin sa. Zuciyar sa tana tafasa tana mashi ɗaci. Kamar an watsa mashi narkarkiyar dalma saboda ya tuna abinda Fauziyya ta nufe shi dashi, saiya faɗa akan Zanira. Da sauri ya miƙe tsaye, magana ya soma yi, "Karki ƙara tambaya na, baniso kuma bazan taɓa so ba. Ki soni a yadda nake. Don't ever try to change me," saiya fita yabar mata ɗakin.

***

Uwar daka Rumasa'u ta wuce da kayanta, babu wanda ya tayata balle su tanka ta. Haka ta gama saita dawo tana kallon Inna. Lokacin Mallam ya wuce aiki saboda akwai assembly, itama Fa'iza ta tafi. Ɗakin daga Aliyu sai Inna ana taɓa hira jefi jefi.

"Inna toh ni me zanci? Banfa karya ba,"tace tana tura mata baki. Kallonta Inna tayi cikin mamaki, "Zoki gwagwiye ni," tace a hasalce tareda watsa mata harara. Babu arziki ta koma uwar daka ranta yana mata ƙuna.

Gashi duk jikinta yana mata raɗaɗi saboda bugun data sha, anan ta tabbatar Rahina muguwa ce azzaluma. Saboda duk ta kumbura mata jiki ga kuma zafi kamar an watsa mata barkono. Inda Rahina ta koya mugunta take tunani saboda sanda suke Islamiya ita take zane yan ajin tas, kowa yana tsoron ta. Ɗaukar wayanta tayi ta sake kiran wayan Latisha amma yaki shiga. Dayake Rumasa'u tanada naci kamar guɗa haka tayita watsa mata saƙonni sunfi goma.

Bayan Aliyu ya tafi shagon sa sai Inna ta fita waje tsakar gida domin ta soma aikace aikace. Sai lokacin Rumasa'u ta fito falo, sauran ruwan zafi ta gani ta haɗa shayi, madarar gwangwani wanda zasuyi amfani dashi gobe a gefe ta gani. Nan ta buɗe ta juye kusan rabi abinta, kuma koda ta gama saida ta kafa baki ta ɗan kurba. Uwar daka ta sake komawa ranta duk ya jagule. Itafa gaskiya zaman talauci yana cin mata tuwo a ƙwarya. Ta ƙosa Latisha ta tashi daga barci domin ta aika mata koda Range Rover ne abin banza ya dauke ta. Dole yanzu ta soma tunani irin na masu kuɗi, yadda Latisha tafi karfin E300 itama haka. Balle uwa uba zasu rinka zama gida ɗaya.

Barci yayi awan gaba da ita saida Inna ta tashe ta domin tayi sallar azahar. Sai a lokacin ta tuna kona asuba batayi ba tana chan tana jaraba. Mitsike ido tayi tana hamma, sanye take da wani leggings duk yayi gashi. Sai riga mai faɗin wuya. Maimakon tayi sallah saita shiga whatsapp. Anan taga Latisha ta saka status tana Airport tareda rubuta,"Goodbye Kaduna"

Kiranta tayi da sauri saboda bazata iya zaman gidansu Inna ba, sai taji yaki shiga saboda Latisha ta saka a flight mode. Nan ta koma ta kirata ta whatsapp. Bugu kusan biyar sai Latisha ta ɗauka.

"Besttttyyy !" tace cikin raha.

"Na'am, tun ɗazu nake kiran ki, ina kika shiga ?" ta watsa mata tambayoyi.

Ajiyar zuciya Latisha tayi saita soma shagwabanta na fama, "Besty ana takura min, yanzu ina jirgi zani Lagos maybe idan kin kirani bazai shiga ba, Wi-Fi nake amfani dashi a jirgi,"

"Eh kam wayanki baya shiga, amma ina neman taimakon ki Latisha. Uhmmm.... Dama gidan danake zama shiya riƙe ni tun ina yarinya, you know... Kingane irin abubuwan nan. Mama na da Babana duk sun rasu, ni kaɗai ce aka haifa," tace tana kuka.

"La haula Besty, na tausaya maki," tace cikin damuwa ƙarara.

Jan majina Rumasa'u tayi sai ta cigaba da magana, "Toh sun bar min dukiya mai tarin yawa, shi Chairman da kuɗina yayi campaign yace zai mayar min, amma kuma har yau shiru bai dawo min da komai ba. Shine zakiga kwana biyun nan ina cikin ƙarancin kuɗi though bamai yawa bane, kawai bana fita dubai da ummara ne. Jiya da nace gaskiya na gaji, jibe yanda yaransa ke facaka da kuɗade na amma ya hanani. Anan ya soma zagina harda duka na. Yanzu ya farfasa min jiki, bakiga yadda na zama ba, sai kuma ya koreni" kuka ta sake barkewa dashi. Kuma da gaske ne, wani zugi ta sake ji na inda Rahina ta jibge ta.

"Oh my God Besty, bansan me zance ba, haƙiƙa labarin ki akwai ban tausayi. Yanzun nan ina cikin jirgi na kunna Wi-Fi. Wallahi ina barci aka zo aka tadani wai na fito, sai naga wani bakin Range Rover sport gama gari, takaici motan ke bani. Driver ne ya miƙa min waya wai ana so ayi magana dani."

Ajiyar zuciya tayi saita cigaba, "Ashe Bukky ce take gayyata na Baby shower ɗinta, kinsan Mike Adenuga?" Latisha ta tambaye Kankana.

"A'a wallahi," ta amsa.

"Okay shine mai kamfanin Glo, dayake kinsan ya ciwo wasu bashi har aka kusan arresting ɗinsa, sai Daddy ya siya rabin kamfanin yanzu nashi ne, kawai dai Mike shine yake fitowa gaba screen amma ba nashi bane. Toh tun lokacin muka ƙulla zumunci dashi. Shine yarinyar sa Bukky take gayyata na baby shower ɗinta. Private jet ta tura ya ɗauke ni, bikinta a Brazil mukaje, so bansan daga Lagos ina zamuje ba."

"Dama naso ne na dawo wajen ki da zama," Kankana tace cikin murya ƙarami.

"Haba Besty ana tare, wallahi ko kaya ban ɗauka ba, na jikina ɗinnan kawai ne. Idan naje chan zan siya wani. Inata sauri ban duba waya ba, dama munje dake. It will be a nice change of environment bayan takaicin nan da kike ciki.... Sorry my dear,"

Tunani Rumasa'u tayi tanaso tace ko zata bata izini taje chan gidansu ta zauna. Maganar Latisha ta dawo da ita daga tunani, "Yanzu wani hotel kike na aika maki da saƙo?"

"A'a naje gurin wasu yan uwan mu. Talakawa ne, bansan harka da irin mutanen kawai dan ta kama dole ne, ni tsoro ma nakeyi kafin na kama cholera kinsan talaka da kazanta,"

"Gaskiya ya kamata na kubutar dake daga wannan jungle ɗin," Latisha tace a fusace.

Ashe duk maganar a kunnen Inna tana jinta, "Lallai Rumasa'u !" tace tana girgiza kai.

Wannan kenan!

#Naseera
#Rumasau
#Mahfooz
#DiyarDrAbdallah
#Dimpilicious
#FullyDimplated


Ainakatiti 💫




Continue Reading

You'll Also Like

14.4K 960 33
The transfer student couldn't me anything more special.But part of me want to help her.Why? Sooha thought to herself, she decided to help the new st...
54.1K 1.4K 21
You, an infamous serial killer in New Orleans, feed on the young. Your days are numbered, but soon you meet a charming man named Alastor. He fills th...
46.6K 1.4K 80
"𝐻𝑎𝑛𝑠𝑒𝑜𝑘𝑎𝑎,𝑎 ℎ𝑒𝑎𝑟𝑡𝑙𝑒𝑠𝑠 𝑝𝑠𝑦𝑐ℎ𝑜𝑝𝑎𝑡ℎ 𝑙𝑖𝑘𝑒 𝑦𝑜𝑢 𝑑𝑜𝑒𝑠𝑛'𝑡 𝑑𝑒𝑠𝑒𝑟𝑣𝑒 𝑡𝑜 𝑓𝑒𝑒𝑙 𝑙𝑜𝑣𝑒 𝑤𝑖𝑡ℎ 𝑠𝑜𝑚𝑒𝑜𝑛�...
62.7K 1.6K 10
مافيا - حب - قسوه - غيره renad231_5 مرت سنه والقلب ذابحهه الهجر ومرت سنه والهجر عيا يستحي الروايه موجوده في انستا : renad2315