SIRRIN B'OYE

De kulsuum_muhd_sadeeq

1.1K 75 14

cin amanar k'auna tare da dumbin Dana sani Mais

1
2
3
4
5
6
8
9
10
12
13
14
15

7

74 11 5
De kulsuum_muhd_sadeeq

★★★★★★
       *_SIRRIN ƁOYE_*
                        ★★★★★★

                *_NA_*

*_UMMA MUHAMMAD NAJAMAGA_*

*_wattpad:-kulsuum_muhd_sadeeq_*

🅿️8

"Daga yau ba sai gobe ba insha Allah zan aiwatar da wannan aikin kafin wancan jarababbiyar ta wai wai toki."
         Dukan su dariya suka sanya domin da shugaba suke.
"Yawwa Mommy shi yasa nake sonki nake alfahari dake wallahi."
          "Haba ! Ƴata in ban miki ba waye zai miki fatana dai muyi komai cikin *_SIRRIN ƁOYE_*  Wanda har abada asirin mu bazai to nuba.".      
     "Haba Mommy karki ji komai yanzu dai abunda ya rage ki samo mana yarinyar da zamuyi wannan aikin da ita."
" Karki ji komai my daughter nah."
      Hira suka ci gaba da yi irin ta uwa da ƴarta wacce suka shaƙu da juna.

*********

"Kinsan dalilin da ya sanya na Kira ki?.".
     
       Saida ta rausayar da kai sannan tace.

"Allah ya taimaka Fulani matar sarki saikin faɗa domin Ni baiwa ce kina da ikon aikata komai a kaina."

       Ai wannan furucin shine ya ƙarasa harda harɗe ƙafa sannan tace.

"Ai kinsan gimbiya maryam ƴata ko.?".

       Saida ta ƙara sun kuyar da kai sannan tace.

"Haba Fulani wa zai kasan ce cikin garin Kano yace baisan gimbiya maryam ba yarinya mai Adalci da tausayin Naga ba bare nida nake jakadiyar ki ai tamkar Tata haka nake.".

         Murmushi tayi shi yasa duk laifin da asabe take yake goguwa a gurin ta domin yadda take ƙaunar gimbiya.

"Yawwa to ita ce tazo zata tafi , Amman tana buƙatar baiwa guda ɗaya cikin bayin in nan.".

      "Allah ya ƙara miki nasara ince dai ba wani Abu bane ya faru.?".

     Murmushi tayi sannan ta kwashe duk yadda sukayi da gimbiya ta faɗa mata.

Itama dariya tayi sannan tace.

         "Wannan Abu mai sauƙi Amman Ina da shawara.".

"OK faɗi muji kinsan ke  akwai babban kai.".

       Cewar gimbiya dake sakkowa daga upstairs.

Dukan su dariya sukayi tazo ta zauna jakadiya ta gaida ta, sannan gimbiya tace.

         "Ke muke saurare  kinsan yau zan wuce da yamma.".

"Yawwa wannan abun yafi komai sauƙi Amman bada baiwa ba za muyi wannan aikin."

       Da mamaki dukan su suka bita da Ido suna son ƙarin bayani, itama Lura da hakan da tayi yasa taci gaba da jawabin ta.

"Abunda yasa wannan aikin baza muyi da bayi ba shine, duk wani munafurci da gulma yana gidan sarauta, bare mu da muke da mahassada a ƙarƙashin mu,baiwa ɗaya za mu ɗauka duka hankulan kishiyoyin ki zai yo kanmu, kinsan tambaya ta farko da zasu fara yiwa kansu ita ce ,da can gimbiya bata nemi yarinyar ba sai yanzu ? Lalle akwai wani *_SIRRIN ƁOYE_* mu da muke so mu aiwatar da komai cikin sirri Dan haka babu baiwa a wannan tsarin Ni ita ce shawara ta."

        Dukan su sunyi shuru da alama zancen ta ya shige su, Fulani ce tace.

"To yanzu ya za'ayi kinsan yau dai gimbiya zata tafi da yamma ko ? To a Ina zaki samo mana yarinyar.?"

      Dukan su kallon su suka maida ga jakadiya suna son suji mai zata ce.

"Indai wannan ne babu damuwa akwai wasu yara suna tare da maman su da baban su Amman masu ƙaramin ƙarfi ne, zanje nace umarnine daga fada Ni nasan wacce zan ɗakko."

        Da sauri gimbiya ta tari numfashin jakadiya da cewa.

"Fara ce ko ɓaka.?"

        Murmushi jakadiya tayi tace.

"Ita ba fara ba sannan ita ba baƙa ba gaskiya yarinyar mai kyau ce ta ƙarshe duk da baƙace."

       Tunda ta fara maganar gimbiya ta fara mata kallon lalle baki da hankali,saida ta gama sannan gimbiya tace.

"Wannan abun bazai iyu ba gaskiya,domin babu abunda yarima yake so irin baƙar mace bayya ma da kika faɗi cewa ita ba fara ba ita ba baƙa ba, Ni kyau baya damuna tunda nima kyakkyawa ce Amman Banda mai wannan color ɗin gaskiya."

        Murmushi jakadiya tayi tace.

"Haba gimbiya ya zanke baki kina ƙin karɓa, dalilin da yasa nace wannan yarinyar shine."

       "Wannan aikin da za'ayi muku dole mu samo kyakkyawa domin koda ƴar ko ɗan sunyi kamar ta babu damuwa,amman ɗaukar marar kyau in ƴaƴan suka biyo waccen tun daga nan zargi zai fara shigowa."

         "Wannan haka yake jakadiya Amman Ni abunda bana so wallahi yarima yana son baƙar mace kullum addu'an shi Allah ya bashi yara baƙaƙe masu kyau."

"Haba gimbiya koni da banyi boko ba ai nasan kissar da zanyi, ke har ƙara Bari zakiyi ya ganta ? Kullum inma gurin ta zaku sai kuke zuwa tare Dan gudun. Faruwar wani abun,bare ma yarima Almustapha mai zayyi da wannan kucakar ƴar matsiya ta."

        Dukan su dariya sukayi domin jin gimbiya ta samo musu mafita lokaci guda.

"Shi yasa nake alfahari kullum da kasan cewar ki jakadiya a gareni."

     Itama sai murmushi take ganin yadda ta sanya iyayen gidan ta  farin ciki.

"Kunga Bari na tashi naje  gurin iyayen yarinyar."

         "OK ba damuwa Amman karki daɗe dan kinsan anjima zan wuce."

"Karki damu yanzu zan dawo insha Allah."

         "Yawwa jakadiya adawo lafiya."

Har ta fita daga falon ta dawo,da mamaki dukan su suka kalleta.

         "Lafiya jakadiya?."

Mahaifiyar gimbiya ta tambaya tana kallon ta.

"Yawwa Amman Ni bazan dawo tanan da ita ba zan sanya a kaimu hanyar earport ɗin saimu haɗu a can kinsan banson wannan munafukan matan baban naki su lura.".

        "Gaskiya jakadiya kanki yana ja."

"Yi sauri lokaci na tafiya"

        Rafar kuɗi ta damƙawa jakadiya..

Suma hirar su suka dasa cikin so da ƙauna.


*******

Zaune suke shida matar shi da yaran shi, yaran shi guda 5 ne duka mata bashi da namji ko ɗaya duka mata ne.

          Kyawawa ne yaran na bugawa a jaradi gasu farare tass.

Daga yanayin yadda gidan yake zaka tabbatar da masu ƙaramin ƙarfi ne.

       Amman da alama sun samu tarbiya sosai.

Wata ce tayi sallama ta shigo gidan.

         Susu biyu ne kyakkyawa ne na bugawa a jaradi gasu farare tass kamar a taɓa su jini ya zubo.

Saida suka fara gaida iyayen nasu sannan suka nufi ɗakin su.

      Kwance suka taradda ita tana karanta novel a wayan ta.

Duka kaman su ɗaya domin babu wacce tafi wata kyau duk kyan su ɗaya.

        "Yaya Aminatu!! Kina kwance abunki kina karanta littafi kinga har mun dawo daga islamiya."..

Murmushi kawai ta musu tana kallon su bata ce komai ba.

         "Yawwa Malam labaran yace mu gaida ki."

Dukan su dariya sukayi Banda ita da take murmushi.

Sallamar jakadiya ce ta sanya su dukan su fito wa daga cikin ɗaki.

       Dake ta ƙware a makirci sai wangale baki take.

Bayan sun gaisa an kowa ya nutsu ya zauna sannan ta fara magana.

"Nasan zakuyi mamakin ganina anan to bakomai bane illa zuwa da nayi in Sanar muku da wani abun farin ciki."

           Duka sunyi shuru suna kallon ta babu Wanda yace ƙala.

"Yawwa ganin wannan halin da kuke ciki ya sanya Ni kullum kaiwa Fulani matar sarki zancen ku na cewa kuna naiman taimako,to yanzu Alhamdulillah domin har an baku kyautar. Gida a bayan gidan sarki mijin ki an bashi mai gadi ƴaƴan ki kuma zasu ke yiwa uwar gidan    sarki wato uwar manyan yaran shi maza Amman Ni ba ita nake yiwa hidima ba Amman ita tafi tausayi."

Dukan su kukan daɗi suka fara lokaci guda Allah ya ɗaga darajar su ta dalilin wannan matar.

Dukan su murna suke daga iyayen har ƴaƴan godiya suke.

       Aminatu kanta na sunkuyo a ƙasa bata ce musu ƙala ba.

Yawwa Amman suma suna naiman wata Alfarma a gurin ku

        "Haba mu kuma wacce Alfarmar ke garemu da har zasu tambaya mukasa yi muku."

"Yawwa to wannan yarinyar tasu da take masaurautar gumel ita ce take buƙatar wacce zata tafi da ita wancan masaurautar domin take ganin wani nata hankalin ta yana kwanciya, shine nace a cikin yaran nan ku bata ɗaya mana."

      Dukan su kowa cewa yake shi zaije Aminatu ko kallon inda suke bata yi domin miskila ce ta ƙarshe.

"To yara dai gasu nan Amman gaskiya a bata Aminatu domin tafi sauran ƴan uwanta nutsuwa."

*********

Kafin wani lokacin sun tare a gidan su na cikin fada inda gobe zasu fara shiga fada kowa cce a nuna mata inda zatayi aikin ta.

Ahaka Aminatu ta musu ba kwana jirgin su ya ɗaga sai masaurautar shugaba lol 😹 ...



*_TOFA JAMAA YANZU ZAAFARA GAME ƊIN FA KUDAI KU BIYONI_*



*_wallahi daga wannan shafin indai banga ruwan comments ba wallahi wallahi wallahi wallahi sau uku na rantse da girman Allah ya koma na kuɗi duk wacce zata siya ta siya wallahi indai babu comments kawai ku tanadi #200 ta siyan SIRRIN ƁOYE_*

Continue lendo

Você também vai gostar

32.5K 3.2K 104
Male Lead pr ဇာတ်လမ်းအကျဥ်း အရှေ့ဘက်နဲ့ဝေးတဲ့မြေမှာ မီချယ်လင် ကြယ်သုံးပွင့်အဆင့်သတ်မှတ်ချက်ကို အကြိမ်ကြိမ်ငြင်းဆိုထားတဲ့ ထူးဆန်းတဲ့စတိုးဆိုင်တစ်ခုရှိ...
1.1K 69 8
Its my imagination don't compare to reality
6.9K 259 101
☆ - Whatever tf happens in my life. Save so you never miss an update !! ☆ - None of the art I repost are never mine , lmaoo !!
19.4K 725 19
Tongkrongan bukan sembarang tongkrongan. Tongkrongan kami bukan kumpulan anak berandal, tapi anak-anak yang insyaallah, gemar beramal. [action, horo...