DIYAR DR ABDALLAH

By Aynarh_dimples

44.4K 6.3K 1.1K

Zuciyar sa yana mashi wasiwasi, abinda yake gudu shi ke shirin faruwa dashi. Bai taɓa samun kansa cikin wanna... More

One - Kankana
Two- Ruwan Sama
Three - Ummata
Four - IPhone
Five - Annoba
Six - Wanene Mahfooz I
Seven - Mahfooz II
Eight - Mahfooz III
Nine - Mabuɗin Zuciya
Ten - Kallon Kallo
Eleven - Farin Wasa
Twelve - Mugun Mafarki
Thirteen- Permanent Stalker
Fifteen - Ƙarfi Yaci
Sixteen - Bazan Barki Ba
Seventeen
Eighteen - Ni Ce Asalin Diyar Dr Abdallah
Nineteen - Naga Wajen zama
Twenty - Mijin Tauraruwa
Twenty-one - Annihilation
Twenty-two - Pound Of Flesh
Twenty-three - Ribar Haƙuri
Twenty-four Bazan Barka Ba
Twenty-five - Love That Hurts
Twenty-six -Rendezvous
Twenty Seven- Idan Tayi Ruwa Rijiya
Twenty-eight - To Be Tainted
Twenty-nine - By Whatever Means Necessary
Thirty - Sun Shuka Sun Girbe
Thirty-one- Miscreant
Thirty-Two - Déjà-vu

Fourteen - Rarrafen Carpet

1K 189 23
By Aynarh_dimples

Assalamu Alaikum Dimplicious Empire, naga ance yanzu na daina posting kullum. Anyway, afuwan ba laifi na bane. Lockdown ya tsagaita kuma na koma aiki. Yasa nace kuzo muyi shawara, typing ƙaramin shafi kullum kokuma dogo kamar yadda nake yi idan na kammala. Diyar Dr Abdallah nawa ne, kuma naku ne. So, let's discuss. #FullyDimplated

Rumasa'u tayi kiran duniya wayan Mahfooz amma bai shiga ba, ta rasa gane dalilin dayasa ya ƙaurace mata akan maganar da bai kama kara ya karya ba. Saidai abinda ta sani bazata karaya ba, tunda ta gansa kuma ta yaba dashi babu mai raba su. Tayi mashi saƙon text yafi sau hamsin. Ta Instagram kuma yafi a ɗirga. Harda hotunan datake ɗauka take tura masa. Idan yaga kyanta zai dubeta ya yafe mata.

Yanzu ta riga ta ƙure haƙurin Rahina, ko magana basu cika yiba sosai. Kawai ana zaune ne gida ɗaya. Dama dama Rahina tana ɗan mata magana, ita kuwa haɗe girar sama dana ƙasa takeyi. Tunda ta roƙe Rahina rancen dubu hamsin ta hanata shine ta ƙullace ta. Kuma ta ɗauki alwashin saita ɗanɗana mata koɗan ta.

Gantalin ta yanzu babu kama hannun yaro, kullum tana titi gidan abinci kala kala tareda yan group ɗin one love ana hutawa. Wata rana kuma tana dawowa da abinci irin su kaza da cupcakes, haka kamshi zai bi ɗaki tana ci tana waƙa ta hana Rahina. Gashi waƙar da takeyi mai ban takaici ne, "Wal bani wal baka, wal hanani wal ƙememe,"

Rahina dariya takeyi cikin ranta sabida in dai akan abinci ne tafi ƙarfi, amma kuma idan tazo da nata su Shawarma tana bama Rumasa'u kuma ko kunya bata ji ta karɓe ta cinye.

Cikin gantalin ta da shige shige ta haɗu da Latisha. Ita ta kasance asalin ajebo rarrafen carpet. Followers ɗinta a Instagram basu fi 250 ba wanda ita Rumasa'u tana kusan dubu tamanin. Latisha kuɗi gareta kaca kaca kuma bata san hayaniya. Wani ɗan group ɗinsu Rumasa'u na One Love zaije kai mata wayanta daya tayata gyarawa.

A marsandi tazo wajen Murtala square inda suke shaƙatawa domin ta karɓa. 2017 E300 4matic ne ɓaka gashi da tint. Motan ya tuna ma Rumasa'u da Mahfooz saboda kalarsa yake hawa. Balle dataga Latisha ta fito daga ciki, sai lokacin Rumasa'u ta tuna ya kamata ta iya tuƙi koba komai zata soma fakan idon su Rahina Bulala tana fita da motar su.

Rumasa'u bata bar wajen ba saida tace a bata number ɗin Latisha. Ta whatsapp tayi mata magana tareda gabatar da kanta cewa sun haɗu ɗazu. Sannan tace ita yar Adamu Fiya Fiya ne Chairman ɗin Kaduna North local government. Sai Kuma take cewa basu gaisa ba ɗazu da kyau ba kamar taga tana sauri, dariya Latisha tayi saita bata haƙuri.

“Dan Allah kuyi haƙuri banida wulakanci wallahi kawai raina a ɓace ne, ba'a wanke min motana ba gashi kuma zan karɓe wayan shine na hau motar kayan miya nazo,” tace cikin shagwaba kamar zatayi kuka. Ita Rumasa'u bata gane abinda take nufi ba, “Daga Murtala square kinje cefane ne halan?”

Latisha ajiyar zuciya tayi, “Ina nufin motar da ake siyo mana kayan miyan shine na tuƙa da kuka ganni ɗazu,” ta sake faɗa cikin takaici. Jikin Rumasa'u ne yayi mugun yin sanyi. Motan tana kimanta shi da miliyan ashirin koda bai kai ba kaɗan ne babu. Anan ta tabbatar da cewa duniyar nan ba daidai bane. Wasu suna kogin arziki su kuma suna ta tsiya. Idan wannan ne motan cefane, tana so taga asalin motar Latisha. Suna cikin wayan sai Rahina ta shiga ɗakin, tana sauraron tafsir ɗin Sheikh Jafar Adam ne na Wacece mijinta yafi. A fusace Rumasa'u ta kalleta tareda daka mata tsawa.

“Dalla malama rage muryan nan bakiga waya nake yi ba,” ta faɗi tana hararar ta. Mamaki ya soma dawainiya da Rahina, lallai Rumasa'u ta soma wuce gona da iri. Ita kuma Rumasa'u bataso abinda zai takura ma Latisha ne. Saboda yanzu ita zata zama aminiyar ta.

Rahina bata rage ba kuma bata amsa taba, Rumasa'u ne ta tashi tana tsaki, “Latisha dear, hold on bari naje garden domin muyi waya da kyau,"

Sunyi kusan awa ɗaya suna hira kala kala, Rumasa'u ta gama karanta Latisha tsab. Rarrafen carpet ce na bugun jarida. Bama a Nigeria suka tashi ba, shekarar su uku da dawowa. Kuma batada ma ƙawaye sosai saboda batada hayaniya. Rumasa'u sai lokacin ta lura yaran masu kuɗi akwai su da basaja. Sune rarrafen ciminti suka damu da yawan followers, sukam cin kuɗin iyayen su suke yi hankali kwance. Saidai ita Rumasa'u batada wani abin tinkaho face followers ɗinta. Sune uwa da ubanta. Suke siyan mata katin subscription, sannan kullum tana cikin karya wayanta ya lalace, haka za'a bata 10k ko 20k tana kashewa a hankali.

“Yaushe zanzo na gaishe da Daddy,” Rumasa'u ta gayyace kanta gidansu Latisha domin ta lura an shawaba ta. Duk zance tana faɗin Daddy ɗinta bata dai faɗi sunan maman ta ba.

“Ai baya nan amma nan da jibe zai dawo, yana Amsterdam yanzu,” tace damuwa cikin muryanta. Daga dukkan alamu tana kewar daddy ɗinta.

Anan suka gama zance su kala kala, Rumasa'u ta riga ta ɗauki alwashin dole ta ƙulla aminta na haƙiƙa da Latisha. Ta lura yarinyar batada matsala kuma bata gaji tsiya ba kamar Rahina. Abin da yafi bata takaici da Rahina taga alert ɗin dubu ɗari ya shigar mata waya. Shine tace ta ranta mata dubu hamsin domin tanaso tayi ankon wata sabuwar aminiyar ta. Amma Rahina ta hanata domin baƙin hali.

Tasan tabbas da Latisha ne bazata hanata ba. Sai yanzu da gane mutane kaɗan ne idan suka bar talauci suka koma arziki suke barin tsiyar dake jikinsu. Koda yake su Rahina basu taɓa talauci ba, dama aji ya hada su Islamiya kuma duk makaranta akwai yaran talaka dana masu kuɗi.

Kashe gari Latisha ta saka wani hoto tana zaune akan dinning table da kofin shayi. Track suit ne wanda ya tsaya dai dai cibiyar ta sai dogon wando, shi amma ya rufe cibiyar. Dayake tanada yalwataccen gashin kai haka ta ɗauki hoton babu kallabi, saita saka caption "I miss Paris"

Rumasa'u batayi wata wata ta ɗauki hoton ta saka a nata shafin, anan Latisha ta bita private tana gode mata.

"Haba besty, babu damuwa mun zama ɗaya yanzu,” tace tana washe baki. “Saidai rigar ki tayi min kyau,” ta sake faɗi.

“Ai ba tsada, $100 na siya a Walmart. Ba wani designer bane. Gucci ne gama gari,” ta faɗa cikin ko in, “kalar ce tamin yasa na ɗauka. Idan kinaso zan ajiye maki.”

“Kai besty harda dawainiya,” ta faɗa kamar bata son rigar alhalin shoki ta miƙe tanayi.

“Ina da wannan abubuwan, kuma bana fita balle na saka su. Gashi kuma banida ƙawaye da zanba.... Idan kina so akwai jakar Alexander Mc Queen duka saina haɗa maki dashi, saidai kiyi hakuri baida wani tsada shima $800 na siya,”

Nan take Rumasa'u tayi fito saboda jin daɗi kuma kamar ta ɗuka tayi sujjada dan murna. Soyayyar aminta ta da Latisha ya shiga ranta kana haushin Rahina takeyi. Jibe rannan danta saka mata abaya shine ta kanne fuska.

Bayan sun gama wayan sai Rumasa'u ta kwanta tana tunani kala kala yadda zata kwakule Latisha. Yarinyar akwai sangarcin ga rashin wayyo. Ko maganar ta cikin shagwaba takeyi kamar zatayi kuka. Anan Rumasa'u ta ɗauki alwashin zata koya mata darasin da bazata taɓa mancewa ba. Zatayi mata welcome to Nigeria inda bazata sake yarda da kowa ba.

Anan dibara ya faɗo mata, saita saka "Goodbye fans" a status ɗinta. Latisha wanda koda yaushe batada aiki tana online har cikin dare saita bita private domin taji dalili.

Sai Rumasa'u tace wayanta yana bata matsala, haka kurum sai tayita kashewa na rashin dalili. Gashi kuma tanada issue da account ɗinta balle takai gyara,”

Latisha bata kawo komai cikin ranta ba, tace mata nawa ne gyaran. Anan tace dubu dari da ashirin ne. Yanzu tanada cash 20k a hannunta. Latisha tace kada ta damu zata bata kuɗin.

Anan ta soma bata labarin wani saurayin ta data tsana. Jiya yazo ya bata dubu dari biyu, abin yayi mugun ɓata mata rai saboda ya raina ta. Ita sanda take Paris bai kai kuɗin datake gyaran gashi ba. Harda hoton sabbin yan Naira dari biyar ta tura mata ta gani.

Da rawar jiki Rumasa'u ta kirata a waya, haƙuri ta soma bata. Ita kuma Latisha sai masifa takeyi, tanata cewa bata san raini. Ita ba abin wulakantawa bane da zai miƙa mata 200k. Sai tace idan ta fita zatayi ma Rumasa'u deposting cikin account ɗinta. Ganin kuɗin cikin gidan yana sakata ruɗani da tashin hankali. Rumasa'u taso tace mata zata je ta karɓa, sai kuma ta tuna abin babu aji. Gwara ta haƙura har a saka mata kafin Latisha ta gane akwai tsiya tareda ita.

Anan ta tambaye Latisha me take so idan zata zo gidan su, tace ita bata taɓa cin abincin Nigeria sai jollof ɗin shinkafa, da zasu dawo an taho da Chef wanda shi asalin ɗan India ne. Shi ke masu abinci kala kala.

Yanzu Rumasa'u tunda tasan abinci shine take so, za taje domin ta samo recipe wanda zata bama chef yayi masu suci.
A gurguje Rumasa'u taje gidansu Mallam a karo na farko, bata lura da cewa suna ta haɗa kayan su ba zasu bar gidan. Mallam ya siya wani gida mai dakuna ciki da falo uku. Saiya saka a bude mashi wasu dakuna aka mayar mashi flat. Yanzu ana ta aikin ne, sun kusan tashi.

A uwar daka taga Inna tana tattaro kayan da zata wanke domin kada aiki ya chaɓe masu lokacin tashi. Inna taji daɗin ganin Rumasa'u sosai, dama tunda ta tafi tunani kala kala takeyi. Sau biyu tana zuwa gidan Chairman Fiya Fiya taji lafiyar Rumasa'u daga bakin masu gadi. Daga su ce mata yanzu ta fita ko yanzu ta dawo. Wannan kawai ya ishe ta samun natsuwa tunda Rumasa'u tana zaune lafiya.

“Inna wallahi na haɗu da wata yar gayu shine takeso na koya mata abincin gargajiya, dayake ba a Nigeria ta tashi ba, asalin yar masu kuɗi ne. Ko hausa bata ji sosai, gatada da bala'in mutunci" tace tana murmushi.

“Dan bata jin hausa shikenan ta zama mai kuɗi, Rumasa'u kiji tausayina kada ki jawo min abin magana dan Allah,” Inna ta gargaɗe ta.

“Haba Inna sai kace baki yarda dani ba, ai na canza halina wallahi,” tace. Nisa tayi saita cigaba da magana, “Nidai ki gaya min yanda ake dambu mai kyau ɗinnan, kingane dai wanda yaran masu kuɗi zasuji daɗi sosai, kinga zan maki tukwici mai tsoka a dubu darin dazata bani,”

“Dubu ɗari kuma?” tace cikin al'ajabi.

Dariya Rumasa'u tayi tana rangaji dakai, “Eh Inna, bafa komai bane wajenta, bakiga motar da ake zuwa cefane ba gidansu. Sai ya siya nan gidan sau dubu. Inna yarinyar ba kalar da kika saba gani bane. Rarrafen carpet ce tafi Rahina gogewa,” saita bushe da dariya data tuna Rahina tana yanayi da Bulala, “Haba wane uban Rahina, baza'a ma haɗasu ba,” anan ta hange wani mayafin ta data mance dashi cikin kayan Fa'iza. Da sauri taje ta ɗauki abinta tasa cikin jaka.

Rai baiso ba Inna ta gaya mata duk yadda zatayi, da waya takai bakin Inna tana recording, taso ta rubuta sai tayita harɗewa saboda ba wani rubutun kirki ta iya ba. Bayan sun gama sai Inna tayi ajiyar zuciya ta kalle Rumasa'u.

“Mallam ya zama principal a makaranta su,” tace murna fal ranta. Anan Kankana ta bushe da dariya, mamaki takeyi yadda Inna ke murna akan wannan abin kunyar. Meye abin alfahari a zama principal ɗin primary? Dama private ne makaranta kuɗi, nawa ne duka albashin a shekara? Bazai wuce wanda Latisha zata siya mai da kayan kwalliya dashi ba.

"Tabdi” tace tanata dariya. Murna tayi data bar zaman nan gidan, idan ba haka ba ina zata ajiye Latisha. Tabbas tasan idan Latisha tazo gidan nan zata kwashe cutar cholera. Duk ya tsufa gashi ginin ƙasa. Kana ganinta kasan tsakaninta da gidan ƙasa sai a TV. Wannan yarinya batayi kamada tana zuwa layin talakawa ba balle ta gani.

Takaicin duniya ya mamaye Inna, tasan Rumasa'u batada hankali amma bata san yakai haka ba. Koba komai ba'a canza ma tuwo suna. Ubanka duk munin sa naka ne, menene aibu dan tayi mashi fatan alheri. Daga nan wata rana idan yana gaba zai iya komawa jami'a yana koyarwa.

Dayake Mallam ya bada tsoffin kujerar su domin a gyara masu, idan sun tashi tafiya sai su tafi da sabo. Anan Kankana ta ƙare ma ɗakin kallo fes.

“Dankari,” tace a filin. Mamakin yadda wannan sabon mukamin takeyi, jibe yadda yazo masu da tsiya. Jakarta ta buɗe sai taga wani ɗari biyu sai kuma dubu ɗaya. Ajiye ɗari biyun tayi gefen Inna, su siya kuka da ɗan kifi su mitsike cikin miya kafin yunwa ta kashe su saita tafi.

A hanya cikin Napep tana duba group ɗinsu na One Love, sai taga ana cewa za'a yi taron jin daɗi. Mutane sukayi ta ajiye dubu hamsin da ɗari. Matsiyata cikin su ne suka ajiye ashirin. Za'a yi a Abuja Ibro Grande Hotel ne.

Tunani ta fara yi kala kala inda zata samu dubu ɗarin gaggawa ta aika domin kada a raina ta. Koda ta isa gida taso tace ma Rahina ta bata dubu ɗari nanda gobe zata bata amma ta fasa. Kuɗin da Latisha tace zata bata take jira yanzu.

Dataje ajiye gyalen data ɗauko daga wajen Fa'iza, sai taga dubu dari na Rahina. Anan ta yanke shawarar tayi amfani dasu sai gobe idan Latisha ta bata saita mayar mata.

Nan ta kwasa ta kai masu sunata kiranta babban yarinya.

***

Ita kuma Nurse Jamila hankalin ta yaki kwanciya tunda aka sace Naseera. Kullum sai taje gidan Dr Abdallah ta samu Hajia Binti domin tayi mata jaje tareda fatan alheri. Yanda suka shiga tashin hankali sosai saita tausaya masu. Jibe yanda sukeda ɗawainiya da yarinyar da ba nasu ba. Saboda ita kaɗai ce tasan asalin inda Naseera ta fito kuma da dalilan faɗawan ta hannun Dr Abdallah.

Nurse ba yau ta saba wannan sana'a ba, ta shahara wajen musanyan yara tareda sace su. Kuma idan mutum baisan ɗansa zai bar mata sai ta siyar. Naseera ce kawai wanda ta sace kuma take zaune kusa da ita. Tunda yanzu ta koma aiki Abdallah Specialist tana ganin Naseera kullum. Bawai tana nadamar sana'ar bane kokuma zata bari. Kawai dai tausayin Dr Abdallah ne.

Tana zaune a falon ta, tsire wanda yasha albasa da cabeji take ci. Hannunta ɗaya yana riƙe da wayar hannu. Latsa wani Number tayi ta soma kira, bugu biyu sai aka dauka.

“Hello, waye ?” aka ce ta ɗayan bangaren a wulakance.

Murmushin takaici Nurse Jamila tayi, dama matar tun sanda suka haɗu batada mutunci gashi kuma har yau bata canza ba, “An sace yarki.... Naseera nake nufi, wanda kika barta a wajen Dr Abdallah,”

Wannan kenan?

#Naseera
#Rumasau
#Mahfooz
#DiyarDrAbdallah
#Dimpilicious
#FullyDimplated

Ainakatiti💫

Continue Reading

You'll Also Like

13.1K 2.1K 22
جۆنگ کوک:بە نەفرەت بیت وازم لێ بێنە چیت لە من دەوێت تایهیۆنگ:ششـ ئازیزم بۆچی هاوار دەکەی ئارام بە بۆ باروودۆخت خراپە ༄༄༄༄༄༄༄ جۆنگ کوک:تـ تۆ چیت کرد ت...
131K 28.3K 96
Title - Dangerous Personality Author - Mu Gua Huang MC- Xie Lin x Chi Qing Chapter 161 + 2 extras ထူးဆန်းသည့် ပြန်ပေးဆွဲမှုတစ်ခုအပြီးတွင် ချီချင်းတစ်...
Peer E Kamil By storybyaina

Mystery / Thriller

31.2K 388 23
salar sikandar & imama he waits 9 years for her bad boy become religious for a girl by = umera ahmed
104K 3.5K 40
Y/N was a teenage introvert who enjoyed having her own space and being alone. She loved listening to music in her room, which was a great escape for...