DIYAR DR ABDALLAH

By Aynarh_dimples

44.3K 6.3K 1.1K

Zuciyar sa yana mashi wasiwasi, abinda yake gudu shi ke shirin faruwa dashi. Bai taɓa samun kansa cikin wanna... More

One - Kankana
Two- Ruwan Sama
Three - Ummata
Four - IPhone
Five - Annoba
Seven - Mahfooz II
Eight - Mahfooz III
Nine - Mabuɗin Zuciya
Ten - Kallon Kallo
Eleven - Farin Wasa
Twelve - Mugun Mafarki
Thirteen- Permanent Stalker
Fourteen - Rarrafen Carpet
Fifteen - Ƙarfi Yaci
Sixteen - Bazan Barki Ba
Seventeen
Eighteen - Ni Ce Asalin Diyar Dr Abdallah
Nineteen - Naga Wajen zama
Twenty - Mijin Tauraruwa
Twenty-one - Annihilation
Twenty-two - Pound Of Flesh
Twenty-three - Ribar Haƙuri
Twenty-four Bazan Barka Ba
Twenty-five - Love That Hurts
Twenty-six -Rendezvous
Twenty Seven- Idan Tayi Ruwa Rijiya
Twenty-eight - To Be Tainted
Twenty-nine - By Whatever Means Necessary
Thirty - Sun Shuka Sun Girbe
Thirty-one- Miscreant
Thirty-Two - Déjà-vu

Six - Wanene Mahfooz I

1.2K 158 23
By Aynarh_dimples

Wanene Mahfooz?

Mahfooz Abubakar Gwaiba yaro ne tilo a wajen Iyayen sa, Abubakar da Phalida. Dan asalin Zaria ne, dangin mallawa wanda ke zaune a gidan Gwaiba. Mahaifinsa ɗan kasuwa ne. Ya shiga sana'ar kasuwanci bayan ya kammala NCE a FCE Zaria inda ya karanta Maths/Chemistry.

Ba kowa ya koya masa sana'a ba illa yayansa Alhaji Sani Kwari. Shima Alhaji sani zuwa yayi Kano tun yana dako da zama a matsayin yaron shago harya kai shi ga samun nasa. Shi baiyi karatu ba. Yanzu haka yanada shaguna guda goma Sha shida a kasuwan Kwari dake Kano. Shi kuma Abubakar a kasuwan Sabon gari dake Zaria yake nashi, saidai yaje Kano ya saro.

Anan ne ya haɗu da Phalida har sukayi auren soyayya. Bayan shekara ɗaya da aure sai Allah ya albarkace su da samun yaron su Mahfooz. Saidai Phalida bata haihu da kanta ba. Cs akayi mata. Koda ta koma gida cikinta bai bar ciwo ba haka yayita ruwa yana takura mata.

Phalida batada aiki saina ziyarar asibiti, amma ya ki ci yaci tura. Haka dai suka cigaba da rayuwa yau ciwo gobe sauki. Lokacin da Mahfooz yakai shekara hudu sai Phalida ta sake ɗaukar wani cikin. Amma dayake babu rabo wajen haihuwa ta rasa ranta tareda babyn.

Hankalin Abubakar yayi mugun tashi, basuda iyaye balle a riƙe Mahfooz. Sannan kuma Alhaji Sani ne kawai namiji a ɗakin. Sauran duka mata ne. Yasan ba kasafai bane miji ya yarda mata ta ɗauki nauyin yaron daba nata ba. Koda agola ne balle yaron ɗan uwa.

Alhaji Sani ya cema Abubakar ya dawo da Mahfooz Kano wajen matarsa domin ta raina Mahfooz. Tunda yanzu haka yanada yara shida kuma autansa bata wuce tsaran Mahfooz ɗinba.

Duka yaransa shida mata ne, baida yaro ko ɗaya namiji. Shima zaiso Mahfooz ya zauna dashi domin ya koya mashi kasuwanci kala kala.

Matarsa Hajia Fauziyya yar ƙabilar Beri Beri ce na jahar Borno. Kuma a lokacin yaranta shida, akwai Aisha, Maryam, Zubaida, Anisa, Sadiya sai Zanira.

Alhaji Sani bai taɓa nuna ma Fauziyya cewa rashin haihuwar ƴa mace yana damunsa ba. Za'a iya cewa itace ta cusa masa ra'ayin saboda halinta. Sanda aka kai Mahfooz gidan babu laifi tana faram faram dashi. Saboda tana tunanin Abubakar zaiyi aure nanda nan su tafi. Ya girma Zanira da shekara ɗaya amma komai tare ake masu.

Harta Abubakar idan yaje Kano yana siyan masu kayan wasa iri daya baya nuna wariya. A gidan Alhaji Sani na Rijiyar zaki ilimin addini dana boko wajibi ne akan kowa. Yace ba'a taɓa daina neman ilimi. Harta shi yana tsayawa karatu a masallaci bayan Isha. Yasa itama Fauziyya tana zuwa Islamiya sannan kuma ta koma Sa'adatu Rimi inda tayi NCE domin ta ƙarasa.

Wata rana lokacin Mahfooz yana shekara shida Abubakar yace ya kamata ya sake aure domin ya dawo da Mahfooz Zaria wajensa. Har anje ankai kuɗin gaisuwan. Yaje kano domin yaga Mahfooz sannan kuma ya taho da kayansa na sana'a wanda yayi order.

Sun wuce tashan yari da ƙadan suka samu hatsari babu wanda ya rayu cikin motan saboda kurmus suka ƙone. Anan Alhaji sani ya sake jin tausayin Mahfooz sosai. Tun daga lokacin ranar Alhamis da Juma'a idan babu Islamiya zai aika a wuce da Mahfooz kasuwa.

Alhaji Sani yana bala'in alfahari da Mahfooz, yaron baida kiwiya shima yana jin daɗin zaman shagon. Gashi idan anzo miƙa leda ko compliment card shi yake maza ya bada. Sannan idan yaje gida yayita bama Zanira labarin yadda kasuwa yake sannan kuma da rana suna cin balagu da shinkafa kokuma kaza.

Babu abinda Alhaji sani ya raga ma Fauziyya dashi wajen fannin abinci. Fridge ɗinta yana ambaliya da nama dasu kifi. Saidai Fauziyya tanada wani abu, akwai ta da kyashi. Tanada bala'in kallon abin mutane. Ga kyamar talaka. Bata bada sadaka komin kankantar sa.

Batasan taga Alhaji Sani yayi wani abin alheri, bataso taga an bama makota taimako. Shi karin kansa zakka da ake bada wa bayan anyi ramadan na hatsi da ba dole bane bazata bari a bada ba. Abinci saiya lalace yana wari zata bama almajirai. Dama kawaici take ma Mahfooz, yanzu kuma haƙurin ta ya gaza.

Yanzu yakai idan Alhaji Sani zaiyi abin alheri saidai idan bata nan ko a ɓoye, idan ba haka ba ta rinka mita kenan tana kumbure kumbure. Ba mutanen waje ba, harta ƴan uwansa ko nata bata ƙaunar taga an ɗaga su. Wani ɗaci ɗaci takeji idan yayi abin arziki.

Sau da dama tana ma mijinta ƙorafi akan meyasa baya zuwa da sauran yaransa kasuwa. Saiya yace mata ai kasuwa ba wajen mace bane, anan zata fara cewa ai ba maza ke saida robobi ba. Duk mata ne suke siyarwa a kasuwa.

"Toh ni robobi nake siyarwa?" ya amsa mata dashi. Anan ta ja baki tayi shiru tana gunguni. Tun daga nan ta soma canza ma Mahfooz, sunada mai aiki amma Mahfooz ke wanke kayan sa. A cewarta tana koya masa tausaya ma mace.

Bayan nan kuma ta soma ƙorafi akan yadda yake jan Mahfooz a jiki, duk yadda zaiyi baza'a ce ɗansa bane. A haka Alhaji Sani ya soma tunanin gwara ya ƙara aure saboda gaskiya yanaso yaransa su gaje shi a kasuwanci.

Haka ya samu wata bazawara Amina suka sasanta kansu. Ta taɓa haihuwa mace da namiji sai mijinta ya rasu. Hankalin Fauziyya yayi mugun tashi. Saboda Amina ta haifa namiji, kishin data keyi da Mahfooz yanzu zata soma yi mai kyau da kuma mai hujja.

Yaran Fauziyya suna kiran Amina da Anty Amarya, sau da dama tana hanasu ce mata Anty amma suka ƙi. A cewarta Amina aiba ƙanwar uwarsu bace.

A kwana a tashi sai ga Amina ta ɗauki juna biyu, anan hankalin Fauziyya ya tashi. Itama saida tasan yadda tayi ta ɗauka ciki. Fargaba fal ranta kafin Amina ta haifa namiji Alhaji Sani ya mayar da duka soyayyar sa wajen yaron.

Mahfooz yana shekara bakwai Amina ta haifa ɗiyarta, an saka ma yarinyar suna Zainab. Alhaji Sani ya kawo ba zai taɓa samun namiji ba sai ya cire ransa. Lokacin ita kuma Fauziyya tanada cikin wata bakwai. Ita ta riga ta ɗauki alwashin cewa wannan karan abinda zata shigo dashi gidan nan ɗa namiji ne.

Tuni Fauziyya ta kore Mahfooz a ɗakinta. Sannan ta gargaɗe shi akan kada ya gayama Alhaji Sani. Yanzu sabon ɗakinsa shine wani kango cikin gidan, two bedroom ne Alhaji yake gina ma kansa. Yayi roofing amma baisa ceiling ba. Ginin yana cikin farfajiyar shima. Da gangan Fauziyya zata kai wani tarkacen da bai kamata ba ta ajiye duk domin ta takura ma Mahfooz. Gashi kuma ceiling ɗin ɗakin yana yoyo.

Idan anyi ruwan duniya a haka zai malale ƙasa. Saidai Mahfooz ya rakuɓe gefe ko ya hau wani tarkacen. Idan ka ganshi da safe kamar wanda aka firgita.

Wata rana tana zaune a gida sai ga ƙanwarta watau Autan su tazo wajenta. Lokacin waya bai yawaita ba kuma tana neman taimakon ta. Ita Auta tana aure a Kaduna ne. Kuɗin hayan su ne ya kare kuma an basu notice. Gashi kuma tanada ciki mijinta kuma baida karfi.

Abinka da ɗan uwa saita kama hanya takanas ta Kano taje wajen Fauziyya. Abin yayi mugun bama Fauziyya haushi, saboda sam bataga dalilin dayasa Auta zatazo wajenta ba. Ita a ganinta wannan yanada daga cikin ƙalubalen aure. Saita zauna gidan ta taji da matsalolinta. Jarabawan aure ne.

Da Auta ta shigo da ɗan buhunta, sannan kuma ga albasa wanda tayi masu tsaraba. Fauziyya ta hakince akan 3 seater tana shan Kankana da Abarba. Ga masu aiki biyu gefen ta, ɗayan tana ɗan danna mata ƙafa saboda tace yayi mata tsami.

Sanyin AC ke tashi ga kuma turaren wuta sai kamshi yakeyi, India take kallo Maine Pyar Kiya. Sabon film ɗin Salman Khan Wanda ya fara yi.

Bayan Auta tayi sallama cikin falon, saita nufa kujera da fara'ar ta zata zauna. Da sauri Fauziyya ta dakatar da ita tana taɓe baki. Yadda kasan ba jinin su ɗaya ba.

"A'a zauna a ƙasa kujerun sabbi ne, kafin ki shafa masu kuɗin cizo," tace mata. Murmushi Auta tayi saita zauna a ƙasa. Dama bawai wajenta tazo ba, wajen mijinta ne.

Bayan ta Labarta mata me ya faru, anan Fauziyya ta soma sababi.

"Inace ke kika ce kina sanshi. Toh meye zaki kawo min matsalar ki? Ni ma da kika ganni da nawa matsalar amma bakiga ina yawo gari gari ina shela ba." ta faɗa a hasalce, saita ɗauki kankana ta watsa baki. Ko tayin ruwa batayi ma Auta ba balle tayi tunanin shan kankana. Ga kuma bala'in yunwar dake addabar ta.

"Yaya kiyi haƙuri, babu shine ya jawo haka. Nima bazan so yau na tona ma mijina asiri ba. Amma yau wata shida ba'a biyasu albashi ba. Shine nace tun ina da sauran ƙarfi bari nazo. Rance zaki bamu ana biyansa zan hau mota na kawo maki,"

"Yo ina kike so na samu kudi? Iyye Auta nace a ina kike so na samu kudi? Shi kenan dan ina zaune babban gida sai kiyi tunanin inada shi? Koko ina sana'a ne," ta fara masifa tana wurwurga hannaye. Anan ne wanda ke mata tausa ta murɗe mata ƙafa. Aikam batayi wata wata ba ta yanka mata mari.

"Yar tselan uwa ke kuma kashe ni zakiyi?" ta koma kanta. Saita sake kallon Auta tana yamutsa fuska, "Gaskiya Auta banda ko sisi, ga dubu daya ki hau mota ki koma gida amma bayan nan banda abinda zan taimaka maki dashi."

Kuka Auta ta fashe dashi, ko kuɗin motan da tayi amfani dashi rance tayi, taso tace ma Fauziyya jibe daham ɗinda ke kirjinta koshi ta cire ta siyar. Amma tayi shiru da bakinta. Rashin Imanin Fauziyya mamaki yake bata, yau da ace itace bazata tambaya ba zata rinka taimaka mata ba. Karo na farkon data tambaya tama hanata.

Kallon Bilkisu tayi mai aikinta tace suje da kayan Auta chan ɗakin su , anan zata kwana. Da kyar Auta ta iya miƙewa domin jiri yana ɗibanta. Azabtaccen yunwa take ji sannan ga ƙishin ruwa. Anan ta yanke shawara bari taje famfo na waje domin tasha.

Haka ta kafa baki akan famfo tayita ƙyanƙyama. Har saida amai ya soma zuwan mata. Anan ne taga Amaryar Alhaji Sani Amina. Ita kuma tazo shanya kayan Zainab. Murmushi Amina tayi mata saboda taga kama da Fauziyya. Saidai wannan tayi fari fat kamar fatalwa ga rama duk ta tsotse. Ita kuma Fauziyya tanada jiki sosai ta cika kujera.

"Ke yar Uwar Yaya Fauziyya ne halan?" Amina ta tambayeta. Dakai Auta ta soma amsata saboda tana tsoron kada Fauziyya ta fito taga suna magana tayi mata tas.

"Allah sarki, kuna kama wallahi. Bamu taɓa haɗuwa ba, ni ce Antin su Zanira." sai Amina ta leƙa hanyar ɗakin Fauziyya tanada dubawa ko tana zuwa. Da bataga kowa ba saita ce suje taga yarta yau sati biyu da suna.

Amina tanada kirki ga fara'a, amma Auta bataso ta shiga tsakanin ta da Fauziyya. Yanzu akan wannan ɗan magana da tayi saita ƙulla gaba da ita.

Akan kujera ta umurceta ta zauna, saita janyo mata centre table gabanta. Anan ta kawo mata lemun kwali sai shinkafa da wake da kaza. Shi kansa farantin data ɗaura abin kallo ne. Ta karramata sosai. Tun ta kasa cin tana ɗari ɗari. Haka ta sake jiki taci. Dama rabon dataci abu tun farau farau data sha da safe.

Ga sanyin AC yana dukanta, anan ta soma gyangyaɗi. Duk ta galabaita saboda kuɗin motan ta bai kai ba, da kafa ta ida ƙarasawa wajen. Ihu taji sai suka duguma suka fita waje.

Mahfooz ne ke ihu yayinda Fauziyya ke kilarsa, ta shaƙe mashi kwala tana zabga mashi muciya tana yi kuma tana zagin ubansa.

"Dan ubanka zaka bani kuɗi na ko saina kashe ka?"

"Wallahi Mommy ban ɗauka ba," yace yana kuka. Anan ta sake zabga mashi mari tana sababi, "Uban waye Mommy? Banace ke daina kirana da sunan ba? Nafi karfin na haifa ɓarawo."

"Kiyi haƙuri Anty, wallahi ban dauka ba,ni bana sata," ya sake faɗi.

"Zakayi bayani yau ɗinnan, daga kaina bazaka sake sata ba" kallon Bilkisu tayi sai ta ce mata ta ɗebo mata ruwa. Anan ta sheƙa ma Mahfooz kana ta soma jijiga shi. Auta har rufe idonta tayi saboda zaluncin yayi yawa. Shi kuma kuka yakeyi yana karkarwa tareda nanata baya sata

Anan Auta ta soma magana a hankali, "Yaya kiyi haƙuri haka. Yaro ne wallahi."

"Bazan yiba, munafuka tunda baki dashi ai baki san darajar suba. Banza shashasha. Karki kuskura ki saka min baki a zancen family ɗina" ta faɗa tana nuna mata ɗan yatsa.

Inda sabo Amina ta saba, kusan kullum ita take bama Mahfooz abinci koya kwana da yunwa. Yaron yanada zurfin ciki duk abinka bazai gaya maka ba. Fauziyya ta hana shi zaman falo, toh dayake Alhaji Sani yana zuwa karatun dare sanda ya dawo yara sun watse. Duk tsammanin sa yana tareda yaran Fauziyya.

Girma kaɗan yake so ya sake yi lokacin yana tunanin ya gama 2 bedroom ɗinsa, daga nan saiya zauna ɗaki ɗaya shima yana ɗaya. yanzu shekarar sa bakwai bai kai kwana shi kaɗai ba.

"A ina kika ajiye kuɗin bari naje na sake dubawa?" Auta tace. Harara Fauziyya tayi sannan tace, "kije showglass ɗina ki kuɗe roses ɗin. Na ƙasan anan na ajiye."

Auta ta shiga falon ta duba, sai ga kudin. Naira hamsin a ciki.

"Yaya wannan ne kuɗin?"ta nuna mata. Kallo tayi taga tabbas shine. Dama ta ajiye ma Zanira ne domin ta siya tuwan madara. Ita kuma bata duba da kyau ba tace babu.

Fauziyya batayi dogon nazari ba ta soma kilarsa. Duk rawar ɗari yakeyi. Sauran ruwan boƙatin ta watsa mashi sai tayi tsaki ta wuce. Auta ce ta rungume shi, nan ta tambaye shi inda kayansa yake domin ya canza. Mamaki tayi sosai da taga cewa kayansa na uncompleted ginin da Alhaji ya dakatar da ginawa. Imani ta sake yi tareda sake tsorata da Fauziyya.

Canza mashi kaya tsab tayi, duka kayan akwai datti alamar shi ke ma kansa wanki. A farfajiyar taga Bilkisu inda ta ce ta bata sabulu. Anan ta famfon waje ta wanke ma Mahfooz kayansa tas. Sannan duka yanan gizon dake ciki saita cire masa. A gaban wajen tayi sallah la'asar.

Amina ta turara gurasa da tsire ta kai mata. Auta ta lura yara na tafiya Islamiya amma banda shi anan ta tambayi dalili.

"Anty Fauziyya tace idan Abba baya nan kada na kuskura naje, na zauna a gida kila zata aike ni." cikin hasala ta ɗauko uniform ɗinsa wanda ya soma bushewa a igiyar shanya ta miƙa. Naira goma dake hannunta kuɗinta na karshe ta miƙa masa ya siya biscuit. Ɗa na kowa ne kuma bakasan wanda zai riƙe maka naka ba.

Rayuwa baida tabbas idan ta mutu zata so a riƙe mata nata cikin aminci. Ashe duk abinda takeyi Fauziyya tana kallo. Batace mata komai ba sai da tazo wucewa ɗakin masu aiki da Magrib. Anan tasa Bilkisu ta fitar mata da kaya.

"Auta bazai yiwu kina yar uwata na jini ba kina munafunta ta. Dan ubanki me ya kai ki ɗakin kishiya ta?" tace tareda saka hannu kugu. Abin yayi mugun bama Auta haushi amma ta dake.

"Wallahi Yaya barka naje mata ba komai ba," saita fara kuka.

"Wannan ke ya shafa amma ni ko'a kwalar rigana. Ki koma ɗakin Amina kokuma kije kango da Mahfooz amma kin gama shiga min ɗaki." saita ja tsaki.

"Wallahi Yaya ba haka bane, kiyi haƙuri bansan ranki zai ɓaci ba"

Dariyar ƙeta Fauziyya tayi, "Nifa bai dameni ba. Allah ne ya nuna min maƙiya na a fili. Ai naga take taken kashe min aure kike so kiyi, kuma nagode. Kina so Alhaji ya sakeni muyi zaman talauci..." bata ƙarasa ba sai ga Alhaji Sani ya iso.

Tayi mugun razana tunda bata tsammanin sa yanzu. Auta ce ta durƙusa ta gaida sa. Cikin fara'a ya amsa.

" Ya Mai gidan naki? " yace." Lafiya lau " ta amsa.

" Muje daga ciki mana, me kike yi bakin kofa kamar bakuwa."

Anan ta bishi falo, Fauziyya banda harara bata mata komai. Anan yayita janta da labarai kala kala. Har ya gano tana da matsala amma ganin Fauziyya bazata iya faɗi ba. Yace mata gobe China zashi yasa ya dawo war haka. Amma zai bama Fauziyya saƙo ta bata. Musamman ya lura tanada juna biyu. Godiya tayi masa sannan ta wuce ɗakin masu aiki.

Bayan minti goma sai ga tray ɗin abinci kala kala Bilkisu ta shigo dashi. Tabbas tasan Alhaji yasa aka bata, anan taci ta kuma kira Mahfooz domin yaci. Ranar a ɗakin ya kwana ta rungume shi. Sai dai baiyi barcin kirki ba. Banda firgici da mugayen mafarke baya komai.

Ta roƙe su Bilkisu su rinka shiga dashi yana kwana wajen su amma suka ce suna tsoron abinda Hajia zata ce. Kuma tasan idan tayi ma Amina magana zata ɗauke shi. Amma kuma Alhaji zai gane mugun halin Fauziyya, kada abin ya zamto silar kashe mata aure kamar yadda ta gargaɗe ta.

Washe gari, tunda asuba Auta ta tashi. Kusan duka aikin gida ita tayi. Tayi mopping yayi ƙal ƙal fiye da yan aikin Fauziyya. Ko ita cikin ranta ta yaba da yanda Auta ta gyara mata gida.

Alhaji Sani yaso ya bama Fauziyya kuɗi domin ta bata amma yasan sarai bazata bata ba. Lokacin ta koma nata ɗakin kara barci bayan asuba, saiya shiga durowan ɗakinsa ya kwaso kaya. Kayan haihuwa ne wanda ta siya, saiya ɗauka ya bama Auta. Riguna, wanduna, safa, feeding bottle, pegs da sauran su. Sannan kuma da super wax guda ɗaya, hollandis biyu sai leshi ɗaya duka ya bata. Shi a nashi tunanin zai siyan ma Fauziyya a China, sati biyu zaiyi ya dawo kuma har lokacin bata haihu ba.

Anan ya miƙa ma Auta Dubu hamsin idan ta tashi haihuwa tayi amfani dasu, sannan dubu biyar tayi kudin mota. Da kanshi ya shiga store ya ɗauko kayan abinci harda su doya. Sha tara da arziki yayi mata tareda karramata.

Allah yaso Auta ta saka dubu hamsin ɗin cikin buhunta. Dubu biyar ne ke hannun ta. Aisha babban yarinyar Fauziyya itace taje ta tada ta, tazo ga Abban su zai barsu da yunwa domin duka abincin yana bama Auta.

Kamar guguwa ta fito sai taga kayan haihuwar ta, bata jira ba ta soma ɗauka. Daka mata tsawa yayi yace ta bar mata. Amma ta kafe su takeso. Anan yace zai siyan mata a China. Shima tace bataso. Wannan takeso, idan ya dawo daga China saiya kaima Auta. Hawaye Auta kawai takeyi abin yana cin mata tuwo a ƙwarya.

"Wai fisabillahi kinga tafiki bukuta amma kika kafe, meyasa bakida imani ne. Yanzu idan ta haihu me kike so tayi amfani dashi?"

"Toh ina ruwana, ni ke kwanciya da ita? Banda hauka ina ruwan talaka da haihuwa? Iyye kasan bakada kuɗi meye amfani daukar ciki saboda kazo kana takura ma mutane, sam bazai yiwu mai kaza yaci kai ba." tace tana jijiga.

"Alhaji karka damu, nima na siya kayan haihuwa ai. Kuma akwai na Aliyu ba komai ya lalace ba," Auta tace tana murmushin takaici.

"Karki damu nina baki kaya kuma sai kin tafi dasu, idan Fauziyya bata yarda ba saita biku ita ta tsaya Zaria," saiya fizge kayan. Da kansa yaje yana sawa a bayan motansa. Driver zai kai Auta tasha inda zata hau mota.

Fauziyya watsa ashar takeyi tana tsine ma Auta," Ni za kizo gidana kice zaki kashe ma aure saboda ina chaɓawa. Da yardan Allah wannan cikin saiya zama ajalin ki. Zaki mutu kafin aurena ya mutu. Annaminiya kada ki sake zuwa gidana," nan tayita zagin ta.

Daga Alhaji har Auta basu ce komai ba, har zata shiga mota sai ga Amina ta fito da Leda. Itama kayan babies ne nata ta ƙulla mata. Sannan ga dankali da kwai ta soya mata tasa a farin roba inda zata ci a hanya.

Ran Auta baya mata daɗi, Fauziyya tayi mata tozarci mara misali. Kuma ta ɗauki alwashin bazata sake takawa taje inda take ba.

Bayan direba ya dawo saiya kai Alhaji Sani Airport inda zai wuce Lagos daga nan sai China. Ashe Fauziyya bata haƙura ba. Tafasa kawai takeyi. Anan ta ɗauko dubu goma daga durowan ta domin su siya mai a hanya. Saita umurce driver akan su wuce Kaduna.

Tanaso Auta tana isa itama ta isa daga nan ta kwace kayanta. Mamaki takeyi wai ace yaran Auta sune zasu saka wannan kaya masu tsada. Bazai taɓa yiwuwa ba wai shan fate ran sallah.

Auta bata faɗa ma Mijinta artabun da akayi ba, domin zai umurce ta akan ta mayar. Nan take ya ɗauke dubu ashirin suka biya hayan ɗakin da suke ciki na ciki da falo. Kayan abincin kuma suna uwar daka ta shigar dasu. Kayan sawan ne suke falo tana sake ƙare masu kallo.

Mijinta ya siya masu ruwan shayi da biredi suma suna ɗanawa irin na ƴan gayu. Saiga Fauziyya ta shigo kamar guguwa. Batama jin nauyin jikinta. Anan taci kwalar riganta ta finciko ta. Shaƙe ta tayi sosai saida idanta ya firfito. Sannan ta zabga mata.

"Almura, ina kayan babies ɗina ko saina maki laga laga na hallaka ki?" tace tana jijiga ta. Tari Auta ta soma saboda numfashi yana sarƙewa.

"Meye haka? Saketa mana." Mijin yace tareda janta. "Haba Yaya Fauziyya, meye haka ?" ya kara.

"Toh faƙara'u alan lalurati bada kai nake magana ba. Kada kasa min baki. Wannan zancen yan uwa ne" tace tana zare mashi ido tareda da nuna mashi yatsa. Anan ta soma duba dube sai taga kayan akan kujera.

"Me kika mata ne?" yace.

Tana hawaye bata iya amsawa ba, wai ace Fauziyya tabita tun daga Kano saboda abinda tafi karfi. Wannan wani irin ƙaranci ne. Ita kam ko kallon su bata sake ba. Kayan taje ta tattara, dama batasan da atamfofin ba, Alhaji ya riga ya soma saka su mota. Kuma yanzu suna wani leda gefe.

Tas ta kwashe kayan yaran harta abin matsa shanya, saita zabga masu tsaki ta soma tafiya, saida takai bakin kofa ta waigo.

"Wallahi kika sake zuwa gidana saina ballaki. Kinje na faɗa maki," sai tayi tsaki.

"Yaya ina tsoron wanda baya tsoron ki," Auta ta amsa tareda fashewa da sabon kuka.

Wannan kenan !

#Naseera
#RumaSau
#Mahfooz
#DiyarDrAbdallah

Ainakatiti 🌠

Continue Reading

You'll Also Like

2.1M 87.9K 93
•UNDER EDITING• Abhimanyu Chowdhary-A mysterious 28 years old man. CEO of Chowdary group of companies. He has looks that every girl craves and go cra...
10.3K 242 21
"yeah, everything we broke and all the trouble that we made, but i say i hate you with a smile on my face" ...
50.6K 6.5K 71
"Se refiere a la belleza de corta duración de la flor de cerezo" ╰──➢ Advertencias ✧ ⁞ ❏. Omegaverse < SLOW BURN ⁞ ❏. Todoroki Bottom! ⁞ ❏. Smu...
46.5K 1.4K 80
"𝐻𝑎𝑛𝑠𝑒𝑜𝑘𝑎𝑎,𝑎 ℎ𝑒𝑎𝑟𝑡𝑙𝑒𝑠𝑠 𝑝𝑠𝑦𝑐ℎ𝑜𝑝𝑎𝑡ℎ 𝑙𝑖𝑘𝑒 𝑦𝑜𝑢 𝑑𝑜𝑒𝑠𝑛'𝑡 𝑑𝑒𝑠𝑒𝑟𝑣𝑒 𝑡𝑜 𝑓𝑒𝑒𝑙 𝑙𝑜𝑣𝑒 𝑤𝑖𝑡ℎ 𝑠𝑜𝑚𝑒𝑜𝑛�...