DIYAR DR ABDALLAH

By Aynarh_dimples

44.4K 6.3K 1.1K

Zuciyar sa yana mashi wasiwasi, abinda yake gudu shi ke shirin faruwa dashi. Bai taɓa samun kansa cikin wanna... More

One - Kankana
Three - Ummata
Four - IPhone
Five - Annoba
Six - Wanene Mahfooz I
Seven - Mahfooz II
Eight - Mahfooz III
Nine - Mabuɗin Zuciya
Ten - Kallon Kallo
Eleven - Farin Wasa
Twelve - Mugun Mafarki
Thirteen- Permanent Stalker
Fourteen - Rarrafen Carpet
Fifteen - Ƙarfi Yaci
Sixteen - Bazan Barki Ba
Seventeen
Eighteen - Ni Ce Asalin Diyar Dr Abdallah
Nineteen - Naga Wajen zama
Twenty - Mijin Tauraruwa
Twenty-one - Annihilation
Twenty-two - Pound Of Flesh
Twenty-three - Ribar Haƙuri
Twenty-four Bazan Barka Ba
Twenty-five - Love That Hurts
Twenty-six -Rendezvous
Twenty Seven- Idan Tayi Ruwa Rijiya
Twenty-eight - To Be Tainted
Twenty-nine - By Whatever Means Necessary
Thirty - Sun Shuka Sun Girbe
Thirty-one- Miscreant
Thirty-Two - Déjà-vu

Two- Ruwan Sama

1.9K 209 61
By Aynarh_dimples


Haka Ruma Sa'u ta zauna sai ciye ciye da lashe lashe takeyi, Rahina batada ƙaranci. Ta tabbata abinci bai tsinke mata ba.

WiFi ɗin gidan aka kunna mata tayi ta bi layi layi a Instagram, tareda amsa comments din da ake mata. Har yanzu dai Qwaro baibi ta kanta ba.

Cikin taƙama Mahfooz ya fito daga bayi, wanka yayi kana ya ɗauro alwala. Yadda yake abinsa zaka san lallai yana bala'in ji da kansa. Ash Jallabiya ɗinsa ya saka saiya wuce Masjid, bayan ya dawo sai yaje durowa ɗinsa ya ɗauko kayan kwallon sa. Miskili ne na bugun jarida.

Gashi ya shahara sosai wajen buga ball, za'a iya ce masa Messi ɗin Najeriya. Yaje Dubai sau biyu wani academy amma basu ɗauke shiba sannan har Under 17 ya buga ma Naija. Yanzu dai yana buga ma Kaduna United ne kafin ya sake samun wani waje a Turai. Sannan kuma shi civil Engr ne, yana aiki a wani campany Julius Berger.

Shima ya shahara a Instagram tunda an san shi duk ƙasar, Uwa uba gashi ɗan masu hannu da shuni ne. Baya rasa hotuna gefen motoci masu alfarma, sannan ya goge, ya iya saka sutura.

Yanada kyau kuma ya cancanci a soshi. Idan yana magana dole zuciyar ka zai ɗan sosu. Akwai hikima ga bala'in kwarjini. Yan mata kullum binsa suke yi suna crushing. Yana kula wanda yake kulawa ayi soyayyar shan miya. Tun farko zai faɗa maki cewa bai tashi aure ba. Sau da dama matan suna tunanin karya yakeyi. Idan suka gwada mashi madarar soyayya zai canza ra'ayi. Amma akasin haka suke samu, daga masu tsine mashi suna ya cuce su, bai aure suba amma sun bashi benefits ɗin masu aure.

Da Mahfooz ya gama saka kayansa, saiya ɗauki takalmin sa ya wuce filin ball. Bai kunna datan sa ba balle ya shiga Instagram. Kwana biyu baya jin daɗin jikinsa. Suna match da yan Eyimba United sai wani ya buge masa gwiwa, toh ya samu ƙaramin injury.

"Rahina me zaka yi ne?” Ruma ta tambayeta yayin da taga ta kwashe takardu ta nufe gefen data keɓe ma kanta a matsayin library.

" Wallahi ina da Impromptu test ne,” ta amsa.

“Inace kin gama, banaga hoton kinyi bautar ƙasa a Instagram ba??? "

" Eh, PGD nake yi,"

"Masters?” ta faɗa cikin sauri.

“Eh toh, bai kai Masters ba. Post Graduate Diploma ne”

Girgiza kai Ruma Sa'u tayi. Amma sam bata gane abinda Rahina tace ba. Ita a sanin ta. Kana gama degree sai masters daga nan ka zama professor. Abin yayi mata sabo wai wani abu PGD.

Rahina tana karatu ita tana chatting, anan tayi updating duka apps ɗinta. IPhone X ne ta siya a hannun wani friend dinta na One Love group. Clean wayace babu inda ya fashe.

Bature yace, "an ideal mind is a devil's workshop” kuma hakiƙanin gaskiya ne saboda tana cikin zaman banzan ta sai dabara ya faɗo mata.

" Bulala, nace ba... Ina admission letter ɗinki na degree zan duba abu ne, " Rahina bata kawo komai cikin ranta ba saita miƙe ta dauko files ɗinta. Anan ta ciro admission letter ɗinta na Kaduna State University.

Cikin murna Ruma Sa'u ta karɓa ta soma dubawa. Data faka idon Lala tana karatu saita ɗauki hoton admission ɗin. Bayan minti biyar saita miƙe tsaye tace zata tafi amma gobe idan Lala ta fito daga test ɗinta tayi kokarin kiranta sai su haɗu.

Ta soma tafiya zata tafi, dayake mirror ɗin yana gefen ƙofa, sai Ruma Sa'u ta ɗauki wani turare mai ɗan karin tsada ta saka Jakarta tareda faɗin, "Ina so," bata damu da ko an bata ba. Ita dai ta dauka.

Miyau mai zafi Lala ta haɗiye saboda taji haushin abin. Turaren yana cikin masu tsadar wajen sannan kadan tayi amfani dashi. Tana lura da Ruma Sa'u ɗazu datake wasan turaruka. Domin harta mirror selfie tayi dasu Video tana faɗin nanne ɗakinta.

Kai tsaye café Ruma Sa'u ta wuce. Anan ta nuna masu hoton tareda faɗin abinda take so ayi mata. Scanning da editing takeso ayi mata. A cire sunan Rahina a saka nata. Tsab ta mance ita shekarar ta biyu da farawa. An juya date ɗin samun addmision amma abinka da wanda bata sani ba, balle idan Fa'iza tana bama su Inna Labari Ruma ba sauraro takeyi ba.

Batama san da wani abu wai shi Matriculation number na. Suma yan café ɗin basuyi mata magana ba. Sun lura baho ce irin yan matan nan marasa abin yi. Anan suka karɓa dubu biyu wajen ta sannan suka tausaya ma wanda zata damfara da admission letter ɗin.

Ranta fari tas Fa'iza zata kiyaye ta daga yau. Zata cigaba da cin karenta babu babbaka. Balle kuma yanzu ta samu ƙawa mai ƙashin arziki. Duniya yana kai mata yadda take so.

A filin kwallon Mahfooz ya soma ganin dishi dishi, baya iya passing kwallo da kyau. Kafin ka sani sai ya taka ƙafar opponet ɗinsa. Aikam bai yi wata wata ba ya kwaɗa mashi mari. Suma yan team ɗinsu Mahfooz suka rama mashi. Anan faɗa ya kacame.

Nan maza suka yi ta bama hammata iska. Shi kam Mahfooz tunda ya sha mari yayi gefe yana jinyar kansa. Ashe wanda ya mare shi ya daɗe yana jin haushin sa. Anan ya sake cin kwalarsa yayi ta kilarsa. Duka yakeyi kamar an aika ya kashe shi. Coach ɗinsu da kyar ya kwace shi. Duk an fasa mashi baki jini sai kwarara yake yi kamar famfo.

Garin banza Mahfooz zai mashi duka. Amma wannan karan abin yazo da rashin lafiya.

Nan aka wuce dashi 'Abdallah Specialist Hospital' dake Alkali Road tunda ansan shi ɗan masu dashi ne kuma ko nawa ne kuɗin asibiti za'a biya mashi.

Naseera tana ɗakin Babanta, babu wani emergency a asibiti sai ta dawo wajen mahaifinta domin tayi mashi jinya. Mahaifinta yanada cutar Aplastic Anemia kuma yanzu haka yana bukatar bone marrow transplant.

Tabbas tasan ita match ne da Babanta, da farko bata maso tayi gwaji ba amma sai tayi. Anan ne tasha madarar mamaki. Watau bone marrow ɗinta bai yi matching da nashi ba.

Anan ta soma gwaji kala kala bila adadin. Amma duka haka abin yake. Harta wasu asibiti ta tura samples amma aka ce mata ga gaskiyar zance.

Sanda take ƙarama ance mata genotype ɗinta AS ne saboda ranar da aka haifeta ƙa'ida ne ayi ma yaro gwaji kafin subar asibiti, amma dataje medical school ta sake ma kanta test inda ya fito a AA. Abin ya bata mamaki amma tasan cewa shima ƙarfen nasara bashi da tabbas.

Yanzu ta kasa saisaita tunaninta waje ɗaya, da farko tasha kila anyi adopting ɗinta ne. Amma kuma da kanta taje durowan da ake ajiye takardu, haka ta rinka bi har shekarar da aka haifeta. Taga cewa tabbas Umma Hajia Binti ta haifeta. Kuma Nurse on duty na Ranar Jamila Magaji.

“Idan Baba bashi bane ubanta toh waye?”ta tambayi kanta tambayar da babu wanda zai bata amsar, "Shi kenan yanzu ba ita bace diyar Dr Abdallah." ta sake ayyanawa.

Wani yar taji a jikinta ta soma tausayin kanta. Duka wani alfahari datake yi akan asalinta ya rushe. Ko ina bata kunyar faɗin Sunanta Naseera Abdallah Kwarbai. Yanzu tasan she doesn't deserve that name.

Haushin Ummanta ya ɗirar mata. Da mutuwa da haihuwa ai duk na Allah ne. Mamaki takeyi yadda tayi saɓon Allah domin ta sameta. Taci amanar aurenta da Babanta sannan kuma ta cuce ta. Gashi yanzu Babanta ya riga ya saka rai da cewa Naseera zata bada bone marrow ɗinta. Ta ina yanzu zata soma gaya mashi ita ba ƴarsa bace. Ita shegiya ce wanda aka haifa ta mugun hanya. Ta ina zata ce masa Ummanta ta cuce su. Tabbas Dr Abdallah zai iya haɗiye zuciya ya mutu.

Sau da dama idan Ummanta tana bata labarin irin wahalar data sha kafin aka haife ta tausayi take bata. Amma ba tayi tsammanin akan haihuwa zata zubar da mutuncin taba.

“Yaushe za'a yi surgery ɗin? ” Dr Abdallah ya tambaye Naseera wanda ke kan sallaya tana tunani bayan ta idar ta sallah.

Murmushin ƙarya ta ƙwaƙulo, “Jiya machine ɗin test baya aiki, sannan yau kuma Dr Chinedu bai zo ba, wai yanada family emergency. In sha Allah gobe za'a yi test ɗin. Cikin satin nan zaka warke.”

Tasan ƙarya takeyi, amma wannan yafi mashi sauki akan abinda yake faruwa.

Beeper ɗinta ya soma ruri, anan ta miƙe tsaye. Labcoat ɗinta ta saka saita masa murmushi ta fice. Murmushi sukayi ma juna ba tareda sun ayyana wani abun a fili ba.

Naseera itace abin alfaharin Dr Abdallah. Duk da tana mace bai taɓa damuwa ba. Shi dama addu'a yakeyi akan ya samu ɗan da zai jiƙan sa. Fata yakeyi ya samu tsawon kwana saboda yaga aurenta.

Emergency ward ta nufa, anan taga masu kwallo sun kawo mutane kusan shida duk da ciwo a jikinsu. Da ita da sauran likitoci da taimakon wasu nurses suka soma basu first aid.

Uku daga cikin su za'a kwantar dasu, sauran ukun kuma bandage ne ake naɗe masu jiki inda ke zubar da jini.

Bayan an kwantar da sauran uku, sai wani daga bisanin wanda ba'a kwantar ba ya dawo yace shima yana so ya kwanta domin ya samu sauki sosai.

Shi a lokacin ya lura da ita, gabansa yayi mugun faɗuwa. Tanada yanayin fuskan da bazai taɓa mancewa ba. Fuskan daya jawo mashi tashin hankali da ruɗani. Fuskan da yafi tsana a duniya. Abin yayi mugun basa mamaki, saidai kuma dama ya taɓa jin ance kowa yanada lookalike ɗinsa a duniya. Nan take tsanar ta ya dirar masa a birnin zuciya.

"Ciwon da kake dashi bamai tsanani bane, kawai kaje gida ka huta zai fi ɓarnar kuɗin asibiti,” ta faɗan masa cikin kulawa.

“Ban san sanabe, babu ruwan ki ban tambayeki ba" ya amsa a hasalce. Saida ta daga ido taga ko waye zai mata rashin mutunci amma duk stitches a fuskan sa. Da kafaɗa ta amsa mashi saita kira Nurse domin su bashi ɗaki.

Washe gari...

Ruwa aka kwana ana yi, garin yayi duhu ga sanyi da yake tashi. Nurse ɗinda take duty tazo wucewa sai taga wutan ɗakin Mahfooz a kunne, duba ƙarin ruwan tayi taga yana shiga saita kashe mashi wuta ta fice.

'Ɗaki ne ciki da tarkace, komai na cikinsa tsoho ne. Sannan ga yanan gizo da wasu manyan manyan qwari. Ga baƙin duhun dayake wajen, banda warin ƙura da tsoffin kaya baka jin komai'

A firgice Mahfooz ya tashi yana salati, saiya ruga yaje ya kunna wutar. Zaman dirshan yayi a bakin kofar yana dafe kansa.

"Same dream... Harda girma na," ya faɗa yana hawaye. A duniya baya san duhu. Yasa yanzu a kalla shekara goma sha biyar kenan kullum da wutan lantarki yake kwana. Idan babu wuta kuma saiya kunna lantern ko candle har a dawo da wutar ko asuba tayi.

Anan ya ƙarasa zaman sa kafin asuba yayi inda ya tashi yayi sallah saiya koma gadonsa.

Zulumi fal ran Naseera, abin duniya yayi mata cinkoso. Yau ne dodon bango zai fito. Ance dama ranar wanka ba'a ɓoye cibi. Idan da sabo yaci ace ta saba da yadda zuciyar ta ke mata bugu. Amma sam kullum ɗaci take ji sabo a ranta.

Fargaba kala kala, sai wani tunanin ya faɗo mata idan yanzu Baba ya kore ta tareda Ummanta akan wannan abin fah. Saboda tana gani a fina finai da kuma Littatafai. Saidai kuma Dr Abdallah mutum ne mai dattako da mutunci. Akwai shi da sanin ya kamata cikin al'amarin sa.

Sanye take cikin doguwar riga pink, ita ma'abociyar kwalliya ce saboda ta iya har na zuwa biki. Saidai tun sanda wannan abu ya faru fuskanta payau yake bai haɗu da hoda ba. An saba mata laƙabi da Dr yar gayu saboda kokarin yanda ta iya murza hoda da jambaki. Gashi hancinta yayita sheƙi na bronzer.

A hanyar kitchen ta haɗu da Ummanta, a dikilce ta gaidata. Ita kuma Umma ta amsata fuska duk annuri. Haɗa kofin shayi tayi tasa ma kanta a flask saita fice. Ga dankalin turawa da sausage Umma tana soyawa amma saboda abinda takeji a ranta yasa ta daina cin girkin ta.

Koda ta isa asibiti ɗakin Babanta ta fara zuwa, a zaune ta gansa DR yana mashi bayanin al'amuran asibitin. Rinsinawa tayi har ƙasa ta gaida shi saita samu gefe ta zauna. Tana cikin waige waige saita lura harya sha kofin shayi. Shine ya umurce su akan bai san su rinka kwana, an hada shi da nurses da zasu rinka lura dashi.

Bayan likitar ya fita sai tayi mugun ajiyar zuciya, kallon ta yayi sai yace, "Dr Lafiya dai koh?"

Murmushi tayi mashi, dama idan kana san ganin murmushin ta toh sai tana tareda iyayen ta. Yanzu kuma ta ware Umma saida Babanta.

"Idan wanda ka yarda dashi duk duniya yaci amanar ka ya zakayi?" ido ta bishi dashi domin taga yadda yanayin fuskan sa zaiyi.

“Abu ɗaya na sani Nasira, kowa makiyin kane. Kuma kowa masoyinka ne. Idan kika rike wannan toh babu abinda zai baki mamaki. Kuma duk nauyin laifin da mutum zai maka, yana da kyau ka zamana mai uzuri. Kila akwai wani dalilin daya sa ya aikata hakan wanda kai baka sani ba," saiya dauko kofin ruwa ya kurba. Anan yayi ajiyar zuciya saiya cigaba.

“Yasa idan abu ya faru ya kamata mutum yayi hak'uri yayi dogon nazari. Na san haƙuri ba ƙaramin abu bane. Yanada wuya saboda zuciyar ka zai ta tafasa sannan ga shedan da zai rinka kawo maka wasiwasi. Amma idan ka dake kabi diddigi al'amarin zakiga ashe ba wani abin tashin hankali bane.”

Da kai ta amsa mashi saita soma duba BP ɗinsa, shi kam binta yake da idanu. Akwai damuwa ƙarara fuskanta. Amma tunda bata kasa dashi ba bai kwasa ba. Bayan ta gama saita fita tayi rounds.

Ta daɗe wajen Babanta har an kusan gamawa. Daki ɗaya ya rage na ƴan kwallon da aka zo dasu jiya. Bata kawo komai cikin ranta ba suka shiga tareda sauran residents. Anan aka gama duba shi.

Sun tafi sai Supervisor ɗinsu ya miƙa mata wani magani taje ta bama Mahfooz Abubakar Gwaiba. Bata san waye ba ta shiga ɗakin farko amma aka ce mata ɗayan ɗakin ne.

Shi kuma tun jiya da brothers ɗinsa suka zo diba shi tareda kai masa kaya da wayansa bai kunna ba sai yanzu. Anan yaga notification kaca kaca. Baibi takai ba sai ya shiga Instagram Explore. Hoton Ruma Sa'u ya gani yana yawo. Shafunan su Arewa da sauran su sunata reposting ɗinta.

Bata burge shi ko kaɗan, ya lura tanada hayaniya. Kullum tana biki kokuma wajen cin abinci. Bai taɓa ganinta a gida ba sai wannan karan. Gata a gaban madubi cikin ɗaki na alfarma. Tayi kyau babu haufi anan ya shagala yana kallon ta. Burin sa yanzu ta zama yar hannun sa. Zaiyi liking kenan sai yaji ana taɓa kofa.

Sallama Naseera tayi tareda tura kofa, saita karasa inda yake domin ta bashi maganin. Bai ɗago ba balle ya kalle ta. Magana ya soma yi cikin izza da taƙama domin ya nuna shi ɗin ɗan wani ne.

"Waye jiya ya shigo ɗakina ina barci ya kashe min wuta?”

Ya bala'in bata haushi, ta lura bai da mutunci. Sannan idan yanada abinda zaiyi yazo yayi mata tunda asibitin mahaifinta ne.

" Ni ce na kashe danake rounds, menene?”

Gyara zaman sa yayi saiya kalle ta. "Hmmm, zanyi maganin ki.” kawai ya furta saiya kwanta.

"Gashi wannan zaka sha sau biyu a rana, da safe guda...." bata karasa ba ya daga mata hannu alamar tayi mashi shiru.

"Dalla malama go and call your supervisors.... Kina tunanin zan yarda da abinda intern or whatever tace ne? " sai yaja ƙaramin tsaki tareda kwanciya yana kallon sama.

An riga an masu ethics a medical school, ba'a faɗa da patient. Yau da sana'ar conductor takeyi da sai taci kwalar sa taga wanda ya ɗaura uwarsa aure.

Fita tayi ta koma bakin aikinta, sam baya gaban ta. Idan irin wannan patients ɗin marasa ɗa'a zata rinka cin karo dasu yafi mata sau dubu akan abinda yake wakana a rayuwar ta.

Ranar ya tafi mata sumul ba wani tashin hankali kuma. Ta lura Mahfooz baida mutunci saita kiyaye shi. Sannan ta ɗauki alwashin yau zata gayama Babanta komai bayan sallar isha. Bawa baya wuce kaddarar sa. Duk abinda zai faru tasan bazata kunyata ba.

Yamma yayi wajen karfe shida, ta haɗa kayanta kenan zata koma gida tayi wanka sannan ta ɗauko ma Babanta abincin dinner.

Har zata fita sai DR Abdallah yace ta biya Kawo ta kaima Nurse Jamila Insulin na diabetes ɗinta. Nurse Jamila tana cikin manyan kuma wanda suka fara aiki a asibitin. Kuma ranar da aka haifa Naseera Nurse on duty bata zoba itace ce ta taimaka tunda DR baya ƙasar lokacin. Yasa yanzu kamar yar uwa take wajen Naseera.

Ta soma tafiya saita tuna Anty Jamila Mijin ta yayi masu gini last week suka koma sabon gidan. Suna jinyar Dr Abdallah basu samu damar sun je sun gani ba.

"Wani anguwa ne?” ta tambaye shi

“Kawo baida wuyan ganewa, ga address ɗin nayi maki copying, ki bama masu gadi kawai sai a ajiye mata"

Napep tayi chata tunda bata san wajen ba, kafin ayi mata kwace ana ganinta mace kuma dole tayi ta tambayoyi. Balle zata dawo asibiti anjima sai lokacin ta tafi da motar.

Mai napep ɗin yaga kalar manya, bai san wajen ba amma ya dauke ta. Da suka kai Kawo anan suka soma tambaya.

Hadari ya doso sannan ga dare. Mutane duk sun ƙare a wani layi da suka shiga. Anan suka ga wasu samari su uku kofar wani daki. Mai napep yace ta sauka ta karasa dakalin da suke zaune. Shi baya so ya sauka wani yayi gaba da napep ɗin.

Ta sauka ta soma gaida su saita lura da irin kalar mutanen. Yan sara suka ne, ga zungureren wuka hannun ɗaya, sannan duka wiwi suke busa. Mai napep shima yana ankara ya burga ya gudu baibi ta kanta ba.

Anan wannan mazan suka soma murmushi tareda damfaro kanta. Ita kam baya ta Soma ja tana addu'a cikin ranta. Miyan bakinta a bushe yake amma tayi kokarin ta soma masu magana.

"Dan Allah kuyi hakuri ban nufe ku da sharri ba. Tambaya nake so nayi amma kuyi haƙuri kubar ni na wuce"

Dariyar ƙeta suka soma yi, "Yar shila karki damu yanzu zamu fige ki mu wuce." ɗaya daga cikin su yace saiya nufeta gadan gadan ya fizgo mata hannu ya janyo ta jikinsa. Anan ya soma lashe mata kumatu yana dariya.

Suma sauran dariya suka soma, banda ƙaurin Wiwi da warin hammata batajin kowane irin wari jikinsa. Idanta ya fito tana basu hakuri. Sunata mata dariya.

"Shegiya tana fah so, jibe ko kuka batayi sai ihun banza. Wannan kana ganinta kaga jarabbaba.... Yasa saina kwasa rabona" sai suka sake fashewa da dariya.

Wani ne yazo wucewa saiya gansu, "Kai meye haka kuke yi?" ya faɗa a hasalce.

"Haba Qwaro karka saka mana baki, yar hannun mu ce fah, kuma nanfa ba filin ball bane. Nan fah area ɗinda muka fi kwarewa ne. Kabar mu muyi abin mu dan Allah." ya faɗa yana lankwasa baki.

Bata san waye ba, kuma koma waye Qwaro yafi su imani. Anan ta kalle shi da kyau. Tunda take bata taɓa tunanin cewa ganinsa zai taɓa mata daɗi ba sai yauzu. Asalima bata fatan su sake haɗuwa. Cikin hanzari ta soma magana.

" Mahfooz dan Allah zo ka taimaka min." idanta a kaɗe yake. Kana ganinta kasan akwai razana ƙarara. Shiru yayi bai ce komi ba. Dama Chemist zashi ayi mashi allura tunda ya sallama kansa a Abdallah Specialist.

Duk kawo an san shi, ana masa laƙabi da suna Qwaro a filin kwallo. Saboda akwai kwari masu tirjiya har wanda suke sati biyu raye ba tareda kansu a jikinsu ba.

"Dan Allah Mahfooz kace ka sanni," ta Cigaba da roƙon sa. Jikinta sai ɓari yake. Gumi kawai takeyi. Ga wani mugun ɗaci datake ji cikin ranta. Zuciyar ta kamar zai fashe, ta kasa saisaita tunani waje ɗaya. Wanda ke riƙe da ita ya sake lashe mata kumatu. Anan tsigan jikinta ya kuma tashi. Daya daga cikin yan daban ya bude ɗakin su dama kofar waje ne sun soma janta.

Qwaro bai hana suba yana kallon yanda take tirjewa tana dambe dasu. Tabbas idan yayi masu magana yasan zasu daina. Ana ganin mutuncinsa. Amma yayi shiru. Anan Naseera ta samu ta yanka ma ɗaya daga cikin su cizo wanda yake kokarin rufe mata baki. Aikam nan ya yanka mata mari. Layin shiru daga su sai Qwaro.

Haka ya tsaya yana kallo, haushi take bashi. Yayi mugun tsananta. Yasan koda sun illanta ta bazai saka ya daina mugun mafarki ba. Bazai dawo mashi da farin cikin sa ba. Bama ita tayi mashi laifin ba, yana ganin sanda aka yi mashi tana rarrafe. Amma still, ubanwa yace tayi kama da makiyan sa.

"Mahfooz dan Allah ka taimaka min," tayi ta nanatawa jikinta sai rawa yake. Dumi taji a fuskanta. A karo na farko hawaye yana sauko mata a idanu na tsawon lokaci. Kadan kadan ya fara sai kuma a guje kamar famfo. Nan ta rinka rero kuka mai ban tausayi. Duk rashin imanin ka saika tausaya mata. Yi takeyi tana shesheƙa. Amma Mahfooz ko gizau, tsananta ya cigaba.

"Nifa ban santa ba," ya faɗa saiya fice.

"Babu ruwana, da banbi hanyar ba dama zasu yi abin su. I did not rape her," yayita nanata ma kansa yayinda yake tafiya.

Anan suka samu suka sake toshe mata baki tareda ƙarasa ingiza ta cikin ɗakin. Duka su ukun suka yi mata fyade sai suka wurgata waje kan titi. Gashi sun kwace mata waya da kudinta.

Tana cikin ruwan take tafiya gashi da bala'in karfi. Bata ko ganin gabanta banda kuka babu abinda takeyi. Anan ta fantsama titi. Wani mota yazo da gudu bai yi tsammanin wani zai shiga ba saboda yanda ake kwarara ruwa. Nan ya kaɗeta tayi gefe.

Anan mai motan yayi salati ya fito a guje ya duba ta. Sake salati yayi dayaga wacece.

"Naseera me kike yi a waje cikin daren nan?”

A hankali ta soma bude idanta, sai taga wanda yake rike da ita ya rungume. Murmushin takaici tayi. Numfashinta yana kokarin daukewa saboda ta galabaita. Da kyar ta iya magana," Uncle Sadiq, sun min... sun min fyade.... Kuma bai hanasu ba... bai hanasu ba.... Ni ban mashi komai ba. Banma taɓa ganin saba amma ya kafa min ƙarar tsana." anan ta sake fashewa da kuka mai taɓa rai.




Wannan kenan!

#Naseera
#Mahfooz
#DiyarDrAbdallah

Ainakatiti ✨

Continue Reading

You'll Also Like

90.1K 3.3K 55
After his first year at the Advanced Nurturing High School, Fukazawa Yato is about to start his second year as a student. With a better understanding...
CONSUME By [ Mary ]

Mystery / Thriller

191K 5.9K 19
There's something odd about the town's most beloved police officer, he is utterly obsessed about a girl and will go to any lengths to have her.
11K 512 26
MAFIA STEP - SISTER OF BANGPINK
12.8K 2K 22
جۆنگ کوک:بە نەفرەت بیت وازم لێ بێنە چیت لە من دەوێت تایهیۆنگ:ششـ ئازیزم بۆچی هاوار دەکەی ئارام بە بۆ باروودۆخت خراپە ༄༄༄༄༄༄༄ جۆنگ کوک:تـ تۆ چیت کرد ت...