HUMAIDAH

By neeshejay

46.5K 3.2K 188

Labarine akan wata youg lady who worked in YUGUDA's House so that she earned money da zata ma mamanta treatme... More

HUMAIDAH
1
2
3
4
5
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
Not an update
Lovelies๐Ÿ’–โค
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
34
33
๐Ÿ”š

35

1.2K 65 1
By neeshejay


*ᎻᏌᎷᎪᏆᎠᎪᎻ*
(ᴛʜᴇ ᴄʜᴀʀᴍɪɴɢ ʟᴀᴅʏ)

           *ᎪYᏚᎻᎪᎡᎢᎾᏌ*
                ωαттρα∂ @neeshejay

_Dedιcaтed tσ_

*H͙  u͙ m͙ a͙ i͙ d͙ a͙ h͙*
(υммυ fυ'α∂)

*ⓟⓐⓡⓣ 176_180*

Pictures din ta da yawa Asiya ta turawa king sosae ya yaba da kwalliyar amaryarsa ji yake inama yaune za'a Kae masa ita gaba daya ya matsu yaji sa a kusa da gimbiyarsa.

Gaba daya ta gaji sosae hakan yasa ana gama event ta shige daki ta cire kayant tareda shiga toilet ta watsa ruwa ko zataji dadin jikinta koda ta fito ta tarar da gaba daya yan uwanta da sun shigo dan ita bata da frnds ko daya sae dae cousins dinta. Suma sae faman cire Kaya suke nan suka fara wanka wadan da Kuma ba dakin suke kwana ba suka wuce dakinsu, itama bata jima ba ta wuce warta dakin Ammi Dan yanzu a Chan take kwana, wani Dan karamin hard cover Mae masifar pink colour Kuma yanada Dan karamin padlock Shima Mae  kyau ta dauka, koda ta shiga ammi Bata dakin sanin Abba ya dawo ne yasa tayi kwanciyarta amma gaba daya ta kasa bacci hakan yasa ta mike take dakinsu ta Kira Asiya ta tayata kwana tunda Ammi Bata nan,bayan sun dawo dakin ne Kiran king a ya Mata ya gajiya nan suka shiga fira har dare ya raba Shima dakyar suka rabu,

Bata kwanta ba sbd ganin karfe 3:19am hakan yasa ta mike ta shiga toilet ta dauro alwala sallah tayi tareda addu'a sosae kafin ta kwanta ba jimawa aka Kira sallahr asuba.

Bayan sunyi sallah ta koma ta kwanta sae kusan 10 ta farka ko da ta tashi ba kowa a dakin wanka tayi ta fito ta shirya cikin doguwar rigar material, Aunty Suwaiba ce ta shigo hannunta dauke da wani cup nan da nan annurin fuskar Humaidah ya dauke Dan tasan abunda Bata so ne aka so Bata ganin haka yasa aunty Suwaiba tamke fuska ta Mika Mata ba Wasa ta karba ta shaye tana yatsinar fuska Kamar zatayi kuka. Bata kulata ba ta karbi cup din ta fita abunta itama fita tayi a parlour ta tararda dukansu dining ta wuce sae da ta dibo breakfast dinta kana ta koma parlour ta zauna.

Bayan ta gama suka fita gaba dayansu sae gdan mama Dan a chan ne zaayi lalle Basu jima da isa ba aka fara Dan already Mae lalle tazo har an ma wasu  amarya aka fara tsantsarwa lallae Mae kyau ja da baki yayi kyau sosae sae kusan 3 ta wanke tana cikin dakin ammi ta gama sallah ta mike kafarta tana lazimi ya shigo wani irin murmushi ya Mata Mae narkar da zuciya itama mayar masa tayi kana ya karasa shigo dakin bakin gado ya zauna Yana karema kafarta kallo sosae lallin ya masa kyau danshi mutum me Mae son shi. Ganin kallon da yake matane yasa tayi saurin boye kafarta tana smiling Shima dariya yayi yace"heartbeat rowa ko"

Dariya tayi tace"ni na isa mama mamallakin lallen rowa ne"

Yace"idan haka ne to meyesa kika boye kafar"

Cikin shagwaba tace"ba yanzu ya kamata ga gani ba" ta karasa da turo baki

Wani abu yaji tundaga kasan kafarsa har cikin kansa cikin ransa yace"ya ilahi da ace an daura Mana aure ba abunda zaesa nayi kissing dinta"

A fili  kuwa yace"baby you are killing me" da sauri ta mike zata fice yayi saurin kamo hannunta sae kawae tayi kasa da kanta kafin ya bude baki yayi mgn sae ga ammi da mama sun shigo ae da sauri mama ta koma ganin wannan ta'asar ammi kuwa rike baki tayi tana sallallami Humaidah da kunya ta rufeta tayi saurin ficewa waje da gudu.

Ammi ta kalli king tace"toh Mara kunya uban yan azarbabi zoka wuce ka bani guri shine zaka saka yarinya a gaba kana koya Mata rashin kunya Anya kuwa Taufeeq"

Sosa bayan kansa yayi yace"Kae ammi mutum da matarsa"

Ammi ta rike baki tace"yaushe aka daura auren ban sani ba"

Yace"ae kodae ba'a daura ba an kusa"

Tace"toh ae saeka jira har a daura din ko"

Fita yayi Yana mita daga cikin daki Ammi ta daga murya yanda zaeji tace"ai da ka dawo ka fada a gabana Mana"

Juyawa tayi taga ba mama Smiling kawae tayi dan tasan ganinsu da tayi ne yasa ta koma hakan yasa ta fita zuwa dibota.

Humaidah kuwa tana fita daki ta wuce tana smiling ita kadae.

Asiya na ganinta tace"ke kuwa lpyn ki kinata smiling Kamar wacce akama albishir da aljannah"

Tace"toh uwar yan sa ido"

Tace"a ba mgnr da Ido bane Naga kina abune kamar sabon kamu"

Ae da gudu Humaidah ta bita ta fice da gudu sae garden.

Jin ta buge da mutum ne yasa tayi saurin komawa baya tana rike goshi dago idon da zatayi ne taga Neehal cikin shiga ta English wears as usual da sauri tace"Dan Allah kayi hkr wlh ban kula da Kae ba ban San kana gurin ba Allah kuwa plss sorry"

Ganin ta rudene yasa yayi sauri daga Mata hannu yace"ya isa waya biyoki ne haka"

Kanta a kasa tace"Ba kowa"

Zaro Ido yayi yace"ba kowa kodae Aljani ne"

Da sauri ta juya baya taga ba Humaidah aiko tsoro ya kamata ta tsala ihu"

Da sauri yasa hannunsa ya rufe Mata baki yace"ke nutsu Mana"

Shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya ganin tayi shiru ne yasa ya saketa yaja hannunta sae cikin garden din, kan kujerar dake gurin ya masauki zama tayi tana kallon ikon Allah har kasa ya duka daka gansa kasan damuwa ta masa yawa Dan yanzu bashi da tunanin daya wuce na Asiya akullum tunanin ta wace hayance zaebi ya mallaketa ganin wannan ne kadae opportunity din yasa ya kudurta fada masa abunda ne zuciyarsa.

Cikin sanyin murya yace"I know it will sound somehow to you but believe me duk abunda zan fada daga zuciyata zae fito bawae kawae daga bakina ba" Dan numfasawa yayi ya cigaba "Asiya tun ranar Dana fara ganinki zuciyata ta kasa samun sukuni ban taba haduwa da wata mace da zuciyata ta kamu da sonta ba Kamar dan Allah Asiya karkice aa idan ba haka ban San wane Hali zuciyata zata shiga ban San yanda rayuwata zata kasance ba tunda nake duniya idan inason abu tofa zan so shine Kamar rayuwata Dan Allah karki juge ni na rokeki" ya daga hannu alamun roko

Jikinta gaba daya yayi sanyi itama har cikin ranta take son Neehal amma ta dau alwashin sae ta gasashi taga ya koma mutum kwarae kana zata yarda da bukatarsa da sauri ta mike tace"dakata Dan Allah kana tunanin zan iya aure mutum fasiki mazinaci Wanda bae maeda Zina komae ba a rayuwarsa toh idan kayi tunanin haka ne gwara ma tun wuri ka canza Danni bazan iya zama da wanda basae Allah ba na tabbata sallahr nan guda biyar ma baka cikawa a hakan kake so na aure ka to taya zamu fara bawa yaran da zamu Haifa tarbiyya bayan babansu ma ba isashshiyar tarbiyya yake da ita ba kayi hkr malam Allah ya hada kowa da rabonsa" tana Kae haka ta wuce cikin gda abunta

Neehal kuwa mutuwar tsaye yayi gaba daya ya kasa daga koda yatsansa ne maganganunta sae yawo suke a jikinsa da kwakwalwarsa wani irin kunya nadama da Dana sine suka dirsar masa bae taba jin yatsani kansa ba sae yau zama yayi tareda dafe kansa haka kawae yaji hawaye na zubo masa saw kawae ya fashe da wani irin kukan nadama sae yanzu yake jin haushin kansa ada suk Wanda ya masa mgn baya damuwa Amma da Asiya ta mishi yaji gaba daya tsanar kansa ta kamasa kuka sosae yakeyi.

Jin yayi an dafasa bae dago ba bae kuma dae kukan basae ji yayi yace"idan kana sonta to ka fara shirya kanka kafin ka koma gurinta da kudurinka a matsayina na Dan uwanka wnn kawae itace shawarar da zan baka idan ba hakan ba Kuma ba Asiya ba ko wace yarinyar data San ciwon kanta bazata auri mutum irinka ba"

Da sauri ya kire hannun king tareda fashewa da wani irin kuka sae yanzu yake ganin yayi wawta nakin bin shawarar tilon yayasan abaya ganin yaki shiru ne yasa king zama gefensa tareda rungumosa jikinsa Yana rarrashi shi mamaki ma yakeyi wae yau Neehal ne ke kuka akan mace abunda yafi rainawa a rayuwarsa sae gashi ta saka shi kuka da idanunsa sae da ya tabbatar da ya dae na kukan ya koma ajiyar zuciya kana ya mike zae tafi da sauri ya riko hannunsa cikin muryar Wanda yasha kuka yace"Yaya Dan Allah kayi hkr duk abunda na maka a rayuwa wlh sae yanzu nake jin na tsani kaena Yaya bana tunanin Allah zae gafarta min abunda na masa sae yanzu na gane rayuwar danayi a baya gaba daya cikin jahilci nayi ta Yaya" ya karasa Yana fashewa da wani kukan.

Sosae ya bama king tausayi Dan baka ya shuga basa baki har yaga ya nutsu kana ya tafi ya barsa agurin cikeda tunanin ta imda zae fara bayaso ya rasa Asiya Kuma yafi so ya mallekata kafin next year sosae yayi zurfi cikin tunanin sa sae da aka Kira sallahr magrib kana ya mike ya tafi masallaci abunda bae Saba ba kenan, bashi yadawo ba sae akayi sallahr Isha Kuma ya samu ya dae daeta da limamin masallacin su akan zae fara koya masa karatu duk bayan sallahr asuba da magrib zuwa isha, liman yace"toh mu fara yanzu ko sae goben"

Da sauri yace"yanzu"

Liman yace"madallah da Ina zamu fara"

Cikin sanyi Neehal yace"malam bansan meye addinina ba nidae kawae nasan ana sallah a cikin sallar Kuma ba suka abubuwan da ake fada na sani ba"
Sosae liman yaji tausayin Neehal Dan Yana cikin jahilci sosae fatansa kawa ace Neehal na daya daga cikin mutane masu saurin rike Abu idan ba hakan ba sae an Sha fama,daga farillan alwala liman ya fara koya masa.
( _toh su malam  Neehal Allah ya taimaka_)

Zaune suke a daki sun idar da sallah nan Asiya tabama Humaidah lbrn yanda sukayi da Neehal cikin tausayawa Humaidah tace"Allah sarki bawan Allah wlh ya bani tausayi sosae"

Asiya tace"Bari kedae wlh sae da nakae zuciyata nesa kafin na fada masa abunda ke Raina wlh Humaidah ba karamin so nake ma Neehal ba amma halayyarsa ce bana so idan Yana so ya mallakeni sae ya shiryu yabi Allah idan ba hakan ba kuwa sae daena mutu da sonshi"

Duka Humaidah ta Kae Mata a cinya tace "bakida kirki wlh"

Harara Asiya ta twasa mata tace"kut yanzu kinfi son na auri mutumin da zae bata future din yarana?"

Humaidah tace"maeda wukar ba haka nake nufi ba"

Shigowar Najwah ne yasa sukayi shiru suka maeda hankalinsu kanta cike da zolaya Asiya tace"maman hudu baki tafi ba"

Zama tayi kan sofa tana jifan Asiya da throw pillow tace"bada ni ba muguwa"

Dariya sukayi gaba dayansu kana tace"yauwa na kira wacca tamin kwalliyar aurena tace zata zo tayi Miki na sauran event din Dan abunda yasa jiya Bata zo ba sbd tana da wani bikine"

Smilingly Humaidah tace"toh Allah ya kaimu babbar kanwa"

Hararanta Najwah tayi tace"au nice karamar kanwa yanzu ko"

Dariya sukayi dukansu ta mike dakyar Dan yanzu cikinta ya Kae wata 7 da sati biyu tace"nikam na tafi Inda nafi wayau"

Asiya tace"da wuri haka"

Tace"toh Yana iya yace min yazo"

Mikewa sukayi suka Mata rakiya har bakin mota Humaidah nata korafin yaki Bari Najwah ta kwana gashi Kuma yazo ya dauke ta da wuri"

Dariya yayi yace"haba matar Yaya ayi hkr kamawa tayi Dan Nima ina bukatar kulawa ko baby" ya fada Yana kallon Najwa tareda winking idonsa daya tace "haka ne baby kyalesu bazasu gane ba sae sun shiga daga ciki" ae da sauri suka bar gurin suna dariya suma dariyar sukayi kana yaja mota suka tafi.


     ★

Washe gari aka shirya kayataccen kamu na gargajiya sosae makeup artist din nan wato *Tafeeda's glamour* ta baje basirarta akan fuskar Humaidah tayi kyau har ta gaji idan ka ganta baza ka gane ta sbd gaba daya an chanza Mata fuska.

Su Asiya ma sunyi kyau ba kadan ba hajiya Najwah da aka tsufa ma sae da aka chanchada kwalli ta yabo sosae sukayi kyau.

Kafin time ya karasa aka haura da amarya saman daddy cikin babban parlourn sa dayasha ado *mykevisuals* ne suka musu hotuna na nunawa duniya itada King da Shima yasha ado cikin dakakkiyar geznar na nevy blue da sirfanin sky blue kyau Dan haka ashokin Humaidah yake sosae kwalliyarta ta tafi dashi Dan mutuwar zaene yayi hotuna aka musu masu kyau da tsari daga baya akayi gaba daya da frnds dinsa da nata sosae suka bada kala Dan Neehal ma sae da yazo sosae kwalliyar Asiya ta mishi kyau Amma ba halin Yabawa haka ma Najwah sae da ta Kira Huzaif yazo aka musu su biyu abunsu Kuma sunyi kyau sosae barin ma inda ya sakata a gaba ya Dora hannunsa akan cikinta tayi dariya tana kallonsa wow readers ku hango.

Cikin kunne king ya rada ma Humaidah"da ni dake ne a hakan zanfi kowa farin ciki"

Smiling tayi tace"Allah ya nuna Mana"

Yace"ameen"

Ammi ta hauro ta kirasu nan suka fita king ma da Bata liyarsa suka wuce. Sosae kamu ya kayatar Dan fuskar kowa ka gani sae cikin annashuwa da farinciki yake anyi barin kudi kamar ba'a San ciwonsu Dan ammi da mama sun bada mamaki sae kusan magrib aka gama kowa ya koma gda da santin bikin.

   

        ★
    ★
         ★

Washe gari Friday bayan sallahr juma'a dubban mutane suka shaida daurin auren *Taufeeq Muktar Yuguda & Humaidah Hayatudden keffi* manyan masu kudin Nigeria duk sun hallaci daurin auren babbn yaron Alh Muktar Yuguda Shima king frnds dinsa daga wata kasa duk sunzo Dan tayasa murna da aka shaeda daurin aure harda kukan farin ciki king yayi, yama Allah godiya da mallaka masa sahibarsa da ya dade Yana mafarki akan matar aurensa Kuma Yana fata ta har abada.

A bangaren Humaidah ma ba karamin kuka tayi ba duk ta bata kwalliyar ta cikin atamfarfa supar da tasha dinki das jikinta, kowa ya ganta sae ya tausaya Mata sbd yanda fuskarta tayi Kara gyara Mata kwalliyar ta tafeeda tayi kana suka fita zuwa daukar photos sosae king ke saka ta ajikinsa kamar ance za'a kwace masa ita.
Bayan an gama suka tafi reception

★★★

Zaune take da wayarta tana duba abubuwa a instagram sosae take jin dadin kallon pics dinda takeyi ganin new post dinda Tafeedah tayi ne yasa tayi saurin shiga page dinta dan ita fan dinta ce sosae Kuma take Mata kwalliya ganin pics din king da wata ba karamin daga Mata hankali yayi ba da sauri ta daniga scrolling nan ta tabbatar da yayi aure da gaske page din yan gdansu ta dinga shiga ban fa taga pics dinda Bata ma gani ba wani irin zafi take ji cikin zuciyarta gaba daya duk wani page idan ka duba pics dinsu ke wayo Best couples of the year itama samun kanta tayi da screenshot din pic dinsu tayi posting tana wishing dinsa HML haka ma Twitter koda ta duba Najwah da Neehal sunyi posting haka ma ilham da sauran frnds dinda ta sani snap ma sae strike ake dasu Dan sun bada kala sosae. Hwaye kawae taji suna zuboma non stop Bata hana kanta ba sae da tayi Mae isarta kana tayi shiru daga nan Kuma sae baccu. Koda Ahmad ya dawo ta nuna mishi Shima ya tayasu murna danshi ba ma'abocin platform bane.

Da yamma akayi rantsatstsiyar walima ta gani ta fada sosae Humaidah tayi kyau Dan tsaraba ta musamman Ammi ta bata wata farar riga doguwa Kamar wedding gown sae head dinta fari sak ta fito Muslim bride

A babban gdan gonar daddy aka gabatar da walimar kuma Masha Allah malama tayi wa'azi sosae Mae tsara jiki da bargo amarya ansha kuka Kamar ba gobe.

Da dare bayan sallahr magrib daddy dasu mama da Ammi suka tarasu a parlour suka musu nasiha akan aure sosae jikinsu yayi sanyi Dan ba kunya iyayen nasu suka sanar dasu hakkin kowannen su Humaidah sarkin kuka sae fama aikin yinsa take.

Bayan sallahr Isha aka shirya domin zuwa dinner duk event dinda akayi ba Wanda ya kayatar Kamar dinner na musamman Neehal da Najwah suka baza kudi domin nunawa tilon yayansu murna ba karya hall din yayi matukar kyaun da alkalami bazae iya rubutawa ba hakama couples din sunyi kyau sosae .

Sosae mutane masu class masu ji da kudi suka taru a gurin dinner din frnds din Neehal big boys duk sunzo bayan sun isa aka jera amarya da ango a tsakiya Neehal ganin wanj frnd din King ya nacewa Asiya ne duk event dinda za'a Yi yasa yayi saurin zuwa ya tsaya suka da ita Dan yaga alama kokarin yake ya jera da ita aiko ba karamin haushi yaji ba sae kawae ya koma baya ya samu wata suka jera tare.

Asiya na kula dashi sae kawae ta dauke kae bae damu ba suka shiga aka fara gudanar da abunda ya Tara mutane. Sae kusan 12 aka gama daga nan tawagar amarya suka rakata har gdanta Basu jima ba suka tafi sae frnds dinta da aka barta dasu.

12:42am su ango suka shigo hamdala king yayi Dan ba karya iyayensu sunyi kokari sosae gdan su Kamar ba a 9ja ba Dan yayi kayau matuka  kamae na parlourn Ash and black ne zama sukayi kana ya shiga daki ya kirata ba jimawa suka fito itada frnds dinta sae barkwanci ya barke siaae sukayi dariya kana sukayi addu'a tareda Yi masu nasiha suma suka kwashi frnds din amarya suka tafi Najwah Kuma Huzaif yazo daukanta.

Bayan tafiyar su taji gdan ya Mata shiru hannunta yaja sae dakinta suna shiga ya ajiyeta kan gado Shima ya zauna dama alkawarinda ya daukarwa kansa da an daura masa aure da Humaidah ba abunda zae fara Mata saw kiss Dan bakinta ba karamin tafiya dashi yakeyi ba musamman idan tama mishi shagwaba ta turo baki,a hankali ya fara kissing dinta itakam Humaidah jin bakin yanayi yasa ta lafe Bata motsa ba har ya gaji ya saketa kana yace"tashi kiyi alwala ba musu ta mike ta shiga toilet sae da tayi wanka kana tayi alwala ta dawo sosae take jin wani farin ciki cikin zuciyarta sae godiya takema Allah daya mallaka Mata masoyinta a matsayin mijinta what a miracle.

Ganin bashi a dakin yasa ta dauki rigar da Najwah ta saka Mata kasan pillow kallon rigar tayi sosae kana ta girgiza kanta tana smiling cire kunya tayi ta saka abunta kana ta bude wardrobe ta dauki zani da Hijab. Sae da ta feshe gaba daya jikinta da turare masu kamshin dadi da Sanya zuciya ta dauko humran da aunty Suwaiba ta bata ta shafa kamar yanda tace"

Bata jima ba sae gashi ya dawo da jallabiya ajikinsa Shima da alama wanka yayi carpet ya shimfida musu ya kalleta yace"tashi muyi sallah mu godewa Allah mallakar junanmu da mukayi"

Smiling tayi kana ta mike yaja su sallah raka'a biyu bayan sun gama yayi Masu doguwar addu'a kafin yayi Mata tambayoyi ba laifi ta amsa sae dae Dan gyaran da baza a ransa ba.

Bayan sun gama ya jawo ledar da suka shigo da ita gasasshiyar kaza ce a ciki haka ya dinga Bata a baki Shima yanaci har suka koshi ya kwashe kayan ya maeda kitchen ita Kuma ta shiga toilet Dan yin brush koda ya dawo ta fito Shima ya shiga yayi nashi,Yana shiga ta dauko wata humaran datafi na dazu masifar kamshi ta shafa tayi sauri ta mayar tareda kwanciya chan gefen gado. Ganin ta kwanta ne yasaka shi kashe wuta Shima ya haye gdon.

Yasin Yaya Ruqusbta hanani ganin komae😂🤣 hakan yasa ban samu damar dauki muku rahoto ba inada daga parlour najiyo ihunta baewar Allah sae da ta bani tausayi
Haka suka raya wanna daren cikeda samun Lada

Wahe gari sae da yayi kamar me Dan gaba daya zazzabi ya rufeta sosae ta bashi tausayi hakan yasa ta komata kwanta bacci bayan tasha magani.

Sae kusan 10am ta farko a lkcn tadanji saukin jikinta sosae ganin baya dakin ne yasa ta mike ta shiga wanka sae da ta Kara gasa jikinta kana ta fito ta shirya cikin Holland dinta Dunkin riga da zani sosae tayi kyau suka da bawani kwalliya tayi ba.

A parlour ta same shi Yana ganinta fito ya mike da sauri ya isa gurinta ya taimaka Mata suka karaso tare sae shagwaba take masa shi kuma yana biye mata breakfast dinda ammi ta aiko dashi ya dauko musu suka ci bayan sun gama yaja hannunta sukayi dakinsa sakin baki tayi tana kallon yanda dakin ya tsaru komae white and sky blue nata Kuma pink and white furnitures din iri daya ne sas dae kowa da nasa wanka ya shiga yayi tana zaune tana game harya fito ya shirya cikin wani yadi Mae laushi gray kana suka fito tana makale a gefensa kamar wadan da akace za'a raba.

Suna isowa parlour sukaji door bell karasawa yayi ya bude ganin su Asiyane yasa yayi dariya suka gaisa suna tambayarsa ya kwanan angonci kallon Humaidah yayi yace"gata nan ta baku lbr"

Turo baki tayi tace"nidae bana so"

Yace "wayyo Allah baby bakya sone na fita da sauri ta juya tana masa Allah ya kiyaye San ta gane me yake nufi dariya kawae yayi ya wuce su kuma suka shaiga ciki suna Mata tsiya nan suka baje suna fira kan a jima baki suka fara shigowa Yi musu bankwana da fatan alkairi.

Najwah ma ba jimawa Huzaif ya ajiyeta nan suka hadu sukayi tayi nan ilham ke Basu lbrn soyayyar ta da malaminta Dan yaro ne Kuma da degree dinsa Computer science rashin aikin yine yasa ya fara karantarwa a islamiya.

Sosae suka tayta farikin ciki Kuma abunda ya Basu mamaki duk da yanda take yace yani ya gani Yana so.

Haka dae suka wuni curr sae gabanin magrib suka tafi. Humaidah harda sabon kuka, wanka tayi tareda kwalliyar ta cikin wani material blue tayi kyau sosae nan ta fito parlour ta kunna burner nan da nan gdan ya kauraye da kamshi haka ma bedrooms dinsu ko Ina sae kamshi yake Yi.

Bayan sallahr Isha king yayi sallama cikin parlour wata irin ajiyar zuciya ya sauke tareda lumshe Ido Yana ma Allah godiya. Humaidah dake zaune a parlourn taji shigowar sa da sauri ta tafi tana masa oyoyo sosae ya sakata cikin jikinsa Yana mae Kara yiwa Allah godiya.

Bayan yayi wanka suka ci abinci gada nan suka dawo parlour suna kallo mikewa tayi ta Shiva dakin ta tareda dauko wannan hard cover din ta Mika masa karba yayi Yana tambayar ta menene tace "ka bude ka gani Mana Amma sae naba kusa" smiling yayi yace"me yasa sae bakya kusa" zama tayi kan cinyarsa tace"sbd koda na mutu zaka karanta kana tunawa da wnn ranar" da sauri ya hade bakinsu guri daya dan baya so ta Kuma maimaita masa wannan kalmar ya yarda da mutuwa gsky ce amma shidae baya son jinta daga bakin ta daga nan lbr ya chanza Nima sae na Kama gabana.

     *A gurguje pls*

Bayan sati daya da aure ya dauketa suka tafi honeymoon a Paris (city of love❤) satin su biyu sun zaga gari sosae tareda nunawa juna soyayya sahihyarta kana suka wuce umrah satinsu biyu suka koma Dubai Dan yanada sakon da zae karbo anan suka bude sabon babin raywarsu wannan tafiya gaba dayansu bazasu taba mantawa da ita ba, wani Dan kareren zobe Humaidah ta siya masu su biyu a ranar da suka fita komae iri daya a cikin sa an rubuta *T&H* a hade sosae king yaji dadin kyautar data bashi nan sukaje aka musu zanen kansu yayi kyau sosae Dan sun fito tsaf dasu haka ma ya Mata alkawarin idan cikinta ya girma nan zasu dawo a masu wani sosae taji dadi. Daga nan suka fara Shirin komawa.

Bayan dawarsu soyayysa tace ban guri haka suka cigaba da kula da junasu sosae Kamar zasu Mae da juna ciki. Sunje sun gaisa su mama da Ammi har  gdan Najwah sunje.

Da king yaji mgnr malam Dawood da ilham ba karamin farin ciki yayi ba ba a tsaya Bata lkc ba aka saka rana nan da wata 7 masu zuwa. Dan ilham tace ita bazatayi koame ba sae walima kadae, bayan da su Humaidah basuyi ba akan ta Bari su rakarkashe Amma fir taki.

Neehal kam alhmdllh sosae yake gane duk abunda malam ke masa ya saka na ransa kafin shekara daya zae bama Asiya mamaki duk da ya dae na kiranta sae dae tunaninta da yakeyi sosae gashi duk ya jeme ya rame.

      Haka rayuwa ta cigaba da tafiya cikeda jin dadi duk da ba'a rasa akasin hakan. Bayan wata tara Najwah ta sunkuto katuwar babynta mace sak ita, barakallah zokuga murna gurin su Huzaif gaba daya danginsa sunji dadin wannan haihuwar nan son Najwah ya linku acikin zuciyoyinsu Dan sosae take samun kulawa daga kowane bangare gdan mama aka kaeta wanka. Bayan kwana 7 aka saka ma yarin su Ayshatul_muddah. Humaidah ji taje kamar ita ta haifi muwaddah tunda aka haifeta kullum suna tare bacci kawae ke rabasu har akayi suna.

Rayuwa ta ciga da tafiya bayan aurensu da wata biyu da kwana shida ciki ya shiga Humaidah hmmm ba'a mgn gaba daya king jiyayi Kamar kyautar duniya aka basa ya rasa Ina zae saka kansa harda babbar kyauta Yama dr nan fa Humaidah ta fara samun kulawa ta musamman.

Zaune yake a office dinsa yana karanta book dinda heartbeat dinsa ta basa sosae yake jin dadin abunda yake karantawa wani page ya bude inda aka rubuta"'*I know that you want to share everything to me, but my favorite is the love you shared.I function superbly because of you, my senses are sharper, and my heart beats a little bit faster.*Dayan page din ya koma yana karantawa "' *There are a lot of times that I am confused, but you cleared everything up. I was sad but you cheered me up, and I was betrayed but you showed me how to trust again.I never asked for so many blessings from God, yet here you are right beside me, and you are more than enough.I would not ask anything from anyone, because you are the one who complete my life, and you are the one that could give me the love that I need.I need not tell you the intensity of my love for you, because I would rather show and prove it to you.* Sosae yake enjoying Karan ta book din aduk sanda ya zauna cikin office aikinsa kenan. Yana cikin karatunne yaji anyi masa knocking daga ciki ya amsa da "come in"

Wani matashen yaro ne ya shigo bae rufe kofa ba sae ga wata budurwa itama ta shigo da sauri king ya mike ganin fuskar da bazae taba mantawa da ita a rayuwarsa ba jiki a mace ta karasa shigowa kanta a kasa dukawa tayi a gurin tareda fashewa da wani irin kuka Mae ban tausayi.

Rufe idonsa yayi Yana jin kukanta nata gaba daya baya son ganinta hakan yasa ya tattara komae nata ya watsar. Cikin muryar na dama tace"Dan Allah Dan girman yarasulallahi Dan son da kakeyiwa mamanka king na rokeka badan na isa ba sae dan Ina neman yafiyarka ka yafemin wlh gaba daya na rasa sukuni a cikin zuciyata na rasa farin ciki ko kadan Dan Allah ka yafemin wlh bazan Kara ba"

Ba karya ta bashi tausayi Amma ya dauke kae  ganin haka  yasa Ahmad bashi hkr sosae sae can yace ya hkr ba kamae Allah ya yafe mana baki daya sosae ta masa godiya kana suka bashi IV din aurensu suka tafi. Shima hada kayansa yayi ya wuce gda.

Da shigarsa kamshin girki dana turaren wuta ya dake sa ga wani sanyi mae ratsa zuciya, jin motsinta  a kitchen ne yasa ya ajiye jakarsa a parlour ya shiga kitchen din gaba daya ta dage sae aiki takeyi ta bayanta ya rungumeta a razane ta saki wani ihu yayi saurin hade bakinsu sae da ta nutsu kana ya sake ta tace"matsoraciya"
Turo baki tayi tana"toh ba kaene ba"

Yace"ba wani me ake dafa Mana haka"

Tace"ur fav"

Smiling yayi tareda Kae Mata peck a kumatu yace"thanks best wife in the world"

Itama smiling tayi tace"nm best hubby" kumatunta yaja kana ya wuce daki danyin wanka itama bata jima ba ta jera koame kana ta wuce daki sukayi wanka bayn sun shirya suka fito cikeda nishadi suka nufi dining.

Rayuwa Mai juyi yanda ta so kwanaki sae tafiya sukeyi sosae. Ranar Friday aka daura auren Beeboh da Ahmad dinta inda anan kano zasu tare king kuma yaje kamar yanda aka gayyacesa,

Zakuyi mamaki idan nace muku a cikakkiyar mace Ahmad ya samu Beeboh dama duk iskancin Bata bin maza Bata taba bada kanta a titi ba hakan yasa Ahmad ya Kara sonfa.

Gidan Kuma yayi kyau sosae Dan ta cire kudinta ta siya Kaya masu matukar kyau. Haka ma sauran kudinta ta bama mijinta akan a gina masallaci da rijiya da islamiya Allah ya Kae Lada ga iyayenta company dinta Kuma wani cousin bro dinsu ya cigaba da kuka dashi Dan ita tace yanzu batada lkhn sa saena aurenta.

Su ilham ma sae shirye shiryen biki ake tayi sosae ammi ke gyarata ciki da bae idan ka ganta baza kayi tunanin ita bace gaba daya ta chanza ta Kara kyau.

Satin ta biyu a gdan su ta dawo gdan Ammai aka cigaba daga Inda aka tsaya.

Yanzu cikin Humaidah wata 7 da kwanaki ganin cikin ya fiti sosae me yasa king daukarta suka tafi Dubai kamar yanda ya Mata alkawari nan suka siyo kayan baby masu kyan gaske sosae sukayi both na maza da matan Dan Basu San me zasu Haifa ba.  Satin su uku suka dawo.

Sanye yake da wani yadi Mae laushi baki ya murza hularsa zanna bukar yayi kyau sosae cikar haibarsa ta Kara fitowa. Tsaye yake gaban gdansu Yana jiran yaron daya aika cikin gdan ya fito ba jimawa sae gashi ya fito yace"tace gata nan zuwa ".

Dari biyar ta ciro ya bashi yace yasha alawa ae ko ya tafi Yana godiya. Bata jima ba sae gata ta fito gabanta ne ya fadi ganin Wanda batayi tsammani ba. Jiki a sanyaye ta karasa gurinda yake tareda dauke kae Bata ce masa komae ba.

Murmushi yayi yace"sannu da fitowa an fito lpy"

Cikin tsiwa tace"da ban fito lpy ba zaka ganni a nan"

Nan ma smiling yayi yace"toh Kamar yanda kika bukata na sae na zama Mae ilimin addini na Kuma chanza halayyana toh gani a gabanki a matsiyin Neehal ba Wanda kika sani a baya ba"

Ita wlh ya bata mamaki dan ba tayi tunanin zae dauki mgnr ta serious ba wani dadi taji cikin ranta amma a fili tace"ka taimakawa kanka sae anjima"

Da sauri yasha gabanta yace"haba Sarauniya Asiya ki tsaya ki fahimce ni Mana wlh gaba daya na chanza believe me idan baki yarda ba zaki uya jaraba hakan"

Tsaki tayi tace"kaga malam nifa anmin miji sannan Kuma ae Dan ma gyara kanka na maka haka bawae dan Ina sonka ba Dan yanzu haka nan da wani wata zaamin aure da Wanda nake so Dan haka umma ta gaida ashsha kaga tafiya ta"

Ae Bata karasa ba sae ganinsa tayi a kasa kwance wani irin ihu tayi tareda durkusawa kasa tana fadin"wlh Wasa nake maka Neehal Ina sonka Allah kuwa Dan Allah kayi hkr ka tashi karka jamin mutane yanzu Allah nikam da Wasa nake kaene mijinda  za'a min aure dashi fa wani wata plss karka min haka wlh idan ka mutu bazan taba yafewa kaena ba"

Da sauri ya mike yace "alhmdllh my Queen"

Zaro Ido tayi daga nan ta shige cikin gda da gudu Dan kunyarsa ta kamata.
Tunda wannan rana suka fara soyewar su cikin kankanin lkc shakuwa ta shiga tsakaninsu Mae karfi.

Ganin haka yasa baban Asiya cewa ya turo Dan ya gaji da ganinsa a kofar gda kullum ba jimawa aka tsaeda magana tare za'a Yi Dana ilham hakan kuwa yama Neehal dadi.

Tunda aka saka rana mama tace zatayi Mata kayan kitchen Dan haka karsu wahar da kansu haka ma king ya dauki nauyin kayan parlour Dana dakin Neehal Humaidah da Najwah kuwa sukace zasu gyara Mata daki,ranar har kukan farin ciki Asiya tayi .

Nan mamanta ta shiga gyara ta sosaw Dan biki sae karatowa yakeyi.  Bayan sati biyu aka aiko da lefen Yar gata Dan Neehal kam yayi kokari sosae abun sae son barka.

To fa ko wane bangare sae shiri akeyi Neehal ya dage akan sae anyi dinner Dan haka suka yanke akan zasuyi dinner da walima kawae itama ilham bayanda ta iya dole ta hkr ta biye musu.

Gaba daya kayan da zasu saka baban ilham ya dauki nauyi har event hakan yasa iyayen Asiya suka Kara jin dadi sae addu'a suke zubawa.

Ranar da lkc ya cika aka fara gudanar da biki duk da Humaidah tayi nauyi haka take daurewa ana wasu abubuwan da ita sosae suka Mata dariya Dan haka sukama Najwah kamar tayi kuka haka take ji duk ranar da suka Mata haka sae king yace gobe bazata dawo ba sae sun bada hkr kana.

Yau aka sakawa amare lalle gaba daya gidan ya hade da hayaniyar yan biki.

Sae washe gari aka daura auren Neehal da Asiya kana aka daura na ilham da Dawood a inda dunbin mutane suka shaeda auren farin ciki abakin ko wanne baa mgn.

Bayan an gama pics aka wuce reception.

Da yamma akayi kayatacciyar walima Dan tasu tafi tasu Najwah dadi tunda dae su itace main even dinsu. Sae kuna da dare akayi hadaddiyar dinner bayan an gama aka kwashi amare sae gdan su.
Toh Allah bada zaman lpy da hkr da juna.




Vote
Comment
Share

Continue Reading

You'll Also Like

243K 8.8K 53
Anhay Sharma:- Cold business tycoon who is only sweet for his family. He is handsome as hell but loves to stay away from love life. His female employ...
41.3K 2K 47
The Rajputs well known as the most powerful and devil's for the people who tries to messed up with them people got goosebumps just by listening to th...
392K 15.6K 48
Vikram, a senior officer, prioritizes his duty above all else, much like his father, ACP Rajendra. He has three siblings: one is an officer, and the...
1.5M 129K 62
RATHOD In a broken family, every person suffers from his insecurities and guilt. Successful in every field but a big failure when it comes to emotio...