🤫SAINA AURI MIJIN 'YATA (TA...

By UMMU_DILSHAD

3.8K 121 2

HAJIYA RAHMATU TA DAKA TSALLE TACE SAITA AURI MIJIN 'YARTA HAJARA WACCE TA RASU BAYAN AURENTA DA UBAIDULLAH W... More

SAINA AURI MIJIN 'YATA TA CIKINA (1)
EPISODE 2
EPISODE 4
EPISODE 5
EPISODE 6
EPISODE 7
EPISODE 8
EPISODE 9
EPISODE 10
EPISODE 11
EPISODES 12
SANARWA

EPISODE 3

278 6 0
By UMMU_DILSHAD

*🤫💔🤫SENA AURI MIJIN ƳATA, (TA CIKINA)🤫💔🤫*

          By

*Ummu dilshad*

*Wattpad_@ummudilshad*

*Facebook_Shamsiya Abdullahi*

*Email_@ ummudilshadauthour30@gmail.com*

*Instagram_@Officialummudilshad*

*Watsapp_07013872581*

*INTELLIGENT WRITERS ASSOCIATION®️✍️*
     (Onward together)

👆Wannan book din daga farko har karshe sadaukarwa ne ga ilahirin Yan kungiyarmu, Ina alfahari daku gabadaya, musamman *My*(Janafty).....sannan *boss* (mom afra) tamu gabadaya muna kaunarki Kuma muna alfahari da ruling dinki agaremu kedin shugabace ta kwarai, bazan manta dakeba *magatakarda*(ZM chubado), tareda sauran members din gabadaya harzuwa kaina, bazan iya lissafoku dukaba saboda innace zan lissafoku kuma infadi irin kyawawan halayyarku, to kuwa bazan taba samun damar rubuta wannan novel dinba gabadaya sedai tundaga page 1 harzuwa karshe zan Kai Ina fado irin Alkairanku Kuma Basu kareba, sakamakon dunbin yawan da suke dashi. Ina godiya mara adadi, Allah yabarmu tare *Son So fisabilillahi*😍😘🥰.

Dedicated to,  *My Zeenat* (ummu Abdul & Islam) uwa ta gari kedin ta dabance a Raina.
zainab Muhammad *(Zee Musty)*. Jinjinar ban girma zuwa ga Ummu Suhaanar. Uwani Koko kema fa banmanta dakeba, dama sauran Yan group din UMMU DILSHAD NOVELS na watsapp, duk inajin dadin addu'oin da kukema Islam, Alhamdulillah tanata samun sauki. Ina GODIYA Sosai.

*BISIMILLAHIRRAHMANIRRAHEEM*

                   🤫_3

Hajiya Rahmatu tana shiga Fallon ta taras Babu kowa, se tashin kamshin Abinci dake Kara karade gidan, sannan Dan madaidaicin TV dake makale a jikin bangon fallon yanata magana.

Ganin haka yasa takara tabbatar wa da cewa akwai mutum a cikin gidan Dan Haka kawai seta samu guri ta zauna, kanta Yana matukar sarawa jitake kamar kanta ze cire, wani irin tukukin takaici na jin haushin mahaifinta Malam Haruna Yana Kara mamaye Mata zuciya, hawayen masu zafi suka Fara zuba daga idanuwan ta, a inda ta Fara yima kanta tanbayoyin da Basu da amsa acikin ranta tana fadin, _menayima *Abba* ne dayasa kwata kwata tun Ina karama baya kaunata? Gashi yanzu yajawo  itama *Umma* ta biyemai, meyasa arayuwa mutane inkayi me kyau ba'a tankawa sekayi akasin Haka sekaji ancika gari da zancenkane? Meyasa mutane basa iyayin temako alokacin da kake bukatar hakan? Meyasa bil'adama ke saurin yanke hukunci akan abunda Basu tanbayi dalilin faruwarsa ba? Meyasa mutane basa yin uzuri akan abubuwa ko halayyar mutane ne? Tanbaya ta karshe meyasa bazaku tsaya ku saurareni, ko ku tanbayeni dalilin son Auren mijin yata Hajara ba????????

Momy.......!!!!!!!!!!!

Na'am! Cikin yanayin razana ta dago kanta da sauri tana kallon Wata kyakkyawar matashiyar yarinya da bazata wuce shekaru 16, wacce ta Dade a tsaye tana fadin Momy... Yafi a kirga harseda ta gaji da Kiran ta tabata sannan ta dago. Momy Lafiya naketa kiranki kin sunkuyar dakai Baki amsaba, Kuma Lafiya naga kina hawaye meke damunki momy? Se alokacin Hajiya Rahmatu ta lura da Sanyin hawayen dake gudu akan kumatun ta, da sauri ta goge tareda fadin Babu komai *Habiba*, Ina *Habib* da *Amira*. A takaice Habiba ta amsa Mata da *suntafi Hadda*, Nima dama inata saurine insamu ingama girkin Nan inkaima *Anty Hajara* asibiti kinsan jiya tace tanaso in dafa Mata fryied rice da kunun Aya da soyayyan Naman rago, to gurinneman namanne na Dade Dan kusan duk masu danyan Naman shanu suka yanka, Amma yanzu na gama zan wuce in Mika Mata,  in 4:00 tayi se inwuce Islamiyya Dan yau zamu fara jarabawa, momy su *Kaka* Kika Bari acan tareda ita Hala?.

Ganin Momyn tasu Bata kulatabane se aikin zubda sabon hawaye da taketa famaryi ne yasa Habiba tsagaitawa da dogon surutun dataketayi tareda tsugunawa agaban momyn tasu tana fadin Momy Wai Dan Allah meke damunkine? Tunda Kika shigo kiketa zubda hawaye? Meke faruwa ne kodai jikin na Anty Hajara ne yayi Kara zafi?

Yanayin yadda Habiba tayimata Tanbaya yasa zuciyar ta gabadaya ta gama karaya, batasan sanda kuka me karfin gaske ya kwace Mata takasa controlling kantaba, wiwi take Kuka me fidda sauti tareda yin sauri tana jawo Yar tata ta kankame tana fadin, *innah nillahi wa innah ilaihirraji'un, Habiba munshiga Uku, asirinmu ze Kara tonuwa, kuda samun ingantaccen ilimi Har abada, muda Kara yin rayuwar jin dadi kila se alahira, saboda Allah yayima hajara rasuwa! Tafada tareda Kara fashewa da wani sabon kuka.

Da sauri Habiba ta janye jikin ta daga na momyn tasu tana fadin,  inna nillahi wa innah ilaihirraji'un, tamike tsaye tareda dore hannayenta biyu akanta tana rusa Kuka tana sanbatu, _yanzu shikenan Anty Hajara, kina nufin kintafi kinbarmu kenan? Kina nufin yanzu bazamu kara ganinki ba kenan? Munshiga Uku burinmu nida sauran Yan uwane shida cika har abada, muda yin aure har abada tunda jama'a kyamarmu sukeyi ke, dagamu har mahaifiyar mu Haka zamu mutu bamuyi aureba, Allah kagani Kuma kana gani Allah kafiddamu._ Tafada tareda kifa kanta ajikin bango tana cigaba da wani sabon kukan.

Jitayi antabata tabaya, da sauri ta waigo, yayinda sukayi ido hudu da Hajiya Rahmatu, ahankali ta juyo da ita tasa hannunta ta share Mata hawaye tana fadin _yi shiru Habiba, In Sha Allah indai Ina Raye dukkanin wasu burika na rayuwarmu zasu cika, domin Allah ya riga da ya bani mijin aure Kuma Wanda na tabbatar da kyawawan halayyar shi na kwarai sannan ze daukeku amatsayin yayan cikin shi, sannan ze rikemu da gaskiya da Amana, sannan har abada bazamu tabayin damunsaniba, domin shi din na dabanne ba kasafai aka fiye samun irinsuba._

Share hawaye Habiba tayi tareda faɗin, Allah Sarki, lallai Allah me girmane buwayarshi ta isarma kowa, Allah baya barin wani Dan wani yaji dadi, naso Anty Hajara tana Raye Kika samu mijin aure me wadannan halayen dakika lissafo, domin tunbayan mutuwar Dady tafi kowa Shan wahala da  gidannan sannan babban burinta shine taga kowa yasamu abunda yakeso daga ciki kuwa harda San taga kinsamu mijin aure.

Wasu sabbin hawayen ne suka Kara gangarowa daga idanuwan Habiba, sannan ta kalli fuskar Momy, tace Allah ya jikan Anty Hajara, ya Mata Rahama, ya gafarta Mata yasa Aljannal Firdausi ce makomarta.

Ameen Hajiya Rahmatu tace sannan tace yanzu kawai ki wuce Unguwa Uku, gidanmu Dan  can Abbanmu yace awuce da gawar, toh ta masa dashi sannan tace to Momy mutafi tare Mana, gyada Kai tayi tareda faɗin A'a Habiba zan zauna in jira su Habib su dawo semu taho tare, To kawai tace tareda wucewa daki ta cire uniform din Islamiyyar da tasa ta fita ta wuce can gidan. Koda taje anriga da anwuce kaita kenan alokacin misalin karfe 3:50pm ne.

Itakuwa Hajiya Rahmatu, Kukanta taci ta koshi sannan ta tashi ta taje tayi wanka ta doro Alwala tayi sallar Azahar wacce alokacin, da akayi sallar batasamu tayiba domin ta tsaya tasa ita mamaciyar tayi tata sallar ne a inda ta temaka Mata gurin yimata al'wala. Dan Haka sallar Azahar din tafarayi tareda zama tanata yin addu'oin nemama Yar tata Rahama da gafarar Allah, har aka Kira la'asar nanma ta gabatar da ita sannan ta debo Abincin da Habiba ta dafa domin marigayiyar,  da niyyar taci Amma Ina kasa cin Abincin tayi zuciyar ta cike fal da damuwa tareda alhinin rasa Yar tata, tafara cin Abincin ne Bayan da tayi wani tunani da take ganin ze iya zama mafita a gareta, Dan Haka se ta tsinci kanta cikin samun saukin damuwarta da Kashi 20% cikin 100%.

Koda su Habib, da Amira suka dawo daga Islamiyya da misalin 5:50pm a Fallo suka taradda ita tana kwance akan kujera idanuwanta a rufe, sukayi sallama suka shigo, ta amsa musu sannan tasa kowa yayi wanka suka ci Abinci, Bayan sunyi sallar magriba, sannan ta fada musu cewa Allah yayima hajara rasuwa, Nan take hankalin yaran yayi matukar tashi a inda suka dinga Kuka da kyar ta rarrashesu sukayinshiru, sannan Bayan sunyi sallar isha'i ta kwashesu, suka tafi gidansu.

Koda suka je kasancewar darene yasa Babu mutane Sosai se makota da Kuma Yan uwa na jiki, Dan Haka suna shiga akasan sun zo saboda karadewa da gaisuwar jama'a da suke Tama Hajiya Rahmatu ta'aziyya. Malam Haruna Yana ban daki ya shigo kama ruwa yanaji an ambaci sunan Hajiya Rahmatu, Kuma yajiyo tata muryar ya tabbatar da cewa itace da sauri, ya fito daga bandakin tareda jefa Mata butar dake Hannunshi Wanda kafin ta karasa gareta dukkanin ruwan dake cikin butar  ya zube ajikin mutanen dake zaune a tabarmar dake shinfide atsakar gidan. Tareda daga murya da karfi Yana faɗin me Kuma kikazo yi gidana Ashe bance Miki karki kuskura ki tako gidanaba? Domin wannan Gidan baya maraba da dukkanin mutanen da suke aikata haramun sannan suna ganin daidai sukeyi, sannan basa maraba da mutane irinki masu tuban muzuru, inhar kinason kanki da arziki kizo ki fita daga gidannan kokuma ki tuba ayanzunnan ki tabbatar min cewa kin fasa aiwatar da wannan mummunan kudirin naki se in yafe Miki yafiya ta har abada, Amma kuwa inkika tabbatar min da cewa har yanzu kina Nan akan bakarki to kuwa tabbas yanzunnan base anje da nisaba zan tona Miki asiri kowa da kowa yasan mummunan nufin da kike dashi Kuma kike Shirin aikatawa.......

Hhhhhhhhhhhhhhh tasaki Wata irin dariya wacce kowa dake gurin seda tsananin mamaki ya kamashi, Domin dariya ce me matukar fidda sauti tasaki wacce tayi sanadin lekowar ragowar jama'ar dake zaune a waje da sunan zaman makoki domin ganin meke faruwa, mamakine ya kama kowa ganin yadda Hajiya Rahmatu take dariya, da sauri kanwarta Rashida ta tashi ta wanke Mata kumatunta na dama  da wani gigitaccen Mari, sannan ta nunata da Dan yatsanta tana fadin, *Yaya Rahmatu* Wai Dan Allah wace irin haukace ta kama kwakwalwar kine zakizo kina Mana shirme kokin manta da abunda ya taramune anan? Karki manta fa yarki Hajara ce ta rasu dazunnan da Rana sannan kizo kina Mana dariya kamar wacce take tsakiyar taron bikin aure kokuma taron bikin Suna, inkinason kanki da arziki kizo kifita kibar gidannan inba hakaba zamu taru mu lakada Miki mugu duka wallahi.

Murmushi kawai tayi tareda kama yatsan da take nunata dashi ta lankwasa shi ahankali ta saukar da hannun sannan ta sakeshi da karfi tana fadin, ke malama kirufemana Baki kinjiko ke asuwa Zaki wani tsomo Baki irin ke ga ta Allah me fadin gaskiya ko, to matsa gefe Baki Kai wannan matsayin ba tukunna, Kinga Wanda ya Isa can tafada tareda nuna mahaifinta Malam Haruna sannan tacigaba da magana.

_Abba ka kwantar da hankalin ka zan barmaka gidanka yanzu ba se anjimaba, Amma kafinnan inaso in tabbatar maka da cewa Ina Nan akan bakata, domin naga alama wannan al'amarin na musamman ne arayuwata shine ze kawomin cigaba, shiyasa nasamu wadanda basa so da yawa ma'ana *Yan bakin ciki*, Kuma da kake maganar Wai zaka tonamin asiri, nama hutash sheka zan tona ma kaina indai cika wasiyyar mamaci zata iya zama wani babban abun da kake tunanin, inka fada ze iya zama tonan asiri agareni...fine jama'a ku saurara kuji Wai mahaifina ze tona min asiri, Dan kwai yata da ta rasu yau tabar wasiyyar cewa in auri mijinta, Kuma na Amince zan aureshi shine kawai bawan Allah Nan yaketa wani bude hanci tareda dukan kirji Yana fadin seyasa an jefeni....kujifa tafada tana jujjuyawa tana kallon mutanen dake zagaye da ita suna ta salati saboda Tsabar girgiza dasukayi dajin zancenta......daga musu hannu tayi tareda faɗin Dan Allah malamai ku rufe bakunan  ku kunjiko? Wannan har wani abune da har naji wasu na cewa Allah ya shiryeni, ridda nayi da zaku tasani agaba, har yanzu fa Ina Nan a musulmata ban fita daga Addinin Musulumci ba. Seta daga yatsanta daya tana nuna sama tareda faɗin *Ash hadu Anla'ilaha illallahu wa Ash hadu Anna Muhammadur rasulullahi* sannan ta karasa da *sallallahu Alaihi wa sallam*. Dan Allah a matsayin shi na mahaifina me yakamata yayi? Kowa shiru yayi Yana raba idanuwa Babu amsa, murmushin takaici tayi sannan tace nasan dukannin ku Baku da abun fada to Bari in fada muku, abunda yakamata ace yayi.....

Nafarko alokacin Dana Fara furta wannan magana, kamata yayi ya Fara yimin magana tareda nuni cewa banyi daidai ba Amma cikin natsuwa ta yadda zan fahimci ba daidai bane, Amma bawan Allah Nan beyi hakaba, inbanda zagi da cin mutumci da yabiyo baya.

Na biyu Kuma seya tanbayeni meye ma dalilina na kokarin aikatawa.

Na uku seya yi kokari gurin samo min mafita ta yadda zan samu wani abunda zai iya sawa inbar wannan kudirin nawa.

Amma duk beyi ko dayaba Dan Haka duk kufita kubar gidannan dannima fita zanyi inbarshi kamar yadda na fita daga cikin mahaifiyata kunsandai har abada nida komawa ko?

Wani dattijone dake baya ya daga murya Yana fadin, yarinya kema kina da gaskiya to Amma......daga mishi hannu tayi tana fadin kaga baba, zefi kyau kayi haƙuri da wannan kalmar ta *Amma* da kafara magana da ita Da kariga da kagama Bata duk wani Abu da kayi niyyar fada Dan bazan saurarekaba.

Tana gama magana ta waigo ta kalli Habiba tace ki kwaso kannenki kusameni a mota mu koma gida yanzunnan, ta juya zata fita kamar daga sama tajiyo muryar Habibar tana fadin......Babu inda zamu biki, cak taja ta tsaya sannan ta waigo afusace tace me kike nufi?

Gyada Kai tayi sannan tace Eh tabbas abunda kunnenki yaji mikine, bazamu bikiba, yanzu Ashe Dama mijin Anty Hajara kike so ki aura, shine dazu kike cemin kinsamu mijin aure, dama shine? Momy karfa ki manta ita yarkice Kuma ta cikin ki, wacce ta auri mijinta Watanni uku da suka wuce, a inda tun Daren ranar da aka kaita Bata kwana agidanta ba se a asibiti yau itace ranar da ta cika Watanni uku cif Kuma yau tabar duniya, Amma Kuma har kike maganar Auren mijinta, sanin kankine dai Koda zaku rage dagake se shi aduniya Babu aure atsakanin ku ko?

Dan Haka kawai ki wuce bazamu  biki ba, gara in mutu ban samu cikar burina ba indai Auren ki dashine ze zama silar samun komaina na Rayuwa. Tsananin takaici ne ya kamata , murmushin kafi kuka ciwo tayi sannan tace, ke yarinya ce bazaki taba ganewaba.............Malam Haruna ne ya karbe zancen da fadin _gaskiyane ita yarinya ce agurin ki bazata taba ganewaba kamar yadda kike yarinya agurina Kuma kema bazaki taba ganewaba, Dan Haka kawai kifita kibar gidannan, dama ita duniya haka take duk abunda kayi shi za'a yimaka, inkina takama ke kin Isa da har Zaki ki jin maganar iyayenki, to kema gashi kin Haifa wacce zata kijin maganar ki amatsayin ki na uwatta. Dan Haka gat Out... Yafada tareda nuna Mata kofa. *Kaji su baba Malam Haruna tsaffin malaman primary masu retired.*

Murmushi takumayi sannan tace Habib da Amira kuzo muje tunda ita bazatajeba, baya suka matsa suna fadin mudai zamu zauna Anan tareda su Kaka.

Wani irin mugun takaici ne ya mamaye ruhinta, afusace ta waigo ta kalli mahaifinnata tace..... Abba na gode kayi nasara ka rabani da yayana Amma kasani har abada bazaka taba rabani da kudirin wasiyyar mamaciya ba, namaka wannan Alkawarin.....tana gama magana tasa kanta tafice.

*Wannan book din na kudine duk wacce take son karantawa, tana iya biyan kudin karatu Naira 200 kacal👌...............ta wannan account din 👉👉👉👉0158547894, Shamsiya Abdullahi, GT Bank. Book ne me dauke da ilimantarwa fadakarwa tareda nishadantarwa,..... sannan akwai dunbin tausayi da sarkakiya Wanda akarshe komai ze warware. Ta watsapp za'a turo da shedar biya👉👉👉07013872581*

*SHAMSIYA ABDULLAHI (UMMU DILSHAD MRS YAHAYA).......✍️*

Continue Reading

You'll Also Like

5.6K 332 14
"he was her dark fairytale,and she was his twisted fantasy" 〜⁠(⁠꒪⁠꒳⁠꒪⁠)⁠〜 This is psychopathic Romance novel which is mix of office rom-com+marriage...
OBSESSED By BVRBIEN

Mystery / Thriller

110K 4.7K 28
obsessed
175K 8.7K 42
After going through a number of disasters I realized that actually I am reborn as the villainess character, more of a brat, Chloe Bourgeois, in a chi...
79.6K 2.6K 80
BANG... BANG..... BANG I jumped up out my sleep to three gun shots. I creep up to my door, opening it up just a little, seeing my father go to my...