MATAR DATTIJO Complete

By Jeeddahtou

90K 3.7K 25

Labari ne mai cike da soyayya tare da fadakarwar da nishadantawar wa, akwai darasi mai yawa da mata zasu dauk... More

MATAR DATTIJO page 1
MATAR DATTIJO page 2
MATAR DATTIJO page 3
MATAR DATTIJO page 4
MATAR DATTIJO page 5
MATAR DATTIJO page 6
MATAR DATTIJO page 7
MATAR DATTIJO page 8
MATAR DATTIJO page 9
MATAR DATTIJO page 10
MATAR DATTIJO page 11
MATAR DATTIJO 12
MATAR DATTIJO Page 13
MATAR DATTIJO page 14
MATAR DATTIJO page 15
MATAR DATTIJO page 16
MATAR DATTIJO page 17
MATAR DATTIJO page 18
MATAR DATTIJO page 19
MATAR DATTIJO page 20
MATAR DATTIJO page 21
MATAR DATTIJO page 22
MATAR DATTIJO page 23
MATAR DATTIJO page 24
MATAR DATTIJO page 25
MATAR DATTIJO page 26
MATAR DATTIJO page 27
MATAR DATTIJO page 28
MATAR DATTIJO page 29
MATAR DATTIJO page 30
MATAR DATTIJO page 31
MATAR DATTIJO page 32
MATAR DATTIJO page 33
MATAR DATTIJO page 34
MATAR DATTIJO page 35
MATAR DATTIJO page 36
MATAR DATTIJO page 37
MATAR DATTIJO page 38
MATAR DATTIJO page 39
MATAR DATTIJO page 40
MATAR DATTIJO page 41
MATAR DATTIJO page 42
MATAR DATTIJO page 43
MATAR DATTIJO page 44
MATAR DATTIJO page 45
MATAR DATTIJO page 46
MATAR DATTIJO page 47
MATAR DATTIJO page 48
MATAR DATTIJO page 49
MATAR DATTIJO page 50
MATAR DATTIJO page 51
MATAR DATTIJO page 53
MATAR DATTIJO page 54
MATAR DATTIJO page 55
MATAR DATTIJO page 56
MATAR DATTIJO page 57
MATAR DATTIJO page 58
MATAR DATTIJO page 59

MATAR DATTIJO page 52

890 36 0
By Jeeddahtou

💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
           *Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

52

Cikin zafin rai muka ji an danno kofar dakin,  ganinta muka yi a kan mu tana huci, a raxane na mike ina tambayarta lafiya Aunty me ya faru? kafin na ankara ta jawo wuyana ta fara xuba min wayar a jikina, cikin zafin nama Munir ya shigo tsakiyar mu kokarin karbar wayar yayi daga hannunta amma ta hana kokari kawai take yi ta kai min duka, cikin fushi ya fara yi mata magana, meye haka mama me yake damunki xaki xo har dakinta ki daketa me tayi miki? da karfi tasa hannu ta ingixa shi ta dawo kaina ta fara dukana, Cikin karfin hali na fara kokarin kwatar kaina saboda ina jin kunyar na rama dukan da tayi min a gaban danta, da karfi ya ja ta yayi gefe da ita, zaginsa ta shiga yi tare da cewa ni nake daure masa gindin yi mata rashin mutunci,kuma nice nasa ya kawo mata karuwa har cikin gida don haka daga ni har yarinyar sai tayi ajalinmu, da karfi ta Kara yin kaina tana fadin sai ta kashe ni, ina matsawa ta danki wuyan budurwar tasa ta shake da kyar ya kwaceta, daki muka shiga ni da budurwar tasa muka kulle kofa saboda yadda take cikin fushi tsaf xata iya hallaka mu, wayar dattijo muka kira, yana jin yanayin yadda nake masa magana ya gane ina cikin tashin hankali.

cikin kuka na fara yi masa bayani, kayi haquri ka sake ni wlh daga yau na gama aure da kai, cike da tashin hankali yake tambayata kafin na bashi amsa ta dawo kofar dakina tana buguwa tana Kokarin balle kofar da kyar danta ya ja ta ya mayar da ita wajenta ya kulle, shi ma kiran wayar dattijo yayi ya shaida masa halin da ake ciki, bangarena ya dawo ganin halin da nake ciki na tashin hankali yasa shi xubar da hawaye, kiyi hakuri Aunty mun san kina hakuri da mahaifiyar mu dan Allah ki cigaba da yi, kada wannan abin da tayi miki yasa ki tafi ki bar mu, kin ga dai a wajenki kawai muke samun farin ciki idan kika tafi bamu san wacce xa a auro mana ba ki tallafi rayuwar mu da ta mahaifin mu ki xauna, budurwar tasa ma kuka take ita kanta ta nuna baxa ta iya cigaba da soyayya da shi ba saboda mahaifiyar sa, rakata yayi ta hau Adaidaita saboda yana jin tsoron ya tafi kai ta gida ta sake dawowa ta dake ni.

A cikin mintunan da basu wuce goma ba dattijo ya iso ganin yadda ta hautsina min dakina ne yasa yayi saurin gane abinda ya faru tarar da ni yayi ina kuka Munir na bani hakuri.

jikinsa a sanyaye ya karaso inda muke, waje ya samu ya xauna yana fuskantar mu, cike da lallashi ya fara min magana, ko baki fada min ba nasan abinda ya faru kuma nasan wadda taxo tayi wannan aika-aikar saboda ita lamarinta baya bukatar karin bayani, amma kafin na xartar da hukunci ina so na tanbayeka munir, cikin nutsuwa ya dago ya kalli mahaifin nasa tare da cewa ina saurarenka daddy.

Gyaran murya yayi sannan ya fara magana, ka dubi girman Allah ka fada min gaskiyar abinda ya faru, kuma duk wanda yake da laifi a cikin wannan fadan, ka fada min ko da kuwa mahaifiyar ka ce kada ka duba alaka ka dubi Allah ka fada min gaskiyar lamari ina so na bawa kowa hakkinsa, saboda ina son na yanke hukunci a bisa adalci.

Cike da nutsuwa ya fara yi masa bayani, gaskiya daddy baxan boye maka ba duk abin nan da ya faru laifin mama ne, domin ita ta shigo ta hau aunty da duka saboda na kawo yarinyar da nake son na aura Aunty ta kula ta, wannan haushin ne yasa tazo tana dukanta, tambaya ya jefo masa, ka tabbatar da cewa niimatullah bata yi wa mahaifiyar ka wani abu na rashin kyautawa ba, da sauri ya amsa wallahi babu abinda tayi mata daddy.

A fusace ya tashi ya fita kai tsaye bangaren hajiya Maryam ya nufa, yau ko sallama bai yi mata ba saboda yadda xuciyarsa take tafasa, a kwance ya tarar da ita tana ganinsa ta wani marairaice ta fara kukan munafunci, dakatar da ita yayi tare da daka mata tsawa, da wannan kukan da kike min da Karar generator duk daya ne a gurina, insha Allah yau rashin kirkin da kike min ya xo karshe daga yau kin gama baxa ki sake yi ba, tunda na aure ki ban samu kwanciyar hankali ba nake cikin damuwa da bakin ciki, nayi hakuri da ke sama da shekara talatin amma har yanxu baki yi hankali ba, na kawo yarinya mai share min hawayena tana yi miki biyayya bata xo miki da tashin hankali ba amma kuma kina son sabauta rayuwarta, don haka ni baxa ki xo ki aikata abinda ba shi da kyau a gidana ba, don haka kije na sake ki saki biyu kuma yanxu nake son ki tattara ki bar min gidana.

Yana gama fada mata ya fita hannu ta dora a ka ta fara ihu, tana rokon ya yafe mata sai yanxu take ganin tayi kuskure saboda irin abubuwan da take yi masa shi da niimatullah, ji take dama ya dawo da ita ta gyara halinta su koma xaman lafiya da kishiyarta, ita kanta tasan niimatullah mutuniyar kirki ce tunda taxo bata taba yin abu don ta musguna mata ba, kuka sosai ta rika yi, tunani ta rika yi ko da wane ido xata dubi iyayenta idan taje tace an saketa saboda duk yan uwanta sun dade da sanin abinda take yi wa dattijo.

Sake dawowa yayi a karo na biyu tana ganin shi ta taho da gudu ta rike masa kafa, ka taimaka kayi hakuri ka mayar da ni mijina wallahi nayi nadama xan gyara halina, murmushi yayi tunda kika yarda na cire ki a raina baxa ki sake cigaba da rayuwar aure da ni ba, hakurina ya kare indai a kanki ne ,ki tattara kayanki ki fita kafin naci miki mutunci kuka ta cigaba da yi tana rokonsa, ganin yadda take kokarin bata masa lokaci ne yasa ya dauketa cak ya ajiyeta a waje ya jefo mata kayanta ya kulle dakinsa.

*dan Allah masu Karatu ku yi hakuri da ganin typing kadan hakan ya faru ne sakamakon lalacewar wayata yanxu ma da kyar nayi muku wannan da fatan xaku yi min afuwa*

*jeeddahtulkhair 😘*

Continue Reading

You'll Also Like

10.6M 246K 60
𝐅𝐫𝐨𝐦 𝐄𝐧𝐞𝐦𝐢𝐞𝐬 𝐭𝐨 𝐋𝐨𝐯𝐞𝐫𝐬 Enzo Mariano is known for being nothing but ruthless. He is feared by all in the Italian mafia. He kills on...
816K 73.3K 37
She is shy He is outspoken She is clumsy He is graceful She is innocent He is cunning She is broken He is perfect or is he? . . . . . . . . JI...
736K 42.7K 36
|ROSES AND CIGARETTES Book-I| She was someone who likes to be in her shell and He was someone who likes to break all the shells. "Junoon ban chuki ho...
514K 27.9K 18
𝐒𝐡𝐢𝐯𝐚𝐧𝐲𝐚 𝐑𝐚𝐣𝐩𝐮𝐭 𝐱 𝐑𝐮𝐝𝐫𝐚𝐤𝐬𝐡 𝐑𝐚𝐣𝐩𝐮𝐭 ~By 𝐊𝐚𝐣𝐮ꨄ︎...