MATAR DATTIJO Complete

By Jeeddahtou

89.8K 3.7K 25

Labari ne mai cike da soyayya tare da fadakarwar da nishadantawar wa, akwai darasi mai yawa da mata zasu dauk... More

MATAR DATTIJO page 1
MATAR DATTIJO page 2
MATAR DATTIJO page 3
MATAR DATTIJO page 4
MATAR DATTIJO page 5
MATAR DATTIJO page 6
MATAR DATTIJO page 7
MATAR DATTIJO page 8
MATAR DATTIJO page 9
MATAR DATTIJO page 10
MATAR DATTIJO page 11
MATAR DATTIJO 12
MATAR DATTIJO Page 13
MATAR DATTIJO page 14
MATAR DATTIJO page 15
MATAR DATTIJO page 16
MATAR DATTIJO page 17
MATAR DATTIJO page 18
MATAR DATTIJO page 19
MATAR DATTIJO page 20
MATAR DATTIJO page 21
MATAR DATTIJO page 22
MATAR DATTIJO page 23
MATAR DATTIJO page 24
MATAR DATTIJO page 25
MATAR DATTIJO page 26
MATAR DATTIJO page 27
MATAR DATTIJO page 28
MATAR DATTIJO page 29
MATAR DATTIJO page 30
MATAR DATTIJO page 31
MATAR DATTIJO page 33
MATAR DATTIJO page 34
MATAR DATTIJO page 35
MATAR DATTIJO page 36
MATAR DATTIJO page 37
MATAR DATTIJO page 38
MATAR DATTIJO page 39
MATAR DATTIJO page 40
MATAR DATTIJO page 41
MATAR DATTIJO page 42
MATAR DATTIJO page 43
MATAR DATTIJO page 44
MATAR DATTIJO page 45
MATAR DATTIJO page 46
MATAR DATTIJO page 47
MATAR DATTIJO page 48
MATAR DATTIJO page 49
MATAR DATTIJO page 50
MATAR DATTIJO page 51
MATAR DATTIJO page 52
MATAR DATTIJO page 53
MATAR DATTIJO page 54
MATAR DATTIJO page 55
MATAR DATTIJO page 56
MATAR DATTIJO page 57
MATAR DATTIJO page 58
MATAR DATTIJO page 59

MATAR DATTIJO page 32

1.7K 60 1
By Jeeddahtou

💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
         *Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

*wannan shafin gaba daya sadaukarwa ne gare ku masoyana wallahi a jiya na tabbatar da irin son da ku ke min babu abinda xan ce da ku sai dai godiya da fatan gamawa da duniya lafiya*

My daughater Aysha yar london, Queen maryam (maman surayya),Maijidda saleh, mabaruka Lawal, Billy santaly, Bilkisu mai gado(maman irfan)Hafsat muhd, Rukayyat muhd, Mom Habib....
Ummieee..........
Kaltuma bala Muhammad.
Sadiya Abdulahi....
Fateemah.............
Aisha.............
Habiba dakare........
Hussaina Junaid......
Haleemah Ibrahreem
Bilkisu Basheer...
Fatima m Sani ummu tauheeder...
Subai'at U Sarki....
Maman Khalid
Maman ikraam
Zaynab Adam
  Ummu Nur
maman haneepa
Hajjo Ahmed
(beauty)
Ummita❤
Ummu Muhseen
Hauwa Muazu
Farida sani
Waleeda sani
Fatima dutse
Mmn yesmeen
Aysha h waziri
Mmn intisar
Teemash❤❤ Saudat sanee yero
Dafseeyya Ameen
Jzaynerb umman amal
Ummi
Afnan &Afrah
.meerah luv
zainab rimi
.hafsat rimi
.Queen billy,Aysha Ahmad Muhammad
Amina jafar Ahmad jby,ShareefahUmmu farouk,Faiza jibril
Maman safwan ( fauxee)
Zainab Ahmad Ameena medabeeno
Ummuo serjeederh
.Nana Khaslim
.zainab
.Hannatu abidjan
sauran masoya ku yi hakuri da sannu xaku ji sunayen ku.

32

Haka na kwana jikina duk ba dadi banda tunanin innata ba abinda nake yi, Allah-Allah na rika yi gari ya waye na tambayi dattijona xuwa gidan innata.

yau ta Litinin kuma a yau din kwanakin amarcina da dattijo ya kare a yau xai koma wajen abokiyar xamana da kwana gaba daya bana jin nishadi saboda ko kadan bana so nayi nisa da mijina, gari na wayewa na kintsa ko'ina na gidana, shiryawa nayi cikin wasu tsadaddun English wears na nufi wajen dattijona, cike da nutsuwa nake taku dai-dai tare da sakar masa murmushin da a koda yaushe yake saka min shi nutsuwa da nishadi, cikin salon soyayya ya bude min hannunsa na fada jikinsa kwantar da kaina nayi a kirjinsa ina kashe masa idanu,cike da shagwaba na dube shi dattijona!!

cikin nutsuwa ya dago kyawawan idanunsa tare da jan kumatuna na'am my Niimatullah?

cikin siririyar murya na fara yi masa magana, dan Allah alfarma naxo nema wajenka angona, shafa gashin kaina yayi, wace alfarma kike nema yar lelen dattijo? kara narkewa nayi a jikinsa sannan na fara yi masa magana. ka bar ni naje gida naga innata yau da tunaninta na kwana na tashi idan ban ganta ba baxan iya bacci ba. cikin kulawa ya bani amsa gaskiya baxan bari ki fara fita yanxu ba amaryar dattijo, satin ki daya fa rabonki da gidan innah amma har kin kosa ki koma, kuma naga jiya innah taxo ta ganki, baba ma da kanshi ya fada min kada na bari ki fara fita sai bayan wata shida, Allah ya sani ina sonki kuma ina kishinki baxan bari ki fara fita yanxu ba, saboda har yanxu kina nan a budurwar ki babu wani kala da matar aure da kika yi baxan barki fita ba wani ya kwace min ke.

turo baki nayi tare da kara kwantar da kaina a jikinsa haba dattijona duk abin nan da ya faru kace ban xama matar aure ba Allah ni dai na xama kawai wayo kake so kayi min, murmushi yayi tare da kanne min ido, baki xama ba fa Niimatullah da saura saboda sau daya abin ya faru idan kina so na barki sai na kara yi kamar sau uku.

da sauri na dago na kalle shi sau uku fa kace,Allah ni dai a'a murmushi yayi min sannan ya cigaba da magana, tunda baxa ki yarda ba sai ki yi ta xama a gida,na rika xuwa ina dakko innah tana ganin ki amma ke dai baxa ki rika fita waje ba har sai kin xama matar aure sosai. kuka na fara yi masa ina masa magiya amma yayi shiru yaki bani amsa, na lura dattijo mutum ne mai kulle, magiya dai nake masa amma har yanxu yana nan a kan bakansa na mayar da ni matar aure.

cike da kulawa ya dube ni my Niimatullah bari na tashi na tafi wajen maman munir tunda yau a dakinta nake, amma gaskiya kafin na tafi ki bani kulawa saboda nasan xan yi missing din ki kafin na dawo, hawaye naji ya fara xubo min daga idona,  yanxu tafiya xa kayi ka bar ni dattijona sai da ka bari na saba da kai sannan xaka tafi ka kyale ni, ni gaskiya baxan iya kwana ni kadai ba sai dai ka mayar da ni wajen innata, hannu yasa ya shiga share min hawayen.

kiyi hakuri my Niimatullah kwana uku kwai xan yi a wajenta sai na dawo gare ki,ina son kwatanta adalci a tsakanin ku ne shi yasa bana son na dannewa kowa hakkinsa, banda wannan dalilin babu abinda xai sa nayi nisa da ke, amma har cikin xuciyata nafi son xama a dakin ki domin shi ne aljannar duniyata, kina min duk abinda nake so kina bani kulawa shi yasa bana son na bar ki ko da na minti daya ne.

cike da shagwaba nace to don yau a dakinta kake sai ka tafi da wuri haka, ai bari xa kayi sai dare xaka je, shafa fuskata yayi ya kara manna ni a kirjinsa, haka ne ka'ida Niimatullah yanxu ya kamata na tafi wajenta naga ya ta kwana ita da yaran mu, tunda dai lokacinta ya shiga kada ki damu xan rika xuwa wajen ki ina ganin ki, Niimatullah ki sani ko da kin yi nisa da jikina soyayyar ki na nan a cikin xuciyata, duk inda naje a duk inda na kasance ina tare da tunanin ki.

rarrashina ya shiga yi tare da romancing dina har sai da na manta dukkan damuwata, kwanciya nayi a wuyan shi ina jin radadin barina da xai yi, don a yanxu na fara sabawa da soyayyar dattijona, ban jin xan iya jurewa rashin shi.

A dai-dai lokacin muka ji an bude kofa an shigo, da sauri muka daga kai don ganin wane ne, matar dattijo ce rike da kugu take kare mana kallo, cikin fushi ta fara masa magana, yau fa xaka dawo dakina amma gashi har kusan karfe goma ban ga keyarka ba saboda tsabar rashin adalci me kake nufi da hakan? saboda ka auro wannan kaxamar yarinya karuwa xaka samu damar wulakanta ni.

shiru dattijona yayi yana naxarin maganganunta, ba karamin xafi kalamanta suka yi min ba, ganin ba shi da niyyar cewa komai yasa nima na mike, cike da tsiwa na bata amsar maganarta, kada ki sake ce min karuwa domin kula da mijinki kika kasa naxo na taya ki kula da shi, kaxawar ki ita ta janyo har ya ganni yaga na dace da rayuwarsa sannan ya aure ni, da kin cika cikakkiyar mace da baki yi sake an yi miki kishiya ba, ki dube shi ki gani da lokacin baya da yanxu daya yake?daga xuwana gidan nan ya canja yayi kiba hankalin sa ya kwanta saboda yana samun abinda yake so. juyawa nayi na koma jikin dattijona na kwantar da kai bisa kirjinsa.

Dattijo yayi mamakin maganganun da Niimatullah ta fadawa Hajiya Maryam, a cikin xuciyarsa kuma yayi nadamar kwancewa uwar yayansa xani da yayi a wajen Niimatullah da har ya fada mata cewa rashin kulawa da shi da bata yi ne yasa ya aureta,(don haka ya kamata maxa su hankalta idan sun je neman aure su daina fadar aibun iyayen gidan su ko don kaucewa samun raini tsakanin uwar gida da amarya).

A fusace ta karaso wajena ta dalla min mari, wata kara mai firgitarwa na saki, cikin masifa take min magana, ni xaki fadawa wannan maganar dan uban ki yaushe kika xo duniya har kika yi wayon da xaki fada min bakar magana, da sauri dattijo yaja hannunta ya fitar da ita,ni kuwa banda aikin kuka babu abinda nake yi.

har falo ya kai ta ya ajiye ta, rarrashinta ya shiga yi kiyi hakuri momyn munir ban auri Niimatullah don na toxarta ki ba, kina da matukar muhimmanci a wajena saboda kece uwar yayana, na auri Niimatullah ne don ta taimaka miki ki gyara rayuwar auren ki da kika bari a baya, idan kika yi kokarin raba ni da yarinyar nan xan iya shiga matsala,ko kina so na fada halaka ne, na rika bin matan banxa? kuma dan Allah ina rokonki ki daina kokarin xagin yarinyar nan kinga tun yanxu ta fara ramawa, sannan ga marinta da kika yi wanda hakan babban kuskure ne tunda dai ba yarki bace, ba kuma kanwarki bace, shawara nake baki ki nisanci yin hakan ko don gudun wata rana kada ku yi doke-doke da ita domin na lura hakurinta ya fara karewa.

shiru tayi tana saurarensa daga bisa ni kuma ta sauke ajiyar xuciya tare da cewa, gaskiya ne abinda ka fada dadyn munir kuma nima naga kuskuren da nayi a baya kuma xan yi kokarin gyarawa, amma ni wannan tsinanniyar yarinyar ce baxan taba kauna ba, kuma wlh mu xuba ni da ita a gidan nan sai ta gudu saboda tsabar wahalar da xan bata.

Godiya yayi mata sannan suka cigaba da hira cikin farin ciki.

Har bayan sallar magariba banga dattijona ba babu shi babu alamar shi, ga shi ba ni da wayar da xan kira shi, kukana ne ya tsananta, a fili nake magana tun yanxu dattijona ya fara wulakanta ni saboda wannan tsohuwar matar tasa wallahi baxan sake kwana a gidan nan ba, bakin kofa na fita inda na tarar da ita a kulle don haka na hakura na dawo, kan gado na fada na rika aikin kuka, a fili na rika fadar da nasan haka aure yake da ban yi shi ba, ji nake kamar na haura katanga na gudu saboda xafin da gidan yayi min, tunanin nasihar da innata take min nayi inda take fada min cewa aure ibada ne dole akwai jarrabawa a ciki, kuma duk inda ibada take tana bukatar hakuri da juriya, wanda idan aka yi hakuri aka jure sai Allah ya bawa mutum dukkan abinda yake nema, wannan nasihar da na tuna ita ta kwantar min da hankali, nayi bacci mai dadi.

gari na wayewa na xuba ido ko xan ga dattijona ya shigo amma shiru bai leko ni ba, don haka na shiga hada kayana ina cigaba da kuka, duk na hargitsa dakin, a dai-dai lokacin naji an turo kofar dakin da nake. muna hada ido nayi gefe da kaina,
cike da nutsuwa ya karaso wajena tambayata ya fara yi, lafiya Niimatullah ina xaki je kike hada kaya?cikin kuka nake masa magana baka sona dattijona gida xan tafi,Allah kuma sai ka sake ni a kan wannan tsohuwar matar taka ka tafi ka barni na kwana ni kadai, Allah sai na koma gidan innata.

rarrashina ya fara yi, kiyi hakuri my Niimatullah wlh ina sonki, kuma aurena da ke mutu ka raba, idan kinga kin fita daga gidan nan sai dai idan ni ne na mutu ko ke kika mutu, amma a auren mu babu saki na riga da na yiwa kaina wannan alkawarin. kuma ban tafi na barki don na wulakanta ki ba sai dan na bata hakkinta kuma na tsayar da adalci a tsakanin ku, kuma jiya ma kin min laifi, me yasa kika cewa matata don bata kula da ni na auro ki, shin yanxu baxan iya yin sirri da ke ba xabina, kina so ki rika tona sirrina ba a wajen innah kawai ba har a wajen mutane, ki sani ina daraja matata saboda uwar yayana ce, baxan bari wulakanci ya shiga tsakanin ku ba, yanxu kina ganin akwai wadda xan bari taxo ta wulakanta ki? ba auren ki kadai ne abinda nayi ba Niimatullah har tarbiyyar ki a hannuna take, baxan bari ki dore a haka ba Niimatullah saboda xan iya mutuwa na barki ko kuma wani abin daban, kuma ina so na hada kan ku ne ku xama tsintsiya madaurin ki daya.  gaskiya guda daya ce baxan iya bari ki rika yin abinda bai kamata ba.

jikina ne yayi sanyi da maganganun da dattijona ya fada min, cikin kuka nace baka ga ita taxo ta fara yi min wulakanci ba har dakina kuma ta mare ni.

na sani Niimatullah amma duk inda babba yake babba ne ya kamata ki girmamata ko don yayan da ta haifa, kuma maganar mari duk nayi mata fada a kan haka kema kuma ki rika girmamata kin ji amaryar dattijo.

gyada kaina nayi alamar eh, cike da xaulaya ya fara min magana kin san ma wani abu ne, ni fa xuwa nayi ki bani kulawa don jiyan nan nayi missing din ki sosai, dago ido nayi ina hararasa Allah baka isa ba sai dai ka koma wajenta ai ba kwana na bane, da sauri ya mika hannu ya damko ni, kokawa muka shiga yi  banda aikin kuka babu abinda nake yi har sai da yayi abinda ransa ke so sannan ya kyale ni.

*follow me on wattpad @jeeddahtulkheer Tijj*

*jeeddahtulkhair😘*

Continue Reading

You'll Also Like

3.2M 204K 90
What will happen when an innocent girl gets trapped in the clutches of a devil mafia? This is the story of Rishabh and Anokhi. Anokhi's life is as...
341K 26.7K 15
MY Creditor Side Story ပါ။ Parallel Universe သဘောမျိုးပြန်ပြီး Creation လုပ်ထားတာမို့ main story နဲ့ မသက်ဆိုင်ပဲ အရင် character ကို ရသအသစ် တစ်မျိုးနဲ...
1.1M 15.5K 38
Ivy Williams had always aspired to complete her university journey without any interruptions or complications. However, not even two months into her...
673K 35.7K 51
𝐒𝐜𝐞𝐧𝐭 𝐎𝐟 𝐋𝐨𝐯𝐞〢𝐁𝐲 𝐥𝐨𝐯𝐞 𝐭𝐡𝐞 𝐬𝐞𝐫𝐢𝐞𝐬 〈𝐛𝐨𝐨𝐤 1〉 𝑶𝒑𝒑𝒐𝒔𝒊𝒕𝒆𝒔 𝒂𝒓𝒆 𝒇𝒂𝒕𝒆𝒅 𝒕𝒐 𝒂𝒕𝒕𝒓𝒂𝒄𝒕 ☆|| 𝑺𝒕𝒆𝒍𝒍𝒂 𝑴�...