MATAR DATTIJO Complete

By Jeeddahtou

89.9K 3.7K 25

Labari ne mai cike da soyayya tare da fadakarwar da nishadantawar wa, akwai darasi mai yawa da mata zasu dauk... More

MATAR DATTIJO page 1
MATAR DATTIJO page 2
MATAR DATTIJO page 3
MATAR DATTIJO page 4
MATAR DATTIJO page 5
MATAR DATTIJO page 6
MATAR DATTIJO page 7
MATAR DATTIJO page 8
MATAR DATTIJO page 9
MATAR DATTIJO page 10
MATAR DATTIJO page 11
MATAR DATTIJO 12
MATAR DATTIJO Page 13
MATAR DATTIJO page 14
MATAR DATTIJO page 15
MATAR DATTIJO page 16
MATAR DATTIJO page 17
MATAR DATTIJO page 18
MATAR DATTIJO page 19
MATAR DATTIJO page 20
MATAR DATTIJO page 21
MATAR DATTIJO page 23
MATAR DATTIJO page 24
MATAR DATTIJO page 25
MATAR DATTIJO page 26
MATAR DATTIJO page 27
MATAR DATTIJO page 28
MATAR DATTIJO page 29
MATAR DATTIJO page 30
MATAR DATTIJO page 31
MATAR DATTIJO page 32
MATAR DATTIJO page 33
MATAR DATTIJO page 34
MATAR DATTIJO page 35
MATAR DATTIJO page 36
MATAR DATTIJO page 37
MATAR DATTIJO page 38
MATAR DATTIJO page 39
MATAR DATTIJO page 40
MATAR DATTIJO page 41
MATAR DATTIJO page 42
MATAR DATTIJO page 43
MATAR DATTIJO page 44
MATAR DATTIJO page 45
MATAR DATTIJO page 46
MATAR DATTIJO page 47
MATAR DATTIJO page 48
MATAR DATTIJO page 49
MATAR DATTIJO page 50
MATAR DATTIJO page 51
MATAR DATTIJO page 52
MATAR DATTIJO page 53
MATAR DATTIJO page 54
MATAR DATTIJO page 55
MATAR DATTIJO page 56
MATAR DATTIJO page 57
MATAR DATTIJO page 58
MATAR DATTIJO page 59

MATAR DATTIJO page 22

1.4K 74 0
By Jeeddahtou

💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
          *Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

*dedicated to Aysha Abubakar shagari (babyn Hajiya) Allah ya gafartawa Hajiya yasa aljannah ta xamo makoma a gareta*

22

Ina shiga ya kullo murfin motar shi, cikin nutsuwa na dube shi tare da cewa gani dattijona, murmushi yayi tare da shafo fuskata, ina jin dadi idan kika kira ni da dattijon ki,cike da tsokana yake min magana Amarya bakya laifi ko kin kashe dan masu gida yau fa xan dauke ki mu tafi tunda baba ya yarda mu tare, dan turo baki nayi ka bari na xama Amaryar tukunna sai ka fada min haka, juyo da fuskata yayi yana kallona, tun yaushe kika xama ai kin dade da wannan matsayin a tare da ke, yanxu rayuwa a gidana ne kawai ya rage miki gyara xama yayi.

yau ina cikin farin ciki saboda samun amincewar baba da nayi a kan tarewar ki, ba karamin dadi  nake ji da hakan ba yau xan yi baccin da na dade ban yi irinsa ba, don tunda al'amarin nan ya faru ban iya bacci cikakke ba, dole na godewa Allah bisa ga niiamarki da yayi min, don samunki babban nasara ne a rayuwata, kamo ni yayi ya hada fuskata da tashi, na kusa fara bacci a yalwataccen kirjinki my Niimatullah

kaina a kasa ina wasa da yan yatsuna duk bayanan da yake min ina jin su a kunnena ban iya ce masa komai ba sai dai gyada kaina da nake yi idan yayi min wata maganar sake kallona yayi, kin san dalilin da yasa na kira ki yanxu? a hankali na dago tare da cewa a'a, fuskanto ni yayi sosai yana kallona gami da yi min murmushi, kasuwa nake so mu je nayi miki siyayyar kayan da xaki rika yi min ado da su a cikin gidan mu.

amsawa nayi da to, bari na je na fadawa innah, riko hannuna yayi yana min asirtaccen murmushin sa mai sanya ni kasala, ki bari mu je mu dawo sai ki fada mata, ko innah ta ji ki shiru baxa tayi xaton komai ba don tasan kina tare da mijinki, jan motar yayi muka wuce kasuwa.

kayayyaki masu yawa ya siya min, kayan sun kai kala arba'in banda sleeping dress na fitina da English wears da ya siya,  wasu abubuwan ma hana shi siye nake saboda ya kashe kudi da yawa.

tare da shi muka shiga gida, muna isa muka fara fito da kayan da ya siya innah tana ta masa godiya, cike da shagwaba na dubeta tare da daga wata riga da ya siya min, kalli wannan yar rigar innah yanxu a ce kamar ni yar musulmai ni xan sakata, sai da nace kada ya siyo min,  ya kama ya siya ki dauketa ki bayar ni bana so, cikin kulawa innah ta dube ni, babu komai idan kin saka Niimatullah tunda mijinki xaki yiwa kwalliya da ita,  wani wajen ne dai ba a yarda ki fita da ita ba.

kallon innah nayi ina son yin kuka Allah ni baxan saka ba sai dai ki bayar wannan ai kayan yan iska ne, da taga dai duk bayanin da tayi min ban fahimta ba sai kawai ta kyale ni, shi kuwa dattijo na gefe yana min dariya.

tashi yayi xai tafi, bayan sun yi sallama da innah ya dube ni, Niimatullah xo ki dakko ragowar kayan da muka bari a mota ki kawo gida,  kallon shi nayi ina turo baki, mu bamu bar wani kaya a mota ba komai mun kwaso ba inda xa ni, dubana innah tayi.

na hana ki wannan gaddamar fa Niimatullah tashi kije ko ba kayan da xaki dakko tunda yace yana bukatar hakan dole ki bi shi, tashi nayi ina tafe ina dukan kasa da kafata har na isa soro na tsaya ina turo baki, murmushi yayi min tare da karasowa inda nake,  my Niimatullah kada ki bayar min da kayan da na siyo domin ki,nafi son na rika ganin matata kamar yar tsana, ko kina so na rika kallon yan mata a waje? da sauri na dago kai nace bana so kuma duk macen da naga tana kallonka ma Allah sai na xaneta.

murmushi yayi, to kinga duk abinda nake so ya xama wajibi kiyi min indai kina son ki rintse min ganina, idan kuma kina so na rika kula yan mata sai qi ki saka min kayan da na siyo, kaina a kasa nace xan rika saka maka.

cike da farin ciki ya rungume ni tare da manna ni a kirjinsa yana sumbatata ina sonki my niima ina son ganin ranar da xan mallake ki amaryata, ki cigaba da sona da kaunata, nasan da cewa matukar zan cigaba da kasancewa a tare da ke, bana jin wata rana zan gamu da hatsarin da nake ji ana cewa so yana da shi, ke ta daban ce kuma ta musamman a cikin rayuwata, ina sonki Amaryar dattijo.

kaina a kasa na amsa da nima ina sonka, yanxu ina kaunar mijina ina jin wani shauki na musamman idan muna tare da juna, har na fara kosawa ya xama mallakina, muna gama magana ya sake ni na koma gida.

*yan uwa ina bukatar addu'ar ku domin ina kan hanyata ta xuwa jigawa*

*jeeddahtulkhair😘*

Continue Reading

You'll Also Like

357K 27.4K 15
MY Creditor Side Story ပါ။ Parallel Universe သဘောမျိုးပြန်ပြီး Creation လုပ်ထားတာမို့ main story နဲ့ မသက်ဆိုင်ပဲ အရင် character ကို ရသအသစ် တစ်မျိုးနဲ...
10.6M 245K 60
𝐅𝐫𝐨𝐦 𝐄𝐧𝐞𝐦𝐢𝐞𝐬 𝐭𝐨 𝐋𝐨𝐯𝐞𝐫𝐬 Enzo Mariano is known for being nothing but ruthless. He is feared by all in the Italian mafia. He kills on...
2.8M 25.7K 9
"Stop trying to act like my fiancée because I don't give a damn about you!" His words echoed through the room breaking my remaining hopes - Alizeh (...
314K 36K 25
"𝒚𝒐𝒖 𝒄𝒐𝒖𝒍𝒅 𝒃𝒓𝒆𝒂𝒌 𝒎𝒚 𝒉𝒆𝒂𝒓𝒕 𝒊𝒏 𝒕𝒘𝒐 𝒃𝒖𝒕 𝒘𝒉𝒆𝒏 𝒊𝒕 𝒉𝒆𝒂𝒍𝒔, 𝒊𝒕 𝒃𝒆𝒂𝒕𝒔 𝒇𝒐𝒓 𝒚𝒐𝒖" ...