MATAR DATTIJO Complete

By Jeeddahtou

90.5K 3.7K 25

Labari ne mai cike da soyayya tare da fadakarwar da nishadantawar wa, akwai darasi mai yawa da mata zasu dauk... More

MATAR DATTIJO page 1
MATAR DATTIJO page 2
MATAR DATTIJO page 3
MATAR DATTIJO page 4
MATAR DATTIJO page 6
MATAR DATTIJO page 7
MATAR DATTIJO page 8
MATAR DATTIJO page 9
MATAR DATTIJO page 10
MATAR DATTIJO page 11
MATAR DATTIJO 12
MATAR DATTIJO Page 13
MATAR DATTIJO page 14
MATAR DATTIJO page 15
MATAR DATTIJO page 16
MATAR DATTIJO page 17
MATAR DATTIJO page 18
MATAR DATTIJO page 19
MATAR DATTIJO page 20
MATAR DATTIJO page 21
MATAR DATTIJO page 22
MATAR DATTIJO page 23
MATAR DATTIJO page 24
MATAR DATTIJO page 25
MATAR DATTIJO page 26
MATAR DATTIJO page 27
MATAR DATTIJO page 28
MATAR DATTIJO page 29
MATAR DATTIJO page 30
MATAR DATTIJO page 31
MATAR DATTIJO page 32
MATAR DATTIJO page 33
MATAR DATTIJO page 34
MATAR DATTIJO page 35
MATAR DATTIJO page 36
MATAR DATTIJO page 37
MATAR DATTIJO page 38
MATAR DATTIJO page 39
MATAR DATTIJO page 40
MATAR DATTIJO page 41
MATAR DATTIJO page 42
MATAR DATTIJO page 43
MATAR DATTIJO page 44
MATAR DATTIJO page 45
MATAR DATTIJO page 46
MATAR DATTIJO page 47
MATAR DATTIJO page 48
MATAR DATTIJO page 49
MATAR DATTIJO page 50
MATAR DATTIJO page 51
MATAR DATTIJO page 52
MATAR DATTIJO page 53
MATAR DATTIJO page 54
MATAR DATTIJO page 55
MATAR DATTIJO page 56
MATAR DATTIJO page 57
MATAR DATTIJO page 58
MATAR DATTIJO page 59

MATAR DATTIJO page 5

1.8K 111 2
By Jeeddahtou

*Jeeddahtulkhair😘*[9/28, 8:53 AM] itz B Y ebrerheem: 💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO* 💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
         *Adam*  *(Jeeddahtulkhair)*

*dedicated to maimuna Aminu othman (Ommy)*

5

A ranar duk kiran da yayi min ban dauka ba yayi min missed calls ya kai talatin, haka ya hakura ya har ya daina kiran. gari na wayewa naji tsayuwar motarsa a kofar gidan mu, tsaki naja wannan tsohon nacin sa yayi yawa kamar tsohon maye, me kuma yaxo yayi min da sassafe haka, sallama yayi da baba ya fita xuwa gare shi.

A dakin soro aka sauke shi magana naji suna yi kasa-kasa don bana fahimtar abinda suke tattaunawa, bayan sun kammala ya fito ya ja motarsa ya tafi.

cikin gida baba ya shigo tarar da ni yayi ina wanke-wanke, kirana yayi da sauri na tsame hannuna daga ruwan wanke-wanken, tsugunnawa nayi cikin ladabi, magana ya fara yi min.

Niimatullah ya kira sunana, cikin sassanyar murya na amsa masa da na'am baba, gyaran murya yayi sannan ya cigaba da magana, kinga yanxu kin fara girma ko yar lelen baba? daga kai nayi alamar eh, to ina so naga na aurar da ke saboda sauke nauyin amanar da na dauka a wajen iyayenki da kuma cika hakkin da musulunci ya dorawa kowane uba a kan dansa.

a xabure na dube shi, aurar dani fa kace baba ka ganni fa yar mitsitsiya har yanxu ban girma ba, ni dai ba yanxu ba Allah. nasan har yanxu ke karama ce yar lele amma ai girma ya fara kama ki, don haka xan aurar da ke yanxu, amma baxa ki tare a dakin mijinki ba sai kin kara hankali da wayo, ina so na baki kariya ne daga fitintunun xamani da matasa ke afkawa sanadiyyar rashin samun abokin rayuwa, don haka xan aurar da ke ga Alhaji Sadeeq fatana dai ki xama mai biyayya a gare ni.

kuka ne yaxo min, hawaye duk ya cika idanuna baxan iya ketare umarnin baba ba saboda kulawar da ya bani a rayuwata ban san kowa ba sai shi da innah, cikin kuka na amsa masa da xan yi biyayya a gare ka baba.

cikin kulawa yace min,na gode Niimatullah Allah yayi miki albarka, amma idan bakya son wannan mutumin kiyi min magana saboda na yi wa kaina alkawarin baxan taba yi miki auren dole ba, girgixa kaina nayi bana 'kinsa baba ina son shi, kawai auren ne bana so gaba daya.  murmushi baba yayi

ki daina cewa bakya son aure Niimatullah aure sunnar Annabi ne don haka daga yau kisa a ranki ke matar aure ce, mikewa nayi na shiga daki wayar innah na dauka na kira Dattijon da ke sona cikin kuka nake masa magana.

me yasa kake son raba ni da gidan da tunda na taso nake a cikin sa, na saba da baba da innata baxan iya tafiya na bar su ba, rarrashina ya rika yi.

duk mace matar wani gidan ce Niimatullah ki kwantar da hankalin ki ko da an daura mana aure baxan tafi dake gidana ba, xan barki a wajen su innah har sai kin kara wayo kin bukaci mijinki da kanki, wani dadi ne ya mamaye min xuciyata, ban san lokacin da nayi wani ihu ba nace yauwa naji dadi, kasan wani abu kuwa??

da sauri ya amsa min da a'a, ko girki fa ban iya ba, innata bata bari nayi girki saboda bata so na kone, kuma kaga ai ba a aure sai an iya girki ko? amma dai na iya shara da wanke-wanke.

shirmen da Niimatullah ke yi ba karamin faranta masa rai yake ba, ko yana cikin damuwa idan ya saurari muryarta sai yaji dadi ya kama shi, murmushi yayi tare da cewa.

kada ki damu sai kin iya komai xan kawo ki gidana kin ji ko yar yarinyata?

murna na rika yi xa a koya min komai,  ranar cikin farin ciki muka rika waya ya tsokane ni na tsokane shi, Kullum yaxo hira sai ya taho min da kayan kwalliya da na gyaran jiki.

da kwalayen biscuit da goro naga ana ta shigo da shi cikin gidan mu, tambayar innata nayi ko na menene, cikin kulawa ta bani amsa.

na daurin auren ki ne Niimatullah, murna na shiga yi har da danne innah ina mata tsalle a ka. Alhamdulillah na kusa xama matar aure nima na fara samun lada, naji ance komai na matar aure ya fi na mara aure lada wai haka ne innata?. murmushi innah tayi kwarai kuwa, ke dai kin yi sa'a tun kina yar karama xaki fara samun ladan aure, murna muka rika yi ni da innah.

da misalin karfe biyu na rana aka daura min aure da Dattijo, ko a ranar ma sai da naje islamiyya, yan ajin mu sai mamaki suke yi wai ina da aure naje makaranta, ni kuwa ko a jikina don ban gama sanin ciwon kaina ba, yan manyan aji sai xuwa suke suna kallona,  wasu su ce nayi kankanta da aure wasu su ce iyayena sun yi dai-dai, kowa dai da irin abinda yake fada.

ina komawa gida na tarar da shi har yaxo, tsintar kaina nayi ina jin kunyar sa, yau a dakin innata aka sauke shi ita kuma innar tamu ta koma tsakar gida ta xauna.

08094136204 yawan comments yawan typing

Continue Reading

You'll Also Like

1.4M 109K 42
"Why the fuck you let him touch you!!!"he growled while punching the wall behind me 'I am so scared right now what if he hit me like my father did to...
4.4M 276K 103
What will happen when an innocent girl gets trapped in the clutches of a devil mafia? This is the story of Rishabh and Anokhi. Anokhi's life is as...
3.6M 286K 96
RANKED #1 CUTE #1 COMEDY-ROMANCE #2 YOUNG ADULT #2 BOLLYWOOD #2 LOVE AT FIRST SIGHT #3 PASSION #7 COMEDY-DRAMA #9 LOVE P.S - Do let me know if you...
2M 110K 96
Daksh singh chauhan - the crowned prince and future king of Jodhpur is a multi billionaire and the CEO of Ratore group. He is highly honored and resp...