MATAR DATTIJO Complete

By Jeeddahtou

89.9K 3.7K 25

Labari ne mai cike da soyayya tare da fadakarwar da nishadantawar wa, akwai darasi mai yawa da mata zasu dauk... More

MATAR DATTIJO page 1
MATAR DATTIJO page 3
MATAR DATTIJO page 4
MATAR DATTIJO page 5
MATAR DATTIJO page 6
MATAR DATTIJO page 7
MATAR DATTIJO page 8
MATAR DATTIJO page 9
MATAR DATTIJO page 10
MATAR DATTIJO page 11
MATAR DATTIJO 12
MATAR DATTIJO Page 13
MATAR DATTIJO page 14
MATAR DATTIJO page 15
MATAR DATTIJO page 16
MATAR DATTIJO page 17
MATAR DATTIJO page 18
MATAR DATTIJO page 19
MATAR DATTIJO page 20
MATAR DATTIJO page 21
MATAR DATTIJO page 22
MATAR DATTIJO page 23
MATAR DATTIJO page 24
MATAR DATTIJO page 25
MATAR DATTIJO page 26
MATAR DATTIJO page 27
MATAR DATTIJO page 28
MATAR DATTIJO page 29
MATAR DATTIJO page 30
MATAR DATTIJO page 31
MATAR DATTIJO page 32
MATAR DATTIJO page 33
MATAR DATTIJO page 34
MATAR DATTIJO page 35
MATAR DATTIJO page 36
MATAR DATTIJO page 37
MATAR DATTIJO page 38
MATAR DATTIJO page 39
MATAR DATTIJO page 40
MATAR DATTIJO page 41
MATAR DATTIJO page 42
MATAR DATTIJO page 43
MATAR DATTIJO page 44
MATAR DATTIJO page 45
MATAR DATTIJO page 46
MATAR DATTIJO page 47
MATAR DATTIJO page 48
MATAR DATTIJO page 49
MATAR DATTIJO page 50
MATAR DATTIJO page 51
MATAR DATTIJO page 52
MATAR DATTIJO page 53
MATAR DATTIJO page 54
MATAR DATTIJO page 55
MATAR DATTIJO page 56
MATAR DATTIJO page 57
MATAR DATTIJO page 58
MATAR DATTIJO page 59

MATAR DATTIJO page 2

2.2K 103 2
By Jeeddahtou

MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
           *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*

*dedicated to Fatima sammani Alatu*

2

Sunana Ni'imatullah muhammad, iyayena yan asalin garin kano ne muna xaune ne a unguwar tarauni, ni kadai iyayena suka haifa,  wannan dalilin yasa suke kaunata duk abinda nake so shi suke min matukar bai saba ka'idar shari'a ba, sai dai tafiya bata yi tsawo ba Allah yayi musu rasuwa sakamakon hadarin mota da ya ritsa da su,wannan dalilin yasa kulawata ta dawo hannun kakannina na wajen uba, suna ji da ni sosai saboda ni kadai ce jikar da suka mallaka kuma ni suke kallo a matsayin mahaifina, kasancewar babana shi kadai dan su a duniya. dangin mahaifiyata duk suna kauyen bichi idan an yi hutu nakan je musu xiyara.

ni yarinya ce kyakkyawa son kowa kin wanda ya rasa, Allah ya tsara min halitta ta dai-dai gwargwado idan ka ganni xaka iya cewa na fito ne daga salsalar buzaye ko larabawa. ni ba fara bace haka xalika baxa a saka ni a layin bakake ba,  amma xa a iya kirana da (chocolate colour)idanuna manya ne kuma farare tas, hancina dogo ne wanda shi ne yake kara fito min da ainhin kyawuna, bakina kuwa dan karami ne, ga kuma dimple wanda yake kara bayyanar da asirtaccen kyauna, ni ba doguwa bace amma kuma baxa a saka ni a layin gajeru ba, xan iya kiran kaina da matsakaiciya, gashin kaina kamar auduga yake saboda santsi da laushi da ake da shi yasa bana yin kitso saboda ina yi yake warware wa, mutane da dama suna kirana da mai kyau, rayuwa mai dadi nake yi tare da kakannina sun hana ni kukan maraici babu abinda na nema na rasa a rayuwata.
Da gudu na fito daga bandaki ina kiran innah, a firgice ta fito daga dakinta tambayata ta shiga yi me ya same ki Niimatullah kuka nake ina nuna mata bandaki, kije ki gani innah na shiga uku,  a raxane ta shiga bandakin ta fara lalube, ni ban ga komai ba Niimatullah, sake rushewa nayi da kuka ki duba pant dina ki gani innah, tana budewa taga ashe na fara jinin Al'ada ne, damuwa ce ta bayyana a fuskarta, bata so na fara da wuri ba saboda har yanzu ban gama mallakar hankalina ba, kwata-kwata shekaruna sha uku a duniya, gyara kayana ta shiga yi sannan ta jawo ni jikinta ta rungume ni, ni kuwa sai faman rusa ihu nake yi, lallabani ta shiga yi kiyi hakuri yar lelen baba haka Allah ya tsarawa kowace ya mace a rayuwarta, wannan ba wani abin damuwa bane ki kwantar da hankalin ki kin ji jikanyata, idona cike da hawaye na dubeta to yanxu yaushe xai tafi? shafa kaina tayi nan da sati daya ko kwana uku wata ma sai tayi kwana sha biyar bai tafi ba, xaro idona nayi kwana sha biyar fa kika ce innah, eh mana amma ya danganta da yanayin yadda Allah ya tsara miki, xai iya tafiya yau ma. bayan ta gama koya min yadda xan kula da kaina da jikina sannan ta yi min nasiha mai ratsa jiki, kinga yanxu kin xama cikakkiyar mace duk abinda yake kan tsohuwa yar shekara dari ya hau kanki don haka ki kula da ibada sannan ki daina guje-gujen da kike yi, kuma kada ki bar wani da namiji ya taba miki jiki ko da kuwa hannunki ne domin yana taba ki ciki xai iya shigar ki, saurin dagowa nayi na dubeta ciki fa kika ce innah, dama idan aka aurar da mace ba a ruwan randar gidan da aka kaita take sha ba? gyada kai innah tayi idan namiji ya taba hannunki ne kike daukan ciki don haka sai ki kula ki kiyaye. narai-narai nayi da ido xan yi kuka, ni dai ki bani magani nasha na daina yi innata, na karasa maganar tare da kwantar da kainaa jikinta, shafa bayana tayi kiyi hakuri Niimatullah xan yi miki addua xuwa gobe xai tafi, da murnata na dago na dubeta, da gaske xai tafi innah? xai tafi ke dai ki kwantar da hankalinki, da farin ciki na kwana a raina tun daga ranar kuma na kulke a rajna duk namijin da yayi min magana baxan sake kula shi ba.

*Jeeddahtulkhair😘*

Continue Reading

You'll Also Like

3.6M 153K 61
The story of Abeer Singh Rathore and Chandni Sharma continue.............. when Destiny bond two strangers in holy bond accidentally ❣️ Cover credit...
357K 27.4K 15
MY Creditor Side Story ပါ။ Parallel Universe သဘောမျိုးပြန်ပြီး Creation လုပ်ထားတာမို့ main story နဲ့ မသက်ဆိုင်ပဲ အရင် character ကို ရသအသစ် တစ်မျိုးနဲ...
187K 2.8K 29
Rajveer is not in love with Prachi and wants to take revenge from her . He knows she is a virgin and is very peculiar that nobody touches her. Prachi...
1.8M 103K 89
Daksh singh chauhan - the crowned prince and future king of Jodhpur is a multi billionaire and the CEO of Ratore group. He is highly honored and resp...