HUMAIDAH

neeshejay tarafından

46.6K 3.2K 188

Labarine akan wata youg lady who worked in YUGUDA's House so that she earned money da zata ma mamanta treatme... Daha Fazla

HUMAIDAH
1
2
3
4
5
7
8
9
10
11
12
13
14
15
17
18
19
Not an update
Lovelies💖❤
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
34
33
35
🔚

16

1K 73 3
neeshejay tarafından

*ᎻᏌᎷᎪᏆᎠᎪᎻ*
(ᴛʜᴇ ᴄʜᴀʀᴍɪɴɢ ʟᴀᴅʏ)

           *ᎪYᏚᎻᎪᎡᎢᎾᏌ*
                ωαттρα∂ @neeshejay

_Dedιcaтed tσ_

*H͙  u͙ m͙ a͙ i͙ d͙ a͙ h͙*
(υммυ fυ'α∂)

*What are eating na baka is falling down masu tambayar Humaidah ko na kuride aa free ne ammamu hadu daku a next book dina na kudi tunda naga haka kuke so fans*😆

*ⓟⓐⓡⓣ 75_80*

........ Alhmdllh jikin abba yayi sauki sosae sae dae bunda ba'a rasa dan gurin da akayi aiki ma ya fara cikowa.

Humaidah Kam har yanzu bata tashi ba an fara shirye shiryen fita da ita Egypt ko Allah zae sa a Dace da Abba next week za'ayi discharging dinsa.

💧💧💧💧💧💧💧💧💧

*Neehal* na zaune a gdan su ilham bayan sun gaisa da dad ne yake tambayar shi ilham din yace ai ta koma skl Bata gaya ma ba

Neehal yace"aa bamuyi waya da ita bae dad"

Dad yace "maybe duk karatunne ya jikin Abban ka naso zuwa yau amma aiki ya tsareni"

Kallon rashin fahimta Neehal yana dad dan shi bae San Abba ba lpy ba dad yace"abujan ce tayi wuyar Shiga wlh amma kafin a sallame shi zanje in Buda shi tunda nace bullet din bae Mae wata illa ba"

Shi Kam dae Neehal abun ya daure mishi Kae ya matsu ya fita ya Kira gda yaji meke going dan ko mom bata gaya mishi ba hakan ma  Najwah dama yasan king ba kiranshi zaeyi ya fada mishi ba.

🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃

*Ammi* ce zaune tareda Asma'u (yarinyar kaninta da suke uba daya) Asma'u tace "wae Ammi nikam Ina ya Taufeeq ne kwana biyu bae shigo Mana ba"

Ammi tace"ehh wlh Nana Abban shine ba lpy shiyasa"

Cikin tausayi tace"Allah sarki Allah bashi lpy"

Ammi tace"ameen ya mgnr Abdullahi da yace zae turo magabatansa najj shiru har yanzu"

Kanta a kasa tace"ehh Ammi tafiyace ta kamasa amma inshallah next week zae dawo"

Ammi tace"Allah ya kaimu"

King ne ya shigo bakinsa dauke da sallama bayan ya zauna ya gaida Ammi Asma'u t gaida shi yace "Ammi mgnr investigation din nan Abba yace shi wae be San wasu enemies dinda ke gareshi ba kuma baya fada da kowa"

Jijjiga Kae ammi tayi tace"da barin wnn aikin kayi Taufeeq koma waye a sannu asirinsa zae tonu Allah ba azzalumin bawansa ba kuma Allah baya bacci idan ma sun tsira anan duniya to a halira fa ranar da ba wani bawa da ya isa ya guduma ubangijinsa ranar da asirin kowa zae tonu ranar da bawanda da ya aikata aikin da bana kwarai ba zae ji kunya a gaban gaba daya al'umma a wannan rana ne idan uwa Mai ciki ta mutu ana hura kaho ta mike zata haifi abunda ke cikin ta amma bazata tsaya ta kallesa ba itama zatayi ta kanta shima yayi ta kanshi ranar da bamuda dabarar komae kuma a ranar ne ubangijin gsky zae bama masu gsky gaskiyar su dan ko akuyace tayi ammafani da kahonta ta cuta ma y'ar uwarta sae Allah yace ta rama kana su zama k'asa a ranar da Wanda ya kashe rae za'a tadasu Baki daya bawan da aka kashe zae kamo wuyan Wanda ya kashe shi yace Allah mai nama wannan bawa naka ya kashe ni wannan ranar abun tsoro ce dan ranar hisabi ta wuce duk tunaninku Amma idan ka zama na kwarae to ko a gurin tsayuwa Allah zae muku rumfa y kareku daga ranar dake addabar mutane bazan gaji da muku basiha ba a kullum saboda wannan wani k'arni ne da muke ciki da bala'e ke faruwa zunubi na wakanuwa an maida Zina da mad'igo ba a bakin komae ba kuma a kanshi ne Allah ya halalakr da mutanen annabi lud zamani me da cin Amana yayi yawa manya manyan zunubae ba a dauke su a bakin komae ba shin ko mutane sun manta da mutuwa ne Bata da lkc kuma Bata kan babba ballantana yaro idan tazo dauke ka kawae zatayi sae dae kawae Kanika a kabari ana maka tambaya a nanne Baki zae raena fata Allah da Sajadah kanshi yana cewa"" To ki d'and'ana,saboda abunda kuka manta na had'uwa da ranarku wannan. Lalle muma mun manta daku , kuma ki d'and'ani azabar da dawwama saboda abin da kuka kasance kuna aikatawa"" (11)

Duk acikin surar ne Allah ya kuma cewa"kuma wad'anda sukayi fasikanci, to,makomarsu itace su wuta koda yaushe suka yi nufin su fita daga gareta, sae a mayar da su a cikinta, kuma a ce musu“ku d'and'ana azabar wuta, wadda kuka kasance kuna karyatarwa game da ita""(20)

Dan murmushi Ammi tayi tace"sae fa kunyi hkr da Ni Kun San Ni baa zama ban tunawa mutum Allah ba dan yawan hakan ma zae saka taoronshi ya ratsaku zu zamto masu tsoron Saba masa a koda yaushe Aya ta gaba tace"kuma lalle muna d'and'ana musu daga azaba mafi girma domin fatan zasu komo(21)

"Ku tsaya ku saurari wannan Aya da kyau """wanene yafi zalunci bisa ga wanda aka tunatar da ayoyin ubangijinsa sa'an Nan ya bijire daga barinsu?""

Kun gani Wanda yafi zalunci kenan Wanda aka tuna mishi da abunda Allah ya fada Amma ya taka ya hau da Wanda yasani kuma ya taka sanin ranar alkiyana zasu hadu da mahallincin su gaba daya  wlh duniya yanzu ta zama abun tsoro gaba daya sae dae muce Allah ya shirya Mana zuri'ar mu gaba daya ya taya mu rikon tarbiyyar su a duk inda suke kuma ya karesu daga mugayen kawaye masu hure masu kunne Dan say kuga yanzu a gda iyaye na kokari gurin bama yaransu tarbiyya sama da shekara nawa amma da aboki daya yazo cikin yini daya zae Bata maka tarbiyyar yaran Allah dae yasa mu dace gaba daya Inga yanzu lkcn sallahr azahar  yayi Dan ga Kira chan an fara"

King ne da jikinshi ya gama mutuwa yace"ehh Ammi Bari nayi sallah na dawo"

Mike wa tayi itama tana fadin "muma ai tashi zamuyi"

🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂

Neehal kam bayan ya ta fito daga gurin dad da sauri ya karasa masaukin sa ya fidda waya ya shiga Kiran mom harta tsinke bata dauka ba kuma Kira yayi dae dae lkcn da ta fito daga toilet Jin wayarta na ringing ya sakata yin tsaki dan tayi tunanin wani ganin Neehal me sae ta dauka "hello son ykk"

Ai baeko tsaya bata amsa ba yace"mom meke damun dad all this while Amma ba Wanda ya kirani ya gaya min"

"Kae dallah rufemin Baki Ina tambayarka ykk amma baka bani amsa kana min wani stupid silly question naka"

Yatsine fuska yayi yace"ai dae mom only my voice zae iya tabbatar Miki dat am doing good kawae Ni dan Allah ki gaya min condition dinda Abba ke ciki"

"Shooting dinshi akayi"

"What ehhwaeeee 🙆🏻‍♂ wake da wannan guts din na shooting abbana do u investigate who is behind it?"

Tace"ehh anayi Kae dallah yaji sauki kafin ka dawo anyi discharging dinsa"

Yace"ok zan kirashi"

Tace"ehhh bye" kit ta kashe wayar



🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒


Bayan dawowar shi daga masjid direct bedroom din Ammi ya wuce a kan sallaya ya taddata bayan sun gaisa yace"Ammi na gama komae gameda ta tafiyar mu"

Tace"Ni Inaga Taufeeq ba sae kaje ba ai sauki na Allah ne idan Allah yaso Bata lpy sae kaga ta tashi zuwan ka bazae sa taji sauki ba"

Yace"ehh Ammi amma inaga ai ya kamata a tafi dani din dae"

Tace"ehh toh amma wa zae zauna da abbanku nasan dae Neehal ko sama da kasa zata hade bazae Shiga office ballanta ya tabuka wani abu"

Yace"ehh haka kuma gashi yanzu dan zaman nan na ciwon Abba komae ya tsaya"

Tace"to ka gani ai gwanda ka tsaya dae inaga dani da Ahmad da Husna kawae mun isa"

Yace"toh Ammi Allah ya kaimu kuma ya bata lpy"

Tace"ameen Bari a kawo maka lunch"

Yace"toh"

Tashi tayi ta cire hijab din jikinta ta linke tareda sallaya ta fita


✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

*Najwah* ce zaune a room dinda aka kwantar da Abba bauan ta gama wayar da takeyi ne ta kalli Abba tace"Abba Ina zuwa zan shigo da Baki"

Yace"toh"

Mikewa tayi rafita Bata jima ba sae gata sun dawo tareda Huzaif da Yaya khaleed da Yaya sirdee bayan sun zauna suka gaida Abba cike da ladabi suka mishi ya jiki da addu'ar samun lpy Mae dorewa Najwah kam kanta na kasa sae smiling takeyi tana satar kallon Huzaif ta gefen Ido.

Mikewa tayi ta kawo musu ruwa a trey

Ya khaleed yace"kanwarmu muda muka zo dubaiya har asibiti kumame zamuyi da ruwa"

Sirdee yace"kaga Yaya dama Ni a gajiye nake kuma Ina bukata"

Dariya kawae sukayi Abba Kam tunda yaga yanda Najwah ke sinne Kae sae ya gane so kuwaye.

Shigowar King yasa suka maida hankalinsu kan kofar bayan ta zauna suka shiga gaesawa dasu Huzaif

Kallon Najwah yayi yace"aa little kice babban bako mukayi yau.. Abba ga sirikin ka shine yaxo gaida Kae" ya fada Yana nuna Huzaif da yayi kasa da Kae

Abba yace"sae yanzu zaku gaya min wato ko aurene sae dae kawae naji daga baya"

Dariya sukayi king yace"haba Abba kasan kanwar tawa da kunya take Ni kuma mantawa nayi"

Abba yace"toh ai hakan na da kyau Allah dae ya kaemu lkc babban Yaya ya zama siriki"

Dariya sukayi gaba daya Nan suka cigaba da firar su


✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

*A kauye* kuma sadeek ya ware tuni har ya koma gona ranar auna zaune a bakin ruwa shida Sabeera sae ga baban Humaidah gaisawa sukayi ba yabo  ba fallasa Nan sadeek yabashi lbr abunda aka mishishi yasa kwana biyu bae ganshi ba Aiko baban Humaidah bae ma tsaya dibar ruwan ba juya direct gurin aikin  baban Isihu yaje Aiko yayi sa'a babu mutane  maqure mishi wuya yayi yace"wlh audu ka dae na haukan da kakeyi idan ka kuma tunanin ba aikatarwa ba cutar da sadeeku sae na maka abunda baka tunanin a garin Nan kawae Ina kyale ka ne amma Naga Kae baka San kawae ci ba to mu zuba nida Kae shege ka fasa"

Kokarin kwance kanshi yake daga rikon da bababn Humaidah ya mishi amma ya kasa sae da ya sake shi ya samu damar mgn "wlh Hayatudden baka isa kamin wani abuba kadin banza"

Baban Humaidah yace"to muzuba nu gani"
Ya wuce fuuuu Kamar iska


✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Yau ta kama ranar da za'a tafi da Humaidah Egypt jirgin dare ne shi yasa Basu samu rakiyar mutane da yawa ba daga Abba sae king da Najwah da kanin Ammi baban Asma'u suka rakasu bayan an kaesu driver ya juya da Abba baban Asma'u ma ya tafi sae ya rage daga king sae Najwah suna gurin har 1:45am flight dinsu ya daga kana suka koma gda.......

_Toh malama Humaidah Allah ya Baki lpy yasa a dace_😞


*Masu kirana ta waya da masu min inbox gaba daya na gode da kulawar ku alhmdllh naji sauki yanzu marasa lpy ma Allah ya Basu lpy Baki daya Ina godiya sosae Allah ya bar zumunci Yan uwar*😘😘


Comment
Vote
Share

@ayshartou

Okumaya devam et

Bunları da Beğeneceksin

364K 18.6K 96
fate : be destined to happen, turn out, or act in a particular way. Often people try to navigate through life with their own plans and wonder why thi...
411K 16.3K 48
Vikram, a senior officer, prioritizes his duty above all else, much like his father, ACP Rajendra. He has three siblings: one is an officer, and the...
319K 9.6K 78
(Fixed/Fan-TL) Top idol group Stardust, whose members disappear like dust. The group that used to have seven members ends with four members... "Is...
924K 26.7K 43
Athena is trying to adjust in her newfound freedom but she is forcefully ripped away from it. But sometimes bad things happen for better!