KISHIYA...

By GaskiyaWritersAsso

13.6K 477 18

fiction story More

LAMBA TA ƊAYA
LAMBA TA BIYU
LAMBA TA UKU
LAMBA TA HUƊU
LAMBA TA BIYAR
LAMBA TA SHIDA
LAMBA TA BAKWAI
LAMBA TA TARA
LAMBA TA GOMA{ƘARSHE}

LAMBA TA TAKWAS

753 39 5
By GaskiyaWritersAsso

[10/8, 20:29] Lovly tah 1: *KISHIYA*














®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }

         🎐 '''G•W•A'''🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼





*NA*






*UMMU NABIL*










*NO.31*




Zama Aunty Momy tayi tace"Wallah zan saɓa maka idan kana saka min ɗiya kuka,haka kawai tunda tace bata so ai sai ka ƙyale ta,imm inyaso ni idan nazo zata bayar,maza yi shiru abin ki maza goge hawayen ki bata ta tasha kinga ai tana jin yunwa".






Goge hawayen ta tayi da ƙyar tana cije baki wai ita zafi ta bata.Mahfuz yace



"Shagwaɓar kawai,Allah Aunty ke kike zugata ma".ya faɗa tare da marairaice face nashi.




"Zaka gamu dani idan baka yi ma mutane shiru ana ba".



Ta juya ta kalli Du'a tace"Wai ina son tambayar ki,meye ya same ki a goshi ne ya fashe?".




Gaban Du'a ya yanke ya faɗi,take ta fara hawaye nan da nan-nan taji abin ya dawo mata sabo kwata-kwata bata ko son ganin Mahfuz kallon Aunty tayi ta nuna Mahfuz da yayi tsaye yana son jin mi zata ce,sai kawai yaga ta nuna shi tana hawaye.


Zaro ido yayi waje tare da tuna kansa yace"Ni kuma yaushe,Allah Aunty Momy lokacin ina shigo wa na dawo daga wurin aiki Na ganta a ƙasa bata motsi shine na kawo ta asibiti".



Cike da mamakin kalaman shi take kallon shi ta fara girgiza kai.shiru Aunty Momy tayi tana nazarin kalaman Mahfuz tace"Kira min Doctor".



"Doctor kuma Momy mi zai yi dama?".



"Nace ka kira min shi ko".

Babu musu ya fita,Mahfuza data bushe da zaman jiran shi,tana ganin ya fito ta miƙe,tunanin ta ya fito ne,don su Tafi sai taga ba wurin ta yayo ba,koma wa tayi ta zauna a zuciyar ta tunani iri-iri fal ya hana ta sukuni.





Tare suka dawo da Doctor lokacin Du'a ta shirya,tana zaune bakin gado suka shigo ɗauke da sallama a bakin su.Aunty Momy tace



"Ahmm Doctor dama ina son ce ne,yarinyar nan tunda ta farka bata yi magana ba Kuwa da wani abu ne?".



Shi kanshi Mahfuz bai taɓa kawo haka a ranshi ba,tunanin guda ko duk cikin shagwaɓa ne yasa yin hakan wato duk inda babba yake yafi yaro zurfin tunani.



"Gaskiya Hajiya ba ƙaramin zurfin tunani kika yi ba,wallah ko arai banyi tunanin haka ba,ganin zata ci zata sha yasa ban kawo akwai wani abu dake damun ta ama yanzu za'a je ayi hoton kai nata idan akwai wata matsala zamu gani".



Haka suka rankaya suka je inda ake hoton kai aka yi cikin lokaci ƙanƙani aka basu suka dawo ma da Doctor,bayan su Du'a sun koma ɗaki.


Bin ciken farko ya nuna ta samu matsala a kanta samakon Buguwar da tayi,jijiyar dake fitar da sautin magana ta samu matsala a halin da ake cike ta daina magana.



Lokacin Da Doctor yake baya nin Mahfuz ji yake tamkar labarin wani ake bashi ba Matar shi ba,kallon Doctor Na'im yayi yace"Wai labarin waye ne kake bani dama?".



Ɗan murmushin ƙarfin hali Doctor Na'im yayi yace"Am sorry to say Matar ka,ta daina magana sai a hankali bazan ce har abada ba,saboda Allah shine mai halitta shine mai rayawa shine kuma mai kashe wa".




"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun,Hasbunalla wa ni'imal wakil,yanzu Maimunatu ta daina magana bazan ƙara jin sautin maganar ta ba kinan,Doctor yanzu babu abinda za'a iya yi mata muryar ta ta dawo Ka taimaka min".




"Am Sorry hakan baya nufin har abada ta daina magana A'a ka taya ta da addu'a komi zai zama dai-dai".




Jiki babu ƙwari ya tashi ya fita a office ɗin ya koma,Mahfuza tana ganin shi ta miƙe tabi bayan shi,suna shiga ɗakin Aunty Momy tace


"Lafiya me ke faruwa,babu wata matsala dai ko?".


Karɓar takar dar hannun shi tayi ta duba da ike ta iya karatun boko nan take ta fara salati,zama tayi cike da alhinin abinda ta gani ta buɗi baki tace


"Allah mai baiwa da ɗaukaka Allah ubangijin mutane da aljanu,haka Allah yake ikon shi,ashe da dalili rashin yin maganar ki".


Ita kam ta kasa fahimtar karatun da Aunty Momy ke yi,kallon ta tayi tayi mata alama da hannun ta alamun me ya faru.Mahfuza tace



"Wai mi yake faruwa ne,ban fahimci abinda kike faɗa ba?".





Hawaye tuni ya wanke ma Aunty Momy fuska tace"Maimunatu ki ɗauki ƙaddara hannun biyu,Allah ya nason bayin sa masu karɓar ƙaddara mai kyau ko marar kyau,Maimunatu sakamakon raunin da kika samu a kanki ya haifar maki da..."kuka ne ya ci ƙarfin ta ganin haka yasa Mahfuza karɓar takar dar hannun Aunty Momy zaro ido tayi tace



"Ta daina magana shikinan ke kuma taki ta ƙare.......







*UMMU NABIL*
[10/8, 20:29] Lovly tah 1: *KISHIYA*





®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }

         🎐 '''G•W•A'''🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼



*NA*





*UMMU NABIL*







*NO.32*



"Ke dalla gafara marar hankali kawai,wannan wani irin magana ne haka,wallah baki da hankali maimakon ki jimanta mata ki tausaya mata shine zaki ce ta ta ta ƙare,ta ta bata ƙare ba,sai dai ke mai mugun abu kawai ke banson wani irin hali gare ki ba wallah"ta inda Aunty Momy ta ke shiga bata nan take fita ba,shiru Mahfuza tayi daga ƙarshe ma ta fice daga ɗakin.




Gaba ɗaya tausayin Mamunatu ne fal cikin zuciyar shi ya rasa yanda zai yi da ransa,yanzu shikam ta ina ta wace hanya zai fara sanar da iyaye Maimunatu,kuka sosai yake babu mai rarrashi sai Aunty Momy da tayi ta maza tace




"Tabbas duk abinda ya samu bawa daga Allah ne,daga gare shi muka zo gare shi zamu koma,lallai ku zamu masu ɗaukar ƙaddara sai kuci riba a rayuwa,ba akan Maimunatu aka fara irin haka ba,ka manta ka rasa mahaifin ka,kuma kayi haƙuri shin wanan ma baza ka yi haƙuri ba,Alhmdulillah tunda ba Rasa ta muka yi ba,kawai dai tausayi ne Allah ya kan sanyawa bayin sa,alokacin da wabu ya same su dole idan har bawa yana da zuciyar musulunci dole ya tausaya,toh ita haka ta ta ƙaddarar take kayi haƙuri ka ɗauki ƙaddara,kuma abinda ke cikin ranka nima shi yake raina,nasan bazai wuce kace Mahaifan Maimunatu ba nima shine a cikin raina,ya zamu yi dole zamu faɗi masu ya zamu yi kayi haƙuri komai yayi farko zai yi ƙarshe".






Gaba ɗaya tufka da warwar da suke tsakanin su Du'a tana jinsu ta gagara ce dasu komi banda kuka da take mai cin zuciya,ga takaicin miji ga kuma abinda ya same ta,shin minene mafita agare ta,anya baza ta nemi Mahfuz daya sawwaƙe mata ba kuwa,gani take idan ta cigaba da zama ƙarshe kashe ta zasu yi tunda gashi har sun kai ga saka ta cikin matsala wadda bata san ranar yankewar ta ba Allah kamin jagora ka kawo min ƙarshen lamarin nan.ta kuma rushewa da kuka.




Aunty Momy ta dafa ta tace"Kiyi haƙuri ki ɗauki ƙaddara kiyi tawakkali ki miƙa lamarin ki ga Allah,komi zai zo maki da sauƙi kinji?".



Gyaɗa mata kai tayi saboda babu muryar magana sai kuka.

Mahfuz yace "banson mi ya jawo maki Wannan ciwon ba Maimunatu ki yafe min don Allah?".



Kawar da kanta tayi gefe saboda wani mugun takaici da yake cin zuciyar ta.

************


Har kusan kwana na biyu sannan aka sanar dasu Mama halin da Du'a take ciki ba ƙaramin tashin hankali suka shiga ba,Ama babu yadda zasu yi haka suka miƙa lamuran su ga Allah tare da nemawa ƴar tasu gafarar Allah.


Ranar suna kuwa haka kowa yasha alhinin halin da Du'a ta shiga,aka yi taro aka watse.

*Bayan Wata biyu*

Sosae Nady take son Hunaida don ko bacci ma tare suke yi,sai da idan ta tashi ta koma wurin Du'a haka ma tana dawo wa daga  Skul ta kanta take farawa ko Wurin Mahfuza bata zuwa,sai dai tayi ɓangaren Du'a acan zata ci zata sha.hatta wanka kuwa.





Zaune suke a bakin gado tana baiwa Hunaida Nono ya shigo ɗakin babu yabo babu fallasa,zama yayi kusa da ita yace

"Ana Feeding Baby ne?".gyaɗa mishi kai tayi alamun Eh.


"Nima za'a bani?".ya tambaya fuskan shi akan ƙirjinta.



Anya wannan kam da hankalin shi,yaushe rabo na da jin maganar shi makamanciyar wannan tunda na samu cikin Hunaida Shine yau zai ce mata haka,ko dai zuwa yayi ya kuma kaita lahirar ya dawo da ita kamar yadda yayi mata a baya.ganin tayi shiru alamun ta tafi tunani ya sashi shafo fuskan ta yace




"Ya dai mekike tunani haka dama?".

Memon ta da Biro ta ɗauke kamar yadda ta saba yi ta rubuta mishi kamar haka:


"Kodai kazo ka sake maimaitamin abinda kayi min a baya?".

Murmushi yayi yace"Ko ɗaya ba wannan ya kawo ni ba,nazo na amshi haƙƙi na ne wanda na manta da yadda yake na kuma manta da garɗin shi".



"Ai Matar ka ta fini wannan abin da kake buƙata,tunda ta fiye maka ni sau dubu miliyan".ta kuma bashi ya karanta.



Miƙa hannu yayi ya karɓa Hunaida,bai ce da ita koma bi yaje ya kwantar da ita a gadon ta,ya rufe ƙofar ɗakin duk tana kallon shi bata ce dashi komi ba.

Kusa da ita ya dawo ya zauna ta ƙokarin zuge zif nata yayi caraf ya riƙe hannun ta da ike zif ɗin ko wanne gefe yake nakan Fulanin ta ta zuge ɗaya zata zuge ɗayan yace

"Barmin kaya na,yau gaisawa zamu yi dasu"zaro ido tayi alamun tsoro da jin kalaman shi ta ɗauka memo nata ta Rubuta mashi

"Wai miye kake nufi ban gane zancen ka ba".

Murmushi yayi tare da zuge zip ɗin gaba ɗaya yace"Zaki gane bari kiga".


Sororo tayi tana kallon shi,bata gama tunani ba taga Ya raba ta da rigar jikin ta sai skit da rage mata.kiciniya ta shiga yi tana ƙoƙarin ƙwace kanta ama abin ya ci tura ji take tamkar dukan da yayi mata watannin baya shi zai yi mata.

Kuka ta shiga yi,ita ba baki ba bare ta roƙe shi,sai kuka tana ji tana gani ya raba ta da komi ya shiga yi mata aiki....







*Wasa farin girki*




Comment N Share



*UMMU NABIL*
[10/9, 09:48] Lovly tah 1: *KISHIYA*




®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }

         🎐 '''G•W•A'''🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼



*NA*

*UMMU NABIL*

*NO.33*

"Hmm ke wallah na rasa yadda zanyi don gani nake rishe zai juyewa mujiya fa,ke yanzu fa naga fa har yana tausayin ta,kuma naga wani lokacin ko nayi magana ma kamar baya jin magana na ma,anya baki ganin kamar aikin bai lalace ba?".ta kalli Nady tace


"Tashi kije wurin su Marwan kuyi wasa kafin na fito".



Numfasawa ta kuma yi ta kalli Mabruka da tayi zuru tana kallon ta,Mabruka tace




"Haka ne a yadda kika bani labari tun daga haihuwar ta har izuwa yanzun gaskiya bamu samu wani cigaba ba ama yanzu matso kiji".


Raɗa tayi mata a kunne,ina daga gefe naga sun kwashe da dariya tare da tafawa Mahfuza tace




"Gaskiya da ban same ki a matsayin ƙawa ba,da nayi asara babba kuwa,kaii naji daɗin wannan shawara,shisa fa da kika yi tafiya kwata-kwata na gagara samun sukuni ama tunda kika cemin kin dawo hankalina ya dawo jikina".


Dariya Mabruka tayi tace"Hmm kedai bari nima ai da ni za'a koma saboda nayi sabon kamu kin san yanzu mazan zuma ce sai da wuta".

"Ahhh sheɗaniya kice mun faso?".


"Hhhh ke idan ana sallah ba'a magana kedai ki zama cikin shiri nan da kwana ɗaya ko biyu zan maki magana".

"Toh ai kuwa ina jira,don ni yanzu hankali na duk ya koma kan aljanar yarinyar nan,yarinya sai kace ƴar aljanu kefa don baki nan baki ganta,Mama ma har yau tunda aka hiafi yarinyar nan bata je ba,ke ita Mama ma tunda ya ƙara aure bai fi sau biyu tazo ba,tunda ta kawo min wani taimako bata kuma dawo wa ba".

"Taɓ aikuwa zanje kice Babyn ta haɗu?".

"Ke sosai ma,kamar ka lashe ta in kai maye ne"

Dariya sosai Mabruka tayi tare da kashe mata ido ɗaya tace"Ahh Malama faɗi gaskiya dai kodai-kodai?".


"Jimin ƴar iska me kike nufi da kodai-kodai?kefa baki da mutunci wallah,kinga ni na tafi ma sai mun haɗu jibin".


Ta miƙe tsaye Mabruka sai dariya take mata,suka yi sallama ta kama Hannun Nady suka fito babu jimawa suka samu motar da zata kai su gida.






Har ya shiga yayi wanka ya fito tana kwance jikin ta rufe da bargo sai kuka take,saboda takaicin daya cika mata zuciya.bayan ya gama shiryawa yazo har inda take yace


"Ki tashi na haɗa maki ruwa gashi can ki gasa jikin ki zaki ji daɗi".

Daga haka yayi fitar shi cikin zuciyar ta tace"Mugu azzalumi sai Allah ya saka min"ta kuma rushewa da kuka.


Yana fita parlour yana gyara zaman wandon sa,Dai-dai lokacin Mahfuza ta sako kai gaban tane ya faɗi cikin ranta ta shiga saƙe-saƙe kala-kala,shima kansa yana ganin ta gaban shi ya faɗi ya shiga muzurai,cike da masifa ta iso inda yake tace



"Daga ina kake?".

"Dam..dam.dama na shiga naga ya suke ne,ita da Hunaida naji tana kuka shine naje mat..."

"Kaje uban me,me kaje yi ɗakin ta ban gargaɗe ka da cewa kar ka kuskura ka kuma shiga har kar ta ba,ko ban faɗi maka ba,shekaran jiya ma na faɗi maka nace duk abinda kake so nima ina dashi zan baka don me zaka shigar mata ɗaki"bakin ta har kunfa yake saboda masifa ta bangaje shi ta shiga ɗakin Ta iske babu kowa sai Ƙarar ruwa da taji a toilet cike da masifa ta juya inda Hunaida ke kwance tana bacci ta ɗauko ta,ji kake tass ta wanke mata fuska da mari ai kuwa nan take ta tsanyara kuka ƴar fuskar da bata kai cikin tafin hannun ta ba,ta kama gashin kanta ta miƙar da ita tsaye tace


"Aljanar yarinya zaki koma inda kika fito ne,tunda na fuskan ci kema matsala ce kamar uwarki"timmmm ta sake ta ta faɗi akan tiles na ɗakin kuka ɗaya tayi ta shiɗe ita kuwa Mahfuza tayi fice war ta,komi akan idon Mahfuz aka yi shi ama sai dai me ya kasa koda ɗaga ƙafar shi guda yazo inda suke bare ya samu bakin yin magana.



Ita kuwa Du'a tana toilet duk taji me ya faru,ita ma ta kasa fitowa daga toilet ɗin tazo inda ƴar ta take sakamakon ƙafar ta da taji tayi mata nauyi idan taja sai taji kamar ɗaure ta aka yi banda kuka babu abinda take yi ta rasa me zata yi.wani kukan kura tayi tare da kiran Sunan Allah sai gani tayi ta fito...

Dube-dube ta shiga yi tana neman inda Hunaida take can ta hangeta yashe a ƙasa ko nunfashi bata yi da gudu ta isa gare ta ta ɗago ta tana jijjiga ta sam ta manta ma da cewar jaririya ce, ɗaukar ta tayi tayi parlour ganin babu kowa yasa tayi ɓangaren Mahfuza buɗe ƙofar ta yi kai tsaye inda Mahfuz yake ta nufa da tana mashi nuni da halin da Hunaida ke ciki.




Cikin zafin nama Mahfuza ta tashi ta hankaɗa ta nan take suka zubewa ƙasa ita da Hunaida tayi gefe ita kuma kanta ya bugu da gini,wani ƙara tayi tare da cewa


"Wayyo Allah na".

Kallon Inda yaji sautin maganar Mahfuz yayi ya miƙe tsaye da sauri......




*Comment N Share*



*UMMU NABIL*

Continue Reading

You'll Also Like

119K 9.6K 95
Ongoing novel လင်းရှင်းလန်ဟာကမ္ဘာပျက်ကပ်ကာလမှာစွမ်းအင် 2မျိုး နိုးထခဲ့ပေမယ့် သူ့ရည်းစားနဲ့ သူ့သူငယ်ချင်းက လအနည်းငယ်စာ အစားအသောက်အတွက်နဲ့ သူမကို သုတေ...
73.2K 9.6K 25
This is the sequel of RRR, so new readers please read it before starting this book. Agneya, the soon to be crown prince of Rakshatra, was bounded by...
61.3K 6K 58
" The darkness closed in around him, like a shroud of silence. Veeranshu's eyes fluttered open, and he was met with an unfamiliar ceiling. Groggily...
Erica By Sam

Historical Fiction

2.9M 108K 60
They say her voice was once bewitching to all who heard it. She was like a siren luring sailors to their deaths on quiet nights... Those are just rum...