KASHE FITILA

By BatulMamman17

231K 17.6K 265

Iyaye musamman mata sukan sadaukar da dukkan farincikinsu domin kyautata rayuwar 'ya'yansu. Haka ce ta faru g... More

1
2
3
4
5
6
7
8
13
9
14
15
10
16
17
18
11
19
20
21
12
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
44
45 and 46
47
48
49
50
51
52

43

4.5K 356 3
By BatulMamman17

*KASHE FITILA*💡43

*Batul Mamman*💖

"Ke nake jira fa" taji ya fada yana murmushi. Dubawa tayi ta ga babu zabin da yayi mata. Idan ya fadi yajin miyar nan yau mai rabata da Anti Ummukulsum sai Allah. Maganin yaji kuwa ko da wasa bata hango kanta tana wannan abin ba...karshen rashin kunya ma kenan! Zabi na uku kuma da wane bakin zata fada masa ma'anar abin da tayi da hannu. Wai waye ma ya aiketa tayi ne?

Ya kula da yadda tayi zurfi a tunani  a ransa yace yau fa an hada mata da aiki. Hannunta ya riko
"Kin bani zabi?"

Rufe ido tayi bakin nan an dan turo shi  tana magana cikin sauri kuma can ciki a hankali yadda ba'a ji sosai tace "Dakayibakajiyajinyatafiba"

"Me kika ce?" Don shi ko kalma daya bai tsinta ba.

Sake maimaitawa tayi a hankalin yace bari kawai ya tashi ya fitar da food flask din da aka zuba miyar. Tayi saurin katse shi

"Uncle cewa nayi da kayi baka ji yajin ya tafi ba?"

Ya daga mata gira daya yana son yin dariya
"Da nayi me?"

"Abin mana" ta amsa tana kara turo baki.

"Wane abu nayi da bashi da suna Umm Ruman?" Ya gane me take nufi amma yana jindadin tsokanarta.

Kamar zata yi masa kuka tace "Uncle ka fa gane me nake nufi...ni dai don Allah ka hakura da wannan"

Shima irin muryarta yayi "ni dai don Allah bazan hakura ba"

Wani siririn hawaye ne ya gani ya fara bin kumatunta sa hannun ya goge shi "dadina da mutum shagwaba. To kiyi kukan idan aka tambayeki a ciki sai kice kiss mijinki ya nema kika kasa. Kuma kinsan ana ganin idonki za'a gane kinyi kuka ayi ta tambayarki sai kin fada. Gara ma ki tashi ki tafi babu ruwana"

Dankwalinta ta kwance ta janyo kasansa ta goge fuskarta tana murmushi "kukan wasa ne fa irin wanda mukeyi a makaranta idan bama son bulala"

Jinjina kai yayi "gaskiya ban yarda ba wannan wayo ne. Kin gama yiwa malamai fitinar 'yan makaranta kuma nima kiyi min"

Dariya tayi "to ba kaine ba..."

Nishadin da yake ji a lokacin ya dade rabonsa da irinsa. Komai na Rumana yana burge shi musamman shagwabarta da kuruciya. Addua yayi a ransa Allah Ya bashi ikon kula da komai nata yadda bazata taba kaucewa hanyar da ta sabawa shari'a ba.

"To naji kinyi min wayo amma ba hakura zanyi ba. Kawai dai kinci bashin da zaki biya nan kusa. Saura na biyu me wannan yake nufi?" Ya sake hada yatsunsa yadda tayi.
Murmushi yaga tanayi harda dan sosa keya. Wannan dabi'ar kuwa yana kyautata zaton a wurinsa ma ta koya domin halinsa ne.

Ita dai yau ta shiga tsaka mai wuya daga wannan sai wannan. Dabara zata yi masa kawai don shima ya hakura
"A film din 'yan Korea ne fa na gani ko ma'anarsa ban sani ba"

Dan fiddo idanu yayi  "baki san ma'anarsa ba amma kika yi min. Shikenan kila ma zagina kika yi. Zuwa zanyi na tambayi waye yake kunna miki gashi a kaina ya kare"

Gani tayi da gaske ya tashi tsaye bata san lokacin da tace
"I love you "

Wata irin juyowa yayi a hankali yana kallonta. Ita kuwa kamar ta nutse a kasa.

A hankali yace "Me kika ce"

"Uncle I love you yake nufi ba zagi bane" idanunta kamar su yo waje don ta tsorata.

Bata san yadda kalmomi ukun nan suka tsaya masa a rai ba tamkar wanda bai taba jinsu ba.

"Naji ma'anarsu amma da gaske kina yi min son so?"

Wannan karon ita ce ta tashi tana neman hanyar guduwa bazata iya jurewa wannan kallon da Uncle Awaisu yake mata ba.

Hannunsa ya ware "Give me a hug kafin ki fita please."

Tsayawa tayi kanta a kasa tana wasa da hannuwanta.

"Kinga komai na tambaya bakya yi ga yaji kin hadani dashi"

"To ai kunya nake ji"

"Bari nayi miki yadda kika koya min"

Ta bayanta ya tsaya ya rungumeta yadda tayi masa wancan lokacin da zai tafi. Da yake ya fita girma da tsaho sai ya rufeta gabadaya ya mata rada mata a kunne
"Ke special SS dina ce Umm Ruman. Allah Yayi miki albarka"

Amin tace a zuciyarta. A zahiri kuwa tace "Uncle idan na fadi ma'anar SS din zaka taimakeni don Allah"

"Toooohhh wane irin taimako kuma. Ko me kike so fada kawai zakiyi"

Kwanukan abincin ta nuna masa.
"Idan na fita dashi fada za'ayi min kila harda duka ma"

"Maganin wannan kawai ki kwana a nan shikenan"

Dariyar da taga yana yi ce tasa ta gane tsokanarta yake yi. Ta tabbatar idan Mama ta ga wannan miyar ko bata ji a jikinta ba kunnenta zai bada labari don bayan fada idan ta kama shi ta murde bata da hanyar tsira.

"Don Allah kace ya zama assignment irin yadda na baka"

Yayi murmushi "Ya zama Umm Ruman, me SS yake nufi?"

Sai da tayi kamar mai tunani kada yace tayi saurin canka sannan tace "Son So"

Ya girgiza kai "sai hakuri ni Sabuwar Sarauniya nake nufi. Jeki kawai idan kinga zaayi miki fadan ki gudu nan" kan katifar ya koma ya dan kashigida. Hankalin Rumana a take ya tashi. Dama shi take tunanin zai rufa mata asiri gashi ta kula kamar bai damu ba.

Awaisu yana kallonta yana dariya.
"Jeki mana idan an gama ki dawo ina son magana dake"

Mamaki take yi amma kuma tasan dama can idan sunyi laifi baya cikin wanda zaka zo wurinsu ya hana a hukuntaka. Sai dai yayi rarrashi idan anyi hukuncin. Duk wanda ya hana a hukunta to fa sai dai idan ya tabbatar mutum bashi da laifi. Kanta ta dan rangwada gefe muryarta tana dan rawa "na tafi Uncle"

Yana danna waya yana dariya ciki-ciki yace "sai kin dawo SS dina"

Ta durkusa zata dauki tray din "yau tun safe kunnena na dama ke dan zafi gashi Mama ita kunne take murdewa. Uncle kana da panadol idan ta murde zazzabi ya kamani sai ka bani"

Wannan karon da kyar ya iya danne dariyarsa "idan kinje ki bata kunnen hagun tunda shi kalau yake maybe bazaiyi zafin da zaki yi zazzabi ba"

Anya kuwa Uncle yana ma sonta ko da ba son so ba ta fada a ranta. Har wani dadi yake ji ga Anti Ummukulsum itama duk wasanta da yara ta iya duka.

Hadiyar yawu tayi da kyar ta tuna rankwashin da Antin ta yiwa Iman jiya saboda ta fasa mata plate. Harda sakin ajiyar zuciya ta sake cewa "bye bye Uncle"

"See you SS" yace daga inda yake.

Tafiya ta rinka yi kamar wadda kwai ya fashe mata. Ko dai kawai tayi tuntuben karya ne kwanukan su zube. Amma kuma masu kyau ne kila ma na baban su Iman Antin ta zuba abincin a ciki. Tana wannan tunanin har Awaisu ya kusa zuwa inda take bata kula ba. Tray din ya karba ya dawo da fuskarta daidai tata.

"Kin canka daidai Son So din Uncle Awaisu. Yanzu me kike so ayi da miyar nan kada a taba min mata"

Murmushinta kamar gonar auduga tace "zuciyata kamar ta fito don tsoro daurewa kawai nayi"

Hancinta ya ja "matsoraciya...jeki ki samo leda sai a juye miyar a ciki. Idan zan fita zan yar don bana fatan kowa yaci kada a kare a gadon asibiti"

"Yau ma tsautsayi ne amma next time me dadi zanyi"

"Ni kam tsoron girkinki ya shigeni Son So"

Dariya ya bata yadda yayi da fuska. Fita tayi ta tafi kitchen ta sami bakar leda har uku ta diba zata fita Mama ta shigo duba nama da take tafasawa.

"Ina zaki da ledoji haka kike sauri"

Da sauri tace "Uncle ne yace na kai masa"

Sanin halinta na rikicewa idan bata da gaskiya yasa Mama tunanin akwai abin da tayi.

"Zo nan Rumana" ta dan kaurara murya

Haba tuni ta karasa rikicewa "Mama don Allah kiyi hakuri tsautsayi ne."

"Me kika yi?"

Har ta soma kwalla ta fadawa Mama yajin miyar. Jira take taji ta kama mata kunne sai ji tayi Maman ta sassauta murya alamar tausayawa.

"Jeki ki dauko min miyar"

Awaisu na jiranta yaga ta shigo a firgice. Flask din miyar ta dauka zata fita yace ina zata kai ta fada masa zata kaiwa Mama ne. Tasowa yayi don yasan halin Mamanta
"Muje na bata hakuri don Allah kada ta taba min mata"

"A'a Uncle idan dare yayi ma sai tayi fadan gara ma ayi yanzu kawai"

Tausayi ta bashi sosai amma kuma duk da yana aurenta yana ganin bai dace ya shiga komai tsakaninta da iyayenta ba kafin ta tare. Hannunta ya riko ya dan matsa "bana son kuka idan anyi miki fada gyara ne kinji ko"

"Uhumm" ta iya cewa jiki ba kwari ta fita.

Tana kaiwa Mama ta bude ta dandana da cokali "wai Rumana kamar wadda aka aika kama maye"

Har ta soma dariya ta gimtse ganin kallon da Mama tayi mata. Kabewa ta ga Mama ta dauko a store dama raba musu akayi har su Anti Ummukulsum din. Ta bawa Rumana ta fere ita kuma ta fita ta nemi yaro ya siyo mata alayyahu. Ga yamma bai samo da wuri ba.

Rumana tana kallo Mama ta hada markade na tumatir zalla da albasa nan da nan ta hada ruwan miya bayan ta dafa kabewar. Basu fita ba sai da ta gama nunawa Rumana yadda zata hada miyar taushen wadda ta kusa gama dahuwa da mai yajin sai ga dandanon yayi daidai saboda tasu ta gidan yawa ce kuma bata saka attaruhu ba ko kadan.

Rumana ta kalla Mama taji ta kara sonta.

"Idan girki ya baci dabara akeyi a gyara ba zubarwa ba. Maza basa son almubazzaranci duk da basu da dabarar kitchen irin tamu. Idan kinyi magriba ki zuba masa wannan miyar ki kai. In koma bazai ci tuwon ba sai kizo a dafa masa wani abincin"

"Mama bazaki fadawa Anti ba ko?"

Murmushi tayi mata "babu mai ji in sha Allah. Amma idan kika kara nida ke ne. Ki kiyaye cin abubuwa musamman tsami lokacin girki. Idan baki kware ba kina bukatar dandanawa. Kuma dole harshenki zai iya jin dandanon da ya bambanta da na ainihin abinci saboda tsami ko zaki"
*****

Sallah taje tayi Mama tasa ta dan shafa hoda sannan ta dauki miya ta fita. Addua Mama tayi mata don yanzu kam ta wuce duka ko murde kunne an zama matar aure.

Da taje kofar dakin tayi ta sallama bai amsa ba sai ta murda kofar. Dakin a bude yake amma yana can waje tare da Harisu dawowarsu kenan daga masallaci. Shiga tayi ta ajiye miyar ta dauko wancan plate din zata tafi dashi sai gashi ya dawo. Da murmushi tayi masa sannu da zuwa sannan ta duka gaban flask din.

"Mama ta koya min na sake wata miyar da waccan din. In zuba maka?"

Kirjinsa ya dafe yana tuna azabar da yasha dazu. Yau naga ta kaina.

"Ki bar tuwon kinji my sweet SS. Tea zan sha kawai ya isheni"

Bata ji dadi ba ta bude harda tura masa shi kuwa ya matsa yana mai fargabar sake zuba yajin nan a bakinsa don gaskiya bai yarda da girkinta ba.

"Wannan tayi dadi sosai kuma na dandana"

"Bakinki dinnan bana yarda dashi"

Cokali ta dauko ta debi miyar ta saka a baki tana kallonsa "ka gani da gaske wannan babu yaji"

"Sai na dandana nima zan yarda"

Diba ta sake da cokalin ya rike hannunta ya mayar cikin flask ya janyota tsaye
"Bude bakinki na tabbatar kin hadiye"

Tana budewa ya saka nasa. Ya kuma yi mata riko mai wuyar kwacewa. Dama abin da yake so kenan.

Da ya saketa ne yace "yanzu na yarda babu yaji zuba min yunwa har ta cinyeni"

Kasa kallonsa tayi saboda yadda yake mata abubuwan dake sakata jin kunya ta zuba masa abincin ta fita kafin ya ankara.
*****

Gimbi sai kai kawo take a daki duniya tayi mata zafi. Ta kira Ovi yafi sau goma ba'a daga ba.

A nasu bangaren Rita ta kalli Ovi ganin yadda take murmushin mxugunta.

"Sis wai me yake faruwa ne kinki daukar wayar Madam Gimbi"

"Kinsan a da naso ne ki auri mijinta saboda mu sami rabonmu a gidan. Amma Boka yace idan akayi auren nan daya daga cikinmu zata rasa ranta. Shiyasa nake ganin gara muci kudinta kawai muyi gaba. Ko maganin da ta karbo last a wurinsa ruwan datti ne kawai nace ya bata "

"Ba kya tsoron kada ta gane?"

"Zata gane amma sai mun gama da ita. Bani wayar naji me take so. Nasan yanzu haukane kadai batayi ba tunda aiki yake ta baci ga aure yayi"

Kafin wayar tayi Gimbi ta dauka rai a bace "Ovi kina kokarin cuta ta nr ko me. Yaya zanyi ta sakin kudi babu biyan bukata"

"Kiyi hakuri Madam Boka yace akwai inda aka sami kuskure wurin aikin da kikayi da maganin"

Da a gabanta take yadda ranta ke kuna kila sai ta kai mata shaka "sai kace wata sabon shiga zaku ce matsalar amfani da magani aka samu? Sau daya aka samu hakan da Maamu tana asibiti"

Ovi jin zata cika mata kunne da fada tace "haba ni nasan akwai inda aka kuskure. To boka yace ko waye silar bata aikin a wannan lokacin sune suke bibiyarki suka hanaki sakat"

Gimbi tayi shiru tana son tuna sunan wannan shegiyar likitar da ta hanata shafawa Maamu magani. Kwafa tayi taja tsaki "akwai wata likita da nake zargi don ta saka min ido lokacin. Ki fadawa Boka yayu min maganinta. A rabata da abin da tafi so duk duniya yadda ta taimaka wurin nesantani da mijina. Zan turo miki 200k yanzu ayi komai a gama da wuri. Ita kuma Rumana idan Awaisu ya dawo garin nan da igiyar aurenta Ovi zan baku mamaki. Bani da kirki ke kin sani. Shi kanshi ba don wannan azababben son da na rasa dalilinsa ba da bai isa ya sha daga hannuna ba"

Bayan sun gama waya Ovi ta cewa Rita ya zama dole wannan karon a biyawa Gimbi bukata saboda kada ta dena yarda dasu. A cikin daren babu fargaba bare tsoro suka tafi wurin Boka. Kayan tsafinsa ya dauko ya rinka surkulle wanda Ovi da Rita duj yawan zuwansu kullum tsoronsa suke yi.

Wata irin kibiya ya soka tun daga kai har tsakiyar wani mutum mutumi ya chake shi a jikin bango.
*****

Cikin barci Dr. Yana taji jikinta yana zafi kamar an hura wuta. Lokacin shadayan dare. tayi aiki ta gaji ga girkin da tayiwa Hajiya surukarta bayan ta dawo. Mujahid ta soma kira yana falo bai ji ba. Ido a rufe har lokacin ta ga Gimbi ta biyota da wuka ta soma kuka tana rokonta tayi hakuri. Shure shure take ta yi a kan gadon har ta fado ta bige da bedside drawer amma bata farka ba. Karar faduwar abu Mujahid yaji ya shigo ya ganta a wannan yanayin.

Duk yadda zaiyi taki bude ido amma ga hawaye yana ta zubowa. Fita yayi a guje ya kira Hajiya Allah Yasa idonta biyu.

Suna zuwa suka ji tana cewa "Gimbi! Gimbi!! Gimbi kada ki kasheni!!!!"

Hajiya ta daga kanta ta dora a cinyarta tana kuka don duk irin zamansu ba wai ta tsaneta bane ko don zumunci. "Yana bude idonki waye Gimbi?"

Jikinta  ne ya saki ta dena motsi sai ga jini ya biyo ta karkashinta yana zuba. Mujahid ya tashi ya fita neman key din mota ita kuma Hajiya tana duba jinin ta dafe kirji.

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun...Yana bari kika yi?"

Sai a lokacin Dr. Yana ta bude ido da kyar maganarta bata fita sosai saboda zafin ciwo "Hajiya kiyi hakuri niyata sai ya cika wata uku zanyi muku kyakkyawan albishir ashe ba me zama bane"

Wani abu ne ya tsaya mata a makwogaro tana tuna yadda cikin mafarki Gimbi kw fada mata sai ta rabata da abin da tafi so. Kuka sosai suke yi ita da Hajiya. Da taimakonta ta tashi ta dan gyara jiki a daren suka tafi asibiti. Sunyi kusan awa biyu sannan aka shawo kan matsalar don jini take zubarwa ba da wasa ba. Hajiya ce take yi mata komai cike da tausayawa tana jira ta sami kwarin jiki ta fada mata wacece ko waye  Gimbi.

Continue Reading

You'll Also Like

1.1K 200 7
Title : A Fox Spirit's Guide To Sleeping With men Associated Name : «不想睡男人的狐狸精都不是正经狐狸精» Author: He Xia « 河夏 » Total Chapters : 6 Chapters This is my...
329K 23.9K 54
Myanmar×BL (Unicode+Zawgyi) Owncreation Total: 49 parts This story is just my imagination. [Unicode] ရှေးခေတ်ကဝိညာဥ်တို့နေထိုင်ရာကို အလည်တစ်ခေါက်သွာ...
531K 84.7K 115
Both Unicode and Zawgyi are available! Title - 穿越之灵植师 Author - Ye Yiluo (叶忆落) Type - Web Novel (CN) Status in COO - 397 chapters (Complete) Origina...
231K 17.6K 51
Iyaye musamman mata sukan sadaukar da dukkan farincikinsu domin kyautata rayuwar 'ya'yansu. Haka ce ta faru ga Maamu har zuwa lokacin da Allah Ya azu...