43

4.4K 356 3
                                    

*KASHE FITILA*💡43

*Batul Mamman*💖

"Ke nake jira fa" taji ya fada yana murmushi. Dubawa tayi ta ga babu zabin da yayi mata. Idan ya fadi yajin miyar nan yau mai rabata da Anti Ummukulsum sai Allah. Maganin yaji kuwa ko da wasa bata hango kanta tana wannan abin ba...karshen rashin kunya ma kenan! Zabi na uku kuma da wane bakin zata fada masa ma'anar abin da tayi da hannu. Wai waye ma ya aiketa tayi ne?

Ya kula da yadda tayi zurfi a tunani  a ransa yace yau fa an hada mata da aiki. Hannunta ya riko
"Kin bani zabi?"

Rufe ido tayi bakin nan an dan turo shi  tana magana cikin sauri kuma can ciki a hankali yadda ba'a ji sosai tace "Dakayibakajiyajinyatafiba"

"Me kika ce?" Don shi ko kalma daya bai tsinta ba.

Sake maimaitawa tayi a hankalin yace bari kawai ya tashi ya fitar da food flask din da aka zuba miyar. Tayi saurin katse shi

"Uncle cewa nayi da kayi baka ji yajin ya tafi ba?"

Ya daga mata gira daya yana son yin dariya
"Da nayi me?"

"Abin mana" ta amsa tana kara turo baki.

"Wane abu nayi da bashi da suna Umm Ruman?" Ya gane me take nufi amma yana jindadin tsokanarta.

Kamar zata yi masa kuka tace "Uncle ka fa gane me nake nufi...ni dai don Allah ka hakura da wannan"

Shima irin muryarta yayi "ni dai don Allah bazan hakura ba"

Wani siririn hawaye ne ya gani ya fara bin kumatunta sa hannun ya goge shi "dadina da mutum shagwaba. To kiyi kukan idan aka tambayeki a ciki sai kice kiss mijinki ya nema kika kasa. Kuma kinsan ana ganin idonki za'a gane kinyi kuka ayi ta tambayarki sai kin fada. Gara ma ki tashi ki tafi babu ruwana"

Dankwalinta ta kwance ta janyo kasansa ta goge fuskarta tana murmushi "kukan wasa ne fa irin wanda mukeyi a makaranta idan bama son bulala"

Jinjina kai yayi "gaskiya ban yarda ba wannan wayo ne. Kin gama yiwa malamai fitinar 'yan makaranta kuma nima kiyi min"

Dariya tayi "to ba kaine ba..."

Nishadin da yake ji a lokacin ya dade rabonsa da irinsa. Komai na Rumana yana burge shi musamman shagwabarta da kuruciya. Addua yayi a ransa Allah Ya bashi ikon kula da komai nata yadda bazata taba kaucewa hanyar da ta sabawa shari'a ba.

"To naji kinyi min wayo amma ba hakura zanyi ba. Kawai dai kinci bashin da zaki biya nan kusa. Saura na biyu me wannan yake nufi?" Ya sake hada yatsunsa yadda tayi.
Murmushi yaga tanayi harda dan sosa keya. Wannan dabi'ar kuwa yana kyautata zaton a wurinsa ma ta koya domin halinsa ne.

Ita dai yau ta shiga tsaka mai wuya daga wannan sai wannan. Dabara zata yi masa kawai don shima ya hakura
"A film din 'yan Korea ne fa na gani ko ma'anarsa ban sani ba"

Dan fiddo idanu yayi  "baki san ma'anarsa ba amma kika yi min. Shikenan kila ma zagina kika yi. Zuwa zanyi na tambayi waye yake kunna miki gashi a kaina ya kare"

Gani tayi da gaske ya tashi tsaye bata san lokacin da tace
"I love you "

Wata irin juyowa yayi a hankali yana kallonta. Ita kuwa kamar ta nutse a kasa.

A hankali yace "Me kika ce"

"Uncle I love you yake nufi ba zagi bane" idanunta kamar su yo waje don ta tsorata.

Bata san yadda kalmomi ukun nan suka tsaya masa a rai ba tamkar wanda bai taba jinsu ba.

"Naji ma'anarsu amma da gaske kina yi min son so?"

KASHE FITILAМесто, где живут истории. Откройте их для себя