Mijin Ummu nah

By MSIndabawa

18.1K 810 12

Labari akan wata yarinya Hafsat wacce mahaifin su ya rasu mahaimahaifiyar sy ta sake aure in da ta auri mugun... More

1-5
6-10
11-15
16-20
21-25
26-30
31-35
36-40
41-45
46-50
51-55
56-60
61-65
66-70

71-75 End

1.1K 50 3
By MSIndabawa

[11/20, 1:18 AM] Antty😍: *MIJIN UMMU NAH*
True life story




By *Maryam S Indabawa*
*MANS*



🌐HAJOW📝🌐

👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧 HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾


Page *71*



Ina fara masa tausa ya fara sakin nishi.
"Uhmm wash Ah!"

Yana fada yana lumshe ido. Tausa ta fara ratsa shi sai ji nayi ya rumgumo ni ya juya dani ta kasan sa.

Kissing dina ya shiga yi ta ko ina. yana shafata tare da fitar da wani irin numfashi.

Na tsorata ganin abubuwan da yake min, jikina rawa yake sosai.

Matsar da yake min har tai min waya hawaye neya fara zubo min.





Hafsat tasha azaba da radadi sosai take kuka kamar ranta zai fita.

Bai bar ni ba sai da ya dauki awa hudu yana abu daya.



Jikin sa yaja ni yana ta lallashi, yana ta zuban addu'a Hafsat Allah miki albarka. Nagode da kika min kyautar mai mahimanci Allah ya jikan Abbu ya dadawa Ummu lafiya da tsawon rai. Allah ya baki zuri'a tagari Allah barmu tare.   Sai samin albarka. Jin dadin addu'ar dake min ne yasa nayi lamo a jikin sa.

Bandaki ya kaini ya tsarkake min jikina ya gasa min jikina sosai sannan muka yi wankan tsarki a tare sai kace Baby ya nadoni a towel ya dauko ni cak.

Gado muka haye lokacin karfe uku da rabi na dare. Lallashina ya fara yi har na koma bacci.

Mikewa ya yi ya hau kan sallaya ya fara godiya da Allah sai da yaji kiraye kiraye sannan ya zauna.

Jin anyi kiran Sallah yasa ya iso gareni. Ina cikin bargo na kudundune saboda zazzabin da ya rufe ni. Bacci nake amman sai ajiyar zuciya nake saukewa.

Jikina ya taba yaji zafi. Tausayi ya kamashi. Kaina yake shafawa a hankali har na bude idon ta.

Dauka yayi ya kaini nayo alwala sannan mukai sallah. mun idar da ya juyo ya cigaba damin addu'a tare da samun albarka.

Daukata yayi ya maidani gado, ya ringa min tausa. A hankali bacci me dadi ya dauke ni.


Sai karfe daya na tashi, na duba babu Ya Haidar sai filo da yasa min abaya da gabana sai kace wata jaaririyar da uwarta ta gama lallabata tayi bacci.

Nayi murmushi na tashi a hankali har yanzu jikina da sauran ciwo da tsamin da yayi. Na lallaba a hankali na nufi ban daki.

Wanka nayi na kara gasa jikina na fito nayi kwalliya cikin riga da siket na wani swiss boyel ruwan goro ne da adon ruwan omo.

Nayi kwalliya ta me kyau na feshe jikina da turaruka masu dadi. Wani kamshi nake fitar wa mai ni'ima da sanyi. Gadon na gyara na koma na zauna.

Ji nayi an rufe min fuska da wani hannu mai taushi, ko ba a fada ba nasan Ya Haidar ne.

Zagayo wa yayi ya zauna kusa dani. Kai na na kifa cikin cinyoyi na. Ina me tsananin jin kunyar sa.

Yace,
"Ai kam sai naga kwalliyar da akai min."

Ya rumgumo ni yana kicuniyar bude min fuskata. Cakul kuli ya dinga yi min,

"To shi kenan mu tafi gado mu maimaita abin jiya."

Cakul kulin da yake min yasa na  dago fuskata ina dariya. Jin abin da ya fada yasa nace,

"Dan Allah kayi hakuri."
"A'ah nidai sai na kara."

Ganin ya dauke ni ya dira akan gado yasa na shagwabe fuska ina masa kukan shagwaba.

"Oh Sorry Habibaty da wasa nake miki."
Daga haka kuma ya fara lallashi.

Dago ni yayi muka tafi daining. Akan cinyar sa ya zaunar dani ya dinga bani a binci har na koshi.

Falo muka tafi yana tsokanata irin kukan da kiran Ummu da Momy da na dinga yi.

Murmushi kawai nayi nai kasa da kai na dan kunyar sa nake ji. Bama kuma ya kawon maganar jiya.

"Hafsat!'
"Uhmm!" Na fada kaina a kasa.

"Nagode sosai bisa halacin da dauriyar da kika yi. Gaskiya ke jaruma ce, na gode miki. Kin faran tan kin mallake zuciya ta banda burin da ya wuce in faranta miki Hafsat."

Kasa na kuma yi da kai na. Dago ni yayi ya hade bakina da nashi yana sumbata ta. Sai da yai me isar sa sannan ya sake ni.

Fuska na shagwabe, hawaye na zubo min.
"Lafiya Baby?"
"Ya Haidar! Ummu."

"Oh to shine kuma zakiyi kuka."
Wayar sa ya dauko ya kira number Ummu.
sai da suka gaisa sannan ya mika mata.

Bayan sun gaisa suka dan taba hira sannan Khadija ta karbi wayar.
Sun jima akan wayar Ya Haidar sai kallon ta yake yana jin dadin ganin ta cikin farin ciki.

Bayan sun gama ya jawo ta jikin sa yana shafa cikin ta.
"Baby na bacci kake?"
"Ya Haidar wane Babyn naka."

"Gashi nan kwance a cikin ki."
Ido ta rufe da hannun ta.
"Wa yace maka da Baby a cikina."

"Ni nasan dashi tinda ni na ajiye shi jiya."
"Uhmm ni ba komai a cikina."

"To shikenan yau zan yi ajiya ta a cikin ki."
"Kai Ya Haidar" na fada ina kokarin tashi a jikin sa.

Jawo ni yayi ya kara rumgume ni."Eh man!"

Ni dai shiru nayi dan ban son maganar ma sai kace bai san kunyar sa nake ji ba.

jijigani ya ringayi har bacci ya dauke ni. kiran Sallah da ake na azahar shi yasa na tashi.
Alwala mukayo ya tafi massalaci.







*INDABAWA*
[11/20, 1:18 AM] Antty😍: *MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY



BY *Maryam S Indabawa*
*MANS*

🌐HAJOW📝🌐

👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧 HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾.





Page *72*










Zaman lafiya muke gudanar wa sosai na cire kunya na ringa kula da mijina dan ni kaina ina mamakin wani abun da nake masa. To in ban ba ya auro wata tai masa na zama koma baya.

Ina son Ya Haidar kamar yadda yake tsananin sona da kaunata. Sam bai son ganina cikin bacin rai ko damuwa. Kamar kwai akan Fa haka ya Haidar ya mai dani.

Kowa kokarin yake yaga yafi dan uwan sa kula da dan uwansa yake.
Har gasar yin abu muke duk dan wannan yace yafi son wannan.

Gaskiya nasan nayi dace da miji na gari wacce kowace mace zatai sha'awar auren sa.

Yadda ya Haidar yake min har mamaki nake ji dan yana shayar dani soyayyar da ban taba zaton samun ta ba.

Kudi kuwa kullum sai ya zube min su duk da ba amfanin da nake dasu. Komai nasa tare muke yi haka nan komai nawa tare muke.

Bama in weekend ne tare muke gyaran gida da girki bayan nan kuma muyi wanka tare kowa yaiwa dan uwan sa kwalliya.

Na yadda Soyayya gaskiya ce. Sannan sai da ita ake samun jin dadin zaman aure.

Munje gidan Hauwa dan yini mukayi acan.

Kullum sai nace ya kaini gun Momy amman sai yace A'ah ba yanzu ba.

Ranar da na cika sati bakwai da safe yace na shirya zamu wajen Momy.

Rumgumeshi nayi na fara sumbatar sa. Martani ya fara maida min.

Ganin in nabiye mishi zamuyi rana wajen zuwan mu yasa na bashi hakuri kan sai mun dawo.

Kitchen naje nai sauri na mata cake da meat pie sai miya da na hada mata ta kaji wacce duk sati sai na aika mata da irin ta.

Wanka naje nayi na fito na shirya cikin wata atampa da akai min dinkin riga da zani.

Purple colour ce da milk. Simple kwalliya nayi na shirya na feshe jikina da turaruka. Milk mayafi da takalmi da jaka na saka.

Turare na debo na saka a jaka ta.
dakin Ya Haidar na shiga naga fitowar sa a wanka kenan.

"Allah Ya Haidar ka fiya son wasa yanzu sai yanzu zaka shirya."
"Eh! Ke nake jira ma."

"To ai gani." Ta fada tana cire mayafi da jakar ta. Akan gado ta daura su.

Mai ta shafa masa sannan ta dauko masa milk shadda. Ta saka masa ta gama ta fesa masa turaruka.

Janyo ta yayi jikin sa.
"Baby kinyi kyau."
"Nagode Ya Haidar."

"Wai ban hana ba."
"Yi hakuri na daina."

"Kin tina."
"Me?"

"Farkon fara shirya ni. Da kikai."
"Kai Ya Haidar""

"Eh!" Ya fada yana kashe mata ido daya.

"Wallahi kai dai duk yadda zamu dau lokaci ba mu fita shi kake so. Kalli agogo fa."
Ta fada tana nuna masa hannun ta.

"Karfe daya saura."
"To shine me?"

"Mu tafi man."
"Ni ban son kiyi nesa dani."

"Ya Haidar ai muna tare."
"Eh! Zaki iya zama a cinya ta a gaban Momy."

Dariya tayi tace,
"Me zai hana muje ka gani"
"Oh Haba."
Ya fada yana bude idanu.

Mayafin ta dauka, sannan ta dauki jakar ta. Jakar ya amsa hannun sa taja suka fita.

Kitchen ta shiga ta dauki fulas din da ta zuzuba wa Momy abubuwan da tai mata.

Kallo ya bita dashi. Ta bude mota ta ajiye a gidan baya sanna ta koma mazaunin driver.

Yana tsaye yana kallon ta. Dagowa tayi.
"Oo Haba Ya Haidar!"

Kai ya juyar.
"Oh Haba Sweety nah taho mana."
"Kai ya langwabar mata dashi."

"Zan rama ne ta fada a zuciyar ta."

Ta fito daga motar lalashi sa ta fara sai kace tai masa wani abu.
"Haba darling dina. Kar muyi rana mana taho kaji."

Ta fada tana kamo hannun sa.
Sai da ta saka shi a cikin motar sannan ta koma mazaunin driver.

Dan tasan in har ta bashi driving din bazai kai ta inda take so ba kuma tafiyar a hankali zai yi yana wasa da hankalin ta.

A wani store ta tsaya, kallon ta ya tsaya yi.
"Minti uku please."

Ta fada tana bude safe din motar kudi ta diba ta fita.

Bayan ta yabi. Bangaren kayan maza ta wuce.

Shadodi ta debo kala shida da wasu boyel su ma kala shida. Sai atampa da less da ta diba.

Shidai yana biye da ita a baya. Har ta gama dibar kayan da zata diba.

Sukaje suka biya suka fito. a mota ta saka sannan suka shiga.

"Sannu Hajaju nah."
"Yauwah My Alhaji."

"Kayan fa."
"Na Dady da Momy ne."

"Dukka wannan."
"Yayi kadan ne,"

"A'ah angode."
Hararar sa tayi ta maida kan ta akan titi.








*INDABAWA*
[11/20, 1:19 AM] Antty😍: *MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY



BY *Maryam S Indanawa*
*MANS*




🌐HAJOW📝🌐

👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧 HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾




Page *73*






bai kara magana ba sai magabar kamfanin da suke. Tana bashi shawara akan yadda zasu gudanar da abubuwan.

"Baby wallahi da ma Kema Business kika karanta."
"Haba!'

"Eh man."
"Hmmm!"

Suna isa gidan tai parking ta fito ta bude masa
"Woo yau Baby na ta maidani matar."
"Yo kai zan bari kai ta fama."

Baya ta bude ta dauko ledar kayan. Daya ya karba da jaka ita kuma ta dauki dayar.

Suna tafe suna hira abin sha'awa duk wanda ya gansu sai sun burgeshi.

A haka suka karasa falon. Ba kowa a dakin. Sama suka haye. Dakin Momy suka shiga tare da sallama.

"Assalamu Alaikum"
"Wa'alaikum salam!"

Suka shiga. Da fara Momy ta mike ta kamo Hafsat ta zaunar akan kujera.

Zanewa tayi kasa tana gaisar da ita.
"Momy ina yini?"
"Lafiya kalao Hafsat! Ya gidan?"

"Lafiya, yasu Dady?"
"Lafiya laou Hafsat."

"Ya gidan ince ba wata matsala."
"Eh babu!"

"Ke dai In akwai ki fada min."
"Momy wallahi babu."

"To masha Allah!'

"Ni baza a bani gun zama ba."
Ya fada yana daga bakin kofa.

"Sai na baka waje ma."
"Amman wallahi Momy yauzu kin rage so da kula dani. Ji fa."
Ya fada yana nuna Hafsat.

"Daga zuwan mu kinja ta gashi sai tambayar ta kike."
"Gidan ku!"

"Ni daman ai nasan kin fison Hafsat."
Ya fada yana shigowa dakin. A gefe na ya zauna.

"Ina yini Momy!"
"Oo sai da ka gama mitar taka."

Kai ya sosa. Ya kuma gaisar da ita.
Bayan sun gaisa taja su Dakin Dady.

Nan ma kan Hafsat a kasa ta gaishe shi sannan ta bashu kayan da ta siyo masa.

Godiya ya dinga mata da sanya mata albarka da addi'ar zaman lafiya da gama wa lafiya.

Amsawa take a cikin ran. Shikam Ya Haidar a fili yake ta amsawa da Ameen.

Daga nan dakin Momy muka shige nan na bata nata kayan. Momy na fadan ai sunyi yawa.

A gidan muka yinin dan Ya Haidar sai yamma ya fita. Sosai Momy ta dinga koyan abubuwa. Na zaman aure da girke girke.
Turaruka kam masu dadin kamshi ta kuma hada min.

Sai bayan isha'i muka tafi dan cewa nayi da sai ya dawo a gidan zan kwana.

Roko na ya fara yi dan Allah kar na fadawa Momym nace
"ai na riga na fada mata."
"Ya salam! Kai Baby."

Kwanciya nayi akan gadon. Dagoni yayi yana magiyar dan Allah in tashi mu tafi tin kan Momy ta hanashi tafiya dani.

Mayafi na da jaka ya dauka. Mayafin ya yafa min sannan ya sakan takalmi. Ya rike jakar yaja hannu na muka fita.

A kasa muka samu Momy,  "Momy mun fito zamu tafi."
"To Haidar sai da safe."

Har kasa Hafsat ta durkusa tana wa Momy sallama. Momy ta dagota suka fito har wajen mota.

Bude mata tayi ta shiga sukai sallama. Sai da taga fitar su sannan ta koma ciki.

Sai da suke shiga wani mall sukai siyayya sannan suka sjige gida.

Suna komawa wanka sukai suka yi shirin bacci suka kwanta.

Ya jawo ta jikin ta. Yana ta jijigata har tai bacci.

Haka suke cikin farin ciki da kwanciyyar hankali.

Saman Lafiya ma lafiya baka taba jin kansu. Duk da zaman tare dole a saba wani lokacin.

Amman Hafsat na da *hakuri da juriya* wannan yasa suke zaman lafiya.

Dan in tai masa laifi zata nashi hakiri haka ko shi yai mata zata fahimtat dashi kuma ya gane ya bata hakuri

Soyayyan kuwa sai wacce tai gaba. Dan Haidar na tsaninin so da kula da ita.

Tana kitchen tana girki dan yau Hauwa tace mata zata zo. Murna take dan haka tin wuri ta kamala komai.

Tana gama komai taje tai wanka tai kwalliya cikin wata orange doguwar riga da Momy tabkawo mata da tafita waje.

Ta feshe jikin ya da turaruka. Karar mota taji tana lekawa taga Motar Hauwa ce.

Da gudu ta sauko kasa tana zuwa ta rumgume ta da katon cikin ta.

Hannun ta ta kamo ta shigo da ita sama suka haye.
"Sannu Maman Biyu. ai da kin bari na zo."
"Hmm ba komai nima ina son zuwan ai."

Lemo taje ta kawp mata da kayan ciye ciye. Suna zaune suna hira tana ci.

Kafar ta Hafsat ke matsa mata.
"Sis kin kusa sauka ko?"
"Wata takwas."

"Samnu maman biyu Allah raba lafiya Ameen!"
"Ameen!"

"Ni fa gida nake son naje na haihu."
"Kai ki tafi ki bar mu."

"Eh to ya zamuyi wata biyu kawai zanyi."
"To Allah raba lafiya."

Hirar yadda zasi gudanar da suna suka dinga yi.






*INDABAWA*
[11/20, 1:20 AM] Antty😍: *MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY LIFE



BY *Maryam S Indabawa*
*MANS*


🌐 *HAJOW* 📝🌐

👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧 *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* ✍🏾✍🏾✍🏾


Page *74*




Ranar tare muka yini da Hafsat. Sai yamma su Ya Haidar suka dawo tare da Ya Nura.

Suna cin abinci suka fice. Sai bayan magariba ya dawo suka tafi.





wata na uku da aure Hauwa ta haihu a Kano ta haihu. ana jibi suna muka tafi ni da Momy da Ya Haidar.

A gidan mu nacan muka sauka inda Khadija ta gyara mana tai mana girki. Momy kememe taki zama wai ita gidan Ummu zata tafi.

Haka muna sauka Ya Kamal yazo ya dauke ta ya kaita gidan Ummu mu kuma gidan mu muka tafi.

Gida ne madaidaici me bene. Katon falo ne. akasa sai bedroom da kitchen a kasa.

Sama kuma falo ne sai dakin bacci guda daya

Orange kalar kaya aka saka a dakin da adon baki. A kasa.

Sama kuma lemon green da milk akai masa ado. Gidan ya tasru ba tarkacen nan.

Muna shiga wanka mukai muka zube akan gado Bacci ne ya dauke mu dan sai yamma muka tashi.

Muna tashi Ya Haidar ya fara rigima sai kace yarro. Duk da nasan abin da yake nufi kyale shi nayi na fara shiryawa dan hankalina yayi wajen Ummu.

Wanka na fito sanye da towel, a gaban muduni na zauna na fara shiryawa. Na gama na murje jikina da turaruka.

"Baby nah!" Yai maganar muryar sa a hankali.

"Na'am Ra'isul Kalbi."
"Juyo ki kalle ni mana."

Juyo wa nayi, idanun sa jajir dasu.
"Hayyati!" Nima muryata a raunane.

Kai Ya langwabar. Tausayin sa ya kamani, jikin gadon ma matsa.

Towel din jikina na zare na yar gefe. Kan sa na fada, rumgumata yayi ya dinga sumbatata. Bargon kan gadon yaja ya rufe mu dashi.




Bamu muka je gida ba sai bayan Sallah isha'i. Shima wajen Hauwa naje naga Baby a can muka hadu dasu Faiza.

Da gudunta rumgimeni tana murnar gani na. Ita ma da nata cikin dan wata shida.

Sai goma muka fito muka taho gida duk yadda naso naga Ummu a ranar ban ganta ba.

Sai washe gari wajen karfe daya muka tafi gida, murma wajen su Khadija da Khairat kamar sa mai dani ciki.

Ummu ma tayi murna da gani na. Haka su Baba lami suka zo duk muka gaisa.

Abbi kuwa shi kawon wancan da wancan duk sai murna gani na suke.

Ana magariba muka tafi gidan su Hauwa. Ranar so nayi ya barni na kwana amman yace gobe da wuri zai kaini.

Ba yadda zanyi haka na hakura dan Hauwa ce ta kara zuga shi kan na bishi.

Yadda naso na tafi karfe goma abin bai yi ba dan sai Sha biyu muka fita a gida bayan Ya Haidar duk ya gama gajiyar dani.

Muna zuwa suka fice, da dare za ayi partyn suna. Har da abokan ango.

Baby taci, sunan Babar Ya Nura, Amina inda ake kiran ta da Meenal.

Me jego ansa kwalliya tayi kyau da ita haka Baby Meenal ma sai kamshi suke.

Akwati guda nayiwa Hauwa da Baby haka su Faiza da Khadija kowa sai da nayo masa tasa tsaraba.
Har Abbi dasu Baba lami.

Ummu ma na mata take ta fadan wai kayan sunyi yawa. Momy ce tace ai sunyi kadan ma.

Ni da ita da Faiza tai mana dinki iri daya na party. Wani milk din less me adon purple colour. Sai mayafai da takalmi ma duk iri daya.

Ya Nura da su Ya Haidar da Kamal kuma suka saka milk din shadda.

Wajen yayi kyau anci an sha anyiwa Baby Addu'a sosai.

Aka tashi lafiya. Ranar dai a gidan su Hauwa muka kwana washe gari da yamma muka koma gida.

Gidan mu muka tafi, sai dare muka tafi.

Washe gari mukaje gidan Kawu Sagir da Baba Ado.

zuminci sosai dan sai d muka zaga yan uwa. Gidan Anty Bilki ne na karshe inda ta hada min kaya. Bayan na kai mata tsarabar ta da ta Sabir Babyn ta.

Satin mu biyu muka daga da kewar yan gida dan sai da nayi kwana biyu a gida shima Momy ce tasa ya barni amman bai so ba

Muka koma gida lafiya. Hauwa nayin arba'in ta dawo da Babyn ta Meenal. Yarinya kyakyawa.



*INDABAWA*
[11/20, 1:21 AM] Antty😍: *MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY




BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*



🌐HAJOW📝🌐

👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧 HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾



Page *75*

Last page.




Godiya ga masoya Mijin Ummu mah. Nagode da soyauyar da kuke nuna w littafin nan. wacce ta dawo kai na baki daya.

Ban da bakin godiya sai dai nace Allah sada mu da alherin sa.

Nagode taku har kullum yar mutan *INDABAWA*
Maryam Suleiman.







*BAYAN SHEKARA TAKWAS*

Anyi bikin Khadija da Khalifan ta inda yanzu ya yan su biyu. Da me sunan Ummu da na Abbun mu.

Bishira ma haka yayan ta uku.

Hauwa bayan Meenal tayi shekara uku ta kuma haifar Namiji aka saka masa Aliyu Haidar, sai Ammar yanzu tana shayar da Khadija.

Faiza kuma Namiji ta fara haifa, aka saka masa Muktar, suke kiran sa da Aslam. sai bayam shekara uku ta haifi mace aka sa mata Hafsat suke kiran ta da little ya'yan ku suke ce mata Momy, Sai Mariya me sunan Ummu da suke kiran ta da Ummu. Sai yanzu da ta haifi namiji aka sa masa suna Baban Faiza.

Haihuwar Hafsat ta fari yan biyu ta haifa duk mata. Aka sawa Babar  fatima suke kiran ta da zuhra sai mai binta Mariya suke kiran ta da kibdiya. Sai namiji dan shekara uku me sunan Abbu da suke kira Ashraf.
Yanzu haka cike ne da ita dan wata biyu.

Sun zo kano saboda yara sun samu hutu sai yai dai dai da haihuwar Faiza.

Zaman lafiya suke yi. Ga zumunci dan yaran su ma baza ka gane dan wancan da wacan ba.






Wata hadadiyar mota Naga ta tsaya a dai dai Ado bayaro mall dake zoo road. Jeep maroon kala.

Yara ne yan mata su biyar suka fito a motar baza su wuce shekara 8, 7 zuwa 5 ba sai karamar yar shekara biyar. kyawawa dasu abin sha'awa.

Sai maza sa suka ma suka fito daga gaban motar wanda babban zai shekara 8  Sai dan shekara biyar da dan shekara  uku.

Hafsat ce ta bude gidan gaba ta fito. Ta kara kyau hasken ta ya kara fitowa.

"Momy!" Ammar ya kira sunan ta.
"Na'am yaron Dady!"

"Kinga Ya Meenal ko."
"Ya meenal mene."

"Wai dan nace yazo na rike hannun sa."
"To jeka ta rike maka hannun man."

"Momy ni Ya Zuhrah ce."
"To jeka gun nata."

Da gudu ya karasa wajen su. Su biyu kamar su daya. Kuma da Hafsat suke kama.

"Ina Yaya Zuhrah."
ya Fada dan ba cika gane su suke ba.
"Ganinan Boy."

Hannun ta ya kama. Dayar kuma ta kama hannun, ashraf.
Me sunan Hafsat kuma tayi wajen Meenal ta rike ta.

Suka shige. Siyayya suke kowa na zabar abinda yake so. Suka gama suka suka biya suka tafi gida.

Rigiyar zaki suka nufa. A kofar gidan. Faiza suka tsaya.
Sai da suka shige sannan tabi bayan su.

Mota taji ta shigo gidan juyawa tayi dan ganin waye. Motar Ya Haidar ce ta shigo.

Tsayawa tayi tana dariya. Yana fitowa ya bude mata hannu da gudu ta fada jikin sa.

"Sannu da zuwa!"
"Yauwah daga ina kuke."

"Siyaayya sukace na kai su."
"Ok. Gobe fa zamu tafi."

"Allah kaimi. Ai mun shirya."
"Da gaske."

"Eh!" Hancin ta yaja suka shige gida.

Suna falo kowa ya baje ledar sa a gaban sa. Suna ciye ciye.

Suna jin sallamar sa suka mike suka rumgumeshi.
"Dady kaga kayan da Momy ta siyo mana."

"kun cewa Momy an gode," "Eh Dady!'

Waje suka tashi suka zauna yaran sukayi dakin su.

Faiza ce ta fito da Baby a hannu Ya Kamal na bayan ta.

Zama sukai sai gasu Hauwa nan sun shigo,
"Kinje kin kwashe mana su gidan ba dadi."
"Haba?"

"Eh man!'
"Su Yan biyu ne suka ce sai an kai su shoprite to."

"Ai da sai a dawo da su ynzu."
Da kan su kinsan zasu koma.

"Yanzu gobe zaku tafi." Faiza ta tambaya.

"Eh! Nace Ya Kamal ya dawo lagos yaki. Amman ina jin sai na hada shi da Dady."
Hafsat ta fada.

"Kuma fa zai fi kullum muna tare ba sai anyi tafiyar jirgi ba." Hauwa ta fada.

"Ke dai bari Allah sai na hada sa da Dady. Aiki yanzu yai wa Yayana yawa."

"Ashe da biyu take son dawowar taka Dear."

"Rabu da ita da tace min dan in ragewa Ya Haidar aiki ne ai da na koma."

Dariya sukai suka ci gaba da hirar su. Yaran kuwa da suka ji gobe yan lagos zasu koma kuka suka dinga yi.

Muna komawa gida Momy tayo waya wai yaushe yaran ta zasu dawo ne,
"Momy gobe zamu taho."
"Toh Allah kaimu lafiya."

"Ameen!"
Mukai sallama.

Muna dira a lagos yaran suka ce kuka gidan Momy zasu. Dan haka drivern gidan Momy mukai wa waya yazo ya debe su ya kai su.

Gida mukayi abin mu.

Bayan wata bakwai Hafsat ta haihu ta haifi nmiji aka sa Masa sunan Dady suke kiran sa da Fauwaz.

A lokacin kuma su Faiza suka dawo lagos.

Zumuncin su ya koma haduwa dan in wannan weekend din sukai acan wani acan suke yin sa.

Soyaya da kualawa da juna kowa yake kokarin yi shi da yan uwan sa.

Haka so da shakuwar su Ya Haidar da Hafsat ta dadu inda kowa baya son rabuwa da dan uwan sa.

Ummu da Abbi komai lafiya inda Yanzu Khairat tana university tana level one.

Yanzu Ya muktar da Abbi sune akan harkar kamfanin

Komai yayi dai dai sai masha Allah zuri'a ta hadu zaman lafiya da jin dadi shi yake gudana a tsakanin su gaba daya.



*ALHAMDULILAH*

Alhamdulilah Ala kulli Halin.

Dukkan yabo ya tabbata ga Allah da kuma annabin sa Annabi Muhammad (SAW).

Nagodewa Allah da ya bani ikon kammala wannan littafin nawa Lafiya.
Alhamdulilah.

Ana kawo karshen littafi na mai suna *MIJIN UMMU NAH*
Sai kuma kun jini a cikin wani sabon littafin na *ASMA'U HUSNAH*

*NA BARKU LAFIYA, ALLAH SADA MU DA ALHERIN SA.*

*DUK WANDA NA BATAWA INA NEMAN   YAFIYAR SA.*

*DUK WANDA YA BATAN MIN NA YAFE MASA*

*Momy nah* *Ummu nah* abar alfaharin ina kaunar ki. Allah yaja min ranki yasa ki ga jikokin ki.

Allah yasa ki gama lpy, Allah dada miki lpy Ameen.
Ina son ki ina kaunar Ki. Allah ja min da ranki ya kara miki lafiya.
Allah kare ki daga duk masu sharri Allah ya sada ki da dukkan Alkhairai.

Ban da bakin yi mki godiya haka nan addua'a ta bame karewa bace a gare ki sai dai kullu kece wacce nake fara mikaww kwokwon bara wajen *Rabbi samawati wal ardi.* Ina fatan kuma Allah ya Amsa

*Ameen*


*ABBU NAH* *ALLAH JIKAN KA DA RAHAMA YASA ALJANNAH KOMA.*


Yar Uwa rabin jiki ayi fada a shirya *Nusaiba Suleiman Indabawa* ina kaunar k Allah barmu tare Allah baki miji na gari.

Gimbiyyah ban manta dake ba *little Yasmeen.* *Hauwa Autar mu, Autar Momy*



JINJINA GAREKI *Anty Rasheedat (Rasheeda Abdullaahi Kardam)*
Ima alfahari dake, ina kaunar ki har cikin rai na. Allah kara miki dauka ka yasa ki gama da duniya lpy, Allah kara basira. Allah biya miki bukatun ki na alheri.

Nagode! Nagode! Nagode! Allah bar zamunci.

Ke kika jibancin littafin nan  nawa har ya kammala Allah saka miki da akhairi Ameen.
Wallahi ban da bakin godiya gareki, sai dai ina kaunar ki zan ta kuna kaunar ku da miki fatan alheri.

*Na gaishe ki Anty Rash*
Allah bar zumunci ina kaunar ki irin dayawa nan bai da a dadi

*Zauren Zumunci online.*
Na gaishe ga dukkan member na ciki Allah bar mu tare ya daurar da zumuncin ya hade kan mu
*Ameen!*

Jinjinga gareku. Allah kara basira da daukaka da zakin hannu Ameen.
*Rashidat A kardam*
*Khaleesat Haidar*
*Aisha MamanAbdul shakur*
*Aysha Ya'u Kura*
*Bilkisu Bilya*
*Safiya Huguma*
*Zeety Maman Hanan*
*Zahra Surbajo*
*Hajara M Bashir*
*Fidausi Fey feey*
*Sadnaf*
*Faxufashion*
*Billy saraki*

*kai dukkan ku writer Allah ya kara basira da hade kannmu tare da zakin hannu Ameen*"


Kawayena bazan manta daku ba *Hauwa Kamilu Zimit*
*Faiza Yahuza*
*Khadija Taiyeb Na'abba*
*Zainab Umar Kunya*
*Amina Sabo*
*Nusaiba Khalit*
*Ummulkhairi Aminu*
*Naima Aminu*
*Naima Hassan*
*Amina Ibrahim*
*Nusaiba Ibrahim*
Wayo da yawa fa Wallahi duk kan ku ina kaunar ku da wanda na ambata da wanda ban ambata ba duk kuna raina


Sisters din
*Maimuna (Yaya Baby)*
*Khadija Muhammad Mahmud*
*Maryam Jaafar*
*Aisha Hamidan*
*Khadija Taiyyeb*
*Fatima Ado*
*Safiyyah Ado*

Duk kuna raina nagode da Supporting dina da kuke.

Bazan taba mantawa dake ba.
*Maryam Yusuf*
*Maryam Zamfara*
*Khadija Kauna*
*Ummu Ayda*
*Ummu walid*
*Aisha (Noor H N)*
*Fatirih*
Da sauran da kuka kwanta min da duk masu son littafi na.
*Nagode sosai*

*INDABAWA HAUSA NOVEL GROUP 1 & 2*
*HAJOW (Hakuti da juriya online writters)*
*Zauren littafan hausa*
*Kasaitattun mata*
*Ina mata*
*RASH kardam. Hausa Novel 1 & 2*

Na gaishe ku yan uwa abokan aiki yana *HAJOW*
*(Hakuri da juriya onlinw writters)*
Allah bar zumunci ya kara basira hazaka da *hakuri da juriya*

*Ameen*


Allah bar zumunci
Ana tare🤝

♥♥♥

Sai kun ganni a cikin sabon littafi na *ASMA'U HUSNAH*


Na barku lpy
daga yar gidan *Suleiman Haruna Indabawa*

*Maryama ce*







*MS INDABAWA*
08062882472

Continue Reading

You'll Also Like

29.4K 864 23
Labarin Yarinyar da ta tashi a tsakanin yayyenta maza, da suke shirye da aikata ko menene saboda ita, ba ta san tsoro ba, rashin ji ya kaita ga haɗuw...
1.5K 61 21
Based on True life event
937 66 16
38.5K 3.3K 22
'YA CE kamar kowa wadda ta taso cikin ɗabi'a da al'ada irin ta BAHAUSHE! "Me ta ke so? Me nene burinta?" Babu wanda ya taɓa tambayarta. Kalma ɗay...