16-20

1.1K 59 0
                                    

[11/20, 12:48 AM] Antty😍: MIJIN UMMU NAH
TRUE LIFE STORY


BY Maryam S Indabawa
MANS

Page 16

Dedicated to you, Zetty, maman Hanan, Allah ya daukakai Allah ya shige miki gaba ya kareki daga sharrin mahassada, Allah kara basira My Zetty prety.


Satin Khadija daya ta warware ta koma makaranta, in Ummu zata siya mata abu sai ya hana wai ana sangartata karatun zatayi ko cin kayan dadi, dan haka ne ma wani lokacin Ummu bata sanin naje dan zanje nai mata siyayya ne na kai mata, sannan duk bayan sati biyu zan mata siyayyar kayan motsa baki, wanda nasan basa samu na kaimata, wani lokacin su Hauwa in sun sani tare muke tafiya kuma kowa da abunda zai kai mata. Dan haka ita bata damuwa da halin sa ta wannan fanin, dan tasan da Ummu na yi mata komai kafin ta ganni ma aiki ne.


Haka rayuwar mu ta ke kasancewa, yanzu haka Asibiti muka tafi, duk kannin mu Asibitin Murtala muka zaba kuma mukayi dace dan duk sun karbe mu.


Cikin Azumi muka fara jarabawar karshe, in da yanzu saura kadn mu gama, Khadija kam ban fasa zuwa mata ba dan da azumi duk sati nake zuwa dan yanzu itama neci suke yi.

Sallah sauran sati muka gama jarabawa, inda su Khadija ma haka, kuma duk kan mu muna sa rai da sakamako mai kyau. Dan da sakamako ya fito duk munce gaba zamu yi wato BUK Zamu tafi gaba dayan mu.

Ansa ranar Hauwa watan babbar sallah, ni na fitar mana da wani codeless pink and blue wanda ni da Faiza za muyi fitar dinner dashi, sai wani material Ruwan goro da Baki, ni na mana su ni d Faiza har da amarya ma da ba sawa zatayi ba, dan har sautin jaka da takalmi na bayar iri daya mu uku aka kawo mana.

Na kawayen mu kuma ruwan zaiba mukai da maroon head, faiza ita tayi mana na fitar daurin aure wata dakakiyar ruwan kasar shadda ce, inda Ummi da kan ta tayi mana atamafar fitar yinin ta, mu uku, sai Ummu da tasa akayi mana order Kananun kaya na children day.

Tin bayan karamar Sallah muka gama siyayyar mu dan ba ma so lokaci ya kure mana, ko da Sallah duk shirye shiryen yadda abin zai kasance muke, dan bayan babbar sallah da sati uku ne, dan haka ana yin babbar sallah muka hau rabon kati dan biki saura kwana goma mun gama.

Zaune nake a gaban mudubi na fito a wanka kenn sai ga wayar ya Kamal nan wai ina gida, nace masa "eh,"
"To gani nan ni da Ya Haidar,"
"Sai kazo," na fada ina kashe wayar."

Kwance nake akan kujera, sanye nake da doguwar riga ruwan hoda sai hula dake kaina ruwan omo, bnyi kwalliya ba amman nayi kyau sosai saai tashin kamshin turare nake, wayace a hannuna ina buga game,
Sallamar Ya Kamal najiyo, dakin mu ya shigo, wata sallamr na kuma ji cikin sanyin murya wacce in da da hayaniya a inda nake bama xan ji taba, na amsa suka shigo Ya Kamal ne a gaba sai na gano mutum ta bayan sa,
"Sannu,"
"Na fada miki ban son wannan sannun taki ko,' ya fada, yana samun gefe na ya zauna, mikewa nayi, dai dai karasowar na bayan Ya Kamal,
kai na dauke, nace, "to kayi hakuri,"
gefen Ya Kamal ya zauna, kaina a kasa ban dago ba nace, "ina yinin ku,"
Ya kamal ne kadai ya amsa, duk sai naji na kasa sakewa sannan ina jin ido a kai na.

Wayata ce tayi kara na dauka, Hauwa ce, cikin sanyi nayi sallama,  "Hafsat gamu nan fa," ta fada bayan ta amsa sallamar,
"Ke dawa?"
"Faiza mana,"
"Sai kunxo, amman fa ni yau ba inda zani,"
"Ai kam sai kinje,"
"Allah Sis wayo kike mana kefa in anyi biki kina da mai yi miki tausa mukuwan fa,"
"Zanzo da kaina nai miki," tsaki nayi dan jin shirmenta, na katse wayar.

Ya Kamal ne, yace, "Ummu bata nan ne," mikewa yayi ya tafi dakin ta, wayata na cigaba da dannawa,

Har lokacin ina jin idon sa akaina, wannan yasa na kasa dagowa, sallamar su Ummu ce yasa ya dauke kansa akaina amman duk da haka ina jin idon sa, Ummu ce, tace, "A'ah Aliyu, saukar yaushe?"
Kasa ya sauka yayi kasa da kansa, sannan ya fara gaishe ta cikin muryar sa mai dadin sauraro da sanyi, yace, "saukar dazu wallahi, na same ku lpy,"
"Yasu Anty Fati, da lagos din,"

Mijin Ummu nahWhere stories live. Discover now