Mijin Ummu nah

By MSIndabawa

19.2K 819 12

Labari akan wata yarinya Hafsat wacce mahaifin su ya rasu mahaimahaifiyar sy ta sake aure in da ta auri mugun... More

1-5
6-10
11-15
16-20
21-25
26-30
31-35
36-40
41-45
46-50
51-55
56-60
66-70
71-75 End

61-65

783 38 0
By MSIndabawa

[11/20, 1:12 AM] Antty😍: *MIJIN UMMU NAH*
true life story


By *Maryam S Indabawa*
*MANS*



🌐HAJOW📝🌐

👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧 HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾


Page *61*





Dagawa tayi, da sallama.
"Baby na!"
"Na'am"

"Me kike baki kwanta ba."
"Na kasa bacci ne."

"Nazo ne."
"A'ah!"

"Oh bakya nema na."
"A'ah ai kaga Momy."

"Gaskiya ni na gaji. Wallahi matata nake bukata."
Shiru tayi.

"Kinyi shiru."
"Eh! Toh me zance."

"Ke bakta bukatar mijin ki."
Shiru ta kara.

"Baby na! Wai ke bakya bukata ta."
"A'ah!"

"To ki fadawa Momy kin warke,"
"In nace na warke shine me?"

"Sai ta bani matata."
"Au dan ban warke bane taki baka ni."

"Eh"
"Ni kuma sai nace na warke Ya Haidar."

"Eh!"
"Wayyo Allah bazan iya ba."

"Saboda me?"
"Haba Ya Haidar, Momyn zan fadawa haka."

"To shikenan zan ce kin warke in ta tambaye ki kice! Eh "
"Toh!"

Kawai tace dan ya rabu da ita. Hira yake son ya ja ta da ita. Amman ita kuma bacci take ji. Tin tana amsa masa har tayi duf.

Bacci ya dauke ta. Saukar numfashin ta yaji, yai murmushi. Barin wayar yai a haka har shima baccin ya dauke shi.

Sai asuba suka ga lokacin da suka dauka wayar nayi ita kadai.

"Ya Haidar kenan."
ta fada tana shiga ban daki.

yau ma sai wajen goma ta tashi. komai tayi ta shirya cikin doguwar rigar material sai ta dauki mayafin kayan ta yafa.

Kanta yasha gyara sai kyalli yake .dakin ya shigo a gaban muduni ya hange ta tana fesa turare.

Karasawa yayi wajen ta. Kallon juna suke ta jikin madubin. Rumgumar ta yayi. Ido ta lumshe.

Sabuda wani kamshi da ya doku hancin ta,

Kan sa ya daura a kafadar ta. janye jikin ta tayi, ido ta juyawa masa tare da kanne daya.

Kallon ta ya tsaya yi, har ta gotashi tai wajen bedside drower. Bayan ta yabi ta dauki dan kunne ta makala sannan ta juyo tana kallon sa.

Kallon ta ya tsaya yi, ita ma haka. Kai ya dan sosa, A hankali ya dinga takowa yana biyo ta. Ja da baya takeyi.

Murmushi yayi, itama murmushin take yi tana ja da baya. Batai aune ba sai ji taji ya kamota ya hade da kirjin sa.

Kan sa ya matso da yana shin shinar wuyan ta, ido ta lumshe, ganin ya fara lugwigwita ta. Yasa ta tura shi kan gado Fadawa yayi.

Ya mike zaune yana murmushi. Itama murmushin tayi. Ta juya. hannun ta ya kamo.

Kallon sa tai da mamaki. Murmushi yayi ya kada kai ya kanne mata ido daya.

Kai ta gizgiza kawai. Hannun ta ya jawo ta fada kansa. Ido ta rufe, bakin ta yake laluba.

Gefe ta yi ta kwanta, suna fuskantar junan su, ido ta lumshe, murmushi ya kara sakar mata.

Kai ta kawar, daya barin. Shi ma juyar wa yayi yana murmushi. Sai numfarfashi take yi.

Shikam dagowa yayi. Yayi wajen fuskar ta yana shinshinar kamshin jikin ta, hannu ya saka a saman cikin ta.

Wata ajiyar zuciya ta sauke. Idon ta a lumshe.  Daukewa yayi ya kamo hannun ta ya hade ya dan haye kan ta.

Iska ya dinga, hura mata cikin kunnen ta. Ido ta rufe da karfi Bakin ta yake son laluba a hankali, da sauri ta dago daga kwancen da take.

Haki take kai kace tasha gudu ne.
mikewa shima yayi Yana dariya jingina da jikin ta. ya daura kan sa a kafadar ta.

Da sauri ta mike tsaye dan Ya Haidar duk ya wani canja mata. Mikewa shima yayi.

Jawota yayi. Ya hadata da bango, bakin su yahade gudaya yana lotsa.
Sandarewa tayi ta kasa hanashi.

Sai da yayi me isar sa sannan ya jawo ta ya rumgume ta. Sunfi minti goma sannan ya saketa.

Hannun ta ya kama suka fita falo. Ba kowa a falon dan Momy na can gyara dakin Dady dan wani satin zai dawo.

Shi ya dinga bata abincin abaki, har ta koshi.




Momy na lura da yadda yake takurawa Hafsat dan haka tace kada ta kuma ganin sa a dakin ta. Ko kofar dakin bata yadda ta ganshi ba.

Zuciya yayi yaki koda zaman gidan duk da kewar da yakeji ta Hafsat






*INDABAWA*
[11/20, 1:13 AM] Antty😍: *MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY







BY *Maryam S Indabawa*
*MANS*


🌐HAJOW📝🌐

👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧 HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾

Page. *62*






Kusan kwanan sa hudi basu hadu ba. Aiki ya koma kullum acab yaje yini sai dare zai dawo.

Da ya dawo zai dibi abinci yai dakin sa. Yana gamawa zai hau aiki da ya gama ya kwanta.

Ya maida kanshi too busy duk dan kar yana damuwa da rashin ta. Amman wani abun kamar kara masa kewar sa ake da son kusantar ta yake.

Ita ma Hafsat sam bata jin dadin rashin ganin sa amman sai ta danne hakan a zuciyar ta dan tasan Momy bazata cutar da ita ba.

Yau Momy ta fita danyo siyayyar abubuwan da take shiryawa bada sanin komai ba.

Kamar ya sani shi kuma ya dawo gida. A lokacin kuma sai yaji yana son ya ganta.

Dakin Momy ya nufa kai tsaye dan yasan bata dakun dai ita.

Da sallama ya shiga amman ba kowa a dakin.

Wajen bandakin dakin ya karasa, jin ana amfani da ruwa yasan Hafsat ce dan yasan ba inda Hafsat take zuwa kullun tana daki.

Kofar ya bude a hankali. Sandarewa yayi ganin ta ciki ruwan kumfa.

Idon ta a rufe ta jingina shi da bango. A hankali ya karasa wajen da take.

Zama yayi a gefen ta ya zura hannun sa cikin ruwan.

Tunani take me zurfi.shiyasa ba taji shigowar sa ba.

Cinyarta ya shafa. Ji tayi wani abu ya bi jikin ta. Wannan yasa ta bude idon ta da sauri.

"Ya Salam!" Ta fada ta rasa me zatayi, dungulewa tayi waje daya.

Kallon ta ya tsaya yi kamar shasha dan duk ta sukurkuta masa tunanin sa.

Ganin ta nade waje daya ne yasa ya daga ta tsaye.

Kuka ta saka mishi dan tasan Momy bata nan yau kashin ta ya bushe.

Kuka take sosai wanna yasa ya sake ta. Ya mike.

Murya a dashe, yace,
"Bari nai miki wanka."

Tana kuka tace,
!A'ah dan Allah nagode."

Murmushi yayi. Ya juya ya fita.
"Ina jiran ki to."
Ya fada mata.

Tafi awa daya a bandakin ta kasa yin komai sai da kyar ta cuda jikin ta ta fito.

Da towel kadai ta shigo ban dakin dan batai tsammanin ganin sa ba.

Da kadan ya wuce cinyar ta.

"Ya Haidar!"
Ta fada tana daha cikin ban dakin.

Yana jin ta yai mata shiru.
"Ya Haidar!"
Ta kuma kiran sa.

Shiru ya karayi.
"Ya Haidar!"
Jin ta kira sa sau uku yasa tace baya dakin.

Fitowa tayi, ta wuce gaban madubi. Zama tai tana shafa mai.

Sai da ta shafa kafafunta sannan ta dage towel din tana shafe jikin ta.

Kamar daga sama akace ta juyo, ta ganshi kwance akan gadon ya zuba mata ido.

Ihu ta saki ta dunkule waje daya,
"Ya Haidar! Dan Allah ka fita."

Kallon ta yayi, kawai . Shifa komai ya tsaya masa.

"Dan Allah!"
Mikewa yayi yana murmushi. Ya fice. Dakin sa ya shige ya fada saman gado.

juyi yake kawai  idon sa jawur. Azaba kawai yake sha.

Yayi dana sanin shigarsa ban daki.

Yana fita taje bta rufe kofar ta dawo ta saka kaya.

Daga ranar bata kuma sa shi a idon ta ba.

Momy Ta hana Haidar tafiya da Hafsat ne saboda, dinner da zasu yi in Dady ya dawo.

Dan ranar da ya dawo a washe gari za'ayi ta a mika masa matar sa.

Su Ummu da su Abbi duk zasu zo haka su Faiza.

Taro dai xa tayi sosai.

Dilka ta kira wo aka karayiwa Hafsat sannan ranar da Dady zai dawo da safe akazo akai musu jan lallai. Hafsat har da baki a kai mata.

A ranar kuma yan Kano zasu taho. Ana game wa Hafsat lalle. Ta sa Idi driver ya kai ta saloon ai mata gyaran kai.  Jamila mai aiki tasa ta raka ta.

Tafiyar ta ke da wuya Su Ummu suka sauka ta wagar su guda.

Shikam gogan bai san komai ake shirya wa ba yasan dai Yau Dadyn sa zai dawo.

Tin ranar da Hafst ta daga masa hankali be kara bari sun hadu dan zai iya aika aika.

Da Yamma Dady ya dawo.

Da Murnar sa ya shigo gidan dan yasan Dady zai sa Momy ta bashi matar sa.

Abinda ya gani shi ya bashi mamaki sau Ummu ya gani zazaune.

Baki ya bude yana kara murnar ganin ta.

Da sauri ya karasa gefen Momy yana mata sannu da zuwa.

Kamal yaje ya rumguma.
"saukar yaushe." "Dazu nan."

"Taso muje gun Dady yaja hannun sa sukai sama."

Bayan sun gaisa dasu Faiza da Khadija.







*INDABAWA*
[11/20, 1:13 AM] Antty😍: *MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY




BY *Maryam S Indabawa*
*MANS*





🌐HAJOW📝🌐

👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧  *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* ✍🏾✍🏾✍🏾







Page *63*

Sai kusan magariba suka dawo saboda wasu kananun kitso da akai mata.

A gajiye ta shigo dakin, da sallama a bakin ta.

Jin hayaniya yasa tace yau Momy baki tayi,

Tana shiga ta hangi su Ummu da gudu ta fada jikin ta tana kukan farin ciki.

Faiza tace,
"Au wai ke baza ki girma ba."

Da sauri ta juyo, ta fada jikin Faiza tana murna.

Khadija ce ta sauko a bene tace.
"Anty!"

Ya salam ai Hafsat mikewa tayi ta rasa gun wanda zataje dan murna.

Ya Kamal yace,
"Hafsy mu."

Gefen sa taje ta zauna. Sai a lokaci, ta lura da Ya Haidar da ya saki baki hanci da ido yana kallon ta.

Kasa tai da ido, tuna haduwar su ta karashe.

"Sannun ku da zuwa."
Ta fada tana komawa jikin Ummu.

"Kai Anty kinga yadda kika kara gaske da kyau. Ga lallan ya kara gaska ki."

"Muga Gyaran kan naki."

"A'ah! Bari"
"Kai Anty."

"Ke gani a daki "
"Toh!"

Sallamar su Hauwa muka jiyo.

Ita da Ya Nura ne. Cikin ta ya kara fitowa.

Ni dai ina jikin *Ummu nah*
bayan an gaigaisa ne sai ga Momy na.

"A'ah Hafst yau gaki ga Ummun ki ko."

Kasa tai da kai tana murmushi.

Dady da Abbi ne suka sauko.

Duk kasa muka zame, kai na na saman cinyar Ummu.

Dady ne yai addu'a sannan kuma yake fada cewar gobe za'ai dinner bikin mu jibi na tare.

Wani sanyi ne ya ratsa Ya Haidar.

Bai san sanda ya Sauke ajiyar zuciya ba. Su Ya Kamal dake gefen sa suka kalle shi.

Ido ya kanne musu. Murmushi sukai.

Dga nan kuma suka wuce daining dan cin abincin dare.

Bayan an gama suka koma falo aka ci gaba da hira.

Abbi daki aka basa a kasan bene.

Sai Ummu da aka bata wani dakin Kusa da na Momy.

Sai mu dasu Faiza da Hauwa da tare itama anan zata zauna duk a dakin Momy muka kwana.

Sai su Ya Haidar da suka tafi boys quater.

Ranar kwana sukai ana hira daga baya kowa mijin sa ya kira sa.

Ganin haka yasa na mike na bar musu dakin.

Wajen Ummu naje muna hira har tai bacci.

Kwanciya tayi sai ga karar wayar Momy dake Wajen.

Ya Haidar ne. Dauka tayi, sallama yayi. Ta amsa.

Shiru sukai.
"Baby nah" ya katse shiru."
"Na'am!"

"Baby na jibi tare zamu kwana."
Ya Haidar."

"Na'am!"
"Ka bari."

"Me?"
"Zumudi."

"Saboda me." "kawai."

"Shikenan haka waccan karon ma kika ce. Allah yasa lafiya."

"Ameen!"
"Baby na jeki bacci to."

Ciwon mara ne ya tada ita. Daga baccin da take.

Cikin kayan ta taje ta dauko magani tasha. Shine yasa ta samu sauki.

Da asuba ta tashi tai wanka ta gyara jikin ta.





*INDABAWA*
[11/20, 1:14 AM] Antty😍: *MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY






BY *Maryam S Indabawa*
*MANS*




🌐HAJOW📝🌐

👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧 *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* ✍🏾✍🏾✍🏾





Page *64*





Da safe lafiya na tashi sai dai dan ciwon da baza a rasa ba.

Kwata kwata ban ga Ya Haidar ba.
Karfe Hudu bayan nai sallah aka zo akai min kwalliya.

Ba a cikin fuska da tarkace ba sai dai an min jagira da su foundation jan baki sai massacara da aka saka min ta raka fiton da tsayin gashin ido na.

Sosai nai kyau, maroon jan bakin da na saka ya kara fiton da kyan lebe na yayi kyau dashi kamar an dasa.

Kitso nasa akai min kanana wanda ya zubo min har gadon baya. Ribon nasaka masa

Wani dankararen Leshi Momy ta kawon. Golden colour ne adon ruwan hoda a jikin sa. Takalmi da jaka duk golden ne. Sai dankunnen gold da sarka da abin hannu da duk ta kawon.

Dikin doguwar riga ce. Wacce ta zaune a jikina. Yayi min kyau sosai.

Su Faiza kallona suka tsaya yi dan ba karamin kyau nayi ba. Ga wasu turaruka da ta bani masu kamshi da sanyi. Sai tashin kamshi nake.

Mangariba nayi aka fara dibar su Faiza da Khadija da Hauwa.

Gidan ya rage daga ni sai su Ummu. Ina daki a zaune. naji an bude kofa.

Shine ya shigo kallo na ya tsaya yi.
Sanye yake da golden din shadda dinkin yar ciki da babbar riga. Sai hula da takalmi suma duk haka. Sai agogon golden color shima.

Dakin tuni ya dumame da kamshin turaren sa. Yafi minti biyar tsaye yakasa dauke idon sa akai na.

A hankali ya karaso inds nake, hannuna ya kamo, ya mikar dani.

"Ina yini Ya Haidar!"
Bai amsa ba sai kallo na da yake. Kaina na dukar kasa.

"Baby na kinga yadda kika koma kuwa. Kinyi kyau wallahi. Ke kullum ma dada kyau kike karayi."
Murmushi kawai Hafsat tayi.

Jikin sa ya jawo ta ya rumgume ta tsam. Dan rumgumar tata shi zai dan sa ya samu sasauci.

Momy ce ta bude dakin. Da sallama ta shigo da sauri na janye jikina daga nashi.

Kai ta girgiza kawai tace,
"Ku fito ana jiranku fa."

Shi ya amsa da toh muka fita. Hannun sa rike da nawa.

A wata sabuwar mota aka kai mu. Motar golding colour ce sai kwalli take.

Wajen ya hadu sosai. Manyan mutane sun halarta.
anyi mana nasiha sosai sannan aka ci aka koshi.

Kyaututuka dayawa na samu daga wajen abokan Ya Haidar dana Dady banda 'yan uwan Dady suna kuwa yazo sai da ya bude jakata ya saka min.

Karfe tara su Ummu suka yafi gida ya rage daga mu sai abokan Ya Haidar.

Kida aka saka inda akasha rawa. Ni dai banyi ba inda daga tsaye amman su Khadija an dage sai rawa ake sha.

Anyi liki sosai inda karfe sha daya aka tashi gaba daya.

Motar da muka zo ita muka koma a ita bayan kowa ya bar wajen. Hannuna rike da nashi kamar za'a kwace masa ni.

Muna zuwa gida shi ya rakani har dakin Ummu sannan ya juya. Wanka nayi na zo na kwanta gefen *Ummunah.*

Washe gari Ummu taso su tafi amman Momy tace su bari akai ni mana. Da kyar ta yadda.

Ina kwance a daki Momy ta shigo rike da wani kofi a hannun ta.

Wani hadin ne a cikin kofin. Dan danawa nayi naji akwai saki gashi sai kamshin kayan kamshi yake. Sai dayan kuma hadin wani abune da madara.

Haka tasa na shaye su. Sannan ta dauko wani hadin turaruka ta bani da wani dan karami tace na shafa shi akowacce gaba ya jikina na.

Na karba, nai mata godiya.

Su Hauwa ne suka shigo ita da Faiza.

Gefena suka zauna,
"Amaryan yayan mu."

Murmushi kawai Hafsat tayi,
"Wai ya naga bakin ki ya qara mutuwa ne."

"Nima dai haka nagani." Inji Faiza.

"Dallah ki kwantar da hankalin ba wata wahala fa." Hauwa ta fada da zolaya.

"Ah toh fada mata dai. Wahalar ta dan lokaci ce zata wuce."

"Yau zaki zama cikakiyar mace kamar mu."

"Wai me yasa kuke yan iskane. To ni ba abinda zai faru."
Dariya suka sheke da ita.

"Hafsat kenan."
Hararra su tayi.

"Dan Allah ku rabu dani inji da abindan ke damuna."
"Haba Sis sai mu barki da damuwa. Kinsan dai damuwar mu taki ce."
"Daure ki fada mana. Kinji."

"Uhmm ni kai na bansan takamaimai me yake damuna ba. Amman dai naji sai faduwar gaba nake."

"Ayyah sannu ai wannan normal ne ba wata matsala."
"Gaskiya kam fargaba ce."

"Kina addu'a a ranki."
"Sabuwar rayuwa zaki shiga. Allah yasa ki shiga a sa'a kema nan da wata tara musha suna."

"Faiza kefa muguwa ce. Ai taci amarcin ta dai ko?"
"Amarci banda wanda suka ci."

Tsaki Hafsat tayi ta juya musu baya.
Dariya sukai suka cigaba da hirar su.






*INDABAWA*
[11/20, 1:14 AM] Antty😍: *MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY



BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*





🌐HAJOW📝🌐

👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧 HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾


PAGE *65*




Daga haka bacci ne ya dauke ta. Sai bayan la'asar ta tashi.

Ummu ta gani zaune,
"kin tashi."
"Eh."

Khairat ce ta shigo,
"Taty kin tashi."

Ta fada tana zama a kusa dani.
"Eh Khairat.  Ya makaranta."
"Lafiya muna ta karatu."

"Yauwah Baby na a kuma dagewa."
"Me kike so?"

"Ni so nake mu koma makkah garin da dadi."
"To shikenan in anyi hutu kisa Ummu ta kai ki."

"Kefa Taty?"
"Zamu hadu acan insha Allahu."

"Taty wai kin dawo nan da zama."
"Eh!"

"Nima Momy tace, dauke ni zatai."
"Ai kam da naji dadi."

Murmushi Momy tayi dan Hafst da Khairat in suna tare sai ka sha dariya dan Hafsat biye mata take su sha hira.

Ba da wanda Hafsat tafi hira kamar khairat daga ita sai ummu da Khadija sai kuma kawayen ta.

"Taty dazu mukaje gidan ki."
"Haba?"

"Allah dani da Ummu da Momy dasu Khdija. Yaya Khadija ma na can muka barta."

Ummu, Hafsat ta kalla.
Ummu ce tace,
"Eh munje gida yayi kyau sai dai fatan zama lafiya da samun zuri'a ta gari."

Kasa Hafsat tayi da kai.
Momy ce ta shigo,
"au kin tashi."

"Eh! Momy."
Fita tayi sai gata nan da filet kasashen nama ne wanda yaji tumatur a ciki. Sai kunun aya da yasha madara.

Dire mata tayi a gaban ta.
"Sauko kici."

Saukowa tayi ta fara ci. Ita da khairat.

Ban daki ta shige ta hada mata ruwan wanka. Da ya sha hadin turarukan wanka wanda har sun kama jikin Hafsat.

Tana gama ci Momy tace taje tayi wanka.

Kayan ta ta cire ta shiga bandakin ta dade tana cuda jikin ta sannan ta fito.

Mai ta shafa da hadin turarukan da Momy Ta bata.

Momy ce ta shigo tare da wata yarinya.

"Yi mata simple makeup." To tace
Kwalliya tai mata me kyau wacce ta kara fito da kyan ta.

Wata Atampa Momy ta shigo da ita a hannun ta da takalmi da mayafi.

Ruwan goro ce wacce akai mata adon da dark green.

Dinkin riga da zani rapper ne. Rigar an mata dinki me kyau wacce aka bi partern din atamfar akai mata ado da stone dark green.

Sai mayafi da bata wani dark green kai bakace mayafi bane dan ya hadu. Takalmin ta ma kalar mayafin ne.

Sai dankunne da sarka da ta saka mata na azurfa wanda akai musu ado da dark green din stone.

Wani turare tazo ta bade ta dashi. Take ta kara bada wani kamshin me sanyi.

Momy ce ta kama hannun ta,
"Hafsat kibi mijin ki, ki zama mai gaskiya, ki rike addinin ki da muhimmanci, ki baiwa ya'yan ku kula da tarbiyya ta addinin musulunci.
nasan kina da tsafta. Kiji tsoron Allah a kowacce hanya kika tsinci kanki.
kiso Allah da mazan sa fiye da kowa, ki daura ya'yan ki a akan son Annabi,
ki zama mai yiwa mai gidan ki addu'a ta alkhairi."

Kuka Hafsat ta saka. Lallashin ta Momy ta fara.
"Haba Hafsat mene na kukan. Ki daina ke da zakije wajen Yayan ki kuma Mijin ki. Nasan Haidar na son ki kuma zai rike ki amana insha Allahu, kar kisa damuwa aranki. Muna tare duk abinda kije da bukata ki fada min. Ba tin yau ba na fada miki ni Mahaifiyar kice ba Sirikar ki ba dan haka ki sake kina fadan abinda kike bukata.
Ga Khairat nan ma zan dauko mana ita kinga ai baki da matsala kuma zan na sa shi yana kai ki gun *Ummun ki.*
ki daina kuka kinji."

Kai ta daga alamar "toh"

"Kin san dai aure sunnah ce, haka nan. Manxon Allah (SAW) yace, Aure sunnah tace. Duk wanda yayi shi tamkar ya sami cikar rabin addininsa ne!"

Haka kuma Abu Ayyuba ya rawaito cewa, Manxon Allah (SAW) yace, Abubuwa biyar suna cikin sunnonin Manzanni, yawan kunya, da yawan sa turare da goge hakora da kuma yin aure."
a takaice aure hanya ce ta tara zuri'ah ta gari ingantacciyar Alumma. Aure ne kan haifar da sahihiyar rayuwa da samar da tarbiyyar tan cikar alumma.
Aure ne kan samar da dangi da iyali da kabila.
Aure ibada ce babba mai mutukar mahimmanci a rayuwa.

Jikin ta Momy ta jata tana lallashi har ta daina zubar da hawayen.

Su Hauwa ne suka shigo su suka cigaba da lallashin Ta.
"Haba Hafsat bakya ganin in Ummu ta ganki zaki tada mata hankali, kiyi Hakuri ki daina kinji."

Kai ta daga musu.

Kamata Ummu  tayi ta kai ta gaban *Ummun ta.*.





*INDABAWA*

Continue Reading

You'll Also Like

4K 108 1
Hatsabibiya ce,wadda bata barin kota kwana,ta yi ƙiriniya iya iyawarta.
20.5K 754 40
Top ranking #1 Kim yoojung #2Jungkooklove #2Don'tleaveme Completed story This story is about three people Ahn ha na Kim Taehyung Jeon jungkook Thi...
18.6K 1K 11
Tabbas akwai ciwo a rayuwar da baka san karshenta ba, akwai tsoro a mafarkin da ka gagara farkawa! Ta ina lamarin ya fara? Ina tsakiyarsa da karshe...
3.2K 168 11
Labari Rayuwar Abra da Mahaifinta.