Mijin Ummu nah

By MSIndabawa

18.1K 810 12

Labari akan wata yarinya Hafsat wacce mahaifin su ya rasu mahaimahaifiyar sy ta sake aure in da ta auri mugun... More

1-5
6-10
11-15
16-20
21-25
26-30
31-35
41-45
46-50
51-55
56-60
61-65
66-70
71-75 End

36-40

719 45 0
By MSIndabawa

[11/20, 12:59 AM] Antty😍: *MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY

BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*



?? *HAJOW* ????

??‍??‍????‍??‍????‍??‍?? *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* ✍??✍??✍??



Page *36*

Dis page is for My group members *INA MATA?*
Ina son ku kamar yadda kuke sona. Kuke son labarin nan. Kuna sani farin ciki sosai nagode

Washe gari, muna zaune ni da Ummu.

Ummu ce ta dubeni,
"Hafsat mene tsakanin ki da Aliyu ne?"

Kasa tayi da kanta cikin girnamawa da nutsuwa ta fara magana.

"Ummu, daman so na yake, kuma jiya ma yayi min maganar yana son ya turo maganar aure."

"Masha Allah! Allah nagode maka, na dade ina addu'a Allah ya baki miji na gari, wanda zai rike ki ya kawar miki da maraicin ki, sai gashi Allah ya hadaki da Aliyu.
tabbas Aliyu yaron kirki ne, wanda ko wacce uwa zata yiwa yar ta sha'awar auren sa! Masha Allah!
Allah tabbatar da alheri, zanje na fadawa kakan ku dan can za su je."

"Toh Ummu. Nagode."
"Amman shine kuka rufeni ko?"

Shiri Hafsat tayi,
"Haba ni dai naga yana ta zaryar."

Wayar Hafsat tayi kara, tana dubawa taga Ya Haidar ne.

Kin dauka tayi,
"Dauki wayar ki, bari na shiga daki zan gyara durowa ta."
Ta fada tana fita daga dakin.

Dauka tayi,
"Baby na! Kina lafiya."
"Lafiya lou."

"Masha Allah! Kinyi wa Ummu maganar."
"Eh na mata gobe zataje wajen ganny ma."

"Ok nina dole, na juya na tafi. Dan naje na fada musu ko?"
Shiru tayi.

"Shikenan nan da jibi zan tafi gobe a wajen ki zan yini. Zan zo Anjima ki rakani wajen Baba Ado."
"Allah kai mu."

Mukai sallama.

Dakin Ummu na tafi na tayata gyaran kayan da aka kawo mata daga guga.

Nasiha take mun ba akan komai ba sai akan aure da zaman duniya.

"Ki kula da mijin ki. Addinin ki da tafta, ki kasan ce me son kamshi duk da nasan baki da matsala ta nan.
Kar ki bari mijin ki ya shaki wani abu a gare ki in ba kamshi ba."

Shiru tayi,
"Ki zama mace ta gari wacce mijin ta zai kalle ta yai farin ciki da alfahari."

"Ba wacce zai kalla yaji ransa ya baci ba. Ki kasan ce mai taya mijin ki da a addu'a a dukkan alamuran da yasaka a gaba.
Ki zamo mai taya shi farin ciki in abun farin cikin ne ya samu haka nan in na bakin ciki ne ki taya shi jajan tawa.
Kina lura da abunda mijin ki ke so da wanda baya so. Da wadan da za suna daukar hankalin sa."

Shiru tayi tana kallon yar tata. Tana son Hafsat ko dan ladabin ta da biyayya. Ga shi ita ta dauko kamar mahaifin ta.
"In har kika rike wadan nan bake ba bacin rai a gidan ki sai dai wanda baza a rasa ba. Amman zaki na ganin budi da walwala ko da kyautata masa da kike.
Allah baki zuri'a mai albarka wadan da zasu miki biyayya kamar yadda kike min."

"Ameen *Ummu nah* Yauwah wai zan raka shi gidan Baba Ado," ta fada kanta a kasa.
"Bakomai. Amman ki kula da kanki."

"Insha Allahu Mami."

Ko da Ya Haidar yazo da addu'ar da yayo mana a cikin ruwan ya taho dashi. A galan yace na kwana bakwai ne. Kowa da nashi.
Ummu da Ni da Khadija,

Sai bayanin yadda zan nayi in zan kara yi a cikin takarda.

" *Ki samu ganyen magarya guda bakwai.*
*Danye ko busashe, sai ki dake shi ya daku. A zuba a cikin a ruwa mai kyau da za'a iya sha kuma ai wanka dashi.*

Sai ki karanta wadan nan surorin
*Suratul Fatiha. Kafa daya.*
*Ayatul kursiyu cikin suratil Bakara aya ta 255.*
*Suratul A'araf (Surata 7) daga aya ta 106-122*
*Suratul Yunus (Surata 10) daga aya ta 79-82.*
*Suratul Kafirun*
*" Fataki 3*
*" Nas 3*
*Allahumma rabi nas hayizil bil ba'asa wa shifa'i Antal shafi la shifa'a illa shafiuk shifa'al layi gadirul shakam ×3*

*Bismillahi Aurtika min kulli sha'in yutila wa min sharri kulli nafsi Allahu yashfika Bismillahi Aurtika ×3*

"In zaki karanta kina yi nufashin ki na shiga cikin ruwan ana sha sau biyu da safe dare.
ana wanka dashi a waje mai tsarki ko ki nemi towel ya jiku kina game jikin ki da shima
Insha Allau akai sati anayi kowane irin sihiri akai wa mutun zai warware. In ba ai maka ba zai kare ka, yana da kyau munayi ko dan tsarin jikin mu.
Ba sai anje wajen wani malami ba insha Allah kai wannan ya isar.

Sai yamma muka dawo gida, lokacin Ummu ta ba ta nan ashe gidan Kakan ni na ta tafi.

Muna dawowa ya tafi gida, dan hade kayan sa.

Washe gari tare muka yini duk da ni ba wata hira muke ba. muna zaune har Ummu daga baya ta bar wajen.

Anan nake fada masa dagin Abbi na sunce inya shirya a sanar dasu ranar da zasu zo. Sosai Ya Haidar yayi Murna. Sai dare ya tafi bayan yace gobe kafin ya tafi zai biyo.

*INDABAWA*
[11/20, 12:59 AM] Antty😍: *MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY

BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*



?? *HAJOW* ????

??‍??‍????‍??‍????‍??‍?? *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* ✍??✍??✍??



Page *37*

A dare na masa cake da meatpie ma soya kaji na nade masa su a leda nasaka a jaka.

Washe gari da safe bayan na gama duk abinda nake gudanar wa.
nai wanka na shirya cikin doguwar rigar atamfa.

Yellow da brown. Banyi kwalliya ba sai dan nayi kyau. Turare na feshe jikina dashi.

Ina zaune sai gasu Ya Haidar da Ya kamal har da Faiza.

Sanye yake da dagon wando baki sai brown riga mai dogon hannu. Sosai yai kyau sai tashin kamshi yake.

Bakin takalmi ne a kafar sa sai agogon azurfa da ya saka.

Bayan sunyi sallama da Ummu, Ya Kamal yace inzo in karasu airport.

Brown mayafi nasaka da takalmi. Shi dai Ya Haidar ba abinda yake sai bina da kallo da yake.

A mota Faiza da Ya kamal ne a gaba, Ni da Ya Haidar a baya.

Muna isa su Faiza suka fita. Ya rage dagani sai Ya Haidar.

Hannuna ya kamo, ya kalle ni.
"Baby na zan tafi amman ki sani dawowa ta sai na shirye shiryen bikin mu. Ina son ki kular min da kanki. Ki sani ni me son kine na har abada.
Zan tafi dake a cikin zuciya ba kuma abinda zai baci na dangane da son ki. Zaki kasan ce kullum kece wacce zan na tunawa dake."

Kallo na ya cigaba dayi, kaina na kasa
"Me Zaki bani da zan na kallon sa in farin ciki."

Wata azurfa ce a hannuna. Guda biyu da ta wajen Abbi na da wacce na siya.

Wacce na siya na mika masa. Bai karba ba sai mikon da zara zarar yatsun hannun sa yayi.

"Saka min." Ya fada bayan ya mikon hannun.

Zura masa nayi, sosai yai masa kyau a hannun. Sumbatar zuben yayi.

Hannu ya zira a aljihu ya zaro wani karamin akwati a aljihun sa.

Budewa yayi wani zuben gold ne a ciki. Hannu na ya kamo, ya zura min.
Sosai yai mata kyau ya kara fito da hasken hannun na.

Sumbatr hannun ta yayi,
Sannan ya jawo ta jikin sa ya rumgume ta. Kasa janye jikin ta tayi.

Fuskar ta ya tallafo ya dawo. Idon ta ya kawo ruwa. Kallon juna suka na minti na sannan tai kasa da kanta.

Kanta ya kuma dagowa ya matso da fuskar sa. Gane abinda zai yi yasa na dukar da kai na.

Murmushi yayi ya kara rumgume ta, janye jikina nayi.
"Har Ga Allah ban son barin ki sai dan dole,"

Kallon sa nayi, sai nayi tausayin sa dan idon sa yayi jawur dashi.

Nima jinai zuciya na zaffi. Kamar na fashe da kuka.
"Kayi hakuri insha Allahu, nan da wani lokacin muna tare."
"Allah yasa. Allah nuna min wannan lokacin."

"Ameen."
Bude kofar yayi, muka fita rike da hannuna. Cikin dabara na zare hannuna. Har muka karasa gefen su Faiza,

Sai da mukaji an fara kiran suna sannan muka mike. Sai a lokacin naji kewar sa.

Dan bansan lokacin da hawaye ya fara zubon ba yana ganin haka ya dawo.

"Haba Baby ya kuma kuka. Kina son hankalina ya tashi ne, kiyi hakuri mun kusa kasancewa tare har karshen rayuwar mu insha Allah."

Ya jawo ni jinkinsa yana lallashi yana bubuga bayana. kara shigewa nayi jikin sa ina cigaba da kukan.

Shima idon sa yayi jawur, ganin nayi shiru yasa yakira Faiza da Hannu ta karaso ya mika mata ni.

Wajen Ya kamal ya isa ya rumgumeshi, dai dai karasowar su Hauwa kenan.

Hauwa ta karaso wajen mu tana dariya kasa kasa, Ya Nura kuma wajen su Ya haidar yaje ya rumgume shi.

"Kamal ga amana ta nan ka kular min da ita kar ka barta tayi kukan komai. In abin ya fi karfin ka ka sanar min. Ka kular min da ita."
"Kar ka damu kasan yadda muke da Hafsat ai baka da matsala."

Rumgume juna suka kara yi. Sannan ya koma wajen su Hafsat.

Da gudu ta karasa jikin sa ta rumgume shi.

Wajen su Faiza ya karasa da ita,
"Faiza ke zan bawa amanar ta dan wani satin su Hauwa zasu taho."
"Kar ka damu ya Haidar."

Dai dai kunnen ta ya kai bakin sa, rada yai mata. Sannan ya sake ta.

Murmushi tayi, shima haka. Ta juya ya tafi yana murmushi.

Yana dago musu hannu.

*INDABAWA*
[11/20, 1:00 AM] Antty😍: *MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY

BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*



?? *HAJOW* ????

??‍??‍????‍??‍????‍??‍?? *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* ✍??✍??✍??



Page *38*

Dedicated to my daugthers.
yara na manyan gobe ina son ku ina kaunar ku Allah barmu tare.
*FADIMATU, HALEEMATU, AMINATU,(MEENAL) mamana ta kaina.*

So love u yarana.


Sai da muka ga tashin su sannan muka tafi.

Gidan Faiza muka tafi, dan ya Kamal yaki kaini gida. muna zuwa ban san lokacin da bacci ya dauke ni ba.

Suna sauka ya kira bata dauka ba. Text yayi mata

Sannan ya kira Ya Kamal yace ai bacci ne ya dauke ta.



Drivern sa ne yazo ya dauke shi.

Wani gida mai girma da kyau ya isa dashi.

Gida ne wanda da ka kalle shi kasan an kashe kudi dan sai ka dauka zane ne.

Driver na ajiye shi ya fita ya fara gaisawa da masu aiki. Suna masa barka da zuwa.

Da fara'a yake gaisawa dasu cikin sakin jiki.

fulawoyi ne cike da harabar gidan.
Wani korido ya mika ya shiga. Ta sada shi da kofa.

Babban falo ya shiga. Ya kara shiga wata kofa wani falon ya kara shiga.

Da sallama ya shiga. Momy ce take saukowa daga bene.

Da gudu ya nufe ta ya rumgumeta da murna kamar ta mai dashi ciki ta tarbe shi.

Sai zuba shagwaba yake ke kace ba Ya Haidar bane sai kice karamin yaro ne.

Daga yace wancan sai yace wancan. Momyn sa kuma sai biye masa take.

Da kyar ta kaishi dakin sa dan yayi wanka. Daki ne mai girman gaske da aka zuba masa kayan more rayuwa.

Komai na dakin ruwan omo ne da farii.
Ban daki ya shiga yayo Wanka sannan ya shirya cikin wando threequater. abinda Hafsat ta bashi ya dauko ya sauko falo.

Ya zube shi a faranti. Momy tace,

"Wannan fa?"
"Wallahi yar ki ce tayo maana."

"Allah sarki Hafsat Allah mata albarka ameen."
"Ameen!" Shima yace.

Suka zauna suna ci. Wayar sa ta dauka taga hoton Hafsat akan screen din.

Murnushi kawai tayi.

Sai bayan la'asar ta tashi daga bacci wanka tayi, tayo alwala sannan tai sallah.

Wayar ta ta jawo, kiran ya Haidar ta gani. Da sauri tabi kiran nasa

"Assalamu alaikum!" Ta fada cikin sanyin Murya.
"Wa'aikum salam!"

"Ya hanya kun sauka lafiya."
"Lafiya lau Baby nah."

"Wasu Maman na."
"Tana lafiya. Kin tashi kenan."

"Eh""
"Masha Allah!"

Daga nan yadan ja ta da hira sannan sukai sallama

Falo ta fita ta tadda Faiza ce kadai. Dainning tayi dan cin abinci.

Kadan taci ta dawo suka zauna hira.

Faiza na tsokanar ta,
"Amaryan yayanmu. Yanzu ashe asan dadin soyayya."

Hararar ta Hafst kawai tayi.
Dariya tayi. Tace,
"Wallahi Hafsat dama ki dawo nan ko dan makarantar ki."

Harararta ta kuma yi.
"Wallahi Ya Haidar ya gamu da harara."
"Ina ruwan ki."

"Da ruwa na ai dole na tausaya masa."
"Sai kiyi tayi."

"Ya zancen dawowar taki."
"Allah sauwake min na dawo ko kunya ma bakiji ba. Wai na dawo gidan kawata da zama saboda makaranta. Ai ko ba a garin Nake ba gara nayi zaman hostel dan kiji. Ina tunanin ki yaje yawo ne?"

"Daga magana Sis."
"Ina jin kin manta wace Hafsat ne ko?"

Ta fada tana daukar wayar ta dan kiran Ya Kamal.

Yana dagawa tace yazo ya maidata gida.

Sai dare Ya Kamal ya tafi kaita duk da haushin Faiza duk da Faiza ta bata hakkuri amman sam ta shareta.

Sai da yakai ta tayo shopping sannan ya kaita gida.


Haidar ne zaune gefen momyn sa.
"Wai baki fadawa Dady yau zan dawo bane?"
"Kai ma kasan yana sane da kai. Aiki ne yai masa yawa kaje ka zauna sai shi yake ta fama."

"Allah sarki Dady na. Ai gashi yanzu na dawo sai ya zauna ya huta."
Murmushi kawai Momy tayi

Sai karfe tara Dady ya dawo. Da murna shima ya tari dan nasa.

Sai da suka ci abinci suka zauna hira sannan suka wuce kowa ya kwanta.





*INDABAWA*
[11/20, 1:01 AM] Antty😍: *MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY

BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*



?? *HAJOW* ????

??‍??‍????‍??‍????‍??‍?? *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* ✍??✍??✍??



Page *39*

My sister never forget wit u. *FATIMA (MIMI), SAFIYYA (NANA), AISHA (HUMAIRA), HAFSAT (SADDIKA).*
Ina son ku. Kune farin ciki na yan uwa na masi sona da kaunata. Nima ina son ku.

Allah bar mu tare ya daurar da zumuncin mu Ameen.



Washe gari da safe ya shirya cikin kananun kaya. Brown wando ya sakaa sai brown riga mai adon baki.

Sosai yai kyau sai tashin kamshi yake. Falo ya sauko. A daining ya hago su Dadyn sa.

Wajen su ya karasa ya durkusa ya gaida Mami sannan Dady.

Daining suka nufa shi ya zuba musu abincin nasu sannan ya zauna.

Bayan sun gama ya mike yace zai tafi,

Dady yace,
"Yau baza ka jirani bane son."
"A'ah Dady ka dan huta ka fito anjima. In ma yau zakai zaman kanee ka zauna ai na dawo, mene na fitar ka."

"Son kenan Allah maka albarka ya baka mace ta gari tare da yaya masu albarka."
"Ameen!"

Ya juya yai sama.

Bayan ya sauko yace,
"Dady in na dawo zamuyi magana."
"Allah dawo da kai lafiya."

"Ameen!"
Ya fada yana fita.

Drivern sa ya taso da sauri ya dauke shi sai company dady sa

Tun daga bakin gate ake masa sannu da zuwa.

Dan Ya Haidar mutum ne mai son mutane, ga kyauta.

Sai da ya shishiga ya gaida ma'aikatan office din sannan ya shiga office din Dady sa.

File ya dauko wanda duk abinda ya gudana a kamfanin aka rubuta ya dauko dan ganin daga ina zai soma.

Office dinshi ya shiga wanda kai baka ce office bane dan haduwar shi da tsaruwar sa.

Zama yayi. Sannan ya zaro wayar sa.

Kan allon wayar ya tsaya kalla. Murmushi yake in ya tuna lokacin da ya dauke ta hoton.

Number ta ya kira.
Assalamu alaikum." Ta fada cikin muryar ta mai zaki.
"Wa'alaikum salam Baby na kin tashi lafiya."

"Lafiya lou gamu a makaranta ma."
"Masha Allah to Allah tai maka."

"Ameen!"
"Wallahi Baby nah ina missing naki."

"Nima haka."
"Dan Allah da gaske."

"Eh."
"Ina son ki kar ki taba mantawa da haka."

"Hmmm!'
"Eh! Bari na barki sai anjima."

"To sai anjima." Ta fada tana kashe wayar.

Aikin sa ya cigaba da gudanar wa. Sai azahar ya samu ya kammala sannan ya fita yin sallah.

Yana idar wa ya koma office. yaci soyar da Hafsat tai masa. Sannan ya koma kan wani aikin sai la'asar ya tashi.

Bashi ya karasa gida ba sai karfe biyar duk Ya gaji.

Dakin sa ya wuce yai wanka ya saka kayan shan iska.

Wayar sa ya dauko ya tura mata sako sannan ya fito yayi dakin Momy.

Zaune Momy take rike da waya a hannun ta.
"Momy na."
"Na'am Haidar."

"Na dawo yau na gaji,"
"Ayyah sannu,"

"Tashi muje kaci abinci." Ta fada tana mikewa. Bayan ta yabi.

Ita ta zuba masa. Sannan ta tura masa. Kadan yaci. Yace,
"Momy ina Dady ne?"
"Ya fita amman yanzu yace zai dawo."

"Ok Allah dawo dashi lafiya Ameen"
"Ameen."

Daga haka kuma sai hirar Kano duk magana sai yayi ta Hafsat. Komai Hafsat

Momy, tace, "wai mene tsakanin ka da Hafsat ne?"
sosa kyeya yayi, yace,
"Sirikar ki ce."

"Da gaske ko da wasa." Ta fada tana murmushi.
"Wallahi Momy ba zancen wasa ba."

"To Allah sanya albarka a tsakanin ku."
"Ameen! Daman maganar da zanyiwa Dady kenan."

"Ok."
"Dan har Ummu ta sanar wa da Kakan su."

"Allah sarki. Allah ya shiwa Ummu albarka amman kuma kaga yanxu muka gama waya bata fada min ba. Ka iya zabe Haidar dan Yarinya ce mai hankali da nutsuwa Allah barku tare."
"Ameen."

Sallah magariba ita ta tada su.

A masallacin kusa da gidan yaje yayi sallah.

bai dawi ba sai bayan isha'i.

Yana shigowa ya tadda Momy a falo kallo suka fara.

Sallamar Dady suka jiyo, tare suka amsa masa ya shigo ya zauna


*INDABAWA*
[11/20, 1:02 AM] Antty😍: *MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY

BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*



?? *HAJOW* ????

??‍??‍????‍??‍????‍??‍?? *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* ✍??✍??✍??



Page *40*

Dis page is ur *UMMU WALEED*

Nagode da son labrin nn da kike.



Haidar ne ya mike ya karbo ledan hannun sa.

Sai da yayi masa sannu da zuwa sannan Dady yace yaje ya dauko faranti da kofina.

Ledan ya bude, kajine a ciki gasasu, sai hadin dankali.

Kitchen ya shiga ya dauko, faranti sannan ya dauko, Lemo a firij.

Shi ya zuzuba masu sannan suka zauna akasa suka ci suka koshi.

Momy ce tayi sama ya rage daga Dady sai Haidar.

"Dady maganar da nace zan maka ce."
"Eh ina ji."

"Dady daman zancen aure na ne."
"Alhamdulilah yanzu, ka shirga kenan ko."

Kai ya sosa,
"Wallahi Dady! Har mun gama magana. mu kawai suke jira."
"Masha Allah. Wace yarinya ce?"

"Dady Hafsat ce yar gidan Ummu."
"Oh Hafsat yar gidan Antyn ka. Masha Allah. Allah tabbatar da alheri."

"Ameen!"
"To yanzu yaushe kake son ayi bikin."

"Dady ni ko nan da sati ne."
Murmushi Dady yayi.
"Ba tana karatu ba."

"Eh sauran wata uku ta gama."
"To masha Allah ai bikin ayi nan da wata biyar ko."

"Dady wata miyar yayi yawa nan dai da wata uku ko hudu."
"To shikenan zan fada wa Yaya Ibrahim sai aje a gama komai Ko?"

"Eh Dady na gode Allah kara girma."
"Ameen! Ko kai fa kannen ka duk sunyi aure sun barka."

"Nima gashi ya taho ai."
"Allah ya sanya albarka yasa ayi damu."

"Ameen dady."

Momy ce ta sakko. Haidar ya mike ya bar musu wajen.

Dakin sa ya shiga ya kira hafsat
hira soyayya yai ta jan ta da ita tin tana nokewa har ta dan sake.


Tinda Ummu ta fara shan tofin take jin dadin jikin ta, dan wani lokacin sai kaga tana ta gumi ita kadai kafin sati kuwa duk ta daina jin wasu abubuwan da takeji.

Su Hauwa sun koma dan wannan karan ma sai da muka sha kuka.

Ya Haidar kuwa har sunje wajen kakanin mu, kakan mu tin kan suje ya sa aka bincika masa waye Haidar kowa aka tambaya bashi da matsala.

Wannan yasa suna zuwa aka gama komai dan a lokacin aka bada sadaki da komai inda nan da wata hudu bayan ta kamalla karatun ta za ayi biki.

Abbi kuwa yafi wata biyu baya gari sai yau ya dawo.

Ina daki ban dai gansa ba amman naji muryar sa.

Washe gari tin safe ya fita ashe can gidan yayar sa ya nufa dake kurna.

Abbi ne zaune shi da Shehu dan gidan Antyna sa.

"Shehu abinda nake so da kai shine kaje wajen yarinyar nan Hafsat kace kana son ta."

Ido Shehu ya zaro, sannan yace,
"Wacce Hafsan"
"Hafsat yar gidan Mariya."

"Hafsat yar gidan matar ka."
Dariya ya bushe da ita ta rainin hankali.

"Baba Umaru har yanzu baka daina shaye shaye bane ya kamata ace ka bar mu. Munayi ai."
"Kai ka nutsu zan ci mutuncin ka."

Dariya ya kuma shekewa da ita.
"Haba Baba Umar sai kace Ba shehiu ba zaka ce zaka ci mutunci na. Ni kuma in zauna ina kallon ka."

"Abin ya bani mamaki ne. Dan nasan ruwa ba sa'an kwando bane. Da zaka ce in tun kare yarinyar nan. Yanzu in naje wajen ta ko kallon arziki baza tai min ba. Kana ganin mutane kitki kintsatsu ma su ilimi ma ba kula su take ba."

"Kasan ko ni waye nayi kisa ga shaye shaye ga rashin ilini sannan kace naje wajen ta."

Dariya Abbi ya sheke da ita,
"Yaro man kaza kenan kamanta waye Umar roci kenan. Uwar tata ma a tafin hannuna take bare ita duk abinda nace tayi sai tayi min kuma ita yarinyar kasan akwai biyayya ga *Ummun* ta sai dai bata ce tayi ba. Na gama mata aikin da in dai nace abu kaza ne to babu canji. Kuma yanzu ma akwai aikin da zanyi akn su gaba daya."

Yayi shiru sannan yace,
"Kai kasan mene munufar hada kun ne."
"A'ah!"


*indabawa*

Continue Reading

You'll Also Like

29.5K 865 23
Labarin Yarinyar da ta tashi a tsakanin yayyenta maza, da suke shirye da aikata ko menene saboda ita, ba ta san tsoro ba, rashin ji ya kaita ga haɗuw...
105K 4.4K 30
Labari ne akan 'yan mata 3 wad'anda suka sha gwagwarmayar duniya suka ga bala'i a rayuwar su kala-kala, labarin ya gino ne akan makirci, yaudara, cin...
16.8K 1K 11
Tabbas akwai ciwo a rayuwar da baka san karshenta ba, akwai tsoro a mafarkin da ka gagara farkawa! Ta ina lamarin ya fara? Ina tsakiyarsa da karshe...
1K 99 30
i don't know if u know that i like u but here are my secret confessions that i often hide to not embarrass myself cause i'm too embarrassed to admit ...