Mijin Ummu nah

By MSIndabawa

18.1K 810 12

Labari akan wata yarinya Hafsat wacce mahaifin su ya rasu mahaimahaifiyar sy ta sake aure in da ta auri mugun... More

1-5
6-10
16-20
21-25
26-30
31-35
36-40
41-45
46-50
51-55
56-60
61-65
66-70
71-75 End

11-15

1.4K 59 1
By MSIndabawa

[11/20, 12:45 AM] Antty😍: MIJIN UMMU NAH
TRUE LIFE STORY
11

BY MARYAM S INDABAWA

Manzo Allah (SAW) yace duk wanda ya karanta qulhuwallahu Ahad kafa x10, Allah zai gina masa gida a gidan aljannah...
    

Khadija kuma da yake makarantar kwana take nan First Lady, sai anyi hutu take dawowa.

Abbi baya yawan zama a Kano, kullum yana Kaduna, sau yayi wata 2 ko 3 bai zo ba,

Kayan abinci kuwa sai dai Ummu ta siya, kullum tana cikin tashin hankali, na rashin kulawar Mijin ta, amman sai dai suyi ta tayatada addu'a.

Hafsat ba inda take zuwa daga makaranta sai gida, in kunga Hafsat awaje to Abbi ne ya dawo, shima gidan Ya Muktar kadai take zuwa dake bayan layin su, da matar sa Anty Bikki mai mutunci, tana son Hafsat, ko dan aikin da take tayata gashi Hafsat na burgeta. Au iowa ma Hafsat burge shi take dan a nutse taje ga hankali,

In ba can sai  gidan kakanin ta. In ko an bata mata rai to, tana kebe kan ta ne daga cikin jama'a dan kar zuciya tasa tayi abinda ba daidai ba. Wani lokacin ta kanje tyi karatu ko taje wajen shakatawa ta huta, duk da akwai makranta amman haka take tafiyar ta, su Hauwa kuwa ranar basa jin dadi., haka zasu dameta da waya.


Samari masu ji daa kansu, suke bibiyar Hafsat amman kallo basa isar ta, dan ma wasu naganin kwarjinin ta suna kasa tunkarar ta. Amman duk da haka suna takura ta.

Rashin son cin abincin Hafsat shi ya jawi mata Ulcer, wacce in ta tasar mata kamar zata mutu, amman duk da haka bata iya cin abinci mai yawa, ita dai rabu da ita da kayan zaki da sanyi, dan komai sai ta hada shi da suga take sha wanda kuma in wata yayu lokacin al'adar ta take shan wuya sosai, dan wani lokacin har a asibiti take kwanciya, dan fita take daga hayyacin ta sosai,
Ko tace ta daina da ta warke xata manta da tasha wata wahala, Ummu tayi ta mata fada, sai dai ta bata hakuri.

Ummu ganin Abbu na hanata bawa su Hafsat kudi, wannan yasa ta bude musu ma'ajiyar kudi a bakin duk mai buka yaje ya cira, ita ma duk wata take zuba musu kudi. Sosai su Hafsat suka ji dadi.



***************

Yanzu haka Khadija hutu tazo shima kuma a dai dai lokacin yazo gida shine fa ya addabe su, wanda kullum cikin hayaniyar sa.

Yau Asabar, da safe bayan mun tashi nagama komai, na shige daki dan bana son na hadu da Mijin Ummu nah, wanka nayi na shirya, sannan nayi falo, ina zaune Ummu ta shigo na gaidata,

Kayan kallo na kunna, na dauko wayata.
Ummu tace "har yanzu Khadija bata tashi ba ko," "Eh," kawai tace,

Cikin dakin ta shig, tace, "Khadija wai ke bakya gajiya da bacci ne, har karfe 11 kina fama.
Khadija tace, "Ummu ramuwar baccin makaranta fa nakeyi,"  ta tashi. Ta diro daga kan gadon, ta fada toilet tayo wanka,  ta gyara dakin.



Falo ta shigo ta sami Hafsat, tace, "Anty kin tashi ashe," kai kadai Hafsat ta kada mata,
Tace, "ina kwana," "lpy kin tashi lpy," "lpy Anty nah,"

Tea Ummu ta hado mana, sai gasashen bread da nagasa shi da kwai da kifin gwangwani, tean nasha nace na koshi, Ummu tace sai na cinye dan dole na dinga tusawa har da hawaye na.

Ummu kuwa na ta fada, wai shiyasa kullum nake a rame saboda rashin cin abinci na.

Bayan mun gama sai ga Khairat ta shigo, kai tsaye wajena tayo,  tace,
"Taty ina kwana,"
Nace, "lpy lou Baby na,"

Tace, "uhnm Taty Awawa zaki ban nasha,  ni bana son ta wajen Ummu taku nake so,"

Murmushi Hafsat tayi tace, "Baby na kin fiya shan zaki ko?"

Ummu tace, "ai ke kika koya mata,"

"Kai Ummu, Khadija shiga daki ki daukon jakar da na fita da ita jiya,"

Khadija ta shige dakin, ta kawo mata jakar, kwalin chocolate guda ta mikawa Khairat tace, "ai tasha gashi nan,"

Hannu biyu tasa ta amsa, tace, Taty a gode," ta fita da gudu, daya kwalin na dauko, na dauki daya na mikawa su Ummu, Ummu tace bata sha, ni da Khadija mukaa hau shan abar mu.

Ina zaune har sha biyun rana tayi zaman ya isheni, mikew nayi na dauki hijab nace, Ummu zanje gidan Ya Muktar, Ummu tace sau kin dawo ki gaidata da jiki.

Nan da na naje nakwankwasa gate tazo ta bude min, "Anty kece a gidan," ta fada tana min murmushi, nima murmushin na skr mata wanda ya kra min kyau, nace, "wallahii,"

Tayi dariya tce, "ki dai Abbi ya dawo," kallon ta nayi dan neman karin  bayani tace, "Eh man sau yana nan kike fitowa, in bayana nan daga makaranta shikenan,"

Murmushi kawai nayi, Anty Bilki tace, "wai gidn cizon ki yake yi ne, in yana nan,"

Kaina na kawar gefe nace,  "ni in yana gidan wallahi gidan baya min dadi sam,"
"Kina Hakuri, wataran sai labari kinji," nace, "shi muke fama yi ai,"
"Ina Khadija?"
"Kin san tana gidan su ai," na fada ina mai mikewa akan kujera. Ido na lumshe,

Murmushi Anty Bilki tayi, dan tasan dan ta rabu dani da magana ne yasa na rufe ido, badan ina jin bacci ko gajiya ba.

Kitchen ta nuf dan girki take yi, can sai ga sallamar Yaya Muktar nan shida abokin sa Murtala,

Mikewa nayi na amsa, sannan muka gaisa. Ya Muktar yace, "Anty yau kece a gidan namu,"
"Wallahi baban yaya," yace,  "ya makaranta," "Alhamdulilah," na bashi amsa.

Dayan dakin na nufa nayi kwanciya ta. Sai daya da rabi na mike. Bandakin dakin na shiga nayo alwala. Na fito nayi Sallah,

Ina sallah Anty Bilki ta shigo ta zauna sai da na iddr na shafa addu'a sannn tace, "taso muci abincu," bayan ta na bi, muka wuce dakin cin abinci.

Acan na samu su Ya Muktar suna cin abinci, kujerar gefen sa na jawo na zauna,

Fried rice na duba cokali daya, sai nama da nasaka da hadin cabeji, Ya Muktar ya kalle ni,  yace,  "haba Anty dan wannan abincin, sai kace wanda Khairat zata ci



MS Indabawa
[11/20, 12:46 AM] Antty😍: MIJIN UMMU NAH
TRUE LIFE STORY
12



BY MARYAM S INDABAWA
MANS

Manzon Allah (SAW)  yace duk wanda ya karanta suratul Kahfi, a ranar juma'a Allah zai cika masa hasken sa har zuwa wata juma'ar yana cikin haske da fariin ciki.

(Allah bamu ikon karantawa AMEEN)










Ya Muktar yace, "ai shiyasa kike kullum,  bakya gaba,"

Murmusho nayi kawai, dan na saba jin haka kowa sai yace, bana kiba. Ganin zai kara magaba ne, yasa nace, "bafa kyau ana cin abinci ana magana,"
"Haka ne fa," ya fada tare dayin shiru.

To abincin ma da na zuva da kyar na cinye shi, Anty Bilki dake kallo na tace, "ke dai Anty ina jin a duniya abinci ne ba kya son cin sa, da kayan zaki ne da yanzu kin zauna kina dan kara,"

Shiri nayi dan nasan yanzu zata iya sa Ya Muktar ya sa na dada abincin.

Sai da muka gama, mukayo falo,  Ya Muktar ya fita.

Robar Ice cream, Anty Bilko ta kawon, tace, "gafa abin,"

Na dago ina Murmush, nace, "Kai! Anty sai da na cika ciki na, amman anjima zan sha,"

"Anty dan Allah taimakan da Cingam mana, in rage ciki na,"

Daki tayi tana fadan sai kace wani abun kirki naci da zan rage cikin.

Kwallin orbit ta mikon, na karba na dauki daya, ci nake cikin yanga, dan ba kowa ne zai san ma ina tauna ba. Dan a duniya na tsani naga ana tauna ana Kas-Kas din nan har ciwon kai yake sani. Shiyasa ni ban fiya cin Cingam na duk da ina so, to ban son naje nayi ban sani ba.

(Yan Uwa dan Allah musan yadda zamu na taunar cingam, wani bai son kararsa, sannan duk wacce aka ganta akan titi tana tauna to yawanci daukar yan tasha ake musu, in dole sai anci, to aci a gida, amma wallahi.maza da yawa basa son ganin ana tauna akan hanya ko kuma ana yin kara dashi. In dan kamshin baki kike so to kiyi amfani da mouth fresh, ko alawa kina tsosa ba wanda ya sani, Allah mu gyara wallahi ba girman mu bane. In dabi'ar wani ce yayi hkri ban fada dan na bata masa ba sai da gyara.)

Anty Bilki ce ta kallen cikin sha'awa, tace, "wallahi Anty kina burge ni, komai naki a tsare,  sannan cikin yanga kike yi,"

"Kai Anty ni ina wata yanga da nake yi,"

"Allah komai naki tsav ga tsafta ga iya daukar wanka duk da kwalliya bata dame ki ba, ga bakya son surutu bare wani ya kawo miki gulmar wani, komai naki na birgeni, kalli cin cingam din ma kamar bakya taunar komai,"

Murmushi Hafsat kawai tayi. Anty Bilki ta cigaba da cewa,

"Allah mijin ki ya huta ba ruwan sa, in ilimi ne masha Allah dukka biyun Arabi da boko, gaki kyakyawa ga tsafta, hankal nutsuwa, ga rashin son hayaniyar ki. Allah da ina da kani je zan masa kamu dan nasan duk wanda ya dauke ki ya gama sa'ar mata, kuma ya gama sa'a a duniya sai dai yayi fatan gamawa lpy. dan kin hada komai da ake burin ssamu,"

"Anty kenan, Ai dan adam bai cika 10 ba, 9 yake, muna fatan dai Allah yasa mu gama lpy,"

"Ameen, amman ke kin fi 9 nan, wai wane saurayin ne, naji ya dace da kanwar tawa,"

"Anty! saurayi! Ai tukunna, kina mana addu'a dai Allah kawo nagari,"

"Insha Allahu zan na tayaku yi, sannan in nazo haihuwa ma bazan manta ba Insha Allahu, zan saka ki a addu'a,  kin san Allah na amsa addu'ar mara lapiya, ko wanda yake kan nakuda, da mai ciwon ciki, toh Insha Allahu zan roka miki, sai muyi ta fatan Allah ya amsa mana,"

"Ameen Antyna nagode,"

"Ba komai, ina kaunar ki Hafsat,"

Na dubeta nace, "Anty sauran wata nawa ki haihu ne,"

"Wata 3 ya rage,"
"Tog Allah sukeki lpy, Ameen,"

Itama Ameen din ta amsa da ita.

Dadare kuwa Ice cream dina kawai nasha nace na koshi, ai kam nasha fada gun Ya Muktar, dan cewa yayi sai naci abinci, sai da nayi kuka ya hakuri ya bar ni.

Sai karfe 8 na dawi gida, dakin mu na fada, akan kujera na kwanta, bacci ne ya dauke ni, cikin baccin na dinga jiyo hayaniya sama-sama.

Tashi nayi, muryar. abbi najiyo, tsaki nayi, dan shi da abin fada da bana fada ba yinsa yake,

Dan shi ko, magaba yake da hayaniya saka jiyi shi.

Daki na shige, kai na na sara min dan dududu baccin minti 20 ne ya dibeni, bandaki na shige dan bana son jin hayaniyar tashi.

Wanka nayi na sanya kayan bacci na, turare na fesa nayi falo, wayata na dauka, 

Ummu ce ta shigo da sallama,  na amsa. 

Gefe na ta zauna tafe, "ashe kin dawo,"
"Eh Ummu, na leka babban falo naga bakya can ne, Anty Bilki na gaishe ki,"
"Ina amsawa, Khadija bata dawo ba ko?"
"Eh,"

"Toh dan Allah je ki kirata kar Abbi ya fara fadan nasa,"

Tih nace, ina mai jin tausayin mahaifiyar mu.
Katon hijab na saka na fice can gidan Umma,

Sallama nayi, wacce ba kowane ya ji ba, Umma na gaisar, na juya na kalli Khadija, nace, "kizo,"

Na juya duk yan dakin kallo suka bini dashi bansan ko na mene ba. Tare muka shiga gidan.

Ummu tace, "Khadija wai meyesa bakya jine,"
"Ummu kiyi hkri," muka hada baki muka fada tace,"Toh Allah shirya min ku," muka Amsa da "Ameen."

Ummu tace, "jeki rufe gate da kofar tsakiya," ta amsa da toh.
Acan ma hira ta tsaya yi da saurayin ta Khalifa. Ummu kuwa dakin ta ta nufa.

Ina zaune har wajen minti 10.....





MS Indabawa
[11/20, 12:47 AM] Antty😍: MIJIN UMMU NAH
TRUE LIFE STORY

13

BY Maryam S Indabawa
MANS


Annabi (SAW) yace duk wanda ya haddace ayoyi guda 10 na farkon suratul khafi Allah zai kareshi daga fitinar dugal

Allah ya kare mu Ameen ya Allah



Wayata na dauka na kira ta amman abin haushi sai naji karar ta a gefena,

Mikewa nayi na nufi gate din, abakin kofa na tsaya na haske ta,  da fitilata, a firgece ta juyo, tai saurin rufe kofar.

Daki na shige sai gata ta shigo, na dubeta nace, "ke wai bakya gajiya da neman magana ne? Kin fi son ki ya jawo mana hayaniya da jawi mana bacin rai ko,"

"Yi hkri Anty na, zan rufe ne yaxo,"

Tsaki nayi na mik na shige daki,

Duk duniya daga Mahaifiyata Ummu, da Mahaifina Abbu (Allah masa Raham yasa Allah makomar sa)  sai Khadija da Khairat, sai kawayena Hauwa da Faiza su kaidai nake kaunar kamar me, ina son su, dan suma suna sona suna kaunata kuma zan iya yin komai dan samun farin cikin su.

Alwala nayo na shige bargo, wayata na dauka na kunna bakara, addu'a na karanto na lumshe idona ban san lokacin da bacci ya dauke ni ba,

Ita kuwa Khadija sai karfe 2 ta kwanta bayan ta gama kallo a System dina, da asuba na tashe ta mukai sallah.

Gado ta koma, falo na fita na kunna karatun alqurani, na mike akan kujera sai 6 sannan na gyara dakin mu da tsakar gida. na nufi kichen, dankali na kwasa na nufi bangaren su Baba Lami, Dije mai yiwa khairat wanki na bawa nace ta ferayen.
dan Jamila naga tana gyara harabar gidan mu, in ta gama kuma nasan wake wanke zata zo tayi mana. Baba lami ita kyma tana daura musu abin kari.

Ruwan tea na daura wanka yaji kayan kamshi, snn na daura farfesun kifi,  ina cikin yi sai ga Dije ta kawon, nan da nan na soya, na gama na shige daki nayi wanka, na waka uniform dina farare kar dasu kamar ba'a sasu, sun sha goga.

Bakin tea kadai na sha, na dauki takalmi na cover shoe ruwan hoda. na saka sai jaka ma ruwan hoda, wayat na dauka na kira Umma, gaida ta nayi, nace na shirya zan tafi makaranta,
"Da kudi a hannun ki," Ummu tace,
"A'ah zan biya na cira yanzu ko in an tashi, sannan yau za'a kafe mana result din mu,"

"Ok toh Allah bada sa'a, da nasara," nace, "Ameen,"

Daki na shiga na fesa turare har lokacin Khadija na aikin nata na bacci, na dade ina kallon yar Uwar tawa sannan na juya na fita.


A makaranta kuwa tin abakin gate muka hadu dasu Hauwa da Faiza, ai kam muka rumgume juna, notice board muka karasa dan duba sakamakon mu, Cikin ikon Allah Faiza ta shige ta dubo mana dukkan mu mun haye, "Alhamdulillah" muka hada baki muka furta tare da murmushi akan fuskokin mu.

Daga can Hall mukayi dan muna da lecture karfe 9, tinda malamin ya shiga sai karfe 12 ya fita, yana fita Malam Najib ya shigo.

Hauwa tace, "Sis kinga cingam dinki ya shigo fa,"
Hafsat tace, "ke rabu dashi,"

Ban dagi na kalle shi ba, dan nasan a hakan ma ni yake kalla,

Faiza tace, "Sis Allah Sir Najin karshe ne, duk Makarantar nan, amman bansan me yasa kike korar sa ba,"

Hafsat dai shiru tayi bata tankaba,
Faiza tacigaba, "Mutumin nan ga ilimi gashi dan gayu, ga Naira to me kuma zaki nema dan Allah, kina gannin yadda yan mata Ke son sa kamar me,"

Hafsat dai shiru tayi batace Ufan ba kuma bata dago kai ba,

Sir Najib ne ya farayi musu murnawadan da suka haye ya kuma kara ja musu kunne dasu dage su fita da sakamako mai kyau sannan, ya daura da musu lecture sai karfe 2. Ya gama musu,
Duk wani motsi na Hafsay akan idon sa take yi. Amman sam yaki dago kai bare yaga idanun ta yaji dadi.

Bayan ya fita suka fiti suka nufi masallaci Sallah sukayi sannan suka wuce cafeteria.

Kujera suka samu suka zauna,  Hafsat ta dubi Hauwa tace, "Sis yau jakata ba kudi, sai an tashima zan biya na cira dan haka ki samo mana abu mu taba mu wuce aji please,"

Faiza tace,  "ni dai Abinci zanci dan yunwa sai kace ban karya ba na fito,"

Hauwa tace., "Acici, Ni dai daga wacce bata cin Abinci, sai kuma mai ci sai kace gara,"

Dariya mukayi mu dukka,

Hauwa tace, "Sis keme zaki ci,"

Hafsat ta yamutsa fuska tace, "Ziza ma ta isheni,"

"Sis tazo muje,"  Hauwa ta fada tana kama hannun Faiza.

Bayan tafiyar su na dauki waya ta, Number Khadija na duba kamar yadda tai min saving da Kidney Sis, bugu daya ta dauka,
"Anty," Khadija ta kirata,

"Uhmm" kadai Hafsat tace,

"Kin je makaranta lpy, ya makarantar,"

"Lpy Alhamdulillah,"

"Inasu Anty Hauwa da Anty Faiza,"

"Sunje kawo mana abinci,"

"To ya akayi ne Anty?  Wallahi yau nayi kewar ki sosai,"

Murmushi nayi na lumshe ido na, nace, "Mie too Sis,"

"Anty," nace, "Na'am"
tare da bude ido na. Sir Najib na hango yayo cafeteria, ido na kawa, nace,
"Sis result ya fito, kuma dukkan mu mun haye,"
Wani ihu Khadija ta saka na murna, wanda yasa na dauke wayar daga kunnena, sai can naji ta fara magana,  wannan yasa na mayar da wayar kunnena, naji tana cewa,
"Anty Congratulation ina taya ki murna ku dawu Anty Faixa, Allah kara basira ya bada nassara, bari na fadawa Ummu, Ummu! Ummu! Ummu!, naji tana kwadawa Ummu kira murmushi nayi na sauke wayat na mayar jaka.

Sir Najib na gano yayo waje na, kai na sunkuyar daya daga cikin kujerun wajen ya samu ya zauna a kusa dani.

"Sir Ina yini,"
"Lpy Hafsat, ya kike ya karatu,"
"Alhamdulillah!" Na fada idona na kallon kasa,
"Wai meyasa bakya son kallona ne, ko tsoro nake baki ne,"
Kai kadai na kada alamar A'ah,
"To indai ba haka bane, dago ki kalleni,"
"Ayyqh Dan Allah Malam kayi hkri, ni wallahi bana iya kallon mutum haka,"
Murmushi yayi sannan yace, "au haba, ai kam ni sai kin kallen yau din nan,  in ba hakaba mu kwanan anan wajen,"

Ganin ina son ya tafi yasa, na dagi da kaina, karaf sai a cikin nashi, da sauri na kawar da kaina gefe.

Dariya yayi yace, "Wow idon ki yana da kyau sosai Hafsat,"
Shiru nayi ina wasa da yatsun hannuna, su Hauwa na hango na sauke ajiyar zuciya,

Magana yake amman ni duk hankalina na wajen su Hauwa, suka karaso da sallamar su, Sir Najin suka gaisar sannan suka zauna.

Faiza takeaway tayo, Hauwa kuma Lemo da Snacks ne, leda Hauwa ta ajiye a gabana, Sir Najib ne ya bude ledar, Nama ta siyon gassashe, sai Ziza Milk.

Murmushi yayi yace, "wannan namu ne kenan," Faiza tace,  "Eh,"

Budewa yayi, ya ajiye gaban mu, yace, "toh Bismillah mu fara ko,"
"A'ah Sir na koshi,"
"Haba dai daure muci man,"

Kai na girgixa nace "A'ah,"
Murmushi yayi yace, "in kunyata kike ji bari naje sai anjima, in an tashi ki jirani,"

Ya mike yayi gaba.

MS Indabawa
[11/20, 12:48 AM] Antty😍: MIJIN UMMUNAH
TRUE LIFE STORY

BY MARYAM S INDABAWA
MANS

Page 14


Deducated to SADNAF Ina son ki wit all ur book Allah kara basira da daukakka, Allah sa kifi haka. Dis page is for u and ur fans.



Yana mikewa, nace, "kunsan dai bazan iya cin abinci anan ba ko,"
"Haka ne," Hauwa ta fada.
Faiza tace, "sai ki bari mu gama mu ai ko,"
"Lah yanzu muka gama waya da Khadija tace in gaida ku," cewar Hauwa ta fada tana danna waya.
"Allah sarki My Khadija ta tana lpy, hutu dai ya kusa karewa,"
Hauwa tace, "Eh, dama ita ce Hafsat ma,"
Faiza tayi murmushi, "ke dai bari da munfi shan.....
"Haba! Ku kuna cin abincin ma surutu, haba dan Allah bakyau fa,"
Shiru suka, sai da suka gama sannan sukace, "munji munyi laifi muna cin abinci muna magana, tashi muje kici naki kar lokaci yayi,"

Ta mikie tana tsakiya Hauwa na gefen dama, Faiza ana hagun, duk wannda ya gansu sai sun birgeshi, kuma indai sun sanka sau sun gaisa damkai banda Hafsat, da abin ya zaman mata biyu, ga rashin son magana ga takuear d Sir Najib ke shirin yi mata.

Sai da mukaje aji, na samu naci na kora da maltina, sannan na dube su ina murmushi nace, "Nagode fa yan uwa,"
Hararata sukayi kawai, mukayo gaban ajin.

Karfe 4:05 muka fito daga dakin daukar karatu, masallaci muka nufa dan yi sallah, muna idar wa muka fito.

Sir Najib na hango zai shiga motar sa da sauri na janye su Hauwa mukai can bayan massallaci nace ina neman wata ne, sai da na bata mana minti wajen 20 sannan muka fito.

Hauwa anan Jan bulo take, Faiza kuma Zoo road. Drivern su Hauwa har yazo dan haka shi ya debe mu mukayo gida, Faiza muka fara saukewa sannan muka dau hanya, anan sharada nasa driver na tsata na ciri kudi sannan mukayi gida. A bakin gate suka direni, ina dafa mata hannu itama haka, duk kamar kar mu rabu.

HAUWA IBRAHIM
Shine sunan Hauwa mahaifinta commissioner ne, su Uku ne wajenn iyayen ta.
Hajiya Halima sunan Maman ta kawar Ummun muce tin daga firanare har yanzu sosai suke kawancen. Amman ni da Hauwa da sai dai mu gaisa in sun zi gidan mu, dan ni ban fiya zuwa gidan su ba, A Ckul of Nursing anan muka hade dan ganin mun san juna yasa muke tare ko yaushe. Wannan yasa muka zama kawaye.

Hauwa sa'a tace dan ma ta banu a kalla wata biyu, Farace tana da dan jiki kadan akwai hanci gata mai fara'a da surutu, akwai kokari.

Ya Jamil sunan yayanta yana malleshiya karatu yanzu haka sai kanwar ta sa'ar Khadijan mu, me suna Bushira itama wannan shekararr zatayu candy.





FAIZA YAHUZA
Faiza kuma mahaifin ta propesor ne a BUK da matar sa Hajiya Aisha, itama ma'aikaciyar ilimi ce malamar makarantar firamare, Su biyar ne, Anty Binta ce babba da ya'yan ta 3, sai Anty Wasila da ya'yan 2, Anty Nasiru dansa 1, sai ya Luknan dake can india yana kartu sai autar su Faiza.

Faiza itana fara ce, bata da iiba kamar ni take, tana da hanci kyakyauwace itama,  Faiza ma akwai dan bazan surutu,

A makaranta muna yawan zama kusa da juna, surutun ta da barkwanci yasa Hauwa janyi mana ita,

Zakuyi mamaki na ni da banda son hayaniya gashi ban da surutu amman yan uwana kamar sa saida ka dan surutu, ba komai yasa nake tre da su ba, sai Allah da ya hdamu muke son junan mu, sannan suna da hankalu ga nutsuwa ilimi duk ba baya ba,  sannn a duk lokacin da suka ganni a cikin wani halin rashin son magna su da kan su suke kyaleni nayi abin da nake so, Hauwa kan ce, "Wallahi mijin ki ya shiga uku ke kam, kawai kizo kiki magana kuma muna miki kina basar wa sai kace kinga hula akan mu, tabb wannan in hula kika gani yakenan?" Sai dai na harare ta kawai,
"Eh kya harareta man, ai zamu ganine nasan in wanda ya zama sarkin zuciyar tane ai bata masa haka ba, amman mu ta maidamu kamar me, Allah sarki mu,"
Nudai sai dai bayi murmushi kawai.

in kuwa suka ga raina ne a bace to sai sun san ydda suka ciren damuwata. Gaskiya ina son Hauwa da Faiza kamar yadda suma suke sona.



Cikin gida na shiga da sallama, Abbi na gani yana amsa waya a harabar gidan, dan kar in gaida shi yasa nayi cikin guda da sauri, kalli na yayi ya girgiza kai.

Ummu na sama a tsakar gida kan kujera nan na nufeta da fara'a ta na durkusa, dafa ni tayi, nace, "ina yini Ummu ya gida,"
"Lpy lou, Hafsat ya makarantar,"
"Lpy Alhamdulillah!"
"Naji sakamakon ku ya fito, kun haye Allah kra bda sa'a Allah yasa ku gama lpy, Allah bada miji na gari kuma,"
Nayi kasa da kai na amsa da "Ameen,"
Na mike na shige daki.

Khadija na kan kujera a kwance, ta mike ta zo ta rumgumeni, "sannu da zuwa, Anty nah,"
"Yauwah ya gidan,"
"Lpy, ya makaranta, ina taya murna,"
"Nagode,"
Na shige dakin baccin mu, hijab kadai na cire naji sallamr khairat ta dawo daga islamiyyah, murryar ta naji tana cewa, "Ummu taty ta dawo,"
"Eh yanzu ta dawo," da gudu ta fado dakin tana kwadan kira "Taty! Taty,"
"Na'am yar gidan Taty ya akayi," na fada ina fitowa daga dakin mu, sama na dagata nace,  "Oyoyo Swt baby na, ya makaranta,"
"Lpy, Taty ina chocolate dina,"
"Oh my Baby! Ki fa rage shan zaki, kinji ko," kai kadai ta daga min alamar toh.

"Muje daki na dauko miki to," tana gaba ina binta a baya, kan gadona ta haye tana jiran in dauko mata, cikin jaka na miko mata, tasa hannu biyu ta amsa tace,
"Jajakallahu bil kairan Taty,"
Ta fice a guje, ina dariya ita a lailai sai ta kwaikwayi yadda muke yin abu, Khairat kenan ina son ki.

Khadija ce ta shigo, ta shige bandaki ta hada min ruwan wanka, "Anty ga ruwan wankan ki can fa,"
"Toh Cwt Sis nagise fa," na shige nayo wanka na fito, mai na shafa kawau sai turare na zira doguwar riga nayo Falo.

Sallamar Sani najiyo a tsakar gida, suna gaisawa da Ummu,

MS INDABAWA
[11/20, 12:48 AM] Antty😍: MIJIN UMMU NAH
TRUE LIFE STORY

BY Maryam S Indabawa
MANS

Page 15

Dis page is ur Anty Yasmeen, love u soo much


Sani kanin Ya Kamal ne, dan gidan yar Ummu mu da ta riketa. bayan sun gaisa da Ummu ya shigo dakin mu, "Hajiya Hafsay em mata,"
"Ah Bro ya kake,"
"Lpy, Ya Makaranta?"
"Alhamdulillah,"

"Yaya Sani Oyoyo! Oyoyo!" Khadija ta fada tana fitowa daga cikin dakin mu,
"Oyoyo Sis nah, ashe kina ciki,"
"Wallahi ya kake ya gida yasu Umma?"
"Duk suna lafiya, ya hutu?"
"Hutu yzo gangara, in zubo maka abinci ne?"
"Eh, kamar kinsan yunwah nake ji kuwa,"

Ta mike ta fita, yadubeni yace, "Yau yan miskilancin ne kenan,"
Dagowa nayi na harareshi dayake kusn sa'a nane, dariya kawai yayi, yace, "wannan mijin ki ya shiga uku, ga rashin magana ga harara tab,"

Shiru nayi masa, yayi dariya, "wato na ci kaina....,"
Karar wayata ce ta katse shi, ina dubawa naga Hauwa ce, murmushi nayi na dauka, "Hafsat ya kin shiga gida lpy, yasu Ummu?"
"Wallahi lpy, yasu Ummi da Bishia?" "Lpy, kinsan me kuwa?"
"A'ah sai kin fada!"
"Ya Nura fa ya dawo,"
Nace, "Inye! Ayi masa sanni da zuwa kan mu hadu, kuma kice nice zan kunce jaka,"
"To shikenan an gama, bari naje na kintsa kar yazo ya ganni haka,"
"To a tahon da kayan dadi gobe,"
"Kice dai kayan sa ciwon ciki, dan sune kayan dadin ki kedai,"
"Eh naji,"
Na kashe wayar ina dariya.

Ya Nura, saurayin Hauwa Ne, kuma dan uwansu ne, shi zata aura dan har an bashi ita, muna gamawa za a saka rana.

Yanzu haka saura wata hudu mu fita asibiti daga makaranta, daga nan shikenan kuma sai jarabawar karshe mun gama.

Sani ne ya dubeni, "ke dawa haka kike ta magana ne,"
Nace, "hauwa ce,"
"Eh, ai nasan sai itan, wallahi yaran nan na hakuri da halin ki,"
"Su waye yaran, sannan kuma kada suyi hakurin ma man,"
Dau dai lokacin Khadija ta shigo da tire a hannun ta. Shinkafa da miyar kaji sai hadin salad, sai lemo da snacks a gefe.

can wajen magariba sai ga Ya Kamal ya shigo, shima yayan Sani ne daga Ya Muktar sai ya Kamal,

Ya Kamal shi keson Faiza kawata, dan shima har manya sunje akace sai ta gama karatun,
muna shiri da Ya Kamal sosai, dan shima yana daukar halaiyata, sannan duk abinda nake so shi yake min, shi ke iya xama dani na rashin magana dan sai yaxo mu bata awa daya bamuce kala ba, duk da in magana ce yana da surutu.

Gefena ya nufo, ya zauna, naace, "Sannu,"
Harara ya watso min, sannan yace, "Ciwo nake da zaki ce min Sannu,"
Baki na tabe, nace "dan nace Sannu,"
"Eh din,"

Mukai shiru, matsowa yayi, yace, "Ya ina mutuniyar,"
Kaina na dauke, dan ko kallo bai ishen ba, bare yasa ran zan bashi amsa.
"Haba Sweety nah, yi hakuri kinji, ya kama hannuna yana lallashi na."
Sani yace, "ai daman kai ke kara sangar tata, yanzu mene abin bata hakuri,"
Hararrar sa nayi, Sani yace, "ke dai sai idanun nan sun fadi zaki daina hararar mutane ko,"
"Kai Sani ba ruwan ka da ita," cewar Ya Kamal,
"Allah baku hakuri, Khadija zo, ya ina mutumin?"
"Ya Sani, yana nan wallahi,"
"Ok yana gari kenan,"
"Eh, yazo jiya,"
"Ok in zan tafi ma hadu," ta dau waya tace, "hello," cikin yanga da iyayi sai kace yana gaban ta, banji amsar sa ba, sai ji nayi tace,
"Oh My Khalifa, kayi hakuri, daman bro sani ke neman ka," tayi shiru da alama magana yake,
"Ok gamu nan toh,"
Ya kamo hannun Ya Sani, tace, "taso yana waje ma yana jiran mu," suka fice.

"Ya Kamal!" Na kira sunan sa cikin shagwaba,
"Ya akayi ne,"
"Dan Allah ka kaini nasha Ice cream mana in anyi magariba,"
"Ok,  toh ina mutuniyar,"
"Kai Ya Kamal,"
"Eh fadan,"
wayata na dauko, ya bini da ido, dan son sanin abinda zanyi, ni kam lambar faiza na nemo,  na kira, tana dagawa na kara a kunnen sa..
Ai kam da ihu ta dauki wayar tana cewa, "kinji Ya Nura ya dawo ko," "Baby nah," taji muryar Ya Kamal, ai tuni ta rage muraya, "Na'am Habibinah,"
"Ya kike ya makaranta,"
"Lpy Alhamdulillah,"
sai hirar soyayya ta balle, kalamai yake ta fada mata masu kwantar da hankali, tsaki na dan ja, na mike nayi cikin daki. Abin na bani mamaki kowa soyayya ji wai Khadijama soyayyar take, Allah ya kyauta.

Kwanciya ta nayi, kiran Sallah najiyo na mike nayi cikin bandaki, alwala na daura sannan na zo na tada Sallah, ko da na iddar ban mike ba ina zaine ina ta tasbihi, har akayi Sallah isha'i sannan nayi na fito falo.

Shima Ya Kamal sai da yaji Sallahar sukai sallama, massallaci ya tafi bai dawo ba sai isha'i, a falo ya tadda ni zaune da waya a hannu,
Ya dubeni yace, "Sis tashi muhe dan ina son zuwa wajen Antyn ki,"
mikewa nayi, na shige cikin daki, After dress na daura na fesa turare, dakin Ummu naje na fada mata zamu fita,
"Allah kiyaye hanya kuma kar ki dade," na amsa mata da "toh."
yaso yaje dani wajen Faiza naki, dole yana siyan abinda nake so ya maidoni gida ya wuce.

Satin Khadija uku suka koma makaranta, kuka sosai muka sha dan mun saba duk tafi sai munyi, kamar kar mu rabu da juna. Rayuwa kenan watarana ma duniyar za mu bari baki daya.

Harkar karatun mu sai cigaba take, tare da nasarori, Wani Farin jini ya kara futon, dan ko a makaranta daga Malamai har dalibai kowa sona yake, dan ma ina da kwarjini, basa iya tarata sai dai su Faiza, suma suna sharar fada min sai dai su bada hakuri.

Satin Khadija biyu da tafiua, nake cewa su Faiza zanje wajen ta, "Ai kam kisa mana rana muje mu gano ta,"
Hauwa tace, "ranar Laraba zamu tinda karfe 2 muke da lecture ranar,"
"Haka ne, Allah kaimu," cewar Faiza.

Ni kam ina gefe duk suka gama tsara yadda za'ayi, "musa kayan makaranta, sai musa After dress tinda daga can makaranta zamu biya ko," duk wannan bayanin na Faiza ne.

Ranar laraba tin karfe 10 Hauwa tazo da drivern su, Wata Bakar Abaya nasaka mai ruwan goran duwatsu, tamin kyau ainun, ruwan goran cover shoe nasaka tare da jakar su, Hauwa sai yaba kyan dani take, Gidan su Faiza mukaje, Momyn Faiza har da bada soyayyun kaji akai mata, sahad muka biya, na siyo mata ice cream da chocalate dan Hauwa tayo mata miya, da snacks, Faiza kuma ta jidi mata biskit da lemo ka, sosai naji dadi nayi musu godiya.

Karfe 11:30 muka isa, har ciki mukaje sannan muka nufi offishin vice, karbar hannu biyu akai mana, daga karshe aka kira mana Khadija,  hall din da ake ganin dalibai mukaje jiran ta, tana gano mu ta kwasi a guje, ta rumgumeni tana murna, ta sake ni tayi wajen Hauwa dagan Faiza, hira muka taba dan sai Karfe 1 muka baro ta da kewar juna, tana ta godiya har da hawayen ta.

Rayuwa muke me ciki da kaunar juna da taimakon junan mu, ina son su Hauwa dan ko ya suka gannin ba dai dai ba zaki yadda zasu na nan nan dani.

Watan Khadija biyu, akayo waya gida bata da lafiya, Ummu da kanta taje dauko ta,  tana dawiwa ta leka gidan Umma dan dubata ance itama bata da lafiya, lokacin ina Makaranta.

Dawowata kenan na tadda Ogan gidan namu wato MIJIN UMMU NAH, yana ta fada kamar zai ari baki, kuma ba akan komai bane sai akan Khadija tashiga gidan Umma, "Ke ahakan ne baki da lafiya, kinsa an dauko ki, zaki fara yawo nifa bazan dauki wannan abun ba."

Daki kawai na shige abuna, sai ga Khadija ta shigo tana hawaye,
"Ke dan me to kika fita,"
"Gaaida Umma fa naje yi,"
"Ciwon karya dai kike yi, duk kin tda mana hankali baki da lafiya ko, in ba haka ba ai ita ya kamata tazo ta gaidaki,"

na mike nayi cikin daki, halin Abbi, Mijin ummu nah na damu na bazu tab yin magan a hankaki ba sai cikin karaji da daga murya, kai Allah ya ban miji mai tausasa kalaman sa akb iyalan sa, bance kada a tsawatar ba dan nasan dole a dora mu akan hanya to amman ai akwai yadda ya kamata ya yi fadn nashi, kuma nasan yanzu haushi yake ji dan Ummu zata siya mata magani, shi bai son abinda Ummu zata taba kudin ta, sai dai shi yai ta cemata kaza yakeso kuma ta bashi sai kace nauyin sa akan ta yake, mu da nauyin namu ma ke akan ta baya son tai mana amman shi yake daura mata nasa, kai Allah kawo karshen wannan alamuran na mijin Ummu nah."




MS INDABAWA

Continue Reading

You'll Also Like

1K 99 30
i don't know if u know that i like u but here are my secret confessions that i often hide to not embarrass myself cause i'm too embarrassed to admit ...
581K 13K 40
In wich a one night stand turns out to be a lot more than that.
50.3K 1.4K 24
U all know nobody need to be alone without parent. This is a story of a girl called nafeesat which lost her parent,she became house girl,at the house...
29.4K 864 23
Labarin Yarinyar da ta tashi a tsakanin yayyenta maza, da suke shirye da aikata ko menene saboda ita, ba ta san tsoro ba, rashin ji ya kaita ga haɗuw...